Showing 192001 words to 195000 words out of 195514 words

Chapter 65 - ME KAMAR SARKI HAUSA NOVEL

YUSRAH   

22 Oct 2024

27297

kome"?.

"No ba haka nake nufi kawai dai komai a sannu yake yinsa cikin sanyi kin gane"?.

"Uhmm" kawai shine abinda Shaukiyyah tace domin Khaldiyyah batasan komai ba ita kuma yanzun data sani batasan ta yadda zataiwa Khaldiyyan bayani ta fahimta ba sai kawai ta kyaleta suje a hakan zata tuna mata sai ranar datai aure washe gari itama zataje ta rama Khimiyyah kam tana gefe komai suke tana jinsu ko tari batai ba hankalinta yana kan wayar dake hannunta tana chatting da Hudayyah.

*** ** ***. ** *** ** ***
Nurain ne a zaune yana kallon Nafisa wacce idonta ya cika fal da hawaye yanata zuba ransa a mugun 'bace yace.

"Nafisat da izinin wa kika je kika zubar da ciki batare da sani naba dama nace miki bana son haihuwa ne ko kuma rainin wayo ne yasa kika aikata min haka"?.

Yana rufe baki ganin Nafisa ta kallo su Mimih tana shirin magana da sauri a gaggauce Zainab ta hana Nafisan dake shirin cewa wani abu ta zafga mata wata uwar ba'kar harara tana cewa "ke kinga ki rufawa mutane baki banza kawai jaka 'yar qauye wacce batai karatun addini ba jahila tsabar ke da'ki'kiya ce zakije ki xubar mana da babynmu yau saikin gane gaskiya kin cuce mu" ta karasa maganar tana kallon Nurain daya sake fusata kamar zata she'ke da dariya tace.

"Kuma abun haushin my choice nima har ina murna da farin cikin Auta ta kusa samun qani sai kuma na dawo aiki naji su Mimih suna cewa wai sunga Nafisa ta dawo daga asibiti da takarda a hannunta tana kuka da suka tambaye ta tace ciki gareta bata so ka sani dan Allah su rufa mata asiri tsabar gidadanci da qauyanci batasan cewa in ciki ya fita dole sai an gane ba humm gaskiya Nafisa baki kyauta mana ba kinyi mana asarar babyn mu" ta karasa maganar tana kau dakai gefe sakamakon dariyar dake ciciyarta ganin yadda maganar data fad'a ta sake sanya Nurain zabura ji yake kamar ya d'aga hannu ya sharara mata mari kasa-kasa Zainab take dariyar mugunta ganin yadda Nafisan tayi shiru ta kasa magana sai hawaye dake zuba tace.

"Kayi hakuri my choice tunda cikin dai ya riga ya fita shikenan saidai ai mata uziri kasan mutum idan bai karatu ba matsalar auren jahila kenan batasan doka ba inaga saidai ka sata a makarantan islamiyyah amma dai yanzun kayi hakuri idan ta sake ka d'au mataki me tsauri a kanta dan gaskiya babu wanda za'aiwa irin wannan abun bai d'auki hukunci ba".

Shiru Nurain yai ya kasa furta koda kalma d'aya tsabar ba'kin cikin da Nafisa ta cusa masa Mimih data d'auko littafi kamar gaske dan taji abinda suke tazo wucewa da sauri ta tsaya tana cewa.

"Ai yaya idan baka sani d'auko tan dakai daga wannan mummunan qauyen ka kawota tsakiyar birni baiyi mata amfani tunda gashi ba'aje ko'ina ba ta fara nuna maka ta waye ta hanyar zubar da ciki kayi tunanin gaba me zata aikata humm ba'a sani ba kawai yaya ka saketa yau ta koma karkararsu"?.

Mimih na rufe baki Nafisa ta d'ago a firgice tana kallon Nurain wanda shima ita yake kallo kai ta soma girgizawa cikin kuka tace.

"Dan girman Allah kayi dan Allah wallahi ba laifi na bane"?.

Zare mata ido Mimih tai tana cewa ''ba laifin ki bane laifin uban kine"?.

"Ke Mimih kada ki sake zaginta duk da kin fita koma dai yaya ne matar yayanki ce ita ya kamata ki bata girmanta".

Zainab tai maganar tana kashe mata ido murmushi Mimih tai kamar gaske harda d'an risnawa tace.

