Showing 174001 words to 177000 words out of 195514 words

Chapter 59 - ME KAMAR SARKI HAUSA NOVEL

YUSRAH   

22 Oct 2024

27295

yake asabar ce babu aiki haka Nurain ya d'auketa a mota tun safe bayan sunyi breakfast yace yau kuma gari zai nuna mata haka taci wanka tayi 'kwam a gaban mota tana hura hanci shikuwa mai amarsu sai murmusawa yake yana fad'a Mata duk sunan anguwar da suka zo parking yana kallon ta yace.

"Bari nazo".

Kafin tayi magana harya bud'e murfin motar ya fice ganin ya tafi gurin wani mai kayan miya gasunan jawur yagar yau gwanin kyau ya tsaya ya bashi kud'i zai zuba masa tana d'aga cikin motar ta zaro ido waje lokaci guda tace.

"Na shiga uku ni Nafisa wa nake gani acan kamar Amatu? Dama nan suka dawo da zama suma suna birni kenan innalillahi anya kuwa Amatuce ba Mai kamarta bace duk da taga itama wannan da hula a hannunta tana d'inkawa"? Tanan ta kara susucewa shiru tai cikin nazari domin wannan taga ta kara girma da tsayi gashi wannan kamar tafi Amatu fari dakyau domin ta sake tabbatarwa kanta yasa ta d'ago tana sau'ke glass daidai Nurain ya kar'bo kayan miyan a babbar leda gari yai zafi ya juyo taga fuskar malam Habu tar da idonta wani irin bugawa zuciyarta tayi da sauri ta bud'e kofar itama ta fita cikin alamun tambaya Nurain yace.

"Yadai ina zuwa haka naga kamar ba lafiya ba".

Kai Nafisa ta d'aga masa duk ta gigice tace da'kyar tace "eh lafiya ina zuwa bari nazo yanzu zan dawo mu tafi" tana fad'in haka kafin yayi magana ta zurbala tayi gaba bai bita ba kawai ya bud'e mota ya shiga ya zauna yana kallonta cike da mamaki yaga me zatai.

Tana karasawa ganin sune da gaske ba masu kama dasu bane gasu sunyi kyau da ki'ba sun haska da dukkan alamu yanzu suna jin dad'i anan ta'be baki tai tana cewa.

"malam baba Habubakari kwandon sukari🤔😳 dama daga gida da kayo gudun hijirar nan ka dawo? Dariya tai tana kallon Amatu tace "Allah hamsha'kiya meye kike min irin wannan kallon kodai kinyi sha'awata ne kin ganni tare da mijina muna zaga gari a had'add'iyar mota wacce nasan har ki gama rayuwar ki bazaki ta'ba shiga cikin mota mai AC ba".

Kan Malam Habu ta koma wanda ya tsaya cikin mamakin son abun duniya irin na Ilyah wato saida ya aura mata yaron nan kenan katse masa tunani tayi da cewa.

"Baba Habubakar sana'ar kayan miya ka gudo nan kanayi ko domin ka tara kud'i masu yawa kaje kafi babana arziki ko? humm aiko wallahi karya ne nagaba yai gaba na baya gobe saidai ya tara a haka zaka qare rayuwarka cikin talauci a gaban tumatur🍅🌶 hum'um Allah ya sauwa'ke️".

Tana rufe baki Amatu ta d'aga hannu a fusace zata wanka mata mari malam Habu ya dakatar da ita.

"A'a mamana 'kyaleta duniya ce taci karenta ba babbaka dana gaba akanga zurfin ruwa badan yaya Ilyah yana wulakanta ni agabansu yana nuna niba komai bane da suma bazasu wulakanta niba amma ba komai rayuwa ce wata rana sai labari ke kuma Nafisa Allah ya shiryeki abinda zance dake kenan".

Murgud'a baki Nafisa tai tana cewa "Amin inda gaske kake nina wuce aci gaba da cinikin tumatur" ta fad'a tana she'kewa da dariya kafin ta juya tana yau'ki da rangwad'a harda sauya tafiya taku d'aya bayan d'aya taje a yangace ta bud'e mota ta shiga Nurain yaja yayi gaba bai tambaye taba Saida dukai nisa sun kusa gida yace.

''wai dama kin sanshi ne naga kin tsaya kuna magana"?.

