Showing 150001 words to 153000 words out of 195514 words
da 'yarka guda daya ka biyasu tunda yanzu kam baka komai a duniya bandasu dama sunyi ba'kin jini ba wacce take da saurayi bazasu ta'ba auruwa ba tunda sun riga sun jibge kalli fa babbar yarka Asma'u tafi su Hassan amma har yanzu tana gabanka hummm ba'kin cikin su ne zai kashe ka balle ba d'a namiji ka samuba taya idan ka tsufa wazai kula dakai sannan matsiyatan 'ya'yan naka kila tsinannu zasu aura talakawa irinka idan ma sun aurun kenan balle a son zuciyarka kayi tunanin sune zasu taimaka maka 'ya'ya maza dasu ake ado🙄 kuma dasu ake more rayuwa🤔 dasu ake nishad'i🙊 dasu ake had'a tafiya🤪 dasu ake had'a karfi da karfe😳 kuma 'ya'ya maza sune komai sukai ado ne🤐 amma ba 'ya'ya mata ba musamman 'ya'yan talaka irinka sukam babu abinda zasu amfanawa mutum banda damuwa da 'kuncin rayuwa kuma banyi qarya ba Habubakar ka duba yanzu sun saka a wani hali sune silar karyewar arzikinka idan baka fahimta ba ko ba haka bane"? Ilyah ya tambaya yana kallon shi.
'Dagowa malam Habu yai yana kallon Ilyah cikin jin takaicin maganar wulakancin da yake fad'a masa amma saiya share ya danne d'acin da yake ji a ranshi yace "niba wannan ya kawoni ba dama nazo ne nai maka sallama yau zan tashi insha Allahu zan bar gari kada na tafi babu sallama kaji jita-jita daga baya a gari babu dad'i muna uba d'aya tunda bani da wani d'an uwa na jini bayan kai komadai menene ubanmu d'aya kuma hannunka baya ru'bewa ka yake ka jefar shiyasa nazo na fad'a maka"
Dubansa Ilyah yai yana cewa "au haba yau zaka bar gari? Gudun hijira zakai kenan to a sauka lafiya ba shine abinda ya kawo ka gurina ba to ai ka fad'a min naji shikenan saika dawo idan kuma inka tafi bazaka dawo ba har abada ma had'u a lahira🙁 sannan qarya ne kace hannunka ya ru'be ka'ki yankewa ka jefar nidai zan yanke kuma na jefar ka gane"¿.
Cike da mamaki malam Habu ya tsaya kawai yana kallonsa ya tabbata yanzu kam Ilyah yayi nisa ya wuce inda yake zato yasan babu imani a tattare dashi ko d'igo tunda har yake zazzaga masa maganganu marasa dad'i haka bayan yasan halin da yake ciki kad'a kai Malam Habu yai yana cewa "shikenan yaya Ilyah zan tafi Allah ya sadamu da alkhairi shine fatana sai wata rana".
Ta'be baki Ilyah yai yana bin bayansa da kallo kafin yace "to to d'an gudun hijira agaida nagaba aida na d'auka zaka tsaya ayi bikin shalele dakai kodan uwar me zaka bani ban gayyace kaba da masu nauyin aljihu ake harka bada talakawa ba".
Shidai malam Habu bai sake ce masa 'kala ba yayi tafiyarsa yanajin 'bacin ran wannan maganar da Ilyan ya fad'a masa amma ba komai lokacin sane wata rana sai labari yana zuwa gida ko zama baiyi ba yaiwa Rakiya sallama yace su fito da kaya waje haka kowa ta dau kaya aka suka fita a gidan abun gwanin ban tausayi inka gansu a wannan lokacin mutane a layi sai binsu ake da kallo Malam Habu yana gaba da Ghana must go a kansa su kuma suna biye dashi kowa suma da kaya suna cikin tafiya sun kusa fita daga qauyen sukaji ana 'kwalla kira.
"Malam Habu Malam Habubakar ka tsaya".
Dakatawa yai tare da waigawa bayansa can nesa ya hango Sadi sai cin gudu yake har ya karaso inda suke yana haki yace.
