Showing 33001 words to 36000 words out of 67570 words

Chapter 12 - DAWOOD COMPLETE HAUSA NOVEL

M SHAKUR   

29 Jun 2024

36746

bayan tayiwa su seeya dake gari tun satin daya gabata waya.

yana gaf da isa bar din wata black jeeb tasha gabansa

burki yaja da sauri tareda qoqarin fara ribas motar sarah ta taresa ta baya.

kallon anguwar yayi yaga tsit gashi dare ne fitowa yayi sbd sarai yagane sarah ce amotar bayansa yana fitowa suma suka fito tsayawa tayi gabansa tana watsa masa kallon banza tace,

poor dr sufyaan,
kaine mai binkicen mutuwar maska da abunda yasamu jass ko?
to bari na sauqaqa maka wahalarka abinda kuke gani SAKAMAKO(SURAYYAHMS?^_-)ne na abinda kukai min,
and there is more to come
saidai im really sorry to say bakanan bare kagani,
yarinyarda kuke ta fafutukar nemewa abokinku bazaku ta6a samuntaba duk da gatanan itace wadda qanin dawood din zai aura dan haka yanzu abinda nakeso dakai shine kafadamin wayene kuke binciken mutuwar maska da jass tare?

fadamin sbd nasan kaida wanine fadaminshi and nikuma zan saka yarana suyi maka sauqi sbd......

wani gigitaccen marin dayasata zubewa qasa baki na jini yasakar mata cikin tsananin takaici da danasanin neman mata sbd da ace yau basuyi neman mataba dabazasu hadu da wannan masifarba ta haduwa da saraah arayuwarsu.,
tabbas yanzu yagane neman mata na daya daga cikin sanadin shigarsu wannan balain dakum.......

saukar wani hakaukacin dukan qarfe yaji atsakiyar kansa nan take ya zube agurin yana shure shure,

daukarsa su seeya sukai suka saka mota suka tafi tareda motar sufyaan din,

tafiya mai nisa sukayi ta daji saida suka kai wani daji mai ruwa suka jefasa ciki tareda motarsa suka tafiyarsa batareda sun tsaya tabbatarwa koya mutuba sundaisan yama mutu dan bazai iya daukar wannan dukanba.

shiru shiru ba sufyaan nan dawood yalalla6a yatashi yakira taheer yafita dashi,

duk inda yakesa ran ganin sufyaan yaje baigansa ba har gidan mammyn maska yaje duk wata bar dasuke zuwa sunje nan hankalin dawood yatashi aahankali yace,

shima yatafi inaji ajikina sufyaan ma yatafi yabarni,

ganin halinda yashiga yasa taheer dawo dashi gida shikuma yakoma yakai report dukkanin polince stations,

cikin kwana biyu tuni dawood yakoma wani iri zuwa lokacin tuni kowa yasan yafara shan alcohol sbd idan yasha yanzu tana bugar dashi sosai haka zaizo yayita zagin mum baruwansa da baqinta
tun tana 6oye 6oyen abun tuni hankalinta yafara tashi tayi kuka babu adadi gashi tuni gidanta yafara cika da yan biki ammq haka zaita abubuwansa idan yayita amai yawuce daki ya kwanta.
duk wani kwanciyar hankali da farin ciki tuni ya qauracewa gidan nan hankalin dadynsa yatashi yafara binciken abinda yasamu rayuwar dansa ya lalace,

tunda mum taji dad zaiyi bincike hankakinta ya qara tashi tayi kuka ba adadi tasamu sarah ta sanar da ita akan tana roqonta data tafi har hankali ya kwanata.

sarah na sanarda siyama akan sudau mataki akan dad sbd har abada bazai ta6a bari ta auri dansaba harararta siyama tayi tace,

idan kika kashesa kina tunanin za'ai wannan auren ne yanzu?
dagasa zaayi gwara kibari bayan auren masan abinyi dashi dan wlh yana gano komai kashemu zaai dan wlh ko hukuma bata kashemuba sai dawood yayimana kisan wulaqanci.

wani yawu saraah ta hadiye sbd sam ita ko maganar mutuwa bataso tsoronta take saidai abu daya data sani duk wanda yadauki hanyar bankado asirinsu kashesa zasuyi dan wlh bazata yarda akashetaba.



