Showing 165001 words to 168000 words out of 195514 words

Chapter 56 - ME KAMAR SARKI HAUSA NOVEL

YUSRAH   

22 Oct 2024

27292

wai zai auro yar qauye humm ta shiga d'imuwa ta shiga damuwa da kukanta ta samu Mom din Nurain amma ta bata ha'kuri tace itama Allah zai kawo mata.

Mimih itace suke uwa daya uba d'aya da Nurain akwai ta da iya wulakanci salo-salo 'yar rainin hankali ce ta bugawa a jarida Zainab ma da take 'yar cikin birni kuma wayayyiya sun goga da ita kafin su daidata balle wannan da zata zo daga qauye tunda taji zai kara aure ga daga inda za'a kawo amaryar tace a'a yaya ba aure zaiyi soko zaiyi kamarsa ya auri village girl heyeee inaa girma ya fad'i rakumi🐪 yasha ruwan kaji🐓 tun bataga amaryar ba ta d'au 'kwarzaba ta zuba mata kullum bata da aikin sai kushe auren balle Meenah da take jin kamar tayi hauka dan takaici Mimih kam har tacewa Dad tayi ya hana Nurain auren ya auri Meenah tunda ta dad'e tana sonshi Daddy shikam yace ba ruwansa ra'ayin sane Mimih har daina kula Nurain tai in yazo gidan sai ta ri'ka kakkare hanci har abun ya bashi haushi ya tambaye ta uban me take rufewa hanci tace masa wai warin karkara yake🙊😂.

🥕OSUN🥕
______Yau da wuri Dauda zai tafi gurin hayar mashin d'in sa kamar yadda ya saba akwai kayan abinci komai a aje sai kud'i mahad'i dazai bayar ya baiwa Indo dubu d'aya akan tayo cefanan kayan miya sannan ya tafi saida ya riga ya dad'e da tafiya wani tunani yazo mata tun shekaran jiya tace masa zataje kitso yace to kuma bataje ba dan haka tunda taga dai ta tambaye shi sai kawai tayi wanka ta shirya da nufin idan anyo mata kitson sai tayo cefanan a hanya dama maman Niseh ce take musu markad'e.

Lokacin data gama shiri ta fito tsaye tayi a kofar d'akin maman Amrat tana kiran sunanta jin shiru yasa tayi tunanin ko ta koma barcin safe ne sai bata tashe taba kawai ta tafi dama tunda ta tambayi Dauda yayi mata kwatance a anguwar ne kuma yana yawan fita da ita yawo ya nuna mata gurare ta sani saboda wata rana.

Tayi sa'a kuwa matar ta gama aikinta na safe tana zaune suna zance da 'yar budurwa wacce ke harhad'a kayan da take abubuwan saidawa na yara irinsu tsami gaye tuwon madara carbin malam alawar Kano da Jigawa dasu aya da sauran su sallama Indo tai musu suka amsa mata cikin fara'a tare da bata gurin zama suka gaisa matar ta kalleta tana cewa.

"Ehem madam ko kaine wanda kuka tare mana kwana baya da dad'ewa anan"?.

Kai Indo ta d'aga " eh nice".

"Ayya haayy na ganka ranar walay da husband naka kun biyo mana tanan kunje anguwa ko"?.

Nan ma kai Indo ta d'aga mata tana cewa "eh munje anguwa ne".

"Ok ok nagane kana wajen gidan madam maman Niseh mai markade ko meyene sunanka"?.

Ita Indo dariya ma abun yake bata qarfi da yaji ta koma namiji tana murmushi tace "suna na Aisha Indo".

"Ayya sunan sofi ni Aysha sunan kaka nace shine ya haife uwana amma ya rasu da dadewa ai mai suna aysha akwai kirki walay".

'yar dariya Indo tai jin da gaske dai tana ambaton mace da alamar wakilin sunan namiji kafin ta kalli budurwar dake had'a had'en kayayyaki tana sarrafawa tace.

"Dan Allah kina koyawa"?.

Kaita d'aga mata "Yeh ina koyawa komi anen akwai wasu abubuwan sana'a mata na hannu da yawa na iya ranar weekend ina koyawa dubu biyar ne shiga iden kana so kaima kazo na koya maka yanzu kudade zasu shigo hannunka ka zama babban ajiya (Hajiya)".

