Showing 162001 words to 165000 words out of 195514 words

Chapter 55 - ME KAMAR SARKI HAUSA NOVEL

YUSRAH   

22 Oct 2024

27277

babu ko d'aya a hannuna haka nake hatta sar'kar wuyana wacce da ita nake da damar zuwa dajin siddabaru yanxu ta 'bata ban ganta bansan ta yadda zan ri'ka zuwa ana komai dani ba Daddy ya zanyi"?.

Dariya Prof yai yana cewa "ok kada ki damu Hudayyah zata kawo miki komai a yau amma ki tabbata ba'a gane ba kicewa mahaifanki zakiyi bakuwa su bari ki fito ki tareta da kanki Dan kada a hanata shiga a garin bincike suga wani abu yau zaki dawo duniyar shan jini idan kin fito kin tareta".

Da sauri Khimiyyah tace "to shikenan Daddy zanyi zan fito na tareta bari naje yanzu na fad'awa ummana domin nasan itace xata fahimce ni saina samu na fito na tareta" ok Prof yace yana sau'ke wayar kafin ya kalli Hudayyah dake ri'ke da photon Muheed tana kallon yace.

"Daughter ki rage yawan tunani a kansa tunda Khimiyyah ta dawo komai yazo karshe yarinya mai hikida da basira ta farfad'o yanxu aka fara wasan kada ki damu kin sameshi muje" yana rufe baki ya murza wani zoben💍 tsafi dake hannunsa suka 'bace daidai Halima ta fito taga sunyi 'bat a idonta a firgice ta fasa qara tana zubewa a gurin ta suma tsabar razani domin batai tunanin masifar da suka debowa kansu har takai haka su ri'ka 'bacewa ba.

MALAM HABU
____Yanzu alhamdulillah malam Habu an fara yi masa d'ayan maganin shed'anun kuma da akai sa'a sai abun yaso a bazata wato dai duk taurin kansu malamin ya gagaresu tun yana tambayarsu suna masa fitsara har takaiga sun fara ihu da 'ka'kaji suna neman ya kyalesu dan Allah zasu fice shikam Malam yai banza dasu saida ya babbaka musu jiki sosai sannan yayi musu gargad'in basu su ba malam Habu ba xuriyarsa koda wasa suka dawo saiya dau mummunan mataki a kansu kuma sun amince sun fita daga jikin Malam Habu kamar yadda sukace har abada shikenaannnn💃 tun daga lokacin Malam Habu ya bud'e babin sabuwar rayuwa Mai cike da farin ciki babu matsalar komai babu damuwar komai daidai yake tafiya bayan abun sadaka daya baiwa malamin duk sati saiya sayi d'an abun arziki yaje ya gaida malamin kuma yayi masa godiya saboda jin dad'i.

🌐KAUYEN ILUH🌐
Bahijjah tana d'aki a kwance tayi d'ai d'ai tana hutawa Iluh yana kusa da ita suna hira Inna tazo bakin kofar d'akin tana 'kwala mata kiran cewata fito suyi sissika za'ai abincin rana.

Zaro ido Bahijjah tai tana tashi zaune tace "mee sissika kuma"?.

Amsa Inna dake bakin kofar d'aki tsaye tai "eh sissikar geron za'ai kunu kiyi sauri ki fito ke kad'ai ake jira Yawuro da Bulgah duk suna can bayan gida'' tana fad'in haka tabar kofar d'akin.

Kai Bahijjah ta jinjina tana kallon Iluh daya maye inda ta tashi ya kwanta ya mimmi'ke baida niyyar cewa komai alhali yasan ita amarya ce kwata-kwata kwanan ta nawa a garin har zata fara wani aikin gida kuma sissika ma abinda bata ta'ba yiba heyyy tabdijan wallahi da sakal.............

Katse mata tunani yai da cewa "Bahijjah ba Inna ce tayi miki maganar aiki ba suna jiranki fa"?.

Had'e rai tayi tana kallon sa tace "Hum'um yanzu tsakani da Allah abinda zakace min kenan"?.

"Kamar ya abinda zance miki kenan ban gane ba"?.

Bahijjah kamar zata rufeshi da duka dan haushi tace "kani jin abinda Innarka tace wai na fita nayi sissika bayan ko wata banyi a gidan nan ba ni wallahi ko dakan yaji ban ta'ba yiba tunda nake balle aikin qarfi irin wannan gaskiya kaje ka fad'a Mata ban iya ba".

