Showing 15001 words to 18000 words out of 44320 words
fatan su kasance tare dasu su zama sanadin musuluntarsu.
Cike da jin daɗi sukayi godiya kana suka ci gaba da tattaunawa da yadda zasu tallata asbitin..
Acan gidan Addawa kuwa da yammaci suna zaune Garkuwa ce da Aunty Nana suka kalli Addawa jin tana cewa.
Zulaihat tashiga kitchen tayi musu girki.
Murmushi garkuwa tayi tare da cewa.
“Addawa bari mu shiga mu taya ta girkin ai abin ya mata yawa ita kaɗai take ta fama”.
Addawa na gyara zama tace.
“Zata iya ai Zulaihat nada ƙoƙarin”
Zulaihat na gab da shiga kitchen tace.
“Allah Aunty Ku huta”.
Khadija na miƙewa tace.
“A muje dai na tayaki”.
Aranta tace gwara dai muje mu ga abinda za'a mana Kada ayi mana abincin Larabawa ko na Amharic wanda ba lallai mu iya ciba.
Daga nan suka shiga kitchen kana su kuma suka ci-gaba da hiransu.
Aunty Nana dake ƙoƙarin kunna gas tace.
“Wai ni har yanzu ba wanda yayi waya da Ishmah?,”.
Khadijah na ɗauraye tukunyar tace.
“Wai ke me matsalar ki da sai kinyi magana da ita na rasa mene matsalar ki yanzu fa da da ba ɗaya bane da in kina tunanin cewa Ƙanwar mijinkine tana zaune agida yanzu fa matar Aurece kuma gurin mijinta take”.
Adai-dai lokacin kiran Ishmah ya shigo wayar Aunty Nana murmushi tayi tace.
“Ƴar halak kinƙi ambato”.
Ta kai karshen maganar tana amsa kiran tana ɗauka tace.
“Ohhh Ikon Allah yanzu dan Allah dan Annabi Ishmah ina kika shiga tunda muka zo ba amo ba labarinki.
Kinje kin rungumi mijinki kunyi shiru wannan abu har ina daga ke har Taj ɗin kun bani kunya".
Cikin sanyi Ishmah tace.
“Wallahi nikam ba ruwana dan ko yatsana bai riƙe ba har da cewa wai na rungumi miji ance Miki ni irinki ne!?”.
Dariya Aunty Nana tayi tare da faɗin.
“Ai dake irina ne da tare zamu zauna kawai sai naga mutum ya canza hanya da ban toh yanzu ina kuke?”.
Cikin sauƙe numfashi ta faɗa mata sunan hotel ɗin da suke.
Aunty Nana na dariya ta juya ta kalli Garkuwa tare da cewa.
“Kin gani ko Garkuwa wai fa a Hotel suka sauka yanzu yaushe zaki dawo?”.
Ahankali Ishmah ta girgiza kai tare da faɗin.
“ Nima ban sani ba Aunty Nana anma anjima idan ya shigo zan baki ki tambayeshi”.
Dariya Garkuwa ta sanya kana tace.
“Madallah kinyi min naganinta”.
Kana ta karbi wayar suka ci-gaba da hira...
Aranar dai haka Taj ya yini tattaunawa da Likitocinsa koda suka gama ranar ma haka ya kwana kamar jiya baiyi bacci ba Ishmah kam bacci take shi kuma yana zaune bakin gadon yana karatu idan ya ɗan gaji da zaman yayi nafila haka nan zuciyarsa ta gaza amsar hukuncin Yah Abana ji yake yi ya rabashi da dukkan farin cikinsa a hankali ya ɗan juyo ya kalli Ishmah da ta ɗanyi juyi tare da matsowa gab da bakin gadon murya cike da bacci tace
“Tajj kayi bacci”. Sai kuma ta ƙare maganar tare da kife kanta alamun cikin bacci tayi mgnar kuma baccin ya kuma danneta, sassayan numfashi ya fesar tare da gyara zamansa ganin fuskantar a kusa dashi a matsayin matar sa kaɗai ne ke sawa yaji zuciyarsa ta ɗan samu sassaucin tarin damuwarsa da ta kauda dukkan shauƙin jiki da zuciyarsa gami da ruhinsa....
