Showing 39001 words to 42000 words out of 58156 words
dai yagama musu lecture d'in yafito, suka shiga gulmarsa akan kallon gurin zaman sopy dayayi tayi.
Daga nan wani ajin yaje yagabatar da lecture, sai karfe biyar na yamma yanufo gida, cikin zumud'in son ganin sopy.
Lokacin daya iso sopy tagama gyara gidan, tayi wanka tad'au kwalliya ta d'aukar hankali, ita kanta fareeda tana mamakin yanda sopy ta ke kwalliya yanzu, suna falo suna hira taji hon d'in motarsa, da sauri tatashi taje tabud'e masa get.
Tun yana mota yake sakar mata murmushi itama tana maida masa murtani, yay fakin takaraso bayan ta rufe get d'in, dakanta ta bud'e masa mota, maimakon yafito saiya jawota cikin motar ta zauna kan cinyarsa.
Ya kura mata manyan idanunsa masu haske yana wani murmushi mai k'ayatarwa, ta hure masa idanu tana murmushin itama, suka tuntsure da dariya, ta ce, my uncle kadawo lfy, saida ya sumbaci kuma tunta sannan ya ce, "lfy lau nadawo, saidai zuciyata tana nan gangar jikinace a makaranta.
Sopy tay wani far da idan ta ce, "da gsk uncle d'ina. Ya lumshe idanu cikin wani yanayi, domin farin nata yatafi da imaninsa, ya bud"e ahankali yana kallonta, sai dai yanzu idonsa yayi d'anja ya ce, "my sopy ina k'yaunarki dayawa, nakan rasa inda zansa sonki, ashe dama haka ma'abota soyayya sukeji??.
Sopy ta shafa k'irjinsa tana fad'in nima ina sonka my uncle d'ina har nakan rasa yanda zan musalta son naka.
Ya rungumeta tsam ajikinsa yana wani fidda numfashi dak'yar, sunkai tsawon minti biyar ahaka, sopy ta daure ta ce, "uncle mushiga ciki ko?.
Ya d'agota yana murmushi, ahankali yace kinsan ALLAH nama manta a inda muke, sopy ta tashi daga jikinsa tana 'yar dariya, ta zagayo tad'ayan gefen ta d'auki jakarsa ta aiki, shikuma ya bud'e baya ya d'auki wata leda suka jera zuwa cikin gida.
Fareeda tana zaune suka shigo, tai masa sannu dazuwa sannan ta gaisheshi, ya amsa cikin fara'a, ya kalli sopy yana murmushi ya ce, "ashe ma mara lafiyamu ta warke?, sopy tayi murmushi batareda tace komaiba.
Taja hannunsa tana fad'in sir muje kayi wanka kazo kaci abinci.
Uncle G! ya harareta ya ce, "waye sir d'in?, sopy tayi 'yar tafiya zuwa k'ofarsa sanna ta juyo ta ce, uncle G!! mana.
Da sauri yanufota, itakuma tashige cikin d'aki tana dariya.
Fareeda tabisu da kallo tana ayyana abubuwa dayawa azuciyarsa, ahan kali ta ce, "dama ace................saikuma tayi shiru, ๐ณnakuma zaro ido waje, wai ita wannan mitakeson fad'ane?????.๐๐
Ad'aki kuwa uncle G sunata zagaya d'aki da sopy yana son kamota, amma tak'i yarda, can yasa k'afa ya tad'ota suka fad'a kan gado suna dariya, yaymata rumfa da faffad'an k'irjinsa ya ce, "waye sir d'in??.
cikin dariya ta ce, "sorry bafa dakai nakeyiba.
ya ce, "dawa kikeyi?, ta ce, "to d'agani zan fad'a.
ya ce, fad'i ahaka mana.
Ta ce, "wlhy kacika nauyi zaka fasa min ciki.
Aiko yau sai dai cikin naki ya fashe dan bazan d'agakiba saikin fad'a.
Sopy ta ce, "wayyo ALLAH na inna kizo ki taimakeni, uncle G! Ya tuntsure da dariya, aii yau saidai ki kira duk wanda zakai kira amma babu alfarma.
Ta ce, "ALLAH kanada nauyi fa, ya ce, "kedai kika sani, batai auneba taji yana shafata, zaitai magana ya had'e bakinsa da nata, saida ya cakud'ata yanda yakeso sannan yabarta.
