Showing 3001 words to 6000 words out of 58156 words

Chapter 2 - Ni Da k'awata HAUSA NOVEL

02 Dec 2024

4833

itakuma zata sayo magani ne.
"Ayya sorry fareeda ALLAH yak'ara sauk'i."
Amin fareeda tafad'a tana fari da idanu.

Abdul yakalli agogon hannunsa gimbiyata yakamata ki wuce dan zaki makara karkisha bulalar makarafa.
Sopy tad'an murmusa gskyar ka habibina dan yasayyadi yananan abakin get, bari nawuce kasan idan ina tare dakai nakan manta kowa da komai.
" nima haka gimbiyata Abdul yafad"a yana kashe mata ido d'aya,,, Adam yace" kuna sha aninku masoyan zamani,, itakam fareeda tayi kicin kichin da rai kamar zata fasa ihu,, sopy ta tab'ata sister barina wuce saina dawo ALLAH yak'ara sauk'i.
"Amin tafad'a ranta a dagule"
Abdul yace" aii barima mu kaita k'yamis aduba miki ita.
Yawwa habibina nakwa gode maka,, bari nawuce sai da daddare mun had'u.
"To shikenan ALLAH ya kaimu my lovely wife.

Abdul yadawo da kallonsa kan fareeda bayan b'acewar sopy,, fareeda tad'anja k'aramin tsaki mara sauti,, Abdul yay saurin fad'in lfy?? Fareeda taid'an yak'e wlhy jinai kaina ya sara.
Okey sorry to muje ko??
Adam yace" aii ni inaga anan zamu rabu, dan wlhy abba ya aikeni amma sai yanzu natuna, kuje da daddare zamu had'u insha ALLAH fareeda ALLAH yak'ara sauk'i,, saida daddare idan munzo tad'i.
To Adam nagode ALLAH yakaimu daren.
""Amin adam yafad'a,, sukai sallama yatafi suma suka tafi.

Tafiya suke cikin nutsuwa kowa da irin tunanin dayakeyi azuciyarsa, har suka isa k'yamis d'in sadiq amma k'yamis d'in arufe.
Abdul yace" inaga saimunje k'amis d'in Rufa'i fa,, kozaki iya??
Tai murmushi babu damuwa muje nida nake neman lfy.
Shima murmushin yayi,, to shikenan muje.
" sun isa k'yamis d'in Rufa'i aka bama fareeda magun guna,, Abdul yabiya suka fito,, saida sukaje bakin titi fareeda tace" Abdul idan bazaka damuba inason muyi wata magana.
"Abdul ya kalleta to ina saurarenki,,fad'a min.
A'a maganar bata tsaye bace,, indai ban takuraka ba musami gurin zama.
Abdul yace" to inaga kibari saida daddare idan nazo saimu zauna muyi maganar mu uku harda Sopy, inaga hakan zaifi ko???
"Fareeda ta had'iye wani kududun bak'in ciki daya tsaya mata a mak'oshi,, jikake k'uuuuuttt!!!
Abdul yace hakan yayi ko?? Fareeda ta girgiza kai,, Alamar A'a,, tacigaba da fad'in mubiyu nakeson muyi maganar dan banaso Sopy tasani,, kasaka mana lokaci muhad'u nida kai kaiwai.
Abdul yay shiru yana tunani, saikuma yaja numfashi, to amma miyasa baki son Sopy tasani?? Fareeda tayi d'an murmushi, babu komai wlhy amma bana son tasani saimun kammala komai sannan, inason nabata mamakine.
Abdul yay dariya to shikenan babu damuwa,, saimu bari zuwa kamar weekend ko???
Babu damuwa indai hakan yayi maka ni agareni babu matsala.
"" to amma kina ganin tayaya zamu kasance tare dake batareda sopy tasaniba?? Kinsan koda yaushe kuna tare.
Indai wannan ne babu matsala nasan yanda zan kauce mata.
To shikenan Abdul yafad'a yana kallon fareeda,, har gida yarakota sannan yajuya,, amma zuciyarsa tana tunanin mi fareeda keson fad'a masa wanda batason safiyya tasani ??? Hakadai yayta tunani har yak'arasa majalissarsu inda suke zama da abokansa da yamma bayan kowa yadawo aiki ko kasuwa.
To masu karatu kubiyo danjin mi fareeda zata fad'awa Abdul ne??? Shin idan ta fad'a masa zaya amince????? Kubiyo ni danjin amsar tan bayoyinku. .................✍🏻



