Showing 27001 words to 30000 words out of 58156 words
gwaggo tafad'a tana mik'ewa, bari nakawo muku ruwa, munata surutu ko ruwa ba'a bakuba.
Uncle G! Ya ce, "bakomai gwaggo da kin barima Aysha saita d'ebo aii, gwaggo ta ce, bari nad'ebo tunda natashi, saima ahad'o da abinci, saidai kuma ban bayar ansiyo maka awarar taka ta famaba, wannan tararrabin rasuwar ya mantar dani,, Aysha taso ki siyo masa, ALLAH yasama bata k'areba kinsan Awarar uwaliya kamar nama take agarinnan.
Aysha ta ce, "to gwaggo kawo kud'in??, ki d'akko a k'ark'ashin filo, akwai d'ari biyu.
Uncle G! Ya ce, "karb'i barmata kud'inta, ya mik'a mata dubu d'aya, ta ce, "yaya daka bari na d'auki d'ari biyun dan wlhy sai kaga anata neman canji ak'isamu.
Ya ce, "to, kuma kiyi sauri, dan karki zauna neman zance.
Aysha tafita tana turo baki.
Gwaggo tashigo da ruwa a kofin silba, ta koma ta d'akko samira ta ajiye gaban uncle G!, ya ce, "yawwa gwggonmu sannunki da aiki.
Ta zauna tana fad'in aii kune da sannu, kuda kuka sha hanya, ya d'auki ruwan yasha, yana murmushi, suka cigaba da hira kafin Aysha tadawo.
Badad'ewa Aysha tadawo, sukaci suka k'oshi yafita danyin sallah da ta'aziyyar rasuwar da'akayi.
Baba yashigo, Aysha taje ta taroshi cikin farin ciki, A'a Ayshatu! saukar yaushe??, aysha tayi dariya baba tun d'azu mukazo harda yayama.
Ya ce, "madallah ina yusufan yake?, baba yanzu yafita sallah baku had'uba?, A'a bamu had'uba, k'ila masallaci juma'a yaje sallar dan sune naji sun tada sallah yanzu.
Saida yay gasuwar yadawo, ya tsugunna ya gaida baba, baba ya amsa cikin fara'a, yusufa! ya jama'ar birni?, dasu kabiru ango??.
Wlhy lfy law baba, yanata godiyar d'awainiya.
Kai haba in banda abin kabiru miye na godiya, abun nawa yake, tunda ALLAH bai nufa zamu d'aurin aurenba.
Aii bakomai baba hakanma angode ALLAH yasaka da alkairi, Aysha aii ta wakilceku.
Sun dad'e suna hira, anan nema uncle G! Yasanar da baba maganar tura manya gidansu safiyya, ckin jin kunya yake maganar.
Baba yayi dariya aii ko yusufa nayi farinciki da wannan magana, wlhy dama zamannan naka ya isheni haka, mutane sai surutu sukeyi wai dan kayi boko kak'i yin aure, sun manta aure lokacine.
Uncle G! Yay k'asa da kai yana fad'in gsky ne baba, amma kuyi hak'uri.
A'a aii bakomai yusufa tunda gashi lokaci yazo, aii mu sadai muce ALLAH ya kaimu lokaci, yasa kuma ayi da ranmu.
Akan leb'ensa ya ce, "amin.
Bayan sun gama tattaunawa yafita domin ganawa da matasan k'ungiyarsa kamar yanda yasaba, domin suma tuni sun hallara gurin dasuke had'uwa tunda sunsan da zuwansa.
Da dadadare aunty hafsat suka zo itada libabatu dan tuni Aysha taje gidajensu takai musu labarin matar da yaya zai aura, harda tsarabarsu, sannan ma shi bai dawoba yana waje.
Basu dad'e da zuwaba ya shigo shima, ya ce, "A'a 'yan uwa kune da daddarennan??
"Sukace mune!!.
