Showing 36001 words to 39000 words out of 67570 words

Chapter 13 - DAWOOD COMPLETE HAUSA NOVEL

M SHAKUR   

29 Jun 2024

36756

kafin ta miqe tashiga toilet cikin sanyin jiki tayo wanka da alwala tafito tasaka doguwar riga mai 'dan nauyi sbd kaf kayan datazo dasu masu 'dan nauyine da rufe jiki kaf.

saidata tayita sauke numfashi tasamu tafito daqyar palo daidai fitowarsa daga bedroom dinsa batareda ta dagoba ta tambayesa gabas,

murmushi yasaki ahankali tareda matsowa kusada ita ya riqo hannunta,

rawa jikinta ya dauka sosai ta rintse idanu sbd kar hawayen ciki su zubo mata.

sakinta yayi yana kallonta ganin yanda jikinta ke rawa sosai,
ajiyar zuciya ya sauke tareda sake riqo hannunta har cikin dakin ya nuna mata gabas matso da fuskarsa zai mata kiss a goshi tayi saurin durqusawa tana sosa qafarta da hannunta ke rawa.

qaramin murmushi yasake tareda juyawa ya fice.

saidata share hawayen dasuka gangaro mata tasamu tayi sallolin tana gamawa ta cusa kai tsakiyar qafafunta cikin taraddadi da damuwar irin zaman dazasuyi da taheer.


ta dade sosai ahaka kafin yasake knocking yashigo 'daukeda kwalin kfc na order abinci dayayo musu ya aje mata ahankali yace,

kici abinci.

ya miqe ya fice.

coke din kawai tasha sai burger data gutsiri kadan ta ajiye sam batajin yunwar cin abinci.

kwashe kayan tayi takai fridge tadawo ta kwanta sbd zazza6i datake ji ahankali.

washe gari saida yayi mata order breakfask kafin yashirya ya fice,

baidawo gidanba sai magrib sosai baiji dadiba sbd wani aikine ya riqesa yayita bata hakuri duk da dai kamarma ya lura tafi nutsuwa idan baya kusa,

kwana biyu baicika zamaba shiyasa yayo mata shopping na komai na abinci duk lokacinda ta buqata taci sbd damashi rayuwarsa aikine kawai,

kullum kafin yafita zaiyi mata knocking yace mata zai fita hakama idan yadawo sbd sam bayason takurata,

kullum da damuwa take tashi da ita take kwana ga tausayin taheer din data faraji sbd sosai yake iya qoqarinsa na ganin ya kyautata mata bai takurataba,

duk lokacinda tayi waya da aleeya aleeyar na qoqarin danne tashin hankalinta da danuwarta ta nuna mata komai yafara sauqi tsakaninta da dawood sbd kawai ta kwantarwada laylar hankali,

tayi kuka tayi farin jin hakan shiyasa tafara sawa kanta dauriya tana dan fitowa palon gidan yanxu duk da tsananin damuwarta,

idan yadawo yanxu takan gaishesa batareda ta dago ta iya kallonsaba hakan ba qaramin dadi yakemasa ba shiyasa yanxu yake qoqarin rage ayuka yana dawowa gidan da wuri,


sannu ahankaki lokaci yafaraja sosai suna tana iya qoqarinta na danne ciwonta da damuwarta gurin fahimtarsa da kulasa duk da harlokacin doguwar magana bata ta6a shiga tsakaninsu ba saidai yana iya qoqarinsa yaga ya kyautata mata sb yagano tana girmamasa da hakan,

abu daya yasani yake kuma damunsa shine yagano har abada bazata ta6a daina son wanda takesoba,
sam arayuwarsa bai ta6a tunanin auren wadda wanine azuciyartaba.


lokacinda suka cika kusan shekara guda agarin bata iya doguwar tsayuwa sbd rashin lafiya takeyi sosai,
aman jini takeyi saidai bata ta6a bari yasaniba,
wani irin haske da rama tayi sosai,
shi kansa baya cikin kwanciyar hankali yayi ramar sosai sbd ita,
komai ya tsaya masa sbd ita baisan ya zaiyi ya kawo sauyi arayuwar auren nasuba yayi iya qoqarinsa abu ya gagara qarshe dai yagano aurensu bazai ta6a zama kamar kowane aureba,

gashi kwana biyun nan mum nayawan kiransa kullum cikin kuka take takai har kusan kwaciyarta ciwo biyu.