πŸ’•BilyπŸ’•
πŸ’•πŸ’•Mrs Abdus'salamπŸ’•πŸ’•πŸ’•
πŸ’•I LOVE YOU MY FAN'sπŸ’•πŸ’•
πŸ’•
5~October ~2016



πŸ”·πŸ”ΉNI DA K'AWATA πŸ”ΉπŸ”·



NA BILKISA IBRAHIM πŸ’•




πŸ”ΆπŸ”Έ5βƒ£πŸ”ΈπŸ”Ά


...................fareeda tafito cikin sharin fita, mama tabita da kallo kekuma ina zakije da yamman nan???
Mama dan ALLAH kibarni naje gidan aunty sadiya gobe in ALLAH yakaimu da safe saina dawo tunda babu makaranta.
Mama ta harareta kinga fareeda kifita idanuna tunkafin na b'ata miki rai,, yaufa kwananki uku da zuwa gidan sadiyar shine yaukuma kice zaki koma,, to waima mizakije yine??
: : fareeda ta turo baki gaba nifa sak'o zan amso awajenta.
Sak'o kuma??? To sak'on mi?? Kuma waye yabada sak'o abaki??
Fareeda tayi shiru dan batasan abinda zata fad'awa mama tabarta zuwaba,, saikawai tacire gyalen ta ajiye saman igiyar shanya,, tana fad'in tunda dai kin hana shikenan.
Mama tai tsaki ke dai kika sani.

Sopy kwance atsakar gida jikin wata 'yar bishiyar mangwaro dake tsakar gidansu,, hannunta rik'e da littafin English tana dubawa, dan exam tana gabatosu,, inna dake zirga zirga a tsakar gida dan k"ok'arin had'a abincin dare, ta kalli sopy safiyya ki tashi ki share tsakar gidannan kar magriba tayifa kina ganin rana tafara jaa.
To inna safiyya tafad'a tana mik'ewa, ta nannad'e tabarmar tafara sharar tsakar gidan,, tana cikin sharar malam ibrahim yay sallama da gudu sopy taje ta taryoshi,, baba sannu dazuwa.
Yauwa safiyan baba,, ya gidan?? Wlhy baba kafiya lao, to madalla.
Ta karb'i ledan hannunsa tana fad'in baba mika sayomin???
Yay dariya safiya way sai yaushe zakibar kwad'ayine kinfa girma,, inna tafito kichin tana masa sannu ya amsa cikin fara'a,, yaja kujera 'yar tsugunno yazauna,, inna takawo masa ruwansha.
Sopy tagama shara ta wanke hannunta, sannan tanufo babanta, baba tunda kaki fad'a min nibari naduba dakaina,, baba yay dariya to duba 'yar baba kankanace nasiyo miki saboda nasanki da son kankana,, ta d'auki ledar tana fad'in nagode babana mai sona.
Inna tace" malam ita kad'ai kasayoma kankarar Kenan? ?? Safiyya tace kai inna kina kishine???
Inna taimata πŸ–πŸ»dak'uwa kinci gidanku nicema nake kishin dake ???
Malam ya mik'e yana musu dariya,, yad'au buta yayi alwala, ita kuma Sopy tazauna gyara kankana, dan tana fashin sallah.

