Showing 159001 words to 162000 words out of 195514 words

Chapter 54 - ME KAMAR SARKI HAUSA NOVEL

YUSRAH   

22 Oct 2024

27253

d'in ya tafi ne naji kace ranar shine yake buga maka kofa sassafen nan wai yazo sallama kafin ya tafi ko yana tunanin zakaji tausayinsa ne ko ka damu dashi"?.

Ta'be baki Ilyah yai "meye damuwa ta da inda zaije saiya dawo idan bazai dawo shikenan wata tsiyar zai bani Habubakar tsanar danai masa zatasa naji tausayinsa ne kina kallon abubuwan da yaran nan suka ri'ka min a kansa"?.

Kai Bara'atu ta d'aga "tabbas na gani amma naji kace kaine ka saye gonarsa da gidansa ko"?.

"Eh nine saboda na wulakanta shi na ba'kanta masa yaji d'aci a ransa saida na bari yazo ya gama 'kasqantar da kansa a guna na ci masa mutunci nayi masa korar kare fata-fata daga kofar gidana sannan na bari aka rushe gidan kafin naje yana tsaye da d'aurin kayayyakin su a gabansu suna kallon ana ni'ke gidan da babbar mota sannan na sayi gidan a gabansu na biya kud'in ko inda suke ban kalla ba humm yana can wasu sun had'u da bala'i tunda shi ya zama karfa idan ya ra'beka duk arzikinka saika talauce".

Dariya Bara'atu tai harda rausaya kai tana cewa "to ko ya d'auka zaka hanashi tafiya ne kace ka bashi gida da jari shiyasa yaxo maka sallama"?.

'kya6e fuska Ilyah yai yana cewa "waa🙄 nine zan bashi gida ya zauna harda wani jari Habubakar fa? ai wallahi da saidai ya kare rayuwar sa a kan layi har abada Bara'atu baki san yadda na tsani Habubakar akan abinda su Hussaini sukai min ba shiyasa kika ce haka mutumin daya jawo sukaita sakani kuka da ba'kin ciki akan 'ya'yansa har yana da baki magana a gabana humm''.

Murmushi Bara'atu tai tana cewa "to balle kuma ni kana gani dai lokacin da yazo gidan nan da 'yarsa akan kace kila yunwa nake ji na auna masa garin kwaki dan kawai nace masa kaima ka fahimci abinda ya kawo shi gidan neman abinci ne shikenan ya ri'ka zazzaga min bala'i harda marin Nafisa tsabar mugunta".

Cizon yatsa Ilyah yai yana cewa "ai ya mari Allah ya isa akan wannan marin ma nayi matukar jin haushin sa shiyasa komai nake masa da gayya garama daya talauce Allah yasa bazai sake yin arziki ba a duniya duk inda ma yaje yadda ya tafi babu komai ya dawo a tsiyace a firgice".

"Amin Amin" Bara'atu ta fad'a harda shafa hannu a fuska kafin tace "humm bari na mi'ke nima tunda yau nice da girki na d'ora kada rana tayi Nafisa su dawo daga anguwar nan bab gama ba ranta ya 'baci🤔 ai duk laifinka ne kaine ka hanata girki a gidan nan saidai taci ta kwanta hatta wanke wanke bata yimin balle shara" ta fad'a tana mi'kewa.

Murgina kai Ilyah yai yana cewa "eh shalele bazatai girki ta ri'ka 'kaurin haya'ki ba ita da zataje birni idan kuma wanke kwanuka ne ki nemo yarinya d'aya a 'ya'yan talakawan garin nan ta ri'ka yi miki daga yau zan ri'ka bada kud'in amma dai Nafisa bazata ta'ba hura wuta ba ita jikinta ba wahala bane 'yar hutu ce".

Dariya Bara'atu tai harda irin fasa kan nan wai 'ya bazatai aikin wahala ba sannan tace "ai shikenan masu 'ya dan ma kwanan nan zamusha bikin kuma tayi sa'a acan ba aiki zatai ba tunda d'an me kud'i tana daga kwance a mimmi'ke za'ai mata komai saidai taci tasha tabi lafiyar gado gaskiya Nafisa fa ta taki sa'a ta iya za'be" ta fad'a tana juyowa ta kalli iya cike da salon munafirci tace.