shiru yayi tareda qurawa takardar gabansa da biron hannunsa ido,
arayuwa yaso layla har cikin ransa yaso su shimfida rayuwar aure ta farin ciki da mutunta juna saidai hakan yakasa samuwa,

babu amfani ko wani cigaba arayuwar dasukeyi tsawon shekara guda babu mai farin ciki acikinsu,
kullum dare yanajin kuka da ciwonta baya barci kamar yanda bata barci,
aikinsa da komai nasa ya tsaya sbd damuwar rayuwar dasuke,
zuciyarta naga waninsa babu ranar dazata daina sonsa dan haka babu ranarda aurensu zai samu chance shikuma har abada bazai iya takurata ba sbd yanasonta kuma zai iya rabuwa da ita taje tasamu wanda takeso sbd yana sonta.


ahankali hawayen dasuka ciko jajayen idanuwansa suka sauko kan takardar hannunsa na rawa ya rubuta mata saki 'daya ya miqe da sauri tareda komawa bakin gado ya zauna ya tallafe kai yana qoqarin saisaita kansa.

ya jima ahaka kafin ya tashi ahankali ya fara kwashe kayansa yana jerawa cikin akwati,
saidaya kwashe komai tsaf ya dauki laptop dinsa zai saka ajakarta yaga envelope ciki ahankali yasake ajiyar zuciya sbd damuwar halinda yake ciki tasa ya manta da envelope din,

fiddosa yayi ahankali tareda 6an6arewa ya bude,

zaro takardu da hotunan ciki yayi lokaci daya hotunan suka zube da hoton aleeya yafara cin karo,

mamaki da faduwar gabane suka dirar masa lokaci daya kafin jikinsa yayi wani mugun sanyi lokacinda ya birkito sauran hotunan yaga matarsa,

hotunan yaqurawa ido kamar ranar yafara ganinsu dukkaninsu,

''''''layla nur yar uwatace rabin jikina ina tsananin kewarta sosai'''''
kalmomin aleeya na farko aranar daya fara ganin hoton layla awayarta,

LALYA-NUR,
nur din dawood itace matarsa layla,,,

watsi yayi da hotunan tareda fuxgo takardun ya bude yakaranta daki daki da address da numbers dakomai sune arubuce ba banbanci sakin takardun yayi ya zame qasa ya zauna baisan me zaiyiba sai kawai ya tallafe kai hawaye masu zafi na tsinke masa sbd har cikin ransa yakeson layla yana fatar wata rana zata iya dawowa garesa idan bata samu wanda takesoba amma ganin wannan gskiyar ya dakatar da komai,

baita6a sakaran zaiyiwa wani abu kukaba saigashi kuka yayi sosai saidai yasan farin cikin dan uwansa yadawo dan kuwa yanxu babu mai hanasa hadasu,

takardar daya rubuta mata yajawo yamayar da sakin saki biyu tareda qurawa takardar ido.

wayarsa ya daga yayi musu booking ticket ya kashe.

toilet yashiga yayo alwala yazo yayi sallar ishai kafi ya miqe ahankali ya dauki takardar ya nufi dakinta,

ahankali yayi knocking,

zaune take tsakiyar dakin tunda tayi sallah take zaune gurin ta kashe wutar dakin,

tasowa tayi asanyaye ta bude qofar ahankali,

batareda ya kalletaba ya miqa mata cikin wata irin murya maisanyi yace,

ki hada kayanki da asuba zamu wuce insha allah.

bayansa tabi da kallo akaro na farko tun rayuwarsu data qare masa kallo,

sanyi jikinta yayi sosai sbd tasan bata ta6a kyautata masa amatsayinta na matarsaba,
takawo masa damuwa arayuwarsa baijiba baiganiba,
meyasa duk wanda yasota yake shiga masifar rayuwa.


ahankali tadawo ta zauna bakin gadon dakin tafeda kunna bedside lmp ta bude takardar.

