Showing 27001 words to 30000 words out of 67570 words
Dan Dole watarana za'a samu sa6ani.
Qarasowa tayi jikinta amatuqar sanyaye,
Da sanyin jikin abinda dawood yayi Mata ta shigo Amma Jin abinda Layla ke fada ya qara sanyaya jikinta.
Zama tayi kusada laylar tana kallonta cikeda mamaki da fargabar ganin sauyi sosai atareda ita,
Idanuwanta dasukai jajir da fuskartama gaba 'daya takalla tuni kafin taji koma meyene idanuwanta suka cicciko Nan take damuwar datake ciki ta dawood ta 6ace asanyaye tace,
Dama Layla akwai abinda harzaki saka wani alqawarin kar afadamin??
Wane irin sirrine da Ni bazan iya 6oye mikiba har kike guduna dashi....
Jin muryar aleeyar tafara rawa yasa tayi saurin riqo hannunta tana qoqarin Hana hawayenta fitowa Amma Saida suka gangaro tace,
Har abada Babu wani sirri dazan 6oye Miki idanma akwai to kisaka aranki Dan ciganki da farin cikinki ne...
Inason sanin koma menene Layla kifadamin tun kafin zuciyata ta buga da fargaba.
Share hawayenta tayi ahankali tace,
Dawood iyayensa sun Masa Mata har antsayar da ranar aurensu bazai ta6a aurena......
Tun kafin laylar takai qarshe kukan datake riqewane ya kubce Mata tayi saurin rungume laylar cikeda wani irin tausayinta dama tanason yin Kuka Dan rage zugin zuciyarta na tsantsar qiyayyarta data hango a idanuwan dawood idan ba kuskuren gani tayiba.
Kuka take sosai na tausayin Layla da kanta saidai tafasa fadawa Layla damuwarta Akan qiyayyarta data gani a idon dawood sbd karta qara Mata damuwa ko ammy bazata fadawa ba zata bar maganar aranta ta Taya 'yar uwarta jimamin abinda yasameta..
Sosai tayi qarfin Hali ta nunawa aleeya ta rumgumi hakan amatsayin dama bashine mijinta ba.
Girgixa Kai aleeya tayi tana fitarda sabbin hawaye tace,
Yanda kikesonsa har abada bazaki daina sonsaba,
Tun zamana dake akwai wasu farin ciki da annashuwa dashine kadai yake sakiyinsu koni bana sakaki duk kuwa danasan babbn matsayin danake dashi agunki,
Layla bazaki iya babushi ba Ni zanje har gurinsa na roqesa yadawo gareki zan qasqantar da kaina na roqesa qasqantarwa ta qarshe Dan yadawo gareki..
Share hawayenta tayi tana qaqalo murmushin qarfin Hali sbd so take arufe maganar dawood da ita gaba 'daya ayau basai ankwanaba ga kanta dake tsananta ciwo zazza6i Mai zafi takeji sosai.
Aleeya na dangana nabarsa har abada Dan haka daki tayani nemosa gwara kitayani mantawa dashi.
Sake rungumeta aleeya tayi cikin tsananin tausayinta da Jin zafin dawood 'din daya za6i wata yabar Layla Nan take taji ta tsanesa Koda zai dawo bazata ta6a barinsa ya auri Laylan ba sbd Bai cancancetaba
Laylanta ta cancanci Wanda yasan darajarta fiyeda komai.
Jin jikin laylar da zafi yasa ta ja hannunta suka koma bedroom 'dinsu ta kwantarda ita tareda ja Mata bargo cikeda kulawa tace,
Have some rest zakiji qarfi zuwa anjima.
Miqewa tayi ta zame kayanta tasa jeans da vest tadawo bakin gadon da laylar ke kwance ta rafka tagumi cikeda tunani da damuwar kanta data laylar.
Itama Layla rufe idanuwan kawai tayi.
Daqyar ammy ke sakin murmushin yaqe hardai Abba ya tambayeta maganar iyayen manemin Layla kawai suke jira su qaraso yanxu.
