Showing 129001 words to 132000 words out of 195514 words
iya aikin nan kawai bari ta fito na bata shawara ta koma 'bangaren doctor ta barwa maza soldier d'in nan"?.
"Maza irin ka"? Aunty Safiyah ta tambaye shi cikin tsokana d'an zaro ido yai yana cewa "niiii a'a tabdijan mazai kaini daji mahallaka ina daga bangaren allura💉 da magunguna💊".
"Ok kasan a barka 'bangaren allura da magani saika barta itama bangaren bindiga🔫 da bullet kowa da kiwon daya kar'beshi ma'kofcin mai akuyi🐐 yasai kura🐆.
Kallonsa Alhaji Bashir yai yana cewa "to kai meye naka na tambaya tunda kasan burinta ne kuma yawe ya fad'a maka Amatullahi me sanyi ce ko kai bazaka fad'a Mata zafi ba saidai ka fad'a mata tsoro".
Dariya Ahmad yai yana kallon Amatu data fito tana sanya hijab yace "ai Daddy ba tsoro ne ya hana nayi soja ba".
"To meye idan ba tsoro ba"?.
"Allah Daddy ka yarda ra'ayi nane".
"Shikenan na yarda kodan abar maganar".
Mi'kewa Ahmad yai yana cewa "sai ku taso ai kun tsayar dani tun d'azu da yanxu na manta da naje gida haba safga da yara ko safga da wahala".
"Wai kai 'kalau kuwa wannan fad'an fa me zakai a gidan idan ka koma ne inace yau ba hospital zakaje ba to maye abin saurin"?.
"Amma umma koba inda zanje nafa baro 'yar mutane ita kad'ai babu kowa gida kuma 'katon gida".
"Umhum dama nasan abinda zakace kenan kamar a kanka aka fara mata Allah ya yaye maka rashin kunya" su Maryam ta kalla tana cewa "amma sai gobe zaku dawo tunda ba school" tun basuyi magana ba Ahmad ya zaro ido yana cewa "a ina zasu kwana mom? Had'e rai Aunty Safiyah tai tana cewa "a gidanka" kai ya girgiza yana cewa "a'a yau zan dawo dasu wadannan yaran banda headache babu abinda zasu d'orawa mutum" ri'ke ha'ba aunty Safiyyah tai zatai magana Alhaji Bashir ya rigata "ok kuje zuwa sallar magriba ka dawo dasu" yana rufe baki Ahmad yace "yauwa daddy haka nake son ji kai kumuje" fita sukai aunty Safiyyah na dariya tace.
"A'a ikon Allah sai kallo Ahmad yafi qarfina daga umm sai umm wai uwar gulma tayi cikin shege" murmushi Alhaji Bashir yai yana kallon ta yace "kinga laifinsa ne yanzu lokacin sane ni nafada miki nan gaba zakigani da kansa zai kira waya yace suje gigin angwanci ne yake d'iban sa🙊 zai dawo daidai😂 yaro man kaza🐔 muma muyi mun sau'ke sai labari" ita dai Aunty Safiyyah dariya take harda tafa hannu saboda tuna baya 'kuruciyar Ahmad sak ta Alhaji Bashir.
Suna kan hanya harsun kusa gidan Ahmad yace "kunyi mata tsaraba"?😲 duk zaro ido sukai suna kallonsa ta mudubin motar ya kallesu ganin shi suke kallo yace "bakuji abinda nace bane"?.
"Amma yaya wacce irin tsaraba"? Maryam ta tambaya tana 'kureshi da kallo.
"Oh tambaya ma kike saboda kin manta? Ita lokacin da tazo gaida mom bata kawo muku chocolates ba to kuma yau zaku ramawa kura aniyarta ku mi'ko min kud'i"?.
"Ni dai wallahi ya Ahmad ban fito da kud'i ba" Maryam na rufe baki Amatu tace "balle kuma ni bansan sanda tazo ba tunda sannan ina garinmu".
"Ai kuma yarinyar haka zaki bayar ko 2k two kece wallahi baku isa mu shiga gidan nan da babu tsaraba ba dan haka zan arawa kowacce ku dubu bibiyu bari muje Sahat".
Zaro ido Nabilah tai "amma dai yaya banda ni"?.
