Showing 12001 words to 15000 words out of 58156 words
dayawa NA Novels dana hirar duniya dana addini irinsu HANYAR TSIRA dan wannan gidan bayin ALLAH suna k'aruwa dashi sosai ALLAH yabiya masu tunatar damu aduk inda suke.
"" irin wad'annan abubuwane sukan d'auke mata hankali bata samun lokacin tunani,, data ta wata 1 uncle kabeer ke siya mata,, shiyyasa batada matsalar MB, saidai takanyi kewar fareeda, Dan tunda suke basu tab'a yin kwana biyu basa tareba,, Dan haka duk kewarta ta addabeta, takan kwaso pictures d'insu taita kallo tana tuna baya,, duk abinda yashafi fareeda sopy ta maidashi wani madubinta,,sai dai idan inna taganta ta gurgiza kai kawai amma tana matuk'ar tausayin 'yar tata.
Su fareeda anata shan amarci,, komai yanata tafiya yanda takeso,, Abdul yana tattalinta komai takeso shi yake mata,, inagama ansamu rabo dan naga tayi wani fari,, kokuwa duk amarcinne oho dai,, mudai 'yan kallone.
Yau sopy anacikin farin cikin zuwan uncle kabeer,, sai hidimar girka masa abinci takeyi, inna taji dad'in yanda taga tasaki jikinta yau tana walwala, dan tunda abinnan yafaru basa ganin dariyar sopy,
Amma yau daka kalleta zaka gano farinciki a tareda ita.
"Sai wajen k'arfe biyu uncle kabeer ya iso, shima yayi farincikin ganin yanda jikin sopy yayi k'yau saidai kawai ramar datayine, tana zaune kusada uncle kabeer dake cin abincin data dafa masa,, takalle sa uncle kana ganin baba zaiyyarda da k'udirinmu kuwa? ?? Uncle kabeer ya ce, "aii dama tunda naga farincikinki ya yauta nasan akan maganar damukayine", karki damu zanyi iya k'ok'arina tayanda zai fahimceni, insha ALLAHU zai amince.
Sopy ta ce, "danayi farinciki mai tarin yawa uncle, nasan hakan zaik'ara nisanta zuciyata daga damuwar data tsinci kanta.
Uncle kabeer yay murmushi hakane my daughter! Insha ALLAHU nan gaba kad'an komai zai zama labari, kedai kiyi k'ok'arin cika min burina,, dan yanzu zaki shirya muje makarantarku mu amso exam d'inki.
Cikin zumud'i ta ce, "angama my dear uncle! Inna dai tanajinsu bata tankaba, dan bata fahimci inda zancen nasu yadosaba.
Sun karb'o sakamakon jarabawar saidai sopy batayi k'ok'ari a WAEC nataba.
Uncle kabeer ya ce, "sopy ya akayi haka tafarune?? Sopy tad'an sosa gefen wuyanta, wlhy uncle! Sannan ina cikin wani yanayine!!
Uncle yay murmushi sannan kina cikin shauk'in son Abdul ko?? "Tasa hanu ta rufe fuskarta tana fad'in "kai uncle".
Ya ce, "i, mana hakane", amma babu damuwa saimuyi amfani da NECO kawai, dama mun gama magana da abokina,, shima malamine a "B,U,K", nasan zai taimaka mana sosai.
To uncle nagode sosai ALLAH yabiya ka kaidai!! Yay murmushi to amin sopy na.
Sai dare uncle kabeer yasamu zama da baba, bayan sun gaisa ya ce, "yaya dama maganar yarinyar nan ne yakawoni.
Baba ya ce, "wace yarinya kenan??
Uncle yagyara zama, yaya yarinyar dazan aura!
Baba ya ce, "to miya faru da ita??
Babu komai yaya babanta ne , dama ya rok'eni akan dan ALLAH nabarta ta k'are karatunta, tunda saura shekara d'aya kacal, to nima sainaga hakan zai taimaka minma na k'arasa gidana, amma yaka gani??
Baba yaja numfashi, to idan haka yafi alkairi ALLAH ya tabbar abba, mudai kullum addu'ar fatan alkairi muke maka, da fatan gamawa lafiya, dan kai yaron kirkine, nak'agu naga ka ajiye iyali kaima.
Uncle kabeer yay murmushi karka damu yaya insha ALLAH zanyi adai k'ara tayamu da addu'a,, sai dai yaya bayannan inada wata buk'ata awajenka!! Inhar ban takuraka ba??