Rufe idanuwa tayi tareda ha'diye wani 'daci a maqoshinta cikeda damuwar abinda zata fada tace,
Saidai ayi hkr akwai wadda iyayensa keso ya aura Dan haka sun fasa zuwa saidai zuwa gaba idan ansamu fahimta.
Fada Abba yahauyi Rai a6ace yace,
Dama dai bada gskia yakeyiba Dan da bazai Raina Mana hankaliba yace zasuzo.
Hakuqi CJ yabawa abban Yana cewa,
Agodewa Allah bama Saida akazo 'daurin aure yace yafasaba.
Exactly fa ai gwara da tun yanxu akasan stand nasu""""mum ce tafada hakan tana nuna tausawarta ga ammy datayi nisa a tunani ko abinda suke fada bataji.
Zuciya ba da'di hakanan Abba da dad suka tsayar da bikin wata biyu Masu zuwa hakanan mum ta haqura badan tasoba sbd da wuri taso ayi.
Koda suka koma gida dawood bayanan Kota kansa batabiba tayita harkokinta cikin farin ciki.
Baidawo gidanba sai dare sosai kallo 'daya zakai Masa yabaka tausayi sbd kwata kwata Bai saba da wahala ba Amma yau ko ruwa baisawa cikinsaba haukacewane kawai baiyiba gurin Kiran layinta yakira yakira,yayi yawo agarin harya 6ata saidaya Kira taheer yaje yadawo gida dashi.
Ganin yanda daqyar yake bude bakinsa daya bushe yasa mum da taheer hankalinsu Fara tashi Nan tahau lallashinsa akan yasha Koda juice ne Amma yaqi.
Wasa wasa saiga zazza6i Mai qarfi ya kwantar dashi adaren Babu Wanda ya rintsa cj cikin tashin hankali yasa sukabi jirgin safe suka dawo Abuja.
Koda suka dawo babu abinda yayi sauqi gashi yahanawa kansa sukuni da daina Kiran layinta.
Da daddare Dr dayazo tasashi yayi mixing alluransa Dana bacci yayi Masa Nan take bacci yayi gaba dashi.
Dr na fita ta 'dauki wayarsa ta duba numbern datake nema ta goge tareda duk wasu massages daga gareta duk wani Abu daya danganceta saidata goge ta 'daga wayar sama ta sakota qasa tareda ficewa daga bedroom 'din.
#mamuhgee
Vote,
Comment,
Follow and share.
[1/13, 11:50 AM] El~hajj: *_DAWOOD_*
_wattpad@mamuhgee_
*22*
Washe gari qarfe takwas na dare jirginda tashigo ya sauka a Nigeria mum da kanta taje airport ta daukota
Sosai saraah ke respecting Mrs Damien ta fannin gayu da iya shiga sbd qaryane tayi dressing Bata burgeka ba gata kyakkyawa kamar ba ita ta haifi manyan zaratan samariba.
Sarah nada manyan boutiques na manyan designers acan new Jersey Amma Kuma tanason ne tazama queen of the fashion empire Amma haryanxu Bata kamo mum ba a harkar shiyasa wani fannin take jin kishinta saidai ba damar nunawa ya ta iya tunda ta haifi Wanda takeso.
Rungume juna sukayi mum na cewa,
There you are,,,welcome sweetheart.
Thank you mum"""tace tana breaking hug 'din kafin suka nufi mota sukai gida.
Lafiyayyan bedroom 'din dake cikin 'dakunan palon mum din aka sauketa saidatai wanka ta saka black jeans da red loose armless top hankalinta ya kwanta sbd Sam batason wahala tanason hutu.
Zaune suke dining sunacin abinci Kai tsaye mum tace,
Sarah dawood nason wata dabam bakeba.
Qwarewa tayi da mugun qarfi cikin sauri mum din ta miqa Mata ruwa tana cewa,
Sorry sweetheart.
Kasa wucewama ruwan sukai tsabar toshewar da maqoshinta yayi ta ture plate 'din gabanta gefe tareda zubawa mum duka idanuwanta Allah kadai yasan dauriya da haqurin datake bawa kanta da zuciyarta na hanawa kanta shararawa mum Marinda saita kifa na abinda ta fada dawood nasan wata ba itaba.