Ta mik'e tana kallon kayanta dasuka cuccurkud'e, ta shagwab'e fuska tana f'ad'in duk kayimin wani iri da kaya, d'aukarta yayi cak yay bayi da ita, tanata watsal2 da bashi hak'uri, amma bai sauraretaba, yadireta a bayin yarufe.
Ganitai ya hau cire kaya, tasa hannu ta rufe idonta, yay dariya yana fad'in k'yadai jidashi, amma yau dole kimin wanka shine hukuncinki.
Sopy ta durkushe kasa ido arufe dan ganin ya cire kaya gaba d'aya, ruwa ya d'iba yazuba mata ajiki, ta bud'e ido da sauri tana kallonsa, yay mata gwalo๐, doledai tayi masa wanka, itama yay mata suka fito๐............................โ๐ป
๐Bily๐
๐๐Mrs Abdus'salam๐๐๐
๐I LOVE YOU MY FAN's๐๐
[12/19, 7:26 PM] mrs bilkisu: 17~November~2016
๐ท๐นNI DA AMINIYATA!!!๐น๐ท
NA BILKISA IBRAHIM๐
๐ถ๐ธ4โฃ5โฃ๐ธ๐ถ
.........Rayuwa mai dad'i akeyi agidan uncle G, yana nuna mata soyayya irin wadda kowace mace take buk'ata a rayuwar aurenta,.
"dan gsky mazan mu na hausawa basu cika nunawa matansu soyayya ba, sukan fifita neman kud'i akan matansu, wani idan ba yazo biyan buk'atarsa ba, matarsa bazata tab'a rab'ar jikinsa taji dad'iba, inko tad'an rab'u jikinsa saiyace bata da kunya, gsky hakan ba dai dai bane, mu mata 'yan son soyayyane da tattali, muna son anuna kulawa akan mu, yakamata mazan mu su gyara, ba ayita nuna miki soyayya awajeba saikinzo cikin gida kiga sab'anin haka, wannan yanasa mata hange hange, ALLAH yasa mugane amin".
Yauma takama weekend dan haka uncle G! yana gida, su duka suna zaune afalo har fareeda, sopy na zaune saman doguwar kujera, uncle G! yana kwance ya d'ora kansa bisa cinyarta suna kallon wani hausa film, fareeda ma na zaune a kujera mai zaman mutum d'aya, itakam ba kallon ne agabantaba, dan taraba hankalinta gida biyu, rabi a kallon tv, rabi a kallon su sopy.
Uncle G yad'ago idanu yana kallon sopy dake shafa kansa ahankali tana kallo, yay d'an murmushi tareda saka tafin hannu ya kare idanunta daga kallon tv.
Cikin shagwab'a ta ce, "kai uncle neman magana ko?, ta cire hannunsa ta rik'e, yay dariya tareda fad'in to aii kece naga gaba d'aya kinbama tv amanar idanuwanki, ni koma kallona ba'ayi.
Sopy ta tuntsure da dariya ta ce, "o, kishi kake da tvn??
Ya d'anja hancinta yana fad'in indai akan Sopyna ne tofa komaima zan iya kishi dashi.
Sopy ta shafa sajen sa daya kwanta luf luf akan kumatunsa, suka zurama juna idanu tamkar zasu cinye kansu.
Sopy tafara janye nata tana d'an murmushi cikin yanayin kasala, shima saiya lumshe nasa idanun yana murmushi.
Fareeda dake kallonsu ta runtse idanu hawaye suka zubo, tai saurin sharewa da d'an kwalin kanta, tana mamakin yanda kullum Safiyya take kasan cewa asamanta, tunda take bata tab'a wuce safiyyaba, gashidai tafi sopy k'yau nesa ba kusaba, gata fara dirarriya, amma tun suna yara, sai sopy ta samu abu kafin ita tasamu, kuma kota samu saitaga na sopy yafi nata, da tana ganin idan ta samu Abdul kamar tawuce da sanin sopyn ne, amma sai sopy tazo ta auri wanda yafi Abdul komai na rayuwa, k'yawu, ilimi, kwarjini, aji, iya soyayya, da tarin abubuwa masu yawan gskg, itakam saitaga kamar batada sa'a a rayuwarta, "muguwar zuciyarta mai sakata a hanya mara b'illewa ta ce, "mata karkice haka, yakamata ki gwada sa'arki akan uncle G,๐ณnace, "itakuwa wannan tana cikin hankalinta๐?????.
Ta kai kallonta garesu, ta kula sunma manta tana cikin falon, dan babu abinda sukeyi sai shan sharafin soyayyar su, uncle G ya matso da bakinsa kusada na sopy, yana nufin suyi kiss, da idanu ta nuna masa fareeda, ya dafe goshi yana fad'in kes.
