Showing 183001 words to 186000 words out of 195514 words
Indon ce yasa tace.
"Indo Indo wai dama da gaske yara suke jiya da naji anzo ana cewa Dalah kin dawo harda d'a"?.
Kallonta Indo tai batare da ta kawo komai daya faru a baya ba tace.
"Eh nice baba Asabe ina kwana"?.
Kamar Asabe zata fasa ihu da'kyar tana had'a ba'ki tace "la la lafiya kin dawo lafiya"?.
"Lafiya kalau ina Bahijjah"?.
Shiru Asabe tai bata iya ce mata komai ba zuwa wani lokaci tace "ta mutu" tana fad'in haka ta koma daki zaro ido Indo tai tana kallon Dalah tace.
"Innalillahi Bahijjah ta mutu"?.
Kai Dalah ta girgiza tana cewa "a'a bata mutu ba tayi aure ta auri wannan yaron Iluh d'an garuwa wanda farko yace yana sonki har sun kawo rokon arziki aka fasa sakamakon zuwa gurin mai gari da akai to shine ya aureta saidai da yake Asaben bata so inaga shiyasa tace miki ta mutu".
Indo bata sake cewa komai ba har Asabe ta sako hijab tazo tana cewa Balarabe "na shiga gidan Markah"?.
"Sai kin dawo".
Tana ji ya fad'i haka ta fice da sauri tana tafe kamar zata kifa harta qarasa gidan tun daga zaure take kwala Kira.
"Markah Markah fito ki tayani kallo yau na fito rana na tagayyara shikenan nikam tawa tazo qarshe na shiga uku na lalace wayyo Allah na" ta karasa maganar tana fashewa da kukan ba'kin ciki da damuwa.
Hankali tashe Markah ke tambayar ta "qawata lafiya miya faru haka"?.
Kai Asabe ke girgizawa cikin takaici tace "yanzu na fito daga d'aki na tarar Indo a zaune harda d'anta ga Dalah da Balarabe sai zance suke nifa yanzu a gidan nan na dawo 'yar kallo bani da kata'bus a cikinsu duk kwarjini na ya disashe kina gani tsinannan yaron nan Iluh tunda yabar garin nan bayan auren ko le'kowa bai sakeyi saboda ya samu abinda yake so baron ma tana shago a rufe koda ubansa yake ciyar da ita acan d'in".
Sauke ajiyar zuciya Markah tai tana cewa "to kema Asabe fa ba haka ake ba kindau abun da zafi tunda kika ga an d'aura auren nan ya kamata ki sallama kiyi ha'kuri amma kin 'ki alhali kinsan kinada hawan jini ga ciwon zuciya so kike ki kashe kanki a banza ko"?.
Asabe na shar'bar hawaye tace "na rasa yadda zanyi da rayuwata ne Markah wannan masifar har ina"?.
"Kinga Asabe yanxu abinda za'ai ki shirya muje ki gano garin da Bahijjan take tunda ni na sani idan hankalin ki ne ya tashi"?.
''ni hankalina bai tashi ba rass nake Bahijjah na sallama ta idan ta dawo garin nan ma saidai ta nemi wata uwar tunda ni ban isa da ita ba".
Kai Markah ta girgiza ''bafa haka bane kin gane ki mata uziri dan Allah ki shirya muje ki ganota kar kice a'a wa Bahijjah take dashi duk duniya bayan ke duk bacin rai haka zakiyi hakuri tunda me faruwa ta riga ta faru".
Shiru Asabe tai tana ta sharce hawaye Markah na bata ha'kuri da kwantar mata da hankali musamman saboda kar tasa ciwonta ya tashi azo a samu matsala da lallami ta samu ta daina kukan sannan tace ta shirya da d'an abun arziki su tafi wa Bahijjan dashi kar ayi mata gori ace tunda aka kaita ba'a je an ganota ba.
