Showing 171001 words to 174000 words out of 195514 words

Chapter 58 - ME KAMAR SARKI HAUSA NOVEL

YUSRAH   

22 Oct 2024

27282

domin kunyar Hajiya Aisha dama daya akai auren 'ki tayi itama tace bazata iyaba ta d'auka anbar maganar sai ji tayi wai an d'aura yau wuni ma tayi tana kukan kunya.

Zama Hajiya Aisha tayi a gefen gadon tana d'aga mayafin ta yayeshi zuwa saman kanta tace "uhm Masha Allah Asma'u gaskiya kinyi kyau dole a biya kud'in sayan baki Alhaji saika biya".

Shikam Alhaji Musa tsaye yayi kawai da murmushi a fuskarsa yace "ok nawa zan biya kenan"?.

Gyara zama Hajiya Aisha tai tana cewa "amarya dubu d'ari ni kuma qawarta dubu hamsin😃".

'Dan zaro ido yai cikin wasa yace "kai dama ke qawar amarya ce bayan yanzun nan a parlor kikace kece abokiyar ango kodai Kinga amaryar tafi angon kyau shine zaki koma 6angarenta"?.

Itama d'an zaro idon tai kamar ta manta d'in nan tace "kuma fa anyi haka ashe ni qawar ango ce ai shikenan a biya amaryar nata nice ma zan biya transfer ko cash wanne take so"?.

"Cash take so aje a kawo mata ko zamu samu bakin ya bud'u".

Mi'kewa Hajiya Aisha tai tana fita zuwa minta biyu ta dawo da kud'i d'aure a kyauro tana ajewa a gaban Asma'u da kanta ke sunkuye tace.

"To amarya na wakilci ango na saye bakin duka sai ayi masa magana nizan tafi Allah ya bada zaman lafiya Allah ya sanya alkairi Allah ya kawo mana arziki mai d'orewa wanda zamuyi farin ciki dashi".

Iya Alhaji Musa ne yace Amin a fili Asma'u ta fad'a a zuciyarta kafin Hajiya Aisha ta juya tana fita tsaye Alhaji Musa yai yana kallon Asma'u datai shiru zuwa wani lokaci yace.

"Husnah😁".

Ji Asma'u tai gabanta ya fad'i ta ma kasa amsawa sai numfashin ta dake fita da sauri kawai ta sake qasa da kanta.

"Husnah".

Ya fad'a a karo na biyu da'kyar ta amsa muryarta na rawa can kasa sosai yaji na'am d'in da tace yayi mamaki domin yasan ba haka take ba sau tari yana jin surunta ita da Hajiya idan sunzo aiki to yau d'in meyasa? Kodan yau rana ce musamman a gareta batai kama da sauran ranaku ba tayi dabam kaiya jinjina yana sake qare mata kallo gaskiya 'ya'yan malam Abubakar kyawawa ne kuma duk kama suke dashi gabadaya fuskarsa suka d'auko kyau iya kyau ya fad'a a ransa kafin yace.

"Kinga ki tashi kiyi alwala bari na dawo" yana fad'in haka ya fita dan ya bata sarari ta samu tayi tana ganin ya fita ta mi'ke tana sauka a gadon jiki a sanyaye ta nufi kofar toilet bud'e ta shiga tayo alwalar tana fitowa yana shigowa ya sako jallabiya coffee ya cire wancan shaddar gaba ya wuce ya musu sallar nafila ta godiya da addu'o'i masu tarin yawa na fatan zaman lafiya da alkairi a tsakaninsu sannan ya mi'ke zai sake fita har yaje ba'kin kofa ya juyo yana cewa.

"Ki tashi kici wannan abun sai kiyi wanka ki kwanta kinji"?.

Kai ta d'aga masa a hankali tace "to" yana juyawa ya fita ta mi'ke tana tana zama a gaban gadon gaban glass table din ta bud'e ledar humm d'irka d'irkan kaji ne guda biyu wanda sukaji kyakkyawan gashi da lafiyayyan kayan had'i da'kyar ta samu ta iya cinye cinya daya🍗 tasha fresh milk mai sanyi sosai sannan ta tashi tana cire doguwar rigar jikinta ta duba sabon towel ta d'auka tana cireshi a ledarsa ta d'aura ta shiga wanka tunda tasan ba dawowa zaiyi ba shiyasa ta sake tayi wankanta hankali kwance daidai ta fito d'aure towel kanta ko hula babu kitson da aka d'an'dasa mata sai she'ki yake gashi ba'ki mai santsi dama duk haka gashin kansu yake kuma akwai tsayi sosai da yawa asali gashin kan Baffah ne Malam Habu ya gada kuma shima ya gadar musu.

