Showing 18001 words to 21000 words out of 67570 words

Chapter 7 - DAWOOD COMPLETE HAUSA NOVEL

M SHAKUR   

29 Jun 2024

36737

'din ya lura saidai ya dauke Kai yaci gaba da wayarsa duk da yadaina fahimtar mesu sufyaan'din suke fada wayar kawai yake.


Nanace data ki tsayuwar motarta Jin Bata shigoba ta fito sbd 'yan kwanakin dasukai sunyi sabo sosai da Layla sbd yanda take janta ajiki ba ruwanta da zamowarta Yar aiki duk da dai ko ammy Bata wulaqantata.
#mamuhgee







VOTE
COMMENT.
[1/13, 11:32 AM] El~hajj: *_DAWOOD_*
_wattpad@mamuhgee_




*14*
Ganin halinda take ciki yasa Hankalin Nanar tashi da gudu takira ammi tana hawaye arikice ammyn ta fito sbd Nanar akwai qara zuzuta Abu.

Hankalinta yatashi itama ganin halinda laylar ke ciki a rikice suke qoqarin kamota sun rasa yazasuyi su fiddota motar sai kuka Nana takeyi duk ta qara ruda ammyn.

Datse wayar yayi Yana rintse ido Dan baimasan meyakeyiba hankalinsa ya 'dauku matuqa.

Shigewa yayi palonsa Amma yakasa zama yasaki qaramin tsaki tareda fitowa.

Jikin motar ya qarasa tareda cewa ammy lemme help.

Matsawa tayi yafara kashe motar ya zura hannu biyu ya fito musu da ita Jin yanda temperature dinta yahau sosai yasa kansa 'dan sarawa da niyar yabasu ita su qarasa da ita Amma sai kawai ya wuce cikin gidan da ita suka bisa da sauri.

A Palo ya kwantarda ita tareda kallon ammyn yafada Mata abubuwan dazatai Mata cikin gaggawa temperature din yadawo daidai.

Da sauri ammy tayi kicin shikuwa takarda da biron daya gani palon ya dauka ya rubuta musu allurori ya miqawa Nana ya ficewarsa sbd zan iya yiwa ammy tsawa sbd ganin kamar Bata sauri taje kicin tayi zamanta..

Kodaya koma flat dinsa direct shower yasakarwa kansa bayan ya tube sbd he's feeling suffocated...

Yana fitowa Kiran jass nashigowa wayarsa yaqi ko kallon wayar ya shirya cikin threequarter fari black da black shirt Mai 'dan kauri sbd sanyin dayakeji kamar fever nasan kamasa.

Sake Kira sukayi ya 'dauka batareda yace komaiba.

Cikin kulawa sufyaan yace,

Man are you alright kuwa coz kwana biyun Nan nidai nakasa gane maka.

Ajiyar zuciya yasaki ahankali Yana sipping coffee din hannunsa akasalance yace,

I don't know man...

Ajiyar zuciya Shima sufyaan din ya sauke sbd yanajiyo damuwa a muryar abokinsa cikin sanyin murya yace,

Saraah nanan tayi parking she's planning on coming to see you..

Qaramin tsaki ya fitar akasalance kafin yace,

Please don't talk about her now..

Cikin mamaki yace,

Amma kaika Fara cewa zakace tazo you were missing her you need her around you.

Sufyaan bansaniba Amma banason ko maganarta yanxu.


Da haka suka kashe wayar su suna mamakinsa shikuma aje coffee dinma yayi Dan jiyayi komaima yafita ransa.

Da daddare ammy ta Aiko Nana kiransa daqyar ya bude bayan tayita danna doorbell yanaji yayi banza saidayaga ba qyalesa za'aiba ya taso ya bude tareda zubawa Nana manyan lazy eyes dinsa.

Saidata rikice kafin cikin rawar murya sbd batasan yazata hada Masa da turanciba yagane tace,

Ammy tace kayi help kayi come,,,,,tana fada tana kwatanta Masa da hannu.


Wani kallo ya watsa Mata fuska a 'daure da sauri ta juya tabar gurin.

Saudaya ba6a lokaci kafin yafito ya nufi flat din fuskarsa kamar koyaushe ba sakewa.