EMIRATE
Ana saura kwana biyu d'aurin aure Asad ya shigo masarauta daga Marshalls islands saidai tunda yazo ba harkar su Ajeeb ne a gabansa ba su kad'ai suke kayansu shikam ko fitowa bayayi yana part d'insa ya tsaya tsayin daka yana bincike damuwarsa ya samu abinda yake so a yanxu shine karshen zancen.
Haka gidan malam Habu ma shirye shirye ake sosai ba kama hannun yaro Asma'u tayi abubuwa sosai saboda business Alhaji Musa ya bud'e mata Mai girma take juya dollars Jamila ma sai wannan karon ta dawo Nigeria tunda aka d'aura aure suka tafi d'anta namiji har yayi wayo sosai shima dai takwaran Alhaji Musa ne suna kiransa Arfat hum Jamila ma ta cika sosai ta murje ta goge ta gano kasar waje da turawa sai bada ki labari take a ranar kwana sukai a d'aki ita da A'I har asuba suna hirar yaushe gamo basu iya runtsawa ba duk da kuwa dama a gidan babu wanda yayi barci sakamakon shirye shirye da akeyi na biki ayi wancan ayi wannan duk wasu kayan cinye cinye Asma'u ce tad'au nauyinsa zata kama musu Hall inda za'ai DJ a gwangwaje data fad'awa Malam Habu ya hanata yace gara tayi sadaka da kud'in zaifi alkairi shine ta ha'kura akai walima🎇🎉 madadin dijen da aka so yi.
MRS AL'AMEEN AHMAD CE😘.
We will meet again nagode🤝.
TYPING📲 Mon Sep 2/24 4:15PM
YUSRAH MUSA ABUBAKAR💋🎠.
👑Më kämär särkï👑
_____________________________
___________________________________
______________
💫 ANNUR WRITER'S ASS💫
Home of hospitality and harmony 🤙 gidan karbar mutane hannu biyu da zaman lafiya🙅🏼♀️.
💨💨💨💨💨💨💨💨💨💨💨💨💨💨
💦💦💦💦💦💦💦💦💦💦💦💦💦💦
💭💭🗯️🗯️💭💭🗯️🗯️💭💭🗯️🗯️💭
Stôry wrîttên nd êdîtîng👇🏿
✍🏼Mrs Äl'ämëën Ähmäd cë😘
OH NI ALLAH CIKI NA🤣 HABA KU KUWA FANS TSORON ME KUKE HAKA🤔? NAJI KUNA CEWA DAN ALLAH KAR NA CIRE AJEEB A LABARIN LITTAFIN BAZAI DAD'I😣 BA KAR NACE AJEEB MUTUWA😔 ZAIYI, NIIIIII🤐 DA YAUSHE NACE HAKA😳 HASASHEN KUNE KAWAI KUDAI KU BARI KUJI YADDA KOMAI ZAI FARU KU BIYO NI A SANNU CIKE DA NUTSUWA CIKIN PAGE NA GABA ZAKU JI KOMAI😎.
🚄Kudai kawai keep your eyes👀 open😂💯💃.>>>>>>>>>>>>>>>>>>>
🙇🏼♀️Ayi ha'kuri idan an samu typing error🔴 matsalar keyboard ne.
69~AL-QADIR
The Omnipotent
70~AL-MUQTADIR
The Determiner.
34~Allahumma salli wa sallim ala sayyidina muhammadin Afralil auwalina wal akhirina.
