Showing 18001 words to 21000 words out of 58156 words
k'ara k'ibaba.
Yanzu tarage yawan tunani, tafi maida hankali wajen karatunta, babama yaji dad'in ganinta sosai.
Taje tagaida maman su fareeda, harma tatayata wasu ayyukan, maman fareeda tanata k'ara lallashinta akan abinda yafaru, sopy ta ce, "wlhy mama ni yawuce awajena, dama can ALLAH yarubuta Abdul mijin fareeda ne, dan haka kudaina ganin laifinta, kud'auka wannan yana cikin k'addarar rayuwarmu ne kawai.
Mama ta ce, "hummm safiyya kenan ke dai mai hak'urice kawai!! Kuma insha ALLAH saikin sami miji nagari wanda yafi Abdullahi k'yawawan halaye, itakam mun barta da wayonta!!.
A'a mama dan ALLAH karkuce haka wlhy har yanzu ina k'aunar fareeda bana son iyayenmu suyi fushi da ita!!, dan ALLAH kuyafe mata!!.
Mama ta tsurama sopy idanu, tana matukar k'aunar yarinyar, saboda hak'urinta ga nutsuwa, lallai d'iyarta tayi asara, tunda har tarabuda safiyya bata koyi k'yawawan halaye daga garetaba.
Nan dai sukaita hirarsu har yamma.
Tayi k'ok'ari taje gidan aunty Nafisa da auty hauwa'u, har gidan aunty zainab yayar fareeda, nanama hak'uri tayita bata, sopy ta ce, " bakomai yawuce".
Ranar lahadi uncle kabeer yazo gidan dan shine zai maidata school, ya d'auketa sukaje yayo mata sayya ta kayan provision da Duk abunda zata buk'ata, 'yar gatan uncle kabeer kenan, har d'unkuna yaymata yasaya mata takalma da hijja bai, da yamma tashirya suka tafi, harda kukan rabuwa da inna da baba.
Amota uncle kabeer! ke tambayarta taje gidan fareeda!? ta ce,:"haba uncle ALLAH ya kiyaeye aii har abada bazanje gidan fareeda ba, saidai idan tazo anguwar magaisa amma bazanje gidantaba!!.
Uncle kabeer yay murmushi saboda kishi??? Tai saurin fad'in uncle aii ni! Har abada bazanyi kishi da fareeda ba, koda d'imma ina bak'in cikin sub'ucewarta daga garenine, da kuma abunda ta aikata saboda son zuciya, amma ni yanzu haka na yafe mata, sai dai kuma bazamu tab'a komawa kamar daba, dan yanzu banida aminiyar data wuce inna da baba, sai uncle kabeer da my auntys d'ina.
Uncle kabeer yay dariya to shikenan kema ALLAH yabaki miji nagari.
Sopy tasa hannu tarufe fuskarta saboda kunya.
Adai dai wannan lokacinne kuma suka iso cikin makarantar, yasamu guri yay parking, ya zaro waya bari nakira abokina yazo yataremu.
Sopy ta ce, "waini waye wannan abokin nakane uncle?? Ni tunda nazo school d'innan ban sanshiba.
Ya ce, "zaki gansa yanzu nan.
Cikin 'yan mintina ya iso, hankalin sopy yana kan waya tana chatin, uncle kabeer yabud'e motar yafito, suka rungume juna shida abokin nasa.
Kai abokina nazata makarantar nan zata zama gurin zuwanka fiye da haka, amma sainaga sab'anin haka, indai har bawani abu bane yakawoka ba, ba'a ganinka.
Uncle kabeer yay dariya karka damu indai nine yanzu zaka rink'a ganina sosai tunda my daughter d'ina tana school d'in!!.
Ya ce, "gsky ne, aii nima yakamata yau nasan wannan d'iyar tamu.
Uncle kabeer ya ce, "aii gata nan amota ma ita nakawo!!
Malamin yay dariya to ta fito, saimu k'arasa office ko?? Murnar ganinka tasa na manta a inda muke tsaye.
Uncle kabeer ya ce, "sopy tafito ga abokin nasa.
Da zumud'inta tafito kuwa, tayi turus tana kallon abokin na uncle kabeer,, ba wani bane illa uncle G!, shima kallonta yakeyi cikin wani yanayi mai wutar fassara,, uncle kabeer! Yay dariya to da alama kumma san juna kenan?.
Uncle G! Yay murmushi, ai d'aliba tace, kaga duk laifinkane kenan???. Uncle kabeer ya ce, "to, kayi hak'uri, ranar dana kawota ina sauri natafi wajen aikine wlhy.
