Showing 33001 words to 36000 words out of 58156 words
dukda tsakura takeyi kuma a kunyace takeci, bai kuma ce mata komaiba yacigaba da kallonsa yana cin abinci.
☆☆☆☆☆☆☆☆☆
Da daddare ya tarar da ita a d'akinta tagama shirin barci harma ta kwanta, ya ce, "taso muyi sallah, saida tayi k'asa da kai sannan ta ce, "ina fashin sallah.
Ya ce, "okey, dama ya tanbayane dan ya tabbatar.
A zatonta d'akinsa zai kwana amma saitaga ya hawo gadon ya kwanta kusada ita, ya jawota jikinsa ya rungume, to ba yadda zatayi tunda babu damar korarsa, saita maida kanta ta kwantar akan k'irjinsa ta hau barci.
♡♡♡♡♡♡♡♡
Rayuwa mai dad'i akeyi agidan uncle G dukda har yanzu babu abinda yashiga tsakaninsu, amma suna mutunta juna kuma uncle G yana nuna mata soyayya, danma kunyarsa datakeji tana sashi k'in yimata wasu abubuwan.
Kullum aunty Asiya saita turo mata kalar girkin daya dace tayi masa ta whatsapp, dan haka take girki mai dad'i da gamsarwa, ta kuma gyare gidan tsaf, uncle G yana jin dad'i dan yanason mutum mai tsafta, kullum sai tayi bak'i 'yan anguwar suna shigowa ganin d'aki da kuma amaryar kanta, kunsan amarya da farinjini, har yara da 'yammata ba a barsu abayaba, kuma duk wanda yazo saita kulla masa cin cin da dubulan, dan sopy bata da rowa, abokansama suna zuwa wasu harda matansu, su aunty Nafisane dai har yanzu babu wanda yazo acikinsu, har aunty Asiya datake kusa, garama uncle kabeer yazo sau d'aya shima da daddarene, kuma bai dad'eba yatafi...............✍🏻
💞Bily💞
💞💞Mrs Abdus'salam💞💞💞
💞I LOVE YOU MY FAN's💞💞
[12/19, 7:25 PM] mrs bilkisu: 3~November~2016
🔷🔹NI DA AMINIYATA!!!🔹🔷
NA BILKISA IBRAHIM💞
🔶🔸3⃣7⃣🔸🔶
............yau kwananta biyu da fara sallah, amma tak'i nunawa uncle G! hakan, batayin sallah saiya fita, kokuma ta kulle d'akin sannan tayi, to gashi gobe zai koma aiki, dan hutunsa ya k'are, suna zaune a falo suna kallon labarai sai sukaji ana kwan kwasa gida, uncle G! ya kalli agogon dake manne a bangon falon, ya ce, "to waye da darennan?, sopy ta ce, "bari naje na duba.
Ya ce, "A'a yizamanki barinaje.
Ta ce, "to.
Yaje ya bud'e wasu 'yammatane su biyu suka gaisheshi, ya amsa fuskarsa babu walwala, dan kunsan uncle G! A gaban 'yammata baya sakin fusaka, ya ce, "yaya dai?, ganin yanda ya had'e fuska sai suka daburce d'aya ta ce, "dama yarinyace tafita gida tun d'azu shine muke tunanin kota zo nan?.
Ya ce, "A'a, babu kowa nan gidan.
Sukace to mun gode saida safe.
ALLAH yakaimu yafad'a yamaida get d'in ya rufe, ya koma cikin gida, sopy ta ce, " Suwaye? ALLAH yasa dai lafiya?.
Uncle G! yazauna yana fad'in wasu 'yammatane wai yarinya suke nema, yarinya kuma anan gidan?, ya ce, "haka dai sukace.
Sopy ta ce, "sudai tasuce ta kawosu zasuce, nima na fahimci haka aii.
Wayarsa ta shiga k'ara alamar kira, ya d'auka, cikin zolaya ya ce, "surikina yagarinne?