Washe gari da safe Ethiopia.
Meymer ce zaune gaban Momynta.
Cikin tsuke fuska Momyn Meymer tace.
“Toh Meymer kin dai yi abinda kike so”.
Cikin matsanancin kuka da zubda hawaye tace.
“Momy me nayi?,dan Allah ki daina cewa nayi abinda nake so”.
Cikin takaici tace.
“Meymey kin sani na sani kinyi abinda kike so Afif ya sake ki ko?”.
Kai ta gyada cikin gamsuwa da jin daɗi tace.
“Eh”.
Cikin rashin walwala tace.
“Shawar da zan baki ki fara Istigfari kafin Sakayya yazo ko Ubangiji zai kawo Miki Sakayyan da sauƙi”.
Da sauri tace.
“Wallahi Allah Momy ba abinda nayi mishi Momy abinda ya aikata fa aka faɗa banyi masa ƙazafi ba”.
Cikin tarin takaici Momy tace.
“Ni dai ban nemi ƙarin bayani ba, abinda zan faɗa Miki ki kama kanki ki riƙe kanki da Dr Zakariyya duk abinda zakuyi sai ki bari sai kin gama Iddah kafin ku fara maganar Aure”.
Cikin sauri tace.
“Momy nifa babu Iddah akaina tunda mu kayi Aure da Yah Afif ko hannuna bai taɓa riƙe wa ba”.
Wani kallon takaici Momy ta watsa mata kana tace.
“Ni dai ban nemi wani bayani ba kawai kiyi zaman Iddah kafin kuyi aure da Dr Zakariyya dan nasan shine aranki”.
Ta ƙare maganar tana mai jin takaicin rabuwar Auren Afif da ƴarta...
Acan gidansu Adaya kuwa Ummi ce da Aminullah tsaye a falo bisa alamu aike ta yiwa Aminullah yanzu ya kawo mata cikin mamaki ta buɗe ido ganin Adaya ta fito tana tafe cikin rausayawa bisa duk kan alamu zata tafi Reharzal ne cikin tarin takaici da bakin ciki ya kalli Ummi itama Ummi kallonsa tayi .
Cikin jujjuya kafada da jijjiga ƙirji tace
“Toh Ummi na tafi ”.
Cikin tarin takaici da Mamaki tace
“Ina zakije Adaya?”.
Ɗan wara idanunta tayi tare da faɗin.
“Ummi kin manta kwana biyun nan ƙuguna da yake ciwone yasa ban samu na naje Reharzal ba yanzu fa wata biyu ne fa kacal ya rage mu tafi India gasar rawa Ummi ki tayamu da addu'a”.
Cikin tashin hankali Ummi tace.
“Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un dama har yanzu Adaya wannan gasar rawar yana ranki”.
“Eh mana Ummi ”.
Ta faɗa tare da ficewa a falon.
Cikin kunci da tarin damuwa Aminullah yace.
“Badan ciwo ba daɗi ba da nace ciwon daya. dami Aunty Adaya ya dawwama ajikinta har Abada saboda ta nutsu ta daina abinda takeyi”.
Cikin sanyin jiki da karaya da lamarin Adaya Ummi ta zauna kan kujerar tare da dafe kanta da hannunta duka biyu.
Adaya kam tuni ta fita tana isa hall ɗin da suke Reharzal ɗin duk suka miƙe tsaye saboda jin an saki wani irin....
*Kunsha typing errors dan banyi editing wannan page ɗin ba*
*BY*
*GARKUWAR MARUBUTA*
[4/30, 10:43 PM] +234 706 616 8286: 📝🕋💉🍇🍇🍇🍇🍇🍇
*INDA RAI*
*BOOK 2 PAGE 3*
*AYASHA ALIYU GARKUWA*
🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇
*Lockpage*
Ido suka zuba mata cike da farin ciki Aunty Nana ta juyo ta kalli Garkuwa dake murmushi sai kuma ta kalli Ishmah dake raɓa gefenta, kai a sunkuye tana tafiya ne cike da sanyin jiki da kaɗuwa da dukan ba zata da kalmar aurenta ya saki mata, gami da raunin da ganin Taj a cikin yanayin da yasa har yanzu hawayenta basu tsagaita zubar da sukeyi ba.
