Showing 3001 words to 6000 words out of 44320 words

Chapter 2 - In Da Rai Book 2 HAUSA NOVEL

HUGUMA   

26 Jan 2025

8684

Ishmah tace.
“Uncle Bello yazo Yah Muhammad waye Uncle Bello ya haɗani dashi”.
Ta ida maganar hawaye na tsatstsafo wa cikin ƙwayar idanunta..
Kai yah Muhammad ya girgiza mata dai-dai lokacin kuma suka jiyo sallamar Abba da kansa Abba na shigowa fuskarsa ɗauke da Murmushi mai nuni da maɗaukakin farin, ciki sauri Aunty Maryam da Aunty Nana suka koma gefe ganin Surukinsu...

Kallon ƙannen Matarsa yayi tare da cewa.
“Hauwa".
Cikin sanyi tace.
“Na'am Ya Abdullahi”.
Fuskarsa ɗauke da maɗaukakin farin ciki yace.
“Alhamdulillah yau dai Allah ya ƙadarta ɗiyarki ta zama matar Aure an ɗaura Auren A'isha Mamana yau itama ta kasance cikin Inuwar Aure”.
Cikin matsanancin farin ciki Aunty Hauwa ta juya tayi Sujudur Shukur Garkuwa kuwa komawa tayi ta jingina da jikin kushin fuskarta ɗauke da wani irin murmushi mai nuni da zallan farin ciki take faɗin.
“Alhamdulillahi³”
Ishmah kuwa cikin wani irin yanayi da yafi kama da tsoro gami da al'ajabi take kallonsu.

Abba kuwa har zuwa lokacin fuskarsa ɗauke da Murmushi ya ƙaraso cikin Falon ɗan risinawa kan Ishmah yayi kana yace.
“Mamana taso”.
Ya ƙare maganar cikin farin ciki.
Ita kuwa Ishmah jiki na tauna da wani irin sanyi dake saƙƙo mata ta yunƙura sai kuma ta gaza tashi.
Ganin haka yasa Garkuwa ta tallafeta ta tashi tsaye.
Hannunta ya riƙe kana suka juya suka fita.

Sai alokacin Aunty Hauwa ta ɗago daga Sujudur Shukur sai kuma ta kalli Aunty Amina dake cewa.
“Yah Ali baka faɗa mana waye mijinba”.
Murmushi yayi tare da cewa.
“Ɗanku zai faɗa muku”.
Ya ƙare maganar yana fita daga Falon.

Ishmah kam cikin sanyin jiki take biye dashi kai tsaye taga ya nufi BQ.

Ahankali ya tura ƙofar ya shiga idanunta ne suka sauƙa akan Taj dake zaune atsakiyar Falon ya jingina kansa da jikin kujera kana idanunsa alumshe ya fuskanci Alƙibla kasancewar ƙofar falon tana fuskantar alƙibla.
Ganinsa ne yasa ta buɗe idanunta cike da tsananin mamaki lokaci ɗaya taji wani irin sanyi ya sake sako mata tun daga kan maɗigar ƙafarta har zuwa tafin ƙafarta.
Abba kuwa hannunta ya cigaba daja har suka shiga tsakiyar falon gaban Taj.
Ishmah kuwa zuciyarta ne ya buga da wani irin masifeffen ƙarfi bawai ganin Taj bane ya bata tsoroba ramar data ga yayi ne yayi masifar bata mamaki da kuma yanayin data ganshi cikin hargitsi da tashin hankali shine yayi matuƙar tayar mata da hankali tare da gigita mata lissafi cikin rawan baki da rawan murya tace.
“Tajjjjj”.
Maganar ya fito ne daga can ƙasan zuciyarta wanda ya maƙale asaman Lips ɗin ta.