Doorbell ya danna so daya ya maida hannunsa aljihun wandonsa Yana gyara tsayuwa.

Ammynce da kanta ta bude tana ganinsa tace yashigo.

A natse yashigo idanuwansa akanta tana zaune ammy ta 'dauko Mata hijab tasaka idanuwanta a lumshe sbd qarfin jikinta dabai dawoba.

Alluran daya rubata tabawa nana tasiyo ta nuna Masa tana cewa,

You wrt these so gasunan ansiyo.

Karbaa yayi ya duba ya aje cikin gatse yace,
Ok sai asamo nurse or Dr dazai Mata.

Kallon Nana ammy tayi tace,

Jiki flat na gaba ki Kira nurse dinda Kika kar6o alluran gurinsa.

Jin kalmar ammyn ta qarshe data bayyana jinsin namiji yasashi kasa tashi ya saukewa Layla data kasa ko qwaqwaran motsi Jin idanuwansa dake yawo akanta.

Da sallama kamilallen saurayin yashigo fuska asake ya gaida ammy ta amsa tana cewa,

Sorry Ahmed Dan Allah Alluran zakai Mata.

Bakomai yace Yana matsowa.

Wani mugun kallo dawood yasakar Masa Yana Masa wani irin kallan wulaqanci da kowa yakasa ganewa ahankali yasaki alluran suka zube qasa tareda fashewa gabaki 'daya.

Kallonsa Ahmed yayi sbd Sarai yaura da gangan yayi Amma baisan dalilinsaba.

Cikin jimami ammy takalli alluran tace,

Subhanallah.

Aa kwantarda ita akwai wasu agida Bari zankawo.

Idanuwansa akan Layla cikeda qarfin Hali yace,

No need for that abarsu let her get some rest zuwa gobe she'll be ok insha Allah.

Allah yasa''''kawai Ahmed yace yafice sbd zuciyarsa a wuya take tun farko da kallon rainin wayo da wulaqancin da dawood din ke Masa.

Ammy kuwa sai alokacin taso ta lurada abinda ke faruwa sbd tunda yashigo lazy eyes dinsa nakanta bayako kawo kunya ko Jin nauyinta akan hakan amma shi agurinsa baima saka wata damuwa ko aibi gayin hakanba sbd su acan basusan wata kunyabama gabaki 'daya.

Ahankali tabar palon tayi kicin gurin Nana tana sakin murmushi ganin Sam shi baruwansa kallonta yake kamar zai cinyeta agaban uwarta.

Indomien da tun dazu ake dafawa laylar ammyn ta juye a plate tareda 'dorowa a qaramin tray Nana takawo Bata tsayaba ta juya itama.

Kallon indomien yayi Yana yamutsa fuska tareda sakin qaramin tsaki Yana tunanin yaxa'ai taci indomie yanxu tea Yakamata Tasha.

Miqewa Yayi yabar palon yatafiyarsa gida Yana cewa,

Ths people are unbelievable...

Yana fita ta bude idanuwanta ahankali tabi inda yafice da kallo tareda sakin ajiyar zuciya.


Washe gari ba laifi taji sauqi sosai Dan har fita sukayi tareda ammy da Nana suka zagayo gari Dan taqara warwarewa.

Da suka dawone suka tarar dashi a balcony dinsa Yana sipping coffee hannunsa 'daya cikin aljihun wandonsa.

A natse ya matso ya gaida ammy Yana kallon Layla data sunkuyar dakai yace,

Hw are you feeling today.

Gud...tace ahankali tana wasa da sarqar hannunta.

Su ammy wucewa sukayi ya gyara tsayuwarsa still coffee dinsa na hannunsa tareda qara zube Mata idanuwansa duk saitaji jikinta na qara sanyi.

Cup din ya miqa Mata Yana cewa,

Want some coffee???

Girgixa kai tayi tana son 'dagowa ta kallesa Amma takasa sbd idanuwansa.

Baida niyar Bari ta tafi saima gyara tsayuwa da yayi jikin motarta Yana cewa,

Kunje yawo ne?

Kasa hkr tayi ta dago ta kallesa tareda sakin murmushin qarfin Hali tace,

Eh.