Cikin sanyi Aunty Nana ta ɗan jujjuya kai, tare da ɗan juyawa ta nufi hanyar fita saboda haka nan taji rauni yana diro mata.
Ita kuwa Ishmah tana shiga bisa gadonta ta faɗa tare da sakin sassayan kukan da yaƙi dannuwa.
Da sauri Garkuwa ta biyo bayanta.
A gefen ta ta zauna tare da kamo hannunta ta tada ita zaune, cikin sanyi da tausasa zuciya tace.
“Haba dai Ishmah, wannan shine irin godiyar da zakiyiwa Allah? Hakan bai cancanci nagartaciyar mace irinki ba, ki sani fa ɗan adam baya tsallake ƙaddararsa, kuma duk managarcin musulmin da ya cika mumuni na gaske, amsar ƙaddara yakeyi a duk san da tazo mishi, a kuma duk yanayin da yazo mishi.”
Sai kuma ta ƙare maganar tare dasa hannunta ta jawota tsaye.
“Shiga kiyi al'wala kizo kiyi salla, ki godewa Allah da ni'imar da yayi Miki, na mallaka Miki miji mafi daraja da tsada a cikin mazaje, miji irin wanda ko wanne uba yakewa ɗiyarsa fata da addu'ar sumu.
Ishmah ki sani fa cewa Allah yayi Miki ni'imar mafi ƙololuwar ɗaukaka, ni’imar samun mallakar Sheykh Afif Muhammad Taj a matsayin mijin aurenki, Kin fini sanin waye Taj domin kece mace mafi kusanci dashi a duniya, harma da mahaifiyarsa tunda yanzu zaki rayu a ƙarƙashin inuwar aurenshi, zaki zame mishi sutura, zai zame miki sutura, kana garkuwanki”
Wasu irin tafassasun hawayene masu tafe da tsananin tsoron Allah da girgiza da girman ikonsa da ƙudurarsa, wai yau itace Aisha Ishmah ake kira a matsayin matar Taj ya Salam.
Shine kaɗai abinda ta iya cewa.
Dai-dai lokacin kuma Aunty Amina wacce take ƙanwa ga Daddy, ta ɗan juyo ta kallesu lokacin da ta fito daga bathroom bisa alamu al'wala tayi.
A hankali ta matso kusa dasu tare da tallafe habar Ishmah tana faɗin.
“Mu yau duk faɗin family d’in mu, cike muke da tsananin farin ciki da bazai misaltu ba, saboda haka dan Allah kada ki raunata mana zuciya shiga kiyo al'wala”.
Kai ta jinjina tare da juyawa ta nufi Bathroom ɗin.
Bayan tayi al'walan ta fitone itama Garkuwa ta shiga tayi.
Bayan sun idar da sallan isha’i zaune suke a tsakiyar Parlour kowa da abinda ke gabanshi.
Cikin kulawa Garkuwa ta ƙara turo mata plate ɗin da ta zuba mata dungulen zabuwar.
“Dan Allah ki cinyeta, dan so nake inga kin cinyeta kafin Oga yazo, dan yace yau da kansa zai-zo ɗaukata dan yana son yayi wa Abba murnar auren Boɗɗinsa”.
A hankali ta ɗan kalli plate ɗin wanda ta ci kusan rabin zabuwar, fork ɗin hannunta tasa, tare da ɗan sabulo tattausaar tsokar da magunguna suka sa tayi baƙi, ido ta rufe lokacin da ta kai tsokar cikin bakinta.
“Ai nima yau bazan tafi ba, sai ta cinyeshi”.
Cewar Aunty Hauwa.
Fuska ta ƙwaɓe cike da rauni tace.
“Cikina ya cika fa”.
Kai Aunty Amina ta gyaɗa tare da cewa.
“Ba matsala Garkuwa bata damun tasha, anjima kan mu tafi zata ƙarasa zabuwar”.
Ta ƙare maganar tana kai cup ɗin ruwa bakinta.
