Showing 30001 words to 33000 words out of 44320 words
rage muku, ku zaku fara jarrabawa, kada kusa damuwar haka a ranku! In sha Allah komai zai dai-dai”.
Haka dai yayi ta kwantar musu da hankalinsu.
Qatar a hankali ta ɗanyi miƙa saboda baccin da ya fara surarta, na yadda ta lumshe idanunta tana jin sautin muryarsa na ratsa kunnuwanta na kusan tsawon 28 mutane.
Sai kuma dukkan kalaman Addawa da Garkuwa suka fara dawo mata.
A hankali ta miƙe zaune, tare da zura sawunta ƙasa kusa dashi.
Buɗe idanunsa dake cike da gajiya, bacci, damuwa, da hawayen ƙuncin zuciya.
Dai-dai lokacin kuma ta zame ta zauna kusa dashi, har kafadarta na ɗan taɓa kafaɗarsa, ɗan gajeren hamma tayi tare da yin mgna a hankali.
“Please Taj kayi bacci, ka bar karatun nan haka ga idanunka fa suna cike da bacci”.
A hankali ya ɗan miƙe tsawunshi tare da sa hannunsa ya jawota jikinsa kan cinyarsa ya ɗaura kanta zuwa kafaɗunta.
Sai kuma yasa hannunsa na dama yana shafa rabin sumar kanta da hular ya zame, a hankali yaci gaba da karatun domin so yake ya kai ƙarshen Suratul Yaseen. Alamun saura masa izufi 15 ya sauƙe Qura'an ɗin a kwanaki uku da ya faro daga Baqara.
Numfashi mai sanyi ya fesar lokacin da ya dire ayar ƙarshen surar.
Iska mai sanyi ya ɗan hura mata cikin kunnenta jin tana mgna ƙasa-ƙasa.
“Kiyi bacci kada kanki yayi ciwo”.
Yayi mgnar yana shaƙan sassayan ƙamshin kullaccar sirri da shu'umar humra dake cikinta, wanda yasashi lumshe idansa.
A hankali ta juya ta ɗan mirgina kanshi tare fuskantarsa, sai kuma ta ƙara lafewa jikinsa murya a tusashe tace.
“In dai bakayi bacci ba. Nima bazanyi baccinba”.
Ta faɗa cikin narkekkiyar murya da tasashi ƙara sunkuyowa a kanta bisa kafaɗarta ya ɗan kife kansa tare da sakin nannauyan numfashi.
Ita kuwa Ishmah cikin sanyi ta gyara kwanciyarta a jikin nasa, tare da sa hannunta ɗaya bisa cinyoyin nasa tayi pillow dashi ɗaya hannun kuma a hankali ta ɗan yi sama dashi kaɗan kan kan ƙeyarsa ta kife tafin hannunta sai kuma ta ɗan zora babbar yatsarsa cikin kwarmin ƙeyarsa inda wani irin tattausan gashi mai sulɓi dake kwance lip-pli a wurin a hankali ta ɗan murza yatsar.
Wani irin lumshe idanunsa yayi tare da fesar da sassayan numfashi.
Mutsu-mutsun da sukeyi ne, yasa tattausar jallabiyarsa fara tattarawa kasancewarta mai tsulɓi
Gyara zamansa yayi ya ɗaura ƙafarsa ɗaya bisa ɗaya, hakan yasa tayi tudu sosai tudun da ya bashi damar gyara kifa ƙirjinsa da kansa bisa kafaɗarta ya cusa kansa tsakanin wuyanta da kanta, tare da manna hancinsa dai-dai ƙasan kunnenta da yake zuba ƙamshi kulaccar sirri cikin sanyin murya da kamar raɗa-raɗa ya fara karanto suratul Mulk dan ɗabbagar sunan da ɗibi'arsa na karantarta surar duk daren duniya, domin itama surace maiyin ceto ranar gobe kiyama.
A hankali take shaƙan ƙamshi turarensa tare da da gyara hannunta na hagu kan cinyarsa ta tallabe fuskantar ɗaya hannun kuma tana murza ƙeyarsa a hankali wanda tuni hakan yana sako mishi wani irin amintaccen sanyin da lunshin ido.