Suna zaune atsakar gida suna cin abinci,, sopy tana gefe tana shan kankana,, inna tace" ni ina tawa kankanar?? Sopy tamik'e tana fad'in wlhy baba idan banbama inna kankanar nanba bazata barni nasha iskaba.
" inna tarik'e baki wayni yaushe safiyya ta rainani agidannan ne malam??? Malam ibrahim ya murmusa bawani raini,, aii ko kurama da 'ya'yanta take wasa a dawa,, itama tana tsokanarkine kaway.
Inna tace" kaidai kana goya mata baya ne kaway,, safiyya tai dariya baba kabarta ai kwanannan zan tafiyata gidan aunty Nafisa hutu saita dad'e bata ganniba,, damma uncle kabeer bashida mata da gidansa zan koma.........yaron dayay sallama yasa sopy yin shiru.
"" kai shamsu lfy ??sopy ta tanbaya,, shamsu yace wanine yace kizo awaje,, wani kuma?? Waye wani?? bashida suna ne??? Shamsu yace nibansan sunansaba amma agidan Alhaji Abubakar mai fata yake.
Baba yace"kaga yaro yitafiyar ka,, gata nan zuwa.
Sopy ta turo baki wlhy nikam baba banason fita tad'innan yau,, baba yace"" tobake kika zab'i mijinkiba da kanki maza tashi kije,, amma kar a zauna wannan doguwar hirar,, tun ana fad'ar gsky har akoma k'arya.
Sopy tace"to baba bari nak'are shan kankanata.
A'a tashikije idan kin dawo saikisha.
Dole tamik'e tatafi badan tasoba.

Inna ta kalli baba,, malam wlhy nidai dan kawai safiyya tanason yaron nan amma nikam bai kwanta min araiba,, banaso akai safiyya gidan nan mai tarin mata da 'ya'ya.
Baba yaja ajiyar zuciya,, hajara babu abinda zamu iyayi face addu'a,, dan neman zab'in ALLAH, ALLAH yazab'a mana abinda yafi alkairi.
"To amin malam"

Awaje kuwa sopy tana fita saita tararda Abdul tare da fareeda suna hira,, lamarin yayi matuk'ar bawa sopy mamaki,, amma saita danne tak'arada wajensu da sallama.
Atare suka amsa mata,, takalli fareeda,, ke sister amma ke 'yar rainin hankalice yanzu nan dama baki tafiba???? Fareeda tace" kibari kawai 'yar uwa wlhy mamace ta kwafsa min tahanani zuwa,, fushi nakeyi shiyyasa kikaga ban shigoba,, yanzuma nazo na ari wayan Abdul ne nakira aunty sadiya nafad'a mata abinda yahanani zuwa.

Sopy taja ajiyar zuciya mai k'arfi,, Abdul yay saurin kallonta gimbiyata miye matsalarki???? Babu komai habibina ykk?? Lfy lau nake gimbiyata.
Nan dai suka dasa hira harda fareeda,, dan tak'i tafiya.
Hakan baisa sopy ta zargi komai ba, dan zuciyarta a tsarkake take,, ta yarda da fareeda da Abdul, d'ari bisa d'ari.

Washe gari saiga aunty sadiya tazo gidansu fareeda,, nanta wuni,, saida mama tashiga sallah sannan aunty sadiya tabama fareeda abinda takawo mata,, tai mata bayani dalla dalla sai dai nima bansan mita bataba masu karatu dan sunshige k'uryar d'akine.
" kukasance tare dani danjin yanda zata kasance.....................✍🏻



πŸ’•BilyπŸ’•
πŸ’•πŸ’•Mrs Abdus'salamπŸ’•πŸ’•πŸ’•
πŸ’•I LOVE YOU MY FAN'sπŸ’•πŸ’•
πŸ’•

