Showing 51001 words to 54000 words out of 67570 words

Chapter 18 - DAWOOD COMPLETE HAUSA NOVEL

M SHAKUR   

29 Jun 2024

36747

sbd koyaushe itace ke datse masa farin ciki,

da gudu ta isa jikin motarsu bilal na ganinta ya fito da sauri ya riqeta ta qanqamesa jikinta na rawa tace,

bilal fitar dani daganan yanxunan numfashina zai bar zuciyana..

da sauri yasakata mota yatayar suka fice layla na qarasowa suna barin gurin taxi ta tsayar tafada tabi bayansu idanuwan na qara rinewa jajir sbd kukanma ya tsaya sai radadi idanuwan kemata har lokacin jikinta rawa yake sosai aleeya kawai takeson ta fahimceta sbd bazata iya daukar ganin tsanarta a idon aleeyaba.

suna isa gida ta fito motar da sauri ko gani batayi sosai tayi ciki ta fada daki tareda rufewa ra sulale qasa tareda sakin kuka mai qarfi kozataji abinda ya tsaya mata aqirji ya fada,

tana shigowa harabar gidan su ammy da nana nashigowa bilal na ganinta ya qaraso da sauri cikeda tsoro da tsananin mamaki da fargaba harzai ta6ata ya tsaya cak tareda qura mata ido sbd tuno halinda aleeya ke ciki hakan na nufin layla tagani shima wani zafi yaji azuciyarsa ya juya cikin tsananin jin zafin laylar yabar gurin batareda ya tsaya sauraron kiran da ammy ke masa cikin tashin hankaliba,

sake shiga sabon tashin hankali tayi ganin halinda take shirin shiga yasa ammy riqota suna shiga dakin aleeya ta miqar da aleeya tsaye tareda kallonta cikin tsananin fargabar halinda taga aleeyar tashiga lokaci daya tabbas tasan layla takai qololuwar aikata babban laifi saidai bazata nuna hakanba yanxu sbd aleeya tadau zafi idan itama ta nuna nata zafin lalacewa kawai abun zaiyi cikin daga murya tace,

aleeya duka wannan abun mu tsaya muji komai tukuna.....

cikin zafi da daga murya ta miqe tareda kallon ammyn tace,

mekikeson naji ammy ne?
i've suffered enough,,abu daya kawai nakeson ji yanxu shine meyasa kikeson na saurara ammyn bayan komai yazo qarshe.

ba haka bane aleeya NUR DA DAWOOD sunason juna tun kafin aurenku dawood shine dr dawood din layla....

wani sabon kallo aleeya tasakarwa ammy kamar zautacciya qwaqwalwarta na juyawa tanaci gaba da jin sauran bayanan ammy tun farko har qarshe sai kawai taji wani mugun jiri ya de6eta layla tayi saurin riqota tana juyowa bata tsaya komaiba ta saukewa laylar wani gigitaccen marinda yasatayin baya daidai isowar dawood yayi sauri riqota tareda bude baki afusace zaiyi magana cikin wani irin karaji da fushi aleeya ta nunasa da hannu tace,

stay out of this wannan is between me and her nobody will interfare tana buqatar amsa dukkanin tambayoyina ayau sbd daga yau THERES NO MORE ALEEYA AND LAYLAH,,,,

afirgice kowa yakalleta layla kuwa kuka tasaki na tashin hankali tareda matsowa jikinta na tsananta rawa cikin wani irin yanayi takalli laylar tace,

meyasa kika za6i ki rusa rayuwata ta hanyar bari na auri wanda baya sona bita6a sonaba,kinta6a tunanin rayuwar qanqancin dazanyi idan na auri wanda wata yakeso baniba....

cikin tsananin kuka layla murya na fita daqyar tace,

duk abinda zanyi sbd farin cikinki nakeyinsa......

