Showing 48001 words to 51000 words out of 58156 words
a kotu.
Ya ce, "Sopyna baki da dama kema, nakula randa natashi k'ara aure zamusha fama, dan kinada kishi, ya k'arasa maganar cikin tsokana.
Sopy ta d'aure fuska tamau.
Uncle G! ya tuntsure da dariya, harda buga kai, yadawo kusada ita, yadafa kafad'ar ta kinga sopyna dawasa nake miki, ke kad'aice matar youseef daga ke babu k'ari.
Sopy tad'an turo baki tana fad'in nidai ban yardaba.
Ya jawota zuwa jikinsa ya ce, "mikike so nayi miki dan ki yarda??, ta d'ago tana kallonsa, ta ce, "kayimini alk'awari.
Yad'an kafa mata idanu na tsawon minti biyu, saikuma ya lumshe idanunsa ya bud'e, ya jinjina kai yana fad'in ni youseef nayi alk'awarin kasancewa da safiyya har k'arshen rayuwata, kuma ita kad'ai amatsayin matata, saidai idan wata k'addara ko jarabawa takawo sab'anin haka a rayuwarmu.
Sopy ta rungumeshi tana murmushi, ta ce, "nima hakan take a gareni hubbina, ALLAH kuma yabamu ikon ruk'e junanamu da hak'uri da juriya.
Uncle G! ya rungumeta yana fad'in amin ya Rabbi sopyna.
Zan iya cemuku dai ayanzu fareeda tad'an fara shiga hankalinta, dan tad'an rage aikata wasu abubuwan saidaifa har yanzu tanan akan bakanta nason mallakar uncle G! amatsayin miji, to itamadai safiyya tanan tana tanadar manya2 makaman yak'ar fareeda, dankuwa kulum tana tashi da shirin kota kwana.
Yaukam sai k'arfe biyu sopy tashiga makaranta, dan batada lecture d'in safe, sai sauri take dan tasan uncle G! yau zaimusu lecture karfe biyu da kwata, cikin sassarfa ta isa class, amma saidai ta makaro, domin kuwa har uncle G! ya shiga.
Taja birki ak'ofar class d'in kamar yanda makararu suke tsaye, tofa saimuce kallon ya koma sama, sai hankalin 'yan class d'in da makararru suka dawo kanta, kowa yana so yaga ikon ALLAH, jiyayi k'amshin turarenta ya yawauta agurin dan haka yad'an juyo ya kalli inda yake zaton take, sukaima juna kallon ido cikin ido, amma sai uncle G! ya basar yacigaba da lecture d'insa.
Wani k'ududun bak'in cikin ya tokare mak'ogwaron sopy, gashi gabad'aya hankalin d'aliban yana kanta.
Uncle G! ya juyo ya kalleta yana wani d'an murmushin mugunta, dukada fuskarta tana yane da nikaf wannan bai hanata murgud'a masa bakiba, ya maida kallonsa ga d'alibai fuskarsa d'auke da murmushi.
Bayan ya kammala lecture d'in ya fito, hannun sopy yakama batareda yayi mata maganaba, sopy tayi k'ok'arin kwace hannunta, amma saita kasa, dan ba rik'on wasa yay mataba.
Har cikin office d'insa ya kaita, sannan yasaki hannunta yajiginna da k'ofar ya hard'e hannayensa a k'irji.
Sopy ta kauda kai gefe dan haushi, hannu yasa ya yaye mata nik'af d'in fuskarta, ta galla masa harar tana murugud'a baki๐, yasa yatsu biyu ya kamo lab'b'anta, yad'an matsesu waje d'aya, ta rik'e hannunsa tana k'ara, dan taji zafi.
Uncle G! ya ce, "o, autar inna da zafine??, ta harareshi da idanuwanta dasukayi jaa, yasaki bakinta yana murmushi, hannu yasa ya d'ago fuskarta suna kallon juna, ya ce, "wannan shine gargad'inki, daga yau idan kika sake makara tofa hukuncin yafi haka yawa.
Ta lumshe idanunta, wasu hawaye suka zubo bisa kuma tunta, wani tsadadden murmushi yasaki tareda sumbatar bakinta, ta bud'e idanu da sauri, suka zubama juna ido, daka gansu kasan kallon k'auna sukema juna, suka lumshe idanu alokaci d'aya kum suka bud'e, uncle G! ya rungumeta tsam zuwa jikinsa.
Sopy ta ce, "a zuciyarta, uncle G! Kenan, zuma ga zak'i ga harbi๐๐ป.
