Showing 21001 words to 24000 words out of 67570 words

Chapter 8 - DAWOOD COMPLETE HAUSA NOVEL

M SHAKUR   

29 Jun 2024

36742

having a headache..I'm ok.

Lalla6asa tayi suka gama wayar tana ajewa ya lumshe lazy eyes dinsa zuciyarsa na tunano Masa saraah sbd itace baya fatar Koda wasa tasan maganar Nur bare taganta sbd yasan hw stupid and crazy she is zata iyayin komai and that he can't dare to take.




****
Duk wata shaquwa da aminci tashiga tsakanin taheer da aleeya sbd arayuwarsa baida friends ko 'daya Bai ma ta6a yinsu ba yayansa shine abokinsa idan Yana gari sbd akwai soyayya da shaquwa sosai atsakaninsu sai yanzu daya samu aleeya yakejinta sosai cikin ransa amatsayin aminiya daya yarda da ita.

Mum kuwa duk da'din duniya ya isheta data gano irin soyayya Mai qarfi da aleeya kewa mi'amor 'dinta sbd duk duniya ba abinda take tsananin so da qauna kamar ka nuna kanason mi'amor dinta.

Uwa uba data Kira CJ ta bugi cikinsa taji abban aleeyar ba laifi he's very rich and famous Dan haka tasan mi'amor dinta his in-laws will be Rich and famous kamarsu just the way datakeson abubuwan sukasance Dan babban burinta shine yanda suka mallaki billions of dollars suke billionaires duk wainda zasu zama in-laws dinsuma su zamo.

Tuni ta qara sakewa aleeya tana qara nuna Mata qauna da kulawa na musamman tareda qara koya Mata abubuwan fashion sbd tanason matar 'dan nata tazamo like no other.

Aikuwa tuni aleeya taqara tsundumawa cikin soyayyatar mi'amor 'din mum din Dan tuni mum ta nuna goyan baya dari bisa dari Dan harma so take tafi aleeyar zaqewa Dan tuni tafara yiwa dawood 'din maganar aure Dan taji ra'ayinsa aikuwa ga mamakinta Kai tsaye yace Mata ya shirya kowane lokaci zai iyayin aure sbd bayason adauki time yanama son zuwa dama yafada musu aure yakeson yi.

Wani irin dadine yaqara kama mum din cikin zumudi tace,

Ok my love saikazo sbd nima banason ka qara wani lokaci ba auren.

Kai tsaye tafadawa taheer da aleeya yanda tayi dashi cewar ya shirya yin aure.

Da daddare takira cj tafada Masa abinda ke faruwa nason juna da dawood da aleeya keyi sosai yayi mamaki sbd yasan Sam dawood baida niyar aure ayanzu sai zuwa gaba qila Amma Kuma daya Kira dawood ya tambayesa shiyace zaiyi aure yanxu Kai tsaye yace Masa eh qilama Nanda 3 months.

Aje waya dad din yayi cikeda mamaki Amma Kuma tuna yaji daga bakin dawood din ai shinkenan abin farin cikinsune.

Ba 6ata lokaci washe gari dasuka gama saka hannu akan partnership nasu dad yayiwa Abba bayanin abinda ke faruwa sosai abban yaji Dadi ranar dasuka dawo Miami da kansa ya tambayi aleeya ba kunya tace eh tanason dawood din.

Ranar murna da farin ciki gurin mum harda wata special dinner sukai having dukkaninsu Abba ma farin cikinsa baya 6oyuwa wannan tafiyar tasu tayi Masa Dadi sosai sbd komai anyisa cikin nasara ga zumunci zai qullu.

Ranar kosu ammy da Layla da aka bugo aka sanar dasu angama komai dasun dawo za'a bawa itama saurayin Layla dama ya Aiko baza'a Bata lokaciba za'ai bikinsu sbd mum dake ganin idan aka tsaya jan time za'a iya samun matsala.