"Haba malam Habu ina zaka je haka dan Allah ka dawo kar kabar garin nan yanzu Ina kasan zaka nufa komai yai zafi maganinsa Allah kada ka yanke hukunci lokacin da kake cikin fushi na rokeka daka sauke kayan nan ka taho mu koma gida karkaje ko'ina".😞
Kai Malam Habu ya girgiza yana kallon Sadi yace "wallahi Sadi bazan dawo garin ba a yaudai na barshi kuma babu mai dakatar dani najishi bawai dan cin mutuncin da yaya Ilyah yayi min ba a'a kawai garin ya fita min arai kuma bazan fasa barinsa ba saidai idan Baffah ne ya dawo yace na ha'kura kaga kuwa abinda bazai yuwu ba kenan domin wanda ya mutu ya mutu Sadi kayi hakuri dan Allah bawai banji shawarar daka bani bane a'a nagode da nuna kaunarka gareni domin abinda kaimin wallahi ko yaya Ilyah da muke uba d'aya baiyi min abinda kaimin ba a rayuwa Allah ya saka maka da alkairi Allah ya kaddara saduwarmu saina dawo" kallon iyalan nasa dake tsaye suna sauraren su yai yace "kai ku muje sai wata rana Sadi bazan gajiya da ce maka nagode bs domin duk garin nan babu wanda ya damu dani koya damu da barina daga garin daga kai sai Rakiya matar yaya Sabi'u bazan ta'ba mantawa daku ba a rayuwata" ya kasara maganar hawaye na zuba masa tuna d'an uwansa ya tabbata da ace Sabi'u yana da rai duk haka bazata faru ba bazai ta'ba shiga damuwa da tozarci ba koda na minti daya babu yadda Sadi ya iya yana tsaye yana kallo malam Habu ya juya sukaci gaba da tafi kamar ya d'ora hannu aka ya rusa kuka dan ba'kin cikin tafiyar malam Habun haka yake ji da yana da gida da gona wallahi daya hanashi tafiya ya bashi yana tsaye tun yana hangosu har ya daina ganinsu hawaye ne kawai yaji yana zuba masa shar shar daga idonsa jiki a sanyaye da'kyar ya d'aga kafarsa ya fara tafiya ya koma gida cikin tarin damuwar inda malam Habu ya nufa yanzu.
Batun su malam Habu kam sunyi tafiya iya tafiya kawai daji suka yanka har dare yayi musu dole suka tsaya a cikin wata rugar fulani suka ro'kesu kwana d'aya kafin wayewar gari kuma sukai sa'a suka samu yan arziki kamar sun sansu haka sukai maraba dasu sukai musu hidima duk da a gajiye suke amma sakamakon mutanen masu fara'a ne yasa malam Habu dasu Binta zama tare sukaita hira harda dariya wacce malam Habu rabon da yayi dariya su gani harsun manta yaushe ne haka suka raba dare sosai sunata musayar magana sannan kowa yaje ya kwanta washe gari saida rana ta fito sannan sukai shiri sukayi musu sallama sukaci gaba da tafiya kamar yadda suka fara basu samu hanyar bi su fita daga dajin ba dole da wani daren ya riskesu a hanya sukai kokarin tsayawa su kwana a dajin saidai wannan karon babu gidan fulani ko d'aya daga daji sai burtali babu kuma d'an abinda zasu kafa tanti su kwana kafin wayewar gari hakan yasa malam Habu yace musu kowa ta gyara d'an wani guri ta shimfid'a zaninta ta kwanta shi kuma yaje ya 'ballo wani babban itace ya dawo yayi tsaye a kansu yana gadinsu ta inda ya samu sau'ki ma akwai hasken farin wata yakan duba kowacce idan an d'auki lokaci saboda gudun kada abu Mai cutarwa ya samesu irin su miciji kunama ko wani mugun 'kwarin da danginsu haka ya kwana tsaye a kansu har asuba sannan suka tashi idonsa kuwa yayi ja sosai ya kumbura karkad'e zannuwan sukai suna mayarwa cikin kayansu yace musu suyi gaba su nemi ruwa ayi sallah tafiya suka cigaba dayi gari ya fara haske suka samu wata rijiya a dajin da guga a kafe anan suka tsaya da gugan wasu sukai alwala saboda lokaci na neman 'kurewa wasu kuma sukai da