Yau takasance juma'a, yaune kuma su aunty Hafsat zasuzo, gaba d'aya sopy ta rikita kanta sai aiki takeyi, domin tarbar bak'inta, ita dai fareeda sai kallon ikon ALLAH takeyi, hakama uncle G! binta kawai yake da kallon mamaki, dan ganin yanda taketa hidima kamar wasu bak'ine daban zasuzo basu libabatu ba.
Wajen k'arfe d'aya da rabi uncle G! yatafi tarosu a tasha..............โ๐ป
๐Bily๐
๐๐Mrs Abdus'salam๐๐๐
๐I LOVE YOU MY FAN's๐๐
[12/19, 7:26 PM] mrs bilkisu: 21~November~2016
๐ท๐นNI DA AMINIYATA!!!๐น๐ท
NA BILKISA IBRAHIM๐
๐ถ๐ธ5โฃ2โฃ๐ธ๐ถ
............Babu dad'ewa uncle G! yadawo d'aukeda su aunty hafsat, cikin matuk'ar fainciki sopy ta taresu, suma dai sunyi farin cikin ganinta, musamman ma Aysha.
Sopy tacika musu gaba da kayan abinci, aunty hafsat ta ce, "o ni, k'anwata yaya zamuyi da wannan abinci haka, saikace masu cikin zani.
Sopy tayi dariya tana fad'in duk nakune aunty, aii d'anyar fata bata fashewa.
Sukayi dariya suna fad'in lallaikam, yau zamuci har mu kasa tashi, fareeda ta fito tana musu sannu da zuwa, suka amsa suna binta da kallo, dan basu santaba, ta zauna tana wasada Sayeed d'an gidan Libabatu.
Uncle G! yafito, jikinsa sanye da farar shadda tas d'inkin nasa dai bodane kamar kullum, tayi masa matuk'ar k'yau,sai tashin k'amshi yakeyi, ya d'ora hula da farin gilas siriri.
Aysha ta ce, "yaya ina zakaje, yad'an kalli bak'in agogon dake d'aure a tsin tsiyar hannunsa, ya ce, "Aysha xanje masallacine ko.
Ta ce, "dan ALLAH zanje.
Ya girgiza kai yana fad'in A'a bazanje dakeba, masallacin nan bakamar na gida bane.
Sopy tafito daga kichin hannunta d'auke da tire, ganin uncle G! ya d'au kwalliya saita tsaya tana kallonsa.
Ya kanne mata ido d'aya, tad'anyi murmushi tana nuna masa su aunty hafsat da idanu.
Shima murmushi yayi tareda d'aga kafad'a alamu, so what, sopy ta ce, "uncle sai ina?, ya ce, "lallai kin manta yau juma'a?, ta ce, "o, masallaci fa ko??, ya jin jina mata kai yana lumshe idanu, ta ce, "to ALLAH ya tsare.
Yad'an yima sayeed wasa yana fad'in amin sopyna, sayeed yashiga wangale baki yana mik'a masa hannu.
Uncle G! ya d'aukeshi yana fad'in yaro masallaci zanje, yad'an yimasa wasa sannan yamaidashi wajen fareeda ya fice yana fad'in saina dawo.
Sukace to adawo lafiya.
Yau kam sunasha hira abinsu, sopy tasha firar gurum, sun kawo masu tsaraba irinta k'yauye, tasu data gwaggo, babama ba'a barsa abayaba.
Sai k'arfe hud'u uncle G! yadawo, sopy ta taroshi amma bakamar yanda ta sababa, saboda yau tana jin kunyar bak'i, ya zauna yana fad'in wash ALLAH!!; na.
Su duka suka dawo da kallonsu gareshi, Libabatu ta ce, "yaya ka gajine.
Ya kwantar da kansa jikin kujera yana fad'in wlhy kuwa sosaima kuwa, sopy ta kawo masa ruwa, ya tashi yakarb'a yasha yana mata murmushi.
Yagama sha ya mik'o mata kofin, ta karb'a tana fad'in abincifa uncle?, ya ce, "zanci dan wlhy ina jin yunwa.
Sopy ta nufi kichin tana masa dariya, ta ce, "a ajiye a dinining ko akawo nan, ya mik'e yana fad'in kawo nan, sai naci muna hira, amma bari nafara watsa ruwa tukuna.
Ta ce, to.
Sunan zaune suna hira yafito sanye cikin k'ananun kaya, sopy takawo masa abinci, yanaci suna hira.
Da magriba yatafi sallah, sukuma sukayi a gida.
Saida akayi isha'i yadawo, yadawo musu da gasashshen tsire mai dad'i, sukaci suna farin ciki.
