Showing 15001 words to 18000 words out of 58156 words
yad'an juyo ya kalleta, dan har ya fara tafiya, ki tambaya mana, taji yafad'a ya wuce abunsa.
Sopy takalli zaliha ta ce, "zaliha plz idan kin sani ki rakani mana? Zaliha ta rik'e hab'a rufani ki sayani sopy, sai dai na nuna miki, dan wlhy bakowa yake shiga wannan offece d'inba.
Kamar ya bakowaba ? To dan me??
Saboda maishi baya bari, kinga kina k'ara b'ata lokaci muje na nuna miki.
Sopy tabita tana mamakin yanda yawancin students a d'in makarantar suke shakkarsa,, dukda school d'in ta kasance university gidan 'yanci.
Da wannan tunanin tak'arasa offece d'in da zaliha ta nuna mata,, a tunaninta baya nan dan haka ta dannakai kawai abinta batareda neman izinin shigaba,, tai sauri jada baya dan ga nin sa zaune akujerarsa ya d'ora k'afarsa saman tebir d'in gabansa, yana latsa waya.
Ya d'ago yana kallonta idanunsa sanye cikin glas, cikin rawar murya ta ce, "sorry ser bansan kana cikiba.
Baice mata komaiba , sai dai ya nuna mata tebir d'in dake gabansa, alamar ta ajiye.
Ta ajiye ta juya zata tafi,, sai taji ya ce, "waya baki izinin tafiya?? Ta juyo da sauri tana kallonsa, dan batai zaton da ita yakeba, amma saitaga shima ita yake kallo, tadawo ta tsaya, ya sauke k'afafunsa kasa, ya ce, "bismilla zauna".
Jikin sopy a sanye ta zauna zuciyarta cike da mamakin wannan irin karfin hali haka.
Yakai tsawon minti biyar bai sake bi ta kanta ba yanata latsa wayarsa, saida ya mula Dan kansa, sannan yad'ago yana kallonta ya ce, "SAFIYYA IBRAHIM KABEER ko?
Dukda ba yau aka fara kiran cikakken sunantaba kamar haka , amma saitaji yau sunan yay mata daban tamkar banata ba, domin kuwa ya iya fad'ar sunan,, kamarma yafi kowa iyawa ..................โ๐ป
๐Bily๐
๐๐Mrs Abdus'salam๐๐๐
๐I LOVE YOU MY FAN's๐๐
[12/19, 7:25 PM] mrs bilkisu: 18~October ~2016
๐ท๐นNI DA AMINIYATA๐น๐ท
NA BILKISA IBRAHIM ๐
๐ถ๐ธ1โฃ8โฃ๐ธ๐ถ
...............ya ce, "koba "k"!, baceba???
"Tai saurin fad'in nice ser."
Ya jinjina kai tare da janyo wata takarda yamik'a mata, waye ya rubuta miki wannan????
Sopy takarb'a tana kallon takardar, test d'in ranarce aii, tad'an gyara zamanta, bawanda yarubuta min nice nayi da kaina.
Yad'an tsura mata idanu wannda yasa dole tayi k'asa da kanta domin kunya, shikuma ya murmusa, Karo na farko dana tab'a ganin murmushin sa, yacigaba da kallon takardar Kenan yanzu idan nace ki sake rubuta min zakiyi kamar haka??.
Sopy ta jin jina kai, ta ce, "insha ALLAHU ser".
Ya ce, "good", takarda da biro yabata, nabaki minti goma sha biyar.
Tad'an kalleshi saikuma ta kauda kai, azuciyarta ta ce, "idan kasaba rainawa d'alibanka hankali, to nikam bazan amince ba, taja takardar tana rubuta amsoshin tanbayoyinsa, tagama acikin minti goma.
Yad'an kalleta cike da mamaki, itama kallonsa take, ya danne mamkinsa dan karta kawo masa raini, ahankali ya furta zaki iya tafiya.
Sopy ta mik'e batare da ta tanka masaba, ta fice abinta.