Farin ciki ranar gurin Layla da ammy kamar me ranar kusan raba dare sukayi suna waya da aleeya da zumudi da farin ciki yasa takasa sukuni gashi tun adaren mum tabawa wani babban fashion empire aikin dinko musu wasu irin dogayen rigunan dazasu saka agurin bikinsu har agama.

Tun tana waya da aleeya kiransa ke shigowa wayarta tana gani tasaki murmushi tun tana fahimtar Mai aleeya ke fada harta daina dukkanin hankalinta yakoma kansa Kuma takasa cewa aleeyar Yana kiranta tana kallo yaita Kira ba qaqqautawa aleeyar da kanta ta gano hankalin laylar baya tareda ita ta kashe wayar tana murmushin farin ciki jitake ta matso tahadu da dawood din Kota samu sassaucin sonsa dake neman rabata da nutsuwarta.


Aleeya na kashewa kiransa na sake shigowa tana 'dauka taji lokacinda ya sauke wani irin kasalallen numfashi tareda cewa,

NUR ahankali kamar Mara lafiya.

Ajiyar zuciya itama ta sauke batareda ta amsaba sukayi shiru dukkansu.

Miskilancinsa ne ya motsa yau Dan haka haka sukai shiru Kati na tafiya abanza tsawon lokaci kafin taji Yana sauke numfashi ahankali alamar yayi bacci.

Murmushi tasaki tareda kashe wayar ta aje sbd ta saba da hakan idan Jan ajinsa ya motsa sai kawai yakira Yana sauraron numfashinta haryayi bacci.

Kwantawa itama tayi tareda lumshe Ido tana sake girmama abubuwan datakeji gameda dawood din.




Washe gari da sabon farin ciki suka tashi sbd ranar su aleeya zasu sauka da kanta tayiwa aleeya wani qaramin chocolate cake da samosas yan kadan.

Ita kadai taje daukarsu suna ganin juna suka rungume cikin farin ciki ba tsalle tsalle ba ihu ahankali tace,

I missed you so very much my love.

Cikin farin ciki aleeya tace,

I missed you more sweetheart.

Sakin aleeya tayi tareda kallon Abba tana murmushi tace,

Abba welcome.

Thank you layla,,hp mun sameku lafiya?

Lafiya qlau abba munyi kewarku sosai.

Hmmm kewa ai sai Bilal sbd kullum saiyi kaman zaiyi min kuka awaya wai munqi dawowa.

Murmushi tayi suka nufi mota bayan ansake booking flights din dazai wuce dasu Abba da ammy yau da yamma.

Rungume ammy aleeya tayi tana cewa,

Ammyna nayi kewarki.

Muma munyi kewar hayaniyarki.

Dariya sukayi dukkansu Nan suka shige bedroom dinsu sukabar ammy da Abba a palon.

Tubewa aleeya tayi tayo wani wanka tasaka jeans da white vest tayi sallah suka fito Palo Nan sukaci abinci gabaki 'dayansu har zuwa qarfe biyar suka Kai su ammy airport suka wuce sukuma suka dawo.


Da daddare kusan kwana sukayi fira kafin suka kwanta sbd gobe Dole zasu Fara zuwa school danma anfara lectures tun last week.

Tunda sassafe kafin layla ta tashi sbd zumudin son ganin dawood din Layla aleeya ta tashi ta 'dauki keys na flat 'din dawood din da layla tace yabar Mata sbd bazai dadeba zai dawo.


Tana shiga babban palon tayi arba da makeken hoton maska daya qara qawata palon yayi kyau harya gaji sbd he is looking so hot a hoton Dan a beach yayi hoton da kayan Shan iska ajikinsa dasuka qara fitarda kyawu da hutun fatarsa.

Wow,,,he is damn hot and cute"""tafada tana dariyar taya laylarta farin ciki.


Saidata qare Masa kallo ta juya ta fice tareda rufe flat din tana komawa ta fada toilet tayi wanka tana fitowa Layla na tashi itama tashiga tayo wankan suka shirya coke da cake Layla taci itakuma Tasha golden morn suka wuce school.