Tsayawa tai cak a kofar toilet din ko murfin ta kasa saki ta rufe balle ta karaso tsakiyar d'akin kamar yadda shima ya tsaya cak a kofar shigowa bedroom d'in ya zuba mata ido humm tabd'i masha Allah wai ammafa ya samu mace anan🙈 uhn inji mai ciwon baki karasa shigowa d'akin yai yana zama a bakin gadon yace.

"Husnah tsaiwar me kike anan kizo kisa kaya man ki kwanta".

Shiru tai ta kasa magana fahimtar dayai kamar tsoron sa take yasa ya girgiza kai yana murmushi dan ya tabbatar yace.

"Ko bakya jin barcin ne"?.

Da sauri yaga ta d'aga masa kai mamaki ne ya rufeshi amma sai bai sake ce mata komai ba yana dai dariya a cikin ransa ya mi'ke yana kashe wutar d'akin idan kallonta a haka ne ya hanata sakewa yana kashewa ta rutse ido da karfi tana rafka salati jinya d'agota sama ya fara tafiya da ita yasa ga hajijiya na d'ibanta tace.

"Innalillahi wa Inna ilaihi raji'un na shiga uku😂".

Kai jama'a ba arziki tasa Alhaji Musa ya kama dariya dole duk da yaso mazewa amma yadda ta furta kalma duk wanda yaji saiya mata dariya direta yai akan gadon bayan ya kunne bedside lamp blue da fari haske kad'an ne d'akin yayi kyau yai kala kallonta yai yana cewa.

"Husnah did something scare you"?.

Shiru tai jikinta na rawa hakan datai ya tabbatar tsorata tayi dashi sai kawai ya rungumota jikinsa aiko jiyai ta saka mai kuka😁 murmushi yayi kawai yana girgiza kai ai dama duk amarya sai tayi haka indai ta 'kwarai ce saidai fa ballagaza bazar-bazar itace ke d'oki kwanciya yai da ita a jikinsa yana d'orats akan kirjinsa sai shashshe'kar kuka take cikin tashin hankali ta'ki ta daina shiru yai yana shafa kitson kanta amma tsoron kada ta sanyawa jikinta zazza'bi da wannan kukan yasa ya matso da fuskarta yana had'a bakinsu ko ya samu tai shiru😘. Uhm uhmmm🙊 nikam bari na fece🏃🏃🏃.

_______Sati d'aya na zagayowa da d'aura aurensu Saleem ya d'auki Jamila yayi Canada da ita yace bazai waiwayo Nigeria ba sai sun zama su uku Jamila shi ga baby😃 balle 6angaren su Asma'u amarsu da qamshi tana gidan Alhaji Musa abinta d'as yana nuna mata soyayyar sugar Daddy😄 sake samun hutu da kwanciyar hankalin datai tana samun abubuwa masu gina jiki humm tuni ta sake cika ido tayi kara tsayi da ki'ba har Hajiya Aisha na tsokanar ta wai ko kwanan nan zata haifa musu twins👭 ita dai in kunya ta isheta saidai tayi dariya ta rufe fuska, haka Hajiya Aisha ta basu kyautar ticket na honeymoon🙈 Alhaji Musa ya d'auki Asma'u suka tafi Switzerland yawan sha'katawa na yan watanni ya ri'ka nuna mata gurare kala kala na bud'e ido tayo kallo humm amma fa tun daga can ta fara rashin lafiya da laulaye laulaye🤭.

Bayan ya kaita asibiti aka tabbatar mata ciki ne wai Allah sarkin dad'i inji 6arawon zuma🍯 rasa inda zai sanya kansa Alhaji Musa yai kamar ya mayar da ita ciki kwana goma tsakani yayi mata sayayya masu yawa sukai shiri suka dawo gida.

Wanda Hajiya Aisha itakam kamar itace ta samu cikin harda kukan murna nan ta shiga nunawa Asma'u kulawa da sabuwar tarairaya bata komai rai da rai tana kwance hatta toilet zataje an aje mai kula da ita idan falo xata fito sai an ri'kota dan kada ta fad'i a samu matsala ayi losing baby.