🌄MARVEL HEYDAY 🌄
Episode 69&70 👑PALACE👑
Da yake Sultana Fatima 'yar Nigeria ce danginta har sun fara zuwa ana gobe d'aurin aure dangin Mami suma haka sukazo daga Bahrain da yawansu larabawa kyawawa farare kar-kar dasu harda 'yan mata su hud'u had'dd'u suna zaune cike da farin cikin had'uwar su guri daya domin ba gari daya suke zaune ba wasu na Riyadh aure wasu na Bahrain d'in wasu a misra Aunty Aleemah kuwa a California mijinta yake aiki suna can tare shekara kusan biyar bata samu tazo Bahrain ba sai yanzu da bikin Ajeeb d'in ya tashi miryoyinsu kad'ai ke tashi a parlon suna zaune sunsa Mami a tsakiya ana hira mai dad'i Ajeeb ya shigo da sallama kallonsa Aunty Futuha tai tana cewa.
"Yauwa Ajeeb dama tun d'azu nake nemanka kaida Asad amma shiru ban ganku ba ina kuka shiga ne kai kana yawo kamar ba ango ba kodai gurin amaryar taka kaje ne? dan da alama kai baban soyayya ne".
Murmushi Ajeeb yai yana zama akan kujera yace "eh gurin ta naje kinsan bana iya nutsuwa idan ban ganta ba a rana ina zuwa gidansu kamar sau goma".
Zaro ido sukai Aunty Aleemah tace "kaiiii Ajeeb soyayyar har takai haka"? Kai ya d'aga "ai harya fi haka ma Aunty Aleemah ko romiyo bazai nuna min yadda ake soyayya ba"?.
"Oh haka ne da gaske"?.
"Kwarai kuwa I have confirmed it".
"Ok shikenan amma Ajeeb in an jima zamuje Arabian night🌃 ko baza ayi ba"? Kai ya d'aga "eh za'a mana ai dama na sanar mata ni dangin mahaifiyata larabawa ne kuma ko ban fad'a ba ta sani da gani babu tambaya menene ni🤷"? Har had'a baki sukai da cewa "Balarabe kuma basarake🤴😍" hannu ya bud'a yana cewa "to kin gani yanzu dame kuka zo min nasan kuna tafe yau shiyasa banyi shirin komai ba kune zaku za'ba min kalar shigar da zamuyi nida amarya ta a gurin yadda zamu burge kowa".
Mi'ko masa wata jaka mai kyau Aunty Futuha tai iya jakar ma abar kallo ce balle ajega abinda yake ciki tana cewa "Eh aiko munzo maka da kayayyaki da yawa domin dama tunda watan bikin ya kama muke shirin harda Abu Sultan ga abokin ka Shuraim dan gidan Ummi Sultana Liyuzah ya bada yallabiya a kawo maka da hirami sannan ya bada Abayat a kawowa amaryar ka muma duka mun taho maka da abubuwan bazata" kai ya jinjina cikin nuna jin dad'i.
Yace "sakallahu khairan gaskiya na gode sosai kuma naji dad'i har bansan yadda zan kwatanta muku ba saidai kawai nace Allah yabar zumunci" Amin 🤲 suka fad'a tare suna bud'e hannu suka shafa a fuska. mi'kewa yai yana cewa "bari na fita zuwa dare zan dawo" fita yayi a falon ya barsu suna ci gaba da hiransu.
Tun bayan sallar magriba ake shirin tafiya Arabian nights humm kowa da jallabiya amma Asad juyi duniya Ajeeb yayi akan ya shirya suje yace wallahi babu inda zaije dole haka Ajeeb ya ha'kura badan yaso ba suka tafi dasu Aunty Aleemah zuwa anguwar su Amatu inda aka kama Hall d'in da za'ai.
Tabd'ijan jama'a ku le'ko kuyi kallon ango Ajeeb da amarya wai zankad'i yasha kwalliya cikin farar kar d'in jallabiya anyi mata adon golden colour a wuyan rigar da hannunta sannan hirami shima golden takalmi ma haka humm dama gashi jinin larabawa abun aba magana fad'ar kyaun dayai.