A hankali ta lumshe idanunta, yayinda shima ya lunshe idanunsa tare daci gaba da karatun yana mai jin ɗumin jikinta da ƙamshimta suna fizgo mayataccen baccin dake damunsa.
Cikin 6 minutes bacci yayi awon gaba dasu, wanda zuwa lokacin tuni ƙarfe biyu ta gota.
Ƙarfe biyar dai-dai ya fara buɗe ifanunsa a hankali, tare dayin addu'ar tashi daga bacci,
da sauri ya sake rufe idanunta saboda ganin yadda ta jawo jallabiyarsa ta tattareta ta yi filon gefen fuskantar dashi, a hankali yake sauƙe numfashi dake nunin da ya samu sassaucin azabar rashin baccin, dai-dai lokacin kuma ta buɗe idanunta tare da yunƙurawa alamun zata taso, still tana riƙe da jallabiyar tasa wanda hakan yasa gaba ɗaya cinyoyinsa bayyana a fili zura idanunta tayi bisa tattausar farar tatarsa da gargasa ke kwance lip-pli a kanta tamkar anayi masu bayin ruwa, so take ta lunshe idanunta Amman ta gaza, saboda kyaun surar cinyarsa.
Shi kuwa Taj cikin sanyi yace.
“Yah Salam Babey mun makara fa”.
Ya ƙare maganar da sa hannunsa ya tattaro gashin ta ya meda mata shi gefen wuyanta, wanda hakan ya bawa fatar wuyanta dama bayya, kusan a tare suka Lumshe idansu lokacin dayayi kissing ɗin wuyanta.
Jan numfashi tayi tare da miƙewa zaune, ta haɗe sawunta tare da kife kanta bisa guiwowinta.
Shi kuwa Taj a hankali ya miƙe tare da nufar Bathroom, wanka yayi kamar yadda ya saba kana yayi al'walan, yana fita itama ta shiga.
Yadda yayin haka tayi, tana fitowa ya miƙe ya nufi Parlour tare da cewa.
“In kin gama kizo muyi jam'i muyi salla ko!”.
To tace tare da nufar drower.
Wani kayan ta jawo riga da wondo ne, sai dai rigar chort sleeve shirt ce, fara ƙal mai ɗan wuya, sai wondon kuma brawn collar ne mai ratsin fari sai doguwar abayar kalan wondon mai igiyoyi biyu.
Sai kuma ɗan gyale fari.
A hankali ta kimtsa kanta cikin kayan.
Masha Allah, tace lokacin da ta tsaya gaban mirror tana rolling gyalen a kanta, domin sosai kayan suka zauna ɗas a jikinta kai kace, dan ƙirar jikinta aka haliccesu, igiyoyin rigar taja ta ɗan ɗaure daga tsakiya wanda hakan ya bawa ƙirjinta damar bayyana, kana tayi rolling kanta ta fidda fuskantar fasalin 0 turaren ta fesa.
A hankali ta fito Parlour, kan sallayan dake can shimfiɗe a gefen sukayi salla bayan sun idar ne ta ɗan juyo ta kalleshi.
“Barka da safiya”.
Ta faɗi tare da kallon fuskarsa, cikin jin sassauci da raraɗin damuwarsa yace.
“Babey kin tashi lfy”.
Sai kuma ya ɗanyi ɗan guntun Murmushin gefen baki yace.
“Wuyanki na ciwo ko?”.
Kai ta jujjuya mishi alamar a'a.
A hankali yace.
“Kin samu lada, kin sani nayi bacci har na tsawon awa uku, kusan mako biyu kenan baccina baya wuce 30 minutes nake farkawa shima sai in ina karatune nake samun ya ɗan fizgeni, shiyasa nake kwana a zaune, Amman yau nayi mai yawa Allah yayi Miki albarka”.
A hankali tace.
“Amin ya Allah”. Sai kuma ta ɗan kalleshi jin yana cewa.
“Miyi du'a Azkar, sai muje Restaurant muyi breakfast”.
Kwaɓe fuska tayi cikin sanyi tace.