Sopy ta daure ta ce, "uncle good evening!.
Ya ce, "ya weekend??
Ta ce, "ALHAMDULILLAHI.
MASHA ALLAH yafad'a yana kama hannun uncle kabeer!, abokina muje ciki ko.
Sopy ta ce, "uncle bari nakai kayan d'aki saina dawo muyi sallama, sannan kun gama.
Okey to shikenan babu damuwa, jeki kai, amma kisamu wasu sutayaki, dan kayan sunyi miki nauyi.
To uncle!.
Sopy takira zaliha awaya sukazo itada wata k'awar zalihar, suka tayata kwashe kayan, saidai gaba d'aya zuciyaryata cike take da tunanin dama uncle G! Shine abokin uncle kabeer??, k'in fita tayi har saida uncle kabeer ya kirata a waya sannan tafito.
Bayanda zatayi dole tanufi office d'in dan uncle kabeer ya ce, "tasameshi a can.
Ahankali ta tura k'ofar office d'in tashiga, office d'in sai tashin k'amshi yakeyi, uncle kabeer ya nuna mata kujerar dake kallonsa tazauna.
Ya ce, "kindai gama ko?? Ta d'aga kai alamar e, ya ce,"masha ALLAH, yagara zama to sopy! Ga abokina malam youseef tare mukai school d'innan dashi, amma dayake shi abincinsa anan yake, to gashi yana aiki anan, munsha gwagwarmayar rayuwa tare, komai namu tarene a school d'innan, gashinan duk abinda kike buk'ata to kizo wajensa ki karb'a, kokuma idan wani abu yashige miki duhu a b'angaren karatu, to kizo zai warware miki, domin wannan dakike gani kwarone, uncle yafad'a yana kallon uncle G!.
Uncle G! Yay dariya kaidai masherancine abokina har yanzu kana nan baka canjaba ko?
Uncle kabeer ya ce, "aii gsky ce, uncle kabeer yacigaba dafad'in abokina ga d'iyata wadda nafiji da ita acikin 'ya'yana, batada damuwa kamar yada nasanar maka, itama tanada kwakwalwar karatu, dan haka ka taimaka mini wajan cika mini kwakwalwarta da karatu.
Uncle G! yataso daga kwanciyar dayayi ajikin kujera, yad'an tsurama sopy idanu tai saurin janye idanunta daga kallon datake masa, yay d'an murmushi, babu damuwa abokina nakarb'a, ainima d'iyatace.
Sopy tana mamakin yanda taga uncle G! yanata fara'a yau, domin yau itace rana tafarko dataga murmushinsa, sannan duk d'agowar datayi saita kamashi yana kallonta.
Sun d'an dad'e suna hira, kafin uncle kabeer ya tafi, saida suka rakashi har wajen motarsa bayan ficewarsa daga cikin makarantar uncle G! Ya juyo yana kallon sopy, tai kasa da kai dan tasan batada gsky....................βπ»
πBilyπ
ππMrs Abdus'salamπππ
πI LOVE YOU MY FAN'sππ
[12/19, 7:25 PM] mrs bilkisu: 22~October~2016
π·πΉNI DA AMINIYATA!!! πΉπ·
NA BILKISA IBRAHIM π
πΆπΈ2β£2β£πΈπΆ
...............yagara tsayuwar sa, aii dole kiji kunya, dan kinsan kinyi laifi.
Sopy tad'an d'ago ta kalleshi, ganin ita yake kallo yasata saurin yin k'asa da kai, ta daure ta ce, "laifin mi nayi??
Ya jin jina kai, okey tunda baki d'auki abinda kika aikata amatsayin laifiba shikena, ya kalli agogon hannunsa, yanzu inada wani aiki, amma zuwa gobe zan jiraki a office, kinada lecture d'in safene???
Sopy ta amsa da e, inadashi.
Okey to karfe nawa zaki fito??
Tayi d'an jim alamar tunani, karfe sha biyu.
Okey bada muwa, jan jiraki k'arfe hud'u, yajuya yana kallon yanda wasu tsurarin d'alibai masu dawowa weekend damasu harkokin gabansu, dayawansu su suke kallo, yad'an girgiza kai, kinga kije d'aki amma karki shanyani, inko bahakaba to zanzo har ajinku gaban kowa muyi magana.
Ta zaro idoπ³ waje.
yay murmushi kina mamakine ?? To indai hakane kik'i zuwa kigani, saidai kawai ki ganni.
Ina saurarenki, yafad'a yana tafiya.
