Showing 54001 words to 57000 words out of 58156 words

Chapter 19 - Ni Da k'awata HAUSA NOVEL

02 Dec 2024

4846

adon mace .
Sopy tad'anci Awarar, dan tayi mata dad'i sosai, bayan tagama ta k'ara kwanciya, uncke G! ya ce, "tashi kid'an zauna ki huta, kar kwanciyar tayi yawa.
Gwaggo ta ce, "A'a kabarta ta kwanta, k'ila tafi jin dad'in kwan ciyar.
Ya ce, "to.

Sai dare su aunty hafsat suka tafi.
Baba ya sissiyoma sopy abubuwan kwad'ayi ya ce, "abata taci, bayan yai mata sannu suka tafi b'an garensu.
Uncle G! ya kalleta yana murmushi, ya ce, "lallai ke 'yar gata ce, kowa jiyake dake, tayi murmushi tana fad'in kokana kishine?.
Ya murmusa tareda d'ora hannunsa akan cikinta, ya ce, "bawani kishi, kema aii gamasu kwace miki fada nan sun kusa zuwa.
Cikin rashin fahimta sopy ta ke kallonsa, ta daure ta ce, "ban gane abinda kake nufiba??, ya kanne mata ido d'aya ya ce, "zaki gane, alokacin da yarona ko yarinya suka fara aikin 'yan kwallo acikinki.
Sopy ta zaro idanu waje ta ce, "kamar ya ya?, ya kwanto da kanta bisa cinyarsa, yad'ora hannunsa saman cikinta, d'ayan hannunsa yana shafa gashin kanta, ya ce, "Inada babbar ajiya awannan cikin, ma'ana saka makon ciyonki na bayyanar yarona ne.
Sopy tasaka hannu ta rufe fuska dan tagane miyake nufi, yay 'yar dariya, lallai yarinya kardai kice yarona d'an farin k'auye za'a maidashi?, to wlhy ban yardaba, garama tun yanzu na fad'a miki, dan banyarda a b'oyema yarinyata ko yarona suna ba, banyarda atureshi saboda yazo a matsayin d'an fariba, yasa hannu ya cire hannunta data rufe fuska dashi.
Saita rintse idanuwa, yakai bakinsa kan nata, yafara al'amura.
Na ce, "hummmm shidai uncle G! baya gajiya dayin kiss, bare kwana biyu ba'a had'uba.

Haka al'amura suka cigaba da tafiya a gurum, sopy tana shan tarairaya, duk abinda ta ce, "tana so sai an nemamata, koda awajen gurum yake kuwa, gwaggo ta hanata aikin komai, d'akinsuma Aysha ce take gyarawa kullum, a b'an garen uncle G! kuwa abin ba'a magana, suma su lubabatu suna bada gudummawa, dahaka sati biyun dasuka d'ebo tacika.
Amma baba da gwaggo sun hana tafiya, sunce tunda ba'a koma makarantar ba to bazasu tafiba sai sopy ta k'ara samun sauk'i, badan uncle G! yasoba dole ya hak'ura.
Shikam yana so su tafine dan yana cikin takura, gashi kuma wata sa'inma sopy a d'akin gwaggo take kwana idan jikin yay tsanani, itama kanta sopyn ya lura yanzu gudunshi takeyi.
Itako sopy bataso uncle G! yazo mata da buk'ata ne, shiyyasa take baya2 dashi, dan bata so yacika takura mata.
Kunsan wani cikin yana faruwa haka.

In tak'aice mu dai saida sukayi wata d'aya dawasu kwanaki, dan saida aka sanar an koma yajin aiki sannan baba yabarsu suka dawo kano.
Sun dawo cike da kewar muta nen gurum, yayinda suma suka barosu da kewarsu.
Tsaf suka tarar da gidansu an gyara, wananan duk aikin aunty Asiyane, sunji dad'i sosai, suna zuwa sai wanka da cin abincin da aunty asiyar ta aiko musu.
Bayan sun gana suka kwanta dan su huta.