🏕️KAUYE🏕️
Hum sannu bata hana zuwa gurin da jirgin sama✈️ yaje tofa wata rana kunkuru🐢 ma za'ace masa barka da zuwa duk nisan turin da akaiwa lilo zaije ya dawo tun ba'aje ko'ina ba Tanko da Mudi sun fara ganin karshen su domin duk abinda sukaiwa malam Habu ya fara dawowa kansu duk wata masifa ba'kin ciki da damuwa da talauci ya fara musu dabaibayi komai suka ta'ba yanxu xai narke asara ta fara shigo musu babu wanda yasan musabbabi koya ankare sai Sadi ya fahimci kawai zallar alhakin malam Habu ne ke bibiyarsu kuma wannan kadan suka gani.

Har gida Tanko yaje ya samu Mudi akan suje gurin boka suji yaya me yake tafiya ko asirin ne lokaci yayi ya fara dawowa kansu Mudi ya amince yabi shawararsa suka je kuma boka ya fayyace musu komai cewa yanzu fa saidai suyi ha'kuri malam Habu ya zarcewa tunaninsu babu abinda suka isa masa a yanzu yayi tasiri a jikinsa kuma idan bazasu manta dama kafin yayi musu aiki anyita da wajewa cewa duk ranar daya karye zai dawo kansu idan Malam Habu bai mutu ba asirin na jikinsa ba suka yarda dan haka lokaci ne yazo sai su d'au shiri .

A damuwance Tanko yace "amma boka yanxu baba wata hanyar da zaka taimake mu asirin muma yabar jikinmu"? .

Dariyar mugunta boka ya she'ke da ita yana cewa "babu nace muku babu Babu wata hanya saidai ku mutu dashi a jikinku ya bibiyar ahlinku kamar yadda kukace ya bibiyi ahlinsa asirin bazai ta'ba barinku ba har abada yayi muku mummunan kamu yagama kewaye jikinku bana son jin wata magana ku tashi ku tafi satin sama ku dawo zan baku wani abun da zakuyi wanda idan kukai sa'a asirin zai fice gabadaya daga jikin ku Sam amma idan kukayi bai fice ba d'ayan biyu ko ku haukace ko ku mutu kun amincehhhhhhhhhhj" ya karasa maganar yana sake 'kya'kyacewa da dariyar tsananin mugunta.

Shiru sukai aka rasa wanda zaice ya amince a cikinsu dan haka yace "ku tashi kuje ku tafi kuyi tunani ku dawo rana ita yau sannan idan zaku dawo ku soyo min manya manyan kaji kuyo min miyar kitse😂" tofa yau ga zilamamman boka.

Amincewa sukai da sharad'in sa jin da sakai ya raba musu biyu zasu warke ko su mutu sun san zasu warke abinda suka d'auka a ransu shine mutuwarsu da wuya bazasu yarda su mutu batare da sunga gawar malam Habu ba, subahanallahi ALLAH kayi mana katangar qarfe da ma'kiya🤲📿🙏..

Bayan barowarsu gurin boka wadannan baka'ken aljanu da bokan ya turawa malam Habu suka dira bagansa kowanne jikinsa a qone har lokacin basu warke daga toya musu jiki da malamin nan yayi ba a fusace suke kallonsa mi'kewa yai yana cewa.

"Meye kuka dawo yi nan ku koma inda na aika ku yanzun nan''.

A fusace d'aya a cikinsu yace "mu koma gidan uban wa? Kanka muka dawo yau dawa taci gida".

Cikin tsawa boka yace "ku koma naceeee".

Zagaye shi sukai suna sakashi a tsakiya suka fara d'aukar sa suna li'kawa da qasa suna tumurmusa shi wannan ya bugushi nan wannan ya buga shi can sai ihu yake suna luguiguita shi kamar an basu wankin babban bargo.

Tanko da Mudi suna cikin tafiya suna sake tsara abinda zasu shiryawa malam Habu sukaji iska mai qarfi na bugosu ga wasu kalar maganganu wanda basu san me ake cewa ba gabadaya dajin ya d'auka daga baya sukaji karar fashewar abu kamar bom ana ihu da kururuwa a firgice suka juya hango sansanin boka sukai ya kamada wuta yana ci sosai har tsiri take ga ihunsa da gudu suka koma gurin hummm komai ya 'kone baka ganin komai sai wuta💥 dake faman ci hankalin su inyai dubu ya tashi Kira suke boka kana ina kada ka mutu boka ka fito ka taimake mu muradin mu yana garek.............................