*******
yau akesa lalle tunda akai aka gama babu mai doguwar walwala acikinsu sai yaqe sukeyi siyama data dawo yau sai murna da farin ciki takeyi sbd ganin ko ahaka ta tarwatsa farin ciki da kwanciyar hankalinsu saidai qasan zuciyarta wani zafi da quna takeyi na kishin taheer dan yanda takejin sonsa da qaunarsa ko layla zata iya kawarwa dan tasamesa.

tunda aka fara bikin take fama da ciwon qirji sosai saidai tana dannewa kar hankalin aleeya yatashi saidai abin yafara bata tsoro sbd har jini jini take gani idan tayi tari,Nana ce kawai tasani take dan kulawa da ita duk da hankalin nanar yatashi sosai da ganin hakan amma ta hanata fada,

duk wani buri da shirin dasukaiwa aurensu bai yiyuba sbd babu wadda zatai kyawun gani musammman ma layla da tuni tafara fita kamannninta sbd rama,

ammy ma batai wani gayyataba hakanan aka lalla6a aka daura auren aranar layla tayi kukan daya haddasa mata ciwon mai tsanani,

tunda bilal yace mata andaura aurenta da taheer,dawood da aleeya ta sulale tashige dakin nana,

rungumeta nana tayi da qarfi ta qanqameta sbd ganin wani irin kuka datake mai cin zuciya jikinta na tsananin rawa,

ita kanta nanar kuka takeyi sosai na rausayin layla kamar ranta zai fita,

ammy tunda akace angamo daurin aure take neman layla sbd tasan yau tanacikin wani mummunan hali,

dakin nana ta nufa tana ganinsu ahaka idanuwanta suka cika taf da hawaye bayasan lokacinda ta qarasoba ta janyo laylar ta rungume hawayenta na tsiyayowa.

kamar daga sama aleeya tashigo dakin nemansu tana ganin halinda auke ciki jikinta ya qara sanyi ahankali ta qaraso tq zauna kusada ammy tareda kiran sunan layla ahankali,

kasa dagowa layla tayi saima wqni sabon kukanne yazo mata mai ratsa zuciya ta juyo suka rungume juna tuni itama aleeyar ta fashe da kuka,

kuka suke sosai kowanne da abinda yake tunawa cikin ransa ammy ma saidata yi kukan daqyar nana ta lallashesu tana sakin ajiyar zuciya ganin sunqi yin shiru yasa takira bilal yana shigowa jikinsa yayi mugun sanyi ahankali ya qaraso ya durqusa tareda jawosu gabaki daya ya rungume yana mayarda hawayenda suka ciko idanuwansa,

koda aka tashi tafiya da amaren qarfe uku na rana abba koda yayi musu nasiha layla bata hayyacinta hakanan dia aka lalla6a suka wuce airport sukabar ammy cikin mummunar damuwa da kuka.
#mamuhgee



idan kunyi hkr zakuga inda zamukai komai na duniya bamai tabbatuwa bane kowa zai girbi abinda ya shuka mai kyau ko mara kyau ko son zuciya.
allah ya tsarkake zukatanmu karabamu da aikin dana sani da biyewa son zuciya.
amin.*_DAWOOD_*
_wattpad@mamuhgee_




*28*
NOT EDITED

Ana magrib suka sauka abuja nan motoci sukazo daukarsu suka nufi gidan,
mum cikin farin ciki take sosai nan gidan yaqara hargitsewa da hayaniyar farin ciki,
layla kuwa tsabar tashin hankali da mugun ciwon da zuciyarta keyi tun amota ta sume musu hankali tashe suka qaraso gidan nan mum takira taheer yazo da dr cikin tashin hankali dan sosai ya damu da jin ciwon amaryar tasa,

ruwa da allurai dr ya daura mata kafin aka barta tadan samu hutu,

kukan da aleeya tasha alokacin saidata bawa kowa tausayi dan kwata kwata batajin farin ciki ko wata walwala duk da kuwa tasamu ta mallaki dawood din datake so,

siyama da saraah kuwa daki suka shige cikin tsananin farin cikin ganin burinsu na gaf da cikewa.

