Showing 138001 words to 141000 words out of 195514 words
dame indai bada 'kasa zai ciko musu ba ko ya sayar da yarinyarsa guda d'aya wama take da suna? Ya fad'a yana kallon malam Habu ganin baya tare dasu tsabar tashin hankalin daya shiga baima san me suke ba dariya Tanko yai yana cewa.
"Hauwa'u Amatu ko?? Mamarsa cene ko 'kanwarsa na rasa ma sunan da yake fad'a mata sai ya sayarta tunda wannan masifar ta sameshi ya biya"
Cikin tsokana da isgili Mudi yace "Amma bari muyi shiru kar muji kunya bamu sani ba ko d'an uwansa Alhaji ilyah zai biya masa"?.
Jin abinda Mudi yace yasa kowa ya mayar da hankalinsa kan Ilyan suji Mai zaice bud'ar bakinsa ba kunya ko kara sai cewa yai "tabd'ijan wanne Ilyan kuke magana amma dai baniba wanine dabam ko? Allah ya sauwake na biyawa Habubakar bashi wallahi yadda nake jin haushinsa akan su Hassan da yakewa wayo fatara tasa yana kar'be musu kud'i Aiko kashesa zasuyi su d'ora masa bindiga a ka dai ina kallo ace inban biya ba zasu harbe shi wallahi saidai yai bunga uban waya hanashi tashi ya nemi kud'in"? Ilyah na rufe baki guri ya d'auki sowa hhhhh suka kuma fashewa da dariyar mugunta har hawaye ne yake zuba a idanun Tanko yana kallon malam Habu yace.
"A'a malam Habu yadai ka zama mujiya mai ba'kin jini kana jin abinda d'an uwanka yace inaga mu iye mukuma muce maka me yanzu fad'a min Ina gasa maganar daka saba idan anyi maka magana yau bakin ya mutu ko umhum uwar bari ba shegiya bace da ubanta kaima yau ka shiga uku taka ta sameka".
Tari da bai kama malam Habu ba baiyi ba kawai kuma badan bazai iya mayar musu da martani ba a'a sai tsabar takaicin maganar da Ilyah ya fad'a a gaban mutane akansa wai uba d'aya? Amma yake tozarta shi haka a gaban mutane jin hawaye na neman zubo masa yasa cikin jarumta da sauri yayi kokarin mayar dasu ba tare daya d'ago kansa ba.
Ganin da me gari yayi kamar Malam Habu baya cikin nutsuwar shi yasa yace "wa kake da suna Alhaji Mansur kace ko? To dan Allah kuyi masa ha'kurin yau ku d'aga masa kafa zuwa nan da sati biyu sannan ya gama had'a muku saiku dawo ku d'auka na roka masa wannan alfarmar".
Kai Mansur ya girgiza yana cewa "ai ba'ace mana mu taho batare da wannan kayan nasa ba sakamakon ya dad'e da fa cewa akai a taho tare da 'yan sanda su tafi dashi saboda yasan ana binsa tsawon shekaru yai shiru bai nemi company ya mayar musu ba da'kyar wasu suka sa baki cewa tsohon costumer d'insu ne amma badan haka saidai yau ya kwana acan".
Kai Mai gari ya jinjina yana kallon malam Habu kafin yace "shikenan amma dan Allah kuyi masa uzirin nan zuwa sati biyun kawai saiku dawo insha Allahu zasu samu kayanku dan Allah kunji dole rayuwa saida uziri balle shi ba kamar yadda suka sanshi da yanzu ba haka yake ba ku masa afuwa"..
"Ok to shikenan ba matsala zamu dawo nan da sati biyun Amma kafin nan ya bada kayan a gurin ka kawai da munzo da mota sai mu d'auka"? Jin sun amince yasa Mai gari yace "eh ya amince zuwa sati biyun".
Bayan sun gama magana da sauran sun kar'bi kayan da zasu kar'ba komai ya shiga manyan motocin da sukazo dasu sannan sukaiwa Mai gari sallama suka tafi daga nan kowa ya fara bajewa sai gulmar malam Habu ake wai yanxu ya zaiyi mutumin da bashi da ko naira biyar akawo masa buhu ba d'aya ba har goma ya cikasu da kayan abinci tabbbb zasuga yadda wannan cakwakiyar zata kare.