Yabita da kallo afili yafurta miskilanci!!, humm kunji masu karatu shiya manta da nasa miskilancin, ahankali ya kwanta da bayansa ajikin kujerar, hannunsa rik'e da takardar data rubuta yanzu, yaja ajiyar zuciya, ya sumbaci takardar ya lumshe fararen ida nunsa masu suffar ganye.๐
Narik'e hab'a dan mamaki, marak'isiyya ta zungureni aunty bily mikenan??? Naja numfashi wlhy nima bansaniba marak'isiyya, saidai musa ido akansa dan gano miye sirrin zuciyarsa,, amma wannan irin subba da yayma takardan nan aii abin tanbayane?? Marakisiyya ta ce, "lallaikam aunty bily.
Sopy na fitowa zaliha ta tareta, sopy miya faru?? naga kin dad'e, Sopy ta harareta to uwar 'yan son gulma babu komai.
Plz dan ALLAH ki fad'a min nasan hakanan banza bazaki dad'e a offece d'in uncle G! ba, sopy tai d'an tsaki to bawani abubane test d'in jiya yasani na sake.
Ban ganeba??
Sopy tai gaba aii dama ke baki ganewa.
Zaliha tabiyota tana naci, dole sopy tagaya mata yanda sukayi,, zaliha ta ce, "lallai abin mamaki uncle G! kenan, kya k'ara gani indai shine.
:::::::::::::::::::::::::::::::โก yau takasance alhamis sopy tana Zaune da 'yar kazaginta zaliha suna duba wani book, gurin akwai yawaytar d'alibai suna shan iska, k'alilanne suke karatu, domin yawancinsu duk tare suke da samari suna hira, wani gay yak'araso inda suke, yay musu sallama zalihace kawai ta amsa amma sopy ko kallo bai ishetaba kanta yana ga littafai.
Saurayin ya zauna kusada zaliha, yayinda sopy ta mik'e ta canja gurin zama,, saurayin yabita da kallo, zaliha way yaushe k'awarki zata wayene??
Zaliha ta tab'e baki babu rana jamilu! dan ita ra'ayinta daban dana mutane.
Ya jinjina kai yana fad'in tofa, jami'a gidan bankashi.
Zaliha ta kalleshi ta k'yalk'yace da dariya suka tafa da gayen.
Sopy dake kallonsu taja tsak'i irin wannan abubuwanne yasa bata sakarma zaliha fuska dan ta kula 'yar komai da ruwanka ce, tamai da kanta ga karatunta.
D'alibai sunata shan hirar soyayya agurin, sai sopy tazama saniyar ware, dan bata bama kowane saurayi fuskar kusantar taba,, batada abokin hira sai littafi ko waya, saikuma idan sun had'u da zaliha, ko kuma tayi tayin chatting abinta.
Uncle G! Yabi dukkan d'aliban da kallo cikin bak'in ciki, shikam irin wannan halayyar bata burgeshi, domin aganinsa rashin tarbiyya da kamunkai ne yake kai d'aliban maida makaranta wani lambun masoya, yad'anja tsaki tareda k'ara jingina a jikin motarsa, karaf idanunsa akan sopy dake gefe tana karatu, Yay d'an murmushi gsky tana k'ara burgeshi, dan yanason mace mai kamunkai, da rik'e mutuncin kai, ya lura yarinyar tanada tarbiyya dan baitab'a ganinta da wani saurayiba, ya dad'e yana saka mata ido amma haryanzu baiga wani abun aibu a tareda itaba,, saidai yakula muskilace tafad'a aji.
Yazo zai wuce duk yawancin d'aliban suka shiga gaidashi,, amma ita hankalinta nakan littatafai, ko kuma tanajinsu tadai sharesune oho.
Shima ya wuce batareda ya kuma kallontaba.