"Amma dama Ina so na sameka kayi wa Salma magana ta canza saurayi gaskiya Adamu gidansu talakawa ne kanaji fa hatsin da suke nomawa baya kaisu shekara da awu suke karasawa amma duk garin nan ta rasa wa takeso sai shi haka ranar Nafisa tace ta gansu shida babansa sai sauri suke kamar zasu kifa 'kafarsu babu takalmi sun nannad'e wanduna kowa rataye da fartanya sun tafi noman kud'i gonar Mai gari hum'um idan baka hanata aurensa bama daga baya maimakon ta samu tana aikowa gida kamar yadda Nafisa zatai itadai saidai daga nan a d'auki gudun mawar abinci akai mata ka samu maimuna kayi mata magana amma ya ka gani"?.

Kai Ilyah ya girgiza yana cewa "ba ruwana tun farko saida nayi mata maganar gidansu yaron nan sanda ya fara zuwa kofar gidan nan yasa a Kira Salma amma sai tace ba komai idan da rabo Allah ya sanya alkairi wai zai iya ri'keta indai da rufin asiri shikenan shiyasa ni kuma nan gaba bayan anyi aure kome zai faru bazan tanka ba kuma bazan nuna na sani ba bazan taimaka mata da lomar abinci ba idan ita Maimunan data goyi da bayanta ne ta kawo min wani qorafin banza sai naci mutuncin ta dan saboda banason harka jeka ka dawo yasa nace su bari me kud'i yazo amma sun 'ki".

Ta'be baki Bara'atu tai tana cewa "ai shikenan mukam yan kallo yadda ba komai dai gidansu Adamu suke dashi kila ko akwati baza ayi mata ba a samu sadakin ma ya fito balle aje maganar daki ance da'kyar ya gina dakuna biyu na kasa ko suminti baiyi ba hatta rufin d'akin da 'kasa yai balle asa ran zaiyi mata 'yar barandar shan iska".

"To nikam Bara'atu tunda Salma ce ta za'bawa kanta ba ruwa na aikina nayi mata kayan d'aki da gara a kaita a ajiye ba shikenan ba nikam na gama fita dabara ta ragewa mai shiga rijiya ko ya kama igiya ya shiga koya dirga🤔.

Ha'ba Bara'atu ta ri'ke tana cewa "ai shikenan d'in Nima abinda zance kenan amma Salma bata more ba zatai rayuwa cikin 'kunci da talauci duk kud'in ubanta da gatan data taso zata je ta auri dangin talakawa😣 tana kallo Nafisa zata ri'ka zuwa a babbar mota a 'koshe dam ta ita tayi jawur abinta ita tana 'kai'kashe kamar 'kanzo'' Ilyah dai bai sake ko tari ba sai Bara'atu daketa mata ita kad'ai tana aiki tare da jin farin ciki a ranta ta wani gurin gara da Salma ta za'bi Adamun ma dan bata so su goga kafad'a da Nafisan kowa ta auri mai kud'i ina tayi zamanta a qauye ta haifi qauyawa Nafisa dake birni ta haifi wayayyu gogaggu🤨.

HUM BARA'ATU MUJE ZUWA DAI GAGGAWAR ME KIKE ME HANKALI YA HAU KURA🐆🐵.

Bikin Bahijjah da iluh ya kankama Asabe bata komai tace ita yanzu Bahijjah ba 'yarta bace komai Markah ake kaiwa take ajiyewa kafin bayan bikin idan Asaben ta sauko ta debo ta kawo mata domin tasan yanxun fushin da take yasa ta'ki kar'ba.

Hatta taron bikin sai a can gidan marka akai ranar da aka d'aura aure Asabe ta gwangwaje da kuka kamar ta mutu tabar duniya haka taji ranar tsabar ba'kin ciki har saida hawan jininta ya tashi anyi biki an gwangwaje dan Bahijjah takanas taje har wani gari ta d'auko d'an DJ tana rawa a layi da yake garin ba'a saba ba haka aka taru fal harda yan sauran qauyukan sai kallonta ake ana gulma ga Asabe can kwance kamar gawa jinya ta tashi da aka zo aka fad'a Mata sai tasa mai DJ ya sake 'kure volume🔉 🔊 babu abinda yai tsalle ya d'od'a mata mari tace wallahi Asabe bazata tada jinyar qarya ta hanata shagali ranar bikinta guda ba dama ai bason auren take ba dan haka babu wata jinya baza'a kashe DJ ba saidai ba'kin ciki ya karta.