Baba ya murmusa karka damu mai sunan baba fad'amin buk'atarka indai batafi k'arfinaba zan yi maka ita.
Uncle ya ce, "batafi k'arfin kaba yaya! " dama dan ALLAH ina son kayarje min namaida safiyya makaranta, dan wannan zaman nata bashida wani amfani, karatu zai matuk'ar taimaka mata wajen mance abubuwan dasuka faru abaya..................βπ»
πBilyπ
ππMrs Abdus'salamπππ
πI LOVE YOU MY FAN'sππ
π
[12/19, 7:24 PM] mrs bilkisu: 15~October ~2016
π·πΉNI DA AMINIYATA πΉπ·
NA BILKISA IBRAHIM π
πΆπΈ1β£5β£πΈπΆ
...............Baba yaja numfashi, abba ban katse maka hanzariba, amma da dai anhak'ura da karatunnan hakanan, tunda ansamu na zaman duniya, sai kuma ayi aure.
Uncle ya ce, "hakane yaya, amma yanzu naga bawani tsayye bane ahannu, amma dazaman banzar gara ace karatu takeyi,, kotana karatun tasamu miji saitayi aurenta.
Baba ya kalli inna, to hajara kinji abinda abba ya ce, "amma ya kika gani??
Inna tai dariya, malam nikam banida shakku akan babnmu, dan haka kabashi dama, nima inaga hakan zai taimakawa safiyya wajen mance wasu abubuwan.
Baba ya ce, "to akira safiyya muji ta bakinta"
Uncle yay murmushi karka damu yaya indai safiyyace mungama magana da'ita.
To, to, kace dama saida kuka gama shawararku sannan aka tuna damu! Dariya sosai uncle yakeyi "cikin dariya ya ce, "A'a yaya mu mun isa; nan dai sukayita hirarsu da wasa da dariya.
TUNATARWA:- inaso naja hankalin iyaye akan ilimin 'ya'yansu, mafi yawan iyaye sukan d'auki ilimin 'ya'ya mata ba'abu mai muhimman ciba,, ni anawa ganin ilimin d'iya mace yafi na kowanne muhimmanci, karku manta uwa itake bada tarbiyya, kuma yara suna tashi ne da harshen mahaifiya, kunga kuwa ilimin d'iya mace yanada muhimmanci matuk'a,, dan zata zama foundetion na ilimin 'ya'yanta,, wannanma kad'ai ya isa yazama abu mai muhimmanci ga bawa mace ilimi,, sannan ko a gidan aure zakaga mace mai ilimi tafi kowa iya rik'e miji da tattalinsa,, dan haka mubama 'ya'yanmu mata ilim addini dana zamani,, ALLAH YASA MU GANE.
UNCLE kabeer yanata k'ok'ari wajen nemawa sopy Admission a (BUK ) da taimakon wani abokinsa aka dace,, dakansa yaymata komai.
To ALHAMDULILLAH komai dai ya kammala,, ranar monday sopy zata fara zuwa makaranta,, π
dan haka tafi kowa fareenciki,, harta k'agara ranar tazo.
Su dai su inna sunata yima sopy nasiha, akan tazama mace tagari mai rik'e mutuncinta da darajarta,, idan ance 'ya mace taje tayi ilimi, bawai ananufin taje tayi iskanciba,, dan dayawa 'yan uwa mata idan suka samu saken zuwa nema ilimi,, sukan d'auka sun samu wayewa daganan sai afara iskanci,, kaiconmu wlhy 'yan uwana mata, har yanzu wasunmu basu fahimci miye wayewaba dayawanmu muna jahiltar wayewa,, ballagar mace wadda ta maida kanta akuya ba ita bace wayayyiyaba,, wanna itace bagidajiya jahila,, mace mai kamunkai da girman kai awajen maza marasa tarbiyya,, mai adiini itace wayayyiyar mace, kuma suma mazan sunfi sonta,, zakaga duk iskancin namiji da mugun halinsa yana burin auren mace tagari, kodashi bai kasance miji nagariba, to 'yan uwana ya kama ta mu gyara, kodan cin ribar rayuwarmu, ALLAH dai yasa mugane.
Su inna dai sunyima sopy nasihohi masu ratsa jiki da zuciya,, sunkuma yimata fatan alkairi da samun nasara arayuwa.