wasu hawayen takaicine suka saukowa aleeya tace,

abinda baki saniba shine kin rusa duk wata rayuwar farin cikina laylah,
wlh kozan rasa raina bazan bari ki auri wanda nasan bazakiyi daraja agurinsaba koda kina sonsa sbd qaunar danake miki tafi haka,
amma me kikayi ta hanyar 6oyemin kina kallo na auri wanda zanyi rayuwar qunci agidansa har abada sbd babu so,
qarin abin haushinma ashe duk wannan quncin danakeyi kina sane da mafitarsa kika za6i ganina acikinsa shin wace irin muguwar qiyayya da qaddara tafi asaki mace ranarda aka kaita gidan aurenta
amma ni aleeya sbd tawa qaddarar daban take tasakani tsananin son mutane biyu dabasu cancantaba
adaran da aka kaini adaren aka sakeni sbd ke NUR,

nayi kuka agabanki nayi abayanki,
nayi rayuwar qunci agabanki nayi abayanki kina saneda akwai mafutar quncina kika za6i kiyita ganina ahaka menayi na cancanci haka NUR karki cemin sadaukarwa ce sbd sam babuta anan......

tsawa ammy ta daka mata ta tsayarda ammyn da cewa,

ammy ayau babu mai magana nice zanyi magana sbd nice aka taru aka rusawa rayuwa,
menayi dana cancanci haka daga wainda nakeso fiyeda komai....
meyasa kika za6i dawood akaina layla meyasa,,,,
meyasa zuciyata ta ringa azabatardani akan wainda suka za6i junansu akaina shin dama so yana zama haka,,

riqota bilal yayi da sauri ganin yanda take kuka sosai kamar numfashinta zai bar jikinta hawayen tausayinta yakeyi sbd tabbas ancutatarda ita ta hanyar qyalewa ta auri wanda baya ko qaunarta shima harcikin ransa ayanxu jin zafin layla yakeyi,

qanqamesa tayi tana tsananta sautin kukanta sbd wani irin radadi da zafi takeji cikin ranta akan layla,

kukanda layla keyi shiya daga hankalin mum da dawood sukayo kanta ganin yanda take jan nunfashi tana kuka
ammy ma hawayen takeyi ga nana dake kuka sosai na tausayinsu su dukan,

rarrafowa tayi gaban aleeya cikin tsananin rudani da kuka tace,

aleeya karki rabu dani kiyimin hukunci daidai yanda zuciyarki zata huce amma wlh banta6a fatar qunci ko damuwa ba ko akan takalminki bare ke,
aleeya narabu da dawood har abada idan hakan zaisa kifahimci banida niyar quntata miki bazan qara ganinsaba na....

wata mahaukaciyar tsawa ya daka mata cikin tashin hankali da tsoron abinda take fada yace,

har abada babu mai raba dawood da nur duk maison fahimtar hakan ya fahimta wanda bayason fahimta dole zai hkr meyasa kunkasa fahimtar abinda nakeso......

wani kallon baqin ciki da takaici aleeya tasakar masa zuciyarta na qara zafi tabbas sone yasa aka dade ana cimata fuska tazama wata wawuya atsakani amma anyi angama koda kuwa sonsu zai kasheta cikin yanayi na rakaici ta katsesa da cewa,

nice kakeson na fahimta sbd kowa dama ya dade da fahimta nice fool dinda takasa sani kuma na fahimta yanxu shiyasa nake albishirin sanarda kai aleeya tabar rayuwarku har abada kuje ku 'dora daga inda kuka tsaya adane rashin sani take wahalar dani banda yanxu danasan komai dama dukkanin alamu sun nuna kun yafe kowa zakuyi rayuwarku ku kadai dan haka kuje idan dan NUR ce bazanyi jayayya dakaiba nabar maka ita har abada kuje na yanke duk wata alaqata da ita zan rayu ko babu ko dayanku....

kallon cikin idonta layla tayi da sauri aleeyar ta juya ta fada bedroom tareda rufowa ta sulale qasa tasaki wani irin kuka mai tsananin qarfi daya daga hankalinsu ammy da mum da bilal dakejin quncinta harcikin ransa sbd tamkar uwa daya uba daya yakejin qaunar aleeya ajininsa.

