Showing 39001 words to 42000 words out of 67570 words
saita kasa magana ta fashe da wani sabon kuka mai qarfi tana cewa,
wane irin balai da masifa ne wannan na jawowa kaina.
kuka tayi sosai harsaida muryarta ta dashe ta miqe daqyar ta fice batareda ta iya cewa qalaba takoma asibiti kukanta na kasa tsayawa.
kodata koma asibiti sabon kuka tasaki aleeya datayi kuka harta fice hayyacinta ita tafara rarrashinta amma sam takasa sbd babban tsoronta na biyu bayan na halunda taheer ke ciki shine makomarta idan CJ yaji itace mafari idan aka gano saraah ce taso kashe taheer.
gudu yakeyi sosai kamar zai tashi babu ruwansa da tudu ko ina fadawa yakeyi gashi police basu bar binsuba gashi sunyi waya anturo musu wasu motocin cike da police sosai suka bude masa wuta amma taqi tsayawa harsunyi nisa da gari sosai sai kawai ya yanka daji cikin rashin sa'a motar ta qwace masa tayita gudu saidata kai gurin wani qaton ice ta dakesa tafara hayaqi,
daqyar ya dago kansa daya bugu harda jini ya fito motar ya bude baya ya cicci6ota sbd tun aqofar gidan ta some batareda taga wanda ya daukotaba,
cicci6arta yayi yakutsa dajin da ita yacigaba da gudu yayi nisa kadan motar takama da wuta sosai daidai isowar police suka tararda takama da wuta nansuka buga suka sanarda wainda ke ciki sun mutu suka juya.
gudu yayi sosai cikin tsakiyar dajin har asuba ga gajiya ga qafafuwansa dasuka fara farfashewa sbd tafita cikin manyan qayoyi,
yana kaiwa gurin wani qaton kogi jiri ya dibesa agurin suka zube asume dagashi har ita.
dad qarfe bakwai na safe ya dira a asibitin mum na ganinsa hankalinta yaqara tashi,
cikin saa dr yafito lokacin yakallesu tareda miqawa dad hannu yace,
mu gode allah he is out of danger wuqar bata samesa a cikiba a gefe tasamesa kuma bata shiga irin sosai dinnanba munyi masa aiki mun 'dinki gurin kowane lokaci zai iya farkawa saidai kuma gskia zai dade sosai bai fara miqewa tsayeba sbd akwai jijiyar data ta6u kadan.
ajiyar zuciya suka sauke cikin farin ciki da hamdala nan dad ya juyo ya kalli mum yasake tambayarta yanda abin yafaru,
kallon gefen aleeya tayi ta hadiye wasu yawu daqyar murya na rawa tace,
matarsace ta sokesa nima bansan daliliba yanxu haka ta gudu police sunbita....
isowar police gurin yasayin shiru tana kallon inspectan.
kalllonta yayi cikin jimami yace,
haj saidaifa haquri yarinyar motarsu ta qone qurmus muna tsaye ta cinye babu wanda yafita acikin.......
ganin sukayi aleeya ta yanke jiki ta fadi agurin bata motsi,
juyawar dazatayi sai ganin ammy da bilal tayi kowannensu ya daskare ga dukkan alama ma suma suman ne sukayi atsaye jin abinda inspectr yafada daga isowarsu.
hankali tashe akayi emergency da aleeya ammy ma nan take hawan jininta yatashi akai gaggawar kwantarda ita sbd kartayi kwalapsin,
bilal kuwa tsayawa yayi cak gaban gadon ammy idanuwansa jajir jijiyoyin kansa har wani motsi sukeyi tsabar tashin hankali sam kwaqwalwarsa takasa daukar cewa 'yar uwarsa ta tafi tabarsa.