“Taj mu koma gida”.
A hankali yace.
“Kin gaji da zaman nan ne!”.
Cikin sanyi tace.
“A'a kaga gobe su Aunty Nana zasu, koma ina son ɗan zama tare dasu”.
Yana ɗan gyara zamansa yace.
“to Saida yamma ko!”.
Da sauri tace.
“No ai in mun kai 12:00 AM
sai ka ƙara biyan kuɗin yau, ni mu tafi yanzu kaji ko dan allah.”
A hankali ya gyaɗa mata kai tare da cewa.
“Hmmm ai dama na kuɗin two weeks na biya. Amman zamu tafi tunda hakan kikeso”.
Daga nan sukayi addu'o'in su.
Ƙarfe goma dai-dai ta samesu a cikin gidan.
Bayan ya gaida dasu Aunty Amina da duk suke Dinning area.
Ya wuce ɗakin Addawa.
Ita kuwa Addawa da kanta ta haɗa musu breakfasts ta miƙawa Ishmah tray.
A bisa kujera ta sameshi zaune, yayinda Laylah ke zaune can gefen gado ta takure jinkinta daketa karkarwa tamkar wacce taga dodo.
Shi kuwa Taj ido kawai ya zuba mata cike da ƙuna da ƙuncin zuciya yana ɗaya daga cikin abinda yasa yakejin kamar zai raba musu gida da Addawa ta riƙe Laylah saboda yadda Laylah ta kasa sakewa dashi a fili yake ganin tsananin tsoronsa a kwayar idanunta wanda hakan ke sashi jin ya tsani kansa da kansa.
Ajiye Tray Ishmah tayi a gabansa tare dasa hannunta ta jawo Laylah da jikinta ke karkarwa tamkar mazari, a hankali tace.
“Ya dai Laylah me ya sameki? Ya kike firgice haka?”.
Sai kuma ta juyo ta kalli Taj ɗin daya taune gefen lip inshi na ƙasa kana ya zura idanunsa wuri ɗaya.
Cikin mamaki tace.
“Taj wai me ke damun Laylah ne, me take tsoro haka?”.
Cikin sanyi ya miƙe tsaye tare da zura hannunshi cikin aljihunsa suit inshi a hankali ya juya ya nufi hanyar fita tare da cewa.
“Ni take tsoro”.
Ya ƙare maganar tare da ficewa, side ɗinsa ya wuce kai tsaye.
Yana fita Addawa kuma na shiga dai-dai lokacin da take cewa Laylah.
“Laylah wai Uncle Taj ɗinki kike tsoro? Me yayi Miki?”.
Cikin sanyi Addawa ta zauna gefensu tare da yin ƙasa da murya tace.
“Eh shi take tsoro Ishmah!”.
Da sauri tace.
“Saboda me?”.
Tana mai ɗan taune lips inta duka biyu tace.
“Tun sanda maganar cewa Taj yayi mata fyaɗe ta fit.”
Da sauri Addawa tayi shiru ganin Ishmah ta sa hannunta duka biyu ta toshe kunnuwanta kana ta miƙe tsaye tana mai girgiza kai tare da jujjuya idanunta da sukayi jazir gaba ɗaya jikinta rawa ya farayi tamkar mazari.
Ita kuwa Addawa sai yanzu ma ta tuna da kashedin Taj da yayi mata na kada ta gayawa Ishmah komai shi da kansa zaiyi mata bayanin.
Sai kuma tabi Ishmah da idanu ganin ta fita.
Sauri-sauri gudu-gudu ta nufi Corridor ɗin, steps ɗin hawa saman ta fara takawa da sassarfa har Lau hannunta na toshe da kunnenta kamar tsoron buɗe kunnuwanta ma takeyi.
Gaba ɗaya idanunta basa iya gani, shiyasa ta gaza hango shi inda yake Dinnin area yake zauna bisa kujerar tare da kife kansa a kan Table ɗin.
Cikin rikitaciyar murya da alamun tsananin girgiza gami da son hafimtar abinda taji ta fara kiran sunansa murya a hargitse.
“Tajj! Tajj!! Tajjjj! Ina kake”..