Kai Nafisa ta d'aga tana murmushi tace "eh na sanshi wani talakan fa'kiran mabaracin qauye ne da daya zauna a garin mu daga baya yayo gudun hijira ya dawo nan ya 'buge da tallar tumatur a kan tebur waishi ala dole saiyayi kud'i da qarfi" ta fad'a tana dariya.

Da sabon mamaki Nurain yace "ai kuma yayi kuskure zafin nema baya kawo samu, to amma kuma tsaya ai naga wannan budurwar ta kusa dashi dake zaune tana d'inki naga ta mi'ke xata kawo miki mari ta fasa meyasa"?.

"Humm wai dan nace idan domin ya tara kud'i ya baro qauye a haka zai qare shine take shirin marina ya hanata naso ya barta ta d'ora hannunta a jikina yau da taga yadda ake wasan 'kyawwa🐈 da 'bera🐀 wallahi sai tayi kwanan bayan kanta".

Sauke ajiyar zuciya Nurain yayi bai sake cewa komai ba har suka karasa gida da yake ba girkinta d'aya da Zainab ba kowa nata take yasa Nurain ya tsaya a main parlor yace Mimih taje kitchen d'in Zainab ta d'auko abu su raba kayan miyar nan taji haushi ji take kamar ta rufeshi da duka saboda ya aiketa a gaban Nafisa wacce tai kiru-kiru a gabansu cikin tsoron irin kallon da suke aiko mata.

Saida Mimih ta d'auko yasa dole itace ta raba kamar ta fasa masa ihun takaici ta d'auka takai kitchen d'in Zainab tana fitowa ya mi'ke yana cewa.

"Ki kawo mata nata itama kitchen d'in part d'in ta yanxu kiyi mata blending d'in wasu wanda zatai mana amfani dashi yau kada kisa yaji sosai a markad'en domin bata so kodan ta riga ta gaji mun dawo daga xaga gari ki mata jallop rice kisa mata isashshan mai kifi iya ita xaki dafawa banda ni domin baci xanyi ba fruits zansha idan kin gama kimin magana kin gane "? Kai Mimih ta d'aga zuciyarta na turiri ji take inama zata jita free ba Nurain ta kama Nafisa kila yau a gidan nan sai tayi mata qaramin rai wucewa sukai Nafisa da tasan dawar garin jikinta sai rawa yake gashi bakinta yayi nauyi balle tacewa Nurain d'in ya bari zata d'auka harda share d'an sauran hawayen ta na tuna irin ba'kar u'kubar da zasu d'an'dana mata idan ya fita.

Kai Mimah ta d'aga tana cewa "wai me ya Nurain yake nufi kece zakiwa wannan village girl d'in girki taci yau kutumelesi tabd'ijan aiko ya d'ebo Mata ya'ki zataga tijara muje kitchen d'in nata yau zataci uban daya haifeta kafin gobe ya bar gidan muje mu soya mata aya a hannu muje kitchen d'in.

D'aukar basket din kayan miyan Mimih tayi suka shiga part d'in Nafisa basa falo suna bedroom dan haka suka wuce kitchen Meelat dake jinjina kai tace "ku tsaya kuji zamuyi mata girki amma ba wanda zai ciyu ba tunda ya Nurain yana gidan saimu 'bullo da dabara musa hikima cikin al'amarin".

Cikin rashin fahimta Mimih tace "ban gane me kike nufi ba taya zamuyi mata abincin da basai ciyu ba"?.

Kai Meelat ta d'aga tana cewa "tsaya kiga abinda abun zai faru da fari bari na d'ebi attaruhu da tattasai masu yawa gashi nasa a blender ke Mimih kunna ki markad'a yauwa mimah d'auko mana katon kifi a fridge nikuma tsaya kigani" gaban gas taje ta kunna tare da zuba manja mai yawa sosai sannan kayan miyan da Mimih ta markad'a ka kar'ba ta juye a ciki dama ba sannan tace.
"Mimah kisa safa a hannunki wannan kifin ki d'an cicciro mana tsokar jikinsa yana d'anye" ta fad'a tana kashe gas d'in ta sauke tukunyar gefe ta d'ora wata da ruwa kadan a take ta d'ebo shinkafa babu wankewa tasa a cikin ruwan ta rufe tafasa daya tasa kwando ta tace babu alamar shinkafar taga wuta maida wancan tukunyar farkon tai tana juye shinkafar akan wannan manja da kayan miyar sannan ta karbi tsokokin kifin da Mimah ta cire ta watsa a ciki tare da rufewa batasa Maggi ba sai uban gishiri yakai rabi gongoni ta juye tare da gaurayawa dukka ta bari shinkafar ta hade jikinta da kayan miyar duk da soyata tai ba ruwa kuma ba dafi a ido kyau kad'ai ga tsokar kifi nan manya manya amma fa a baki dakaci wannan gara kayi kwanan yunwa sau d'ari karamar cooler ta d'auko ta juye shinkafar a ciki ta rufe tare da sau'ke numfashi tace.