sulalewa qasa tayi tareda sakin wani irin kuka ahankali jikinta na rawa,
wace irin masifa ce wannan aure shekara guda ace ansaketa,
wace irin damuwa zata sawasu ammy da wannan sakin?


kuka tayi na fitar hankali tana zaune har asuba tamiqe daqyar sbd jiri da ciwon kai tayo alwala tayi sallah,

tana idarwa ta hada kayanta tsaf cikin akwati ko gama rufewa batayiba yayi mata knocking.

sake damqe hakardar tayi cikin hannunta tareda jawo akwatinta ta fito tareda qurawa fuskarsa ido tanason taga idan da sauran tausayin ya mayar da ita,

dauke kansa yayi tareda kar6ar akwatin yayi waje dashi,

cikin mota yasaka yayi saurin shigewa gaba kusada mai taxi din yazauna.

ahankali ta bude bayan ta zauna tareda sunkuyar dakai idanuwanta na qara rinewa,

harsuka isa airport suka shiga jirgi babu wanda ya iya cewa qala acikinsu saima qoqarin hana ha'duwar fuskoki dasuke,

tunda suka shigo jirgi hankalinta yaqara tashi kukanma tuni ya qafe mata sai idanuwa datake rarrabawa awahalce sbd sosai take agalabaice,

ana kiran magrib suka iso gida,

mum na ganin danta ta rungumesa tareda sakin wani irin kuka ahankali shikansa baqaramin dauriya yayiba gurin hana kansa kukan sbd he is really broken,

hawayensa ya mayar tareda rungume mum din yana bubbuga bayanta ahankali batareda ya iya cewa komaiba,


tunda suka ha'da ido da juna kowacce idanuwanta sukai jajir nan take,

kukan dake son zuwar mata take qoqarin dannewa sbd mugun ganin datayi,
kallon juna suke ba qyaftawa,
sunkuyar dakai aleeya tayi hawayenta suka sauko ahankali,

daqyar laylar ta iya 'daga qafafuwanta dasukai mata mugun nauyi ta qaraso gabanta ahankali tace,

aleeya,,,,,

rungumeta aleeyar tayi da sauri hawayenta na sake 6allewa,

kaka layla tasaki tareda qanqameta tanason magana takasa,

zama sukayi bakin gadon dakin mum takasa dauke idanuwanta daga aleeya,

wani irin baqi da wata muguwar ramace atattareda ita tako ina jiki da fuska sai idanuwanta dasuka futo sosai sbd rama,

riqo hannunta layla tayi da hannunta dake rawa yakasa tsayawa cikin muryar kuka tace,

aleeya meyasa kika 6oyemin damuwarki?
meyasa zaki danne damuwarki sbd tawa,
wlh nayi baqin cikin ganinki ayanda kike ayanxu,
aleeya mutafi gida mukoma gurin ammy....

wasu sabbin hawayene suka gangarowa aleeya ta sharce cikin wata irin sanyin murya mai amon ciwon datake daukedashi cikin zuciyarta tace,

arayuwata bayan iyayena dake babu abinda nakeso sama da dawood,
layla ada ina cewa zuciyata bataimun adalcin son wanda baya sonaba saidaga baya nagano qaddaratace,

wasu hawayen ta sharce tareda sunkuyar dakai tace,

rayuwar aurena daban takeda takowa,
kullum da soyayyar wata mijina ke tashi ya kwanta da ita,
kullum dare bana kwanciya sai lokacinda mijina yadawo yana fadar sunanta abakinsa,
kowane dare zai kwana yana ciwo yana kukan rashinta ina zaune ina tayasa kukan rashinta,

tun ina zaman jiran dawowarsa nakoma kowane dare nice nake zuwa 'daukosa daga mashaya,

banida hutu,banida sukuni,na rasa walwala,na rasa farin ciki,

ciwo nacinsa yaqi yarda da ayi masa magani babu abinda yake fata koyaushe fiyeda mutuwa,
ya tsanane fiyeda mutuwarda tarabasada aminansa,
ya lalace,rayuwarsa ta lalace,
yakoma babu sauran abu mai kyawun gani atare dashi,
na tsani kaina da rayuwata dana zamo sanadiyar shigarmu awannan halin nidashi,

layla ina cikin mummunan quncinda nake ha'diyesa nikadai kullum tsawon shekara 'daya....