daqyar aka lalla6ata aka kaita sashen mijinta suka dawo sashen mum aka baro acan,

tagumi ta rafka da hannu biyu hawaye na tsiyayowa daga kumburariyar fuskarta da tuni ta sauya sbd kuka.


tsakiyar dare ya dawo gidan guraren biyu saura,
tunda motarsa tashigo harabar gidan mum dake zaune tsakiyar gadon dakin dad tana jiran dawowarsa sbd dad baidawoba daga gurin daurin aure ya tsaya acan sai anwatse zuwa jibi zai dawo,

saukowa tayi ta fito fuskarta adaure ta fito harabar gidan ta tsaya gaban motarsa tana jiran yafito,

taheer ma jin dawowar dawood din yasashi fitowa dama baiyi bacciba sbd tunanin ya jikin layla yake yanxu,

yana fitowa ko gefensu bai kallaba ya wucewarsa riqe da kwalbarsa dama su keys jikin mota yake barinsu,

kiran sunansa mum tayi baiko sauraretaba ya wuce ya shige palonsa,

daga kwalbar hannunsa yayi ya buga da qasa lokacinda yaga komai na sashen an sauya ansaka sabbi,

qarar fashewar kwalbar tasa mum da taheer qarasowa palon da sauri,

wani kallo ya watsa musu murya a sama yace,

meye wannan?

daure fuska mum tayi tareda gyara tsayuwa tace,

aure akayi maka kuma matarka nanan ciki tana jiranka,
me kakeson mayar da kankane dawood for god sake ace yau kwananka biyu rabonka da gidannan sbd kawai banxar mace.......

tsawar daya daka matane yasa aleeya dake la6e fitowa,

ja sosai idanuwansa suka sakeyi yace,

har abada nur itace rayuwata idan kin daukeni amatsayin 'danki haryanxu to dole zaki kira sunanta da respect,
banida mata aduniya idanba nur ba,
na tsani duk wata mace dazata soni matuqar ba nur ba,
wannan dakike magana akanta itace macen danafi tsana fiyeda mutuwar data rabani da maska,
wlh mum danki zai mutu babu mata idan har ba nur bace....

shut up'''''tace da qarfi cikin takaici da zafin zancensa takallesa cikin kakkausar murya tace,

Nikuma idan nice mahaifiyarka bazaka wulaqanta wannan auren na aleeyaba,
ta wace hanya zanyi maka bayani ka gane auren nan is for your own gud mekakeso bayan wannan fadamin......

NA SAKETA.....shine zancen daya katseta dashi batasan sanda ta 'daukesa da wani mahaukacin mariba saida ya sakashi zubewaba kasancewarsa abuge,

cikin kwalbar gurin ya fadi nan take duka hannuwansa biyu suka fara futarda jini sosai ya dago jajayen idanuwansa dasuka cika taf da hawaye ya miqe
taheer yayi saurin matsowa zai riqosa ya daga masa hannu tareda shigewa daki ya bugo qofa,

tsakiyar dakin ya zube tareda dunqulewa hawayen idanuwansa na gangarowa ahankali yakira sunan NUR dasu MASKA jini nacigaba da zubowa daga hannuwansa.

da lalaben bango aleeya ta mayarda kanta daki ta sulale da6as tsakiyar dakin jikinta na rawa tsawon mintina kafin daqyar tasamu wani irin kuka yazo mata tasakesa da qarfi,

wannan wace irin qaddarace tasameta ta auren wanda ke tsananin qinta harya iya sakinta daren datazo gidan,
wace qaddarace wannan data sakata auren wanda zuciyarsa ta mace gurin son wata dabam,

kuka takeyi sosai har tana shidewa jitake zuciyarta da qirjinta na ciwo ta sulale qasa ta kwanta tana sake sakin sabon kuka.