"Ubanwa kika fi zane? harda ke man kuma kina komawa gida ki kar'ba min kud'ina agun Daddy" ya karasa maganar yana parking a bakin Sahat ya fito suma dole suka fito suna turo baki suka shiga ciki tare bangaren kayan za'ki haka ya ri'ka jibga mata chocolates🍬🍭🍡🍫 suna shan kallon sa dan wallahi sukam ba ruwansu ai matarsa ce🤨.
Saida ya gama sannan suka fito suna shigo mota suka wuce cikin tsokana Maryam tace "ya Ahmad nawa ka ara mana"?.
Hankalin sa nakan tu'ki yace "ina ruwanki" rufe baki tai tana dariya Amatu kam tunani take akan abinda ta gani dazu a laptop har suka 'karasa gidan bayan yayi parking sun fito jiransa sukai yai musu jagora suka shiga gidan tana zaune a parlor ta d'au kwalliya cikin less da glass cup🥛fal da had'add'iyar marada mai d'umi tana sha kai Maryam ta jinjina a ranta tace.
"uhm aure manya ji dan Allah😂".
''Ke uban me naji kince😁"? Ahmad ya tambaye ta yana juyowa rufe baki tai tare da fatan Allah yasa baiji ba tace "ni ba komai nace ba" "ok yayi karasawa cikin falon sukai da murmushi akan fuskar Lailah tamike tana rungume Ahmad🙈 ta bashi kiss zaro ido sukai suna kallon juna Amatu da sauri ta juya musu baya murmushi ne ya su'bucewa Maryam kawai ta girgiza kai Nabilah kuwa ta tsayar da idonta tarrr akansu tana kallon yadda ake soyayya😝.
Sakinsa Lailah tai tana kallon su tace "sannunku da zuwa sisters sai yau kukazo ku zauna karasowa sukai suna zama Ahmad kam ciki ya wuce Lailah kuma tai hanyar kitchen taje ta had'o musu kayan ciye-ciye da shaye-shaye ta kawo musu tana cewa "bismilllah kuci bari nazo" bin bayan mijinta tayi ta basu guri su d'an sake.
Tana barin parlon Maryam tace "tofa bari nai gulma ji dan Allah matar nan ko kunyamu ta wani rungumeshi shima harda kara matseta a jikinsa yana zullo mana ido😂🙊".
Dariya Amatu tai tana cewa "ke kuma sa idon naki haryai yawa laifin waye dakin juya musu baya kamar yadda nayi shikenan da kin hutar da kanki bakiga komai ba balle abun ya dameki".
Ta'be baki Maryam tai tana cewa "Hum'um wallahi bazan juya musu baya ba ni nace su rungumi juna🙈 ko yanzu suka fito suka sake runguma zan kalla".
Murmushi Amatu tai tana girgiza kai ta d'au apple guda daya tana ci bata sake magana Maryam kam ledar tsarabar da sukayowa Lailah ta d'auka tana d'ebo chocolate da sauri Nabilah tace.
"Aunty Maryam kar yaya Ahmad ya fito ya sameki da chocolate fa kinsa halinsa"?.
Bud'ewa Maryam tai tana cewa "wallahi saina sha garama kiyi shiru🤫".
"A'a Maryam karfa yazo yana gwangwazarki bazamu iya cetonki ba" Amatu ta fad'a tana kallon kofar shiga part d'in Ahmad.
"Allah Amatu kome zaiyi saina sha inace dama aro yabamu kud'in? To a nawa 'bangaren na d'auka" tana rufe baki taga sun fito ya sanya kayan shan iska jesi mai adon fari da blue d'an kau dakai Amatu tai tana cewa "ya Ahmad amma yanzu zaka mayar damu"?.
Dakatawa yai yana kallon ta yace "na mayar daku ina"?.
Kai lallai jishi da wata magana kamar baisan me nake nufi ba "nace na mayar daku ina amma badai gida ba"?.
"Eh gida".
"Sai anyi sallar magriba bakuji me Daddy yace ba yanzu lokacin Wasa ne".
Cikin alamun tambaya Amatu tace "wasan me"?.
"Dame kika ganni? 'kwallon qafa zamuyi idan kuna sha'awar kallo ku biyomu"😝 yana fad'in haka suka fita a falon shida Lailah dake ri'ke da ball a hannunta kai Amatu ta jinjina tana cewa.
"Uhm yaufa nake ganin duniya Maryam kina jinsa fa abinda yake cewa wai mu bisu muje muyi kallo muga me"?.