Tsananin fushi da tsantsar kishinda mum ta hango a fuskar saraah 'din yasata Jin Dadi aranta taci gaba da cewa,
Yes saraah nayi iya qoqarin ganin na rabasu na kasa saima wani sabon problem 'din ya 6ullo,
CJ yazabawa mi'amor wata matar har anyi fixing date saidai Ni ke nakeso shiyasa nakiraki kiraba dawood da waccar yarinyar nikuma na Miki alqawarin bayan aurensa da wannan da dadynsa keso zan aura muku juna.
Wani murmushin baqin ciki da takaici tasaki na yanda tazama wawuya tanacan tana bugun gaban bamai dawood sai ita ashe ananan ana Mata yankar baya.
Mrs Damien I love your son to the core extent dazan yi fiyeda abinda tunaninki zai 'dauka.,
Me kike cewa?na zauna ina kallo harsai wata ta auresa kafin Ni na auresa,,no no that is impossible..
Hakan shine bazai ta6a yiyuwaba bare yafaru dukkaninsu su biyun zan nuna musu babban kuskuren dasuka tafka nason abinda nakeso.
Murmushin qarfin Hali mum tayi ta kwantarda murya tace,
Calm your self down saraah
Dole zamu Bari bayan auren idan ya aureki saimu Kori waccan sbd idan har dawood Bai auretaba har abada cj bazai ta6a barin ya aurekiba so Dole Zaki zage dantse kema kitayani muga wannan auren ya yiyu Dan musamu cikar burinmu.
Shiru tayi tana nazarin maganar mum saidai har lokacin zuciyarta tiriri takeyi takuma kasa yarda da mum ba yaudararta takeyiba sbd she knows how cunning she is a harkar business ma bare tun da da'dewa tanada labarin mum batasonta da dawood meyasa yanxu takesonta dashi.??
Kallonta mum tayi tana yamutsa fuska cikeda baqin cikin kallon saraah 'din sbd batajin har abada zata iya Bari 'danta ya aureta sbd she will never have the respect she deserves as a mother of the man she's marrying Dan haka kawai zataci moriyar gangane ta yada korenta.
******
Kwana biyu sosai layla tadawo itake tausayin aleeyar sbd yanayin data shiga na ciwon dataga layla ta kwanta kwana biyun.
Sam aleeyar Batada walwala Wanda layla tafara zargin kamar akwai abinda ke damunta bayan damuwar ciwonta saidai batasan menene ba.
Sbd sauqaqawa aleeyar yasa ta saki jiki sosai ta nuna ta warke ba sauran abinda ke damunta duk da kuwa wani irin ciwo da damuwa takeji cikin ranta.
Zaune suke a bedroom din ammy sbd basa sakewa sosai acan sbd siyama data kasa ta tsare
dukkaninsu sunyi shiru
Dawowa tayi kusada aleeya ta zauna tareda qurawa madubin da aleeya ta qurawa Ido itama murya a sanyaye tace,
Na Dade da sawa zuciyana dangana Zaki iya cire damuwar hakanan..
Juyowa gefenta tayi ta kalleta ahankali kafin ta maida kallonta cikin madubin tace,
Kina 6oyemini ne Amma inajin ciwonki da damuwarki azuciyata,
Ina tsananin Jin zafi da haushin dr daya kawo damuwa da kuka akan fuskar danake tsananin baqin cikin Naga ko damuwa akai....
Riqo hannunta layla tayi tana kallonta ta cikin madubin idanuwanta na cikowa da hawaye,
Aleeya meyasa kike tunanin nima banajin zafin ganin wannan damuwar a fuskarki,
Na cire damuwarsa.....
Ina Miki sha'awar samun rayuwar farin ciki atareda Taheer.
Fa'duwa gabanta yayi da qarfin ta juyo da jajayen idanuwanta takalli aleeyar numfashinta na fita da sauri.
Yes layla,bazan ta6a samun kwanciyar hankali ba da sukuni ko natafi Dan nasan kinada damuwa aranki.,
Meyasa abubuwa suka Fara canzawane da wuri haka,?