kukane maicin rai ya sarqeta ta zame qasa tareda cusa kai tsakiyar qafafuwanta tanayi sbd ta jima tanason yazo amma ya daina zuwa sbd masifa sai yanzu,


jajir idanuwanta suka sakeyi kukan take tsananin buqata amma takasa samu,

damqe takardar hannunta tasakeyi jikinta na tsananta rawa,
shiru sukayi dukkaninsu tsawon lokaci aleeyar na kuka kafin ta dago takalli laylar taga itama duk ta zabge sai qashi ahankali ta bude baki zatai magana layla tayi saurin miqewa tana qoqarin mayarda kukanta tana sake damqe takardar sakinta ahannunta.


tasowa aleeyar tayi riqota taga yanda take jan numfashi,
zaunar da ita tayi bakin gadon tana qoqarin tambayarta saiga mum tashigo,

sunkuyar dakai layla tayi tareda gaidata asanyaye ta amsa tareda qura musu ido dukkaninsu taga yanda suke gasar rama da da qashi ta juya da sauri ta fice tana dafe qirji duk da dai danta yafi bata tausayi.


duk yanda taso fadawa aleeya maganar sakinta kasawa tayi sbd fargaba da gudun qara mata wata damuwar,

da daddare tana zaune qasa jikin gado ta dunqule shiru idanuwanta har lokacin jajir suke,

turo qofar dakin yayi ahankali yashigo da sallama sbd dama yanada tabbacin batayi bacci ba,

dagowa tayi tai masa kallo daya tareda mayarda kanta ta sunkuyar damuwarta na qaruwa,



saraah acikin daren ta fito dakinta da juice dinda tahada da gubar dazata bawa mum acikin daren sbd korar karen datayi mata bayan tagama gaya mata har abada bazata bari danta ya auretaba,

girgiza glass cup din tayi cikin qunar zuciya,
idanuwanta har wani jiri jiri take gani dasu tsabar buguwa sbd giya tasa tayi tatul sbd baqin ciki da takaicin mum,
idanuwanta arufe suke data aikata koma meyene akan mum din,
fitowa tayi ta nufi dakin mum din sbd batasan su layla sun dawoba,

cak ta tsaya qofar dakin jin abinda taheer kefada,


layla nasoki tun kafin naganki,
naso mu shimfida kyakkywar rayuwa mai dorewa,
hakan bazata ta6a samuwaba sbd akwai soyayyar 'dan uwana aranki,

dagowa tayi da sauri ta kallesa da jajayen idanuwanta yace,

na sakeki ne tunkafin nasan da soyayyarki da danuwana sbd aurenmu baxaita6a samun chance ba,
rayuwar aurece da babu soyayya,shaquwa da qauna acikinsa,
kiyi hkr sbd koda babu so acikin auren yanada zafi saki agurin kowace mace saaidai inason kibani dama na gyara muku abubuwan dasuka lalace.

sai alokacin hawaye suka gangaro mata sunkuyar dakai sbd batajin akwai gyara a alamarinsu.
#mamuhgee._*DAWOOD*_
_wattpad@mamuhgee_




*30*
NOT EDITED




girgixa kanta tayi tareda bubbugasa da hannu tana sake bude idanuwanta dasukai jajir tana qoqarin son qara fahimtar me taheer din yake fada,

kasa jurewa sauran zancen nasa tayi tai wurgi da cup din hannunta cikin bugaggiyar murya tace,

bazaka ta6a rabani da dawood ba kabawa wata,
dawood nawane nikadai,
nikadaice zan auresa,
babu wanda ya isa yarabani dashi...