sulalewa mum tayi takoma gida afusace ta banka qofar dakin sarah tareda fusgota ta jehota waje tareda watso mata kayanta tace,
duk wata masifa data afkomin nida yayana kece,
nayi baqin ciki da dana sanin kawoki gidana,
kin tarwatsa rayuwar yayana,
na hana yarona farin ciki ina kallo rayuwarsa ta ta6ar6are sbd ke,
yanxu kinzo kinyi qoqarin kashemin taheer inaji ina gani na maqalawa wata sbd kar laifin yashafeni gashi ta rasa ranta ta rasu ta sanadinki amma bazan iya fadaba sbd dole nima saina fuskanci sharia dan haka tun kafin kowa yasani kitashi kibarmin gidana bana buqatar sake ganinki inason gyara abubuwan dana lalata da kaina.
muqewa sarah tayi tana kallon bayan mum din ido a waje,
juyawa mum tayi tayi ido biyu da dad tsaye idanuwansada fuskarsa qunshe da tsananin 6acin rai,
mummunan faduwa gabanta yayi wani mugun zufa ya karyo mata tadaga qafa zata matso ya daga mata hannu da ido jajir,
sarah na ganin haka ta sulale takwashi kayanta tabar gidan.
cikin wata irin murya mai tsananin sanyi yace,
faraah kanki kika cuta,
dasaka hannunki cikin lalacewar danki,
dasaka hannunki cikin mutuwar yar mutane,
bazan miki komaiba sbd haryanxu duniya bataimiki darasin daya kamata saidai nizan dauke 'dana mutafiyarmu bazaki sake ganinmuba insha allah dawood ma zan dawo na daukesa sbd yanxu matarsa na buqatarsa na rashin yar uwarta datayi.
matsowa tayi da gudu ta zube gabansa tareda riqo qafafuwansa tasaki wani irin kuka mai qarfi ya zame qafafuwansa ya wuce ya tattaro duk wasu takardu da abubuwan buqatarsa dana taheer yafice tabisa har jikin mita tana kukan tashin hankali amma ko kallonta baiyiba yawuce da gudu yabar gidan.
yana isa asibiti cikin qanqanin lokaci yasaki kudi sosai nan take suka samu flight aka saka taheer suka tafiyarsu bataredama taheer din ya farfadoba.
#mamuhgee.
vote and follow pls.*_DAWOOD_*
_wattpad@mamuhgee_
*31*
NOT EDITED
wasu tsofaffin masu kamun kifine suka iso bakin ruwan tun daga nesa dayan ya hango kamar mutane kwance ya qurawa gurin ido saida suka matso sosai yace,
baffa kaga wasu mutane kamarma mataccine.
kallon gurin baffan yayi tareda qara matsowa yagansu da sauri suka qaraso baffa ya durqusa yasa hannunsa a bakin hancin dawood yace,
wannan da sauransa bai mutuba bari muji macen,
itama yana sawa yace da ranta maza debo ruwa hamisu,
da sauri yayi bakin rafin ya debo ruwa nan take suka zuba musu amma cikinsu babu wanda ya motsa saima fuskar layla data wanke tafito fes,
qurawa fuskarta ido yayi yana qoqarin tabbatarda kamannin duk da akwai sauyi na girma da shekaru sosai atareda ita,
laylah'''' ya furta ahankali cikeda mamaki sbd tabbas bazan manta layla da bilal ba sbd shine yaso riqesu son kudi da zuciya ya hana amma yayi nemansu daga baya harya gaji yadawo qauyensa,
kallon dansa hamisu yayi yace,
maza da sauri jeka kakirawo manasu abu agonarsu da muka wutosu,
ko minti goma baayiba suka dawo hankali tashe nan yace sukama masa dan allah gidansa zai kaisu.
daukarsu sukayi suka koma cikin qauyensu bayan tafiya mai 'dan tsawo,
suna shiga gidan aka shimfida tabarma tsakiyar dakin dasuke aje baki aka kwantar dasu layla harda saka mata matashin kai.
kowa na ficewa ya kalli matarsa yace,
halima ki dora min ruwan zafi sbd suna tsananin buqatar dumi ta yanda zasu farfado da wuri
kaikuma hamisu maza hadomin maganin sanyi dana kai.
to baffa yace tareda shigewa wani daki da sauri.
komawa yayi dakin yarufesu da abun rufa yafito.