A b'an garen fareeda kuwa al'amira sai ahan kali, dan ba komai take nema ta samuba, sauk'in tama tana agidan su sopyne, amma tayi bak'i ta rame kamar ba'itaba, kullum sai inna ta ce, "taje ta gaidasu mama.
Badan tasoba take zuwa, dan idan taje gidan sai mama ta had'e mata rai, daga ita har baba basa sakar mata fuska, lamuran suna damunta, amma tasan laifintane.
Yau ma tana zaune ad'akin sopy nada, ta had'a kai da guywa, hawaye suna kwaranya a idanunta, tana tuna rayuwa irin ta gidan sopy, duk da uncle G! bamai kud'i bane, amma yana k'ok'ari akan iyalinsa, yana wadatasu da cima mai dad'i, amma nan daga tuwo sai shinkafa, tarik'e kai tana hawaye.
Araina ne ce, "su fareeda anji jiki, an shiryu badan ALLAH ba๐Ÿ˜œ.....................โœ๐Ÿป





๐Ÿ’žBily๐Ÿ’ž
๐Ÿ’ž๐Ÿ’žMrs Abdus'salam๐Ÿ’ž๐Ÿ’ž๐Ÿ’ž
๐Ÿ’žI LOVE YOU MY FAN's๐Ÿ’ž๐Ÿ’ž
[12/19, 7:26 PM] mrs bilkisu: 27~November~2016





๐Ÿ”ท๐Ÿ”นNI DA AMINIYATA!!!๐Ÿ”น๐Ÿ”ท




NA BILKISA IBRAHIM๐Ÿ’ž



๐Ÿ”ถ๐Ÿ”ธ5โƒฃ7โƒฃ๐Ÿ”ธ๐Ÿ”ถ


BAYAN WATA TAKWAS
...........Rayuwa mai gudu da sauri, daga safiya tayi sai gari ya waye, fareeda dai an shiryu da gsk, dan takoma makarantar islamiyya, gashi takoma wata shiru2, batada burin daya yuce tasamu miji tayi aure itama ta zauna agidanta, kullum kuma tana cikin yin istigifari, takan shiga gidansu ta taya mama aiki, dukda har yanzu mama bata sakar mata fuska, haka aikin inna duk ita takeyi, damuwar ta d'aya sopy, dan har yanzu sopy bata yafe mataba, ko gidan tazo bata kulata, gaisuwama sama2 sukeyi, kullum burinta ALLAH yakawo randa sopy zata yafe mata sukoma yanda suke da.
Inna tana k'ok'ari wajen yiwa sopy nasiha akan tayafema fareeda tunda ta shiyu, duk sanda tazo gidan saita yimata irin wannan nasihar.
To itama sopyn tayarda fareeda ta canja, amma tanaso tak'ara shiryuwane kafin ta ce, " ta yafe mata, dan tuni ta yafema fareedar batadai furta bane kawai.

GIDAN SOPY
Sopy anata fama da k'aton ciki, wanda da'alama ranar haihuwa kawai ake jira, dan tama daina zuwa makaranta.
Afalo na isketa itada uncle G!, tana zaune a saman kafet ta mimmik'e kafafuwa, tasaka filet d'in kankana a tsakkiya tana sha, uncle G! Yana gefenta kwance a doguwar kujera.
Ya kalleta ya tuntsure da dariya, sopy tajuyo tana kallonsa, ta ce, "miya baka dariya? hubbina!.
Cikin dariya uncle G! Ya ce, "wlhy ke kika bani dariya sopyna, jibi yanda kika mik'e kafafu kina shan kankana, ALLAH kirage ci, nakula aranafa saikici abinci sau biyar.
Sopy ta murgud'a baki๐Ÿ˜ tana fad'in to waye yaja mini?, aii dai kowa yasan da bahaka nake da ci kamar jakaba ko?.
Uncle G! Ya kwashe da dariya, ya ce, "aina kusa kad'a miki tanbarin acici kazar gona.
Sopy ta watsa masa harara, saikuma ta shagwab'e fuska tafara kukan shagwab'a, ya sakko yana gintse dariya, kusada ita ya zauna yana shafa bayanta ahankali, acikin kunnenta ya ce, "yakamata kibar shagwab'a, dan kinkusa zama momy.
Yasa hannu ya share mata hawayen fuskarta.
Ta ce, "to ba kaibane kake tsokanata, ya sumbaci kuma tunta yana fad'in to yi hakuri na bari maman baby.
Yanzu mikikeso nayi miki danki huce, ta nuna masa k'afafunta da sukayi d'an fushi.
Yay murmushi dan yasan mitake nufi, ahankali yafara mammatsa mata kafafun, ita kuma tafara lumshe idanu, ya ce, "karfa kiyi mini barci 'yammata!!.
Sopy tad'an bud'e idanu tana murmushi, ta ce, "kasan kuwa harna fara jin barcin wlhy.
Ya ce, "aii ke yanzu kin zama kasa, dan ko fira bak'ya barinmu muyi, b'urun2 saikice aje akwanta, ta ce, "to yazanyi hubbina!, nima ba laifina bane, ya ce, "gsky ne laifin babynane, yafad'a yana kanne mata ido d'aya.
Ta ce, "yauwa hubbina wai yaushe kacema Aysha zata zo?, ya ce, "sai ranar juma'a, tunda ta ce, "Al'hamis za'ayi musu hutu.
Sopy ta ce, "ALLAH ya kaimu, yakuma kawo mana ita lfy.
"Amin uncle G! Yafad'a yana murmushi.