kicin tayi lalabo wuqa ta fito tana cigaba da cewa,

dawood nawane nikadai,,,

tana kawowa qofar dakin yana fitowa bata tsaya komaiba ta caka masa wuqar,

qara da salati mai qarfi yasake lokaci daya tareda zubewa qofar dakin tana ganin haka tayi dakinta da gudu daidai fitowar mum da gudu cikin tashin hankali kuma taga shigewarta 'daki da gudun amma batabi kantaba tayi tsakiyar palon inda tajiyo qarar taheer,

arikice layla ta taso tareda durqusawa gabansa tana kiran sunansa batasan sanda tasa hannu ta birkitosaba wani razannan ihu tasaki ganin wuqa da a gefen cikinsa bata tsaya komaiba ta zare wuqar daidai isowar mum gurin tareda kunnu wutar palon taganta da wuqa ahannu ga taheer din kwance cikin jini,

wani mahaukacin ihu da qara tasaki tareda jefar da wayar hannunta ta qaraso da gudu hartana faduwa ta damqosa tana kiran sunansa da qarfi cikin tashin hankali,

kuka layla keyi sosai nan su Nana da sauran masu aikin gidan suka fito arikice dan harsunyi nisa a bacci tuni,

cikin tashin hankali nana takirawo aleeya tana zuwa da gudu ta tsaya turus ganin abinda ke faruwa arkice ta matso cikin tashin hankali tace,

mum muje hospital tun kafin wani abu yasamesa.

kuka mum keyi sosai saidai aleeyarce tafita da gudu takirawo maigadi suka shigo shima arude ya daukar musu shi yasaka amota,

jiki na rawa takalli mum tace,

mum muje.

da sauri mum din ta miqe hartana hadawa da gudu suka wuce da mugun gudu dan har lokacin kamar yana numfashi,
tun ahanya takira dad tana kuka tasanar dashi masifar data samu taheer nan take ya katse kiran yace komai tsakar dare zai taso asuba ya iso sbd yana ghana.


kasa miqewa layla tayi saida Nana ta dagata daqyar sbd rawar da jikinta keyi matuqa ga kukan tashin hankali datakeyi.


suna isa asibiti daqyar aka kar6esa da sharadin saisun kawo police sbd police case ne,

share hawaye mum tayi cikin wani irin zafi da 6acin rai mai tsanani tacewa aleeya tazauna ita zataje takira police,

daga asibiti direct office na commisioner of police ta nufa nan take aka bada motar police.


saraah kuwa tana shigewa daki jikinta yafara rawa dan tuni giyar tasaketa tsabar tashin hankali ta dora hannu akai tace,

na shiga uku menayi,
yanxu shikenan mum taganni na kashesa nima kasheni zaayi wayyo allah na shiga uku,

birkice kayanta tayi ahaukace tafara neman passport dinta acikin daren zata gudu bazata bari akamata ba,

wayarta ta dauko hannuwanta na tsananin rawa ko zama wayar batayi dakyau ahannunta ta danna kiran siyama tana tsiyayo hawaye,

siyama na dauka ta fashe da kuka tace,

siyama ina cikin matsala wlh kasheni zaayi bansan ya zanyiba,
bansan meyasa nakasa riqe kainaba na kashesa,
siyama kitaimakeni na kashe taheer....

tashi zaune siyama tayi daga kwancen datake tareda saukowa daga gado tace,

me kike cewa?

wlh siyama bana cikin nutsuwata ba kashesa nayi niyaba,,,fada mata komai tayi cikin tsananin kukan tsoro saijintayi siyama ta kashe mata waya.

sake kira tayi siyama taqi dauka sai kawai ta zube wasa tareda fasa sabon kuka tareda harhada sauran kayanta ta zuba jaka ta fito da sauri cikin tashin hankali sai kawai taji jiniyar motar police cikin harabar gidan,

daki takoma da gudu tana sakin fitsari cikin wandonta wani irin gumi yafara jiqota tako ina,

suna shigowa palon cikin zafin muryan mum ta nuna layla dake zaune palo cikin rashin sukuni tayi kuka har baya fita tace,

inspecter gatanan itace ta cakesa da wuqa sbd batasonsa takeson kashemin 'da.

arazane layla da nana suka dago takalli mum da jajayen idanuwanta dasuka qanqance sbd kuka cikin rawar murya tace,

bansan wayayi ba ahaka nasamesa wlh bazan ta6a cutatar da taheer ba mum.