Uncle kabeer ya ce, "haba malam daka d'aukeni sikin aii saika kwantar da murya.
Uncle G! yay dariya, aii dan baka kusane amma atsugunne nake yanzuma.
dariya sukayi gaba d'aya, uncle kabeer ya ce, "sonake nace maka yakamata gobe muje wajennan damukai magana ranar.
okey to babu damuwa saimuje, ina uwar biyu?, uncle G ya tanbaya.
Wlhy kaganta nan tana tayimin shagwab'a kasan mai ciki sai ahankali, ina my sweet Sopy?.
tana nan lfy gata nan kusadani.
To kagaishemin da ita saida safe, zataji ALLAH ya kaimu goben lfy.
Bayan ya ajiye wayar ya kalli sopy, kabeer yana gaisheki, ta turo baki cikin shagwab'a ta ce, "shine baice abaniba.
Yanda tayi maganar saita burgeshi, ya ce, "to bari nakira shi saiku gaisa, karkiyi kuka 'yar gatan uncle kabeer, zoki karb'a wayan.
Azatonta da gsk yakeyi, saita tashi taje wajensa, tana k'ok'arin durk'usawa k'asa, ya jawota jikinsa, yana fad'in kinga wajen zamanki nan.
Ta ce, "to kira mini uncle d'in mu gaisa.
Yaja hancinta aikece uncle d'in, bawani kiranshi dazanyi, tashima na aikeki, ta tashi tsaye, saida yayi mata wani shu'umin kallo sannan ya ce, "yauwa je d'akina ki d'akko min ALKUR' ANI yana nan gefen gado.
sofy ta ce, "to, shaf tamanta shirinta, bata kuma gane manufarsa ba, tanufi d'akinsa ta d'akko Alkur'ani, ya karb'a yana wani shu'umin murmushi mai kamada na mugunta, saman tebir ya ajiye Alkur'anin ya ce, "Sopy dama kin fara sallah?.
Gabanta ne ya fad'i rasss dan tanbayar tazo mata a bazata, ta daure ta ce, "e, ya kwanta a kujerar yana wata 'yar dariya ta mugunta.
Sopy ta ce, "mugu d'an masa.
Daga nan kallo suka cigaba dayi, saidai kallo d'aya zakayima sopy kagane tana cikin wani hali mai kamada tsoro.
K'arfe goma dai dai ya mik'e yana fad'in tashi muje mu kwanta dare yayi, Sopy ta mik'e jiki a sanyaye tayi gaba yabita abaya yana mata gwalo😜.
Bayan sun shiga d'akinta ya ce, "ki sameni a d'akina yau acan zamu kwana, yafice abinsa batareda yajira amsartaba , tabishi da kallo kamar zata fasa ihu.
Ba yanda zatayi dole tayi sabon wanka tayi shirin barci, tad'an dad'e tana sak'a wasik'ar jakai, zuciyarta cike da tsoro da fargaba, ya lek'o ya ce, "wai har yanzu baki gamabane?, ta mik'e kamar wadda kwai ya fashewa a ciki.
Ad'akinsa ya ce, "tabiya shi suyi sallah, raka'a hud'u sukayi yayta kwararo musu addu'oi, iyakar sopy ta rink'a cewa amin, ya dafa kanta yay addu'a harda 'yan kwallansa, a zuciyar sopy ta ce, "namiji da kuka?.
Bayan sun idar ta linke sallayar, ya canja jallabiyarsa zuwa kayan bari, yajuyo yana kallonta bazaki cire hijjabin bane?, ko bakijin zafi.
Ta d'aga kai alamar e, yay d'an murmushi a zuciyarsa ya ce, "duk dai wayon amrya sai ansha manta, yak'araso ya zauna kusada ita yakama hijjabin ya cire, tad'an takure jikinta kamar maijin sanyi.