Sopy tabishi da kallon mamaki, wai mutum mai aji da nuna isa, mai ilimi wanda 'yammatan! da samarin! university ke son yay musu magana, shine yau agabana, yake buk'atar naje wajensa, tad'anyi murmushi mai k'ayatarwa tanufi hostel.
D'aliban dasuka gansu aka d'auki gulma zuwa hostel, wasu kuma ganinsu harda uncle kabeer saiba su kawo komaiba aransu, to ALLAH yashiryi magulmata dai.
Washe gari sopy tanata harkokinta, dukda gargad'in da uncle G! yay mata baisa tayi yink'urin zuwa office d'insaba.
Shikam gaba d'aya hakalinsa yana kanta, karfe d'aya da 'yan muntina yashigo musu lecture, saboda shi tak'i zama gaba, amma wannan bai hana idonsa lalibota ba.
Zaliha ta ce, "sopy wai kin kula da kallon da uncle G! Yake miki kuwa, wlhy tun d'azu hankalinsa yana kanki.
Sopy ta harareta, to uwar magul mata, ke bama karatun kike saurareba, wanda yake kallone agabanki, ni kibarni naji karatu, tana d'agowa suka had'a ido kuwa, tai surin kauda kai gefe.
Yagama lecture nasa yafita.
Har k'arfe hud'u tayi sopy batada niyyar zuwa office d'in uncle G!, tanata harkokinta abinta, suna zaune itada Nadiya, tana koya mata wani aiki.
Nadiya ta ce, "kai sopy kekam kin more wlhy, ina son mutum mai kwakwalwa arayuwata, wannan yana d'aya daga cikin abinda yasa kike matuk'ar birgeni.
Sopy tayi murmushi kekam Nadiya kinada yawan tsokana.
Nadiya ta ce, "wlhy babu wani tsokana gsky ce nake fad'a, kuma kema kin sani, saidai ki godema ALLAH.
Kafin sopy tayi magana wani saurayi ya k'araso wajen, ya ce, "waye safiyya ibrahim kabeer!!? Sopy ta amsa da nice, ALLAH yasa lafiya?? Saurayin ya ce, "lafiya k'alau, dama uncle G! ne ya ce, "kizo yana office d'insa, sopy tad'anja tsaki sannan ta ce,"to ina zuwa.
Aii kije kawai danni ba komawa zanyi office d'inba.
Nadiya ta ce, "kitashi kije bakisan miya faruba, badan tasoba ta mik'e tanufi office d'insa.
Saurayin ya kalli Nadiya, Nadiya dan ALLAH uncke G! Surayin yarinyar nan ne??
Nadiya ta girgiza kai, A'a, ba saurayinta bane, amma nima bansan dalilin dayasa yake nemanta ba, amma kai miyasa ka tanbaya?
Naje wajensane, shine ya ce, "nakira masa safiyya ibrahim, toni abunne yabani mamaki, danshi bai cika kula matan makarantar nan ba.
To babu abinda yake tsakaninsu, kuma maza dai kunzama magulmata.
A'a bawani gulma daga tambaya?.
To miye na tambayar, shin uncle G! Ba mutum bane, koko shi bazai iya yin soyayyaba ne?? Inma hakane wlhy nikam zanyi farinciki.
Saurayin yay dariya aii munga shi baya kula mata, gashi kuma kun mutu asonsa, kamar makarantar nan babu wani namiji sai uncle G!, bakuda wata hira sai tashi, komai uncle G!, tamkar wanda aka halitta da gold.
Nadiya ta ce, "yanada kamun kaine, ya iya rik'e mutuncin kansa fiyeda sauran malaman da d'alibai, baya wasa da kowa, gashi kuma mai aji da ilimi.
Saurayin yay gaba dan jin haushin furicinta.
Safiyya ta nufi office d'in uncle G!, saida taje k'ofar takasa shiga, tadad'e a tsaye, dan takasa kwankwasawa, ganin wasu d'alibai suna kallonta yasa ta daure ta kwankwasa ahankali batayi zaton zaijitaba ma, amma sai taji ya ce, "yes come in.
Ta d'auki tsawon minti biyu bata shigaba, ganin batada fafita yasa ta tura k'ofar office d'in tashiga, wani k'amshi ne yadaki hancinta, tashak'a tad'an lumshe idanu.
Cikin muryarsa mai dad'i ya ce, "shigo mana".
Cikin sanyin jiki ta ida shigowa ta maida k'ofar ta rufe,, ta jingina da k'ofar.