Aunty Maryam da yanzu ta shigo ne tace.
“Ai kada ku damu a barmin wannan aikin, ni daɗi nake ji inga na tisa mutun a gaba yasha magani”.
Cikin sanyi da ya gaza barin ruhi da jinkinta tasa hannunta ta amshi kwanon Ƙasaitacciyar mace da yake ɗauke da damun.
Lumshe idanunta tayi domin sosai damun yayi mata daɗi a bakinta sai dai, ina cikinta ya cika rabi tasha kana ta ajiyeshi.
Tana hamdala domin tun safe bataci komai ba.
Ƙarfe tara dai-dai duk ummomin ta suka tafi, bayan sun jaddada wa Garkuwa ta bata ta cinye sauran.
Ƙarfe goma dai-dai, Oga ne, zaune da Abba a falonshi tare kuma da Taj.
Sosai sukayi hira daga bisani.
Sheykh ya kira Bobbuga rumbun Abboi ɗinsa ta fito su tafi.
A hankali ta sauƙe numfashi tare da cewa.
“Yauwa yanzu dai hankali ya kwanta tunda kin ƙarasa kazar, kin shanye damun kuma”.
Cikin sanyi Ishmah ta ɗan shafa cikinta da bazakace a ciki zabuwar nan da damun nan sunka samu muhallin zamaba.
Sai kuma ta ɗan kwaɓe fuska jin Garkuwa na cewa Maryam.
“Akwai kuma haɗin jan Nama dama na dafa mata, yana cikin fridge da safe ki ɗumashi sai ki bata ta cinye, garukan nan kuma dasu tsumi, sau uku zata rinƙa sha safe da yamma, da rana”.
Da sauri tace.
“Toh wannan kam sune zasu zama abincina ko yaya, zasuyi min yawafa Aunty Garkuwa”.
Murmushin tayi tare da ɗaukar mayafinta tana yafawa tace.
“Ai haka nakeso suyi miki yawan, Sheykh Afif ya banbance tsakanin aya da tsakuwa.”
Tana gyara mayafin jikin ta, ta fara binta a baya ganin ta nufi hanyar fita tana faɗin.
“Toh Maryam na barku, da aiki.
In sha Allah zuwa jibi kuma zan turo mata dahuwar zuciyar farin rago.”
Suna fita Maryam tace.
“Kada ki damu, mun gode sosai a gaida gida”.
A hankali suka iso harabar gidan.
Tsaye suka samu Oga da Taj.
A hankali suka ƙaraso kusa adasu dai-dai lokacin da Sheiykh ke cewa.
“Wannan ba matsala in sha Allah, zanyiwa Capting Sadik sale mgna akan visa ɗin, masu rakiyar tunda nasan na ango da amarya kam can ne zasuji daku”.
Cikin sanyi Taj ɗin ya bashi hannun tare da cewa.
“Amman dai za'a bamu aron Garkuwa ko, tayi mana rakiya”.
Da sauri duk suka kalleshi jin yana faɗin.
“Kai kuyi haƙuri bazan iyaba”.
Cikin sanyi Taj ɗin yace.
“Haƙuri zakayi”.
Yana ɗan murmushi yace, .
“To yanzu dai bari muji ta bakin Sadik ɗin muji ko zaku samu visa ɗin, duk yadda mukayi dashi zakaji ni”.
Ya ƙare maganar tare da bawa Taj ɗin hannunsa sai kuma ya ɗan juyo ya kalli Ishmah dake gaidashi yace.
“Barka dai amarya, Allah ya sanya alkhairi yabada zaman lafiya”.
A tare Taj da Garkuwa suka amsa, ita kuwa Ishmah ƙasa tayi da kanta tare da ɗan kaɗa kanta jin Garkuwa dake shiga motar nace mata.
“To sai da safe, zamuyi waya”.
“Allah ya bamu alkhairi”.
Amin suka amsa kana yaja motar suka tafi.
A hankali ta ɗan juyo ta kalleshi, da sauri tayi ƙasa da kanta ganin shima ɗin ita yake kallo.
Cikin sanyi murya tace.
“Ya ƙafarka?”.