Ya ce, "inga fuskarki kamar wani abu a saman idonki, ta d'ago fuska batare da wani tunaniba, ya kama fuskarta da hannu biyu yakai bakinsa kamar zai hure mata abun, bata ankaraba taji bakinsa a cikin nata, kissing d'inta yakeyi cikin kwarewa, ahankali ya kwantar da ita saman gadon, dahaka hannuwansa suka fara shiga inda baitab'a zuwaba, Sopy tafara hawaye, nidai ganin uncle G! yau dgske yake, yasa nayo waje abina, dan kar kallon kurullar yayi yawa🙈😜..................✍🏻
💞Bily💞
💞💞Mrs Abdus'salam💞💞💞
💞I LOVE YOU MY FAN's💞💞
[12/19, 7:25 PM] mrs bilkisu: 4~November~2016
🔷🔹NI DA AMINIYATA!!!🔹🔷
NA BILKISA IBRAHIM💞
🔶🔸3⃣8⃣🔸🔶
...........Safiyya yau anzama cikakkun mata, saidai tasha wahala sosai sai kuka takeyi, uncle G ya rugumeta yana lallashi da sa mata albarka, ya kwantar da'ita ahankali ya ce, "bari nayi wanka sai kema kiyi.
Bayi yashiga dominyin wanka zuciyarsa cike da farinciki irin wanda baitab'a shigaba a rayuwarsa, lallai aure rahamane kuma ni'ima ne.
Sopy taja bargo ta kudundune danjin sanyi yana shigarta, wani wahalallen barci ya d'auketa, uncle G! yafito yana fad'in my sopy tashi kiyi wankan, ganin tayi shiru saiya hawo gadon, ya yaye bargon saiyaji jikinta da zafi rau, gashi dukta jik'a filon da hawe da zufa, yad'agota zuwa jikinsa yana fad'in sorry Safiyyana, ALLAH yay miki albarka kinji, ya azurtamu da zuri'a tagari, zanin gadon yasa ya goge mata fuskarta, ya kwantar da'ita, yanufi kicin.
Shayi ya had'o mata mai kauri, yatada ita zaune, ta ce, "itafa ta k'oshi, ya ce, "daure kisha kinji, saikisha magani mukwanta, lallab'ata yaytayi tad'ansha kad'an, ya bata magungunan zazzab'i, sannan ya rungume matarsa suka shiga barci mai dad'i.
☆♡☆♡☆♡☆♡☆♡
Bai san yayi b'arnaba saida safe, dan sun makara, yatada ita dan tayi wanka tay sallah, amma takasa tafiya, tanayin taku d'aya taji wani azababben zafi ya ratsa har kwakwalwarta, cikin shagwab'a ta ce, "woyyo ALLAH na inna.
Uncle G ya k'araso da sauri ya tallafota zuwa jikinsa ya ce, "yaya dai?, cikin shagwab'a ta ce, "zafi.
D'aukarta yayi cak yakai bayi, ruwan zafi ya had'a yaymata gashi, tanata zuba masa shagwab'a, ya taimaka mata tayi wankan tsarki, sannan ya nad'ota a tawul kamar wata jaririya.
Tana idar da sallah ta kwanta akan sallayar dan barci takeji, uncle G! yashigo da tire a hannu ya dire agabanta, sopyna tashi kiyi break saiki kwanta gaba d'aya, da k'yar ya lallab'ata taci soyayyan kwan da shayi, bai takurataba dan lallab'ata yakeyi, bayan tagama ya kwashe kayan yazo ya canja zanin gadon, sannan ya d'auketa ya maidata saman gadon taci gaba da barcinta, shima ya kwanta yarungume kayarsa suka lula duniyar barci.
Sai k'arfe d'aya da wani abu suka tashi, sopy ce tafara tashi, ta lallab'a ahankali ta gudu d'akinta, uncle G! yana kallonta yay murmushi kawai dan ganin yanda take sand'a, shima tashi yayi yashiga wanka.
Itama sopy ad'akinta wankan tashiga, dan har yanzu jikinta ciwo yakeyi, tafito tayi kawlliya mai sauk'i tasaka doguwar riga ta atanfa, tana tsaye gaban madubi tana fesa turare uncle G! yashigo, ya rungumeta tabaya yana fad'in kingudo kin barni to gani na biyoki aii.