gora bayan sun idar suka d'ora tafiya dama babu wanda yasa rai da abinci a wannan dajin dan haka ma yunwa bata damesu ba basu daina tafiya ba kuma basu tsaya hutawa ba saida suka daidaici lokacin sallar Azhar sannan suka tsaya da ruwan gorunan da suka d'uro sukai alwala sukai sallah a karkashin wasu bishiyoyin goba ayaba🍌 mangoro kashu sun nuna matuka sunyi ja sosai tun suna sama domin a daji suke ba wajajen mutane bane balle a yagesu amma suna kallo Malam Habu ya hanasu su ta'ba yace musu idan sunci maishi bai sani ba sunci haram domin na wani ne a cikin gona suke kuma zasu biyashi a lahira kawai suyi ha'kuri su rike yunwarsu Allah zai basu halak a gaba haka suka mi'ke cikin 'kwarin gwiwa sukai gaba sun d'anyi tafiya suka had'u da wani gida 'kwal shi d'aya a dajin sai shanu masu yawa gasu nan sunata kiwo wasu suna kwance da alama dai gidan fulani ne tsayawa sukai a waje sukai sallama da Mai gidan bayan ya fito Malam Habu ya tambaye dan Allah ko zasu samu kindirmo na sayarwa su matafiya ne daga gari kaza suke kuma sun kwana a dajin nan sun wuni amma basu samu abinci sunci ba cikin tausaya musu d'an fulanin ya musu izinin shiga ciki sannan kuma babu dafaffan kindirmo sai d'anye ya tatso musu suna zaune matarsa ta kawo musu ruwa suka sha shi kuma ya aje musu yana daukar kwando ya fita daga gidan.
Zuwa wani lokaci ya dawo d'auke da kwandon a kansa fal kayan marmari ya sauke yasa matar ta d'ebo ruwa ta wanke ya kawo musu yace suci kafin a 'kare abinci sunyi mamaki wato dai wannan gonar kayan ta wadannan fulanin ne malam Habu yayi gaskiya da yace suyi ha'kuri zasu samu halak a gaba gashi kuwa da sukai ha'kurin sunci halak d'in mai abun da kansa ya basu duk da sanda ya hanasu tsinka kowa ransa ya biya.
A gidan suka karasa wuni har bayan sallar la'asar ganin kada lokaci ya 'kure musu suba masana daji ba basu San karshensa ba yasa malam Habu yaiwa fulanin sallama yace zasu d'ora tafiya tambayarsa sukai inda zaije daga yace shima bai sani ba yana son fita dai daga dajin ya samu hanya ne dan haka sukace masa ya tsaya ya kwana gaskiya yanzu idan yace zai fita a dajin dare zaiyi masa saidai gobe da safe su sashi a hanyar inda ya kamata yabi godiya ya musu sosai kuma yayi farin ciki da karamcin da suka nuna masa dashi da Iyalansa.
Washe gari da safe bayan sun karya sukai wanka a gidan domin tunda suka baro gida yau kwana uku babu wanda jikinsa yaga ruwa inba na alwala ba bayan sun gama shiri haka d'an fulanin ya wuce gaba domin ya fitar dasu a dajin harda matarsa suka tafi saida suka kaisu ga'bar dajin suka sasu a hanya sukayi musu kyakkyawan kwantance inda ya kamata subi sannan sukai bankwana harda basu dubu goma d'an fulanin yayi yace malam Habu yai 'karin guzurin tafiya Allah ya tsare ya kaisu lafiya duk inda suka nufa ya saukesu cikin sa'a godiya sosai Malam Habu yayi musu har saida sukace masa ya isa babu komai kafin suka sake gaisawa da sallama suka wuce su kuma fulanin suka juya zuwa gida.
Kamar yadda sukai musu kwatance haka suka ri'ka bi sannu a hankali duk wata alama da fulanin suka fad'a musu zasu gani sun gani har suka samu suka fito daga dajin sai gasu a wani karamin gari wanda ba mutane da yawa wani mutum da suka fara had'uwa dashi Malam Habu ya tambayeshi dan Allah nan wanne gari ne ya fad'a masa sunan garin yayi masa godiya sukai gaba a wannan garin ko zama basuyi ba suka tari 'yan mashina malam Habu yace su kaisu bakin titi inda zasu samu mota.