Maimakon ta bari tunda taga Asabe a yadda take sai juyata ake tsabar yadda jinin nata yahau batasan inda kanta yake ba amma kawai da dare daga garin su Iluh akazo da mota d'aukar ta ko sallama jiki na mazari zata fice taje su tafi Markah ta hata tace ta bari ga a yadda Asabe take nanda sati idan taji sau'ki sai ayi rakiyar amma haka Bahijjah ta 'ke'kasa qasa tace wallahi yau dai kwanan d'akin mijinta zatai bazata sake kwanan anan garin ba idan jinya Allah ya sauwake babu wanda ya isa ya hanata taji tunda Markah ma tayi iya kokarin ta bata saurare taba wa zai magana ta tsiyata shi ta fige masa gashin arziki.

Dole haka Markah ta wuce gaba dasu Mairo aka d'auki Bahijjah suka kaita qauyen su Iluh humm so hana ganin laifi gara garinsu sau d'ari akan qauyen baifi gidaje goma ba kuma ba had'e suke ba a warwatse can gida can gida haka suka gama abinda zasuyi suka taho jiki a sa'bule kamar ruwa ya cinyesu domin acan ko d'aki basayi kuma rugace sai bukkoki🏕️ masu rufin yayi😔.

Koda suka dawo jikinsu a sanyaye Markah da Mairo basu nunawa Asabe komai ba dan kada tashin hankalin yayi mata yawa kawai dai sun sake dubata tare da fad'a mata cewa sunkai Bahijjah d'akinta lafiya, jin haka yasa hawaye yayita ambaliya a idanuwan Asabe tana daga kwance ba'kin ciki ya danne mata harshe ta kasa magana sai kai kawai take girgizawa ha'kuri sosai da lallashinta su Mairo sukai tare da nuna Mata babu komai ta daina damuwa tunda kaddarar Bahijjah ce auren Iluh sannan suka tashi sukai mata saida safe suka tafi haka Asabe taita gurzar kuka kamar ta mutu tabar duniya Balarabe yana zaune a can gefe ya zuba mata ido kuma yana sauraren duk hirar da sukai dasu Markah amma tari dabai kamashi ba baiyi ba sai alhamdulillah kad'ai da yake furtawa a cikin zuciyarsa domin har tausayin Indo ya kamashi da da Asaben take 'kulaficin sai an baiwa Iluh gashi ita kuma yau tayi kukan bashi tata 'yar ashe dama tasan zaluntar Indon zatai sai kuma Allah ya tsallakar da ita daga tarkonta ya tabbata a yanxu Indo tana cikin kwanciyar hankali kuma abu daya dake damunsa shine ya dawo da Dalah d'akinta abinda ya rage masa kenan yanxu a rayuwa insha Allahu gobe zaije gidansu ya sameta akan komen tana mi'kewa yai yana kallon Asabe daketa faman tsinewa Iluh baice mata'kala ba ya nad'e tabarmarsa ya shige d'aki.

🥕OSUN🥕
Indo tana zaune a d'aki suna zancensu da angoriyenta Dauda shi yana kwance yayi matashin kai da cinyarta sai dariya suke abinsu cikin nishad'i sukaji anyi sallama da sauri Indo ta janye kansa tana tashi tsaye ta koma kan kujera ta zauna harda d'an zaro ido.

'Dan harararta Dauda yai yana cewa "bismilllah kasaso maman Niseh shigo ciki muna nan


Dariya Maman Niseh tai tana shigowa tace "aina dauka bacine kuna yi nace ina salama shiru ashe kana gida yau baka fita ba dama nace bari nazo naga amaryar ka ne".

Maman Niseh bayerabiya ce a mokoftansu take suna mutunci sosai da Dauda tunda dad'ewa ko gida idan zai tafi ita yake barwa ajiyar mashin d'insa.

Tashi zaune Dauda yai yana kallon yadda Indo ta kame guri d'aya kamar zaiyi dariya yace "wallahi maman Niseh kin ganta nan cousin d'ina ce".

Zaro ido maman Niseh tai da irin surprise d'in nan tace "to abun nan na irin gida kukayi dama da gaske ne kanayi da kace min kana son yar uwa naka zaka aureta"?.