Uncle G! ya ce, "oh, Safiyya namanta, albishirinki?, da sauri ta ce, "goro fari tas uncle.
Ya ce, "to saiki kawomin goron sannan, sopy ta ce, "to mikake so?, yay shiru alamar tunani, can yad'ago yana mata wani irin kallo, wanda har yabata kunya, ta duk"ar da kai k'asa.
Uncle G! ya ce, "alawar madara nakeso, ta yi d'an murmushi, dan ta fahimci inda yadosa, ta ce, "to kad'auka ka samu.
Babu wanda ya fahimci inda zancensu yadosa, sai fareeda Dan haka ta had'e rai, tana jin haushi, azuciyarta ta ce, "jara babbu kawai,๐
Ya murmusa, ya ce, "to, Asiya ta haihu d'azu, tasamu d'a namiji.
Sopy ta k'an k'ame Aysha tana murna, ta ce, "uncle yaushe zamu?, ya ce, "to sarkin zumud'i aii k'ya bari sai gobe ko.
Ta ce, "ALLAH yakaimu.
Su aunty hafsat sukace amin.
Saida sukaga kowa ya kwanta sannan suka tafi d'akinsu suma, a d'aki uncle G! ya rungume sopy yana fad'in, yaufa ranar tadaban ce, ta d'ago tana kallonsa, ta ce, "miyasa yau tazama tadaban?.
Ya murmusa, ya ce, "kedai zoki bani alawar madara, sopy ta rufe fuska tana fad'in kai uncle ALLAH karage abinda kakeyi, agaban su aunty kake fad'ar wata alawar madara.
Ya ce, to aii basu ganeba ko?, ta ce, "aiiko sun gane, sundai yi shirune kawai.
Ya jawota saman k'irjinsa yana fad'in, bawani ganewa dasukayi, saidai idan fareeda dan naga tanata b'ata rai.
Sopy ta sumbaci k'irjinsa ta ce, "banida matsala da wannan.
Uncle G! yayi dariya, ALLAH sopy ke muguwace, nakula kwanannan kin sako fareeda a gaba fa.
Sopy ta ce, "niban sakata gababa, nagadai kawai rainin hankalinta yafara yawane.
Nafito ina fad'in bari nad'an lek'o su fareeda suma, d'akin na tura ahankali nashiga, suduka sunyi barci, babu wani mai kwakwkwaran motsi, da sauri nafito, nadawo d'akinsu uncle G!, amma saidai kash harsun rufe d'aki, nadawo baya da haushi, dan naso naga miye alwar madarar da sopy zata bawa uncle G!, dan nima naje nabawa nawa mijin๐๐................โ๐ป
๐Bily๐
๐๐Mrs Abd[12/19, 7:26 PM] mrs bilkisu: 24~November~2016
๐ท๐นNI DA AMINIYATA!!!๐น๐ท
NA BILKISA IBRAHIM๐
๐ถ๐ธ5โฃ3โฃ๐ธ๐ถ
..........Su aunty hafsat suna jin dad'in zama da sopy, to itamadai sopyn gareta hakane, tanajin a zuciyarta idan da haka dukkan dangin miji suke gsky da an zauna lfy a akasar hausa.
"" dan kiyayyar dangin miji tana tasiri wajan ruguza tubalin ginin rayuwar aure, tana haddasa gaba da kiyayya nazumincin family guda biyu, yanasa 'ya'ya da tsanar dangin mahaifinsu, adalilin k'iyaya dasuke nunawa mahaifiyarsu, to ALLAH yasa mu gyara amin.""
Uncle G! ya umarcesu da su shirya yakaisu suyi barka suduka, amma sai fareeda ta ce, "ita bazata jeba, zata zauna agida.
Uncle G! ya ce, "yaza'a abarki agida ke kad'ai ai zaki takura, karki damu babu abinda zai faru sai alakairi, tunda suka fad'a da bakisu sun yafe miki.
Fareeda dai tatsaya tsayin daka akan bazata jeba, haka suka hakura suka barta.
Uncle G! yanaso yayi barci agidan, amma saboda gudin abinda zaije yadawo saiya hakura yafita.
Su sopy suka shirya suka tafi, bayan ummy tazo tayi musu jagora.
Da gudu sopy tashiga gidan tana kiran aunty Asiya, taje ta mamik'e katon jaririn da aunty Asiya ta haifa, wata sabuwar kaunarsa tana ratsata, jitake kamar itama tasamu k'ani ciki d'aya.