Saboda yanayin rayuwa,, sai uncle kabeer ya nema mata gurin zama a hostel, dan kar wataran kud'in mota ya gagareta,, itama hakan yayi mata dad'i, dan zaman anguwar yana d'an sata tayita tuna wasu abubuwan,, kuma idan tafita sai mutane suyita kallonta,
wasuma har nunata sukeyi, to, tasan idan tayi nisa da anguwar zata sake, ta kuma manta da abubuwan dasuka faru abaya.
Ku kasance dani akoda yaushe, ina muku fatan alkairi ...................βπ»
πBilyπ
ππMrs Abdus'salamπππ
πI LOVE YOU MY FAN'sππ
π
16~October ~2016
π·πΉNI DA AMINIYATA πΉπ·
NA BILKISA IBRAHIM π
πΆπΈ1β£6β£πΈπΆ
.............Sopy ana makaranta, komai yana tafiya yanda takeso, sai dai tak'i sakin jiki da kowacce k'awa, duk da ana nuna mata anabuk'atar yin k'awance da'ita, bakamar wata zaliha, itadai sopy tana burgeta, sai dai sopyn tak'i bata fuskar dazata kusanceta, itakam sopy tana tsoron makirci irin nad'an adam ne, dan wadda ta yarda da ita, ta amincewa ita tafara saka mata shakku game da halayen d'an adam, wannan yasa take nisantar 'yammatan makarantar, sai dai tadage tana fahemtar abinda ake koya musu, kuma yanayin tasiri arayuwarta da kuma alk'awarin data d'aukarwa kanta da uncle kabeer.
Yau tanada lectures d'in safe, dan haka ta tashi tayi shirinta, cikin siket da riga na atanfa jaa da kore, tad'akko fareen hijjabi har k'asa tasaka, tad'an fesa turare mai sauk'in k'amshi, dukda bawata kwaliya tayiba tayi k'yau, dan sopy tanada k'yau irin wanda in kacika kallonta zai k'ara k'ayatar dakai, dukda bak'ace bak'inta yanada k'yawun kallo, gata da jiki maik'yau, irin wanda mutane sukan kirashi karuwan jiki, dolene idan kaga surar sopy komin ustazan cinka ka k'yasa, dan haka koda yaushe takan sance cikin hijjab, saboda idan har tasaka gyale tafita sai tasamu samari samada goma sunce suna sonta, wasukuma kwarjinin ta yake hanasu furtawa.
Tafito kafad'arta rataye da jar jakka, tafiya take cikin nutsuwa kanta ak'asa, tad'an kalli agogon hannunta mai sauk'in kud'i, tad'an tab'e bakinta, kai barima nazauna anan tunda munada sauran lokaci.
Tana nan zaune, saitaga d'alibai nata saurin shiga aji,wasuma harda d'an gudu, ita dai kallonsu takeyi, amma batayi wani yink'urin tashiba, zaliha tak'araso tana fad'in "lallai safiyya kina ganin kowa yana k'ok'arin shiga aji, amma ke kina zaune, yau munada lectures da "uncle G" kuma idan har yariga ki shiga aji tofa "k" bazai barki kishigaba......tak'arasa fad'a tana k'ok'arin tafiya, kafin sopy tace,"wani abu tuni zaliha takai k'ofar class.
Sopy tamik'e itama tanufi class d'in sai dai kash tana kaiwa ga k'ofar ajin shikuma malamin da zaliha takira uncle G yashiga.
Sopy ta tsaya cak abakin k'ofa, ta daure ta ce, "malam good morning!
Saida yay mata wani kallo na rainin hankali, sannan ya ce, "morning! da ganan yaja bakinsa yay shiru.
Sopy tai tsaye abakin k'ofa domin bai bata izinin shigaba, tana nan tsaye wasu 'yammata suka k'araso suma, d'aya acikinsu ta ce, "A'isha yaukam munzo arashin sa'a uncle G!! yarigamu shiga, wadda aka kira A'isha ta tab'e baki, ki ce, "sarkin 'yan girman kai yashiga, nikam wannan malami bansan miya d'auki kansaba???
Sopy dai tana tsaye tana jinsu, sai dai zuciyarta cike da tambayoyi, akan toshi wannan malamin wayeshi??? Ita dai yau kwananta hud'u a school d'innan, amma bai tab'a shiga a jinsu ba sai yau, to shikuma waye????
Ta maida kallonta gareshi, yana sanye da wani farin yadi mai laushi, rigar da kad'an ta wuce d'uwawunsa,k'afarsa sanye da bak'in takalmi,hakama hannunsa yana d'aure da bak'in agogo,, idanunsa cikin farin gilas siriri,, dukda dukannin kayan dake jikinsa bawasu masu tsada bane, amma shikam sun zauna dai dai da tsarin halittarsa.