Saida Mai gari ya bari kowa yabar gurin daga shi sai malam Habu da sauran wasu yan majalisarsa mutum biyu ya kalli malam Habu yana gyaran murya yace.
"Am nikuwa malam Habu idan bazaka damu ga wata shawara dazan baka ko Allah zaisa ka amince ta yadda zaka biyasu kayan nan batare da tashin hankali ba"..
Kallonsa malam Habu yai yana cewa "amma me gari taya kenan wannan kayan da suke bukata a gurina bana karamin kud'i bane dame zan biyasu na tabbata ko yar gonata guda daya da nake nomawa na sayar kud'in bazai isa Wanda zan basuba"?.
Gyara zama me gari yai yana kara yin kasa da murya yace "eh shiyasa nace idan ka amince za'a biyasu ta ruwan sanyi saidai zamuyita da wajewa ka fara bani abinda zan nema a gurin ka yanzu ni kuma nayi maka alkawari koda zasu karo wasu buhuna goman zan biya maka bashinsu amma saika yarda da farko to mekace mun zama abokan har'kalla"?.
Cikin rashin fahimta malam Habu yace "abokan har'kalla kamar ya nifa ban gane inda ka dosa ba me gari akan me kake magana ne kamin bayani a warware yadda zanfi fahimtarka"?.
Me gari yana gyara rawanin daya kusa fad'owa muryarsa da d'an in'kina sakamakon baisan a yadda malam Habu zai kalli maganar dazai fad'a masa ba yace "so nake ka bani auren 'yarka guda d'aya a cikin su hud'un😳 akwai wacce nake so jiyama tazo ta wuce ta nan gurin har nake tambaya wannan kuma daga Ina dan ban ganeta ba saboda girman data 'kara sai akace min wai 'yarka ce ko"?.
Cike da kad'uwa malam Habu yace "wacce daga ciki kake magana" ya fad'a yana 'kure me garin da kallo dan a iya kwatancen dayai ya fahimci kamar Amatu yake nufi😲.
Kamar a mafarki yaji me gari yace "sunanta Amatullahi ko?ita nake nufi wacce ta dawo daga tafiya kwanan nan ita nake so idan har ka yarda ka bani auren ta ni kuma zan biya maka bashin duka amma me kace"?.
Tabdijan🤪😡 wani irin kallon baka da hankali ka fara hauka ne malam Habu yaiwa Mai gari yana cewa "mamana kake nufi? Ai me gari ko auren babbar 'yata Asma'u bazan iya baka ba balle mamana indai sainayi maka haka dana biya wannan bashin da suke bina na za'bi zaman gidan yarin shekara ashirin ban amince ba ka barni Allah zai horemin na biya su.............
Cikin lallami me gari yace "haba kai kuwa malam Habubakar dame zaka biyasu bayan baka da ko sisi kazo na taimake ka arziki yana binka kana guduwa wallahi indai ka bani auren ta zan baka kyautar gona ta zan baka shanu ka had'a amalanke sannan zan baka jari kuma gidanka kaga duk katangun suna bukatar gyara zansa a gyara maka harda sutura zan d'inka maka masu yawa kaji🤔"?.
Mi'kewa malam Habu yai a fusace jin yana neman kawo masa zuciya wuya da zancen banzan da yake masa ya karkad'e rigarsa yana kallon me gari da shima ya bishi da kallo yace.
"Zan sake maimaita maka kaji ko 'yata Asma'u bazan iya baka aurenta ba balle mamana ka gane indai sai nayi haka ne zan biya bashi sai na sayar da 'yata gara nayi xaman gidan yarin shekara ashirin" yana fad'in haka zaiyi gaba me gari daya mike har rawanin nasa na fad'owa kasa bai tsaya d'auka ba yace.
"Haba malam Habubakar arziki ne yake binka tsiya na korewa ka yarda wallahi da gaske nake maka zan baka komai da kake so" jin maganar da yake sake maimaitawa yasa malam Habu jan tsaki cikin takaici ya bar gurin yayin da Mai gari ya bud'e murya yana 'kwala masa kira amma ko waigoshi baiyi ba.