Ummy tak'araso da su aunty hafsat cikin d'akin, aunty asiya ta ce, "ALLAH ya shiryaki sopy, shine kikayo gaba kika bar baki abaya.
Libabatu ta ce, "ai bakomai tana murnane, anan suka wuni, akasha fira, su aunty hauwa'u ma sunzo, da zainab da Nafisa, aiko akasha hira kamar sun saba dasu aunty hafsat.
Muna nan zune saiga gayyar 'yan professional writer suma sun iso, sopy tayi matuk'ar farin cikin zuwansu, tashige cikinsu anata shan hira da tambayar ina fareeda ta ce," musu tana gida suka barota.
Sai wajen karfe biyar muka bar gidannan, bayan munci munsha daga mai k'yau, can na hango marakisiyya da madina sunata k'atuwar lauma, nayita harararsu dan karsu bamu kunya, amma ina saida sukaji sunyi nak, harda tambayar sopy wai kozasu sami wanda zasu kaima saratu ta fatima pii, dan karsu basu labari suji haushi akan su basu ciba.
Da haushi ya isheni saina yo waje batareda najira amsar da sopy tabasuba๐๐.
Agajiye suka shigo gida, sun tarar da fareefa a falo tana kallo, tayi musu sannu da zuwa, suka amsa suna zama, sopy ta ce, "fareeda uncle fa??.
Saida ta yatsine baki sannan ta ce, "bai dawoba.
Ko babu komai sopy taji matuk'ar dad'i da faruwar haka, dan dama bataso tabar fareeda da uncle G! agida d'aya su kad'ai, dukda tayi matuk'ar yarda da uncke G! d'in, amma tana tsoron sharrin shaid'an uban had'in tuggu, dakuma fareeda uwar gidansa, uwar cin amana.
Agurguje sopy tayi wanka, tazo ta d'ora abinci, saboda kar uncle yadawo babu abinci agidan, kan kace mi gida ya kaureda kamshi mai dad'i, Libabatu taje kichin d'in tana tsokanar sopy, wai mitake dafa misu su manyan masu gida, sopy tayi dariya tana fad'in ai kune na robar, yanzu ina had'awa na k'arfenne, suka tuntsure da dariya harda tafawa kamar k'awaye, kai jama'a wannan zama yana burgeni, dangin miji kamar danginka.
Sai gab da magriba uncle G! yashigo, agurguje yay wanka yanufi masallaci, sai bayan isha'i yashigo, sannan suma sunyi sallah, yashigo musu da kayan marmari, sukaci abinci suka k'oshi sannan aka shiga hira mai dad'i, saida sha d'aya tayi uncle G! ya ce, "bari suje su kwanta dan gobe sunada makaranta, badan angaji da hirarba kowa yaje ya kwanta.
Da safe da wuri sopy ta tashi tahad'a karin kumallo, suka shirya sukaci itada uncle G!, suka bar musu nasu, sukai musu sallama suka tafi, suma suka bisu da addu'ar dawowa lafiya.
A maranta sopy tana tareda Nadiya, dan yau bataga zalihaba rediyo mai jini.
Haka suka cigaba da karb'ar lectures har zuwa karfe shidda na yamma, uncle G! ya d'akkota suka dawo gida.
Lafiyayyen abinci suka tarar su aunty hafsat sunyi, dan haka suna yin wanka sukaci abinci bayan sunyi salloli.
Haka rayuwa taci gaba da tafiya, kullum sopy sukan biya suga jariri kafin su tafi makaranta, takan had'a musu abincin safe ta gyara gidan kafin su tafi, sukuma suna yin na rana, saidai sopy ta lura fareeda bata aikin komai agidan sai su aunty hafsat, itadai saidai abata taci ta kwanta tayi barci, dan haka faridar tayi wani irin k'yau tak'ara farida kiba.
Sopy bata tab'a tanbayarta miyasa bata aikiba, dan bata bukatar hakan.
Da haka akasha sunan d'an gidan uncle kabeer, yaci sunan baban su sopy wato ibrahim, za'a rinka cemasa khalil, anrak'ashe an kwalle, ansha shagali, fareedama taje wajen sunan, saidai tanata rab'e2 saboda tsoron 'yan uwa saita saka nik'af, ba wanda ya ganeta saisu zainab, suma sai suka shareta sukayi kamar basu ganetaba.
Mukan baruwanmu, danta shagalinmu mukeyi, uncle G! ma sun had'ama abokansu walima dai2 karfinsu, anzo antayasu murnar samu d'a.
Sai wajen sha biyu suka koma gida, kowa yanemi makwanci ya kwanta saboda gajiya.