"Oh sorry na manta ne 'bacin ran rashin babyn mune yasa nace Mata haka kiyi hakuri Aunty Nafisa na😂" ta karasa maganar tana sakar mata zazzafar harara ganin ta d'ago tana kallon ta kafin ta kad'a kai tayi gaba Mimih na wucewa Zainab tace.

"My choice kayi hakuri kar kasa damuwa a ranka komai ya wuce".

Tsaki Nurain yai batare daya kalli inda Nafisan take ba dan ko ganinta yanxu bai son yi muryarsa da alamar fushi yace.

"Get to the point".

Tsiru-tsiru Nafisa tai domin batasan me yace ba kuma bata kawo da ita yake ta d'auka ko tsakaninsa ne da Zainab saida taji cikin tsawa yace.

"Ki 6ace min da gani kafin na 6allaki" jin abinda yace yasa da gudu Nafisa ta mi'ke tana kuka tabar falon tsaki ya sake ja a karo na babu adadi yana cizon yatsa Zainab kam tana gefe sai murmushi take tana rausaya kai mi'kewa yai zai fice yace.

"Ina da tafiya zuwa Singapore ranar Monday ki kira Mimih yanzu su d'auko Auta zamuyi sallama dasu"?.

Kai Zainab ta d'aga "ok my choice amma idan babu damuwa ka biya min kud'in jirgi na zuwa sai nayi na dawowa ina son zanga qasar please" ta fad'a a marairaice.

"Ok shikenan" shine kawai abinda yace mata kafin ya fice tsalle Zainab tayi cike da murna domin tasan tunda ransa ya 'baci indai baiyi nesa da Nafisa ya huce ba tofa akwai matsala shiyasa take so ta bishi su tafi tare taje ta d'auke masa hankali su dad'e basu dawo yadda Nafisan zata gaji ta gudu qauye koda tasan ma bazata iya zama ba domin su Mimih bazasu barta Tasha koda ruwa ba tsabar wuyar da zasu d'an'dana mata.

🌑🌚INSIDER🌚🌑
BAYAN WATA HUD'U
_____Khimiyyah ce zaune tare da Hudayyah a gurin Muheed dake d'aure Hudayyah na sake jaddada masa cewa har yanzu yana da damar cewa yana sonta zai aureta shima yana fad'a Mata kalma d'aya bazai ta'ba auren taba koda ace zai rasa rayuwarsa ne.

Gurin Prof Jibril da Mr Famous dake gefe Khimiyyah tayi ga kuma Danual Chai daya koma wata kalar siffa a gabansu yana fad'a musu sirrin daya sake binciko musu ta yadda mutum zai iya zaka kowacce halitta yake son komawa karaawa tai tana cewa.

"Daddy please kayi wani abu akan wannan yarinyar yanzu fa maganar da nake maka tana cikin masarautar mu ta auri wannan ma'kiyin cousin d'in nawa wanda ya kusan kasheni sannan itace masaniyar wannan 'kungiyar tamu ka gaggara d'aukar mataki a kanta kasan cewa fa wanda aka aura mata yana son samo inda muke kayi tunani daga ranar daya gane da akwai sirrin mu a hannun wannan yarinyar akwai matsala fa shikenan mun fad'a tarko kuma shi mutum ne mai matukar fikira wanda ba'a iya tararsa ya gagara idan muka bari sai bayan yasan bayanan mu zamu d'au mataki tofa gaskiya bazamu iya ba sannan mun rusa tasiri da qarfin da muke dashi bayan haka Ina alkawarin da kuka d'aukarwa shugaba Diranah kafin ta baku amanar 'kungiyar ta sadaukar da ranta saboda tasan ko bayan bata nan zaku iyaji da koma wanene mai son ganin bayan kungiyar da maison ta rushe wannan sadaukarwa da shugaba Diranah tayi ya kamata a girmama hakan ta wajen ganin an sake sabon tsari ta yadda zamu sake komai ta inda ba'ai zaton mu ba baza'a iya gano mu ba mu qarawa qungiyar mu karfin da duk wanda yace zai tukareta zai hallaka ne ya zama mun sake tashi tsaye muma mun jajirce fiye da da abin kunya ne ace duk yawanmu mun kasa baiwa 'kungiyar mu tsaro yadda ya kamata abu na qarshe please Daddy ka goge dukkan bayan da ka sakarwa wannan yarinyar domin itama jar wuyace jaruma ce barazana ce ga kungiyar mu".