Haka rayuwa taci gaba da tafiya, karatu yana tafiya yanda sopy ke buk'ata, domin tana fahimtar komai dallah dallah, daga ranar kuma bata k'ara yarda tamakara lecture d'in uncle G! Ba, da duk wani malami,, dan ta zauna ta tsarama kanta lokaci tayanda zai amfaneta harma ya amfani waninta,, matsala d'aya tafara fuskanta shine yanda samarin makarantar suke matsa mata, itakam ayanzu ta tsani halin maza dan tundaga abinda Abdul yay mata tayima maza k'ud'in Goro, tana matuk'ar bak'in cikin namiji ya ce, "yana sonta, amma tana iya bakin k'ok'arinta domin kaucewa dukkan wani namiji, ta maida hankalinta akan karatunta gaba d'aya,, tana kuma k'ok'arin mancewa da abinda ya faru a baya, dukda har yanzu zuciyarta tana k'aunar fareeda, idan tatunata takanji matuk'ar kewarta da begen ganinta, haka son Abdul yana nan azuciyarta amma tana addu'ar ALLAH ya yaye mata sonsa, yakuma mantar da ita shi.
Su fareeda amare, ana gidan Abdul ana shan amarci, sai dai tana fuskantar matsalar yanayin zaman takewar gidan, gidane mai matuk'ar yawa, wanda yatara iyaye da 'ya'ya da jikoki, ga matan yayyensa suna shiga rayuwarta,, tagayawa Abdul amma yak'i d'aukar wani mataki, ga yaran gidan basuda wata cikakkiyar tarbiyya, dan kwata kwata yaran basa respert d'in na gaba dasu, sun raina yayyensu da matan yayyen.
Fareeda tafito daga kichin hannunta d'auke da kula, Abdul yashigo ransa ab'ace, tad'anja baya dan ganin yanda yafad'o babu ko sallama, ya wuceta batareda ya ko kalletaba, asanyaye tabishi zuwa d'aki, yana kwance akan gado yarufe fuskarsa da filo, tasa hannu tacire filon tana fad'in my love! bakada lafiya ne???
Cikin matuk'ar masifa ya ce, "asibiti ne ni.
Tad'anja baya tana fad'in ALLAH yabaka hak'uri.
Ya maida kansa yana fad'in kayane nad'e gammo na d'ora miki, yaja tsaki.
Fareeda ta zauna jagwab saman kujerar madubi, ta rintse idanu tana fad'in na shiga uku kardai ace Abdul zai fara juya min baya, lallai dolene na nemi zuwa gidan aunty sadiya.............โ๐ป
๐Bily๐
๐๐Mrs Abdus'salam๐๐๐
๐I LOVE YOU MY FAN's๐๐
[12/19, 7:25 PM] mrs bilkisu: 19~October ~2016
๐ท๐นNI DA AMINIYATA๐น๐ท
NA BILKISA IBRAHIM ๐
๐ถ๐ธ1โฃ9โฃ๐ธ๐ถ
..............zaliha tak'araso dad'an gudunta, tana fad'in kai sopy shine kika taho kika barni?? Sopy tajuyo tana kallonta, ato naga ke kwalliyace damuwarki , bayan kinsan wannan d'an hayak'in shine zai farayi mana lecture yau.
Zaliha ta ce, "to muje aii akwaima sauran lokaci.
Jikin wata bishiya suka zauna kafin lokaci yayi.
Zaliha ta zunguri sopy, sopy! Sopy!! Ga mutuminki!!.
Sopy ta juyo, waye kuma mutumina? Karaf idanunsu suka had'u a karkashin inuwa d'aya,, tai saurin janye nata dan ganin wajensu ya nufo.
Wad'anda suke wajen suka shiga gaisheshi, yak'araso cikin tak'ama yana sanye da bak'in wando da jar riga, sai zabga k'amshi yakeyi, sajen nan ya kwanta luf luf akan k'yak'yk'yawar fuskarsa, azuciyar Sopy ta ce, "yaukuma k'ananun kaya aka saka".