cikin qanqanin lokaci aka hada ruwan zafi da magunguna nan suka shiga gyaran qafafun dawood da sauran raunikan dayaji akai
layla kuwa inna haleema ce tayi mata.
duk wani abu daya kamata sunyi musu suka fito jiran farkawarsu sbd numfashinsu yafara dawowa daidai yake fita kowane lokaci zasu farka.
har maraice babu wanda ya farka acikinsu ataqaice sai tsakiyar dare dawood ya fa bude idanuwansa daqyar sbd tsananin nauyin dakansa yayi masa,
tunowa yayi da nur da sauri ya dafa ya tashi zaune a wahalce yace,
NUR.
agefensa yaganta kwance tana fidda numfashi ahankali fuskarta ya qurawa ido idanuwansa na cikowa da hawaye yana qara gasgatawa kansa NUR ce agabansa yau,
abinda ko amafarki baikawoba,
shi kwata kwata babu ruwansa da wani canzawar datayi farin cikinsa da burinsa dai yau ga nur agabansa,
ahankali yakai hannunsa na rawa ya riqo nata da qarfi yasaki ajiyar zuciya tareda rufe ido hawayen dasuka taru suka gangaro.
wani irin wahalallen murmushi yasaki hawaye na fito masa yace,
har abada bazaki sake barina ba kina farkawa zamu daura aure anan batareda sanin kowaba mu tafiyarmu muyi rayuwarmu mu kadai tunda banida kowa yanxu.,
dad bayada lokacina,
mum ta lalatamin rayuwa,
maska yatafi,
jass yatafi,
sufyaan ma yatafiyarsa,
taheer ma yatafiyarsa da matarsa yabarni duk sbd sunga na lalace nazama wani abu daban
nur nasan komai nazama bazaki gujeni ba.
jin motsinsa yasa baffa dahiru fitowa yashigo dakin cikin farin cikin ganinsa zaune yace,
masha allah''''tareda miqa masa magani
kallonsa dawood yayi dakyau tareda kallon qofar waje yace,
ina ne nan 'din?
kwantarda hankalinka kasha maganin tukuna ni kamar kawu nake agurin layla nan gidana ne kuke ayanxu.
kar6a yayi ya shanye kai tsaye tareda muqa masa cup din yana mayarda kallonsa ga NUR sbd ko dauke ido akanta bayason yi,
lurada hakan yasa baffa dahirun miqewa ya fice yana murmushi ahankali.
yana zaune gabanta idanuwansa qyar akanta har akayi kiran sallar asuba qiri qiri a dakin yayi sallar su baffa kuwa sukai masallaci,
basu dawoba saida gari yayi haske sosai suna shigowa idanuwan dawood suka ganar masa kamar yaga sufyaan yashigo gidan.
girgixa kansa yayi tareda juyowa yakalli NUR yajuya yakalli qofa yanason fita yagani amma yakasa sakin hannunta daidai lokacin kuma ta motsa tareda bude idanuwanta ahankali.
a fuskarsa idanuwanta suka sauka ta lumshe ido ahankali tareda sake budewa sbd bata gasgata mai idanuwanta da zuciyarta ke nuna nataba,
murmushi tasake tareda qara damqe hannunta dake cikin nasa murya amatuqar mace,
yace,
nine NUR,bude idanuwanki kigani.
tashi tayi tareda qura masa idanuwa suna cikowa da hawaye da sauri yasake matsowa yana girgiza mata kai kartayi kuka shima hawayen na cikowa daga idanuwansa.
rufe idanuwa tayi tareda sakin siririn kuka ahankali wani yanayi takeji azuciyarta wanda duk yanda taso danne cewa na farin cikin ganinsane takasa,
sake 'dora masa jajeyen idanuwanta tayi yau dawood 'dinta ne agabanta riqeda hannunta dama shine ya dauketa daga hannun police,
ahankali ta bude baki saikuma takasa magana ta hawaye suka gangaro mata shikuwa tsabar farin ciki jikinsa har wata irin rawa yakeyi ya miqe da sauri haryana tuntu6e yaleqo tsakar gidan yace,
kawu kazo ta tashi abata magani itama.