Kai Indo ta d'aga "eh Ina so idan na koma gida zan tambayi mijina zan zo ki koya min".

"Ok Indo saina ganka karka manta idan ya dawo ka fad'a masa fa wanna abun akwai amfani yana kudi".

To Indo tace tana mayar da hankalin ta kan matar tace "am dama kitso nazo ko kinayi"?.

Kaita d'aga "eh ina yin kiso mana".

Kallonta Indo tai tana cewa "ai na d'auka ko ba daidai nazo ba domin nan akai min kwatance ance idan nazo ganka poster board a waje da hotunan kitso ni daban gani ba har juya na d'auka ko nayi 6atan kaine tunda niba 'yar gari bace"?.

"A'a Indo bakai 'bata ba nan ne walay yara ne suke lalata mun abun da akwai kuma sai bansa wani ba tunda ansan inayin kison zuwa anjima da bakazo da wuri ba saidai ka kama layi da yawa kana ganin mata sunzo ayi musu kiso masu kyau na iya kiso bari na maka kuma ka gani" ta karasa maganar tana d'auko doguwar kujera da take zama akai harda sako riga ta musamman tazo ta zauna suna hira tana yalyala mata kitso har aka gama Indo ta saka hijab d'inta ta mata kitson kuwa ya d'auru tamau kamar da inji akai gata da sauri matar tuni harta gama mata duk da tana da yawan gashi dubun hannunta ta mi'ka mata tana cewa.

"Nawa kike kitson"?.

Kar6a tai tana cewa "ayya Indo ai kai amarya ne na amare nayi maka idan ango ya gani zai biyaka kudi meyawa na dubu da dari biyar nayi maka amma ka barshi dari biyar din tunda kai bako ne nan gaba da dubu da dari biyar zaka zo kaji😂".

TAB KACE YAU SU DAUDA BA SHAN JAR MIYA🍅🌶️ INDO TAYI KITSO DA KUD'IN🤣.

Sak Indo tai tana binta da kallo tace "wai kitson ne akai min na duba d'aya da d'ari biyar ko kud'in koyan abinda nace zanzo ne"?.

Kai ta girgiza mata "a'a kudin kison kane kudin koyan wannan shi dubu biyar ne ka gane kison ma a hakan rage maka nayi na dubu daya da dari biyar nayi maka fa sofi (tsofi☺️)"?.

Jin haka yasa Indo bata sake cewa komai akan kitson ba tayi mata godiya zata fita matar tace "kada ka manta nan da sati daya ka taje gashinka ka wanke ina nan Ina kiso sannan idan zaka zo kazo ka da dubu daya da dari biyar kaji" murmushi ya'ke Indo tai tana cewa.

"To nagode sai na dawo" tana fad'in haka ta fita a hanya tana tafe tana zulumi me zata cewa Dauda tsautsayi yasa tazo kitso an kar'be dubu, dubu fa ziyau tabd'ijan bata ta'ba jiba sai anan ta saba acan gida ta zauna ayi mata a naira d'ari ko d'ari da hamsin amma nan umm bari taje daga gida taga ya zatai kafin ya dawo.

Tana shiga sakamakon rana ta farayi taga maman Amrat zaune a wajen kofar d'akinta ta hura wutar gawayi sallama tai tana kallon maman Amrat din lokaci guda kuma ta she'ke da dariya tana cewa.

"Nashiga uku maman Amrat wai dama haka ake kitso da tsada a garin nan ban saniba naje gurin wata bayerabiya na tura mata kai saida ta gama min na bata dubu tabani canji sai cewa tai wai a hakanma na dubu da d'ari biyar tayi min amma nabar d'ari biyar d'in gashi kud'in da zanyi miyane nikam yau bansan me zancewa yaya Dauda a gidan nan ba"?.