Da mamaki yake kallonta jin abinda tace kafin yace "baki ta'ba ko dakan yaji ba kikace? To waye yake muku aikin gidanku ko kina zaune mahaifiyar ki take komai bakya taya ta"?.

"Ni bana aiki kuma itama ba ita takeyi ba Indo ce".

"Oh wacce da zata aura min 'yar gidan kishiyarta abin bai yuwu ba humm saiya fad'o kanki to nikam bani da bakin magana kawai ki tashi kije ki kama musu aiki ke kin taki sa'a ma tunda aka barki kikai kusan sati uku baki komai ba mu garin nan a al'adar mu tun washe garin da aka kawoki dakinki zaki fara aikin gida uwar miji ta daina komai intai surika saidai tana zaune ayi komai akai mata Kinga lokacin da yayana Sado ya auro Bulgah hum gabadaya girman gidan nan saita share tayi wanke wanke tayi girki ta kai shanun Baffah kiwo tayowa awakai ciyawa ke hatta wankin kayan Inna Dana Baffah ita kad'ai takeyi saida ta samu d'ayan yayan nawa Shima ya aure ya auri Yawuro sannan ta samu sassauci suke komai su biyu yanxu sun sake samun sau'ki suma zuwanki dan haka ha'kuri zakiyi mu haka al'adarmu take ki tashi kije".

Kai Bahijjah ta jinjina tana ta'be baki tace "na tashi naje ina? Gaskiya fa bari na fito fili na fad'a maka indai haka ne bazan iya ba taya zan zama baiwa karfi da yaji aure nazo ba bautar tsakar gida ba ka gane dan haka kaje kaiwa Innarka bayani mu garin mu ba haka ake ba bamusan da wannan ba jikina ba jikin aiki bane".

Tashi zaune Iluh yai yana kallonta yace "me kike nufi nine zanje nacewa inna bazaki iya aiki ba tsabar bani da kunya mufa fulani ne kin gane muna data ido dan haka idan ba so kike na nuna miki 6acin Raina ba ki tashi yanxun nan kije kuyi aiki dan garin ku ba'ayi kin baro garin ku dole da al'adar nan zaki amfani".

Mi'kewa Bahijjah tai ranta a 'bace tace "amma................,...

Katseta yai "amma me? Kinga Bahijjah karki sa raina ya 'baci domin Inna zataga kamar nine nake goyon bayan ki idan Inna ta had'ani da Baffah zansha fad'a ne dan haka kawai kije".

Jin abinda yace yasa Bahijjah ko tsayawa ta dau hijab batai ba tsabar 'bacin rai kawai ta tafi haka a karkashin wata 'katuwar bishiyar d'orawa ta gansu kowacce da sanduna sai bugun dami damin gero suke kamar maza ko sallama batai ba tsabar takaici taje kawai ta tsaya domin gaskiya itafa bazata iya wannan aikin ba akan haka saidai aurenta ya mutu ta za'bi zama karamar bazawara akan masifar da taga tana tunkarota.........................

"Hijjah bismilllah mana ga naki sandan nan yanzu aka 'ballo miki kar rana tayi" Inna ta fad'a tana nuna mata.

Kallon sandan Bahijjah tai d'anye sharaf yake da alama zaiyi nauyi kamar zata ce ita bazatai ba domin bata iya ba sai kuma ta fasa ta d'auki sandan a bisa dole cikin rashin iyawa da rashin sabo ta fara bugawa numfashin ta yana sama yana qasa haka suka gama aka koma kan bakacewa Bahijjah dai ba'kin ciki kamar zai kasheta suka wuni suna aiki jikinta yayi butu butu duk qaiqayi gashi data koma zatai wanka Iluh bayanan ya fice babu sabulu ga yunwa da takeji balle ita kunu ba masoyinta bane haka ta zauna a kofar d'aki zaman jiran dawowarsa kamar ta d'ora hannu aka ta fashe da kuka haka takeji itadai zata fad'a masa bazata iya zaman wannan rugar tasu ba gara ya tattara su koma can garin su ko a shagon da yake kwana ne ta yarda zata zauna akan nan domin inta yarda taci gaba da zama anan zuciyarta ce zata buga a banza da ciwon ran aiki.


🏙️KANO🏙️
Humm Saleem fa ya yazo ganin gida Alhaji Musa sai ji dashi yake kamar wani jaririn goye yace wannan yace wancan tsabar shagwa'ba wani San idan yana magana saikai tunanin mace ce idan ba ka ganshi ba.