Yana zaune a kujerarsa, gabansa da tarin takardu, yana dubawa inaga namasu test ne, dan ya kware wajen yima d'alibai test, jin anyi shiru yasashi d'agowa, azatonsa komawa tayi, amma saiya ganta atsaye, tana kallonsa, ya ce bismilla zoki zauna.
Ganin fuskarsa babu walwala yasa ta k'arasa ta zauna a d'aya daga kujerun dake gaban tebir d'in gabansa, yacigaba da duba takardun gabansa, batareda yakuma bi takan taba, yad'auki tsawon minti bakwai, kafin yad'an d'ago ya kalleta, tana zaune kanta ak'asa tana wasada wani zobe dake yatsanta na biyu, yad'anja numfashi sannan ya maida kansa ga aikinsa.
Cikin muryarsa mai amo da taushi ya ce, "yauma da bansa a nemomin keba da bazaki zoba ko?? Yacigaba da fad'in babu k'yau sab'a alk'awari dai.
Sopy ta ce, " azuciyarta aii ni ban maka alk'awarin komaiba,, amma afili saita te ce, "aii dama zanzo.
Ya ce, "aii koma bakizoba ni zanje nemanki, dan na matsu muyi magana, tad'ago tana kallonsa, yana duba takardunne yana maganar.
Yad'ago zai mata magana, tayi saurin maida kanta k'asa, ya murmusa, tareda mik'ewa yanufi inda take, d'ayar kujerar dake kallonta ya zauna, k'amshinsa ya yawaita agurin, yay gyaran murya tare da fad'in kinsan abinda yasa nake nemanki??.
"Ta girgiza kai"
Yad'ora kafarsa d'aya saman d'aya, ya kwantar da bayansa ajikin kujerar,, saida yay mata kallon mintina uku sannan yaja numfashi, ina son na tambayeki samarinki nawa???.
Da sauri sopy tad'ago tana kallonsa, amma saiya gimtse fuska dan baya son raini.
Ta maida kanta k'asa tana cigaba da lankwasa yatsun hannunta suna k'ara.
Ya ce, "ina sararenki!!.
Sopy ta daure ta ce, "ni fa banida saurayi, cikin shagwab'a tayi maganar.
Yay murmushi tareda fad'in masha ALLAHU, yakuma ce wa," to yaushe kika shirya yin Saurayin?, nanma saida ta kalleshi sannan ta ce, "banda lokacin aikata hakan.
Nanma saida ya murmusa, ya ce, "masha ALLAHU, yataso daga kwanciyar dayayi, ya ce, "toni na shirya yin auren safiyya, domin matata tarigaya ta iso, ba wasa nazo dashiba, domin inda buk'atar yin aure yanzu, yaya kenan??.
Sopy ta ce, "a zuciyarta, to ni ina ruwana da shirya yin aurenka ne??
Yaci gaba dafad'in nina shirya kefa?? Dan inason muyi aure ba soyayyaba, idan kinje gidana zan nuna miki dukkan soyayyata.
Sopy ta ce, "ban ganeba??
Ya murmusa zaki gane nan bada dad'ewaba, kije kiyi tunani akaina, kabeer yasanar dani komai daya shafi rayuwarki, dan haka bakida matsalar yimin bayanin kanki, nakuma yimiki alk'awarin mantar dake abinda yafaru dake abaya, sannan daga yau karna sake ganinki da zaliha, dan batada tarbiya, nasan bak'ya kula samarin makarantar nan, to karki fara domin inada kishi mai tsanani, zan iya komai yayinda naga abinda zai tada min kishina, ya mik'a mata wani littafi mai d'an girma, ga wannan ki karanta lokacin dakika samu dama, zaki samu dukkan abinda ya danganceni acikinsa, dukkan tarihina yana nan.
Tasa hannu biyu ta karb'a, ya d'akko lemon dake saman tebir d'in ya mik'a mata, sorry ga wannan kisha!.
Ta girgiza kai A'a nagode.
Ya ce, "kina nufin bazaki shaba, ko kina kyankyamin abin hannuna ne??.
Tai saurin girgiza kai, ya ce, "to karb'a kisha, ta ce, "aii ina azumine.
Ya ce, "wow nice, azumin me kenan??, ta ce, "na nafila.
Ya kuma cewa nice, aii haka akeso, to idan kinsha ruwa wace addu'a zakiyi akan aurenmu?.
Ta k'ara k'asa da kai, batareda tayi maganaba.