Sopy tayi murnushi, cikin tsokana ta ce, "irinku d'aya aii.
Yay saurin kallonta, ya ce, "dawa??.
Tayi dariya mai k'ayatarwa ta ce, "da...........sallamar dasukajine yahanata k'arasawa, suduka suka maido kallonsu ga k'ofar.
Su Nadiya suka shigo da sallama, su biyarne, uncle G! yatashi zaune yana fad'in lallai yau munada manyan bak'i, sannunku da zuwa.
Sopy taje ta rungume Nadiya, da sauran yammatan, harda zaliha, suka k'araso cikin falon.
Kowacce ta rusuna ta gaida uncke G!, ya amsa cikin fara'a, ya ce, "zuwa babu sanarwa?
Sukayi dariya tareda fad'in aii muna son bama sopy mamakine.
Ya mik'e yana fad'in ayko kun bata, sannunku da zuwa.
Sopy ta dire tire agabansu, cike da kayan motsa baki, nan suka zauna anata shan hira, da labarin makaranta, fareeda dai babu abin fad'a sai binsu take da idanu.
Zaliha! ta ce, "kai Safiyya kinyi k'yau wlhy, kodai mun samu ne??.
Sopy! tad'an harareta cikin wasa ta ce, "kun samu me???.
Suka tun tsure da dariya, ayeesh! ta ce, komun samu baby mana, ikilee! tai saurin cewa kema daga gani kinsan mun samu aii.
Sopy ta ce, "kudai wlhy 'yan iskane, nidai babu ruwana.
Ridallah! ta dafa kafad'ar sopy tana fad'in, barsu sopy!, suma nanda wani lokaci zaizo kansu aii, indai cikine, Nadiya! ta ce, bar 'yan iska, ALLAH yasa uncle G! yajisu.
Sopy ta ce, "aii nasanma yana jinsu Nadiya.
Gaba d'aya suka zaro idanu suna fad'in da gske yana jinmu???.
Sopy ta tuntsure da dariya tana fad'in matsorata, nandai sukaita hirarsu da dariya, wadda fareeda tazama 'yar kallo, dan duk sun wuce da ajinta.
Uncle G! yafito cikin k'ananun kaya yanata zabga k'amshi, sopy ta bishi da kallon tuhuma, shima ya fahimci mitake nufi, dan haka ya d'an murmusa, sannan yabi su ayeesh da kallo ya ce, "kuna nan ko har yamma??.
Suka ce, "da anyi la'asar zamu tafi, ya ce, "okey babu damuwa harna dawo.
Ya maida kallonsa ga sopy data had'e rai kamar zatayi kuka, ya ce, " 'yammata ya dai??, sopy ta turo baki gaba ta ce, "wai ina zaka???, yay murmushi, wajen budurwata zani hira.
Da sauri ta kalleshi, idanunta suka ciko da kwalla ta ce, "wlhy to ban yardaba, aii kai kace yau babu inda zaka, tazo ta kwace key d'in motar, takoma saman kujera ta zauna, suko su ikilee sai kunshe dariya sukeyi.
Ahan kali yatako yazauna kusada ita, ya sak'alo hannunsa ta bayanta ya tallafota zuwa jikinsa, ya ce, "sorry my sopy, wasa nake miki, ALLAH wajen kabeer zanje.
Ta kalleshi tana hawaye, to kabari anjima saikaje, yasa hannu ya share mata hawayen fuskarta ya ce, "A'a kiyi hak'uri naje yanzu, tunda kunada abokan hira, nima sainaje muyi hira da uncle kabeer, aii bazan dad'eba.
Ta kuma turo baki, amma aii cakayi sai la'asar zaka dawo, yad'n had'eta da jikinsa yana murmushi, A'a, yanzu nafasa anjima kad'an zan dawo, ta ce, "da anyi azahar, ya ce, "nayarda, ya kama hannunta yana fad'in tashi ki rakani.
Suna fita ya rungumeta tsam ajikinsa, cikin kunnenta ya ce, "sarkin shagwab'a, kinata zuba shagwab'a agaban su Riddallah ko???.
Ta b'oye fuskarta a k'irjinsa tana fad'in aikaine kasa nayi, ya sumbaci goshinta toshikenan saina dawo, dan idan nabiye miki bazan fitaba, yashiga mota suna dariya.