Da safe da wuri sopy takoma gidan uncle kabeer ta taya kannan aunty asiya aiki suka gyara ko'ina tsaf.
Satinsu libabu biyu sukai haramar komawa gida saboda yara dasuka baro, uncle G! ya had'a musu shatar ta arzik'i suka tafi suna kewar sopy itama tana kewarsu, har kuka tayi konace sukayi, dan har auty hafsat saida ta matse hawaye, shikansa uncle G! yaji babu dad'i, dan zuwan 'yan uwansa ya k'ara masa farin ciki, saboda k'yaunar dayake musu, fareeda kanta saida tad'an matse hawaye saboda sabo, dahaka dai suka tafi suka barmu da kewa๐ญ.
Yau tsawon kwanan su aysha biyu da tafiya, gida yakoma yanda yake, yau babu aiki dan haka sopy taje ganin masu jego, tabar uncle G! yana barci ad'akinsa, fareeda kuma tana falo.
Fitar sopy babu dad'ewa zuciya tashiga zuga fareeda bisaga gurguwar shawara, har zuwa sha biyun rana bata gama aminta da shawarar zuciyartaba, saidai zuciyar tata taci gaba da karanta mata tafsir mai wuyar fassara, ta kalli agogo karfe sha biyu da kwata, tad'an murmusa tanada tabbacin ba yanzu sopy zata dawoba, tamik'e da suri tashiga wanka, tafito ta tsara kwalliya, mudai muna lab'e muna kallon ikon ALLAH, tagama tsaf tad'akko wata yololiyar rigar barci tasa ka, ta feshe jikinta da turare, d'akin uncle G! mukaga ta nufa, kunsan ALLAH nikaina 'yar rahotonku saida numfashina yaso ya d'auke, amma haka na lallab'a nabi bayanta.
Ta shige d'akin tana ran gwad'a, ta maida k'ofa ta datse da key, tabi uncle G! dake kwance saman lafiyayyen gadonsa da kallo, dagashi sai gajeren wando yan barcinsa hankali kwance, dan yasha maganin mura.
Fareeda ta k'awata fuskarta da murmushi tana wani sake gyara zaman rigarta, tabbas yau saita aiwatar da abunda tadad"e tana buru, koda sopy tayi nasarar hanata auren uncle G! tofa yau saitayi nasarar had'a makwanci da ita, dan babu makawa saita saka uncle G! ya bata ruwan dazai gusar mata da k'ishir warta.
Ta taka ahankali harzuwa jikin gadon nasa, ahankali takai hannu zata tab'ashi kamar an ce yafarka, saiya tshi afirgice, cikin tsoro da fargaba yake kallon fareeda babu abunda yake ambata sai ""inna lillahi wa'inna ilairraji'un, "" wallahu galibun ala amrihi, wad'an nan sune addu'oi in dasuke fita daga kan lab'b'ansa, fareeda kuwa tana gabansa tana wani jujjuya jiki da salo2 na yaudara, wanda shaid'aniyar zuciyarta take koyar da'ita.
Adai2 wannan lokacinne kuma sopy tadawo, ta tab'a k'ofar taji arufe, bataso ta tadashi dan haka taje d'akinta ta d'akko wani key d'in, bata damu da rashin ganin fareedar ba, dan atunaninta tana kichin tana girki.
Ji sukai ana bud'e k'ofa, cikin tsananin tsoro da firgici suka maida hankalinsu awajen, sopy ta bud'e k'ofar saidai tuni zuciyarta ta yi tsawa maikama da saukar aradu, ko kwaran kwatsa, binsu take kawai da idanu, dan kallo d'aya zakai musu kaga alamun rashin gsky atareda su............................โ๐ป
Turkashi musu karatu, komai zai faru a wannan gida yau, lallai kila yau sai an kwatanta yak'in duniya nafarko awannan gida. Nima kaina a tsorace nake bare fareeda da uncle G!!!!!!!!!.
Kuyi hak'uri darashin type na kwana biyu.
๐Bily๐
๐๐Mrs Abdus'salam๐๐๐
๐I LOVE YOU MY FAN's๐๐
[12/19, 7:26 PM] mrs bilkisu: 24~November~2016
๐ท๐นNI DA AMINIYATA!!!๐น๐ท
NA BILKISA IBRAHIM๐
๐ถ๐ธ5โฃ4โฃ๐ธ๐ถ
...........Sopy tayi wani wawan tsale ta cakumi wuyan fareeda, wata muguwar shak'a tayi mata irinta mutuwa, idanun fareeda