Dariya itama maman Amrat din tayi tana kallon Indo tace tabd'ijan dama wannan matar haka take tsadar kitso ne da ita ai bansan xakije da na rakaki gurin wacce take min bai wuce d'ari biyar ko d'ari bakwai a wajenta wallahi hu'um nima fa haka wannan matar tai min farkon zuwanmu garin nan naje gurin ta tayi min kitson nan Ina baki labari aike tayi miki da qauna iya kud'in kayan miya ta kar'be hum toni gabadaya kud'in abincin daya bani zanyi ta kar'be gashi a lokacin ko karyawa banyi ba kuma ya riga ya tafi gurin aiki sai dare yake dawowa bansan kowa a gari ba haka na dawo gida nayi lamo babu kobo ba sisi ranar naci ubana na yabawa aya za'kin ta wallahi haka na wuni Ina kuka tsabar yunwa daya dawo na fad'a masa maimakon yaji tausayi na yatafi da sauri ya nemo min abinci naci haka ya zauna ya sani gaba ya ri'ka min dariya saida yaga ina kuka da gaske iya qarfina kafin ya tashi ya fita ya sayo min wani abu naci sannan fa na dawo hayyacina yace min tayi magani na mai kitson gobe ma dan Allah na koma gunta ta sake kwace kud'in nidai shiru nayi ina zare ido ya kazar da taga wuka tunda nasan bani da gaskiya kema idan ya dawo kila haka zakuyi amma kinga yanzu abinda zai faru tunda ni miya zanyi kiyi abinci saina baki miyar wacce idan ya dawo zaice kada ki fad'a masa ki bari saiya ci sai kice gashi ga abinda ya faru kawai" maman Amrat ta karasa maganar tana kallon Indo wacce tai shiru yanzu can ta d'ago suna had'a ido sai kawai suka sake suka kwashewa da dariya Indo harda buga kafa tace.

"Tabd'i yau da drama a gidan nan humm yaya Dauda to shikenan dai nagode maman Amrat bari nima na fito da kaya naxo na d'ora" ta fad'a tana nufar d'aki har lokacin ita kad'ai sai dariya take haka nan taji bazata koma koyon abun da tace zataje bama Dan kar ta tambaye ta miyasa ta daina zuwa kitso gurin ta gara ta tambayi maman Amrat idan tasan wata wacce ta iya taje a koya mata amma gidan wannan bayerabiyar mai kitson saidai kallo ita dashi😁.

MRS AL'AMEEN AHMAD CE😘.
Yusrah Musa Abubakar🌹💓💯.

We will meet again🤗.

🤟🤟🤟🤟🏼🤟🤟🏿🤟🏻.

TYPING📲Sd Aug31™/24 02:10PM
YUSRAH MUSA ABUBAKAR💋.

🙅🏿‍♂️Nifa I no girman kai 🙆🏻‍♀️ if you are fushi😡 dani to wallhi you are just'batawa kan k lokaci🕝.

Yusrah---musa---bintu---Abubakar---Muhammad ta kowa ce yar Aliyu.

FATIMA MUSA ABUBAKAR
ABUBAKAR MUSA ABUBAKAR
NAJA'AT MUSA ABUBAKAR
AISHAT MUSA ABUBAKAR🤝.
💃🏻ALL
🤸🏻‍♀️4ME.

65~AL-MAJIDU
The Illustrious
66~AL-WAHIDU
The Unique

32~Allahumma salli wa sallim ala sayyidina muhammadin Sahibul mu'kami mahmudi.

🌄WED ND DISCONTENT 🌄
Episode 67&68
🏕️KAUYE🏕️
_____________Bikin Nafisa yazo amma banda Salma sakamakon Adamu ya roki alfarmar a kara masa lokaci bai karasa wasu abubuwan ba kuma yanzu ba kud'i a hannunsa dan ana haka iyana Nafisan za'ai sai dariya takewa Salma da isgilin zatai aure a gidan wuya wanda hatta kud'in sadaki ma yace baida shi balle azo kan akwati hum'um Salma bazata more dad'in duniya ba saidai ta ri'ka aiko mata da busasshen abinci idan ta tara🤪.

Haka takanas Ilyah da kansa yaje ya sayo kaya na alfarma da fariya daga kan suturar da zasu sa a bikin zuwa kayan abincin da za'a ci wani ma basusan taya ake sarrafashi ba haka ya jido da yawa ganin arahar kud'i balle da akazo kan kayan d'aki musamman Nafisa da za'a kaita birni saidai Nurain yayo mata waya yace kada taje da ko cokali an zuba mata komai data fad'awa Bara'atu dariya har kunne tana hankata baki Nafisa tayi dace kayan d'aki ma miji ne ya zuba mata gaskiya Nafisa zata ca'ba a gidan Nurain😀. Uhmmm inji me ciwon baki.