"Tom saura juice🍹 ya rage mana".

Da mamaki Mimih tace "juice kuma meelat dama mu bayinta ne"?.

Dariya Meelat tai tana cewa "ayya Mimih na kwantar da hankalin ki bari kiga kalar dazan mata wanda na tabbata tayi kur'ba d'aya idan ta gigice humm ku kalleni kawai" ta fad'a tana d'ebo attaruhu da tattasai tasa a blender tasa albasa da citta sannan ta d'ebo gishiri tasa ta saka ruwa kadan ta rufe ta markad'a su sosai saida suka had'e jikinsu sannan tace abun tace shayi ta tace ruwan ganin yayi ja fau baiyi kala da wani juice sosai ba yasa ta d'auko spiece mai kalar yellow ta saka saiya haska yayi kamar juice din abarba da kwakwa juyeshi a babban jug tayi tana kallon su tare da d'age gira tace.

"To kunga yadda ake girki ko yau zakaci ubanta muje d'aukar kuular Mimih tai Meelat na ri'ke da jug din suka shiga falon da sallama Nurain yana zaune suka wuce dinning area suka aje suna dawowa da ido Meelat tai musu maganar cewa karsu tafi su tsaya suga abinda zai faru zama sukai kamar gaske suna taya Nurain dake zaune kallo.

Nafisa tana zaune a bedroom tana waya da Bara'atu ta manta da wasu su Mimih da Nurain yasa suyi mata girki sai dariya take tana cewa.

"Wallahi Umma da gaske nake d'azun nan mun fita yawon ganin gari da Nurain kamar a mafarki munbi ta wata anguwa saiga baba Habubakar a gaban tebur da Amatu kusa dashi na takaice miki magana a gurinsa Nurain ya sayo mana kayan miya yau wallahi nikwa da Nurain d'in ya tambaye ni waye shi nace masa wani fa'kirin mabaracin qauye ne ya taso ya dawo nan da yaga barar bazata kaishi ba ya 6uge da sana'ar tumatur".

A tare suka kwashe da dariya Bara'atu harda doka kafa cike da jin dad'i tace "yauwa yar albarka nagode miki da baki nuna kanin ubanki bane balle ya taimaka masa ko ya ri'ka masa alkairi baki sani ba idan ya biyo layin hummm Habubakar a birni share Nafisa zanga uban dazai tara ya dawo dashi qauyen muna nan muna jiran dawowarsa a tsiyace kamar yadda ya tafi kada ki damu kinji kedai kisa ido sosai ki tabbatar kinsan sirrin dukiyar Nurain kinji" to Umma saida safe Nafisa tace Bara'atu dake Shirin mi'kawa Ilyah wayarsa tace.

"To Nafisa mu kwana lafiya amare mutanen binni uhm ana can ana jin dad'i nifa tun ranar ta tambaye ni wai yaya bikin Salma anyi nidai nace mata a'a bansan miyasa aka d'aga sosai ba".

Ta'be baki Ilyah yai yana cewa "tunda ita ce ta nace sai Adamun nikam ina ruwana ranar ma saida na samu fa'kirin uban nasa akan zancen auren amma cewa yayi wai na kara musu lokaci wallahi abubawan har yanxu sun rasa yadda zasuyi babu kud'i maganar da nake miki a yanzu kam Adamu baya gari wai ya tafi neman kud'i kona sadaki ya samo".

Kai Bara'atu ta jinjina tana cewa "hum'um ni dama da Maimuna zataji shawara ta da sai Salma ta had'a kayanta ta tafi gurin Nafisa ko wata biyu ta samu idan akai sa'a itama sai kaga ta samu miji acan ta huta zaman wahalar da take nemawa kanta domin auren irin su Adamu matalaunta wanda talauci ya gama samun gurin zama a jikinsu bala'i ne amma tunda tana sonshi bazata ga haka ba".