Haka 6angaren amarya Amatu itama doguwar rigace fara da manyan fulawoyi golden ajiki takalmi da gyale duk golden sauran mutane kuma kowanne yasa ba'kar abayat masa sun sa coffee jallabiya kamar larabawan gaske kowanne ya kima rawani su Aunty Futuha da yake sune masana haka suka wuce gaba suka tsara musu yadda akeyi abun ya burge kowa haka aka qare abubuwa cikin shau'ki sai karfe takwas suka koma masarauta a gajiye duk sun baje suna hutawa amma Aunty Fadilah sakamakon bataga Asad ko kad'an ba yasa ta mi'ke ta tafi nemansa.
🕰️Misalin 'karfe tara da mintuna na dare Asad yana zaune a cikin parlon part dinsa da laptop a gabansa sai faman aiki yake ya d'au zafi sosai gabadaya ya birkice sai yaga kamar ya samu wani d'an bayani game da abinda yake nema sai kuma yaga error ransa duk ya gama 'baci tsuka yaja mai 'karfi yana ture laptop din ta fad'i 'kasa mi'kewa yai jin duk jikinsa yana ciwo ga bai samu abinda yake son samu ba yayi hanyar bedroom domin ya samu yayi wanka.
Jin sallamar mace yasa shi kallon kofar shigowa ido ya zuba mata irin na yaushe gamon nan amma baiyi magana ba saidai ta hangi jin dad'in ganin ta a cikin fararen idonsa zama tai da murmushi a kan fuskarta tana cewa.
"Barka da dare Asad ya kake"?.
Komawa yai yana zama har lokacin bai daina kallonta ba yace "Aunty Fadilaty sannu da zuwa kun dad'e da sauka ne ke dasu waye ne ina budurwa ta😳"?.
'Yar dariya Aunty Fadilah tai tana cewa "oh har yanzu baka daina tsokana ba Asad karfa daga wasa abu ya zarce gaske"?.
"To Aunty Fadilaty idan ya zarce ma huluncin Allah ne a rubuce yake, amma baki fada min tare dawa kuka zo ba"?.
"Eh to munzo da Auntyn ka Ma'asumah da ummin mu tace dole ne tazo auren jikanta Ajeeb itace zata amshi amaryarsa".
'Dan murmushi Asad yai tuna cewa gobe iyanzu d'an uwansa Ajeeb ya zama ango sai yaji yana masa murna da hakan 'kwarai kuma ya naiwa Annur ma fatan kaiwa wannan matakin dama shikam baya lissafi da kansa babu aure a tsarinsa baya ra'ayin sa ko kad'an koda ace gaba zaiyi yafi son mace jaruma mara tsoro jajurtacciya wacce zata jure kowacce irin wahala shiyasa bazai iya auren macen da kawai hutu ta sani ba idan bai samu irin macen da yake so ba tofa bazai aure akan lokaci ba saidai idan yayi ritaya daga aikin soja😛.
"Asad tunanin me kake"?.
Dawo da kallon shi kanta yai batare daya bata amsa ba yace "ok muje part d'in Mamin" kai Aunty Fadilaty ta d'aga tana mi'kewa suka fita tare suna tafe suna hira dan sosai Asad ke son matar jinin su ya matukar had'uwa 'kanwar Mami ce ita kuma a Riyadh take aure yaranta uku mace daya ZARAH sai maza biyu.
Yasha mamaki ganinsu da yawa harda wadanda ya dad'e basu had'u ba ga larabawan 'yan mata suna rawa a gefe sun kuna wa'kar "ana ahibbu ya habibi" cikin nishad'i ganinsa yasa suka tsaya d'aya bayan d'aya ya kallesu su hud'u ne Hajir Yusriyyah Muyassara da Fujirat 'ya'yan Aunty Futuha da Aunty Aleemah sai kuma Aunty Naizarah lallai bai kyauta ba ya dad'e basu had'u ba yaushe har yaran nan suka girma haka kallon su yai suna gaidashi yace.