Yaja kujera 'yar tsugunno yazauna, suka gaisa, sukai masa godiyar tsaraba, ya ce, "wace tsaraba kuma aii ni! banyima kowa tsaraba ba.
Aunty hafsat ta ce, "e, auta tace k'anwar muce tabamu ALLAH dai yasaka da alkairi yakuma kawo mana ita lfy.
Uncke G! Ya ce, "to amin, yakuke da yaranku da mazajen!! ku?
Suka ce, "duk muna nan lfy.
Ya ce, "aii haka akeso.
Baba yashigo yana fad'in tofa yau gidan biki akene?
Sukayi dariya, kowa ta gaidashi, sannan sukace munzo sannu da zuwane.
Baba yazauna yana fad'in ince ko har Aysha taje muku?.
Sukace aii baba tun d'azu ma kuwa.
Ya ce, "auta kenan sarkin hidima, nan dai sukayita hira, harma baba yay musu bayanin maganar auren yayansu.
Sunyi murna kwarai da gsk.
Washe gari uncle G! Yataho damasu kawo kud'in aure, anyi musu tarba ta mutunci, daganan komai ya gudana, atake kuma baba ya saka ranar aure nanda wata hud'u, iyayen uncle G! Sunji dad'i domin kuwa babu wani jan rai, bayan sun kammala uncle G! Yakaisu tasha suka hau mota domin komawa gida.
Haka rayuwa tacigaba da gudu da sauri, sopy tana karatu, kuma sukan yi hira jefi jefi da uncle G!, Dan bai cika takurata ba, saboda Baya son tasamu matsla a karatunta, yakan taimaka mata akan abinda yashige mata duhu, dukda har yanzu tananan cikin jin kunyarsa bata cika sakin jikintaba idan yana guru, zuwa wannan lokacin kuma labari yabaza makaranta cewa uncle G! Zai auri safiyya.
Wasu har zuwa suke takanas domin ganin mai sa'ar data samu zuciyar tsadajjen namiji mai aji da ilimi irin uncle G!, dayawa sukanyi mamakin ganinta, dan azatonsu farace k'al kuma mai shegen k'yau๐ฉ๐ป, wasu sukance dama masu k'yau basu cika zab'ar mace mai k'yauba, wasukuma sukanga safiyyan tadace da uncle G! D'in, domin itama tanada k'yau, sai dai k'yawunta mai b'oyuwane, irin wanda saika cika kallonta ko kana tareda ita kullum kake gani, to koma dai miye 'yammata saiku saurara domin kuwa safiyya itace tauraruwar uncle G!, dan shiyyasan sirrikan daya gano agareta.
Magulmata dai anata aikin gulma, yayinda wasu 'yammatan suke jin haushinta dan sunnunama uncle G! D'in so amma yay burus dasu, itakam ko kallo basu ishetaba dan bata shiga sabgar kowa, garama Nadiya sukan d'anyi hira amma itama bakomai tasani dangane da sopy ba.
Dan sopy ta daina k'awa bare AMINIYA, anriga anmata tabo azuciya akan AMINTAKA............โ๐ป
๐Bily๐
๐๐Mrs Abdus'salam๐๐๐
๐I LOVE YO[12/19, 7:25 PM] mrs bilkisu: 29~October~2016
๐ท๐นNI DA AMINIYATA!!!๐น๐ท
NA BILKISA IBRAHIM๐
๐ถ๐ธ3โฃ0โฃ๐ธ๐ถ
........Akwana atashi babu wuya gurun "UBANGIJI", biki dai ya kankama, dukkan gidajen biyu sunata shiri, hakama uncle G! Yayi wuyar gani, ita kanta sopy baganinsa takeyiba, sai idan yaje musu lecture, ko kuma idan ya kirata a waya su gaisa.
Yau da yamma Sopy tashigo anguwarsu, tana shigowa layinsu tayi kicib'is da Abdul, suduka gabansu ya fad'i, yabita da kallon k'urullah, itako ta tamke fuska kamar bata tab'a dariyaba, ta ratseshi zata wuce, da sauri yasha gabanta, takauce zuwa gefensa nanma ya tareta.