mum ma zubewa tayi akujera tana hawayen tashin hankali meke shirin faruwa da ita da yayantane,wannan wace irin masifa ce ta 'daukowa kanta?

jiki amace taheer ya lalla6ata yakaita har bedroom dinta takwanta ya fice.

a wannan daren aleeya tayi kukan daya haddasa mata shiga mugun yanayi,
dawood ma yayi kukan rashin abokansa har yafice hayyacinsa sbd jinin dayake zubarwa,
nur kuwa tunda ta farka tsakar dare takasa motsi sbd da sabon ciwon qirji ta farko har wani sarqewa numfashinta keyi.

mum kuwa duk inda kwanciyar hankali yake ya qaurar mata takasa riqe tashin hankalinta tausayin danta takeji amma shaidan da son zuciya nason hanata barinsa.

asubar fari aleeya ta hada kayanta wainda bana lefe ba wainda abba yayi musu dabam,
bayan tagama hada kayan tsaf ta zauna bakin gado tayi shiru tana jinjina quncin datakeji dan tasan rayuwarta ta riga ta ruguje sam bazata iya fadawa laylaba sbd ganin halinda take ciki itama ayanxu.

miqewa tayi ahankali tareda fitowa palo daidai knocking dinda taheer yayi na zuwa tafiya da dawood sallar asuba a masallacin gidan,

bude masa tayi yana ganin yanayinta hankalinsa yayi mugun tashi ya shigo ciki yana kallonta ita kuwa qoqarin tsayarda hawayenta takeyi tace,

ka kaini airport tun kafin kowa yatashi asan halinda ake ciki.

girgixa mata kai yayi murya a mace yace,

aleeya babu inda zakije sbd haryanxu da aurensa akanki dan abuge yake ajiyan.

girgixa masa kai tayi sabbin hawaye na sauko mata tace,

hankalinsa yadawo jikinsa tun lokacinda mum takira sunan NUR 'dinsa.

aleeya bazaki tafiba ki zauna ki taimaki rayuwar wanda kikeso ta hanyar dawo dashi cikin nutsuwa da kamalarsa,
koda kin tafi zuciyarki baza ta6a daina sonsaba,
ina roqonki daki zauna kitayani mu daidaita rayuwarsa sbd yana tsananin buqatar hakan kuma ki yarda dani baiyi sakin nanba yana cikin hayyacinsa amma zamuje muyi tambaya gurin malamai masana.

sabon kuka tasake ahankali tareda zubewa kan kujerar gurin tana toshe baki,

asanyaye ya matsa jikin qofar dakin yayi tura
abinda yagani yasashi qarasawa da sauri ya tallafosa yana kiran sunansa da qarfi,

jin haka yasata tasowa cikeda tsoro da fargaba tagansa kamar barai ga jini kwance a qasa.

cikin tashin hankali akayi asibiti dashi mum ko sallar asuba batayiba saidai tayita acan,

daga ita har aleeyar kuka sukeyi taheer na duk abin duniya ya ishesa sai kaida kawo yakeyi,

yan biki washe gari saidai saraah ce ta sallamesu suka koma,
tsabar wulaqanci ta mota suka sakasu suka tafi umman siyamaa kawai sukasa jirgi bayan uban kudaden dasuka bata nan tayita sake dorasu ahanya tana sanya musu albarka,

layla tana bude idanu da nana tafara cin karo sbd dama bada ita zaa komaba anbar musu ita aikine,

daqyar ta tashi zaune tana lumshe ido cikin azaba ahankali tace,

zanyi sallah nana.

kamata tayi takaita toilet tayo wanka da alwala tazo tayi sallah tana idarwa ta jingina da gado tareda lumshe ido tanajin babu abinda tafi buri da buqata yanxu kamar tarabu da auren taheer  tabar gidan.

cikin sanyi da rawar murya Nana tasanarda ita dawood na asibiti,

sosai taso dannewa amma saida nana tayi dana sanin sanarda ita.