Kai Ilyah ya murgina yana cewa ''nikam ba ruwa na ainace idan ya kasa ri'keta bazan taimaka mata dako lomar abinci ba tunda ta yarda ai shikenan ga fili ga mai doki sannan da kike maganar wai ta had'a kayanta ta tafi gurin Nafisa so kike taje suyita wannan shegen fad'an nasu acan tasa Nurain ya sakota kinga an 6ata biyu ko ita bata auru ba taje tasa an sako wacce tayi"..

Zaro ido Bara'atu tai tana cewa "kuma fa haka ne gara da Allah yasa kayi wannan hasashen da wuri nikuwa har nasa araina Maimuna tana dawowa daga tafiyar nan zan fad'a mata tona fasa kowa yayi zamansa a inda yafi so nasan ko yanzu Nafisa tazo tafi qarfin raini bata da sa'ar gwaji a garin nan"..........

Shiru Salma tai duk abinda suke fad'a tana jinsu sun manta tana d'aki kuka kawi takeyi mara sauti tana share hawaye kuma abinda tasa a ranta shine zata auri Adamu koda ace kullum saiya fita ya nemo da aci zata zauna dashi zaman lafiya yafi zama d'an särkï.


Batun Nafisa Kam suna gama waya ta gyara kwanciya tana kunna kallo a waya Nurain ya shigo bedroom din yana kallonta yace.

"Ok na d'auka kinyi barci da naji shiru kizo kici abincin sun gama miki" jiki a sanyaye Nafisa ta mi'ke kamar zata fashe da kuka ya juya yana fita tana biye dashi batai tunanin sunan nanba ta d'auka suna ajiyewa zasu tafiyarsu qamewa tai ta'ki karasowa ganinsu zazzaune suna mata wani kallo.

"Kije kici abincin sun gama".

Shiru Nafisa tai cikin zulumi kafin ta d'aga kafa da'kyar kamar mai ciwon cinya ta fara tafiya taje ta zauna duk hankalinsu suka maida kanta ta yadd Nurain bazai fahimci komai ba bud'e kuular tai a bisa dole taga abincin d'an mitsitsi da'kyar in zata koshi juyeshi tai duka a plate tasa cokali amma me lomarta daya tana taunawa da sauri ta fito dashi cike da azaba ga yaji ga qarnin d'anyan kifi ga shinkafa d'anya dagowa tai tana kallon su wata uwar harara suka zuba mata duk su hud'un wanda ba arziki ta d'auke kai daga saitinsu tanajin idonta na kawo hawaye tsabar yaji.

Tashi Mimih tai tana cewa "bari nadan sha kayan marmari a gurin Aunty na" ta karasa maganar a wayance tana zuwa dinning d'in ta zauna Nurain hankalinsa nakan TV baisanma abinda suke ba.

Zama Mimih tana kallon Nafisa tare dayin kasa da murya saboda Nurain tace.

"Ke dabba abincin namu ba dad'i ne aina d'auka dabbobi basu san daidai ba komai aka basu zasuci dan haka maza yanzun nan ki cinye wannan abincin kafin na hallakaki gobe" ta karasa maganar tana zare mata ido da sauri Nafisa taja plate a bisa dolenta ta fara tura shinkafar da'kyar tana runtse ido su Meelat suna zaune suna kallonsu ta gefen ido dariya na cinsu batare da Nurain ya ankare ba Nafisa ta cinye wannan abinci sannan ta bata juice tare da cewa ta shanyeshi tas haka ta kar'ba tana xubda hawaye ta shanye ta kuma hanata bud'e baki tai shid'ar yaji kawai ta nuna mata kofar bedroom da sauri Nafisa ta shige da gudu cike da azaba agigice dan taje ta samu ruwa tasha yar dariya Meelat tai a hankali tanaiwa Mimih jinjina da hannu kafin suka mi'ke suna cewa.

"Ya Nurain saida safe".

Shikam sai lokacin ma ya lura babu Nafisan a gurin amma bai kawo komai ba tunda dama sanda ya shiga yanxu ma saida ya tasheta ta fara barcin dole da tsoron kada suyi girki taci shiyasa a ransa yayi zaton ko barcin zata koma.