[12/19, 7:24 PM] mrs bilkisu: 6~October ~2016



πŸ”·πŸ”ΉNI DA K'AWATAπŸ”ΉπŸ”·


NA BILKISA IBRAHIMπŸ’•




πŸ”ΆπŸ”Έ6βƒ£πŸ”ΈπŸ”Ά


................Yaud'in takasance asabar babu makaranta su sopy suna gida,, fareeda ce tadoso gidansu sopy hannunta rik'e da filet a rufe tashigo da sallama,, inna dake d'aki ta amsa mata,, tak'arasa d'akin inna ta gaisheta inna tace" yasu ladidin?? Lfy lao inna tamace na gaisheki wai anjima zata shigo kuje asibitin dubiyar nan.
"" A toshikenan babu damuwa saita zod'in,, kishiga safiyyan tana nan a d'akinta tana shirin tfy gidan hauwa'u,, nazatama tare zaku??? Eh dama tare zamuje to sai zanje gidan aunty sadiya nakai mata sak'o kinsan ita kuma bata zuwa gidan,, amma inna kai sak'on zan isketa acan d'in.
Ato shikenan ma,, itama d'in shirmene yake damunta kawai,, sadiya ba innarta bace??
Fareeda tayi murmushi bahaka bane inna laifin aunty sadiyarne aii,, tafad'a tana mik'ewa.

D'akin sopy ta shiga, sopy na zaune tana kwalliya fareeda ta zauna kusada ita 'yammata wannan irin kwalliya haka' saikace maishirin zuwa gasa??? Sopy ta harareta ke bakiga takibane??? Nitunda nake dake ma bantab'a ganin kinyi irin wannan gayunba wlhy????
"Fareeda ta tura mata filet d'in datazo dashi, tana fad'in shike nan kin rama.
Sopy ta bud'e filet d'in tana fad'in mikika kawo min??
Wlhy waynar filawace nayi dasafe,, to naga baki shigoba shiyyasa nabiyoki da ita.
Sopy tace" kin k'yauta kuwa dama tund'azu nakasa karyawa.
" saboda mi??
Wlhy bako mai kawai dai yaunatashi duk jikina babu dad'i ga gabana sai fad'uwa yakeyi. Fareeda tace tofa lfy dai""
Wlhy nima bansaniba 'yar uwa.
To ALLAH yatabbatar mana da alkairinsa,,, fareeda tafad'a.
"" sopy tace'' amin dai.

Tare suka fito kowacce tahau mota zuwa inda zata.
hauwa'u tatari 'yar uwarta da murana,, sopy tace" aunty ina Arfat yake?? Yana wajen kareema yarinyar makwaftan mu d'azunnan tazo ta d'aukeshi suka tafi.
" kai aunty wanan d'an yaron kika bari aka fita dashi da wannan safiyar?? To yazanyi auta yariga yasaba dasu,, tashigo kawo min abune yamak'ale mata. Toni dai ki aika akawo min yarona! Karki damu zata kawoshi,, wai yana ganki ke kad'ai ina K'AWAR taki fareeda???
"Itama tana nan zuwa taje gidan sadiyane takai sak'o zuwa anjima zata zo.
To shikenan ALLAH yakawo ta nitashima ki d'ora mana abincin rana,, dama d'inki zanyi.
Kefa kinji matsalarki mutum baya zuwa gidanki ya huta dayazo saikin manna masa aiki, tafad'a tana kumbura baki.
Aunty hauwa'u tace" kekuma gashi baki son aiki ko?? Haka zamu kaiwa Abdul d'in ke,, inma zaki dage kidage wannan gidan nasu mai tarin 'ya'ya da mata,, dan agidan za'a ajiyeki tunda dukkan matan yayyensa anan suke zaune.
Sopy ta tashi daga kwanciyar datayi,, to aishi yace" ba anan zamu zaunaba zai kama mana haya.
Aunty hauwa'u ta tab'e baki to ALLAH yasa hakane???
"Sopy tamik'e tana fad'in hakanema.
Miza'a dafa?? Aii inaga tuwon shinkafa za'ayi. Sopy tace" kai kukam kuda inna bakuda matsalar data wuce ta tuwo?? Aunty hauwa'u tai dariya,, toshi abban Arfat yakeson ci.
Nikam gsky bazanci tuwo daranaba,, zan dafa mana wani abu nida fareeda kafin tazo! Duk yanda kikayi cewar aunty hauwa'u.