hawaye mum din ta sharce tana kallon inspecter tace,

itace sbd kowa yaganta agabansa da wuqa ahannunta,,,,

mum wlh bani bace,banyi masa komaiba mum ina qoqarin cire masa ne.....

matsowa yayi da ankwarsa tareda daka mata tsawa yana cewa asa mata ankwa sutafi da ita idan taci azaba tayi bayani dakyau.


sarah dake la6e tayi saurin barin qofar takoma tsakiyar dakin tana jin dadin samun hanyar tserewa duk da dai harlokacin hankalinta amatuqar tashe yake tasake danna kiran siyama,


siyama na kashe wayar tarasa ina zatasa kanta sbd tashin hankali da baqin cikin saraah,
tabbas ta ta6ota a inda ba'a ta6awa,
wlh saita kasheta itama matuwar taheer dinta ya mutu kuma wlh saita hanata samun abinda takeso aduniyarnan komenene,

shigowar wani kiran yasa ta dauka amatuqar fasace kafin tayi magana saraah tarigata da cewa,

siyama nasamu mum tacewa police layla ce dan haka dasun tafi zan fito kiyi sauri ki kiramun su seeya kice sujirani a airport komai dare ko asubanci zan sauka a airport na lagos yanxu zan fito....

katse kiran siyama tayi hawaye na tsiyayo mata tace,

wlh kinyi bankwana da kwanciyar hankali tunda kika rabani da taheer har abada bazaki ta6a samun dawood ba wannan alqawarina saina lalata rayuwarki saraah yanda ko kare bazai kallekiba.

wayarta ta 'daga kai tsaye ta nemo number dawood ta danna masa kira,

kira take bai dauka takasa dainawa jikinta har rawa yakeyi zuciyarta kamar zata fado ga hawaye sun kasa tsaya mata babu abinda takeson gani kamar taheer dinta,

sake kira tayi cikin maye ya 'dauka ahasale yace,

you fool bakusan inkun kira baa daukaba ku saurara idiots...kashewa zaiyi tayi saurin cewa,

NUR CE.

kwalbar hannunsa ya saki ta watse tareda miqewa tsaye nan take yaji giyar tasakesa cikin wata irin sanyayar murya yace,

NUR?

daidaita muryarta tayi cikin dakewa tace,

Nur 'dinka na gidanku ayanxu haka police zasu tafi da ita kaje karka bari sutafi da ita daga baya zankira namaka bayani kayi sauri kaje...


bai tsaya tunanin komaiba ya ture wanda ke gabansa yabar gurin da gudu isanuwansa har wani cikowa da hawaye suke dan tsabar farin cikin dabaita6a sanin akwaishiba.

wani irin mugun gudu yake yana tsiyayo wasu irin hawayen farin ciki zuciyarsa har wani bugawa takeyi da qarfi kamar zata faso qirginsa.

da wani irin mugun gudu da horn yashigo kwanar layin gidan daida lokacinta police biyu suka fito da ita daga gidan nana na biyedasu tana kuka kamar ranta zai fita,

kasa gasgata idanuwansa yayi sai kawai yayi cikinsu aguje da motar yayiwa motarsu wani mugun bugu nan take tafara hayaqi da gudu ya fito ya damqota ya cilla cikin motarsa yayi ribas yabar layin da mugun gudu babban inspectern da mum aguje suka fito cikin tashin hankalin jin qarar bindiga suka tararda tuni motar dawood din tabar layin,

da gudu suka shiga motarsu suka rufa masa baya.

sabon tashin hankali da baqin cikine tasowa mum tadawo cikin gida daidai leqowar sarah tana hada gumi,

kallonta mum tayi dakyau nan take wani zargi yafado mata gabanta yayi mummunan faduwa ta hadiye wani mugun miyau ta nufota tareda bude qofar dakin taga akwatinta da passport tayi saurin kallonta murya na rawa tace,

saraah kece kika kashesa.....

kuka tasake da sauri ta matso tana cewa,

wlh bansan lokacinda na.....

wani mahaukacin mari mum tasakar mata saidata kife ta nunata da yatsa

19, December 2024
Barirah Salihu

Thanks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login