Batun su Mimih kuwa suna fita suka fara 'bab'baka dariya suna shewa har part d'in zainab suka fad'a mata ga abinda ya Nurain ya musu sumaga abinda sukaiwa Nafisan ta'be baki zainab tai tana murmushi batace komai lallai ta yarda da Nanah da tace mata iya meelat da Mimah sun isheta balle ga Mimih da Meenah humm tana zaune ta sani zasu kora Nafisa karkara basai tasa baki ba.

MALAM HABU
Yau Aisha tana gidan Asma'u sakamakon jiya bata da lafiya suna asibiti acan suka kwana ta haihu yau da safe mace da namiji😉 A'i da Binta suma suna can iya Saude ce a gidan domin malam Habu da sukaje asibitin ganota tare da Amatu suka dawo yadau kwandunan tumatur dana attaruhu su albasa da tattasai ya fita dasu da yake titi ne kad'ai ya raba tsakanin gurin sana'ar sa da gidansa yana ta baiwa mutane kayan miya ko zama baya samu yayi Amatu tana zaune a gefen bencinsa na zama tana d'inki hularta harta kusa kasheta.

Wata ba'kar kyakkyawar mota mai 'kirar range Rover ce ta parker a gefen titin sai 'kyal'kyali take baka ganin wanda yake ciki saidai na ciki ya ganka, tooo Bari mu le'ka muga waye a ciki.

Ajeeb ne ri'ke da sityarin motar yana kallon Ameer wanda shima ke kallonsa da mamaki yace.

"Ajeeb lafiya naga ka tsaya"?.

Kai ya d'aga masa "eh lafiya wani abu na gani bari nazo ko kazo muje tare".

"No jeka dawo ina jiranka" Ameer ya fad'a yana jingina bayansa da kujera tare da rufe ido.

"Ok bari na dawo bani minti biyar" fita Ajeeb yai yana zuwa gurin Malam Habu da sallama daidai ya gama baiwa kowa suka gaisa yana cewa.

"Dan Allah wannan 'yarka ce"?.

Kai Malam Habu ya d'aga "eh 'yata ce".

"Ok ka bani dama nayi magana da ita anan a gabanka dan Allah"?.

Nanma kai Malam Habu ya d'aga masa yana cewa "ba damuwa bismilllah".

Cikin girmamawa Ajeeb yace "nagode sosai" kafin ya juya inda Amatu take yana gyara tsayuwarshi yace "am wannan hulan na saidawa kike''?.

Kai Amatu ta d'aga "eh na sayarwa ne".

"Ok yanzu wannan d'in zatai nawa"?.

Daina d'inkawa Amatu tai tana kallon hular tace "zata iya takai dubu biyar ko shida ko kuma dubu shida da d'ari biya hawa hawa ce".

"Ok mu gani" Ajeeb ya fad'a yana kar'bar hular ya fara dubawa tayi kyau sosai kalolin zaren su fito amma yafi so ayi musu iri daya su shida mai Martaba mai girma Alhussain da su mi'ka mata yai yana cewa.

"Ina son kimin irinta guda shida duka iri daya ki fad'a min kud'in a nawa zakiyi"?.

Shiru Amatu tai zuwa wani lokaci tace ''tunda da yawa kake so zaifi sau'ki ka biya kud'i sayo yanki da zararrika saidai kawai ka biya kud'in d'inkawa idan a haka zaka saya gaskiya da tsada"..

"Ok bari to nakawo miki kud'in sai kiyi mini lissafin abubawan" to tace ya juya yana d'auko kud'i a mota Ameer baice masa komai ba tunda yaga hular da yake d'agawa maybe a kanta sukai magana komawa Ajeeb yai tayi masa lissafi tas ya d'au kud'in ya biya harda na d'inkin kowacce zata d'inka masa akan dubu uku da d'ari biyar sannan yace.

"Idan kin gama taya zan sani sai nazo na kar'ba"?.

"Bani da waya saidai kasa numbar a wayar babana ta fad'a tana mi'ka masa karamar tecno kar'ba yai yasa mata har zai juya ya sake tsayawa yace.

''ina fata anan anguwar kuke"?.

Kaita d'aga "eh anan muke ga gidan mu can" ta karasa maganar tana nuna masa kallon gidan yai kafin yace "ok sai naji ki dan Allah

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login