Ta ƙare maganar muryarta na rawa hawaye na zubo mata.
Cikin sanyi ya miƙe tsauye yayinda zuciyarsa ke duka tara-tara farga da kiɗimar kaddai Addawa ta gaya mata cewa yayiwa Laylah fyaɗe harma tana da ciki ne suka diro mishi in one second.
A sabule ya taho gareta, murya a daskare yace.
“Gani”.
Da sauri ta juyo ta inda taji muryarsa hannunta tasa ta kamo hannunsa kana ta jawoshi zuwa tsakiyar Parlour sake hannunsa da tayi da kuma mutuwar da jikinsa yayi ne ya sashi zamewa ya zauna bisa kujerar 3 sitter dake bayansa.
Ita kuwa zubewa tayi bisa guiwowinta cike da tsoro murya na rawa tace.
“Taj me nakeji? Me gaskiyar abinda Addawa ta faɗa?”.
Cikin wani irin matsanancin fargaba da tashin hankali gami da tsoron, kada itama Ishmah tayi mishi irin hukuncin da Yah Abana da Ummeeynshi sukayi masa, yana taraddadin kada tayi mishi yakicewar da zaisa ta nesantasu da juna, itace kaɗai sauran yaƙininsa a duniya, ya zata ɗauki waɗanan kalaman in ta gujeshi ina zai saka ransa?.
Jin ta daura hannunta kan guiwowinsa tana jijjigawa da ƙarfi tare da fashewa da kuka tana faɗin.
“Tajj ka gaya meke faruwa? Please kayiwa Allah da Manzonsa kada ka ɓoye min komai meyasamu Laylah?”.
Kanshi ya ɗago tare da zuba mata ido cikin Tsananin damuwa da fargaba yace.
“Ma'eesha nayiwa Laylah fyaɗ....
Da sauri ta tsananta jijjiga guiwowinshi ba tare da ta bari ya ƙarasa faɗar abinda yake son faɗamatan ba domin heart and brain ɗinta bazasu iya ɗaukar nauyi da munin kalaman ba ji take zuciyar tamkar zata fashe cikin tsananin kiɗima gigita gami da tashin hankali da tsananin tsanan furucinsa na karshe da ta katse shi ta hanashi ƙarasa tayi wani irin miƙa tare da jujjuya kanta tana yarfa hannunta na dama na hagu kuma ta ɗaurashi kan ƙirjinta dake barazanar fashe cikin rawar murya tace.
“Wallahi tallahi bazan ci gaba da zam....
*Littafin INDA RAI na kiɗine ki biya ki karanta cikin aminci da salama 1k ne kacal 0661110170 GTBank Aisha Aliyu Garkuwa, sai ki turo min shaidar biyanki ta wannan number 09097853276 in kuma Niger kike 1000fc ne jaka ɗaya kacal kenan zaki biya. In kuma baki biyaba kika karanta min littafina wannan kuma kede Allah*
By
*GARKUWAR MARUBUTA*
[4/30, 10:43 PM] +234 706 616 8286: 📝💉🍇🍇🍇🍇🍇🍇
*INDA RAI*
*BOOK 2 PAGE 8*
Irin zazzafan ajiyan zuciya mai fizge numfashinta.
Da sauri ta miƙe tsaye saboda jin numfashinta na shirin barin gangar jikinta.
Ita kuwa Laylah da sauri ta nufi Parlour da gudu tana kiran Addawa da ƙarfi.
Wanda har Taj dake sauƙowa daga sama ya jiyota cikin mamakin yaxu gaba da sauƙowa saboda jin yadda Laylah ke aunawa Addawa kiran mafarauta, sai kuma ya fara sassarfa tare da sauƙa cikin kaɗuwa sabido jin Laylah na cewa Addawa.
“Aunty Ishmah ne tana ta kuka, Addawa ta kasa zama numfashinta fita da ƙarfi”.
Kusan a tare suka shiga ɗakin.
Cikin tashin hankali ganin yadda numfashi Ishmah keyi sama da ƙasa ne, yasashi saurin isa hareta dai-dai lokacin da jiri ya fara ɗibanta.