Jin zaliha tana gaidashi sai itama tadawo hayyacinta, ta gaidashi itama ya amsa da lfy, kowa yazuba musu ido, shima ganin haka sai kawai ya wayance da tambayarsu wacece sakina musa?? Zaliha ta ce, "uncle G! Muma bamu santaba, sopy ko bama ta tankaba, yajuya yana tambayar sauran d'aliban dake gurun, suma sukace basu santaba, yajuya yatafi, yana maijin haushin kansa, way sai yaushe yarinyar nan zata fahimci inda nadosa ne?? Ko sotake saina furta mata da bakina ne?? Yad'anja k'aramin tsaki, yarinyar nan miskilancin tafa yayi yawa, gashi sonta yay masa shigar sauri, batareda ya shiryaba, ya lumshe manyan idanunsa masu suffar ganye๐, ya salam! Yafad'a tareda fitarda huci daga bakinsa.
Office yakoma yazauna, yajingina bayansa da kujera, idanunsa a lumshe tamkar mai barci.
K'ofar aka kwankwasa, ko motsawa baiyiba, saida aka buga sau uku sannan ya ce, "waye"?.
Wata zazzak'ar murya ta ce, "nice!!
Ya d'anja tsaki, ya ce, "kowaye ya shigo, ahankali aka turo k'ofar wata k'yak'yk'yawar yarinya fara tas tashigo.
Ya ce, "kowaye yafad'i abinda yakawoshi!, cikin rawar murya ta ce, "dama dadynane ya ce, "kazo ku gana idan kasamu lokaci.
Yabud'e fararen idanunsa wad'anda sukai d'anja ahanlin yanzu, sai dai har yanzu yana kwance a kujerar, yabita da kallon rainin hankali, miya faru yake nemana?
Ta gyara tsayuwa yanaso kuyi maganane.
Ya jinjina kai, toki sanar dashi yazo shi yasameni dan bana zuwa gidan kowa, kumama inada ayyukan yi masu yawan gaske.
Kuma indai akan maganar damukayi dakene, karma yafara zuwa wajena, ke kuma ina mai k'ara gargad'inki akan kifita hanyata, inko bahakaba zan cigaba da b'ata miki rai fiyeda yanda kike tsammani.
Yanuna mata hanyar fita, zaki iya tafiya dan inada aikin yi.
Ta marairaice fuska tamkar zatayi ihu, ta ce, "plz uncle G! ka daure muyi magana dan mu fahimci juna, wlhy ina tsananin k'aunarka, ka daure kasoni, nayimaka alk'awarin zan kasance yanda kake buk'ata, wlhy nayi maka alk'awari.
Uncle G! Yataso daga kwanciyar dayayi ajikin kujera, yad'an tsura mata idanuwa bahijja!! kamar yanda nafad'a miki tun farko, ba soyayya takawoni makarantar nan ba, bake kad'ai kika tab'a cewa kina sonaba, kuma suma amsar dana baki ita nake basu, ina mai baki shawara daki hak'ura kema kamar yanda suma sauran suka hak'ura,, kuduka bakwa cikin irin matar danake son aura, dan haka ina mai baki shawarar ki sama ranki hak'uri, daga yau kuma karki sake zuwa office d'ina, danni ba'a shigo min office saida dalili, kuma dalilin ma wanda yashafi karatu,musamman ma mata, ya nuna mata hanya zaki iya tafiya.
Taja numfashi idansu, har sun iya hakura da kai toni tabbas bazan iya rabuwa dakaiba, kaine mutum nafarko dana fara so kuma kaine na k'arshe, zan sanar da mahaifina yazo kamar yanda ka buk'ata, tunda kai kace bazakajeba, tana gama fad'a tafice abinta.
Shima tsaki yaja, yamik'e yana fad'ar ashe zaki mutu da son nawa kenan, dan har abada bazan sokiba, littatafai ya d'iba yafice shima, dan ya gudanar da lecture.
Ajinsu sopy yanufa, kamar yanda yasaba haka ya aikata, yahana makararru shiga, babu b'ata lokaci yashiga gudanar da lecture.