Kallon Indo Dauda yayi daidai itama ta d'ago da mamakin dama yana sonta ne gira ya d'age mata yana kashe ido kafin yacewa maman Niseh.

"Eh itace tayi ko na iya za'be"?.

Kai maman Niseh ta d'aga tana murmushi tace "walay Doda ka iya zabe sosefa wannan beauty Ale bada zeman lafiya nima yanxu na samu makociya zaki rika shiga min muna hirako"?.

"Kai Indo ta d'aga "eh zan shigo miki insha Allah".

"Yewa ameryan Doda ashe wayeya ce ka iya zabe bari na tafi na baro yan makade a gidan kuma Niseh bata nen Ikki ma bata nen sun tafi school" ta fad'a tana mi'kewa.

"To maman Niseh ki gaida gida mun gode sosai saita shigo miki" Dauda ya fad'a yana kallon Indo data mi'ke tsaye yace.

"Wato shine dan kinji sallama harda ture min kai ko"?.

Shiru Indo tai tana turo baki tace "to ai nayi tunanin shigowa zatai kai tsaye.

"Haka kawai saita shigowa mutane d'aki kai tsaye kamar wata mara hankali kedai kice har yanzu qauyanci ne bai barki ba kamar baki dad'e a nan d'in ba".

Jin abinda yace yasa Indo ta had'e rai zatai magana yace "zo nan" gumm tai da bakinta tana d'an matsawa wajen kofar fita ganin guduwa take shirin yi yasa ya mi'ke wuf tayi zatai waje ya dam'kota yana dawowa da ita cikin d'akin ya rungumeta ta baya kenan suka ga an d'aga musu labule wata yarinya ta shigo a d'ayan d'akin suke haya da sauri ya saketa yana matsawa baya ya koma kan katifa ya zauna dariya Indo tai tana kallon sa ganin ya harareta yasa ta rufe baki cike da tsokana tayi masa magana da ido kai ya jinjina irin bari yarinyar ta fita zasu had'u ne zaro ido tayi tana masa gwalo kafin ta mayar da hankalinta kan yarinyar tana cewa.

"Amrat me ya faru"?.

Itakam yarinya da ba abinda suke ne a gabanta ba tace "wai gashi inji momyna mun dawo daga anguwa da daddy ya sayo min a hanya shine tace na kawo miki".

Kar'bar kwanon Indo tai kayan marmari ne a ciki a wankesu tas tace "yauwa Amrat kicewa mamanki na gode" ta tace har zata fita ganin kanta an fara tsefewa maybe a anguwar da sukaje ne ta'ki aka 'kyale ta dama da lallami Indon take mata tazar ko a gida dan haka tace.

"Amrat kukan taza kikai"?.

Kaita d'aga "eh wata ce acan wai saita yimin kitso ni kuwa inata kuka".

Ri'ko hannunta Indo tai tana cewa "oh ayya sannu Amrat d'ina yi ha'kuri ta ja miki kai ko rabu da ita zo zauna na karasa miki a hankali" ta fad'a tana zaunar da ita zaro ido Dauda yai dan ya fahimci inda Indo d'in ta dosa amma saiya shareta yana yin qwafa kafin ya mike yana d'aukar key d'in mashin ya fice yana cewa.

"Huyim yarinya gama zille zillenki zamu had'u ne".

Ita dai Indo dariya tai bayan fitarsa tace "oho dai kafin mu had'un aina huta ko haba wallahi ya Dauda akwai cuta ni bari ya dawo ma naga mangoro ya nuna a gidan maman Niseh d'in nan muje ya tsinko min raina ya biya🤔" ta karasa maganar tana fara gyarawa yarinyar gashinta daidai maman Amrat tazo bakin kofar tana cewa.

"Assalamu alaikum ke kad'ai dan Naga takalma biyu"?.

"Eh ni kad'ai ce maman Amrat shigo da d'ayan ya fita" shigowa tai ganin yadda Amrat ta zauna ake mata taza hankali kwance tace.

"Lallai yarinyar wato mukaje dake Ummi tana so ta miki kitson three babies kika 'ki amma da yake mun dawo gida har falli ana miki tazar kina zance ai shikenan zan Kira ummin na fad'a Mata nace duk ranar da kuka had'u kikai mata kaud'i ta zane ki" ita dai Amrat batai magana ba sai Indo datai dariya tana cewa.