"Oho masa Allah ya Ahmad d'in nan wani lokacin idan yai wani abu yadda kikasan na kamashi da duka haka nakeji amma fa yin auren nan ya sake susutar dashi gara mu lalla'ba a jima ya mayar damu gida salin alin karatun fatiha aiko bazan sake xuwa ba sai nan da kamar shekara".
Dariya Amatu tai "shekara dai Maryam tab fad'a kike amma dai sannan saidai kizo sunan baby ko"?.
Zaro ido Maryam "baby? suna fa kikace ya Ahmad da d'a? Uhmmm wai ranar za'aga girgiza😛".
"Meyasa kika ce haka"?.
"To Amatu kina ganin yadda yakeyi a gabanmu inaga su kad'ai ne a gidan"?.
"Maryam sa idon ya isa haka ki kyalesu lokacin sune".
"Hum lokacin sune kam tunda gashi nan harda fita 'kwallon ball nikam bari nayi kitchen dan gaskiya wannan abincin data kawo mana ya huce wani zan d'ebo" Maryam ta karasa maganar tana d'aukar plate din tai hanyar kitchen Nabilah kuma ta mi'ke tana fita kallon qwaqwaf suka bar iya Amatu a falon wacce ta rufe idonta kawai tana tunanin a inda wannan 'kungiyar take.
🏕️'KAUYE🏕️
Kamar yadda aka sanyawa bikin Dauda da Indo da kuma 'kanwarsa Fatima za'a bata wani saurayi Sadam ba'a sanya lokaci mai tsawo ba sakamakon Dauda da yake son zai koma Osun tafiya sannu sannu kwana nesa yau alkawari ya cika an d'aura Indo ta zamo amarya a gidan Daudansy😝 Asabe kamar tai hauka ranar gashi Bahijjah bata gida wai tabi Iluh zata gano garinsu🙊 humm Asabe tayi kuka tayi ba'kin ciki har saida hawan jini ya hauta haka tana ji tana gani aka kankatsa biki akai hidima kwana biyu da d'aurin auren Dauda yad'au amaryarsa suka tafi Osun tare abinsu cas haka 'bangaren Dalah tayi farin ciki da wannan rana ta godewa Allah ta qara yanzu bata da damuwa ta daina kwana cikin fargaba da halin da Indo d'in take yanxu tasan zata koma rayuwar 'yanci.
Gari fa gabadaya ya karkad'e su malam Habu sun dawo saidai basuzo da ko naira biyar ba 'yan fashi sun taresu a hanya sunyi musu duka kuma sun 'kwace komai wasu su tausaya wasu suyi dariya irinsu Tanko da mudi kai wani abin mamaki harda Ilyah a masu murna dan dama tunda suka tafi kullum yana cikin tunani baya samun kyakkyawan barci saboda kada malam Habu yaje ya samo dukiya yazo ya fishi kud'i har wata rama yai ta fargaba hankalinsa bai kwanta ba sai yanzu da suka dawo yaga bai shigo da komai 'kauyen ba hatta riga ma sai d'an gidan malam zayyanu aboki Baffah ne ya d'inka masa guda d'aya😥.
Majalisa kowa da kowa ana zaune Malam ya karaso da sallama a bakinsa yana samun guri ya zauna suna gaisawa da jama'ar da aka jima ba'a had'u ba ko numfashin tafiyar dayai bai gama tsirga masa ba Tanko dake kallonsa yana 'kunshe dariyar mugunta ganin har lokacin da sauran ta'bo a jikinsa ya kalleshi cike da sha'kiyanci yace "a'a alhaji Malam Habubakar mai ruwan nairori kaga d'an Baffah na Sabi'u d'an uwan Ilyah attajirin 'yan 'kauyen nan me nake gani haka meke faruwa ne wato a kwana a tashi babu sallama ba d'aga hannu sai ji muke wai kun tashi kun tafi neman kud'i kaida Sadi batare da kun sanar mana ba saboda bakin hali Dan karmu biku sai gashi dubunku ta cika a hanyar dawowa 'yan fashi sun tareku sun muku tsinannan duka sun 'kwace komai kila dama kayan da kuka taho da shi da kud'in ba halal d'inku bane wayasani ko sata dama kuke da kukaje shiyasa alhakin mutane yasa aka tareku aka kar'be dukiyar da za'a zo a mana tunkaho ana bubbud'a mana kafad'u ana hura hanci hhhhhhhhhhh mudi kaji da Allah".
Ya karasa maganar yana she'kawa da dariya had'e rai malam Habu yai cike da takaicin maganar da Tankon ya fad'a masa ransa a'bace yana shirin mayar da martani Sadi yace.