Ta ce, "malam bani hanya nawuce.
Ya ce, "haba gimbiyata ninefa Abdul d'inki mai sonki da k'aunarki, wlhy ina kewar rashin ganinki, dan ALLAH ki tsaya muyi magana.
Ta balla masa harara tareda jan wani mugun tsaki ta ce, "kaga malam tunkafin na shuka maka rashin mutunci kabani hanya na wuce, wlhy Abdul natsaneka.
Ya rinyse ido ya bud'e dan tabbas kalmar tata ta daki zuciyarsa, ya marairaice murya yana fad'in, Sopy nasan baki tsaneniba haryanzu kina sona, kina cikin b'acin ran abinda yafaru abayane, dan ALLAH kibani dama namiki bayani yanda zaki fahimceni, kece kad'ai nakeso kuma ashirye nake dana aureki ahalin yanzu.
Sopy ta tuntsure da dariya, sannan ta tamke fuska tamkar ba ita tayi dariyarba, ta nunashi da d'anyatsa ๐๐ปโนAbdul wai kaine! kake tunanin zama mijina!, tad'an murmusa, Abdul har abada bazan zama shashashar macen dazanyi miji irinkaba, ka d'auka SAFIYYA IBRAHIM KABEER ta sub'uce maka har gaba da abada, ta ciro kati daga jakarta ka karanta wannan shi kad'aima ya isa yabaka amsa, inama gayyatarka, dan nasamu miji mai tarin ilimi k'yau, aji mutunci, kai idan ina lissafa maka abinda ya dangan ceshi tofa sai mu kwana anan,kuma katashimin ahanya kafin natara maka mutane wlhy.
Jiki asanyaye yamatsa mata ta wuce, tunda yafara karanta katin yake fitar da numfashi mai kama da nishi, yajingina da bango gudun karya fad'i, cikin murya kamar mai kuka ya ce, "fareeda kin cuceni ALLAH ya isa tsakanina dake, kuma wlhy yau saikin gayawa aya zak'inta, yanufi gida kamar mayun wacin zaki.
Da sauri muka bishi dan muganewa idanmu abinda zai faru.
To bari mugani fareeda kota zubur da cikin??.
Tunda nagabato b'angarenta nakejin ihun kukanta, wanda inada tabbacin suma mutanen dake gidan sunajinta, amma babu wanda yay yink'urin zuwa yaga abinda yafaru.
Nak'arasa d'akin da sauri nida madina, Abdul ne ke lakad'awa fareeda dukan 'yan danbe, duk yaji mata ciwo, amma wannan baisa ya daina d'irkartaba, dak'yar muka iya kwatarta, ya bimu da kallo yana huci kukuma daga ina??.
Madina ta ce, "tofa, Abdul maida wuk'ar mu bak'in fareeda ne, yaja tsaki tozaku iya tafiya aii ko.
Na ce, "kayi hak'uri Abdul kabari mu taimakawa fareeda kaga duk ciwone a jikinta, wata uwar harara yasakarmin, to aii ko uwar tace tazo gidannan saita fita, tunda sunce sun sallama mini ita, bareku gayyar sod'i, wlhy tun kafin nabud'e idanuna kubar gidannan idan kuwa bahakaba tokuwa jikinku zai fad'a muku.
Aii kafin yagama rufe baki madina uwar 'yan tsoro taja hannuna munyi waje, ta ce, "humm aunty bily naga mutuminnan yafara haukacewa wlhy zai iya dukanmu, kekam gaki lutiya idan yasamu wannan tsokar aii kinga takanki.
Na balla mata harara ina fad'in ALLAH madi kin rainani, ni son k'ibar nan tawa nakeyi idan baki saniba.
Amma gsky Abdul bashida mutunci irin wannan duka dayake mata kamar wata karuwarsa, kuma muta nen gidan sunaji amma sunk'i cetonta.