Ahanyarsu ta zuwa aleeya ke driving layla kuwa massages din dawood take replying sai wani irin sahirtaccen murmushi takeyi sbd yanda duk ya 'daga hankalinsa zai dawo tana lalla6atasa akan yabari yadawo Taredasu dad dinsa sbd koyazo shikadai su anan bazasu bashi aureba Saida iyayensa.

Kallonta aleeya tayi tace,

Naga hotonsa 'dazu you two will make the best perfect couples.

Kallonta Layla tayi tace,

Kingansa da gske?

Yes dazu kina bacci naga hotonsa.

Murmushi layla tasaki tana sake kallon hotonsa dasukai tare dake wayarta aranta tace,

Dama I know my aleeya zatace kayi.

Suna Isa school suka shiga kowa yayi gurin lectures dinsa sbd Layla medicine takeyi aleeya Kuma law.



Ahankali suka Fara nisa akaratunsu sbd exams ma suke rubutawa kuma zuwa lokacin tuni aka yanke shawarar tsayarda ranar bikinsu danma antsaya jiran dawood din Layla yazo da iyayensa sukuma su dad 'dinsa daya tuntubesu da maganar yaushe zasu koma Nigeria sukace sai next month sbd sukuma anasu tsarin so suke sai su aleeya sungama exams saisuxo ayi komai gabaki 'daya.


Ranar dasuka gama exams washe gari suka wuce Lagos sukuma su mum aranar suka sauka Abuja dawood kuwa sai washe gari zai sauka daga baya su sufyaan zasu biyosa sbd kar saraah tayi zargin wani Abu.


Ranar dasuka dawo tun a airport suke mamaki da tsokanar Bilal ganin yanda lokaci 'daya Yana Shirin zama saurayi Dan harma ya kusa kamosu a tsawo.

Ranar gidan cikin farin ciki da nishadi suke komai sbd gida ya kammale.

Ana saura biyu su mum zasuzo Lagos ammy tabugawa anty Nana tafada mata maganar neman aurensu aleeya daza'azo atsayar da date.

Siyama na zaune Koda ummanta ke waya da ammy taji duk abinda aka fada ta ta6e Baki tana cewa,

Duka dukafa Basu Dade dafara University ba shine za'ayi musu aure.

Numfashi umman tasake kafin tace,

Ba Dole suyi musu auren da wuriba kinaji tace bazaa dauki lokaciba za'ayi sbd aurene za'ayi na yayan billionaires sbd mazajen ko wacce ba'ama qasarnan suke zauneba.

Wani kallo siyama tayiwa umman tana juya zancen cikin ranta kafin tace,

Wai harda ita sadaka yallan ba'a qasarnan zatai aureba.?

Saikuma kiyi tunda ke kin kasa tsaida ruwan Ido ki tsayar gashi harkin gama degree saiki tsaya kiyita kallon anayi.

Wani 'daci ta ha'diye a maqoshinta tareda aje nail polish 'din datake shafawa a hannunta ta miqe tana cewa,

Lokacin komawata gidan yayi.

Harararta umman tayi tace,

Ki tsinci uwar me acan bayan duk buhun wulaqancinda sukai Miki Akan sadaka yallah.

Wani shu'umin murmushi tasaki tareda kallon umman tace,

Kika sani nima idan inacan abban yahadani da 'daya daga cikin yaran rich mutanensa.

Baki umman ta washe tana cewa,

Hakane kumafa...wlh maza shirya gobe kitafi kafin kitafi kisayi 'yan mayukan Nan Masu Dan tsada ki qara fito da kyawunki tunda ba finki akayi ba.
#Mamuhgee








Vote
Comment.
[1/13, 11:37 AM] El~hajj: *_DAWOOD_*
_wattpad@mamuhgee_




*17*
Washe gari motar asuba tabi zuwa Lagos taso shiga jirgi Amma sbd karma ta tambayi ammy kudin ticket kamar yanda tasabab idan zata gudun kar ammy tace tayi zamanta yasa tashiga mota
Tunda suka dau hanya ta kwantarda kanta tareda rufe ido cikin ranta tana kissima yanda zata Hana auren Layla auren mijin yadawo kanta.