Fareeda kam ta isa gidan aunty sadiya,, sadiya tabita da kallo lallai fareeda wannan irin kwalliya haka??? Duk ta tarar Abdul d'ince??? Fareeda tayi dariya auty sadiya ya rankine,?? kefa kikace na cake sosai.
" sadiya tace" gsk yane d'iyata, suka tafa nuna dariya.
Fareeda tace" yaya dai kin kammala girkin??
Aii komai ya kammala yanzu Abdul kawai zamu jira.
Fareeda tai wani ihu ALLAH yabar minke aunty na,, kina cikin aikina.
Sadiya tai dariya ALLAH yashir yaki fareeda,, yanzu dai ki kirashi dan muji yaushe zai iso??
"" to auntyna, fareeda takira Abdul yacemata aii gama shinan ahanyar zuwa,, tak'ara yimasa kwatancen layin?? Fareeda takuma yimasa kwatance sannan ta kashe wayar.

Sopy tagama abinci tazauna kusada aunty hauwa'u tana fad'in wash ALLAH yaudai saina sha maganin gajiya zan iya barci.
Aunty ta harareta way safiyya mikike son zamane?? Da dai keba raguwa bace wlhy.
Sopy tai dariya dama can dan ban gama sanin ciwon kaina baneba,, amma yanzu ina.
"" aunty tace" zaki gaya musu yarinya.
Kareema tai sallama hannunta d'auke da Arfat,, sopy ta karb'eshi da sauri tana fad'in oyoyo my son! Tai kissing d'in kumatunsa.
"" kareema ta gaisheta,, aunty hauwa'u tace kareema sannun ki! Kareema tai dariya kai aunty saikace wani aiki,, umma cema tace nakawoshi yasha nono amma ba kuka yakeba.
Aunty hauwa'u tace" aii nagode wlhy badankeba da Arfat bazai barni nayi d'inkin nanba,,, nibansan yanda zanyiba idan kinyi aure??? Kareema tafita da gudu wai kunya takeji,, su sopy sukasaka dariya.......................✍🏻



πŸ’•BilyπŸ’•
πŸ’•πŸ’•Mrs Abdus'salamπŸ’•πŸ’•πŸ’•
πŸ’•I LOVE YOU MY FAN'sπŸ’•πŸ’•
πŸ’•
[12/19, 7:24 PM] mrs bilkisu: 7~October ~2016


πŸ”·πŸ”ΉNI DA K'AWATA πŸ”ΉπŸ”·



NA BILKISA IBRAHIMπŸ’•



πŸ”ΆπŸ”Έ7βƒ£πŸ”ΈπŸ”Ά


..............Abdul ya iso yakira fareeda yay mata kwatancen inda yake,, suka aika wani yaro ya taho dashi zuwa k'ofar gidan,, amma sai yaja tunga yak'i shiga gidan,, fareeda tafito cikin dogon hijjab harda saka nik'af shi baima ganetaba dan haka yad'an ja gefe domin bata hanya,, tai masa sallama ya amsa yana binta da kallo,, tai dariya Abdul nicefa fareeda baka ganeniba ne??
Abdul yace"tofa wlhy ban ganekiba naga kinsaka nik'af nina zatama matar aurece!!
Fareeda tai dariya wlhy nice,, kashigo mana!!
A'a yaza ayi nashiga gidan mutane batareda izinin mai gidan ba???
Karka damu baya nan kuma yasan da zuwanka, kashigo kaway dan ALLAH.
sayda yay jim sannan yace" kina ganin babu matsala fareeda!
Babu wata matsala kamar yanda nagaya maka yasan da zuwanka,, kafinma katafi zai dawo gidan.
" to shike nan muje"
Har falon aunty sadiya suka kaishi yazauna yana shak'ar iskar fanka,, fareeda tafito zuwa tsakar gida ta iske aunty sadiya a kichin,, aunty sadiya tace" yaya dai yashigo?? Fareeda tace" yanama falonki zaune. Sukai dariya, sopy tacire nik'abi tad'au wata hoda a cikin leda ta kuma shafawa ta d' au kwalli tashafa,, aunty sadiya tamik'o mata turare ta fesa,, sannan tace" nayi my aunty??? Sadiya ta jinjina kai kinyi d'iyata komai yaji,, d'auki abinci kitafi nima zanzo mugaisa.
To shikenan auntyna fareeda tafad'a tana d'aukar tiren da kulolo ke kai.