Murmushi Shima yayi harsaida kumatunsa suka lotsa yace,

Ok nima inason zanje yawo but banida abin Hawa so wll you mind taking me out tomorrow.

Bakada friends ne Dole sainice zan riqa fita dakai.

Su6uce Masa qaramar dariya tayi for the first time datayi Masa doguwar magana yace,

I have the best friends in the world amma the're not hia but you'll know them soon Dan haka bye see you and don't forget you're taking out tomorrow.

Murmushi tasaki tareda girgixa Kai ta wuce tana cewa,

Silly.



Tana shigowa ammy takalli fuskarta cikin ganin yanda murmushinta yakasa gushewa ne yasata sakin murmushi tace,

Finally one of my daughters is inlove.

Zaro Ido tayi tareda wucewa bedroom da sauri tana cewa,

Ammy gaisawafa kawai mukayi.

Tana shiga 'daki takira aleeya Amma Bata sametaba ta jefar da wayar tana cewa,
Ths stupid Network yaqi Bari muna magana da juna yanda mukeso.

Zamewa tayi ta kwanta ahankali kan gadon tana tuno guntuwar firarsu.



Washe gari taje school taqarasa musu komai da wuri tadawo tayi baccin mintuna ashirin sbd fuskarta ta'dan sake daga 'yar ranar data shawo a school.

Tana tashi tayi wanka tana fitowa ammy tashigo 'dakin cikin fara'a tace,

My son in-law yazo Amma nasashi cin abinci Dole so take your time and dress properly.

Murmushi kawai tayi tazauna tayi shafa ta shirya cikin loose gown black Mai adon maroon sequence.,

Wayarta kawai ta 'dauka sai car keys ta fito palon qamshin turarenta na AMBER ELIXIR dake tashi ahankali.

Samosas din da ammy tabasa yaci guda daya tareda goge bakinsa da tissue ya miqe Yana kallonta itama shitake kallo cikin ranta tana mamakin haske da lafiyar fatarsa dake glowing kamar mace.

A natse take driving yace takaisa malls malls na garin yagani.

Dayake itama ba sosai tasan garinba haka dai sukaita yawo suna gurin wani coffee shop su jass suka kirasa lokacinda ya miqa Mata waya yace ta gaisa da friends dinsa mamaki kashesu maska yayi lokacinda suka ganta sbd video call.

Sosai tasake suka gaisa tana murmushi Nan sukaso Fara yimasa tambayoyi yayi saurin datse Kiran Yana kallonta fuskarsa daukeda murmushi.

Ana Kiran magrib suka dawo zuwa lokacin tafara sakewa dashi.

Tarkacen siyayyar dasukai ta aje a Palo ta wuce daki tayo alwala tazo dakin ammy tayi sallah hankalinta kwance cikin farin ciki.
#mamuhgee








VOTE
COMMENT.
[1/13, 11:32 AM] El~hajj: *_DAWOOD_*
_wattpad@mamuhgee_




*15*
Ranar ammy taso yazo Nan yaci abinci Taredasu Amma Layla tace aa sbd ganin ammyn sai 'doki takeyi.

Washe gari Dole ta qyale ammyn tasa Nana takirasa ya Dade kafin yazo tace yaci abinci dasu Bai musaba sukayi lunch tare duk ya hanata sukuni da shegen kallonsa ammy madai badan ta qoshiba ta miqe sbd shiyake kallon itakejin kunya.


Suna gamawa Bai tafiba suka zauna Palo su sufyaan suka Kira Yana dauka suka gano a inda yake sukace yabawa Laylan.

Kar6a tayi Cikeda wayewa da Raha suka gaisa da ita dukkaninsu kafin suka kashe.

Kallonsa tayi tana murmushi tace,

Your friends are nice.

Nafada Miki I have the best friends in the world.

Nima nafada maka I have the sweetest,the nice's friend and also a sister in the world.

Dariya sukayi dukkaninsu ahankali kafin ya miqe ya tafi.