Lokacinda ya sauka a Abuja taheer ne da kansa ya daukosa daga airport cikeda murna da farin cikin ganin 'dan uwansa suka rungume juna sbd sun Dade Basu ha'du shi taheer baya zama sbd aiki shikuma Bai cika zuwaba tunda su mum suka tarki zama Nigeria.

Koda suka iso gidan anshirya Masa dishes na lunch kala kala cikeda farin ciki mum ta qarasa ta rungumesa atare itadashi sukace,

I missed you my love.

Itakuma tace,

I missed you more mi'amor.

Direct part 'dinsa da aka gyara aka zuba komai yanda akasan yanaso da duk sauran abubuwan amfaninsa duka mum tasiyo tazo dazu tun daga can aka Kai luggages dinsa.

Saida yayi wanka ya kwanta ya huta Yana tashi Nur yafara Kira tana ganin numbers ta Nigeria tasaki wani lallausan murmushi sbd farin ciki da wani irin kwanciyar hankali dataji ya shigeta.

Tana 'dauka taji lokacinda ya sake ajiyar zuciya ahankali tareda Kiran sunanta can qasan maqoshinsa Wanda dagashi har ita Saida tsigar jikinsu ta tashi.

Akasalance tace,

Do you really have to do this Everytime?


Lumshe Ido yayi tareda sake bu'de Baki daqyar yace,

you're my life Nur,,I love you and know all I'm feeling is I can't live a life without you in it,
Duk duniya yanxu Kece kawai abinda nake nake tsananin son samu so just tell su ammy su shirya I'm coming tomorrow.

Ajiyar zuciya tasake ahankali tanajin sabuwar qaunarsa da sonsa na qara shigarta murya qasa qasa itama tace,


Thank you.

Qasa qasan Shima daqyar yace,

Tell me how much you love me...

Words can't describe it just keeps one thing in mind har lokacinda numfashina zai bar jikin Kaine ka'dai zaka zauna azuciyata wannan matsayinkane Kuma alqawarine bazai ta6a canxawaba.

Shiru yayi jikinsa na qara mutuwa sbd yazamo cikin jininsa jikinsa yake duk lokacinda muryarta ta sauka cikin kunnuwansa sai dukkanin jikinsa ya mutu saidai dayake dama baida hayaniya ko kazar kazar baza'a ganeba saisu jass kawai dadukasan halin abinsu.


Shiru sukayi dukkaninsu tsawon lokaci can Kuma murya a kasalance yace,

Do you miss Nur.

Murmushi tasaki kafin tace,

No.

Wat"""yafada da sauri tareda tashi daga kwancen zaiyi magana ta rigasa cikin murmushi Mai sauti tace,

Silly"""""""tafada ahankali tareda kashe wayar ta aje fuskarta na qara wanxuwa da murmushin data kasa dainawa.

Aleeya data sata gaba da kallo harda tagumi sai dariya take tana ganin ta kashe ta tashi zaune a tsakiyar gadansu tana leqa fuskar laylar dake nuna tsananin sonda zuciyarta ke Masa tace,

Hmmm anya Layla dawood 'dinnan Bai tafi da fiyeda rabinki ba yabar Mana saura.

Harara ta watsa mata still fuskarta 'daukeda murmushi batareda ta Bata amsaba.

Sake matsowa tayi jikinta ta kwantarda kanta a cinyar Layla din tace,

Layla koda Ni bansamu soyayyar mi'amor ba zan dawwama cikin farin ciki ke kinsamu soyayyar Wanda kikeso tunda bamu taru mun rasaba.

Kallon fuskar aleeyar tayi cikin sanyi Jin yanayin muryarta,,
Shafa gashinta dake tsefe tayi itama cikin sanyi dason qarfafa Mata gwiwa tace,

Ina roqon Allah idan har Dole 'dayanmu ne zai samu farin cikin samun soyayyar Wanda yakeso to yazamto Kece sbd Ni zanyi farin ciki naji Dadi idan Kece kike tareda abinda kikeso sbd Ni na 'dandana naji ko haka na tuna zanji Dadi.