Madina tayi dariya aii ni dad'i nakeji wlhy ALLAH yasa yay mata abinda yafi hakama, aii maganin maci amana kenan, kad'amma tagani.
To yaudai lefe ya iso na sopy, mota guda muta nen GURUM sukayo domin kawo lefen Safiyya.
Akwati uku da karami na sama, babu laifi uncle G! yataka rawar gani, dan lefennan saidai mak'iyi amma yayi atalauce ba a sarauceba, anyi musu tarba ta mutunci, irin wadda suka tabbatar da sunzo gidan karamci, sun kuma tabbatar d'ansu yasamu d'iyar gidan tarbiyya,agidansu fareeda aka amshi lefen dan babanta ne zai d'aurama Sopy aure, aka had'a musu shatara ta arzik'i sukatafi, suna yabon wad'annan muta nen kirki.
Sopy tagama shirinta tsaf, tafito tana fad'in inna nashirya bari natafi kafin su cinyeni da masifarsu, bakamar aunty Nafisa sai bala'i takemin ina b'ata musu lokaci.
Inna ta ce, "to adawo lfy, kuma aii sunfiki gsky tun yaushe suke jiranki amma kina d'aki kina lank'andi, aii mijinki yaga takansa, mutum yay ta abu kamar kwai yafashe masa aciki.
To yi hak'uri inna bari natafi ina k'ara b'ata lokaci.
To ki gaishesu, kicema yayar taku gobenfa sutaho da wuri dan ayi aikin cin-cin d'innan agama da wuri.
To inna zan fad'a mata, tatafi tana dariyar inna, tunda bikinnan yamatso kullum tana kan aikin abubuwa bata ko hutawa .
๐ถ๐ธ3โฃ1โฃ๐ธ๐ถ
..............Da sallamarta tashiga gidan, suduka suka hauta da jaraba, aunty hauwa'u ta ce, " 'yarrainin wayo, kin zauna kinata yan kwana mu, saikace mu zai amfana, gwarama ki nutsu dan wannan mijin naki d'an kwalisa gara kije masa zam zam d'inki, ki rik'e abinki tunkafin wata takwace miki, irin wad'anna rubibinsu akeyi.
Sopy ta tab'e baki, nidai baruwana, dan tun wurima idan wannan zancen zakumin na koma, aunty asiya matar uncle kabeer ta tuntsure da dariya, barsu d'iyata wad'annan yayun banzane zoki zauna, aunty nafisa ta ce, "karma tazauna aii ita zai amfana bamuba, hakadai sukaita tsokanar sopy tana musu shagwab'a.
Gyarata suke kamar babu gobe, tundaga jikinta harzuwa inda ba'a fad'a๐ sunsha gyara, zata zauna agidan auty Nafisa dan suci gaba da gyarata, tunda bawasu k'awaye garetaba wad'anda zasu takura mata.
Bata zuwa ko'ina daga d'aki sai tsakar gida, kunji 'yar gatan auntys d'inta, wayartama ankarb'a ankashe, hankalin uncle G! Duk yatashi yanaso yaganta kodan su tattauna amma hakan tak'i samuwa.
Ya kira uncle kabeer ya tambaya?.
Uncle kabeer ya ce, "lafiyarta k'alau wlhy, nima haka nemanta nake amma tak'i yarda naganta, way tana wani gida b'oyo.
Tofa, uncle G! Yafad'a, to watake b'oyemawa??.
Uncle kabeer ya ce, "agonta mana.
Uncle G! Yay dariya to shikenan tunda dai lfy ai da sauk'i, amma yakamata kazo gobe mu had'ufa.
Okey to badamuwa, zuwa k'arfe hud'u zan shigo insha ALLAH.