A hankali ya ɗan matso kusa da ita, murya can ƙasan maƙoshinsa yace.
“Alhamdulillah”.
Ya faɗa tare da ɗan ƙara matsowa jikinta.
Sai kuma ya ɗan jujjuya kanshi yana ƙarewa harabar gidan kallo ba kowa.
Hannunshi yasa ya jawota jikinsa sassauƙan rugguma yayi mata tare da ɗan manna lips inshi kan goshinta ya dire mata sassayan kiss murya can ƙasan maƙoshinsa yace.
“Ki yafewa Tajj ɗinki Ma'eesha”.
Cikin sanyi ta ɗan lumshe idanunta kana ta buɗesu a hankali. Sai kuma ta ɗanyi saurin matsawa baya, saboda hango Yah Muhammad.
A hankali ta nufi cikin gida.
Shi kuwa Taj BQ ɗin ya wuce shida Yah Muhammad.
Washe gari da safe, cike suke a Parlour Daddy.
Cikin sanyi Ishmah ta kalli Yah Rabi'u ɗan Bappa Bello dake zaune ba tare da ya fara cin abinci ba.
“Yah Rabi'u kaci abinci mana”.
Kanshi ya ɗan jujjuya tare da cewa.
“Ina azumi ai”.
Da sauri Rahama tace.
“Kai Yah Rabi'u dan Allah ka karyashi muna haɗe kowa nacin kai kuma ka wani ce kana azumin”.
Cikin mutuntaka da nagarta yace.
“Azumi mukeyi dani da Yah Abubakar wanda mukayiwa Allah al'ƙawarin duk randa Ishmah tayi aure, zamuyi azumi uku uku domin gode mishi”.
Cike da tarin mamaki ta kalleshi.
A ranta tace.
A kaina, shin dama ashe har haka rashin aurena ke ciwa yan uwa tuwo a kwarya.
A fili kuwa sunkuyar da kanta tayi, yayinda wasu siraran hawayen ke zubo ma.
Cikin sanyi kuma duk suka kalli Adam daya saki wata doguwar ajiyar zuciya murya cike da rauni yace.
“Ni saboda aurenta nake azumi uku cikin ko wanne wata, sai gashi yanzu kuma da auren yazo, ji nakeyi tamkar ace an fasa saboda, bana son tayi nesa damu, domin itace ta meye mana gurbin Daddy a gidan.
Ita muke gani muji sanyi itace ta danne maraicinmu, mukan shiga ɗakinta muyi tamkar yadda mukeyi a ɗakin Daddy”.
Da sauri Yah Abubakar ya ɗan dafa hannunsa dake kusa da nasa tare da girgiza mishi kai.
Sai kuma duk suka kalli Hamisu wanda ya miƙe tsaye tare da ficewa yana zubda hawayen tunowa da Mahaifiyarsun da kuma nesa da yayarsu zatayi dasu.
Da sauri kuma duk suka kalli Rahma yar auta data saki shesh-sheƙan kuka murya na rawa take cewa.
“Yanzu zamu ƙara fuskantar maraici, ni bazan ma zauna a gidan nan ba in ta tafi”.
Da sauri Yah Muhammad ya jawo hannunta tare da cewa.
“Zo nan auta, ba gamu ba, duk abinda kikeso zamuyi miki”.
Ita kam Ishmah tuni take zubda hawaye masu zafi.
Sosai take jin rashin mahafiyarsu ya sabunta garesu.
Yah Rabi'u ne ya gyara zamansa cike da hikimar Addini ya fara yi musu nasiha mai ratsa jiki wacce tasa gaba ɗaya suka fara samun nitsuwa.
Ethiopia
Cikin sanyi Abpu ya koma ya kishingiɗa jikin kujerar dake bayanshi.
Tare da fesar da zazzafan numfashi cikin alamun rashin ƙoshin lfy yace.
“Zuwa yanzu dai dole in cire batun auren Adaya a raina.
Wata ƙil itace Allah ya bani Zakka a cikin yayana.
Allah yaji ya gani nayi iya iyawata shine shaidata, kamar yadda shine mai shiryawa,
To ina fatan ya shirya min ita fiye da bada tarbiyata in tana da rabon shirya,
In kuma bata da rabon shirya ina roƙon Allah ya yafe min kada ya kamani da zunubanta”.