Bazan takuraki ba Amma nasan taheer zai maye Miki gurbin Dr,zaisaki farin ciki sbd yasan darajarki Yana tsananin qaunarki zai soki yanda har abada bazakiyi danasanin kasancewa dashi......
Aleeyaaa""""ammy dake tsaye bakin qofa takira sunanta da 'dan qarfi sbd ganin Bata lura da halinda Laylan tashigaba,
Rawa jikinta keyi sosai idanuwanta sunyi jajir takasa 'dauke idanuwanta daga bakin aleeyar.
Da sauri ta miqe kafin ammy ta qaraso Bakin gadon ta fice da sauri tana toshe bakinta sbd kukan dakeson kubce Mata.
Qofar 'dakin ta jingina tana shesheka ahankali Dan bazata dakinsuba sbd siyama na dakin.
Cikin zafi ammy tace,
Me kike fada ne?meyasa zakiyi Mata maganar wani ayanzu bayan bakisan zafin datake ciki ba azuciyarta,
Duka duka yaushe maganar dr tabarta dazaki Fara Mata wannan maganar Dame kikeson taji???
Kallon mamaki aleeya kewa ammy jiki amatuqar sanyaye sbd ganin yanda ta 'dau zafi akan maganar.
Ammy bazan ta6a takurata ba kinsani kawai inaganin idan anbawa taheer 'din dama zai Bata farin ciki Sosai nasani sbd nasan waye taheer koba komai inaga Bai kamataba ta zauna cikin damuwar Wanda baidamu da halinda zata shigaba ya tsallake yabarta.
Ya isa haka banason sakejin maganar taheer insha Allah zansamo mafita komai zai daidaita Layla zata auri Wanda takeso...
Jin furucin ammy yasa laylar tayi saurin juyowa tana kallonta da ajajayen idanuwanta ta dawo cikin dakin
Matsowa tayi tareda share hawayenta murya na rawa zuciyarta na nauyi sbd da abinda zata fada tana kallon tace,
Banason Dr na haqura dashi nabarsa har abada,
Girgixa Kai ammy tayi tace,
Wannan zancene kike fada na harantawa kanki abinda Bai haramta agarekiba.
Idan hakane na amince da auren taheer sbd haramtawa kaina auren dawood.
Kallonta ammy tayi da sauri cikin tashin hankali sbd Bata taba tunanin abinda laylar zata fadaba kenan tace,
Kinada hankali kuwa,
Abin naki yafara yawa wannan karon bazan bariba abin yayi yawa ga Mari ga tsinka jaka.
Murmushi Mai ciwo tasaki tace tareda juyowa ta fuskanci aleeya da idanuwanta suka cicciko sbd tausayin layla tareda Dana sanin Fara maganar taheer saidai Batada za6i taheer shine Wanda takeda tabbacin zai goge damuwa da hawayen laylarta.
Share Mata hawaye Layla tayi tace,
Zan auresa ne kawai Dan Kece Kika za6arminshi,
Zan auresa ne kawai sbd nasan bazaki ta6a zabarmin cutaba Koda shi cutane agareni na yarda na auresa sbd kince kinamin sha'awar aurensa...
Rufe Mata Baki aleeya tayi tana girgixa Kai da sauri hawaye na sauko Mata tace,
Bazanso ki auri Wanda bakyasoba zamu hakura da auren gabaki 'daya sai ranarda Kika samu Wanda kikeso.
Murmushin tasaki tareda share hawayenta tace,
Hakan bazata ta6a faruwa ba.
Rungumeta aleeya tayi tareda sakin kuka ahankali.
Hawayen da ammy ke riqewane suka gangaro tayi saurin juyawa ta shige toilet sbd sun karyar Mata da zuciya tana fatar Allah yasa hakan shine mafitar wannan masifar data kunno musu Kai.
#mamuhgee
#vote
#comment.
[1/13, 11:50 AM] El~hajj: *_DAWOOD_*
_wattpad@mamuhgee_
*21*
Washe gari sai guraren qarfe goma ya tashi
Idanuwansa kawai ya bude ahankali ya sauke kan bedside clock yaga time.
Lumshe idanuwansa yayi cikin wani irin zafin zuciya da takaici sbd yagane allaurar da akai Masa kasancewarsa qwararren likita..