Haka malam Habu ya shiga gida a susuce tun kafin yai magana yaga dukkan ahlin gidan kowa kuka yake babba da yaro wato har an samu wani magulmacin yazo ya sanar musu bai iya ce musu komai ba kawai ba'kin ciki ya gama rufeshi musamman yadda ya kalli Amatu tana kuka sosai ga maganar da me gari yake masa akan ya bashi aurenta baisan lokacin da wasu baka'ken hawayen damuwa suka fara zuba daga idonsa ba ga hajijiya na d'ibansa da sauri ya shige d'akinsa yana rufe kofa kawai ya kwanta shima yana rusa kuka kamar karamin yaro😥.
INDIA CHENNAI🍒
Sakamakon ganin jikin Khimiyyah da sau'ki alhamdulillah yasa Mami tace Ajeeb da Annur su taho gida kafin suma ita da Ameer da Khimiyyan su biyo bayansu saboda kadan ya rage ta karasa warkewa saboda anyi mata wankin 'kwa'kwalwar cikin nasara kuma likita ya tabbatar musu zata dawo cikin hankalin ta saidai har yanzu bata magana muryarta rawa yake bai fita sosai sakamakon sha'ke mata wuya da Asad yai a wancan lokacin.
Ranar da Mami tayi musu zancen tafiya gidan da yake suma a matse suke a ranar sukai duk abinda ya dace washe gari suka biyo jirgin sassafe suka dawo Nigeria saidai a Abuja international airport anan suka sauka dama already tun kafin suje Mai martaba yasa motocin taryarsu sunje suna sauka ba 'bata lokaci daga airport d'in Abujan suka wuto Kano.
Wani wuri a cikin asibitin inda aka rubuta silent please🙏 da manyan ba'ki wata qofa likita ya bud'e yana shiga zaune ya tarar da Khimiyyah a gefen gadon ta jingina bayanta da bango murmushi yai yana karasawa ganin aikin dayai mata kullum sake samun sau'ki take saidai abu d'aya ne wato har yanzu bata magana amma idan kayi mata zata nuna alamar tasan abinda kake cewa zama yai akan kujerar dake kusa da bed yana bud'e file d'inta ya d'auko certificate d'inta na wata takarda da aka kawo masa yanzu yana bi a hankali yana duba meya kamata gaba ayi mata dan a samu ta karasa warewa kamar daga sama ko a mafarkin haka yaji saukar muryarta tace.
"Doctor ina son zamuyi wata magana ta sirri dakai batare daka sanar da wadanda suka kawo niba dan Allah ya zama sirri tsananin mu har abada kayi min wannan alkawarin🤲"?.
A zabure cike da tsananin mamaki doctorn ya d'ago yana kallon ta kafin ya bud'e baki yace "yaushe kika fara magana ko yanzu"?.
Kaita d'aga "eh doctor yanzu ne na fara duk da na dad'e da farfad'owa kuma na dad'e da sanin inda kaina yake hankali na ya komo jikina duk abinda ka nuna min zan fad'a maka meneshi dama dan 'yan uwana suna gurin ne shiyasa na'ki kulaka duk abinda kake tambaya tak sakamakon bana so susan cewa na dawo cikin hankalin nawa sosai zanyi amfani da wannan damar nayi wasu abubuwa amma saida taimakon ka please doctor"?.
Kai ya d'aga mata yana cewa "ok Ina jinki me zakice wanne abu zakiyi"?.
Huci Khimiyyan ta fitar tana jin ina ma ace yanzu tana gida dama ace an sallamesu sun koma masarauta hummmm 'kwafa tai tana kallon doctor tace "d'aukar fansa😠😳".
Cikin rashin fahimta doctor yace "ban gane d'aukar fansa ba me kike nufi"?.
Rufe idonta daya fara kad'awa tai tana cewa "Ina nufin zan d'auki fansa ne akan wanda yai min haka amma saida taimakon ka".
Gyara zama doctor yai cikin mamaki yace "oh wai dama mutum ne ya miki haka subahanallahi wanne irin jarumi ne kuwa tabd'ijan wallahi Khimiyyah all my thoughts ko daga irin benin na mai tsawo kika fad'o lokacin dana fara yi miki aiki haka nayi tunani"?.