kuka takeyi da qarfi sosai sbd bata ta6ajin zafin datakejiba a qirjinta yanxu jitakeyi kaman ta hadiyi zuciya ta mutu,,
sonsu su biyun ajininta yake saidai har abada ta yafesu sbd suba alherineba arayuwarta they hurt her so deeply morethan she can take,


kukan datake duk iya qarfinta ya daqa hankalin kowa cikin wani irin mugun yanayi layla ta miqe cikin wani irin mugun yanayi ta fice gidan dawood yabi bayanta da sauri saidai yana fita tana shigewa texi 'dinda ta tsayar sukabar gurin da gudu.

arkice ya juya ya shiga motarsa yabi bayansu jikinsa na wata irin rawa sbd tuni zuciyarsa tafara bugawa da qarfi.
#mamuhgee


vote and comment.*_DAWOOD_*
_wattpad@mamuhgee_




*38*
not edited.


wani irin mahaukacin gudu yakeyi yana duba gabansa sosai sbd sosai motarsu tayi masa nisa yana kaiwa round trafficlight ta tsayar dashi kota kanta baibiba ya wuce da gudu daidai lokacinda aka sako wasu motocin nantake sukai wani irin karo kankace me tuni gurin ya rikice da holdup wasu nata zaginsa bai tsaya sauraronsuba ya bude motar da sauri yafito yana kukkutsasu harya fice cikinsu yaga ko alamar motarsu laylan ya dafe goshinsa tareda rufe ido cikin wani irin mugun yanayi na tsoro da fargaba.

wani police ne yazo ya tsaya agabansa yanata faman zuba masa fada akan holdup daya hada ahankali ya juya yashigar motar yafara matsawa har hanya tafara samuwa nan gurin yafara sakewa yasamu hanya ya dauki hanyar gidansu da gudu,

yana isa su sufyaan na harabar gidan sunata faman kiransa,

yanayin shigowarsa da parking dinsa yatabbatar musu da babu lafiya nufarsa sukayi kowanne na qoqarin tambayarsa amma baimasan sunayiba saidai ya nufi flat dinsu ahargitse ya dudduba koina bata nan yafito harabar gidan yana qoqarin sake fita jass ya riqesa cikin daga murya yace,

wai bakajine,menene yake faruwa ka kasa fadamana duk kasa hankalinmu yatashi?

kallonsu yayi da jajayen idanuwansa wani irin zafi na tasowa daga zuciyarsa yace,

akaro na biyu aleeya tasake shiga tsakanina da farin cikina sbd jikina nabani NUR barina zatayi sbd aleeya,,,,,aleeya itace babbar matsalata arayuwa kaji yanda take yiwa matata ihu kuwa,she even slapt her bayan tasan she's pregnant and now nur left sbd gudun 6acin ran aleeya ya zanyi da rayuwatane?
bansan meyasa tunfarko ba nafara soyayya now i'm stuck wit this two best friends zance ko sisters.

dafe goshinsa yayi yana sakejin ciwo cikin ransa,
ganin kamar yana buqatar taimakonsune yasa suka dunguma yawon duk wani motopark da stations nemanta amma babuta babu mai kamada ita nan hankali ya qara tashi mum tun tana daurewa kasawa tayi ta miqe ta fita nema itama sbd harga allah tasamo danta ya daidaitu daqyar bata fatar akoma inda aka fito,
ta yarda tabi sai layla.


har dare suna abu daya amma babu alamar zaa ganta,
hankalinsu bai qara tashiba saida sukaga dawood na neman shiga wani hali babban abinda yafi jijjiga duniyarsa shine sabon sonta da dansa ko yarsa dake cikinta,

duk yanda sukaso dawowa gida har gobe qiyayi haka suka raba tsakiyar dare suna nema shiga tashin hankali,

asubar fari dole suka dawo gida jiran kira daga stations dinda suka bayarda reports reports,

duk yanda mum taso ko ruwan coffee yasha yakasa sha gashi har wani jiri jiri yake gani daqyar yayi sallar asuba ya sulale yaqara ficewa basu saniba.