Tashi zaune yayi Dan Babu Wanda yakeson ya amsa Masa tambayoyinsa kamar mum sbd idan ba itaba ya tabbata Babu Wanda zaisa ayi Masa alllurar bacci yanason yasan dalilinta nayin hakan.
Zuro qafafunwansa qasa yayi sai akan wayarsa da sauri yakai hannu Yana cewa,
No no no no please..
Kaca kaca screen 'din yayi ya shafe ba'a ganin komai kamarma ta mutu gabaki 'daya.
Yanda zuciyarsa ke tafarfasa ne yasa ya aje wayar tareda nufar toilet yayo alwala yayi sallar asuba Yana qara Jin zafin allurar d sbd irin yanda yayi lattin sallar.
Yana idarwa ya miqe tareda 'daukar wayar ya nufi gurin mum.
Yana shiga ya tararda suna rigima da taheer akan yanason Layla tunda Wanda ke nemanta ya fasa itakuma tace Sam ba'a zuriarta ba 'yar tsintuwa sbd tasan 'ya 'daya Tak Abba yakeda ita.
Basusan dashiba saijin tayi ya riqo hannunta yasaka Mata wayar idanuwansa taf da hawaye sunyi jajir Yana qoqarin rage zafin rai da tsananin fushin dayazo dashi yace,
Cikakken bayani zakiyimin akan abunda yasamu wayana bayan kingama fadamin dalilinki nasawa aimin allurar bacci.
Kallonsa tayi takalli taheer dashima fuskarsa ke 'daure sosai
Itakan wane irin masiface ke Shirin rufo Mata ta hanyar 'yayanta akan mata shi dawood Nur shikuma taheer Layla.
Mai aikice ta qaraso da warm milk da mum tasa adafa Masa
Wata gigitacciyar tsawa ya daka Mata wadda tasa mum firgita tana kallonsa cikin tsananin mamakinsa tace,
Mi'amor komai nayi I did it for your own good,,I mean can't you see hw stress and....
Meyasamu wayana?
I know you broke it mum,
Why?
Why? Did you realize wat you did by doing this...idan har kinyine danki rabani da ita then you are wrong,
You are wrong mum sbd har abada bazai ta6a faruwa,
You called me your love but I don't see anything like that anan mum,
Zan Baki shawara amatsayina na 'danki,
Kibarwa Allah komai yayi ikonsa ayanda yaso sbd idan Kika matsa akan haka ina gujemiki abunda zai biyo baya sbd Zaki iya rasa 'dan ki har abada..and one more thing maganar aure banayi bazanyi ba
And i'm leaving this house now coz I can't spend another minute hia,,I feel suffocated.
Riqosa tayi niyaryi ya juya yabar gurin sbd hawayen idanuwansa zasu iya zubowa kowaneokaci.
Duk wani Abu dazai buqata ya ha'da ko wanka baiyiba ya fito har lokacin zuciyarsa zafi da ra'dadi take masa ba abinda yake son gani kamar Nur sbd ganintane kawai zai yaye Masa qunci da ciwon da zuciyarsa ke Masa.
Kallon taheer mum tayi cikin tashin hankali tace,
Honey please kaje karka barsa yatafi please don't let him leave....
Girgixa Kai yayi cikeda tausayin 'dan uwansa dashi kansa da Allah yabasu selfish mother da she can do anything to get wat she wants.
Fita yayi ya nufi gurin dawood Amma cikin rashin sa'a Bai tarardashiba ya wuce.
Gurin mum yakoma ya kalleta yace,
Yatafi and and I will follow his steps anytime soon nima zan iya tafiya idan Kika hanani samun Layla.
Juyawa yayi ya wuce yabarta da Baki sake,
Takaici da 6acin Rai taji yataso Mata Dan sunga tana lalla6asu sukeson su riqa yin abunda sukaga dama,
Zata nuna musu itace ta haifesu basune suka haifetaba.
Taheer na Isa bedroom 'dinsa yakira aleeya yafada Mata shizai auri Laylan idan tabasa dama yayi alqawarin Bata farin cikin dazata manta komai.