Bayan tafiyarsa ta dawo falon, su zaliha suka shiga tsokanarta, way irin wannan shagwab'a haka, sopy ta ce, " 'yan sa ido, kwa gaji kubarmu, gaba d'aya suka shek'e da dariaya, banda fareeda data maida kanta kan tv.
Anan suka wuni, sunsha hira sosai, dazasu tafi sopy tabasu kayan kwalliya acikin kayan lefenta, suka tafi suna godiya, da ajandar zata shigo makaranta ranar litinin....................โ๐ป
Assalamu alaikum, ina godiya ga d'umbin masoya, dasuka turo min sak'on addu'a ga sister na datake asibiti, harma wad'anda basu samu damaba, ngd sosai da addu'arku ALLAH yabar zuminci.๐๐ป
๐Bily๐
๐๐Mrs Abdus'salam๐๐๐
๐I LOVE YOU MY FAN's๐๐
[12/19, 7:26 PM] mrs bilkisu: 17~November~2016
๐ท๐นNI DA AMINIYATA!!!๐น๐ท
NA BILKISA IBRAHIM๐
๐ถ๐ธ4โฃ6โฃ๐ธ๐ถ
.........yau har sopy tagama aikin gyaran gidan fareeda bata fitoba, da kuwa kullum tare sukeyi, sopy tagama aikinta tsaf batareda tayi wani tunaniba, ko neman fareedar, bayan ta kammala komai tanufi d'akinta, fareeda na kwance abinta saman gado ta k'udundune da bargo, kallo d'aya sopy tayi mata tashige bayi abinta, dan ita azatonta fareedar barci takeyi.
Tana shiga fareeda ta mik'e, ahankali tafito tanufi dani d'in da'aka cika da kayan break, saida tabi kowanne ta bud'e taga abinda ke ciki, sannan tanufi kicin tana yatsine fuska.
Ta fito hannunta d'auke da robar gishiri, da sauri na lab'e dan kar ta ganni, ta bud'e ta barbad'e soyayyen dan kalin dashi, ta kuma bud'e sauran ta zuba har cikin ruwan zafi, da sauri ta maida ta koma d'akin ta kwanta kamar yanda take da.
Sopy tafito tana 'yar wak'arta ta, ta zauna tayi kwalliya mai tsari, wando da riga tasaka na fakistan, rigar tatsaya mata iya cinya, tayi k'yau sosai.
Tana shirin fita fareeda ta tashi tana wani mik'a alamar yanzu ta tashi a barci, sopy ta kalleta tana fad'in fareeda ince dai lafiya ko??.
Fareeda tad'an yatsina fuska ta ce, "mikika ganine sopy??.
Sopy ta girgiza kai, babu abinda nagani, naga yau kin dad'e baki tashiba ne kawai.
Fareeda ta zuro k'afafubta k'asa tana fad'in wlhy jiya nadad'ene ina nafikar dare shiyyasa yau namakara, na lurama har kin gama aiki ko??.
Sopy ta jin jina kai tana murmushi, aii babu damuwa, garama da kika huta, tai waje tana fad'in ki shirya muna jiranki a falo.
Fareeda ta rakata da harara, tana fad'in 'yar rainin wayo, aii na daina tayaki bautar gidannan, nafiso nima nashigo amatsayin matar gidan, dan bazanta wahalar banzaba.
Sopy kuwa d'akin uncle G! tanufa, tad'an zauna gefen gadon kusada shi tana shafa fuskarsa, ahankali ya bud'e idanu akanta, suka sakarwa juna murmushi, ya mik'o mata hannunsa wai ta tadashi, takama hannunsa tana fad'in ALLAH yasa na iya tada kai uncle d'ina!, dan kayi nauyi dayawa, yajawota tafad'o jikinsa, yasa hannu biyu yay mata zobe, cikin kunnenta ya ce, "nine mai nauyin ko??.
Ta d'ago tana kallon fuskarsa sukayi murmushi, ta sumbaci k'irjinsa, yaja wata sassanyar ajiyar zuciya tareda k'ara rungumeta.
Cikin sanyin murya ta ce, "my youseef tashi kayi wanka ko??, yad'an lumshe idanu, cikin shagwab'a ya ce, "saidai idan zakimin da kanki??, tad'an zaro idanu waje tana fad'in nifa nayi wanka aii saina b'ata jikina.
Ahankali yatashi da'ita zaune shima yatashi yana mata wani sihirtaccen kallo, cikin sanyin murya ya ce, "kinyi k'yau sopyna.
Tayi murmushi tareda fad'in nagode hubbina.