Nikuma ina roqo da dafatar dukkanin 'yayana su samu soyayyar wainda suke so har abada.

'dagowa sukai atare sukaga ammy tsaye hawayen da kowaccensu ke riqewa na tunanin halinda zasu shiga idan hakan dasuke tunani takasance suka gangaro musu da sauri ammyn ta qaraso ta rungumesu itama jikinta na mutuwa.


Washe gari Layla ta sanarda ammy zuwan dawood da iyayensa ammy tafadawa Abba shikuma ya bugawa cj ya fada Masa Dan suxo su ha'du da iyayen dawood din layla a tsayar da Rana tare.


Threequarter yasaka black da black shir Mai hadeda hula ya fito ya nufi gurin mum dinsa sbd dad bayanan tunda ya iso Bai gansaba.

Dama tunda yatafi takasa sukuni sbd baici abinciba Kuma gashi batason damuwarsa tanason yasamu isashen hutu kar ciwon Kai na stress yakama Mata shi.

Yana shigowa palon ta aje magazine din hannunta tareda miqa Masa hannu ya qaraso ya zauna kusada ita.

Kallonsa tayi Cikeda kulawa tace,

Bakaci komaiba haryanxu my love.

Kallonta yayi cikeda qaunarta aransa yace,

No mum nasha milkshake banajin yunwa yanxu I want to talk to you and dad abt sumthing serious..

Murmushi tasaki tana kallonsa tace,

Ok kabari sai dad dinka yadawo after dinner we'll talk Amma right now I wanna tell you something,

Zuba Mata lazy eyes dinsa yayi sbd Yana iya hango zumudi da farin ciki akan face dinta da abinda takeson fada.

Well you see my love Akan maganar aurenka ne munason zuwa jibi idan mukaje a tsayar da ranar auren gashi haryanxu bakuga junaba shine nakega why not Kai gobe ka wuce kafin jibi muzo kun...ga ju..na.....

Rawa muryarta tafara da I ina sbd kallon daya tsareta dashi
Daqyar tasamu zancen yakai qarshe tace,

Meyasa kake kallona haka.


Lumshe Ido yayi tareda riqo hannunta daya yace,

Sorry I didn't get wat you're saying ne.

Ajiyar zuciya tasaki ta 'dauka zaice yafasa ne tasaki sabon murmushi tace,

Yarinyarda muka za6ar maka nake nufin kaje kuga juna tunda kace kaima ka shirya aure kakeso....

Zame hannunsa yayi daga nata Yana sake kallon fuskarta yaga idan da gaske take.

Ganin Yana qoqarin miqewa yasa tayi saurin riqosa zatai magana ya katseta da cewa,

Bansakaku Nemo min kowaba Koda nayi maganar zanyi aure nafada ne sbd nasamu wadda nakeso Dan haka tun wuri mum kidaina maganar nace zanyi aure Kun Nemo wata.

Murmushin qarfin Hali tasaki cikin sigar lallashi tace,

Come on sweetheart idan kaga yarinyar zaka sota, she's very beautiful, classy,rich and.....

Zare hannunsa yayi tareda barin gurin yakoma part 'dinsa gaba 'daya.

Bayansa tabi da kallo tanajin wani irin zafi na taso Mata duk da split AC kusan guda uku dasuka sanyaya palon.

Komawa tayi ta zauna zuciyarta na tsalle sbd Sarai tunda yace bayaso bayi zaiyi ba itakuma tunda taso wannan auren bamai hanashi sai Allah duk yanda tasan zatayi ayi auren saitayi Amma Kuma batason takura 'danta.

Taheer ne yashigo Ganinta cikin yanayin yasa yaqaraso ya zauna kusada ita tareda Kiran sunanta.

Kallonsa tayi da sauri tareda sakin ajiyar zuciya ta riqo hannunsa tace,

Darling kaga abinda mi'amor ke shirin yimana ko?
Wai yanada wadda yakeso baimada lokacin abinda mukeyi.