Ya ce, "kunyarki tayi yawa, amma zsn rage miki ita, dan dama haka nakeson matata ta kasance mai tarin kunya da nutsuwa, gashi ALLAH ya kawo min alokacin danake tsananin buk'ar hakan, wannan week d'in zanje gida nasanarda iyayena nasan zasuyi matuk'ar farinciki, dan kullum burinsu kenan, gashi dama sunsan kabeer, dan haka ki zauna da shirin zama matata nanda k'arshen shekara 2016.
Tayi saurin kallonsa, ya kashe mata ido d'aya, ina fatan kin shirya salo salo na soyayyar dazaki nuna min, danni mutumne mai buk'atar a soshi da nuna min tattali yak'arasa fad'a a hankali.
Itadai sopy takasa koda k'yak'yk'yawan motsi, dan ita mamaki ma yake bata, ko ina miskilancin da jan ajin nasa?? Dama yana magana haka??.
Kamar yasan tunanin datakeyi, ya ce, "kina mamakina ko? To daga yau kibari, domin ni mijinkine, ina fatan kwaykwayon {MANZON ALLAH S A W} ne, domin ya nunama mana yanda zamu so matanmu da kuma yanda zamu zauna dasu, dan haka kinada matuk'ar aiki agabanki,, ki shirya kuma.
Ya d'auki wayarta dake kan cinyarta, nomber d'insa yasa yakira wayarsa, sai kuma yacigaba da binciken wayar, babu wani abu mara k'yau aciki, saima hotu nanta masu k'yau, yagama gani ya mik'a mata.
Ta ce, "bari natafi kar mutane su zargi wani abu.
Ya gyara zama karki damu dasu, danni basu bane agabana, amma duk da haka na fahimceki, nima bana buk'atar kowa yasan wannan maganar sai an gama komai, kinji ko.
Ta jinjina kai alamar to.
Ya ce, "to tashi kije dan yamma tayi, sainazo barka da shan ruwa....
Aii kafin yarufe baki tayi waje.
Ya kwanta ajikin kujerar, ya lumshe idanu yana murmushi, ya ce, "ya ALLAH ka mallaka min wannan baiwa taka mai tarin nutsuwa da addini.
"muda muke a lab'e, ni da su pii pii mukace amin ya Rabbi.....................βπ»
πBilyπ
ππMrs Abdus'salamπππ
πI LOVE YOU MY FAN'sππ
[12/19, 7:25 PM] mrs bilkisu: 23~October ~2016
π·πΉNI DA AMINIYATA!!!πΉπ·
NA BILKISA IBRAHIMπ
πΆπΈ2β£3β£πΈπΆ
..........kwance take bayan ta gama shanruwa, tayi zugum dan kuwa tana duniyar tunanin abinda yafaru d'azu, tsakaninta da uncle G!, ta tuna yanda yake magana cikin gadara da bada umarni.
"Toni na shirya yin aure safiyya, domin matata tarigaya ta iso, bawasa nazo dashiba, domin inada buk'atar yin aure yanzu,"
Tayi murmushi, tareda sake tuno wata maganar tasa.
"Dan inason muyi aure ba soyayyaba, idan kinje gidana zan nuna miki dukkanin soyayyata".
Taja numfashi tareda gyara kwanciya, wato shi baya lallashi, kai tsaye yake magana babu wani kwala kwala, to amma shi baisan ba'a umarni a soyayyaba ne?.
Ta tuna inda yake fad'in, daga yau karna sake ganinki da zaliha dan batada tarbiyya, nasan bakya kula samarin makarantar nan, to karki fara domin inada kishi mai tsanani, zan iya komai yayinda naga abinda zai tada min kishina".
Ta murmusa, su uncle G! Masu kishi, to ina ruwana da kishinka, ni nan dakake gani maza duk d'aya na d'aukeku, a kan mizani d'aya nasakaku, taja ajiyar zuciya domin jin an kwala kiran sallar isha'i, tamik'e domin gabatar da sallah.
Saida ta kammala komai na al'adar rayuwarta, sannan tazauna domin duba book d'in da uncle G! Yabata, ga gajiyar azumi, tazauna tana fad'in wash ALLAH!! aii duk gajiyar danayi bazata hanani karanta book d'innan ba, tai saurin kallon wayarta datake wringing sabuwar nomber ce, dan haka ta share, saida aka k'ara kira sannan tad'auka tana mita, tai shiru batareda ta amsa ba, daga camma ank'iyin magana.
Ta daure ta ce, "kowaye idan bazaiyyi maganaba tofa zan kashe".
jitai wata sassanyar murya ta ce, "assalamu aliki?.
Sopy taja ajiyar