๐Ÿ”น๐Ÿ”น๐Ÿ”น๐Ÿ”น๐Ÿ”น๐Ÿ”น๐Ÿ”น
Yau dawuri uncle G! yafita dan zaiyi lectures d'in safe.
Sopy ta tashi tad'an gyara gidan iya inda zata iya, dan yau bata jin dad'in jikinta kwata2, tana dai daurewane dan bataso tahana uncle G! fita aiki, tad'an cije leb'e ta rik'e bayanta da hannu d'aya, tadafe kujera da d'ayan.
Tad'an dad'e tsaye tana shan azabar ciyo, daga bisani yalafa, ta rarrafa dak'yar takoma bedroom.
Tana zuwa tazube agado, tanata murkususu, saidaga baya wani bacci mai dad'i ya saceta.
Agigice ta farka domin jin wani azababben ciyo, mai kamada na fitar rai, ai bata san sanda ta silmiyo daga gadoba, babu abinda takeyi sai salati da kiran sunan ALLAH, dak'yar ta iya d'aukar wayarta, batare da tasan nomber ko wayeba takira kawai, ALLAH yasota aunty Asiya takira, dak'yar ta ce, "plz kowaye yazo ya taimakeni zan mutu.
Aunty asiya bata jira ta karasa ba, ta fito da sauri daga gida, gidansu ummy ta mik'a khalil, agurguje tazo gidan, sanda ta iso sopy harta fita hayyacinta, dan kuwa haihuwa ce gadan2.
Aunty asiya ta rik'eta tana mata sannu.
Ita dai sopy babu abinda takeyi sai ambatar sunan ALLAH, da duk addu'ar datazo bakinta, zuwa can tasaki wani uban nishi, jikake wani kacam, d'a yafad'o, yana tsanyara ihu.
Aunty Asiya ta ce, "masha ALLAH, sopy sannu da aiki.
Aunty asiya takira ummy ta ce, "ta turo mata mamarsu.
Babu dad'ewa mamarsu ummy tazo, aka yanke cibiya, tareda d'auke sargad'ed'iyar yarinya maikama da babanta, maman ummy ta ce, "masha ALLAHU, da zuwan wannan k'yak'yk'awar yarinya duniya gidan gwa gwarmaya.................โœ๐Ÿป