Ta karasa maganar tana kallon Prof wanda ke gyad'a kai kamar yana jin music🎶.

"Daddy magana nake ba kace komai ba"?.

Dariya Prof yai yana dad'a risawa kamar mai sonyin rawa yana kuma kallon yadda tsafin da Danual Chai ke nuna musu kafin yace.

"Never mind kada ki damu Khimiyyah kema jaruma ce sannan bazumu kasa ba wannan kungiyar a shirye take taga bayan koma wanene yake son ganowa babu wani abu da 'yan tawagar mu baza taji dashi ba kin gane zan d'auki mataki amma kafin nan a daren yau zan saki shafinta na internet sannan zanyi amfani da wannan damar naga abinda nake hari ya yuwu idan tarkon mu ya kama kurciya guda biyu tofa fa'kat karshen magana bamu da wani tashin hankali sama dasu biyun nan kowa ya gajiya yayi laushi cikin lamarin mu wasu sun ha'kura my a sun qaryata cewa babu mu zamusa hakan yayi aiki ace babu mudin a dakatar da masu binciken mu mukuma a daidai wannan lokacin ne zamu bayyanawa mutane muyi ta'bargaza mu kashe na kashewa mu d'ebo na debowa mu karawa qunkiyar mu qarfi kinsan da jini take aiki"?

Kai Khimiyyah ta d'aga "ok Daddy na gane amma fa sar'kar daka bani na rasata sam kuma kaga dole saida ita zan samu damar shigowa nan".

"Wannan ma nasan da haka muna so zamu sake sabuwar sar'ka ne Mai tambarin sifelin din sunan kungiyar mu sannan za'a rabawa kowanne d'a 'kungiya ta yadda idan za'ai taro ka sani inda matsala ka sani kin gane ko"?..

Kaita d'aga "eh na fahimta Daddy" ta fad'a tana mayar da hankalin ta kan Hudayyah ganin ta saita Muheed da bindiga zata harbeshi yasa da gudu taje tana fisgewa tace.

"Haba Hudayyah me kike yi wannan gayen shine rayuwar idan kika kashe shi ke kuma kiyi yaya"?.

Fashewa da kuka Hudayyah tai tana dur'kusawa a gurin tace "ai dama na ha'kura dashi ne zan kashe shi tunda baya sona sannan Nima na kashe kaina domin rayuwata batare dashi ba batada amfani ki bani bindigar nan Khimiyyah''.

Ta fad'a a zabure ta mike tana kokarin kar'ba hanata Khimiyyah tai tare da janyeta daga gurin Muheed tayi wani 6angaren da ita domin ta rarrashe ta.

🌃 MARSHALL ISLANDS🌃
_____Marshall islands misalin qarfe d'aya da rabi na dare Asad yana zaune a bedroom baiyi barci kawai laptop ce gabansa yana aiki iya Isham ne kwance ya bararraje yana sharar barci ya rufe jikinsa duka da bargo jin Isham d'in yana magana yayi tunanin ko farkawa yai amma sai yaga ya sake juyi kai ya girgiza yana mayar da hankalin sa fuskar laptop d'in..

"Asad wai dan Allah miyasa baza ka ri'ka hutawa ba"?.

Isham ya fad'a cikin muryar barci yana kallon sa batare da Asad ya juyo ba yace "kayi barcinka Isham yau ranar dabam take nafi ko yaushe d'aukar zafi kawai ka kyale".

"Ok shikenan Asad Allah ya taimaka" ya fad'a yana komawa ya kwanta.

Asad bai sake magana ba ya juya kan abinda yake shiru Isham yai yana kallonsa gaskiya Asad ya damu yana matukar bu'katar hutu saidai yasan bazai ta'ba hutawa ba harsai yaga ya samu wannan yarinya.................................

Katse masa tunani Asad yai ta hanyar mi'kewa dayai yana kallon laptop da tsananin mamaki yace.

"WHAT"?.

Zabura Isham yai yana tashi zaune shima dai yaga abinda ya tada hankalin Asad d'in da sauri ya wullar da bargon ya diro kasan carpet tare da 'kure laptop d'in da ido yace.