Yauma kamar kullum suna zaune a falo shida Hajiya Aisha tanace masa ya tashi yaje ya gano yan gidansu yace mata sai an jima zaije sai lallai take kamar kwai akan yaje yanzu amma ya'ki sam sai girgiza yake yana kad'a kai yana cewa.

"Allah Allah nifa nace miki sai anjima zanje ba yanzu ba".

Ri'ke baki Hajiya Aisha tao tana kallon sa tace "oh nikam Saleem anya zaka girma kuwa wai har yanzu baza daina shagwa'ba ba yaushe zaka daina kenan"?.

Dariya yayi har dimple dinsa yana lotsawa kafin yace "saina fara ganin 'ya'yana Mom".

Zaro ido Hajiya Aisha tai tana cewa "to 'ya'yanka dai aure zakai ka samu matar ne"?.

Kaiya d'aga mata "eh gaskiya ni na samu kuma dama inaso na fad'a miki keda Dad fa".

"Wacece a ina take"?.

Hajiya Aisha ta tambaya cikin zumud'i tana sake kallon sa d'an juyar da fuska yai yana murmushi kamar mai jin kunya yace "ban san sunanta ba".

"Baka san sunanta ba? To a ina take ko acan kuka had'u karatu taje"?.

"A'a Mom bafa acan muka had'u ba anan gidan na ganta".

Cike da mamaki Hajiya Aisha tace "anan gidan kuma da yaushe nayi ba'kin 'yan mata kwana kusa ne"?.

Kaiya girgiza "no ba ba'ki bane wacce take miki aiki".

"Eye Asma'u kake nufi ko Jamila"?.

"Nifa Mom bansan sunan suba amma dai karamar domin babbar ai zamuyi sa'anni Mom idan ma nafita da kadan ne" ya fad'a yana kallon ta.

"Ok Jamila kenan kake nufi indai ba Asma'u ba domin su biyu suke zuwa kullum".

"Eh ita nake nufi sunanta Jamila? Nice name amma Mom za'a bani ita zaku bari na auri 'yar aiki ko a'a saina samo wata"?.

Kai Hajiya Aisha ta d'aga "eh mezai hana ka aureta shalele ita ba mutum bace kodan tana yar aiki? humm babu wanda yafi karfin jarrabawa saboda haka karka damu baby Daddynka ya dawo zan sameshi akan maganar kaji".

"Ok Mom much appreciated Ina godiya".

Da dare bayan Alhaji Musa ya dawo daga office ya yayi wanka da sallah yana parlon sa yana hutawa Hajiya Aisha ta shiga da sallama tana cewa.

"Alhaji kaci abincin kuwa kayi hakuri wallahi sallah nayi shiyasa banzo da wuri nayi serving d'inka ba".

Murmushi yana kallon ta yace "haba ke kuwa yada dogon bayani haka kamar bansan halinki ba aina sani tunda naji shiru na fahimci uziri ne ya hanaki zuwa".

Cikin jin dad'in yabonta dayai yasa ta sake sabon zama tana kallon sa hankalin sa Shima yana kanta tace.

"Alhaji nikam idan bazaka damu ba zan baka wata shawara"?.

Kaiya d'aga mata yana cewa "ok Ina jinki meya faru wacce irin shawara ce me kika hango min wanda niban hango ba"? ya karasa maganar yana mayar da hankalin sa kan TV da murmushi a fuskarsa domin duk lokacin da zata fad'a masa wani abu haka take cewa.

Gyara zama Hajiya Aisha tai tana fuskantar sa sosai tace "duk da bansan a yadda zaka d'auki maganar ba amma zan fad'a maka Alhaji mezai hana ka auri Asma'u 'yar gidan malam Habubakar😳"?.

Cikin mamaki wanda ba arziki ya juyo yana kallon ta jin abinda tace wanda aransa bai ta'ba kawowa haka zatace masa ba yace.

"Na auri Asma'u kuma Aisha"?.

Kaita d'aga masa "eh Alhaji ko Allah zaisa a dace kasan lalume a duhu bakasan inda zaka samu sa'a ba nidai burina naganka da d'a naka koba nice na haifa ba zanyi farin ciki a wannan ranar har bansan yadda zan musalta maka ka fahimta ba".