Wani irin feelings sukeji Mai qarfi gameda junansu sbd sabo da shaquwar dayashiga tsakanisu cikin kwanakin ga uwa uba ammy data 'daure Masa ta hanyar koya Masa cin dishes kala kala wasu baima iya cinsuba haka zasu zauna ana koya Masa cinsu sometimes idan yanaci saiya kirasu sufyaan Yana nuna musu sunai Masa dariya sbd su San 'dan San wasu abubuwan sun Saba cinsu a gida.


Ta 6angarenta kuwa bata fadawa aleeya ba tabarshi as a surprise to her duk Randa suka dawo duk da dai yanada wuya su ha'du sbd yakusa kammala abunda yakawosa yakoma.

Wani irin so yake Mata dabaisan kalarsaba Dan kuwa jiyake there's no way dazai iya rayuwa babuta,
Sanyinta,da yanayin rashin son hayaniyarta kamarsa yasa baya iya sukuni Sam yanzu batareda yakirata ba takaima yafara zama kamar wani chewing gum 'dinta Dan kusan yawancin kwanaki tare suke zuwa school.

Aduk lokacinda ko sunansa ta tuno sai murmushi da farin ciki sun sauka a zuciyarta musamman takejinsa wani babban 6angare na jikinta dabazata iya rayuwa Babu ba.

Yini sukeyi agida tare idan zata fita ya dinga binta da kallo kenan kamar Mara lafiya baida sukuni ko walwala saita dawo.

Ita Kam ammy ba abinda yafi Mata haka da'di yanzu aleeya kawai tarage itama kullum saita Mata adduar Allah yakawo Mata nata Dan tuni ta sanarwa abban Layla tasamu miji farin ciki sosai yayi saidai baitambayi komai akansaba yace abari saiya dawo Dan next week zasu dawo.

Da daddare daqyar tasamu yabarta ta waya sbd Dan yanda ya narke mata sosai ita har mamakinsa take sbd da gani mum dinsa ta 6atasa da gata kamar yaro ga yanda ya iya narke Mata akan saitayi masa firar soyayya yaji Dadi shi bai iyaba shi tasa kalar soyayyar ta Ido ce Dan kuwa idan ya zuba Matasu wani lokacin ko motsi Bata iyayi Kuma ba ruwansa da duk Wanda ke guri zuba Matasu yake ga idanuwan badai kashe jiki da rikita mutum ba.

Daqyar tasamu ya haqura ta kashe wayar tareda danna Kiran aleeya.

Cikin sa'a tashiga.

Tana dauka kusan atare suka saki ajiyar zuciya kowanne bakinsa da magana.

Cikin farin ciki aleeya tace,

Oh my...my layla I missed you so much na matsu nadawo I have alot to tell wlh.

Murmushi Mai sauti tayi tana cewa,

Dagajin muryarki kina cikin farin ciki is there anything I shud know.

Dariyar Jin Dadi tayi tareda gyara kwanciyarta a gadon bedroom 'din mum data dawo da kwana Nan sbd kawai hotonsa dake 'dakin ta shafi hoton tana lumshe Ido tace,

Inasonsa Layla,,,,
Ina tsananin sonsa infact ban ta6a son wani da tsanani hakaba kamarsa....

Lumshe idanu Layla tayi sbd fuskar dawood 'dinta data Fado Mata a Ido.

Cikeda Taya 'yar uwarta murna tace,

And waye wannan dayakeson birkita zuciyar aleeyana.

Mi'amor..... layla zuciyata takamu da tsananin sonsa dahar nakejin kamar bazan iya rayuwaba idan na rasashi,
Wani lokacin Kuma jikina na sanyi idan nayi tunanin qila bazai Soni ba Wanda wlh Layla bazan iya cirewa zuciyata sonshiba....ta qarasa zancen muryarta na karyewa.


Sanyi itama laylar jikinta yayi cikin sanyi tace,

Bazaki ta6a rashiba insha Allah Zaki samesa sbd kome yakeji dashi nasan kema kin Kai duk inda cikakkiyar mace Mai aji da gata takai.

No Layla Baki sanshiba,,I'm nothing compares to gata,kudi,ilimi,class,kyau da wayewar dayake dasu kawai kimin addua Allah yabani shi ina sonsa Layla.

Ganin halinda aleeyar tashiga yasa tafasa fa'da Mata maganar dawood datai niya saitayita rarrashinta da Bata qwarin gwiwa.