"Asad me nake gani wannan abinda kake nema ne ai ya fara samuwa gashi bayanai ya fita yar Nigeria ce ita kuma cikin masarautar ku fa innalillahi amma wacece Asad wa kake tunanin zata kasance nasan dai ba'a cikin bayi bane a ina take ko a cikin sisters d'inka ne"?.

Shiru Asad yai ya zubawa laptop d'in ido cike da tsananin mamaki d'agowa Isham yai ganin abinda yake kallo yasa yace.

"Asad say something mana kayi magana did something scare you"?.

Kai Asad ya girgiza masa baice komai ba har lokacin sai zama dayai yana yin copy d'in bayanan nan saida ya gama sannan ya d'ago yana kallon Isham yace.

"Isham zanje gida yanzu".😳

Zaro ido Isham yai yana kallon sa kafin ya kalli agogo yana cewa "Asad gida kuma a yanzu haba dai qarfe biyu fa da mintuna ka bari gari ya waye"?.

Kai Asad ya girgiza "no Isham I cannot a yau zan tafi bazan jira gari ya waye min anan ba tashi ka kaini airport".

Mi'kewa Isham yai yana cewa "ok Buddy muje" rufe laptop d'in Asad yai yana d'aukar wayarsa suka fita a wannan tsohon daren Isham yad'au mota yakai Asad airport sannan ya dawo gida shima bai iya komawa barci saboda taya Asad d'in murna ganin abin nemansa ya fara samuwa.

*** 👑PALACE👑 ***
__________________________
________Mami tana zaune a parlonta ita kad'ai da safe tana waya da Aunty Fadilaty da murmushi a fuskarta ganin an bud'o kofa yasa ta mayar da hankalinta kan kofar Asad ne yashigo yana tsayawa bai karaso ba ya qame daga nesa fuskarsa ba walwala ya sanya hannuwansa a cikin aljahun wandonshi ya tsume ya kame guri d'aya sauke waya Mami tai tana kallon sa cike da tsananin mamakin yaushe ya dawo ko jiya da dare ya shigo tofa ai ta d'auka sai yayi shekaru baizo gida ba saboda abinda Ajeeb yayi masa d'an murmushi Mami tai tana cewa.

"Asad lafiya dai miya faru ya ka tsaya anan ko wani abu ne? ka shigo man yaushe ka dawo"?.

Qarasowa yai yana mata sallama ya zauna tare da gaida ita amsawa tai tana sake qare masa kallo lallai ba qalau ba yanayinsa ya nuna kamar akwai damuwa,.

Da kulawa irin ta uwa da d'anta ta sake ri'ko hannun sa tana cewa "Asad lafiya ina nufin kana cikin walwala naga kamar naga akwai abinda ke damunka haka ne"?.

'Dan rufe ido yai yana sauke wani irin numfashi a ransa yana tunanin taya zai fara fad'awa Mami abinda ya kawo shi zatai masa kallon kamar duk da bai nuna kulawarsa ba saida ya tashi buqatarsa ta kawoshi..................

"Asad wai lafiyar ka qalau kuwa"?.

Kai ya d'aga a hankali muryarshi ba kamar kullum ba da alamar akwai matsala yace "Mami ina son kimin magana wannan yarinyar"😳.

Tsananin mamaki ne qarara ya bayyana a fuskar Mami har tana sake qureshi da kallo tace "Asad kaine ko kuwa Ajeeb ne"?🤔.

Ta karasa maganar tana sake bud'e idonta akansa tunda bayan kama da suke da juna muryarsu ma d'aya ne maybe ko Ajeeb ne ya tsume irin yanayin Asad d'in yazo tsokanar ta dan yaga mai zatai tana son tabbatarwa Asad ne ba Ajeeb ba amma ta kasa yarda cewa shine yake magana akan Amatun domin tasan babu abinda zai kawo Asad gida yanzu daga tafiya wata hud'u kawai saidai in larura amma sai tace bari ta gwada wani abu dan ta gane waye ne a ciki tace.

"Asad lafiya kake nemanta"?.

Murya can qasa yace "eh kimin magana da ita ki tambaye ta tana amfani da laptop ne"?.

Kai Mami ta girgiza tana cewa "Asad meyasa ka fiya jin kaine? kai mezai hana kaje ka sameta ka tambaye ta sai nice zanyi maka jagora"?.

"Eh Mami akwai dalilin da yasa na biyo ta wajenki ki fahimta".