ganin kamar abin yafi qarfinta yasatakira wayar aleeya tasanarda ita aikuwa nan hankali yaqara tashi taheer yadawo gida aleeya datasha kuka wani kan wani,

dr aka sake kira yayi mata allurai tareda qara daura mata wasu ruwa,

tunda taheer yashigo ta rintse idanuwanta gabanta na tsananta nauyi
dr na fita ta bude ahankali tareda kallon aleeya datai wani mugun fadawa dare guda ahankali tace,

kiyi hkr zaiji sauqi insha allah.

share hawaye aleeyar tayi tana jinjina kai batareda ta iya maganaba.

kallon yanayinta taheer yayi saiyaga kamar batason kallon gefensa ya juya ahankali ya fuce tareda sawa aka hado mata tea mai kauri yakawo mata tareda miqa mata ahankali yana kallon yanayinta,

batareda ta dagoba ta kar6a ta aje gefe,

zama yayi bakin gadon yasake daukar cup din ya miqa mata murya a tausashe yace,

kisha ko kadan ne.

wani abu daya taso mata ta danne tareda kar6a ahankali ta kur6a.

yana ganin haka ya miqe yakoma asibiti.

kwanan dawood biyu a asibiti aka sallamosu saidai ko aranar bai kwana gidaba saida asuba yadawo ko kallon aleeya data kwana palo zaune daram tana jiransa baiyiba ya wuce bedroom dinsa ya kwanta.

share hawayenta tayi tareda miqewa ta shige daki tayi sallah ta fara wani sabon kuka sbd batasan wazata fadawa halinda take cikiba batason qarawa layla damuwa ammy kuwa batason daga mata hankali,

kwananta biyu kusan satin layla biyu a sashen mum mum itama da gangan ta qyaleta sbd batason wani abu yashiga tsakaninsu tun yanxu,

itama laylar sosai tafison hakan sbd sam ko haduwa da taheer din bataso,
ga sabon tashin hankalinda take ciki na ganin rayuwarda dawood yafada tayi kuka aranar harsaida kukan yadaina fitowa na tausayinsa da kanta harma da halinda aleeya ke ciki sbd dukkanin alamomi sun fara bayyana da tana cikin tsananin damuwa da quncin zuciya,

aranarda dawood din yayo wani dare akai rikici sosai arabar gidan shida mum da taheer aleeya banda kuka babu abinda take sbd sosai yakashe musu jiki da maganganunsa,

layla dake tsaye jikin window sulalewa tayi cikin wani irin gunjin kukan tausayinsa,
bata ta6a tunanin sonda yake mata yakai hakaba dan itama sosai maganganunsa suka daketa zuciyarta zafi take sbd babu abinda takeson kasancewa dashi yanzu kamarsa.

aleeya da mum ma sosai suke hawaye
ayau aleeya datasan inda zataga NUR dinsa datayi alqawarin nemota sbd abinda taji tagani yanxu ya sake tabbatar mata da har abada dawood bazai kalli wata mace idanba nur ba,
ita kuwa zata iya sadaukar da nata farin cikin kan nasa matuqar zataga nur din.

ko a wannen daren babu wanda yayi bacci acikinsu musamman dawood aranar yayi kukan rashinsu maska arayuwarsa jiyake dama rayuwarsu ta baya tadawo dabazai ta6a bari yafada soyayyaba.

washe gari taheer yagama hada komai na tafiyarsa dazaiyi da layla cyprus sbd sosai yakeson tafara sakewa dashi sbd sam yakasa gane inda aurensu ya dosa sbd sosai yalurada gudunsa take ko ganinsa batasonyi yanason su fara fuskantar rayuwar aurensu dan idan suna gidan mum bazata ta6a bariba.

sosai hankalin mum yatashi daya fada mata tafiyar batasan sanda tafara kukaba ahankali tace,

taheer haka zaka tafi kabarni da dawood acikin wannan halin dayake ciki,
kana gani ciwo nacinsa amma taurin ransa ya hana yabari ayi masa magani,
taheer dan allah karka tafi kabarni cikin wannan halin ina tsananin buqatarka akusa.

girgiza kai yayi ya lalla6ata akan bazai dadeba zasu dawo.