duk yanda taso bawa zuciyarta dangana da rarrashi saitaji takasa sbd mutane biyune data fifita qaunarsu fiyeda komai suka taru suka karya zuciyarta da yardarta akansu,
tanason dawood so mai tsanani data za6i zaman rayuwar qunci agidansa sbd sonsa kuma ta shirya hakan har qarshen rayuwarta saidai duk sonda take masa tafison laylanta fiyedashi meyasa layla taza6i 6oye mata komai?
zata iya bawa layla jininta da qodarta bare abinda takeso amma suka za6i baqanta mata fiyeda fada mata komai tun farko,

dafe zuciyarta tayi tana cigaba da rero kukanta sbd qunci da zafi takeji sosai cikin ranta idan har haka ake sadaukarwa to itakam tata batazo mata a dadiba don kuwa nata cutatarwane,ancuceta anbarta tana jinyar banza abanxa.

tun tana kukan da qarfi harta koma ta lafe saidai hawaye,

abba daya dawo yana fada sosai akan sunbarosa asibiti batareda anyi abinda akaje yiba cikin sanyin murya da fargabar yanda zai dauki zancen ta zayyane masa komai,

shiru yayi yana jujjuya zancen cikin zuciyarsa kafin yasake ajiyar zuciya yakalli ammy cikin sanyin murya yace,

wannan alamari tabbas qaddarane sbd matar mutum hausawa sunxe kabarinsa ce saidai duk muduka amatsayinmu na iyaye munyi kuskure musamman keda kike uwa mace kuma kinsan komai amma kika qyale,
datun farko kin fadamin koda baki fadawa aleeyarba saimu samu mafitarda zata 6ulle bakamar irin wannanba,

maganar gskia naji zafi matuqa kuma wlh banga laifin aleeyaba sbd an cutatar da ita ta hanyar 6oye mata alhalin idan itace nasan tabbas bazata 6oyeba abu mafi zafima shine ace ansaketa ranar da aka kaita kuma tsabar cin fuska da zarafi ace tacigaba da zama tana yimasa bautar kula dashi baya gidan giya baya club sannan duk da haka qarshe ace sunyi aure wani gurin duk baa nememuba saida taji maganar ciki shin a ma'auni na hankali mezaisa ran mutum bazai 6aciba kokuwa so ake tayita hadiyar ciwo da qunci ita kadai bayan duk wanda ta jima tana diba,

shin idan ta cancanci haka daga dawood wannan fine babu matsala amma agurin yar uwarta datakeso fiyeda komai dan nasan tabbas dazaa bawa aleeya zabin ta hakura da iyayenta tabarwa layla zata iya bakomaine yasata hakaba face 6oyewarda akai mata ana tunanin bazata iya hakura dashiba kuma wlh kowane dan adam akayiwa haka zaiji zafi,

agaskia banji dadiba kwata kwata sbd ancutatarda aleeya kuma kece silar komai sbd idan ita layla tayi tunanin wannance mafita saiki lurarda ita ba wannance mafitarba ki dage ki jajirce ki nuna mata kece uwa,

karki dubi kasancewarta marainiya kice bazaki takurataba ki nuna mata abinda ya cancanta sbd wannan babban kuskurene ace bazaa iya rufe ido ayiwa maraya fadaba sbd gudun 6acin ransa gashi inda komai yazo yanxu,
nikaina amatsayina na mahaifi nayi babban sakaci amma insha allah yanxu zan tsaya tsayin daka kan iyalina,

ayanxu kam tunda alamura sun lalace zan danne 6acin raina adaidaita komai tukuna sbs bazanso kan yayana ya rabeba idan komai ya daidaita nasan abinyi.