Da sauri ya tallabota ta afka cikinsa, da ƙarfi ya ruggumeta tsam a jikinsa.
Addawa kuwa salati ta saka cikin kaɗuwa take kiranta.
“Yah Salam Ishmah meke damunki? Afif mu tafi asibiti da sauri”.
Cikin ji muryar Addawa can sama-sama, da ƙarfi ta rumtse idanunta dake kwaranyar da hawaye tamkar an buɗe igiyar ruwa, murya na rawan kuka tace.
“No Taj bana so, kada ka kaini hospital, ni lafiyata ƙalau”.
Ta ƙare maganar cikin yayyankewar numfashi.
Da sauri ya tallabo kanta da tafukan hannunsa duka biyu, idonsa ya zuba cikin nata cikin muryar dake nuna damuwarta itace damuwarsa yace.
“Ma'eeshah numfashinki baya fita, ki bari muje asibitin, bana son rasaki, bana kuma son Ummeeyna ta ratsani ba tare da Yah Abana da Ummeyn sun yafe min ba”.
Ya ƙare maganar da sunkuceta tsam kana ya nufi hanyar fita da ita, itama Addawa bayansu tabi da hanzari tare da juyowa ta kalli Zulaihat lokacin da suka fito Parlour.
“Zulaihat ku zauna a gida bari muje asibiti, ki kula da Laylah”.
Cikin sanyi Zulaihat tace.
“Toh Addawa sai kun dawo”.
Dai-dai lokacin da suka shiga Corridor ɗin da zai fiddasu wajen.
Da sauri Ishmah tasa hannunta na dama bisa ƙirjin Taj ɗin tana ɗan bubbuga cikin alamun a ɗimauce take mgna da fizgo murya.
“Yah Sheykh lfyata ƙalau please dan Allah dan Annabi kada ka kaini asibiti bana so”.
Wani irin kallo ya zubawa fuskantar domin ya sani a iya tsawon zamansu in dai ta kirashi da Yah Sheykh to tabbas mgna ce ta gsky takeyi mishi, ba wasa ko ƙarya ciki kuma muddin ta haɗashi da Allah to yasan babban abune da take son a bari ko ayi shi, dan yana cikin abinda yasa bai taɓa cewa yana sonta ba, kafin aurensu domin da ake ta cewa son juna suke, yake cewa to ko dai gsky ne, ranar tayi ta roƙonshi da Allah da Manzonsa kada ya kawo makamanciyar mgnar nan a abotarsu ta rantse cewa, ba wannan mgnar shiyasa bai samu damar ida ƙudurinsaba saida tura ta kai bango.
Da sauri ya juya ya nufin kan steps ɗin da zai sadashi da part ɗinsa, saboda jin yadda taketa ɗan bubbuga kafaɗarsa tare da magiya gami da haɗashi da Allah.
Da sauri Addawa ta mara musu baya.
Suna shiga Parlour ya kwantar da ita bisa 3 sitter, sai kuma ya dire guiwowinsa ƙasa tare da ɗan ɗaura hannunshi kan goshinta kana ya ɗan sunkuyo kanta, tare da mannan lips inshi kan hancinta.
Hmmmmmmmmm taja wani irin na kasashshen numfashi saboda jin yadda yake bata taimakon gaggawa dan hana numfashinta ɗaukewa.
Zazzafan numfashi ya fesa mata kana ya zuƙo nata sassayan numfashi dake gab da komawa cikinta ya fizogoshi da ƙarfi.
Wani irin miƙa tayi tare da sauƙe ƙaƙƙarfan ajiyan zuciya da ya tabbatar da daidaituwar numfashinta.
Kusan a tare Addawa da Taj ɗin duka dire ajiyar zuciya dake nuna samun nitsuwarsu.
A hankali yake ci gaba da shafa goshinta tare da ɗan sa yatsarsa manuniya yana ɗan kwantar da gashin girarta ɗaya da ya hautsine.
Gefen kanta Addawa ta zauna bisa hannun kujerar murya cike da kaɗuwa da kulawa tace.
“Kina da Asma ne?”.