Basu karasa ba suka zuba a guje suna ihu sakamakon ganin yadda bokan ya canza halitta ya fito da wata siffa Mai muni wuta na cinsa yana ihun neman agaji yana binsu da gudu suma gudun suke suna ihu basu san ta inda suke biba duk sun zubar da takalmansu saida suka kusa zuwa gari bokan ya fad'i wutar ta karasa cinyeshi tas ya zama toka suna tsaye suna haki sukaga ba'kar guguwa ta taso tazo fuuuu ta d'ebe tokar tai gaba da ita.

Kukan tashin hankali ba'kin ciki rashin sanin madafa kowannansu keyi a gurin suka zuba suna d'ora hannuwa aka suka ri'ka gurza ihu babu Mai jinsu balle a tambaye su dalili. Hummm komai nisan dare gari zai waye Abinda ka shuka shi zaka girba🙅.

🏙️KANO🏙️
Yau Nafisa ta shirya Nurain yace zai kaita gurin mahaifiyar sa ta wuni mata sai murna take zata rabu da u'kubar su Mimih yau zata d'an samu hutu tana zaune gaban Mom d'in Nurain bayan ta gaisheta gashi ya tafi office ya barta ita kad'ai jinta take a takure danma yau jama'a ce maybe daya dawo office da wuri ya d'auketa daga nan ya mayar da ita gida ya barta tayi wi'ki-wiki ta kame jikinta guri d'aya kallonta Mom tai tana cewa.

"Yauwa Nafisa kike sunan naki ko?.

Kai Nafisa ta d'aga kamar mai tsoron magana ko wacce take jin zazza'bi muryarta na rawa tace "eh sunana Nafisa ".

Kai Mom ta d'aga ''ok Nafisa bari kimin wani abu kafin ki tafi inaso kiyi min tuwon gero👍 (Biski) amma kiyi shi da tauri irin yadda kuke yinsa kada yayi ruwa nafi so naji ina 'bam'bararsa da'kyar kin gane? sannan sai kiyi min miyan alayyahu akwai komai a fridge kisa ganda sosai a ciki kuma kisa kayan kamshi da spices suma su fito ina matukar son tuwon biski amma ban iyaba bansan yadda ake ba Alhaji ma yanason kayan karkara kuma gashi bamuda kowa a qauye banda babanki da suke huld'a dashi tashi kije ina zuwa kitchen d'in ki fara had'a kayan kafin nazo idan banzo da wuri ba ki kunna gas ki d'ora amma ki lura dashi sosai tunda da ba amfani kike dashi ba Saida kika zonan karya cutar dake".

Cike da tsananin rud'ewa Nafisa ta d'ago tana kallon Mom bayan ta gama yi mata lissafin abinda take so innalillahi yanzu me zatace mata bayan batasan komai akan haka ba Bara'atu ta sangartar da ita ko ruwan zafin da zatai wanka saidai ita ta dafa Mata tunda take bata ta'ba d'ora tukunya ba tashiga uku ta lalace yau ya zatai me zatace wanda zata fita hatta ashana tsoron kunnata take balle taji ana mata maganar wani abu da batama sanshi ba bata ta'ba ganinsa waishi gas😆.

"Nafisa tunanin me kike tashi kije kitchen ina zuwa yanzu zanga yadda kikeyi Kinga idan kika gama koya min kema kin huta ko? ai Nurain yayi daidai daya auro d'iyar karkara kodan farin cikin mahaifansa muna son cimar qauye😊 tashi maza kije".

Mi'kewa Nafisa tai jiki a sanyaye kamar an tsoma akuya a ruwan sanyi haka ta fara tafiya inda Mom d'in ta nuna mata ta bud'e kofa ta shiga humm wangamemen kitchen ne ta gani mai girma cike da kayayyakin aiki iri dabam dabam ga kuma wata kofar nan da alamar store ne shiru tayi ta tsaya tsam guri d'aya tana kallon komai bata ga abinda ta sani ba balle ta fara tunda azzaluman 'yan matan nan basu ta'ba barinta ta shiga koda kitchen d'in part d'inta ba kwal (gawayi) suka sayo buhu guda suka sashi a garden da mangal kullum anan take girki cikin zafin rana gashi Nurain bai saniba sun gargad'e ta duk ranar data nuna masa koda yar alama ce uhm nayi azabar da zasu d'an'dana mata bata fad'uwa basa barinta koda ruwa ne a fridge ta d'auka tasha saidai na tap kullum Nurain idan ya dawo zai taho mata da lemuka da yogurts iri iri amma sune ajalinsa bata ta'ba d'an'danawa ba ko sau d'aya ba idan aka koma 'bangaren fruits ga ayaba🍌 kankana🍉 dabino gwanda🥑 guava🍈 kwakwa🥥 Apple🍎 zaitun inibi🍇 amma duk haram dinta bata ta'ba ci ba tayi kukan ba'kin ciki ta 'kara gaci ga kwanan yunwa babu damar ta fad'awa Nurain karsu had'iyeta.