"Dan Allah dan Annabi badan niba malam Habu kada ka tanka musu idan kaddara ce bata wuce kan kowanne bawa ba Dama tun farko a rubuce take abinda muka tara bazai zo 'kauyen nan ba badan haka ba wallahi kudai👉 ya fad'a yana nunasu da yatsa yaci gaba da cewa "da saidai ku zamo 'yan kallo hum bakuba hatta Ilyah da yakejin duk garin nan shine mai tashen kud'i yafi kowa arziki wallahi koshi baida bakin magana da ace dukiyan da muka tara tazo garin nan kuma insha Allahu zamu sake komawa nan ba da jimawa ba zakuga irin alherin da zamuzo dashi saikun kasa furta komai kuma Nina fad'a muku wata rana zakuyi dana sanin wannan abinda kukeyi".
Baki bud'e Tanko, da Mudi suke kallon juna kafin suka sakar masa wata uwar harara Mudi yace "tofa sannu d'an iya ikon Allah Sadi yau kaine har kasamu damar furta wata magana wato zama da malam Habu ko ya koya maka ya'ba magana? Hum aiko kanada aiki babba a gabanka garama tun farko kaja gefe kamar yadda sauran sukai idan kuma ka'ki zakai bayani".
Mudi yana rufe baki Tanko yace "fad'a masa dai dan Naga shima yanada masifar shishshigi, Sadi babu ruwanka anan da Malam Habu mukeyi badakai ba karamin alhaki ka gane"?.
Kai Sadi ya jinjina "ai Tanko indai kunyi da Malam Habu tamkar kunyi da dani ne".
Wani irin kallo Tanko yai masa yana cewa "au haba? Ko shiyasa ka gayyaceshi kuka tafi bara har wata kasar kuka 'bige da sata kuma kukai rashin sa'a da yake ba dukiyarku ce ta halal ba a hanyar dawowa kukaci na jaki a gurin 'yan fashi"?.
Kafin Sadi yai magana suka ji muryar Malam Habu yace "uban waye ya fad'a maka sata muka je"?.
Gyara zama Tanko yai yana sake fuskantar malam Habu sosai cikin son 'kular dashi yace "Wa kake tunanin zai fad'a min dawa kukaje garin waye ya gayyaceka ba Sadi bane? To shine munje yo masa bangajiya washe garin da kuka dawo anan muka bugi cikinsa ya fad'a mana komai da kuke acan" Tanko ya karasa maganar yana kallon yadda Sadi ya zaro ido waje cike da mamakin sharrin dayai masa danshi idan ba yauba tunda suka dawo baiga Tanko ba kallon malam Habu yai yaga a yanayin yadda zai dau maganar da Tankon ya fad'a masa yana cewa.
"Wallahi sharri yai min Habubakar bansan komai ba ni tunda muka dawo ban ta'ba ganinsa ba sai yau Amma kaji tsabar 'karya danya had'amu harda wai sunje min ban gajiya a ina"? Ya fad'a yana hararar Tanko dake murmushi.
Caraf Mudi yace "ka tuna mana munje gurin ka washe garin da kuka dawo kodai sannan rad'ad'in ciwo bai sakeka ba baka gane su wayeba shiyasa ka saki baki ya layar uban tafiya ka fad'a mana sirrin ku"?.
Dafe kai Sadi yai jin zasu sashi a uku yace "Allah ya tsinewa mai 'karya indai abinda kuka fad'a a kaina haka yake gaskiya ne Allah ya tagayyara mai 'karya Allah yai d'ai d'ai dashi🙊".
Shiru su Tanko sukai yayin da Jama'ar gurin suka fara cewa Amin Amin kallon malam Habu yai yana cewa "wallahi Habubakar ba gaskiya bane abinda suka fad'a basuje gurina ba kuma ni bamu had'u dasu na fada musu komai ba ko a mafarki".
Ta'be baki Malam Habu yai yana mi'kewa ya kalleshi yana cewa "karka damu Sadi ba yauba na sanka koda kowa zaici amanata Banda kai sharesu kawai taso mu tafi idan isgili suke mana wanda ya jarrabe mu yana jinsu kuma babu wanda ya isa tsallake 'kaddararsa sannan garani iyalaina suna Sona suna alfahari dani sun fahimce ni basa guduna duk irin halin Dana shiga amma wani fa ba iya gidansa ko anguwarsa ba hatta dukkan mutanen gari tsine masa suke suna Allah wadai da tofin alatsine akansa saboda ya wadata kansa ya hana ahlinsa ga rashin yafiyar iyaye wai wanda yake da wannan ta'bon ne har ya samu bakin magana tsabar rashin hankali dayake shi laifi tudu ne ya take nasa ya hango na wani"? Malam Habu ya fad'a yana kallon Tanko dake dafe da kirji yace.