"Wato ku yaran nan duk abinda yazo ranku shi kuke yi ko meye abin burgewa a rawa musamman ma ke Hajir kin fi kowa kodai mawa'ki zaki aura"?.
Rufe fuska Hajir tai tana cewa "Allah a'a ni ba mawa'ki bane saurayi na ustaz ne🤣 kuma ka tambayi Aunty Fadilah ai ta sanshi kwanan baya munje gidanta dashi".
Kallon Fadilah Asad yai da alamar tambaya yace "wai haka ne Aunty Fadilaty"?.
Kai aunty Fadilah ta d'aga tana dariya tace "ba haka bane bakaga a yadda yaje gaida niba kamar ya taso daga filin kwallo".
Zaro ido Hajir tai "kai Aunty Fadilah Allah yanzu zakisa yace na rabu dashi dama wancan zuwan dayai na ma saida yace na rabu da Zayad kuma wallahi Adeel mutumin karki ne".
"Ri'ke baki Aunty Fadilah tai cikin 'yar tsokana tace "tofa Hajir babban lamari wato Adeel harya sace zuciyarki kamar haka a gabanmu kike yabonsa ah lallai kam shiyasa duk abinda yarinyar nan Zarah tai nake cewa zuwa min ziyarar da kike ne a gurin ki ta koya idan ta kama rawa da malgwad'a kamar tarwad'a abin har mamaki yake bani"
Dariya sauran suke yayin da Hajir ta fara bubbuga kafa kamar zatai kuka dan tasan maybe Asad ya sake mata iyaka da wannan Adeel din kallonta yai kamar bazai magana ba sai kuma yace "Hajir idan kin tabbata da gaske kike abinda kika fad'a zan zo Bahrain zanyi bincike a kansa".
Da sauri Hajir tace "eh Allah na yarda kuma basai ka bari na sani ba ka min bazata ta gidan Aunty Fadilah ko gidan Ummi Hadiyyah"
"Ai ba shawararki nake nema ba can you be quiet🤫 ita Muyassara bata dashi"? Ya tambaya yana kallon yadda ta zaro ido jin abin yazo kanta Caraf Hajir tace "tana dashi sunan sa Nurul-qalbih" juyawa Asad yai yana kallonta kamar mai nazari sai kuma yace "da gaske sunansa kenan ko kuma kece kikasa masa hasken zuciya"?.
Hajir kamar ita ake tambaya da sauri ta sake cewa "itace tasa masa hasken zuciyarta" rufe baki baki Muyassara tai jin 'karyar da Hajir d'in ta shirga mata tace "Allah ba nice nasa masa ba sunansa kenan" tafi Hajir tai "aiko ba sunansa kenan badan kar yace kema zaiyi bincike a kansa ne kika gigice harda komawa kalar tausayi kamar zaki kuka" harararta muyassara tai "oh to ko kukan zanyi" rausaya kai Hajir tai "oho waya sani"
"Kai kumin shiru haka bana son jin komai zan zo Bahrain din ai duk ba tsira zakuyi ba".
Shiru sukai suna kallon sa daidai ya kar'bi jaririn dake hannun Aunty Naizarah yace "wannan yaron kine dama kinyi aure"?
Kaita d'aga "Eh kusan shekara biyu ma ai kasan rabuwarmu dakai tun a rasuwar Abu Samir bamu sake had'uwa ba" kai ya jinjina daidai Ajeeb ya shigo yana waya gud'ar da su Aunty Fadilah da Aunty Aleemah suka sakar masa ne yasa Ajeeb sauke wayar da sauri yana toshe kunnensa yace.
"Kai auntis wannan ai sai kusa mutum jinsa ya d'auke na tsawon da'ki'ku irin wannan 'kara kamar ina ramin gyare duk gud'ar ta miye"?.
"Oh really zakace bakasan ta meye ba"?.
Zama Ajeeb yai kusa da Asad yana cewa "yes but I've comfirmed it bansan komai ba 😝 na miye"?.