lokacinda taheer yakirata awaya yasanarda ita maganar tafiyar qiris yarage ta zube tsabar firgici da tashin hankali.

sulalewa tayi qasa jiki na rawa ta zauna kusada aleeya dake zaune shiru tayi nisa a tunani.

zazzare idanuwa taitayi sbd danne kukanta kar tayi gaban aleeya taqara mata wani tashin hankalin dan tana iya qoqarinta gurin danne damuwarta gaban aleeya dan yanzu kowa nada tasa kalar damuwar.

da daddare tayi kuka mara iyaka kafin ta dangana tana fatar allah yasa kafin tadawo aleeya da dawood sun daidaita.

washe gari tunda suka suka wuce bayan aleeya tasha kuka ajikin layla sbd yanzu taqara tabbatarda rayuwar qunci zatayi arayuwar aurenta,
kukan datayi harsaida jikin layla yaqara yin sanyi sbd sosai aleeya ke bata sosai.

suna barin gidan hawayen datake dannewa suka tsinke ta lumshe idanuwa ahankali.

kallo 'daya yayi mata yaji jikinsa yayi mugun sanyi.

wayarsa ce tayi ringin yana dauka ahankali yace,

yes junaid.

daga can 6angaren junaid din yace,

barr dama maganar binciken mu ne na marigayi maska jiya mun samu ganin sambo wanda shine mutum na qarshe da maska yagani a adamawa kuma duk wasu bayanai na abunda yasakasa na nemo wata yarinya yabamu bayanan harma da hotuna gasunan ahannuna.

gud job junaid thank you,
yanxu ina hanyar zuwa airport kasameni kabani takardun yanxu.

ok sir insha allah.

kusan atare suka isa airport din ya miqawa taheer din babban envelope dinda ke daukeda bayanan kafin ya wuce.

cikin jakar laptop dinsa yasaka envelope 'din suka wuce sbd jirginsu da aka fara kira.





tunda suka wuce sarah takasa zama sai kaida kawo takeyi cikin rashin sukuni,

kallonta siyama tayi tace,

wai lafiya kika kasa zama?

tsayawa tayi tareda dafe goshi cikin rashin sukuni tace,

hakanan nakejin hankalina bai kwantaba akan taheer sbd kinsanfa seeya yace sun gansa da wani 'dan bincike a hotel ranar.

aje wayar hannunta siyama tayi tana qoqarin daure abinda ke taso mata tace,

to me kike tunani yanxu?

murmushi sarah tayi tace,

so nake shima na koya masa hankali tun wuri sbd......

kallonda siyama ke matane yasa tayi saurin hadiye zancenta murya na rawa tace,

me...me meye haka?

wani mugun riqo siyama tayi mata idanuwanta na fitowo sbd masifa cikin wani irin yanayi tace,

wallahi duk kika ta6a lafiyar ko takalmin taheer ne saina aje duk wani abu dake tsakaninmu na lalata rayuwarki ta yanda har abada bazaki mantani ba.,

qwacewa sarah tayi da qyar tana fito da ido tace,

kina nufin musa masa ido asirinmu ya tonu?

bansan wannanba amma abu daya nasani duk wanda ya ta6a taheer wlh saina lalata rayuwarsa kowaye bazan 'daga masa qafaba koda uwardata haifesa ce zan iya wullawa akansa bare ke dan haka ki kiyaye.

zarar wayarta tayi ta fice zuciyarta na tafarfasa.

wani mugun kallo sarah tabita dashi tareda jan numfashi mai zafi tace,

zan nuna miki nice boss dan nikeda kudi banxa kawai.
#mamuhgee_*DAWOOD*_
_wattpad@mamuhgee_




*29*
NOT EDITED



cikin dare suka isa cyprus suna isa gidan ta shige bedroom dinda ya nuna mata ta rufo qofa tareda sake ajiyar zuciya sbd atsananin takure take zama akusa dashi cikin jirgi da motarda takawosu gida.

saidata jima azaune shiru

19, December 2024
Barirah Salihu

Thanks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login