Kai Khimiyyah ta girgiza "no mutum ne shiyasa nima nake so nayi amfani da wannan damar na rama abinda yayi min ta hanya mafi sau'ki doctor abinda zance maka shine zaka fad'a ma wadanda suka kawo ni"?.
Kai doctor ya d'aga yana cewa "ok ina jinki fad'i duk yadda kike so ace musu nikuma I will try to do my best na ganin na fad'a musu komai har su yarda da abinda na fad'a".
Murmushi Khimiyyah tai tana jinjina kai tace "doctor so nake ka fad'a musu cewa na samu lafiya na warware na dawo daidai amma game da wankin 'kwa'kwalwa da akai min dole wata rana ciwon zai d'an ri'ka tashi ana yimin uziri wasu lokatan bana cikin hankalina nake yin wasu abubuwan kuma koda a furuci ne shin doctor zakai min wannan taimakon"?.
Kaiya d'aga mata yana gyara zama yace "ok babu damu I'll but dole saidai na soke wannan papern na yau ayi wata ta qarya domin wannan result d'in ya nuna kin samu cikekkiyar lafiya ta haqiqa babu sauran matsala kinga idan aka basu ba damar dazan fad'a musu abinda kike so ayi miki kuma sa'a kikai naje reception nemansu naga basa nan maybe sun d'an fita da yanzu na basu takardan".
Zaro ido Khimiyyah tai tana sau'ke ajiyar zuciya tace "gara da basa nan doctor alhamdulillah na gode sosai da wannan taimako".
Mi'kewa doctor yai yana cewa "ok no vex🌹 karki damu ai dama muna irin haka a patient's😷 d'in mu bari naje office saina sake takardan" yana fadin haka ya bud'e kofa ya fita wani irin murmushi Khimiyyah ta saki tana jinjina kai tare da haskota sanda ta koma gida za'ai bele'u dan saita hana kowa zaman lafiya idan zata d'au fansarta komawa tai kwanta kawai tana tunano lokacin da Asad yake tumurmusarta da dukkan qarfin sa🤪😂 mtswww taja tana gyara kwanciyar ta kafin doctor ya dawo ta sake fad'a masa wani abu guda data manta bata fad'a masa ba.
🏕️'KAUYE 🏕️
Ilyah na zaune a kofar gidansa wani yaronsa daga cikin yaransa dake masa aikin bin kasuwanni da kayayyaki yana zaune a gefensa da kud'i Mai mugun yawa yana 'kirgawa dami dami Hassan da Hussaini suka fito ganin yasa suka tsaya Hassan ya kalleshi yana cewa.
"Wai baba Ina maganar mu ta kwana ne yarinyar nanfa ta dawo tayi kyau ta zama 'yar birni kaje kada wani yamin shigar sauri wallahi da saidai garin nan ya kama da wuta dan sai anyi mummunan ya'ki akan Amatu zan iya kashe mutum gara makaji ka sani".
Kallon sa Ilyah yai cike da fargaba kamar baisan akan me yake maganar ba cikin basarwa yace "batun mu name akan me kake magana yaushe zaku koma neman kud'in ku kafin ku dawo zansa a Gina muku manyan gidaje wanda babu irinsu a 'kauyen kuma ku auri duk yarinyar da kuke so?.
Ta'be baki Hassan yai shima jin yadda Ilyan ya kamo wani shafin da ba zancen suke ba yace "batun aurena da Amatu nake maka maganaa akai ba gini ba in a ruwana da gida idan zan gina bana bukatar taimakon ka koda bulo daya ne zanyi da kaina nidai damuwata kaje mun ro'kon arziki sonake a had'a bikinmu dana wannan shegiyar 'yar taka Nafisa idan kuma ba haka ba wallahi saidai itama a fasa natan sai lokacin daka amince da namu idan ka'ki zamu Bari sai saurayin nata yazo mu tumurmusa shi agabanka muyi masa tsinannan duka mu faffasa masa glass d'in motarsa sai naga ta tsiya haba idan banda gidadanci anace maka ga gabas kana ga yamma ana ga ruwa kana ga wuta kodan bari na sake maimaita maka watakila kud'i ya fara susutar maka da 'kwa'kwalwa cewa nai magana nake maka akan Amatu yar gidan kawu Habubakar gashi ta dawo so nake na aureta mubar nan garin nan ya isheni kandin kifi zanyi daga ruwa na koma mai Ina aurenta zaka nemi ni ka rasa nayi can zanje na bud'e sabuwar harka da sabuwar duniya yanzu Ina tunanin ka fahimta tunda nayi maka magana da yaren da zaka gane"?.