Tai kasa da kai dan kunya, ta ce, "ina kwana?, lafiya law sopyna, yaya kuka?, da kiransu inna da baba.
Hannu tasaka ta b'oye fuskarta🙈, dan takula zolayarta yakeyi, ya ce, "bari naje massalaci nadawo
Ta ce, "to adawo lfy, karfa ki dafa komai zanzo mana da abinci, dan yau ranarkice Autar inna.
Ita dai murmushi kawai take, amma kunya ta hanat yin magana.
Babu dad'ewa yadawo musu da abinci, lokacin sopy ta gyare gidan ta bad'eshi da k'amshi, da kansa yarink'a bata abincin, ita kuma tana zuba masa shagwab'ar datake k'ara masa sonta.
uncle kabeer yakirashi ya ce, "subar tafiyar sai gobe.
aii dama surikina dole abarta sai goben, dan dama zankiraka, yau babu mai ganina a waje.
Kai mutumina saboda mi? Uncle kabeer ya tanbaya.
A'a, basai kajiba kaidai abar kaza cikin gashinta kawai goben ma had'u.
ALLAH yashiryaka youseef kazama marakunya yanzu.
Uncle G yay dariya, idan yatashi ya shiryamu tare nida kai, suka tuntsure da dariya kowa yakashe wayar.
Haka uncle G yacigaba da tarairayar sopy awannan rana, komai shi yake mata, sopy ta ce, "a zuciyar wato su maza abinda suke so kenan?.😜....................✍🏻
💞Bily💞
💞💞Mrs Abdus'salam💞💞💞
💞I LOVE YOU MY FAN's💞💞
[12/19, 7:26 PM] mrs bilkisu: 4~November~2016
🔷🔹NI DA AMINIYATA!!!🔹🔷
NA BILKISA IBRAHIM💞
🔶🔸3⃣9⃣🔸🔶
................JAMA'A!!! yakamata mu way wayi fareeda amaryar Abdul😜,
Saida na d'an lek'a saboda gudun jarabar ummar Abdul sannan nashiga, ba kowa atsakar gidan sai yara daketa wasa, ban kula kowa ba nashige abina, dan yaran gidan ba kunya suka cikaba, atsakar d'aki na tarar da fareeda tayi d'ai d'ai, sai dai kallo d'aya zaka mata kagano tana cikin damuwa, dan kuwa tarame tayi bak'ik'k'irin sai dogon hanci da idanuwa gwalo gwalo, sai ciki ritsitsi a gaba.
Ta tashi da sauri dan jin sallamata, tana ganina tasa kuka yauwa bily! wlhy nayi farincikin ganinki, dan ALLAH ki taimakeni wlhy Abdul zai kasheni a gidannan, ga kowa ya tsaneni bily! plx ki taimaka min.
Na zauna ina fad'in fareeda! wane irin taimako kikeso in miki, kindai san halin mijinki da surukarki.
Bily! wlhy idan baku taimakeniba kasheni zasuyi yanzu haka tun jiya cikina da bayana suke ciwo amma yak'i kaini asibiti, tunda akayi bikin Safiyya! al'amura suka k'ara lalacewa, ya ce, "yanda narabashi da Safiyya! to nima bazanyi farinciki ba a gidansa, ta rushe da kuka mai tsanani.
Kamar daga sama Abdul! yafad'o d'akin, yabini da kallon rainin hankali, wayke bily! kike kowa? Banace karna k'ara ganinki a gidannanba ne?.
Na ce, "haba Abdul, kaiwa "ALLAH DA MANZONSA", kabari na taimakawa fareeda! kaga batada lafiya, kasan kuwa mai ciki saida kula.
Harara ya watsa mini, cikin fushi ya ce, "wlhy idan baki bar gidannanba zan karya miki k'afar dama.