Numfashi yasauke Dan dama yasan za'ai haka tunda ba'ayiwa dawood 'din gwari gwari ba tun farkon zancen.

Lallashin mum din kawai yayi yace ta kwantarda hankalinta dawood din zai amince idan ta lallashesa tai Masa magana.

Akan haka ta miqe tayi sashen dawood din sbd tunda yafara haka baxata ta6a Bari dad yajiba sai dawood din ya amince sbd dazarar yaji zai bawa dawood din wadda yakeso Koda kuwa basuda kudi sosai.

Tana zuwa a Palo ta tarar dashi zaune idanuwansa a lumshe.

My love""""takirasa ahanakali tareda zama kusadashi.

Tashi zaune yayi tareda zuba Mata idanuwansa Bai ce komaiba.

You see my love wannan yarinyar danake fada maka tafi duk wasu models da...

6acin ransa yayi qoqarin dannewa yace,

Mum tunda kin sawa ranki maganar yarinyar Bari na yanke zancennan,
Banasonta ko 'yar gidan waye Kuma baxan auretaba wadda nakeso ita zan aura wai for godsake mum me can you go right now.

Kanada hankali kuwa Ni kake cewa na fita.,ita wannan da kake tada jijiyan wuya akanta 'yar wacece dazata sa kana 'dagamin murya.

Rufe idanuwansa dasuka kada sukai jajir yayi kafin ya bude yace,

Mum ko Yar waye,koba Yar wayeba ita nakeso ita zan aura and thats final idan kikace bazan auretaba then ki shirya tarar abinda zai biyo baya and one more thing kidainama sako maganar auren watacan sbd that will never happen sbd I rather die Dana auri wadda ba Nur ba so please mum mubar wannan maganar.


Baki tasake tana kallonsa zuciyarta na tafarfasa da maganganunsa.,
Nan take kishin Nur din daya fada ya rufe zuciyarta yanda duk duniya ba abinda 'danta keso da qauna kamarta Amma yau son wata yasa Yana fada Mata mgn,
Wata irin tsanar Nur din daya fada ta cika zuciyarta tanaji aranta bazata ta6a barinsa ya auretaba sbd tun yanxu Yana Mata haka akanta idan ya aureta shikenan zai rage sonta koma ya daina sonta.

Girgixa Kai tayi tana cewa,
Inaaaa.

'daure fuska tayi cikin 'daga murya tace,

Bazaka auretaba yarinyar danake so ka aura ita zaka aura kodan ciwon sonka dake neman kasheta and thats final sannan duk kafadawa dad dinka wani Abu Akan haka daga lokacin kasa aranka bakada mahaifiya a duniya sbd na yafeka daga lakocin.

Qura Mata idanuwansa dasuka qara rinewa yayi zuciyarsa har wani tsallen 6acin Rai takeyi yace,

Bazan fada Masa ba Amma inanan kan ra'ayina bazan auri kowace bitch ba idanba Nur duk Wanda zai mutu ya da'de Bai mutuba anrufe.

Qarasowa taheer yayi tareda riqe mum cikin taushin murya yace,

Mum Please abar maganar aleeyan tunda yace bayaso kibarshi da wadda yace Yana so Mana.

Lafiyayyan Marin datakeson saukewa dawood tini ta sauke Masa tsantsar 6acin ranta na qara bayyana ta kallesu su duka cikin kausasa harshe tace,

Koyanaso ko bayaso saiya aureta kuma wlh cikinku duk Wanda yafadawa dad 'dinku na ciresa acikin jerin 'yayana and one more thing ka shirya gobema zamu je gidansu aleeya anfasa saka auren nesa kusa za"a sakashi.

A fusace ta juya tabar part din
Wani zafi da 6acin Rai yakeji a zuciyarsa ga wata irin tsanar aleeyar dayake Kama kowane lungu da saqo na zuciyarsa sbd wannan

19, December 2024
Barirah Salihu

Thanks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login