yana gama fadar haka ya miqe yashige toilet ransa ba dadi ko kadan sbd sosai ransa yayi 6aci amma kasancewarsa babba dole ya danne 6acin ransa sbd samun alamuran su daidaitu dan idan ya nuna 6acin ransa aleeya zatafi qara hawa.

ajiyar zuciya ammy tasake cikin tsananin sanyin jiki da damuwa tareda fargabar halinda aleeya da laylan suke ciki yanxu,
tabbas tayi kuskure amma insha allah angama daga yanxu bazata taba barin wata 6araka sake shigowa tsakanin yayantaba.


tsakar dare ammy tashigo dakin ahankalin tareda lalubar wutar dakin ta kunna batai mamakin ganin aleeyar zaune daram tsakiyar gadoba tayi zuru tareda nisa ciki tunani idanuwanta sunyi wani irin mugun ja da kumburi fuskartama gabaki daya tayi jajir sbd kuka,

qarasowa tayi ahankali ta zauna bakin gadon jikinta amatuqar sanyaye da tausayin aleeyar sbd tasan ko aje adawo aleeyarce zata cutu,

hannu takai ahankali ta dafo kanta tareda kiran sunanta murya a shaqe,

dagowa aleeyar tayi takalli ammy tareda amsawa daqyar,

aleeya ni uwace datayi babban kuskure ina fatar zaki yafemin harma da layla..

rufe ido tayi ahankali hawayen ciki suka gangaro tasaki wani wahalallen murmushi mai ciwo tace,

ammy bana fushi daku saidai dolene zanji zafi da ciwon abinda akayimin,

kina tunanin zanta6a daina qaunar NUR?
qaunarta acikin jinina take ko kadan bazan iya daina qaunartaba sbd qaunace daga allah tsakanina da ita saidai nakasa gane meyasa tayi tunanin nibazan iya hkr da dawood ba ta za6i cutatarda rayuwar mutane da dama,
shin ammy kinkuwasan zafi da 'dacin dana dandana aranar dana tare aranar aka sakeni meyasa duk mutanen danake so sunkasa fahimtar irin soyayya da qauna danake musu,,,

sharce hawaye ammy tayi sbd tsananin tausayin 'yarta ganin yanda har lokacin tana qaunar layla da zuciya 'daya,


kuka tasake mara sauti tana cewa,

ammy nice da hannuna na mari laylana,
laylana nada ciki maimakon nayi farin ciki amma nice na mareta da kaina wannan wace irin qaddarace,
meyasa suka za6i farin cikinsu akan na masu qaunarsu shin meye laifina dan inayi musu qauna mai zurfi?

share hawaye aleeyar tayi tareda zamewa ta kwanta jikin ammy murya na rawa tacigaba da cewa,

har cikin raina bana buqatar layla ayanxu ina buqatar zuciyata tasamu sarari tukuna sbd ganinta yanxu naqarawa ciwukan zuciyata zafi.

shafa kanta ammy tayi cikin muryar banhkr tace,

aleeya ki yarda babu wata qauna ko soyayya aduniyarnan datafiki agurin layla,
layla namiki qauna irin wadda kike mata sbd tun asali komai datayi tayine sbd taza6i rabuwa da wanda take tsananin so sbd ke,
ta za6i yarda da auren qaninsa sbd ta haramtawa kanta wanda takeso duk sbd kene,
wannan cikin na jikinta isharane sbd allah yayi da akwai rabo atsakaninsu koda aure kobabu aure dole zaa samesa tunda allah ya qaddara to maixai hana mu taru mu rungumi qaddarar gabaki daya.

shiru tayi tareda rufe idanuwanta ahankali zuciyarta na qara nauyi.

ammy anan ta kwana gurinta tana qara fahimrarda ita kuskuren dasuka taru suduka suka tafka.