Ya ce, "woow nice name, daga yau haka za'a ringa kirana ko??, tai wani walay da idanu ta ce, "inhar kana buk'ata??.
Ya mik'e yana fad'in aii namafi kowa buk'ata.
Takama hannunsa suka nufi bayi, taimasa wanka fas sannan suka fito, ta shiryashi cikin k'ananun kaya, dan yau babu aiki.
Falo suka fito sunata zabga k'amshi mai dad'i, fareeda na zaune itama taci kwalliya cikin atamfa aiket da riga, sopy tabita da kallon dan ganin kwalliyar datayi.
Fareeda ta basar daga kallon da sopy take mata, ta d'an zamo daga kujerar ta ce, "yaya youseef ina kwana??.
Uncle G! ya amsa da lfy lao fareeda, kin kwana lfy??.
Ta ce, "Alhmdllih.
Ya ce, "masha ALLAH.
Dani suka nufa domin yin break, sopy tafara k'ok'arin had'ama uncle G break, saida ta zuba masa komai sannan ta turama fareeda kamar yanda ta saba.
Uncle G yaja filet gabansa yana fad'in yauwa 'yar albarka, laumar farko dayayi ya kume azaune kamar gunki, dan jin wani aza babben gishi har kwa kwalwarsa, yaja kofin shayun da sauri ya kurb'a domin neman sauk'i, amma saidai kash shima shayin haka yake.
Fareeda tana kallonsa, amma sopy bata lura da halin dayake cikiba, dan hankalinta yana kan zuba abincinta.
Uncle G! ya d'ago idonsa dayayi d'anja yana kallon asopy, sopy ta d'ago suka had'a ido saita sakar masa murmushi, amma ganin yanda fuskarsa ta canja sai jikinta yay sanyi ta ce, "hubbina yayadai???.
Ya daure ya ce, "ci abincin kiji.
Ta d'iba ta kai baki, dan ita azatonta yayi dad'ine sosai, jin gishiri zauzau yasata d'agowa da sauri tana gallonsa, shima ita yake kallo, fareeda da dad'i ya kashe ta, ta d'iba takai baki, da sauri ta zubo dashi a hannunta ta ce, "Sopy yaya haka??.
Sopy ta maido da kallonta gareta, zuciyarta sai bugawa take da sauri2, wasu hawaye masu zafi suka zubo afuskarta.
Amamakin fareeda saitaga uncle G! ya matsa da kujerarsa kusada sopy, ya kamo hannunta ya rumtse anasa, yasa d'ayan hannun yana share mata hawayen, cikin sanyin murya ya ce, "sorry safiyya!, karki damu, aii kowa yana kuskure a rayuwarsa, tunda haka bata tab'a faruwaba dole muyi miki uzuri.
Sopy ta kwanto da kanta saman cinyarsa tana shashshekar kuka, ta ce, "ngd uncle d'ina daka fahimceni.
Ahankali yake buga bayanta kamar wata jaririya, ya ce, "to ya isa haka nan, kinsan bana son kukanki.
Ta d'ago suna kallon juna, sukaima juna murmushi, yasa hannu ya kuma sharemata hawayen, ta ce, "uncle bari naje na sama mana wani abun mai sauk'i.
Ya jin jina kai yana murmushi.
Fareeda tabisu da kallo cikin matuk'ar bak'in ciki da haushin rashin samun nasara, mik'ewa tayi tabi bayan sopyn zuwa kichin.
Abu mai sauk'i sukayi, dukda sopy ce rabin girkin, dan fareeda bak'in ciki ya hanata yin wani aikin kirki.
Yana zaune afalo yana kallo suka fito, ya tashi yana fad'in yauwa sannunku, dani suka zauna suna break d'in, uncle G! sai kod'a abincin yake dan sopy ta saki jikinta, dan har yanzu bata cikin walwala, wai abincin yayi dad'i, harma yafi na kullum.
Sopy tayi murmushin k'arfin hali, ta ce, "uncle kana dai fad'ane kawai.
Ya ce, "da gsk nakeyi sopyna, ki kuma tambayi fareeda ma, yafad'a yana kallon fareeda datakeji kamar ta tashi tabar wajen, tai saurin k'irk'iro murmushi, cikin daburcewa ta ce, "ALLAH sopy da dad'i.
Sopy tayi murmushi ta ce, "to shikenan ngd.
Bayan sun gama, uncle G yafita, sopy kuma tanufi d'akinsa dan ta gyara.
Fareeda tana zaune abin