Ya ƙare maganar murya cike da rauni.
Yah Ma'aruf dake gefene ya ɗanyi saurin motsawa kusa dashi.
Aminullah kuwa ƙaninta hawayene suka tsinko mishi.
Ummi kuwa murya a sarƙafe tace.
“In sha Allah zata shirya, tunda kace Allah.
Ta dire mgnar tana nazari yau kwana uku kenan Adaya bata fita ko tsakar gidaba tun randa wanda akace mijinta ne yazo ya saketa.
Yah Ma'aruf ɗinne yaci gaba da tausa sa Abpun.
Mamanshi kuwa k’waffa tayi ƙasan lips tare da juyawa ta fice Allah ya sani lamarin Adaya ya fara damunta, dan yana damun mijinsu kuma itama duk inda taje sai ace ƴarsu cikin takaici tace.
“Shegiyar yarinya mai kama da ifiritu minaljinni, ta buwaye mu ai ta nuna mu, Allah ya shirya.”
A dai-dai lokacin a can Parlour Abba kuwa.
Sheykh Tajuh Usman Bauchi ne tare da Babban ɗansa Sheykh Tijjani Usman Bauchi.
Sai Uncle Bello.
Da kuma Taj dake tsakiyarsu.
Bisa dukkan alamu magana mai mahimmanci suke tattaunawa
Bayan sun gama duk tattaunawar tasu, sun tsaida matsayar tafiya da masuyin rakiyar kai amaryar.
Sai ƙarfe goma su Sheykh Tajuh Usman Bauchi, suka fita tare da tawagar zakiransu, suka kama hanyar Bauchi, bayan ya ƙara kebewa da Taj ɗin.
Cikin sauƙe numfashi Uncle Bello ya kalli Abba da kuma sauran yaran nasu kana yace.
“To Alhamdulillah, abu yazo mana a lokacin da bamuyi zaton zai-zo mana a hakanba.
Sai kuma ya ɗan kalli Yah Muhammad tare da cewa.
“Masu zuwa rakiyar nanfa, bazasu wuce 6 ba, ni in a son samu nane ma mutum biyu kacal”.
Kai Yah Muhammad ya jinjina tare da cewa.
“Toh gsky nima hakan naso, toh shi ɗin ne yake nunin da aje ɗin saboda wai hankalin Ishmah zaifi kwanciya, kuma Abba ma zaifi samun nitsuwa in ya san inda Boɗɗinsa take”.
Murmushi ya ɗanyi kana yace.
“To ka kira Goggo Dijan ku. ƙanwarsu Abba kenan. da takwararta Khadijah ƙanwar Ishmah kenan mai Binta.
A gefen mu su zasuje, sai kuma ummarku ɗaya.
Sai kuma matarka ko matar Abubakar, sai kuma uwar ɗakinta Garkuwa.
Biyar kenan ko?”.
Da sauri Yah Abubakar yace.
“Eh”.
Yana gyara zamansa yace.
“To sai ita Ishmah da mijin nata, bakwai sun fito ba.”
Cikin sanyi Taj ɗin yace.
“Eh yanzu mukayi waya da Sheiykh yace, min yayi magana da wani ƙaninsa cewa, za'a samu Visa, sai dai na mutum takwas za'a samu kuma ranar Laraba jirgin zai tashi.”
Cikin sauke numfashi Yah Abubakar yace.
“To sai asa Adam cikon na bakwai ɗin, kar suje ba namiji ko ɗan aike zai musu, kuma Aunty Nana taje, In sha Allah daga baya zanje da Maryam kam”.
Cikin gamsuwa Abba yace.
“To Allah ya sanya alkhairi aje lfy a dawo lfy.
Khadijah ma da Dija sun cemin sun taso suna hanya ma”.
Shiru sukayi jin Yah Muhammad na cewa.
“Toh Amman Uncle Bello ko dai Ummace zataje madadin Nana”.
Da sauri Uncle Bello yace.
“Wannan tunda muka dawo Umrah take fama da mura, gashi matar Rabi'u nada