Tunowa datayi laylar nada abun fada Mata yasa ta saki muryarta ta nuna ba damuwa tace,

Ehemm inajin naki bayanin sbd daga yanayin murmushinki 'dazu I sense sumthing fishy.

Qoqarin buge zancen tayi da cewa,

It's nothing kawai....

No no no karmu Fara haka kawai ki fadamin inason naji Are we inlove?"""ta tambaya tana dariya.


Rintse idanu laylar tayi da sauri kamar aleeyar na tareda ita cikin sanyi tace,


He is very nice and kind.

Wat??? Malamin makaranta ne hala?

Bude Ido tayi tace,

Aa.

To ina nakejin he is nice and kind inason naji kince he is very hot and cute.

Dariya suka sake dukkansu layla tace,

Idan akan hot ne zan ce Miki he is not hot but fire gaba 'daya.

Ihun murna aleeya tasaki tana cewa,

Wayyo na matsu nadawo mu ha'du Amma kafin Nan inason gaisawa dashi gobe.

Ok ok insha Allah.

Shiru aleeya tayi cikin sanyi tace,

Layla kinasonsa sosai ko?

Lumshe idanu tayi cikin sanyin murya itama tace,

Banta6a tunanin arayuwata zanso namiji hakaba aleeya,
Da farko naso na yaqi zuciyta akan sonsa duk da bansa daliliba Amma bansamu kuzarin yin hakanba,
Sonsa yariga yazamo wani babban 6angare ajikina.

Jin zancen nason sasu wani yanayin mutuwar jiki yasa aleeya tace,

Hmmnn harna Fara Jin kishinsa zai ragemin fili azuciyarki.

Fa'duwa gabanta yayi da qarfi Jin maganar aleeyar duk da acikin wasa tayita.

Ahankali tace,

Aleeya har abada Babu Wanda zai ta6a babban matsayin dakike dashi azuciyata,
Matsayinki a zuciyata yafi qarfin duk wani matsayi da kike tunanin kinadashi agurina,
Karki hada kanki dashi sbd shi zuciyata yakama ke kuwa jini da ruhi.

Hakan na nufin Bazaki iya rayuwa Babu zuciyaba da jini da ruhi.

Murmushi tayi kawai suka kashe wayoyinsu kowanne jiki ba qwari.


Ana saura kwana uku su aleeya su dawo yasamu Kiran gaggawa daga new Jersey Nan hankalinsa yayi matuqar tashi Dan Kai tsaye yace ba yanxu zai dawoba ganin da gaske yake yasa maska Kiran Layla ya fahimtar da ita Dole ana buqatar dawood din gashi yace bazaizo ba and sunfi kowa sanin idan yace NO Babu Wanda ya Isa ya canzasa ko waye.

Damuwa da fargaba Mai qarfice tashigeta lokacinda maska yayi Mata bayani Dan dawood din baifada mataba.

Acikin dare kasa daurewa tayi sbd fargaba kafin safe idanuwanta sun kumbura bawai Dan kukaba sai Dan rashin barci da tunanin daya sakar Mata ciwon kai.

Yana sauke idanuwa akanta yaji hankalinsa yayi mummunan tashi coffee ma da ammy tabasa kasa Sha yayi ya aje Yana zuba Mata ido alamar son sanin abinda ke damunta.

Zama tayi tareda kallonsa duk saitaji taqara rikicewa.

Miqewa Yayi yatsaya akanta tareda sake tsareta da Ido.

Kasa daurewa tayi ta dago ta kallesa cikin sanyi tace,

Maska yakirani.

Sai alokacin ya lumshe Ido Amma cikin 'dan 6acin Rai da takaicin maskan daya fada mata. Maganar komawarsa.

Zama yayi tareda sakin ajiyar zuciya idanuwansa akanta cikin maqoshi yace,

Ba yanzu zan tafiba saisu mum sun dawo next month inason suzo gurinsu ammy sai abani ke dake nakeson komawa.

Kallonsa tayi idanuwanta na qara ka'dawa tace,

Zaka iya komawa kafin next month din saika dawo maska yace your career is at stake idan baka komaba so please kaje if not for your self me.