TO ALLAH YAKAIMU.
yau k'unshi amma babu amarya, inna sai fad'a takeyi akan b'oye Sopy amma sunk'i fito da'ita saidai subata hak'uri, can gidan aka kai mai k'unshi tamata ta'iya sosai wlhy karkuga yanda Sopy tayi k'yau kamar ba'itaba, jikinnan yasha gyara, Nadiya kad'ai tasan inda take, dan ita take kula da abinda yashafi k'awayensu na makaranta da wanda sukayi secondary tare.
Sai a daren d'aurin aure aka dawo da sopy gidansu, inna ta rud'e daganin k'yawun da sopy tayi, sai latsa jikinta take tana fad'in kaga yara da dabara mikukaima auta na ne tayi haka?.
Su aunty asiya sai dariya suke ma inna.
Inna ta ce, "A lallai dole nabaku tukuyci dan gyaran dakukaima autata yayi.
MASU IYA MAGANA SUKANCE RANA BATA K'ARYA SADAI UWAR D'IYA TAJI KUNYA, to haka kuwa wannan ranar take ga uncle G! da Sopy.
Ayau dai and'ara auren Youseef Hussein Ahmad da Safiyya Ibrahim kabeer, karkuso kuga wankan shaddar da ango yayi, yayi kyau matuk'a, da yawan d'alibansa da malamai 'yan uwansa sun halarci d'aurin auren, mutanen GURUM kuwa aii ba'a magana, matasan garinsu d'ai d'aine basu zoba, sai washe baki yake dan farin ciki wasuma bai sansuba, lallai naga taron gagarimin d'aurin aure, abin sai wanda yagani.
Dak'yar na iya nemo muku amarya sopy, itamadai taci gayu cikin wata atamfa mai k'yau, idan natsaya bayyana muku kwalliyarta sai nacika littafin, amma dai tabbas ta had'u tamkar zata gasar sarauniyar k'yau, tana zaune itada k'awaenta agidan su fareeda, dukkanin 'yan professional writer da Zumunta sunje, sunkumayi rawar gani wajen mik'awa Sopy gudummawa, canna hango Hauwa lele๐ kusada amarya, to sopy saimuce ALLAH yasanya alkairi.
Wajen k'arfe hud'u aka shirya amarya domin kaita garinsu uncle G!, dan sai ankaita can sun gama bikinsu, daga baya sai angonta yadawo da ita gidansu dake nan kano.
Sopy sai kuka take, dan iyayene suka zagayeta ana mata fad'a da nasiha, irin wadda akema amare, "sai dai wasu amaren basa d'aukar irin wannan fad'an saboda kunnen k'ashinsu", to ita dai sopy da alama komai yana zama a kwakwalwarta.
Da haka dai aka d'ungunma da amarya zuwa GURUM dake acikin k'aramar hukumar Tsanyawa, tareda gayyar 'yan uwa da abokan arzik'i, a k'awayenta Nadiya ce kawai taje, muma dai munbi ayari nida gayyar 'yan group d'ina dan kar abamu labari...................โ๐ป
๐Bily๐
๐๐Mrs Abdus'salam๐๐๐
๐I LOVE YOU MY FAN's๐๐
[12/19, 7:25 PM] mrs bilkisu: 30~October~2016
๐ท๐นNI DA AMINIYATA!!!๐น๐ท
NA BILKISA IBRAHIM ๐
๐ถ๐ธ3โฃ2โฃ๐ธ๐ถ
.........A garin GURUM su Sopy sun sami tarba mai k'yau, daga dangin uncle G!, Suma sunada kirki, ananma biki aka d'ora, da daddare matasa suka warware kid'in daya bama dangin sopy sha'awa, atak'aice an dai sha shagali.
Washe gari bayan sallar azuhur dangin sopy sukayi haramar komawa kano, bayan an k'ara yima amarya nasiha da jan kunne akan sirikanta da dangin mijinta, suka tattaro suka taho, aka baro amarya tana kwasar kuka.
Da k'yar gwaggo ta lallasheta dan ad'akinta suka barota, daga k'arshe gwaggo ta lallab'ata tayi barici, kunga sirikan kwarai masu tattalin matan 'ya'yansu.