Shigowar Mom ganin tsaye ta 'kame guri d'aya yasa tace "a'a Nafisatu ya akai kika tsaya anan ko kayan aikin har yanzu baki gama saninsu ba"?.

Kai Nafisa ta girgiza jiki a sanyaye cike da fargaba da tarin dana sanin 'kin tsayawa ta koyi abinci datai lokacin da Bara'atu take fad'a mata jinta take a banza sai gashi data tsaya ta koya yau abun saiyài mata rana da hawaye a idonta dan batasan a yadda Mom zata d'au maganarta ba tace "tuwon ne ban iya ba😳".

Zaro ido Mom tai tana cewa "subahanallahi kina qauye acan aka haifeki kika girma baki ta'ba zuwa ko'ina ba amma kice wai tuwon ne baki iya ba?.

Shiru Nafisa tai tana 'kar-'kar da ido ta kasa magana Mom taci gaba "ai shikenan ba matsala idan kin ta'ba ganin yadda maman ki tayi ki tsaya zanyi sai kina nuna min yadda zansa komai yayi daidai yadda nakeson yayi tauri kin gane".

Kaita d'aga cike da kunya tana sauke ajiyar zuciya a hankali dan kada Mom ta jita tanan taji d'anji dama-dama tana tsaye tserere Mom ce ke komai abun data nuna matan ma kad'an ne saida ta gama ta sauke sannan tace ta koma parlor abinta bari tayi miyar ma kawai dama 'yar aikinta tayi tafiya ne shiyasa don ta fahimci kamar Nafisan bata iya komai ba amma tayi mamaki yaran qauye da suke tashi da 'kwazo da aiki wannan kuma yadai🤔 kodan ai mahaifan a qauyen ma iri dabam dabam ne wasu na koyawa wasu kuma babu ruwansu.

Saida ta gama bayan sallar magriba tace Nafisa taje part Mimih tayi sallah a tsorace ta shiga bedroom d'in duk da tasan bata nan amma gani take kamar zata shigo yanxu ta sameta wuta-wuta tayi sallah afujajan ta antayo waje ta dawo parlor ta zauna shiru shiru Mom bata fito ba har akai kiran sallar isha nanma fiii ta tashi dagudu taje tayo ta fito daidai Mom ta fito itama daga nata part d'in ganin yadda Nafisa take waige-waige yasa tace.

"Lafiya ko wani abune ya tsorata ki"?.

Da sauri Nafisa ta girgiza kai tana cewa "a'a ba komai".

Zama Mom tai akan kujera tana cewa "ok kije kitchen ki sako abinci yau babu mai mun aiki tayi tafiya''.

Nan ma kai Nafisa ta sake girgizawa cike da kunya ta kasa sannan ta gama taci duk tasan idan bataci anan ba ta koma su Mimih bazasu barta taci ba saidai idan Nurain ya dawo gidan‽ Tuna hakan dayai yasa batasan lokacin data mi'ke tayi hanyar kitchen ba ta d'ebo tazo babu kara ta zauna taci son ranta tasha ruwan roba yaudai ta d'ana🍶.

Sai kusan karfe goma na dare Nurain yazo da kansa suka tafi tare taji dad'i sosai da yake dashi ne su Mimih harda dur'kusawa har kasa suna gaida ita a fake suna mata nuni shikuwa dad'i neyake kamashi suna manyansu suke girmama masa mata domin ba wacce bata shekaru ba haka suka wuce abinsu Meelat na rakasu da harara dad'in abunma iya sune Zainab tana part d'inta a parlor tana aiki a laptop indai ba yanzu ta shiga bedroom ba.

Washe gari da

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login