๐Ÿ’žBily๐Ÿ’ž
๐Ÿ’ž๐Ÿ’žMrs Abdus'salam๐Ÿ’ž๐Ÿ’ž๐Ÿ’ž
๐Ÿ’žI LOVE YOU MY FAN's๐Ÿ’ž๐Ÿ’ž

27~November~2016




๐Ÿ”ท๐Ÿ”นNI DA AMINIYATA!!!๐Ÿ”น๐Ÿ”ท



NA BILKISA IBRAHIM๐Ÿ’ž



๐Ÿ”ถ๐Ÿ”ธ5โƒฃ8โƒฃ๐Ÿ”ธ๐Ÿ”ถ

...........tsaf suka gyara jaririya da sopy, Aunty Asiya takira uncle kabeer ta sanar masa, shikuma yasanar da uncle G!, dan danan labari ya karad'e dangi, har muta nen Gurum labari yakai musu, acanma murna ce ta kaure, da addu'oin fatan alkairi ga jaririya, bak'uwar duniya.
Uncle G! ya iso cikin murnarsa, bai damu da makwaftan dasuke zaune afaloba, suka gaidashi tareda yimasa barka.
D'akin sopy ya isa cikin matuk'ar zumud'in son ganin jaririyarsa, yana shiga ya rungume sopy dake bakin gado tana shafa mai, dan batajin ciwon komai, saidai aunty asiya ta ce, "ta shirya suje asibiti aduba lafiyarta itada baby.
Sopy tad'ago tana kallonsa, suka sakarwa juna murmushi, ya ce, "sannu sopyna, ya jikinki??, sopy ta ce, "komai nomal hubbina.
Ya ce, "masha ALLAH, aunty asiya tashigo da sallama, suka amsa, ta mik'a masa jaririyar da'aka shirya cikin fararen kayan sanyi masu laushi.
Yasa hannu biyu yakarb'a, ya tsura ma jaririyar ido kamar zai cinyeta, yad'an mannata da jikinsa tareda lumshe idanu yana zubar da hawayen farinciki.
Sopy tasaka hannu tana share masa, yad'an dad'e ahaka sannan ya bud'e idanu, ya sauke akan jaririyarsa, mai tsananin kama dashi, tanata barcin ta.
Tad'an motsa kad'an, yay saurin fad'in sorry my dear, yad'an jijjigata kad'an, takoma barcinta.
Sopy ta ce, "hubbina santin baby ya hanaka magana ko??, yad'ago yana murmushi, ya ce, "sopyna k'yautar d'a!! dabance, bazan iya misalta miki irin farincikin danake cikiba yau wlhy.
Sopy ta ce, "aii naga alama, dadyn baby!!.
Uncle G! ya ce, "haka zancen yake, amma zonabaki sunan babyna, sopy ta mik'ama uncle G! kunnenta, ya gwargwad'a mata, tayi wani murmushi tana fad'in inko haka ta kasance to kayi halacci hubbina!.
Ya ce, "ko? Sopyna!.
Ta ce, "ALLAH kuwa.
Ya ce, "anyi an gama, barima kiga nayi maya hud'uba.
Uncle G! yay mata hud'uba sannan suka tafi asibiti dan aduba lafiyarsu.
Haka akayita hidima, koda yaushe gida cike da 'yan barka, su aunty Nafisa kuwa kullum sai sunzo, fareedama tazo saidai sopy bata sakar mata fuskaba sosai, itako fareeda bata damuba tanata rungume jaririya danji take wata irin k'aunar yarinyar tana shigarta.

Yau muta nen gurum sukazo mota guda, aka had'a musu cima masu dad'i, sukaci sunata santi, sai yamma suka tafi akabar su aunty hafsat da libabatu da aysha anan, komai yana tafiya yanda akeson gwaggo ta had'o ma sopy kayan barka sosai, mutane sunata santi kayan, dan gwaggo ta taka rawar gani.
Yau kuma aka kawo naman k'auri daga gidansu sopy, suma sunyi k'ok'ari, dan d'an akuya guda uncle kabeer ya siyo aka gyara, suma sunyi rawar gani wajen had'o kayan barka, ayau kuma shima uncle G! ya kawo nasa kayan barkar, abindai sai wanda yagani, komai dai2 saidai mak'yi zai kushe.