Libabatu ta gyara b'angaren da su sopy zasu zauna kafin sutafi, wato b'angaren uncle G! Kenan, acan gefe yake akatange babu ruwanta da sirikanta saidai idan sun shiga, gyara sosai tayi ma b'angaren, ta amshi turaren wuta wajen gwaggo taje takunna, tak'ara da da wasu turarurrukan data gani ad'akin, azuciyarta ta ce, "oh ni liba, kaga d'akin yaya kamar na mace, nan dai tagama tafito.
Uncle G! Kuwa bayan yagama hidimar sallamar bak'i masu tfy, saikuma yashiga sabgogin sallamar 'yan uwa da abokan arzik'i dake nan, dakuma mammaida kayayyakin da'aka aro na mutane.
Sai gab da magriba aka maida Sopy b'angarenta, aunty hafsa da kanta ta had'a mata ruwan wanka, Sopy ta ce, "nagode aunty!, aunty hafsat tayi murmushi bakomai k'anwata jekiyi wankan, dan muma tafiya zamuyi, lubabatu nacan tana jirana, sai da safe.
" Sopy ta ce, "to ALLAH yakaimu.
Bayan fitar aunty hafsa Sopy tashiga wanka zuciyarta cike da tunani iri-iri, tagama wanka tafito sukayi kicib'is da lubabatu, lubabatu ta ce, "to amarya muzamu gudu gida, sai gobe nazo cin kazar amarci, kifa ragemin.
Sopy tayi d'an murmushi ta ce, "to.
Libabatu tana tafiya sopy tashiga d'akin, tabi d'akin da kallo babu wani tarkace, katifa ce k'atuwa an lailayeta da zanin gado, sai wardrobe ta zuba kaya itama k'arama, sai kujera doguwa a gefenta akwai firij, saikuma wani tebir da kujera agefensa cike yake da littatafai, da alama library d'in uncle G! Ne, ba laifi d'akin yayi k'yau a talauce ba a sarauceba.
Ta zauna tashafa mai tayi kwalliya mai d'an sauk'i, wata atamfa tasaka siket da riga, sun kama jikinta sosai, ta ja k'aramin tsaki nikam bana son kaya su matseni, amma na lura duk haka aunty hauwa'u ta d'inka min kayana.
Haka ta zauna tana gyaran kai tana mitar d'inkunan, nace ashe Sopy tanada gashi ba laifi, dan dai tana b'oyeshine, tagama ta gyara gurin, sannan tahau sallah, bayan ta idar ta zauna agurin har aka kira sallar isha'i, ta tashi tayi.
Ta cire hijjabin kenan tanufi waje akwatin ta dan d'aukar k'aramin hijjabi wanda baikai girman wanda tayi sallarba.
Uncle G! Ya shigo d'akin da sallamarsa, Sopy tarikice tarasa inda zata dosa, wajen akwatin ko kuwa wajen hijjabin data gama sallah yanzu?.
Shima uncle G! Tsaye yake kam cikin farar shadda k'al yaukam harda hula, sai bulbula k'amshi yakeyi, fuskar nan tasa fayau da annurin angwanci, ya kasa koda motsi dan d'imautuwa da surar Sopy, ya tambayi kansa? wai dama haka sopy take da diri da cikakkiyar sura ta d'aukar han kali, lallai dolene ya godema ALLAHn daya halicci wannan k'ak'yk'yawar sura.
Ahankali ya k'arasa gareta, tasaka hanu tana kare k'irjinta๐
, ta rintse idanu danjin uncle G ya mannata da jikinsa, cak ya d'auketa ya dire saman kujera, shima ya zauna, kallonta yakeyi sama da k'asa kamar yau yafara ganinta.
Itako kanta yana k'asa tana wasa da zoben hannunta, ta daure ta ce, "ina yini?, yaja wata sassanyar ajiyar zuciya tareda kama hannunta ya r'intse anasa.
Jitayi tsigar jikinta