Dogone amma ba canba, amma tabbas baza'a kirashi gajereba,bak'ine amma mai haske, yanada manyan idanu farare tas, wad'anda saboda haskensu har akan iya ganinsu tacikin kwalbar dake idonsaπ, dan har wani k'yalli sukeyi, kumatunsa zagaye yake da bak'in gashi sid'ik wanda ake kira saje, hakama bakinsa zuwa gemunsa shima zagaye yake da bak'in gashin, kansa babu suma mai yawa dan da'alama yanayin aski saidai ba irin tal tal d'innanba, domin akwai gashi kwance akansa bak'i sid'ik yasha mai sai k'yalli yakeyi, yanada d'an jiki dankuwa baza'a kirashi siririba,amma jikinsa yay masa k'yau.
Yad'an juyo yana kallon su sopy dake waje, yaji ajikinsa tabbas ana kallonsa, sopy tayi saurin d'auke idonta daga kallonsa, shima saiya d'an tab'e baki yacigaba da bawa d'alibai darasi akan English domin shi malamin turancine.
Yagama lecture d'insa, harda yin test, yazo fita sopy tamatsa gefe tabashi hanya, ko kallon inda suke baiyiba ya wuce abinsa, d'aya acikin 'yammatan nan uku taja tsaki, kai wannan gay d'in akwai rainin hankali saikace d'an wani da wata.
Bayan fitarsa suka shiga, class suka cigaba da karb'ar sauran darasi.
Sopy zaune ajikin wata bishiya, tana duba books nata, dan bitar abubuwan da'akai musu, zaliha tazauna a kusada sopy tana fad'in 'yar uwa dama kinanan?? Tun d'azu nake nemanki!!
Sopy tajuyo tana kallonta, e, ina nan, inad'an yin karatune.
Hakan yanada k'yau zaliha tafad'a tana murmushi.
Sopy ta maida kanta bisa karatunta, saikuma ta d'ago ta ce, "yauwa zaliha dan ALLAH bani labari gameda "uncle G" malamin d'azu da safe.
Zaliha ta gyara xama cikin zumud'i, dan ganin sopy yau takulata,, ta kaikaice tafara zabgo Zance tamkar 'yar jarida.
Nidai ayanda nasani sunansa malam yuseef Husain Ahmad, Gurum amma anfi kiransa da uncle G, malamin English ne, mutum ne mai aji, baya son wasa, bakuma ya wasa da kowace d'aliba, dan baya sakarwa kowa fuska, inhar kayi sake yashiga aji kafin kashiga, tofa ranar bakada rabo amasu samun darasinsa.
Yanada ilimi fiye da tunanin mai hankali, dan ayanda naji, nan makarantar yayi, yafita da face class na Resold dan haka suka d'auke shi aiki, zan iya ce miki iya abinda nasani kenan gameda tarihinsa.
Tad'anyi dariya k'awata kar dai kema kin kamu da son sa?? dan wlhy rabin 'yammatan makarantar nan duk son sa sukeyi,, harso suke yayi musu magana,, amma shi kam ko kallo basu isheshiba, shiyyasa suke cemasa mai girman kai.
Sopy ta harareta kekam na lura ke 'yar rainin hankalice,, daga tanbayarki tarihin mutum saiki min fassara, to kuwa idan kinason mu shirya dake kidaina min irin wannan.
Ganin ran sopy yab'aci, zaliha tashiga bata hak'uri.
Fareeda zaune ta zabga uban tagumi babu abinda yake damunta sai tunanin sopy, ba k'arya tayi missing d'inta, sai dai haryanzu bata tab'aji azuyarta ta cutar da sopynba, bare tayi nadamar Hakan, Abdul yay kissing d'in kuma tunta, tai saurin juyowa tana kallonsa, ya ce, "miye damuwarki?? Tad'an yatsina fuska ta ce, "sopy nake tunani wlhy nayi missing d'inta my love!
Abdul yad'an tab'e baki, yana mik'ewa kinga wannan matsalarki ce, ni yanzuma tashi ki kawo min abinci dan yunwa nakeji wlhy,, fareeda ta harareshi oh hakama zakace matsalata ce???
To inada matsala da damuwarki ne?? Cikin jin haushi fareeda ta ce, "A'a.
Ya ce, "to, kuma, zakiji haushina??