Kaiya girgiza yana cewa "amma Aisha Asma'u fa 'yar cikina ce nasan da ace Allah ya bani haihuwa dazan haifi sa'ar ta".

Ajiyar zuciya ta sau'ke tana cewa "haka ne Alhaji amma ai anayi mutum nawa ne suke auren 'yan cikin nasu garakai zatai sa'ar dan'ka na fari kake haskowa inaga wadanda kawai dan ra'ayi suke auren 'yan matan wasu ma sai kaga basufi sa'annin yaransu na hud'u ba kuma sun auresu".

"Kuma ke a ganinki malam Abubakar zai bani aurenta ne"?.

"kwarai na tabbata wannan mutumin d'an arziki ne zai baka koda ace bakai masa komai ba kuma ka gwada ka gani Alhaji amma nikam ina maka kwadayin auren yarinyar haka nan bansan miyasa ba dan Allah kada kace a'a ka sameshi wallahi shawara mai kyau ce kaji"?.

Shiru yai cikin nazari da tunani shikam yana jin kunyar tunkarar malam Habu da wannan babbar bu'kata duk da yasan bazai ta'ba hana shiba amma dai gaskiyar magana bazai iyaba yana jin nauyi...........

Muryar Hajiya Aisha ce ta katse masa tunani "Alhaji kabar 'bata lokaci akan tunani Allah da gaske nake magana komai da nake fad'a maka kuma kaga auren mutum biyu zaka nema domin d'azun nan shalele yace min shikuma Jamila 'kanwarta yake so kaga shikenan fad'uwa tazo daidai da zama".

Kasa magana ma shikam Alhaji Musa yai sai zulumi da tunanin ta yadda zai 'bullowa al'amarin yake iya Hajiya Aisha ke magana tana sake lalla'ba shi da bashi qwarin gwiwa akan auren domin taga alamar har lokacin baiyi accepted din nasa auren da Asma'un ba.

Bayan sati biyu Amatu tana zaune a dakinsu babu kowa ita kad'ai ce tana duba laptop d'inta kamar kullum saidai yau aikin assignment take ba bincike ba ba zato kwatsam taji saukar abu a d'akin kamar zai zubar da gidan gabadaya yadda taji dirarsa da mugun 'karfi a firgice ta d'ago tana kallon gurin arba idonta yai da 'yan mata biyu tsaye da kayan tsafi jawur a jikinsu fuskarsu sun fanteta da kaloli sun zagaye idanuwansu da ba'kin kwalli kome saninka dasu bazaka ganesu ba a wannan shigar (Khimiyyah ce da Hudayyah🤔) suna tsaye sun zubo mata ido kamar yadda itama take kallon nasu cike da tsananin mamaki a ranta kafin batare da jin wani tsoro ko d'ar ba tace.

"Su waye ku daga ina kuke me kuke nema anan meya kawo ku"?.

Kallon juna sukai suna murmushi sannan suka jinjina kai kallonta Hudayyah tai tana cewa "ke kada kiso sanin komu su waye domin zaki hallaka kin gane ba wannan ya kawo mu gurin kiba idan da ace zuwa mukai don kisanmu ai bazamu 'boye miki siffarmu ba".

Matsowa kusa Khimiyyah tai tana cewa "ke bari kiji abinda ya kawo mu gurin ki munzo ne muyi miki gargad'i na farko kuma na karshe akan shishshigin da kikeyi kina neman jefa rayuwarki cikin risks indai baki saurara kin dakata haka kin nutsu kin d'auke hankalinki akan muba to Ina mai tabbatar miki da an kusa kaiki kabari domin duk wanda yasan sirrinmu bai kamata ya rayu ba duk mai son gano wani dake cikin 'kungiyarmu kashe shi muke mu ma'kiyan kashe shi muke dan haka kada ki kuskura tsautsayi yasa ki sake bincike a kanmu zakiga sakamakon taurin kai sannan idan muka tafi kika fad'awa wani zakiga 'karshen ki abu na karshe mi'ko min laptop din nan" Khimiyyah ta fad'a tana mi'ka mata hannu.

Wani banzan kallo Amatu tai mata tana cewa "waye zai baki laptop din amma dai ba dani kike ba domin Wallahi koda uwarki kike tafiya duk inda zakije bazan bayar ba kin gane baki da fuskar da za'a kalla ki razana mutum balle har ki sanya tsoro yayi tasiri a raina maza maza kuyi gaggawar barin nan kafin kuga yadda ake hauka domin na fiku d'anyan kai duk abinda kukaje a ranku na zarta ku".