baidawo gidaba saida su jass suka fita nemansa hankali ba kwanceba,
koda suka dawo gida wahala da yunwa tafara zabgesa wuni guda,
mum kuwa tayi jimamin tayi kukan zuci acikin kwana na uku tuni kukan fili yafara bayyanar mata sbd masifar data hangowa kanta kan 'danta,

duk iya nema da bincike anyi babu nur babu labarinta tun abu na sauqi sauqi haryayi zafi abba dakansa yafara nasa aikin sawa nemanta hankali tashe
ammy ma kam rashin hankali yadawo sabo ganindai ta tabbata ba'aga laylaba ta 6ata,

duk yanda aleeya takaiga daurewa abin cinta yake cikin ranta da jikinta sbd wata irin rama da lafiya data fara qaurace mata babu layla ga dawood kwance sosai babu lafiya,

bilal kam kallo daya zakayi masa kasan baya cikin kwanciyar hankalin 6atan yar uwarsa ga aleeya ma dayake gani yana rage kewar layla batada walwala kwata kwata yanxu kullum tana daki,

cikin sati biyu alamari yayi tsanani kullum cikin yiwa dawood allurar bacci ake har taso fara ta6a masa qwaqwalwa suka daina yimasa aikuwa nan take ciwo yadawo sabo babban abinda yafi daga musu hankali shine mugun ciwon cikin dayakeyi sosai nan suka duqufa bincike suka gano giyar dayayishace abaya ta ta6a masa qoda nan suka duqufa magani amma kamar basayi,

sannu ahankali damuwa da quncin dasuka fito yafara dawowa kamar da,
mum duk ita inda tashin hankali yakai tana ciki tayi kuka har idanuwanta sun rikide
lokacinda abun yayi tsanani hankalinsu jass yatashi suka sanarda dad da taheer halinda ake ciki nan take dad ya shiryo zuwa yazo duk yanda mum taso yaqi bari tagansa yayi iya kwanakinsa suka wuceda dawood din sbd aikin dazai masa acan.

bayan tafiyarsu kullum ammy agidan take wuni itada nana suna rage mata damuwa,

aleeya sosai take jinyar kanta amma haka ta daure tashirya taje gurin mum din aranar data dawo gida tayi kuka sbd ganin ko yanxu rayuwar mutane da dama na neman lalacewa ta sanadin rashin layla to idan wancan karon laifin layla ne yanxu nawaye?


anyi masa aiki cikin nasara saidai sosai yadaga musu hankali gida yakeso su koma kar layla tadawo bayanan,

hakanan suka tattaro suka dawo dashi aka dora jinyar anan,
sannu ahankali ciwo ke cinsa babu abinda yake fata ayanxu irin mutuwa sbd yatabbarda soyayyar layla itace ajalinsa,
zafi da ciwo mara sassauci yakeji cikin zuciyarsa matuqa,babu abinda yakeson gani irin laylarsa sbd duk inda take ayanxu ta haife cikin dake jikinta da wata daya,

rufe idanuwansa yayi ahankali yabudesu ciki azabar ciwo wasu irin hawaye masu dumi suka gangaro masa tabbas nur itace rayuwarsa.

tari yayi ahankali mum tamiqa masa tissue yarufe baki yana tarin yana dago tissuen ahankali yaga jini ya lumshe idanuwansa daqyar cikin azaba tareda 6oye tissuen kar mum ko su jass sugani,

hankalinsu baqaramin tashi yayiba ranarda yaringa kwararo aman jini nan suka kwashesa sukai asibitinsu,
lokacinda sukaga result din bincikensu akansa kuka sosai jass yazauna yanayi sufyaan na qoqarin danne nasa gurin lallashinsa sbd sun sadaqar da shima rasashi zasuyi kamar yanda suka rasa maska tabbas dasun tabbata marayu idan babu maska babu dawood.


tsawon wata hudu da dawowarsu babu siyama babu dalilinta ga ummanta ta daga musu hankali da koke koken nemanta nan hankalin ammy yasake tashi ga abba sosai hankalinsa ke tashe gurin ganin ansamo inda layla take kusan shekara kenan babu labari,

tareda abba ayau suka sauka porthrct direct headquatr suka nufa gurin jin bayaninda akakirashi

19, December 2024
Barirah Salihu

Thanks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login