Dariya Aleemah tai tana cewa "eh gud'ar taya ka murna ce kasan dole muyi maka gud'a gobe iwar haka ka zama ango Ajeeb kabar sahun tuzurai irin su o'o🤩".
Murmushi Ajeeb yai yana kallon Asad daya hade gira jin abinda tace Ajeeb da 'yar fara'a a fuskarsa yace "uhmmm Aunty Aleemah kenan aurena mai ganinsa saiya shirya surprise ne".
"To surprise ya wuce gobe kasha manyan kaya kuje mighty Alhussain ya kar'bo maka alkawarin ri'ke 'yar mutane cikin kima ai tayi dace baka da fad'a ba kamar Asad ba shikam matarsa Allah yasa mai ha'kuri ce idan kuma itama mai zafi ce irinsa hummm zakusha rabiyar fad'a" kai Ajeeb ya jinjina yana cewa "tabbas kinyi gaskiya Asad kamar kububuwa haka yake a tafashe zafi wane yaji in kinji ana soja marmari daga nesa shifa Asad tuwon 'kaya ne miyar allura baisan wargi ba" dariya tai "hhhh lallai kam naga alama amma duk da haka ai ya.............................
Katse musu magana Aunty Fadilah tai daidai ta fito daga bedroom din Mami ta 'karaso gurin da murmushi fal fuskarta tana cewa "Asad muga hannunka" 'Dagowa yai daga wasan da yakewa yaron hannunsa yace "miye a hannun nawa"? "Babu kaidai mu gani man" bai bata ba kawai ya tsaya ya zuba mata ido tamke gira tai tana cewa "Asad wannan kallon naka ai sai kasa mutum ya 'kwaru please bring me your hand✋" mi'ko mata yai yaga dai me zatai masa babu zato yaji ta shafa masa abu a hannu sai tashin 'kamshi yake bud'e idonsa yai akan abun yana cewa.
"Subahanallahi Aunty Fadilaty meye wannan kika shafa min" ya karasa maganar yana jin zuciyarsa na tashi kamar zaiyi amai dariya tai tana sakin gud'a tace "wannan lalle ne na shafa maka".
Had'e rai yayi "lalle? Innalillahi wa inna ilaihi raji'un meye had'i na dashi kuma amfanin me yake"? "Amfanin dole a shafa maka tunda zaka zama ango".
Kai ango kuma sake had'e fuska yai "wanne irin ango? Ajeeb dai zakiwa haka ba niba kawai kin 'bata min jiki".
'Dan zaro ido Aunty Fadilah tai "oh sorry haka ne mantawa nai but tun d'azu Ajeeb aka shafa masa nasa, kodan ai ba matsala tunda kai Hussainin ango ne ko" shiru yai yana kallon Ajeeb wanda yake dariya wata uwar harara ya sakar masa wato silarsa yasa an bata masa jiki sannan tsabar iskaci yake masa dariya mi'kewa yai yana kallon Fadilah yace.
"Good night Aunty Fadilaty".
"Mu kwana lafiya Asad" ta fad'a da fara'a ajewa Naizarah jaririnta yai yana fita shima Ajeeb bai jima ba ya musu sallama yabi bayansa a bedroom ya samu Asad yana tsaye jikin window daga shi sai 3Quarter da singlet fara iskar waje mai sanyi na shigowa ta windon tana kad'a gashin kansa dake she'ki jin motsi a bayansa yasa ya juyo suna had'a ido da Ajeeb ya sake d'aure fuska yana cewa.
"Wato dan wulakanci Ajeeb gashi nan kasa a dalilinka jikina sai warin lalle yake".
Shima Ajeeb din hade rai yai yana d'auke kai ya karasa bakin gado ya zauna ya kalli yadda lallen ya 'bata masa farar rigar jikinsa yace "da nai maka me? Dama nace Aunty Fadilah