Baki bud'e suke kallonta mamaki ya cikasu wato dai ta nuna jarumtakarta a fili ta cancanti jinjina wannan da alama za'a fafata da ita to su yanxu me zasuwa Prof Jibril daya ce kada su koma daba laptop d'inba zasuji kunya su biyu kuma suna cikin kayan tsafi su kasa yi da mutum d'aya kuma mace kallon Hudayyah Khimiyyah tai da ido sukai magana kafin cikin zafin nama Khimiyyah tayi wuf zata d'auke laptop din wanda dama Amatu already a ankare take dasu tana cikin shiri itama a zafafe ta janye laptop din tana d'aga wata kwalbar lemo dake kusa da ita da dukkan qarfinta ta dokawa Khimiyyah a hannu wanda saida kwalbar ta fashe tuni jini ya fara zuba ihu Khimiyyah tai cike da azaba Hudayyah data zaro ido da sauri ta matso ganin jinin har tsartuwa yake yasa ta sakarwa Amatu wani micijin🐍 tsafi yayo kan wuuuuuu baki a bud'e mi'kewa tsaye Amatu tai tare da d'aukar wani sanda dake jingine ta d'aga zata kwad'awa micijin ya 6ace 'bat huci Hudayyah cikin kunar tana kallon Khimiyyah dake du'ke tana lashe jininta daya zuba kafin ta d'ago tana kallon Amatu wacce ke ri'ke da sanda zatai magana Amatu ta d'aga mata hannu.

"Kinga malamai kun ishe shi wannan kuje ku nemi mahauci irin ku wanda baida aikin yi kun gane mayu kawai ke ki daina lashe wannan jinin are you a witch"? (Mayya) nace ku mayu ne to kun ganni nan ni Hauwa'u Abubakar nafi qarfinku.

Mi'kewa Khimiyyah tai a fusace tana tada tsafi suka sake yowa kanta duk su biyun daidai Binta ta karaso kofar d'akin tana cewa.

"Mamar gida anan nake jin ihu ne"?.

Da sauri su Khimiyyah suka 'bace sai d'an haya'ki kadan shigowa Binta tai ganin haya'ki yasa tace "wannan hayakin kuma daga Ina ko wutar da A'i ta hura a kitchen ce dama yana shigo muku baku fad'a ba"?.

Kai Amatu ta girgiza tana cewa "a'a baya shigowa".

"Oh to ina ganin yau din ko iska ce take kad'oshi da yake yau an tashi da iskar ai shikenan me kikeyi ne duk muna waje yau harda su Asma'u basuje aiki ba Hajiya tayi tafiya ga kaji can malam ya kawo munata gyarawa kar ace bakya gurin ki fito".

To Amatu tace bayan Binta ta fice ta tsaya kallon d'akin komai ya koma tsaf tsaf a gyare kamar babu abinda ya faru cafd'i hatta kwalbar data fasa ta koma yadda take gudarta🍶 jinin ma babu tsaki taja tana cewa.

"Humm dama ai tun daga ganin sunan wannan tsinanniyar 'kungiyar nasan bata mutanen arziki bace harda jini kuke sha waini zaku nunawa fear and fear barazana in action😂? sai kuma tayi dariya tana cewa "wallahi ina daidai daku na mu zuba mu gani saina kawo baku mamaki nice karshen zaluncinku banzaye kawai ma'karyatan banza da wasu tatsuniyoyin ku na rainin hankali mtswwwwogon tsuka tana d'aukar laptop d'inta tayi waje.

GIDAN NURAIN
Sosai Zainab ta kwantar da hankalinta kamar auren Nurain d'in baya cin raita amma tayi mamakin yadda ta iya dannewa bata nuna masa ba sai wata sabuwar soyayya da suka bud'e babinta suke zubawa juna a bangare guda kuma ta roki alfalmar bayan biki tana so 'kanninta Mimah da Meelat zasu Dan tsaya suyi mata gyare gyare a part d'inta da nasa dan bataso yar aiki taga asirin su da kuma goge gogen kayan kitchen kuma ya amince mata a ranar tayi waya dasu tace suzo Nurain shima yana da 'kanwa gud'a d'aya sunanta Mimih da kuma 'yar riko sunanta Meenah taso Nurain amma ya'ki tayi bi tayi kuka ya'ki aurenta tana bala'in kishi da Zainab ana haka taji

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login