Takaici ne da ba'kin ciki suka rufe Ilyah yana kallon Hassan zaiyi magana Hussaini yace "yauwa Hassan fad'a masa dai baba Nima dai ta Hassan d'infa Ina maganar auren mu akan Aisha ta kwana domin gaskiya na matsu nayi aure kuma dai rana d'aya zamu bar nan kawai yanzu ka tashi muje tunda ga kud'i nan a gabanka kamar yayi kawai ka mike muje tare guri kawu Habubakar yanzu ayi neman auren nan a gabanmu tunda kawu Habun babanmu ne ba surukin muba".
Mugun had'e rai Ilyah yayi yana kallon su cikin 'bacin rai yace "wallahi babu inda zanje nemawa kowanne shege a cikin ku aure tunda baku da hankali baku mayar dani komai ba ai na dauka zaku iyayin auren batare da neman shawara taba sai kuje kuyi naga da yadda zakuyi d'in shashashun banza mahaukatan wofi wannan ba'kin cikin da kuke sani saikun gani kuma a 'kwaryarku".
Kallon juna sukai suna ta'be baki jin abinda yace kafin Hassan ya jinjina kai yana cewa "Aiko wallahi baba tunda kace haka zakaga yadda akai tijara mun shiga birni mun waye ba wani so'ko'kon dazai fad'a mana wayewa a garin nan banda matata Amatu Dan haka ko alkali sai munje ya d'aura mana aure dasu kuma zaka gani Hussaini zo mu tafi dan idan naci gaba da tsaiwa anan yadda baba yake karanta min wannan gidadancin zan iya wanka masa mari😲😳 mu tafi kawai na daina ganinsa kafin na fusata".
Dariya Hussaini yai ganin yadda Ilyah ya zaro ido sai kawai ya du'ka yana d'aukar d'aurin kud'i guda daya a jikin 'kyaro yace "wannan zaikai dubu hamsin Dan haka mun d'auki kud'in zance nida Hassan yau kaine zaka biya mana kud'in hirar da zamuyo" yana fad'in haka suka wuce muryar illyah na rawa kamar zai fashe da kuka yace.
"Hussaini ka dawo min da kud'in nan Kona tsine maka"?.
Waigowa Hussaini yai yana cewa "tsine min d'in mana idan ka tsine min nabi duniya wayai asara bayan kai ka rasa" yana kaiwa nan ya juya da sauri yaci gaba da tafiya dan Hassan tuni har yayi masa nisa bai tsaya sauraron maganar ilyan ba.
GIDAN BALARABE
Asabe dai fatan ta baici ba yadda take so bai samu ba da fari boka yace mata aiki zaici harta kwantar da hankalinta akan wannan batun ta manta ma da wani ilu sai gashi kwatsam rana tsaka taga su Inna sun sauka a gidanta da asubar fari😂 da Dan d'aurin kayansu kamar yadda suka zo a lokacin Indo tashin hankali ne 'karara ya bayyana a fuskar asabe wanda batasan sanda tad'au tabarya ta bisu da ita ba tana surutai a layi tayiwa su Innah korar kare fata-fata ta'ki kar'bar ro'kon arzikin Iluh kuwa daya fita tantiranci suka had'a baki shida Bahijjah ya rakasu gidan Markah yace Asabe ce tarosu wai ta kar'bi ro'kon arziki domin tana jin kunyar Bahijjah 'yarta ce ta fari Markah kuwa tayi kiran Mairo suka kar'bi komai tare Asabe batasan komai ba sai kusan kwanan ashirin da biyar a jita-jita taji wai-wai ana tayata murna a anguwa wai ashe auren Bahijjah zatai zata bata Iluh d'an garuwa jin abinda aka cewa yasa a hargitse tayi gidan Markah kamar zata tashi sama taje tana kwala mata kira tun daga layi harta shiga gidan ta ri'ka Danna mata zagi da masifa