Na zaro ido waje😳, A'a, Abdul name dazan zauna ka karya min k'afar dama, ka cuci mijina!!, kaga tafiyata, fareeda! ALLAH yabaki lafiya, nai waje.
Abdul! yaja tsaki yana fad'in bak'ar banza kawai, na ce, "oho nagodema "ALLAH" dayayini haka, aii fari bashine k'yauba.
Ina fita yashiga jibgar fareeda! Kamar ALLAH ya aikoshi, dan ubanki banace karna sake ganin wani naki a gidannanba, koda kud'in ubanki muka gina gidan?, dukanta yake kamar yasamu jaka, itako sai ihu takeyi, nanko jini yafara ambaliya, yau dai ansamu ummarsa tashigo wajen, ta ce, "Abdul mitayi makane?.
Umma kibari na kashe shegiyarnan tunda iyayenta ma ba sonta sukeyiba, dak'yar umma ta karb'eta.
Ina tsaye a k'ofar gida tausayin fareeda! duk ya cika min ciki, sainaga an kwasota kamar kayan wanki jini nata kwarara, ko numfashin kirki batayi.
Mai adai daita suka tare, suka tafi asibiti.
To fareeda tsuntsun d'ai da yaja ruwa shi ruwa kan doka,, kowa kuma yataka rawar wani tofa yarasa filin taka tasa,, ALLAH dai ya shirya.
☆ ☆ ☆ ☆ ☆ ☆ ☆ ☆ ☆ ☆
Agidan uncle G! Kam Sopy sai shan tarairaya take, yanzuma suna falo zaune suna hira, kan sopy yana saman cinyar uncle G!, hannunsa na shafa gyararren gashinta daketa tashin k'amshi.
Cikin murya mai dad'i da taushi ta ce, "uncle G!!, ya ce, "Na'am Sopyna ya akayi?, tai shiru dan tana jin shakkar fad'ar abinda ke ranta, yad'an lek'a fuskarta ya ce, "miye damuwarki amaryata?.
Tasa hannu tarufe fuska dan jin kunya, yay 'yar dariya sopyna ai kunya ta k'are kuma, yanzu an wuce wajen, dan Safiyya! tazama youseef!, youseef! yazama safiyya! koba hakaba?.
Ta ce, "hakane"
Ya ce, "ato.
Fad'imin kome kikeso indai baifi k'arfinaba zan mikishi.
Ta ce, "komiye?.
Ya ce, "e.
Dama maganar komawata makarntane dan ALLAH yaushe zan koma, kaga anata wuceni a karatu.
Sai da yad'an murmusa sannan ya ce, "to, kibari saikin warke, saiki koma, tunda nima jibi zan koma aiki, hutuna ya k'are.
Saida ta shagwb'e murya sannan ta ce, "ALLAH nifa lfy ta k'alau.
Kai sopyna fad'i gsky dai, kecefa d'azu kikace min jikinki duk ciwo yakeyi harda kuka kuma.
hannu tasa ta rufe fuska tana dariya, ya ce, "ato, kedai kika fad'a da kanki, dan haka kibari sai nestweek sannan mun k'ara shan amarci saiki koma.
b'oye fuskarta tayi acinyarsa, tana fad'in kai uncle ALLAH kana bani kunya.
Ya d'ago duskarta yana murmushi to bani kunyata sopyna.
Ta ce, "to, bayanzuba.
Ya ce, "nikam yanzu nakeso, yay kissing d'in goshinta, ta runtse ido kam dan kuwa sumbar ta shigeta.
Ya ce, "sopy matsoraciya mai kuka, dan ALLAH uncle kayi hakuri karka min da zafi, wayyo innata baba kazo ka taimakeni, yafad'a yana kwaikwayon muryarta.
D'aki ta nufa da gudu, dan taga zolayar tayi yawa.