Taj kuwa sai alokacin ya samu damar ɗago kansa duk da cewa ya amsa sallamar su amma bai ɗago kansa ba saboda yanda yake jin kansa ya masa nauyi arayuwarsa yana tuna abubuwa da dama daga cikin abubuwan da suka yiwa rayuwarsa rubdugu a cikin kwanakin nan, daga cikin abinda suka fi Daga masa hankali shin taya Ishmah zata karɓi sabon lamarin nan da baƙon alaƙar aure da yasa aka kulla musu ba tare da izinin ta ko saninta ba.
Hankali ya ɗago kansa ya ganta da Abba cikin sanhi ya yunƙura.
Abba ne yafara girgizasa masa kai tare da faɗin.
“Koma ka zauna”.
Ba musu ya koma ya zauna Abba kuwa akan 3sitter dake fuskantar Taj ya zauna kana yaja hannun Ishmah ta zauna a ƙasa ya zamana duk suna gabansa.
Ahankali ya riƙo hannun Taj ya buɗe kana ya riƙo hannun Ishmah ya ɗaura akan nasa sai kuma ya saki nannauyan ajiyar zuciya haka nan yake jin kansa cikin wani farin ciki mai daɗi yau ya sauƙe abu mafi nauyi dake damunsa acikin zuciyarsa, yau Auren Ishmah shine abu mafi daɗi arayuwarsa sama da shekaru goma baiji abinda yasa shi farin ciki ba kamar wannan.
A lokaci ɗaya Taj da Ishmah suka saki wani nannauyan ajiyar zuciya asanda hannunsu ya haɗu...

Cikin girma da Dattako da sanin Yakamata Abba yace.
“Tajuddeen ga Matarka”.
Jin wannan kalmar yasa Taj ƙara sauƙe nannauyan ajiyar zuciya kana ya sake Runtse hannun Ishmah dake cikin nasa.

Ishmah kuwa jin kalmar da Abba ya faɗane yasa zuciyarta ya buga da masifan ƙarfi, wanda hakan yasa ta Runtse idanunta da tsananin ƙarfi.
Sai kuma ta buɗe jin Abba yace.
“Aisha”.
Sunan da baya kiranta dashi sai da babban dalili ahankali take ƙoƙarin buɗe idanunta amma sunyi mata nauyi saboda kalmar da taji ya daketa sai kuma ta sake ƙoƙarin buɗe idanunta jin ya kirata a karo na biyu nan ma still idanun nauyi suka mata da ƙarfi ta buɗe idanun jin Abba ya sake kiranta a karo na uku.