A hankali ta jujjya mata kai alamar a'a, shi kuwa Taj yatsarsa yasa kefen kuncinta ya goge mata hawayenta dake kwaranya, cikin sanyi murya yace.
“Ma'eesha meke damunki? Meya saki kuka? Ki gaya min koma menene zanyi maganin abin bazai sake sa min ke kuka ba”.
Ido a lumshe tace.
“Taj Laylah ke ƙara tabbatar min wai da gaske anyi mata fyaɗa wai ka maida ita tamkar matar aurenka, tun sanda kuka dawo Nigeria, Laylah tace min a ɗakinta kake kwana, saboda duk sanda kake Ethiopia ne ake kwana mata a ɗaki, Laylah tace min bindiga kake nuna mata kasata dole ta tsiraita, kuma kaima ka tsi...”
Ina ta kasa ƙarasa kalmar dan tayiwa harcenta nauyi.
Addawa kam ido ta rumtse da ƙarfi, don ta fahimci kenan Laylah tayi mata cikekken bayanin kamar yadda tayi mata cikekken bayanin yadda Taj ya maida ta, tamkar matarsa.
Cikin zubda hawayen ta miƙe ta fice daga Parlour'n tana mgnar zuci.
“Na sani Tajuddeen Namijine daya amsa suna na miji, na kuwa san cewa lafiyeyyene da yake da buƙatar mace a kusa dashi, wacce yake so take sonshi wacce zata iya ɗaukar nauyin buƙatar sa, a matsayin halittarsa ta cikakken namiji, duk da na ɗan fahimci ƙarfin tattalirsa da buƙatarsa gadon kakansa ne, gashi an aura mishi wacce baya so bata sonshi, ban yarda ko amincewa hakan zaisa Tajuddeen yayi fatali da iliminsa nutsuwarsa, kamalarsa har ya lalata ƴar da ya ɗauko amana daga hukumar kula da marayun Palastine ba, Tajuddeen an cuci yarinyar nan, an tozarta rayuwarta an liƙa maka baƙin fenti.
Amman na sani in sha Allah gskya zatayi halinta domin da wuya haƙƙinta da kai da zuciyata taƙi yarda zaka aikata ya bari waɗanda sukayi wannan makircin su samu zaman lfy.
Ko dan haƙƙin tarwatsa tsakaninka da iyayenka da matarka duk da muna kyautata zaton zatayi haƙuri da kuskurenka inma kai ka aikata”.
Koda ta iso Parlour bata iya amsa mgnar da Zulaihat da Laylah sukeyi Mataba, saboda ɓacin rai da mgnar zuci da take yi.
A can Parlour Taj kuwa, kife kansa yayi a gefen kanta, so yake yayi mgna Amman ina ya kasa sai wani irin rawa da lips inshi keyi kamar wanda aka saka cikin dusar ƙanƙara.
Ita kuwa Ishmah idanun ta dake zubda hawayen ta zuba mishi tare da ci gaba da yin sassayan kuka tana faɗin.
“Taj kayi mgna mana”.
Cikin fizgo mgnar zuci yace.
“Kiyi haƙuri Babey wlh ni n...”
Da sauri tasa yatsunta ta toshe kunnuwanta tare da fashewa da kuka tana faɗin.
“No! No!! Nooooo!!! Taj kada kace min da gaskene”.
Kife kanshi yayi ya kasa mgna sai karkarwa da jikinsa keyi.
Ita kuwa Ishmah kukan taci gaba dayi.
Ethiopia
Adaya ce kwance bisa gadon ta, sai juyi takeyi, tare da jan gajerun tsaki a jere a jere, hannunta ta manna bisa wuyanta.
Da sauri ta cire hannun saboda yadda taji jikinta, yayi zafi.
Juyawa tayi ta gefen hagunta tare da lumshe idanunta tana mai jin ɗan karen gajiya da zazzabin da yakeda nasaba da rawar data wuni yi kai kace injice itan.
Da kyar dai ta samu wuraren ƙarfe ɗaya. bacci yayi awon gaba da ita.
Doha Qatar.
A hankali take sauƙe ajiyan zuciya a jere a jere bisa alamu tana cikin kukan