dawowa yayi da sauri ya sake zama kusada ita jikinsa na rawa sai farin ciki yakeyi yana share hawaye
wani irin mugun tausayinsa da tsimin sonsane ya taso mata ganin hawayen dayake jikinsa sai rawa yakeyi.
baffa da hamisu ne harma da inna halima suka shigo atare daukeda koko mai zafi.
kallo 'daya tayiwa baffa taganesa duk da ya manyanta bata manta fuskarsa ba sbd duk da shegen son kudinsa awancen lokaci bai qyamacesu ba.
cikin kulawa yace,
layla ya jikin?
gangaro mata hawaye sukayi ahankali tace,
baba dahiru....saikuma tayi shiru tareda sunkuyar dakai tana cigaba da tsiyayar hawaye.
zaunawa inna halima tayi kusada ita tareda miqa mata kamata suka miqe takaita har bayi tayo fitsari tareda alwala tazo suna zaune tayi sallah akabata kako takasa sha saidai maganin tasha daqyar suka zauna jigm jigum kafin baffan yayi gyaran murya a sanyaye yace,
layla a jeji muka tsinto ku bakin ruwa keda wannan danake tunanin qila mijinki ne,
layla wlh tun ranar dana rabu daku nake nemanku sbd nayi nadamar abinda nayi muku duk da dama nayi muku hakan ne koxaku fitar da kudin saigashi kodana dawo nayita yawon nemanku banganku ba haka na haqura na tattara nadawo qauye ga 'dana nan hamisu da maidakina halima sai wani baqonmu dashima hadari yayi muka tsintosa tsawon shekara guda da rabi haryanxu yakasa tuna komai akansa saidai wani lokacin kamar zai tuno saikuma abin ya birkice.....
sai alokacin dawood ya dago da sauri ya kalli baffan tareda miqewa sbd tabbas idanuwansa dazu sufyaan ne suka hango masa aida sauri ya fice haryana tuntu6e da sauri yana cewa,
sufyaan,,,,sufyaan,,suf.....
cak ya tsaya tareda qurawa sufyaan din dake tsaye bakin qofar dakin dayake ido
dafe kansa yayi wasu irin sabbin hawayen farin ciki mara misaltuwa suka gangaro masa a haukace ya fuxgosa ya rungume yana kiran sunansa cikin kukan farin ciki.
yanda ya fixgosa da yanda yake masa ihun kiran sunan sufyaan a kunne yasa yafara jin wani dummmm da jiri na dibarsa ya dafe kai da sauri sai ganin sukayi ya zube qasa baya motsi.
hankali tashe dawood ke kiran sunansa jikinsa na rawa da sauri su baffa suka daukesa aka kai dakinsa suka shimfide nan aka debo wani hayaqi sukai masa baffa ya riqo dawood din suka fito akabarosa shikadai baffa yace,
koyaushe wannan turaren ke taimaka masa gurin tuno wani abu kuma wani lokacin ana dacewa saidai daga baya abin ya birkice sbd babu wanda zai tuna masa bayansa saidai yau muna fatar haduwarku tasa ya dawo daidai sbd bai ta6a mana hakaba dan haka insha allah wannan alamar samun sa'a ce.
numfashi kawai ya sauke batareda hankalinsa ya kwantaba yakoma bakin dakin da nur take ya zauna tareda dafe kansa da yanajin babu ranar datafiye masa wannan ranar sbd ga nur ga sufyaan saidai abun nason rage masa armashi.
qurawa bayansa ido tayi tacikin dakin wani sonsa na fixgarta zuwa garesa ta sunkuyar dakanta zuciyarta na zafi tunowa da mijin aleeyarta ne ayanxu ba nata bane.
juyowa yayi ya kalleta saiyaji ya rage rudanin dayake ciki yasakar mata wani wahalallen murmushi awahalce.
zaman jiran farfadowar sufyaan yayi a qofar dakin tareda tsare qofar dakinda layla ke ciki da ido.
baffa kuwa fita yadanyi yabar hamisu sbd kar sufyaan yatashi bakowa inna kuwa tahau aikin sanwar abinci.