'Daukarsu sukai a jere bayan an gama ciniki suka fita dasu daga garin suka kaisu bakin titi wajen 'yan yuniyan masu tsare mota biyansu hakkinsu malam Habu yai sannan yaje gurin yan yuniyal d'in yace musu Kano zaije to sukace masa amma ya jira kafin a samu mota komawa yai ya zauna zuwa wani lokaci da aka samu mota kamara ce ma taxi🚗 babu kowa a ciki suka tare masa ita aka saka musu kayan a but sannan suka shiga bayan direban ya sallami 'yan yuniyal d'in ya shiga suka tafi.
A hanya yake tambayar su wacce anguwar za'a kaisu malam Habu yace shi baisan sunan anguwanin Kano sosai ba idan badan yanajin radio ana fad'ar wasu ba murmushi driver yai yana cewa "nima kuwa kaga ba d'an Kano bane daga yola na taso na dawo nan farko bakaga irin wahalar danasha ba kafin na zama d'an gari a farawa nafara zama ina haya mai gidan ya tashe ni ya zuba wasu tsabar wulakanci ba laifin tsaye bana zaune ba hanashi kud'in hayarsa nake ba amma ya tozarta ni daga nan na tashi na dawo d'orayi a nan ma mukai fad'a da Alhajin da nake hayar a gurin sa nan shima dai ya koreni yanzu maganar da nake maka Ina anguwar kabuga jan bulo na samu wani d'an arziki tunda na kama hayar gidansa ko banida kud'i yana d'aga min kafa kusan shekara goma maganar da nake maka a yanzu idan za'a kar'bi kud'ad'en hayar gidajensa ni yake wakiltawa ya yarda dani fiye da yadda kake tunani ko wannan motar da kake gani shine ya saya min nake haya kuma kwata-kwata a wata cewa yayi na ri'ka bashi dubu goma ai kafin a samu irinsu Alhaji Abubakar masu kyawawan zuciya za'a tona suna wuya a yanxu Malam humm".
Shiru Malam Habu yai cikin tunani ko yai nasa magana idan zai hadashi da Alhajin? Eh kawai ka tambayeshi tunda bakasan inda zaka samu sa'a ba jin zuciyarsa ta bashi shawara yasa ya d'ago yana cewa "a wata nawa kuke biya kud'in hayar"?.
Kai driver ya jinjina har malam Habu ya tsorata ya d'auka kud'ad'e za'a fad'o masa sai yaji yace "ba wata wata ake biya ba yanayin yadda ka kama gidan dakuna biyu da toilet da kitchen dubu d'ari ne a shekara".
Sauke ajiyar zuciya malam Habu jin sai shekara ma ba duk wata ake biya ba yace "ko zaka had'ani dashi idan munje kano d'in Nima dama bansan inda zanje ba banida kowa bansan kowa ba kawai daka na taho neman kud'i".
Kai driver ya d'aga masa yana cewa ''ok ba matsala amma gaskiya yanzu baya gari yayi tafiya zuwa wata 'kasar sannan indai ba yana da wasu gidajen a wasu anguwanin ba bana tunanin akwai sauran wanda suke empty ba mutane a ciki gaskiya ba lallai ku samu ba yanzu wacce anguwa zan kaiku"?.
Shiru Malam Habu yai jikinsa yayi sanyi har saida ya sake tambayar sa sannan yace "kaimu can anguwar da kake meye ma sunanta"?.
"Jan bulu" driver ya fad'a yana kallon sa.
"To ka kaimu can Allah ya dafa mana🤲" Amin driver yace🙏 daidai sun shiga Kano ya tsaya yasha mai kafin ya tashi mota ya d'ora tafiya zuwa wani lokaci ya shiga anguwar saida ya samu inda ya kamata ace ya saukesu gurin da ba fuskar mutane ba inda yake da wani kango sannan ya tsaida mota suka fiffito ya bud'e but ya sau'ke musu kayansu Malam Habu ya biyashi yayi masa godiya sannan drivan yace masa karya damu zaiyi waya da Alhajin zai tambaya masa idan akwai zuwa Nan da karfe goma na dare zai ganshi ya dawo gurinsu to malam Habu yace masa ya sake masa godiya.