Koda sukazo wajen kwanciya saitaita d'ari d'ari dashi, dan tsoron kar abinda yafaru jiya yasake faruwa, uncle G! ya rungumeta yana fad'in kwantar da hankalinki sopyna babu abinda zan miki barci zamuyi, ita dai tayi shiru amma zuciyarta cike da tsoro, ya cire mata rigar barcin dake jikinta way haka yakeso sukwana.
Bargo yaja ya lullub'esu ya cika hannuwa da🙈kundai gane, sukayi shiga barci mai dad'i...................✍🏻
Assalamu alaikum, ina mik'o d'unbin gaisuwa ga masoyana a duk inda kuke, da godiya mai tarin yawa, ngd da bibiyar books d'ina da kuke yi, harma wad'an da suka fara karantawa yanzu, luv u oll😂😂😂👍🏻.
💞Bily💞
💞💞Mrs Abdus'salam💞💞💞
💞I LOVE YOU MY FAN's💞💞U MY FAN's💞💞...✍🏻
💞Bily💞
💞💞Mrs Abdus'salam💞💞💞
💞I LOVE YOU MY FAN's💞💞
[12/19, 7:26 PM] mrs bilkisu: 4~November~2016
🔷🔹NI DA AMINIYATA!!!🔹🔷
NA BILKISA IBRAHIM💞
🔶🔸4⃣0⃣🔸🔶
.............Yau tsawon kwanan fareeda uku a asibiti, ta haihu amma d'an baizo da raiba, kuma tun randa su umma suka kaita asibitin basu sake way wayarta ba, yau kuma tana tashi tayi gamo da takarda saki uku a gefen gadonta, kuka take rurus tana dana sanin hali irin nata, yau ga wanda ta fifita akan iyayenta ya gujeta, ta raba zuminci mai dank'o da kusancin dake tsakaninta da aminiyarta saboda Abdul, ta cutarda masoyiyarta saboda Abdul, ta yaudari abar k'aunarta saboda Abdul, taci amanar aminiyarta saboda Abdul, amma yau yarasa abinda zai saka mata dashi sai saki uku, sakin wula k'anci da toxarci, itakam ta shiga uku yanzu wazata dosa, tasan daga iyayenta har yayyenta babu mai saurarenta, tasan babu wadda suka tsana kamar ita ahalin yanzu, takuma rushewa da kuka mai tsuma rai, wata sister tashigo tana fad'in baiwar ALLAH lfy kiketa kuka haka?.
Fareeda ta ce, "babu komai.
Okey sister tafad'a, dama an sallamekine, dan wani mutumi yazo yabiya kud'in.
Fareeda ta ce, "to ngd, ta had'a inata inata tabar asibitin, zuciyarta cike da bak'in ciki, dan bata san inda zata nufaba, tasan ko giyar wake tasha bazata fara zuwa gidansuba, Dan mahaifinta ya gindaya mata sharad'i akan zuwan irin wannan ranar, takuma amince saboda lokacin giyar son Abdul tana kwasarta, lokacin da idanunta suka rufe ta manta da zuwan irin wannan rana, yauga ranar tazo mata batareda taci ribar abinda ta shukaba, saima asarori data tafka marasa adadi, wanda bazasu lussafuba, haka tacigaba da tafiya tana zubar da hawaye batarda tasan inda ta dosaba, ga jiri na d'ibarta saboda yunwa dan ta manta rabonta da cin abinci, ji kake wani kuwwwwwwww kacammmmm!!!!!, wani mai mota ya b'arar da ita a titin, da sauri mai motar yafito yana salati, kan kace mi mutane sun fara taruwa a wajen, mai motar ya ce, "a taimaka masa yasakata a mota, asibiti ya nufa da'ita cikin hanzari.
♡¤¤¤¤¤♡¤¤¤¤¤♡¤¤¤¤¤¤¤♡
Sopy tanata safa da marwa dan tun d'azu take kiran uncle G! Yak'i ya d'aga, ta kira uncle kabeer ya ce, "basa tare, aii saita k'ara rud'ewa, can taji ana kwan kwasa k'ofa tatafi da sauri ta bud'e, saitaga uncle G!, cikin