tsawon lokaci yana zaune agurin ga rana ta hudo sosai
kasa hkr tayi ta miqe ahankali ta fito tareda yimasa kallo daya ta dauke kai ahankali tace,
inson zanga sufyaan din.
miqewa yayi da sauri ya nufi dakin suna shiga ko minti biyu batayiba ta juyo ahankali tace,
kaxauna ciki akwai rana waje.,,tana fadar haka ta fice da sauri tana kaiwa qofar dakinta tajisa abayanta ta juyo da sauri tareda kallon fuskarsa a wahalce yace,
bazaki fita ko qofar gidaba ko?
cikowa idanuwanta sukayi da hawayen tausayinsa ta girgixa masa kai hawayenta na saukowa tace,
bazanje ko qofar gidaba.
dakin sufyaan din yashiga yana waiwayenta tareda 'dauke tsohon labulen dakin dan ya tsare qofar dakin datake da ido.
zaman jigum jigum sukayi har kusan yamma baffa yadawo ya zauna tsakar gida yaci abinci tareda shiga ya dubo jikin sufyaan yafito yadawo dakin layla ya zauna da kyau tareda kallonta yace,
layla ina bilalu?
sunkuyar dakai tayi murya asanyaye tace,
yana gida.
gyara zama yayi yana sake kallonta yace,
layla mahaifinku tun yanada rai niya barwa amanarku harya rasu nayi sakaci babba dan haka nakeson nasan sanin menene yafaru naganki a jeji?
shiru tayi tsawon lokaci tana jan numfashi kafin ahankali tafara zayyano mata tarihin rayuwarsu bayan rabuwarsu dashi har zuwa gudowar da dawood yayi da ita akan ana zarginta da kisan tsohon mijinta.
shiru yayi zufa na karyo masa inna halima kuwa harda hawaye sharkaf.
dawood dake bakin qofar dakin jin zubewarsa sukayi da gudu hamisu ya tarosa saidai tuni yayi mummunan suma.
ruwa aka zuba masa ya farfado yana bude ido kallo daya yayiwa layla dake raku6e tana kuka ahankali ya sunkuyar dakai sai kawai ya fashe da wani irin kuka mai ciwo yana buga kansa jikin bango da qarfi.
ganin mummunan halinda yashiga zai illata kansa yasa su baffa riqesa ya qwace tareda jawota da qarfi ya qanqame cikin jikinsa yana cewa,
bazan iya rayuwa badekeba kice zaki aureni nur wlh bazan iya rayuwa bakeba.
daqyar su baffa suka qwaceta kamar daga sama sukaji ance,
DAWOOD.
dukkaninsu atare suka juya yana ganin sufyaan ya qarasa da sauri suka rungume juna atare suka fara sakin sabbin hawaye.
sufyaan ne yafara janyewa tareda qurawa nur ido yamaido kallonsa ga dawood yace,
dawood nur itace matar taheer...
rintse idanuwa dawood yayi wasu sabbin hawaye suka fito ya juyo ya kalli baffa tareda riqo hannunta ya damqe cikin nasa yace,
taheer yasaketa sbd nine yanason nasamu abinda nakeso kuma yayi hakan ne dan yasan bai ta6amin nur ba zan iya aurenta inason a daura mana aure ayau....
da sauri ta kallesa tareda qoqarin zame hannunta tana girgiza kai tace,
bazan aureka ba.
matseta yayi da qarfi cikin zafi da daga murya yace,
saikin aureni sbd kece silar duk wannan masifar akan wani banzan tunaninki,
meyasa ni bikiyi tunanin halinda zanshigaba kika za6i barina akan wata dabanmasan da wanzuwartaba,
enough of all this stupid qaunar dakikewa aleeya kinbata abinda takeso now its my turn dole nima zaki aureni.
tureta yayi ya juya yana dafe kansa cikin tsananin 6acin rai da fushi ga wata irin sarawa dakansa ke masa.