RANAR SUNA.
yaune akasha sunan baby wadda taci sunan BILKISU MAI GADON ZINARI", lallai uncle G! yay mini halacci kuma nagode.
Bayyana muku yanda taron suna yakasance b'ata lokacine saidai fa, ansha shagali na ban mamaki, groups dayawa sun halacci taron sunan baby Bilkisu!, irinsu.๐Ÿ‘‡๐Ÿป
๐Ÿ’žPROFESSIONAL WRITER
๐Ÿ’žZUMUNTA GROUP
๐Ÿ’žHAUSA NOVELS
๐Ÿ’ž MANSHAT NOVELS
๐Ÿ’žPRECIOUS WRITER' FORUM
๐Ÿ’žIKKIAM'S NOVELS
๐Ÿ’žHAUSE OF NOVELS
๐Ÿ’žSO DA K'AUNA GROUP
๐Ÿ’žFASHION & NOVELS
๐Ÿ’žBEST FRIEND'S
๐Ÿ’žLABARUN LITTATAFAI
๐Ÿ’žHAUSA NOVEL BOOKS
๐Ÿ’ž MACE MUTUM GROUP, ma sun halacci wannan taron suna, harma da groups d'in daban fad'aba, suyi hak'uri amma suma duk mun gansu.
Dahaka taron suna yatashi lafiya, akabar mai jego da jaririya Bilkisa, tareda dadynta uncle G!!!.
An kawo musu tsohuwar dazata kula dasu, har suyi arba'in, AYSHA ma ta nan anbarta, saboda wasu ayyukan.

Bayan arba'in, baby Bilkisu tayi b'ul2 da'ita gwanin sha'awa, tana shan tarairayar iyayenta, dan uncle G! yana dawowa aiki zai d"auketa sallah ce kawai takesawa ya ajiyeta, ranar weekend kuwa ai ahannunsa take wuni, yayta mata wasa tana b'angale baki, sunje Gurum yawon arba'in, an kaiwa gwaggo da baba sunga jikarsu, takosha addu'oi, awajen kakanninta.
Ananma kano sun zagaya gidajen 'yan uwa da abokan arzik'i, daga baya sopy ta tattara takoma makaranta itama..................โœ๐Ÿป



WASA KWAKWALWA.
wannan sak'one daga gareni, inaso ku fad'i abinda yake ranku game da wannan littafi mai suna NI DA AMINIYATA!!!.
SHIN WA๐Ÿ‘‡๐Ÿป
โ˜†WAKUKAFI TAUSAYI??.
โ˜†WAKUKAFI JIN HAUSHI??.
โ˜†WAKUKAFI SO???.
โ˜† WAYAFI BIRGEKU??.
Karki bari ayi babu ke, fad'i ra'ayinki, ko gyara gareni agun danayi kuskure.
Idan kuntashi, kusaka sunanku, da gruop d'in dakuke, dakuma ra'ayinku.
Inanan ina jiran sak'wanninku, ta hanyar gruop gruop d'inku, dan saikun rubuta ra'ayoyinku kafin mu kalmashe bakin wannan labari, daga nan zuwa ranar litinin.
Plz karkuyi sanya, nagode sosai da k'yaunarku gareni.
SAINA JIKU๐Ÿ“ข๐Ÿ“ข๐Ÿ“ข๐Ÿ“ข!!!!!!!!!!!!!.