"Ko nayi 'karya ne Tanko"?.
Mi'kewa Tanko yai yana cewa "kaga malam Habu ka daina yi dani eh ban wadata iyalan nawa ba kai me zai hana ka d'ebo dukiyar gidanka ka wadata su sannan zansan ka damu dasu har haka in kuma zaka debesu ka had'a danaka ka ri'ke kofa a bud'e take nayi maka izini kaje ka d'iba na bar makasu duka mutum yana fama da ba'kin talauci yana sawa wani ido ban kula da iyalan nawaba da zama irin na gidanka cikin yunwa ba gara mutum ya mutu babu aure ba kaima me kake baiwa iyalan naka har zaka damu Dana wani kayi ta kanka"..
Kai Malam Habu ya d'aga yana kallon Tanko yace "kuma fa kaima kayi gaskiya da zama irin na gidanka gara mutum ya zauna babu aure na yarda da wannan shiyasa na'ki yin auren tsabar asaranci na zauna tuzuru sai iya kwartanci da 'kananan yara a guna Ina basu kud'i saboda jahilci gaskiya ne Tanko kayi magana anan da irin wannan mutumin gara kai da baka wadata iyalan naka".
Dariya guri ya rud'e kowa yana kallon Mudi Dan kaf gurin sunsan dashi malam Habu yake waye wanda ya'ki aure inba shiba kuma kullum 'yan iskan 'yan Mata daga wasu 'kauyukan suna zuwa masa ansha ganinsu Dan haka bashi da bakin magana balle ya musa kowa cewa yake "Allah dai ya biya Malam Habu gaskiya kana sanya mu nishad'i" Mudi kam sak yayi jikinsa yai la'asar kamar an jefa akuya a ruwan sanyi ransa na turiri gashi yana tsoron yai magana kada Malam Habun ya sake gasa masa wata maganar da zaizo yai dana sani yana kallo malam Habu da Sadi suka bar gurin mutane sai cagwada suke masa amma Saboda yasan halinsa ne tari dabai kamashi ba baiyi ba.
🌃 MARSHALL ISLANDS🌃
Asad yana zaune tare da Isham yana fad'a masa cewa akwai wanda ya gano 'kungiyar kuma mace ce saidai bai santa ba baisan a inda take ba ko 'yar waye Isham ya matukar kad'uwa kuma ya karaya dajin batun yana ganin kamar tunda haka ta faru shikenan Asad yayi losing komai kamar yadda shima Asad d'in a nasa 'bangaren yake jin hakan kallonsa Isham yai yana cewa.
"What do you do now bayan daka gano an samu wacce ta sani a ina take"?.
Kai Asad ya girgiza yana kallon laptop yace "I don't know Isham".
A damuwance Isham yace "amma Buddy mai zai hana kad'au hutu koda na wata d'aya ne ka zauna guri d'aya ka samu nutsuwa kayi bincike a hankali saikafi fahimtar komai".
'Dagowa Asad yai yana kallon sa jin abinda yace cikin nazari kuma yaga kamar hakan shine daidai ya kar'bi hutun ya tsaya guri guda ya samu yayi bincike akan koma wacece kuma dama yana son zuwa gida gurin Abba (mai martaba) daga nan saiya tsaya ya bincika sosai acan d'in ma zaifi samun nutsuwa fiye danan babu takurar Kiran wayar Clarah da damunsa akai akai.....
Muryar Isham ce ta katse shi "Buddy tunanin me kake ko shawaran dana baka batai ba"?.
Kai Asad ya girgiza "no tayi zuwa gobe zanje nayi magana da sir murtih Jonah Ina so zamu had'u da sir Jalalunddeen kafin na tafi domin wannan al'amarin babba ne inaso na tambaye shi ko akwai wanda yazo cikin jami'an mu yace an samu wanda ya gano abinda ake nema Kuma wai mace? Mace dai"? Asad ya karasa maganar da surprise sosai a fuskarsa wanda yasa Isham ya saki dariya yana