"Ai babu inda zata koma balle ta daketa ranar da zaku tafi a gurina zata zauna kuje ku dawo ko Amrat"?.

Kai Amrat ta d'aga "eh Aunty Indo bazan koma gurin Aunty Ummi ba tunda ta zageni".

"Kaikaikai lalala harda zagi ah gaskiya bazaki koma mata ba ehe kinyi fushi sai tazo biko har gida sannan zaki sauko" murmushi maman Amrat tai suna gaisawa da Indo domin yau wuni guda basa gidan sai yanxu suka dawo haka suke idan mazajen su basa nan saisu had'u a d'akin mutum d'aya suyita hira abinsu kamar yan uwan juna.

👑EMIRATE👑
______Zaune Khimiyyah take a d'aki ita kad'ai tana waya da Hudayyah tana fad'a Mata wasu abubuwan da akai bata nan sannan tana tambayarta Ina ta shige tsawon lokaci anan take fada mata wani bros d'inta ne ya mata dukan mutuwa domin ta shigar masa d'akin sirri ta goge sa'kon da Prof Jibril ya turawa Danual Chai kuma aka samu akasi bayanan da sunan 'kungiyar network ya hankad'osu cikin laptop d'in Asad baro baro ya gani ita kuma lokacin karfe hud'u na asuba idonta biyu da waya a hannunta ta fahimci komai kuma taga komai a tata wayar shine Mr Famous ya kirata yace Lallai tasan yadda zatai ta shiga ta goge komai idan ta bari asirin su ya tonu sakacin tane shine ta bari ya tafi masallaci ta shiga tana gama gogewa yazo ya ritsata yai mata mummunan duka.

Tana rufe baki Hudayyah ta she'ke da dariya tana cewa "kuturun ubancan amma wallahi yayi min daidai kai har naji ya burgeni tabd'ijan irinsu nake so jarumai masu tsantsan karfi kinsan wannan gayen dalilin da yasa na barshi kenan ban bari su Daddy sun kashe shiba sabida shima jarumi ne amma yana da taurin kan tsiya har yanxu maganar da nake miki ya'ki ya amince ya kar'bi soyayya ta".

Zaro ido Khimiyyan tai "ke wai da gaske kenan yaya zakiyi idan ya'ki kar'ba dan banga alamar zai kar'ba ba tunda har aka zo yanxu"?.

Ta'be baki Hudayyah tai "sai nasa a kasheshi duk da sonsa ya riga ya shige min 'bargo da jijiya gara na kashe shi maybe idan na bud'e ido na daina ganinsa zan ha'kura dashi".

Kai Khimiyyah ta girgiza "a'a Hudayyah kar kiyi haka da ki kashe shi alhalin kina sonsa gara a d'aura muku aure dashi tilas ko yana so ko baya so Ina ganin zaifi akan abinda zuciyarki ta baki shawara ko"?.

Kai Hudayyah ta d'aga "eh kuma fa haka wallahi Khimiyyah kin iya kawo shawara shiyasa wallahi nayi ba'kin cikin rashin ki lokaci mai tsawo abubuwa da yawa sun 'bace min kila da kina nan da yanzu na aureshi amma na gagara bakiga irin azabar da nasa ake d'an'dana masa ba amma a banza yanzu yaushe zaki zo mu had'u"?.

Kai Khimiyyah ta girgiza "babu rana Hudayyah domin kinsan yanzu ba irin da bane na riga nasa likita ya nuna cewa ciwona zai ri'ka tashi lokaci zuwa lokaci kinga baza'a barni na ri'ka fita ni kad'ai ba hatta school fa saida guard nake zuwa suna ankare dani ana tashi zan shigo mota mu dawo masarauta nikam nata banji dad'i ba amma zansan yadda zanyi yanxu idan kin koma gida ki had'ani da Daddyn ki".

"Ok Ina kusa dashi ma bari na bashi sai kuyi magana" mi'ka masa Hudayyah tai kar'ba yayi da murmushin banza a fuskarsa ya kara a kunne yana cewa "hello ours ya ake ciki miye labari kwana da yawa".

Kai Khimiyyah ta d'aga "eh Daddy na dawo bayan lokaci mai tsawo amma fa yanxu an samu matsala an zuba min tsaro sosai Daddy kuma abun tsafi yanxu

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login