Sopy agaba take zaune, duk d'agowar datayi sai sun had'a ido da uncle G!, dan haka ma saita daina kallon inda yake, amma tanaji ajikinta har yanzu yana kallonta, kamar yanda yasaba yauma ya ce, "zaiyyi test.
bayan sun gama test yabisu yana karb'a, yazo karb'an na sopy, saida yafaki idon sauran d'aliban sannan ya ajiye mata wata takarda, ya karb'i ta hannunta, da ido ya nuna mata takardar daya ajiyemata, batace komaiba tad'auka kawai.
Bayan fitarsa kowa yafito, kafin ashiga wata lecture d'in.
Sopy batabi takan takardar uncle G! ba, dan bata d'auketa dawani muhimman ciba...............โ๐ป
๐Bily๐
๐๐Mrs Abdus'salam๐๐๐
๐I LOVE YOU MY FAN's๐๐
[12/19, 7:25 PM] mrs bilkisu: 20~October~2016
๐ท๐นNI DA AMINIYATA ๐น๐ท
NA BILKISA IBRAHIM ๐
๐ถ๐ธ2โฃ0โฃ๐ธ๐ถ
............fareeda al'amura sun fara canja mata, dan yanzu Abdul yafara canja yanayin zaman nasu, ga masifar datake fuskanta wajan ummarsa, dan ummar Abdul masifafface, dukkan matan gidan tsoronta takeji, saboda masifarta.
Ta kula tunda likita ya ce, "tanada shigar ciki, tafara fuskantar matsala wajen Abdul, yafara nisantarta, Baya yin fira da ita yanzu, bakuma yadamuwa dasu kwana gado d'aya.
Lamarin yana damunta, gashi yahanata zuwa gidan aunty sadiya, ya karb'e wayarta tuni, yauma tana zaune ta yi tagumi, babu abinda take buk'ata sai nama,, tasan kuma Abdul bazai saya mataba, ga cikin nata mai shegen tsurfa da kwad'ayi, ta cije leb'e hawaye suka zubo mata akumatu, lallai idan har rayuwa tajuya mata baya to kuwa taga ta kanta, dan yanzu batada wanda zata tunkara tasamu sauk'i, aminiyarta tayi mata nisa, nisa kuma mai tarin yawa, tasan yanzu babu wadda sopy ta tsana kamar ita, garashin 'yan uwa, ga rashin iyaye, tafashe da kuka, kuka take tamkar ranta zai fita, nikam na tab'e baki dan wlhy ko kad'an banji tausayin taba, na ce, "ni!, barima natafi wajen k'awata sopy, nagano muku takardar da uncle G! Yabata.
Sopy zaune akatifarta, gabanta kankanace yanke a filet, tad'akko littatafanta tana dubawa, hankalinta akwance, zuwa can tabud'e book d'in data saka takardar uncle G!, madina ta tab'ani yauwa aunty bily tad'akko book d'in data saka takardar nan, ALLAH dai yasa takaranta muji, na ce, "to amin deena!.
Tana bud'ewa takardar ta fad'o, ta d'auka tana jujjuyawa, dan ta manta kota miye, harta cigaba da karatunta saikuma ta d'akko takardar tana d'an tadubawa.
Ahankali tabud'e, takardar sai k'amshi takeyi, tad'an murmusa, sannan tafara karantawa kamar haka.
๐Assalamu alaikum. ๐
Gaisuwa dafatan alkairi, ina fatan wannan takardar zata sameki yayin da kike cikin nutsuwarki.
Ina buk'atar ganinki a office d'ina gobe idan ALLAH yakaimu, karkuma ki shanyani, ga kuma nomber na nanan, da daddare ki kirani ko kimin filashin, dan ina buk'atar ganin nomber d'inki.
๐kihuta lafiya๐
Youseef Hussain Ahmad Gurum. {Uncle G!!}.
Sopy ta d'an tab'e baki, lallai kam, saidai kayi hak'uri dan bazan iya aikata ko d'ayaba aciki, takai takardar wajen hancinta tashak'i k'amshi ta lumshe mayan idanunta.
Madina ta ce, "tofa kodai itama ta kamu ne??