Bata nuna Masa amincewaba tace yabari zatai magana da laylar tukuna.
Daganan direct gurin dad yanufa yasanardashi shi yanason layla zai aureta
Mamaki sosai dad 'din yayi kafin yayi farin ciki ba 6ata lokaci ya 'daga ways yakira abban yafada Masa kusanma abban yafi dad din murna sbd koba komai 'yayansa zasuyi aure gida 'daya bazasu rabuba Nan suka yanke ha'dawa ayi tareda nasu aleeya ayi gabaki 'daya.
Hamdala taheer yayi tareda rungume dad din yayi Masa godiya tareda fada Masa zaiyi tafiya zuwa gobe zaikoma Miami akwai wani aiki daya baro Bai qarasaba.
Washe gari da taheer da dad sukai tafiya akabar mum kadai sai ma'aikatan gidan.
Tun jiya takasa sukuni mafita kawai take nema ta raba dawood da son Nur ta cusa Masa na aleeya.
Shi taheer yasha da ita sbd Batada wani za6i tunda yafadawa dad 'dinsu tasan Babu abinda zai Hana auren zata Bari daga baya tayi maganin laylar matuqar ta yarda tashigo gidanta amatsayin suruka.,
Yanxu damuwarta da rashin sukuninta na dawood ne.
Waye zai raba dawood da Nur????
Shine taketa kaida kawo tun safe tana fada.
Ajiyar zuciya tasake tareda sakin wani shu'umin murmushi tace,
SARAAH..
wayarta ta 'daga Babu 6ata lokaci takirata.
Hello Mrs Damien"""tafada cikeda mamakin ganin Kiran mum awayarta.
Hey sweetheart hw are you?
M gud mum wannan surprised call 'dinfa I hope zakice nafadawa family na zakuzo ganinsu ne.?
Dariyar qarfin Hali mum tayi tareda cewa,
Yes sweetheart shine abinda nakeso muxo muga familynki akai qarshe ayi auren Nan naki da mi'amor but I don't think that will ever happen.
Wait Mrs Damien mekike fada ne I don't get wat you're saying.
Yes sweetheart idan harkinason mi'amor for your self Dole duk abinda kike ki aje kizo Nigeria.
Mum wai are you serious?
I mean like seriously..
Yes darling kibari idan kinxo zan Miki bayani okay?
Ko amsa Bata bayarba ta datse Kiran tareda sallamar client 'dinta dake gabanta takira p.a dinta tace duk abinda yake ya aje yaje duk yanda zaiyi yayi Dole gobe ta sauka a Nigeria.
#mamuhgee
#vote
#comment.[1/16, 11:24 PM] El~hajj: *_DAWOOD_*
_wattpad@mamuhgee_
*25*
NOT EDITED
koda ya isa adamawa ko hotel 'din dazai kwana bai isaba saida yanufi gidansu aleeya,
bai wani sha wahalaba ya isa gidan saidai cikin rashin sa'a mai gadi yasanar dashi suna lagos acan sukefin zama,
dafe goshinsa yayi cikeda damuwa kafin yayiwa maigadin godia ya wuce,
hotel room yakama yayi salloli tareda ordern ruwan lipton da black coffee sbd hakanan yakejin baya iyacin abinci mai nauyi.
shiru yayi tareda qurawa ruwan lipton din ido wannan shine karo na farko dabaiyi ordern giyaba tun girmansa,
yau kuwa sam baya shaawar shanta sbd tunda yaga result din dawood yafara shanta yaji ya tsaneta sbd yasan zataiwa amininsa illa dan haka koda zai hanasa shanta saiya fara raba kansa da shanta wannan alqawarine ya dauka bazai qara shantaba insha allah,
kur6a biyu yayiwa lipton din ya ajiye sbd kwata kwata bayada apatite,
wayarsa ya 'daga yakira wanda yakeson gani yace yazo yasamesa a hotel,
cikin qanqanin lokaci wani babban saurayi ya iso yayi knocking room din yabude masa ya shigo,
cikin girmamawa yace,
dr barka da isowa nigeria,
murmushin qarfin hali maskan yasaki tareda cewa,
thank you
19, December 2024
Barirah Salihu
Thanks