Fareeda dai taimasa banza tafice domin kawo masa abinci......................βπ»
πBilyπ
ππMrs Abdus'salamπππ
πI LOVE YOU MY FAN'sππ
π
[12/19, 7:25 PM] mrs bilkisu: 17~October~2016
π·πΉNI DA AMINIYATAπΉπ·
NA BILKISA IBRAHIM π
πΆπΈ1β£7β£πΈπΆ
................yauma duk k'ok'arin sopy nagujema tarkon uncle G!, amma saida ta fad'a, dan kuwa harya shiga aji, tad'an cije leb'enta, dan bak'in ciki, tabishi da kallo yana tsaye gaban allo, yauma cikin manyan kaya sai dai yau shaddace mai ruwan k'asa, d'inkin dai tamkar na ranar, dan rigar itama bata wuce d'uwawun saba, amma yau babu glas.
Sai da yagama lecture d'insa sannan ya ce, "kowa yashirya yin test, kuma yau har nawaje su shigo.
Wannan magana tasa tabawa mafi yawan d'aliban mamaki, domin duk yanda kuke dashi inhar yarigaka shiga aji tofa bazaka shigoba, bare idan zayyi test, amma yau dakansa yabuk'aci su shigo.
Bayan shigowar su sopy da ragowar makararru, ya gabar musu da tanbayoyin.
A hankali yake takawa cikin class d'in bakajin motsin komai sai takunsa, kowane d'alibi ya duk'ufa wajen aikinsa, k'amshin turarensa duk ya gauraye class d'in, yak'araso dai dai inda sopy take zaune, yazuba mata idanu dan ganin batayi wani yunk'urin rubuta wani abubama.
Jin antsaya akanta yasata d'agowa, kallon ido cikin ido sukaima juna, sopy tai saurin janye nata idon dan baxata juri kallon saba, jikinta asanyaye tamaida kanta ga takarda.
Shikam wani abu yaji yasoki kansa harzuwa babban d'anyatsan kafarsa, yarintse ido yabud'e, ya salam yafad'a tare da jan ajiyar zuciya, ya wuce abinsa yana cigaba da zagaye d'alibai dan kar suyi satar amsa.
Lokacin daya basu yana cika yakarb'e, yafita abinsa.
Zaune yake a offece yana duba takardun jiya, dasu sopy sukayi teat, har yazo kan wata takarda danaga ya kurama ido, yajuyata yak'ara juyawa, sai kuma yak'ara maimaita sunan SAFIYYA IBRAHIM KABEER, tabbas yarinyar ce yafad'a afili, domin lokacin dayake zagaye sunan daya gani akan takardar gaban ta kenan, ya cire gilas d'in idonsa, yakuma murza idon dan tabbatar da abinda yagani shin gskne kokuwa idanunsane suke masa gizo??
Amma yasan ba gizo bane, domin sopy ita kad'ai tazauna, bare ya ce, "wajen wani ta kwafa".
Yacigaba da juya takardar yana kallo,, aka kwan kwasa kofar domin neman izinin shigowa.
Ya ce, " who is that?
Daga can akace nine.
Yay dariya come in, my gay!.
Abokinsane malam faruk, shima lecturer ne a makarantar, yabashi hannu suka gaisa, ya kalli takardar hannunsa, my man! lfy naga kanata juya takarda??, ko watace ta ce, "tana sonka??, dan na sanka akwai farin jini."
Uncle G! Ya kalleshi aii idan wannan nema da sauk'i.
Malam faruk ya gyara zama to minene yafaru??
Kasan wani abu?? "A'a saika fad'a,, wato wata yarinya ce tabani mamaki wlhy, jiya namusu lecture, to sai takasance acikin makararru, yauma haka, amma abinda yabani mamaki nayi musu test , saikuma ta amsa mini komai dai dai, yamik'a masa takardar, karb'a kagani.
Malam faruk yakarb'a yana dubawa, ya jin jina kai , lallai wannan yakai ayi mamaki, dukda akwai mutane masu kwazo da kwakwalwa aduniya,, kai kankama abin misaline, dan haka karkai shakku.
Uncle G! Yad'an tab'e baki yana fad'in hakane abokina.
Sopy suna zaune itada zaliha a kofar wani class, saiga uncle G ! Yafito daga ajin, hannusa d'auke da littatafai, suka gaidashi sau d'aya ya amsa musu, har yad'an gotasu saikuma ya dawo, litta taffan hannunsa ya mik'awa sopy, cikin muryarsa mai dad'i ya ce, " ki kaimin offece d'ina.
Cikin rawar murya sopy ta ce, "aii ni bansan offece d'inkaba,