Tana buɗe idanunta yace.
“Mun daɗe muna barwa Allah zaɓi akan lamarin aurenki bana bacci acikin kaso ɗayan ukun ko wanne dare arayuwata A'isha acikin shekaru bakwai ɗin nan addu'a nake ina faɗawa Allah ya Miki zaɓi da miji mafi Alkhairi, wanda zai riƙe ki da amana da gaskiya. Nayi ta shan ƙunci arayuwata a lokuta da dama idan al'amarin aurenki ya ɓaci amma nakan miƙa lamurana ga Ubangiji na kan yarda da cewa lallai suɗin ba mazanki bane da Ubangiji ya hukunta, da su mazan kine A'isha da dole sai anyi Auren”.
Sai kuma ya sauƙe nannauyan ajiyar zuciya mai cike da farin ciki kana ya cigaba da cewa.
“Allah ya amsa mana a lokacin daba muyi zatoba bamunyi tsammani ba Allah ya sauƙaƙa mana abinda yayi tsanani. Alokaci ɗaya Allah ya bamu abinda muka rasa tsawon shekaru wanda hakan ya tabbatar min da cewa Taj shine mafi. Alkhairin da mukayi ta roƙa miki ni da majaifiyarku atsawon shekaru bakwai zuwa takwas da kikayi ba aure, haka ya nuna min cewa Taj shine mafi Alkhairin da Mahaifiyar ki tayi ta roƙa Miki har lokacin da zata bar duniya.
A'isha a yanzu Tajuddeen ya tashi a matsayin abokin mutuncinki ko matsayin abokin sanayya Tajuddeen mijine agareki wanda aljannarki take ƙarƙashin diga-diginsa. Yau an daura aurenki da Tajuddeen a masallaci Lamiɗo ya samu shaidun dubban Al'ummar Annabi musulmai manya da yara sun shaida aurenki da Tajuddeen, kuma inaji a jikina in sha Allah zai share miki hawayen da maza da kika aura a baya sukayi ta ƙunsa miki kamar yadda aurensa ya share mana ƙuncin tarin masu neman airenki sai komai ya kankama su kuma ce sun fasa”.
Ba Ishmah kaɗai ba hatta Tajuddeen wani irin bugun zuciya mai sarƙafe da tunani ke fusgarsa.
Abba kuwa cikin kamala ya cigaba da faɗin.
“Tajuddeen mijine agareki, wanda kuma yasan komai a kanki, kuma yanzu mijinki ne wanda Aljannarki take karkashin ƙafarsa, kuma mijine da in kin mishi biyayya zanyi farin ciki dake, kana mijine da in kika zauna tare dashi zanyi alfahari dake, nayi Miki wannan zaɓin batare da neman izinin kiba duk da kasancewarki bazawara wacce shariya tace a baku dama kuyiwa kanku zaɓi, kiyi haƙuri ki yafe min da rashin baki wannan damar.
Ban zaɓa miki shi domin na gaji dake ko bana sonkiba a'a sai domin ina ji ajikina wannan shine zaɓin da Allah ya Miki A'isha.
Bani ne nayi Miki zaɓi ba Allah ne ya miki zaɓin. Ni dai Fatana zaki min ɗa'a kiyiwa mijinki ki biyayya ki zauna lfy dashi, ki maida yan uwansa naku, iyayensa naki”.
Tuni hawaye ke kwaranya a idanunta kwata-kwata bata cika fahimtar duniyar da takeba sai kalaman Abba da duk suke zama a kanta tamkar hadda suna ratsa ma'adanin ƙwaƙwalwarta tana jin yanda suke ratsa dodon kunnenta suna bugun zuciyarta. yanayin da taga Taj aciki shi yafi ɗaga mata hankali.
Ahankali ta buɗe idanunta da suke jiƙe da hawaye ta tsakan kanin gashin idonta take kallon ƙafarsa dake gefenta wanda ke kumbure sai sheƙi yake inda Kwalba ya yankesa kafin ya fito gida.
Abba kuwa kallonsa ya mayar kan Taj tare da faɗin.
”Taj na mallaka maka Mamana da yaƙinin zaka riƙe min amanarta da yarda cewa abinda ka faɗa gaskiya ne na mallaka maka Mamana da yaƙinin kai mutum ne nagartacce dan haka ga Mamana amana ce na baka”.
Kai kawai Taj yake gyaɗa mishi domin baya jin zai iya mgna Abba ya bashi kyauta Mafi daraja da gode mishi yayi kaɗan saidai addu'a da kyautatawa ɗiyarsa..
Cikin jin daɗi Abba yace.
“Allah ya muku albarka”.
Da kyar ya iya motsa lips inshi yace.
“Ameen”.
Abba kam miƙewa yayi ya fita yana mai sa musu albarka tare da jan ƙofar ya rufe.


A hankali ya kalli gefen damanta inda wayarta ke zaune jin tana ringing.
Bappa Kawu. Ya faɗa a ransa a fili kuma ɗaukar wayar yayi tare da amsa kiran tare da yin sallama