Girgixa Mata Kai yayi Yana tamke fuska.

Rikice Masa tayi sosai saidata ha'da da hwaye Yana ganin hawayenta jikinsa yadauki tsananin rawa baitaba shiga tashin hankali ba arayuwarsa kamar yau dayaga hawayenta danji yayi kamar qwaqwalwarsa zata buga..
Da gudu ya amince akan zaije dagacan zai wuce Miami gurinsu mum saisu dawo tare.

Jinya yadawo yi sbd zazza6in daya rufeta daga ranar.

Cikin qanqanin lokaci tayi wani iri musamman rama ta rashin cin isashen abinci.

Ammy har tausaya musu take itama duk saita shiga damuwa ganin yanda duk ta 'daga Hankalinta shikuma suk ya susuce yakasa nutsuwa Dan Shima ramar yayi sosai sbd Sam hutu ya qaurace Masa ko agurin bacci wani lokacin har qarfe goma Sha 'daya Yana gidan Yana kwantar Mata da hankali duk da Shima kullum saisu jass sun kwanatar masa yake samun qarfin gwiwa.


Ana gobe zai tafi ranar ko Nana saidatayi hawayen tausayin Layla sbd kwana tayi da wani irin mugun zazza6i Amma da safe Yana Ganinta yaso rikice musu Dole ta daure tabawa kanta qwarin gwiwa daqyar ya yarda takaisa airport bayan yabawa ammy da Nana kyautar maqudan kudi Masu.

Suna Isa aka kira jirginsa
Riqe hannunta yayi yanason yayi magana yakasa sai kawai yakai hannun bakinsa yayi kissing ya fito da sauri ya wuce Dan zai iya fasawa kowane lokaci.

Yana fita ta kwantarda kanta kan sitarin mota hawaye Masu zafi suka gangaro mata kafin taja motar daqyar tabar airport din.
#mamuhgee







VOTE
COMMENT.
[1/13, 11:36 AM] El~hajj: *_DAWOOD_*
_wattpad@mamuhgee_




*16*
*_All thanks to Allah gameda qauna da masoya ke nunamin nida rubutuna,_*
*_Gskia bansan dawood yasamu kar6uwa da wuri hakaba sai yanxu so thank you all for the love.....mamuh loves you more._*




*_This page goes to members na zauren biebie Isa,,,Layla Nur and aleeya na godia..._*






Tana dawowa daga airport ta kwanta Nan danan zazza6i Mai qarfi ya sake kwantada ita kuka takeso tayi kota samu sauqin abunda takeso a qirji da zuciyarta Amma yaqi zuwa saima wani irin yaji da idanuwanta ke Mata na Jan dasukai.

Hankalin ammy tashi yayi sosai nan tafara rarrashinta tana Bata Baki sbd kobata fadaba tasan ciwon na rafiyar dawood ne.

Ita gabaki 'daya ma alamarin tsoro yafara Bata wannan wace irin soyayya ce tun ba'aje koinaba tafada cikin ranta cikeda tausayin laylar.

Cikin kwana biyu ta canxa sosai duk da tana qoqarin ganin ta sake sbd kullum sai sun raba dare suna waya hardar yanxu dabasa kusa narke Mata yake kamar zaiyi kuka itama wani lokacin da hawaye suke rabuwa ta wayar gashi tunda yaje suka daina video call sbd yace akwai wadda bayaso taganta Koda mistake ne datace waye Bai Mata qarya ba yace Mata ex-girlfriend dinsa sbd hakan na 'daya daga cikin qualities dinsa shi baya qarya baya 6oyo.

Ranar daya fada Mata Saida yabawasu maska tausayi sbd shiru tayi taqi magana jiki na rawa yakashe ya danna Mata video call
Hawaye yagani fuskarta suna tsiyaya Nan yahau kawo zance kala kala cikin tashin hankalin ganin hawayenta saidataga kamar zai sawa kansa ciwon Kai gurin qoqarin lallashin ta goge fuska tareda sakin siririn murmushi tace,

Ok Ya isa haka you need to rest ji hancinka yanda yayi ja alamar you're

19, December 2024
Barirah Salihu

Thanks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login