Bayan driver ya tafi suna nan zaune kamar marayu umartarsu Malam Habu yai cewa su tashi su shiga cikin wannan kangon suyi sallah amma karsu shiga da kayansu tunda ba tambayar meshi sukai ba ya sayo musu ledar pure water guda biyu ya kawo musu kowa ta d'auka tai alwala sukai sallah yana tsaye yana jire musu kayansu saida suka fito shima yayi tasa alwalar a matsayinsa na ba'ko baisan ko'ina ya tafi neman masallaci daka ya samu akusa yayo sallah ya dawo sai kuma yunwa da take damun kowanne nan kuma birni ba qauye bane balle ace za'aga masu abincin saidawa a layi suna yawo dashi nan saidai restaurants ko masu saidawa a shaguna.
Sunata zaune zaman jiran tsammani har wani yaro yazo wucewa da bokiti a hannunsa tambayar sa malam Habu yai.
"Kai anan garin a ina ake sayar da abinci"?.
Kallonsa yaron yai yana cewa "babu inda ake sayarwa saidai kaje gidan cin abinci".
Kallon bokitin hannun nasa malam Habu yai ga kuma fork da plate🍽️ dan haka yace "kai me kake sayarwa"?.
Amsa yaron ya bashi "gurasa ce mai 'kuli amma ta kare saina d'ebo wata zaku saya"?.
Kai malam Habu ya d'aga "eh zamu saya idan ka d'ebo ka kawo mana kayi sauri yanzu" to yace yana yin gaba ba'a dad'e ba ya dawo ya ciko bokitin yace guda d'aya d'ari haka suka saye masa ita du saida bokitin ya koma gida.
Har bayan sallar isha suna nan zaune shiru shiru sunata jiran drivan nan daya kawosu ya dawo ya fad'a musu ko an samu amma har dare yayi nisa kusan karfe sha biyu ba labari harsun cire rai saigashi yazo da mota yayi parking bayan ya fito yace.
"Kayi hakuri malam wallahi ba mantawa nai daku ba nayi kiransa tun d'azu uzirin gida ya hanani dawowa kaga munyi waya dashi yace min babu sauran gidaje a hannunsa kayi hakuri saidai zanyi kokari na lalubo muku wani amma kafin nan ku shiga kangon nan ku aje kayanku nasan mai gidan sunansa Alhaji Musa mutumin kirki kafin dai na samo muku gidan hayar da zaku zauna nasan zai barku".
Kai malam Habu ya d'aga yana cewa "to shikenan na gode Allah ya saka da alkhairi" mi'kewa yai yana d'iban kayan suna shiga dashi sannan ya shikuma ya tafi haka suka kwana a kangon amma saboda tsoron nan ba garinsu bane basusan ya tsarinsa yake ba kada su ta'ba kayan wanda zai wulakanta su yasa tun kiran sallar farko na asuba malam Habu ya tashesu bayan yayi alwala ya fita xuwa masallaci tare da basu umarnin idan sunyi sallah kada su zauna su d'ebo kayan su dawo waje kada mai gidan yazo musu zuwan bazata kamasun dayai a ciki ya jawo musu matsala shiba wani kud'i ke gareshi ba.
Aiko suna ana shiga sallah bayan anyi sallama wuta-wuta sukai suka fita da komai waje kamar yadda ya umarcesu sai a wajen suka yi 'yan addu'o'i gari yayi haske malam Habu ya dawo dukka suka gaidashi bakin A'i da baya shiru ta kalleshi tana cewa.
"Oh ni A'i na fad'o daga sama na zarce rijiya gaba dubu Malam muna d'an zaman mu a gida cikin rufin asiri Rakiya tayi mana sutura ta bamu gurin zama haka kawai ka tashi tafiya batare da kasan inda zakaje ba kuma kaiba gurin kowa kazo ba ka kawomu tsakiyar birni