๐Ÿ’žBily๐Ÿ’ž
๐Ÿ’ž๐Ÿ’žMrs Abdus'salam๐Ÿ’ž๐Ÿ’ž๐Ÿ’ž
๐Ÿ’žI LOVE YOU MY FAN's๐Ÿ’ž๐Ÿ’ž

[12/19, 7:26 PM] mrs bilkisu: 28~November~2016





๐Ÿ”ท๐Ÿ”นNI DA AMINIYATA!!!๐Ÿ”น๐Ÿ”ท




NA BILKISA IBRAHIM๐Ÿ’ž



๐Ÿ”ถ๐Ÿ”ธ5โƒฃ9โƒฃ&6โƒฃ0โƒฃ๐Ÿ”ธ๐Ÿ”ถ

.............haka rayuwa tacigaba da tafiya, su sopy suna rainon baby bilkisu, yanzu haka tafara zama, uncle yadawo da Aysha wajensa, an nema mata makaranta tana yi anan, haka sopy tana zuwa makaranta kuma tana fahimta, abunda bata ganeba uncle G! yana nuna mata.
Adai2 wannan lokacinne kuma aka sha bikin fareeda da wani d'an anguwarsu salmanu, yanada mata d'aya da yara uku, fareeda ta aureshine kawai amma badan yayi mataba, dole ta aureshi dan zaman gidan ya isheta, gasu baba sun dameta akan tafito da miji, to hakadai aka rurrumata aka kaita, indama ALLAH yasota ba gidansu d'aya da kishiyarta ba, gidan hayane d'aki d'aya ya kama mata, suna had'akar bayi da kichin da sauran 'yan hayar gidan, bawata cimar arzik'i, shinkaface fara da mai da rana da safe kuwa koko da k'osai shima idan kin samu, da daddare tuwo, dan haka fareeda duk tafita hayya cinta ga wani uban bak'i datayi kamar ba itaba, shiyyasa kullum cikin kuka take da nadamar abinda ta aikata abaya, ALLAH yasotama sopy tayafe mata harda uncle G!.
Agidan sopy kuwa abun su d'anas komai yana tafiya yanda suke so, ga mijinta yana nuna mata soyayya mai tsafta, koda yaushe k'ara tattalinta yake, itama k'ara sonshi take kullum, ga 'yar d'iyarsu abin sha'awa da burgewa.
Aunty asiyama ta sake haihuwar mace, itama suna cin soyayyarsu da uncle kabeer, komai yana tafiya musu dai2.
Haka yayun sopy sumadai Alhmdllh, komai dai2.
Mutan gurum ma a b'angarensu komai nomal masha ALLAH.


BAYAN SHEKARA TAKWAS.
Nayi shiri nida 'yan kazagina su madina, gidan uncle G muka nufa dan mu gano muku halin da suke ciki, tun a tsakar gida nafara gamo da yara biyu duk maza, 'yan kimanin shekara 6, d'aya ya ce, "mas'ud mima momy ta ce, "mukarb'o mata?.
Ya ce, "kaji mus'ab d'innan bakai ta gaya mawaba, zaka wani tambayeni?.
Mas'ud ya ce, "to mukoma mu tambayo?, tafd'i mus'ab yafad'a yana kallon mas'ud, ya ce, "wlhy bazan komaba kana ganin aunty bilkisu tana nemana ta daka saboda na d'aukar mata sweet d'azu, idan zakaje keje ina nan ina jiranka, dan baxan shiga cikin gidaba harsai dady yadawo.
Madina ta kalleni ta ce, "da'alam yarannan fa yaran sopy ne, bakiga kamabane??, na ce, "nagani madee kuma inaga tagwaye ne.
Ana cikin haka saiga uncle G! Yadawo, dagu su mas'ud sukaje suka rungumeshi, shima yataresu da murna, d'ai2 ya d'aukesu yana d'agawa, ya ce, "yaran dady sai ina??.
Mus'ab ya ce, "momy ce ta aikenmu kuma mun manta, uncle G ya ce, "to kumuje ciki.
Mus'ab ya ce, "dady ALLAH aunty bilkisu zata dakeni, uncle G ya ce, "kamata laifine ko??, mas'ud yay saurin fad'in dady sweet ya d'aukar mata, uncle G ya ce, "lallai kayima aunty bily babbab laifi, yafad'a yana jan hannunsu.
Muka gaidashi muma, sai asannan ya gammu, cikin murmushi ya ce, "lallai yau munada babbar bak'uwa, bily kece agidanmu?.
Nayi dariya na ce, "nice uncle G!, kuna nan lafiya?, ya ce, "lafiya k'alau muke, kushiga mana, aii sopyn tana ciki, mukace to.
A falo muka tarar da bilkisu rik'e da wata 'yar k'yak'yk'yawar yarinya, wadda zata kai shekara d'aya.
Bilkisu tazo ta rungume dadynta, yashafa kanta yana fad'in aunty bily ga takwararki, ta ce, "dady wace takwarata??, ya nuna mata ni, da sauri tazo ta rungumeni tana gaisheni, naja hannunta muka zauna saman kujera, su madinama suka zauna.
Uncle G! Yad'auki karamar yana fad'in little sopy ykk??, yarinya ta shiga tsalle

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login