"Ok shikenan na fahimta saboda kana jin kunya kar ace ka'ki kar'bar auren yanzu kuma ka dawo ta ra'bi zaka amsa"🤭"?.

Kaiya girgiza da sauri har yana zabura yace "noo Mami ba haka bane ba nazo dan wata manufa bane har gobe Ina nan akan bakana yarinyar nan ba matata bace kawai akwai wasu abubuwa da nake son na tambaye ta shiyasa nake so nabi ta gurinki ki had'a ni da ita bana son ayi min wani kallo dabam".

Kai Mami ta jinjina tana "Me zaka tambaye ta"?.

"Magana ce tsakanin mu dan Allah Mami kimin wannan duk burina yana a haka a abun dake wajenta idan itance amma saida taimakon ki".

"Asad maganar gaskiya indai ba kar'barta kayi matsayin matarka ba had'uwar ku bata wani da amfani baka da abinda zakace mata dan haka bazaka ta'ba ganin taba Asad na gaji da wannan karka mayar damu qananan mutane kawai ka rubuta mata sallamarta😣".

Shiru Asad yai nad'an wani lokaci har Mami ta cire ran zai sake mata magana sai kuma taga kalleta yana cewa "Mami ni bani da ala'ka da wannan aikin Ajeeb ne domin ba matata bace mine tsakanin mu dazan bata sallama indai zaman jirana take zata iya tafiya gidansu yanzu bazan ta'ba waiwaye ko kallonta da sunan wife d'ina ba please Mami try to understand dan Allah🙏.

Sosai Mami ke kalloshi jikinta yayi mugun sanyi ta rasa me yasa Asad yake a murd'e indai ba shine yay ra'ayin abu ba tofa akwai gagarumar matsala......,...

"Mami baki ce komai ba"?.

"Humm to Asad mizance ka karya min duk wani qarfin gwiwar da nake dashi akan kamar nan gaba zaka yarda ka sauko ka kar'bi yarinyar nan amma sai naga sa'banin yadda nake zato da fatan kasancewa? Shikenan Asad ka kyauta saidai ka sani gaskiyar lamari bazan iya maka abinda kake soba kayi da kanka"🙄 mi'kewa tai zata bar gurin Asad da yaji zuciyarsa ta tsinke yace.

"Mami ina zakije please ki saurare ni ina da babbar hujja akan 'kin kar'bar auren danai babu wanda zai amincewa uziri na idan baki saurare niba keda Abba"?.

"A'a Asad baka da wata hujja akan wannan bazan maka uziri ba kawai ka rufe min baki ka mayar da hankali ka tsaya kayi tunani idan kayi haka ka juya dason bijirewa abun ba d'an uwanka Ajeeb dayaga ya isa dakai ko mai nasara ba hatta mahaifan yarinyar nan baza suji dad'i ba domin ba'a auri 'yarsu dan a wulakanta musu ita ba kuma kai naga alamar yunkurin ka kenan tun farko rashin sani yaja komai da nasan dakai ne za'ai auren dama Ajeeb ba yana komai dan kansa bane toda zan dakatar dashi karya soma kawai ya aureta zaifi wa kowa kwanciyar hankali to mai faruwa ta riga ta faru bansan akai Ajeeb kewa ba wallahi da ba'a kawo wannan matakin da muke kai yanzu ba kodan yanzun ma bata 'baci ba Asad ka saketa a mayar da auren nan kan Ajeeb😲 zanfi samun nutsuwa a kanka domin dama yarinya dashi tai soyayya ba dakai ba dashi ta sake dashi ta saba ta sanshi da fara'a sannan ya nuna mata kulawa wacce ta dace amma zan sake baka lokaci kaje Kayi nazari🤔 domin kana buqatar hutu sannan ka daina yin allurar nan akai akai karka ja 'kwa'kwalwarka ta samu matsala ka karasa burkicewa a haka ma ya lafiyar kura🐆 balle tayi hauka Asad kaje ka sake sabon nazari a nutse duk abinda zuciyarka ta yanke maka zuwa gobe da safe kazo ka sanar dani ina jira" tana fad'in haka ta bud'e kofar bedroom ta shige.

Idon Asad na kallon qasan kyakkyawan blue & white carpet d'in dake zagaye da parlon yayi shiru shiba tunani yake ba kuma ba maganar zuci yake ba ya dad'e a gurin a zaune ko motsi baiyi ba daga baya ya mi'ke yana

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login