ficewa yayi gidan da sauri sbd jiyake ma kamar numfashinsa zai sarqe iska yakeso,
bayansa sufyaan yabi da sauri yana kiran sunansa amma tuni yayi nisa.
jiki asanyaye baffa yakalleta yaga yanda take kuka harda shesheka yasan tabbas tana tsananin son dawood kamar yanda shima yake sonta dan yagani a idanuwanta kuma tun frko aurensa shine maslahar datafi amma suka za6i haka gashi abibda yabiyo baya,
abu dayane ko ayanzu mafita kuma maslahar komai shine aurenta da dawood kuma shima zaiyi farin ciki da hakan dan haka cikeda muryar rarrashi yace,
layla inaga shawara anan kibari adaura muku auren saikuje ku fuskanci kowa azauna ayanke shawarar abinyi sbd shikadaine mafitar ceton kanku ku duka,
amatsayina zan iya aurar dake sbd sani da mutuncin danayi da zama da mahaifinku dan haka zanje yanzu gurin mai gari nayi masa bayanin komai idan auren zai yiyu gobe insha allah nizan daura muku aure dakaina kuma ina roqonki alfarmar karkice aa.
girgiza kai tayi da sauri tareda shigewa daki ta zame qasa tafara rero sabon kuka.
#mamuhgee
vote and follow._*DAWOOD*_
_wattpad@mamuhgee_
*32*
NOT EDITED
bayanta baffa dahiru yabi da kallo yana jinjina alamarin kafin ya nufi dakinsa ya zauna yana sake nazarin alamarin,
baifitoba sai maraice yayi alwala shidasu dawood suka wuce masallaci har lokacin sosai dawood yake cikin yanayi na jin zafin abinda laylar ke shirin yi duk da dai yasauki alqawarin kobataso saiya aureta yagaji da wannan azabar datake gana masa arayuwa.
amasallaci bayan sallar magriba baffa yasamu mal liman yayi masa bayani akan rasuwar mijinta dakuma auren dasukeson adaura,
dogon naxari mal liman yayi kafin ya nisa yakalli baffa dasu dawood din yace,
tabbas zata iya aurensa tunda wancan qaninsa din kunce yarasu saidai dole sai bayan tagama takaba...
shiru baffa yayi na seconds kafin ya dago murya a tausashe yace,
eh to babu wani abu na aure daya ta6a shiga tsakaninsu hasalima basuyi rayuwar irinta zaman aureba kuma kafin rasuwarsa yabata sakinta ahannunta.
sake gyada kai mal liman yayi yasake cewa,
eh to zasu iya aure amma idan son samune zaifi subari zuwa gaba kamar......
katsesa sufyaan yayi dafara zayyano masa komai daga farko zuwa qarshe.,
mal liman yayi shiru tareda qurawa dawood ido yana jinjina kai yace,
sannu dauda.
kallonsa kawai dawood yayi da lazy eyes dinsa shidai fatarsa kawai ace zaa daura auren.
tabbas daura musu aure bai haramta ba dama dai nasone subari tayi kwana biyu kamar zaifi amma tunda abun hakane gobe takasance alhamis jibi ranar jumaa insha allah da safe sai a daura auren,allah yasa hakan shine mafi alkhairi arayuwarsu duka.
amin sukace dukkaninsu dawood najin wani sanyi da kasala na shigarsa sbd yasan babban burin rayuwarsa ne zai cika idan NUR dinsa tazamo matarsa,
godiya sukai masa sosai kafin suka miqe,
basu koma gidaba saida sukai sallar isha suna komawa suka shige daki duk da zuciyarsa a tsananin takure takedason ganinta amma hakanan ya daure sbd yasan idan ya matse mata zatacene bazatai aurenba gwara yabata space har yasamu adaura auren,
yanaji inna halima nayiwa baffa complain taqi fitowa har lokacin kuka takeyi yayi zuru tareda mayarda dukkanin hankalinsa kan qofar dakin datake,
sufyaan dake qoqarin sanardashi maganarsu saraah ganin hankalinsa baya jikinsa yasa yabari harsai bayan auren idan hankalinsu yadan
19, December 2024
Barirah Salihu
Thanks