Cikin sanyi Bappa Kawu yace.
“Taj ko?”.
Cikin sanyi yace.
“A'a Mijin Ma'eesha ne!”.
Sassayan numfashi Bappa Kawu ya fesar tare da cewa.
“Uhmmm kace mai sa'a kenan da yayi ta buge soyayyarmu.
Mai hasken taurari da yayi nasarar samun mallakar Ishmah.”
Cikin ɗan jin sassaucin kishi yace.
“Dama ai kune kukayi tayi min kutse a muhallina”.
Ya ƙare maganar yana kallon Ishmah ta gefen idonshi.
Ita kuwa Ishmah gefen lip inta na ƙasa take ta tsotsa.
“Yanzu dai ai bamu da bakin mgn tunda kayi nasara akan mu, dama na kirane inyi mata fatan alkhairi da sallama da neman gafarar ta Amman fa in ka amince”.
Yana ɗan sauƙe numfashi yace.
“Na amince duk da dai nasan yanzu kai tunanin neman amincewata”.
Cikin sanyi ya manna mata wayar a kunnenta lumshe idanunta tayi jin Muryar Bappa Kawu na cewa.
“Aisha na kasance ɗaya daga cikin waɗanda suka shaida ɗaurin aurenki keda Tajuddeen miji ma ɗaukaki, ina mai tayaki farin ciki domin Allah yayi Miki zabi da mijin da yafimu duk manemanki da komai haƙurin da kikeyi duk sanda aurenki ya watse kike maida komai ga Allah har aci gaba da yin zumunci da iyayenki Kinga Allah yayi Miki kekkyawan sakamako da miji na kerewa sa'a, inayi Miki fatan alkhairi. Allah ya baki zaman lfy da zuriya ɗaiyiba, kiyiwa mijinki biyayya kiyi kuma haƙurin zama gidan miji, ni kuma ki yafe min akan yadda mgnar aurenmu keta zama kamar yaudara.”
Tunda ya fara mgnar hawayenta suka fara kwaranya cikin sanyi tace.
“A'a ni bakayi min komaiba Mukhtar ba yaudara bace kawai dama can Allah bai ƙaddara kasancewarmu ma'aurata ba ne. Na yafe maka nima ka yafe min a zaman da mukayi.”
Murya na rawa yace.
“Na yafe miki A'ishah kuma zanci gaba da zumunci da Abba”.
Daga nan ya katse kiran saboda hawayen dake zubo mishi.

Shi kuwa Taj ajiye wayar yayi a gefentan tare da lumshe idanunsa kana a hankali ya m....



Littafin INDA RAI na kiɗine. Ki biya ki karanta ki rabu da haƙƙin wani a kanki 1k ne 0661110170 GTBank Aisha Aliyu Garkuwa sai ki turo min shaidar biyanki ta wannan number 09097853276. Mutanen kasar Niger kuma 1000fc jaka ɗaya kenan rak zaku biya ta wurin Mommy +22790899076.




By
*GARKUWAR MARUBUTA*
[4/30, 10:43 PM] +234 706 616 8286: 📝🕋💉🍇🍇🍇🍇🍇🍇

*INDA RAI*

*BOOK 2 PAGE 2*

*AYASHA ALIYU GARKUWA*






To Kufa matson ayi gyara saboda sauyawar weather kun san cewa, muna buƙatar gyara, dan kauda busher da jiki yake yi a samu damshi da ni'ima da ɗumin jiki.
Kayane gasu nan kala-kala ko wanne irin haɗi kikeso akwaishi carans. Haɗin amarya budurwa mai ƙarancin shekaru da mai matsakaicin shekaru da kuma mai ɗan yawan shekaru. Kana haɗin amarya bazawarar da take da ragowar ƙuruciya, da mai matsakaicin shekaru da wacce shekaru sun ɗan ja, hadi dai-dai da halittarki ƴar uwata, ƙawata, ƙanwata, ƴata, ƴaƴata, kai harma da ke kakata, akwaisu masu maida tsohuwa yarinya, duk mutuwa da sakewar fatar nan zata tattare ta tsuke ta matse ta rayu da ni'imtaccen yayyafin gyaran zaman aure.
To wai ke mai jego ina kike akwaisu fa naku haɗin, in ma yawan haihuwa yasa wurin ya sake ya kuma ƙafe, barden goyo ko ɗanyen goyo, akwai haɗinku.
Zaki min bayanin me matsalarki!
Sakewa ne? Rashin ni'ima ne? Rashin feeling ne, ko rashin kuzari ne.
Duk fa akwai haɗinshi sai in Miki haɗinki dai-dai aljihunki
Bana barin kuɗin Customers na suzo su koma duk ƙanƙantarsu ko yawansu saboda set ɗin kayansu hawa-haeane.
Akwai manyan set akwai kuma ƙananan. Ƙananan set ɗin daga 40k ne zuwa ƙasa 35k 30k 25k 20k 15k 13k 10k sai ɗan autansu ɗan robor ƙasaitacciyar macen 5k akwai abu kusan kala biyar a ciki. Sai kuma manyan set ɗin daga 50k ne zuwa sama 60k 70k 80k 90k sai sha kunɗum uban aikin 100k. In kin shirya yar uwa kawai bulbulo min kuɗi in bulbula Miki kaya 0005388578 Jaiz back Aysha Aliyu Garkuwa sai ki turo min shaidar biyanki ta wannan number 08069423567. Gareku mutanen Niger kuma ina ita tura muku kaya, in kina da mai amsa Miki shi a Kano ko Sokoto.