Tai sallama ak'ofar palon cikin irin wata murya wadda itama batasan tana da itaba,, Abdul ya amsa tareda mik'ewa yatarota tiren hannunta ya karb'a yana fad'in wannan tire haka aii yayi miki nauyi dayawa.
Fareeda tazauna tana murmushi Abdul yad'ago suka had'a ido,, jiyay wani abu yashige jikinsa tundaga kansa har zuwa yatsun k'afarsa,, yarintse ido yana fad'in yasalam!!
Fareeda tace"Abdul yaya dai???
Yasakar mata tsadadden murmushi babu komai ina cikin wani irin farin cikine dana kasance dake.
"Fareeda tace" tofa Abdul nikuma?? Ko ka manta ba gimbiyarka bace sopy??
Abdul ya b'ata rai kinga idan muna magarmu ki daina sako mana wata sopy.
Fareeda tayi murmushi to nabari my love kayi hak'uri kabar b'ata ranka.
""Fareeda tazuba lemo akofi tabasa, yakarb'a yashanye,, takalleshi abincifa,, yay mata murmushi abani naci dama kamshinsa yanata cikamin hanci.
Fareeda tazuba masa farar shinkafa da miya yaci ya k'oshi suna hira,, saida yagama suka nutsu,, fareeda tace" Abdul yamaganar mune??? Abdul yay mata wani kallo na masoyi zuwa masoyiyarsa yace"ina saurarenki aii dama maganarce takawoni gareki my love!!
Fareeda tai wani murmushin mugunta tace" yayi k'yau,, tasowa tayi tadawo kujerar kusa dashi, takanne masa ido d'aya yay murmushi.
Shima yajuwyo sosai suna kallon juna,, suka k'urama juna ido kamar zasu cinye juna,, fareeda ce tafara janye nata idon tana murmushi,, cikin karsashi tace"my Abdul!!!!
Abdul ya amsa murya asark'e. Taja ajiyar zuciya Abdul ina matuk'ar k'aunarka fiye da mai buk'atar ruwa acikin sahara,, ina begenka fiyeda d'an da ke buk'atar nonon mahaifiyarsa alokacin dayake kuka, ina son kasancewa dakai tamkar bawan dake k'aunar bud'ar ido yagansa a aljanna, ina burin tara zuri'a dakai fiyeda talakan da ke burin tara dukiya, ina burin kozamu mutu mu mutu tare tamkar laila da majnun.
Hawaye suka zubo akuma tunta, Abdul yasa hannu yashare mata hawayen,, cikin sark'ewar murya yace" nima ina sonki fareeda ina k'aunarki, ina burin aurenki, ki kwantar da hankalinki insha ALLAH kece uwar 'ya'yana.
Fareeda tad'ago kai dasauri tana kallonsa dan ALLAH Abdul da gsk kake???
Abdul yay murmushi da gsk nakeyi fareeda insha ALLAHU zaki zama matata.
" fareeda tai dariyar farin ciki,, tace" to amma yanzu yaza muyi da sopy???
Abdul yace" zan fad'a mata bana ra'ayinta yanzu, kece ra'ayina!!
A'a Abdul bahaka za'ayiba kawo kunnanka

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login