Na ce, "to madina waye yasani, saidai mucigaba da kallon ikon ALLAH.
cigaba tayi da karatunta, amma lokaci2 takan kalli takardar tayi murmushi.
..yauma kamar yanda tasaba tashirya tsaf, cikin zani da riga na jan les, tasaka hijjabinta har k'asa, tad'auki jakkarta tafita, kai tsaye aji tanufa dan tanada lecture a dai dai wannan lokacin, bayan sungama karb'ar lecture d'in yawancin d'aliban suka firfito, itakam tana zaune abunta, saida taji zafi yafara isarta sannan ta tashi tafito, dan yau bataga 'yar kazaginnataba wato zaliha, gurin data saba zama tazo tazauna, amma yau ba karatu takeba, waya tad'akko tafa chatin da uncle kabeer, sai faman murmushi takeyi wanda yake k'ara k'awatar da k'yawun fukarta.
Uncle G!, dake tsaye ajikin wata bishiya yaja ajiyar zuciya tareda lumshe idanu, karfa yarinyar nan ta zautashi, dan wlhy jiya dak'yar ya iya barci, yadad'e yana jiran kiranta, amma har yay barci bata kiraba, yasan kuma takaranata letter d'insa amma tashareshi, tacigaba da harkokinta hankali kwance, shi gashi nan tabarsa cikin damuwa, dan wata irin soyayya yake mata mai tsanani, wadda yake ganin 'yammatan!! dasuke cewa suna sonshi!! tasu soyayyar ta k'aryace, ya rintse ido yabud'esu akanta, wani k'ayataccen murmushi tasaki wannada yasa kumatunta lotsowa, shima saiya murmusa.
Gaba d'aya yinin yau zaman jiranta yazauna yi, amma batazoba, gashi yau bashida lecture dasu, duk sanda aka kwankwasa k'ofar office d'insa saiyayi tsammanin itace, amma sai anshigo yaga sab'anin hakan, har zuwa yamma batazoba, ya tattara yafita shima cikin damuwa, dan yaso sugana.
Itakam sopy tana sane, amma ta share tacigaba da sabgogin gabanta, tun wajen k'arfe 3:30pm tagama lectures nata, amma tayi tafiyarta d'aki batareda tabi takan uncle G! ba, duk da tasan yana office yana jiranta, dan duk yau bata gansaba ma.
Yau tsawo kwana biyu da uncle G!, yabama sopy letter domin buk'ar ganinta, dakuma bata izinin kiransa a waya, amma bata aikata ko d'ayaba, dukda abin yana cikin ranta, amma ta danne ta nuna baidameta ba, yauma data kasance juma'a kuma bai shigo musu lecture ba, gashi tana shirin zuwa gida weekend, dan haka tashirya bayan gama lecture karfe 11:15am tayi tafiyarta, lokacinma uncle G! Bai shigo school d'inba.
Bayan shigowarsa yayta baza idanu dan son ganinta, amma ko alamarta bai ganiba, baimaga k'awartataba zaliha,, shikam baya son tanbaya, dan kar akawo masa raini, dole yahak'ura yabarma monday, dan yaci alwashi ranar monday kobata nemeshiba tofa shi zai nemeta, dan bazai iya rik'e sonta azuciyarsaba, batareda ya sanar da itaba, domin sonta yayma zuciyarsa baban kamu wanda babu yanda za ayi ya iya hak'urin rik'eshi, shima mota yashiga yanufi gida...................โ๐ป
๐Bily๐
๐๐Mrs Abdus'salam๐๐๐
๐I LOVE YOU MY FAN's๐๐
[12/19, 7:25 PM] mrs bilkisu: 21~October~2016
๐ท๐นNI DA AMINIYATA๐น๐ท
NA BILKISA IBRAHIM ๐
๐ถ๐ธ2โฃ1โฃ๐ธ๐ถ
...........safiyya ana gida anashan weekend, inna tayi farincikin ganin yanda sopy ta canja, tasaki jikinta sosai sai dai haryanzu tananan arame, dan bata