Spjdd.
Matse hannunta dake cikin nasa yayi, tare da rumtse idanunsa da ƙarfi.
Itama rumtse idanunta tayi cike da bugun zuciya kusan a tare suka ja numfashi mai kama da ajiyar zuciya ba tare da sun sauƙe numfashinba.


Acan cikin gida kuwa baki ɗaya shiru sukayi a falon suna jin recording ɗin kalaman Taj da ya riƙa faɗa a Falon Abba kafin su tafi masallaci wanda Yah Abubakar da bai daɗe da shiga ba ya saka musu.
Garkuwa kam Murmushi take tana gyaɗa kanta.

Bayan sun gama saurara Yah Abubakar ya kashe kana ya maida wayarsa cikin aljihu tare da cewa.
“Alhamdulillah, dama bahaushe yace wani jinkiri Alkhairi ne hakan ya zamewa Ishmah baiwa ta samu Mijin nunawa Sa'a ”.
Murmushi Garkuwa tayi cikin matsanancin farin ciki da kasantuwar abin tace.
“Abinda nake faɗa da fata ya zama gaskiya ko kuma ince abinda muke faɗa ai tuntuni na daɗe da gane cewa Sheikh Afif son Ishmah yakeyi amma taƙi yarda shi kuma zurfin ciki ya hana shi bayyanawa saboda iya abinda na fahimta da Ishmah ita batama fahimta ba, shi kuma zurfin ciki ya hana shi ya fito fili yayi bayani.
Amma tuni ni nasan wannan amintaka tasu tafi ƙarfin abota ko amintaka sai ko so, sai dai soyayya mai ƙarfi”.
Da sauri Aunty Hauwa tace.
“Abinda nima kullum nake faɗa wa Ishmah amma ta gaza fahimta ta kasa ganewa bare ta yarda”.
Cikin dariya sosai harda riƙe ciki Aunty Nana tace.
“Habawa bawan Allah yaji soyayyarta zai kashe sa acikin zuciyarsa, itama taƙi fahimta ita sam bata ma gane ba yaga in yaci gaba da ajiyewa soyayyarta zata fasa masa zuciya ta kashe shi.
Gashi tasa yazo ya fallasa sirrin zuciyarsa agaban su Abba”.
Dariya suka sanya tare da juyawa suna kallon Aunty Maryam dake cewa.
“Tana ƙasa tana dabo, ai ni dama tun randa muka haɗu dashi a Mall ɗin Abaya a Saudi naga harda su bata niƙab daga baya ya ƙara da bata Safar hannu nace, wannan fa sonta yake, Amman a lokacin naƙi yarda da maganar zuciyata dan ina tsoron kar akasa min Yayana Barrister Kamal gashi kuwa bamu tsiraba”.
Sai kuma ta maƙawa Rahma harara jin tana cewa.
“Mu kuma kikayi mana wuff da Yah Abubakar ɗinmu ba”.
Dariya duk suka saka cike da raha.
Cikin gyara zama Garkuwa tace.
“Aikam da gaskiyar Taj in ba haka ba sai amasa sakiyar da Babu ruwa”.
Murmushi Yah Muhammad yayi still idanunsa na zubda hawaye cike da farin ciki yace.
“Wallahi ya mance cewa agaban Abba yake ya mance cewa agaban mutane masu tarin shekaru yake baki ɗaya ya mance inda yake, kawai zubo kalamai yake akan Ishmah tamkar ruwa na zubowa daga sararin samaniya”.
Murmushi Yah Abubakar yayi yana tuna yanda Taj ke magana da duka gaskiyarsa.
Yah Muhammad kam cikin jin daɗi ya cigaba da cewa.
“Kawai faɗin abinda yake ji acikin zuciyarsa yake na fahimci idan ba abarshi ya faɗi wa'anan kalaman ba zuciyarsa zata iya bugawa ta fashe, Shiyasa Abba ya kasa cewa komai sai murmushi yake yana kallon yanda yake maganganu kamar wahayin maganar ake masa”.
Murmushi Rahama tayi cikin jin daɗi tace.
“Kai Alhamdulillah yau burin Daddy ya cika bayan ranta”.
Baki ɗaya suka haɗa baki wajen cewa Allah ya jikanta da rahma Allah yasa ta huta...

Anutse Garkuwa ta kalli Rahama tare da cewa.
“Yanzu me zakiyi Rahama?”.
Kai Rahama ta girgiza kana tace.
“Ba abinda zanyi Aunty Garkuwa ni na rasa mai ma zanyi arayuwata farin ciki kawai nake ji”.
Garkuwa kuwa kallonta ta mayar kan Adam tace.
“Yawwa Adam ka Kaita gidana zan kira Paulina akwai sakon da zata baku ku kawo min da sauri ina jiranku”.
Kai Rahama ta gyada tare da faɗin.
“Toh”.
Batare data miƙe ba.
Cikin sauri Garkuwa tace.
“Sauri fa nake dashi abu yazo mana abaxata a ƙurarren lokaci ba dole muma mu fara gyara da gaggawa da rawan jiki”.
Murmushi Aunty Hauwa tayi tare da faɗin.
“Allah dai ya miki albarka Garkuwa Ubangiji Allah ya biya ki ina son wannan al'amari ya kasance, kina samun ladan gyara zamantakewar ma'aurata ke Rahama maza tashi”.
Mikewa Rahama tayi Adam kuwa kallonta yayi yace.
“Toh kizo mu tafi”.
Kai ta gyaɗa kana tabi bayansa suka shiga motarsa yaja suka tafi.

Garkuwa kam suna fita ta janyo wayarta ta ta kira Ikraam tare da faɗa mata ta gayawa mai akinta Paulina tashiga dakin kaya ta lissafa mata wasu abubuwa na Musamman da take buƙata ta bawa rahama ta kawo.

Kafin Rahama su isa tuni Paulina ta gana haɗa kayan har ta kawowa Ikraam ɗin.
bayan Rahama ta shiga sun gaisa Ikraam ta miƙa mata ledar tare da cewa.
“Momyna tace idan kun zo in baku dama gashi an haɗa tun kafin kuzo”.
Karɓa Rahama tayi kana tace.
“Toh mungode”.
Sai kuma suka juya suka fita suna fita madadin Adam yabi hanyar gida sai taga ya ɗauki hanyar gidan Hajja Umma ɗan ware idanunta tayi tare da cewa.
“Yah Adam ina zamuje”.
Yana murmushi yace.
“Wannan abin farin ciki Ni nake so inje in yiwa Hajia albishir duk da nasan cewa Uncle Naseer da Uncle Ali nacan dasu aka ɗaura Auren amma sauri nake kada su rigani isa wajen suyi mata albishir”.
Kai ta gyada tare da faɗin.
„Toh shikenan ”.
Koda suka isa suka faɗawa Hajja Umma farin ciki ya rufe ta atake hawaye ya shiga bin kuncinta still tana murmushi kasancewar abu biyu ne ya haɗu mata Auren Jikarta da kuma tuno ɗiyarta da Allah bai nuna mata wannan auren ba da take ta fata da burin ganinsa basu daɗe anan ba suka fito suka dawo...

Acan gida kuwa kusan baki ɗaya ƴan Uwa sun hallara wannan yakira wancan lokaci ɗaya suka taru Al'amarin auren Ishmah yazo abazata anata addu'ar Allah ya bayyana mata mijin Aure na Alkhairi sai Allah ya saƙƙo musu da abin alokacin da basu zata ba basu tsammata ba abin yazo musu abazata Akuma ƙanƙanin lokaci Yah Muhammad da har zuwa yanzu bai tashi gaban Aunty Hauwa bane ya juya ya

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login