A ranar d'aurin aure Hassan da Hussain suka diro 'kauyen sun sayo sabuwar mota dal a ledarta sai walwali take ko'ina suka gifta sai kallon motar ake ana tunanin waye Dan wasu a zatonsu ma waiko malam Habu ne ya dawo har ya zama mai arziki saida akaga wadanda suka fito daga cikin motar sunsha ba'kin glass suna muzurai suka zagaya suna bud'e murfin motar baya a'a tofa abun ya motsa yana dukan rai inji mai wa'ka tab su Bara'atu sai a shirya tarbar ba'kin da ba'a san da zuwansu ba domin su Hassan sunyo tsintuwa kowa da budurwarsa yazo😳.

Dan su Hassan suna tare da yan matansu suma da gani yan biyu ne kansu d'aya kuma kamarsu d'aya daga can suka zo dasu fulanin Yaounde ne a yankin Cameroon kowacce ta she'ka kwalliya andau wankan ala tsine uwar me 'karya gaba Hassan suka wuce su kuma suka bisu a baya umm kowa baki ya sayi sai kallonsu ake su kuma suna bubbud'a kafad'u suna hura hanci sun da kyakkyawan ladies zasu yiwa 'yan qauye burga.

Bara'atu tana cikin taro sai kaiwa da ansha adon lace da sar'ka sai juyi take akai mata albishir gasu Hassan can sunxo saida gabanta ya fad'i tun kafin ta gansu balle da taga harda ba'ki wani yawu ta had'iye tana kallon su da ya'ke a fuskarta tace.

"Sannunku da zuwa ashe kuna hanya harda ba'ki ku karasa d'aki ina zuwa".

Ta fad'a tana komawa wajen da ake hidima d'akinta da mutane sosai d'akin umma Maimuh ma haka sai kawai suka bud'e nasu d'akin suka shigar dasu dama already tun daga can sunyo tanadin kayan cinye cinyen su basu bukaci komai ba Hussaini ya dauko musu shi a but din mota suka baje suna shagali basu gaisa da kowa kuma basu damu ba.

Shigowar Bara'atu da babban tray fal da abinci sak ta tsaya gu daya tana kallon su itakam batasan lokacin da wadannan 'ya'ya nata zasuyi hankali ba jiki a sanyaye ta karaso tana aje musu da murmushin dole tace.

"Saura ruwa bari a kawo muku yanxu".

Tana rufe baki Hassan dake d'ayar cinyar kaza yace ''haba umma wanne irin ruwa amma ba na rijiya ko rafi kike magana ba saidai a nemo musu pure water".

Kai Bara'atu ta d'aga da sauri gudun kada su bada ita a gaban ba'ki tana cewa "to Bari nemo muku yanzun nan" tana kaiwa nan tayi waje da sauri harda tuntu'be Ilyah kadai take so ya shigo ta sanar masa zuwansu shima yayi taka tsantsan a samu a rabu lafiya tunda yanzu su sun zama qarfen qafa masu wuyar cirewa.

Bayan sun gama haka suka fantama dasu yawo layi layi har gidan malam Habu ganin gidan babu alamarsa sai fili ga tulun qasa a gurin yasa tun a hanya kafin suzo gida suka tambaya ina ya koma akace musu bayan tafiyarsu ga abinda ya faru sannan Ilyah ne ya saye gidan kuma Malam Habu a yanxu babu wanda yasan a duniyar da yake sai Allah sun sha mamakin Ilyah duk da yana mahaifin su da suka dawo gida kuwa tsiya iri iri suka sauke masa harda ya jira wutarsa tana nan tun daga yanzu an hura masa ita tana ci jira kawai take ya mutu tabalbaleshi dad'in abun ma a kofar gida sukai masa ba a gaban yan matan nasu ba su suna cikin gidan gurin dangin Bara'atu.

Da dare yayi ganin yadda mutane akai shimfid'a a waje kowa ya kwanta dayake lokacin zafi ne yasa Hassan kiran Bara'atu gefe yana cewa.

"Wai umma a ina 'yan matan mu zasu kwanta ne dare fa yayi barci sukeji"?.

Kallon sa Bara'atu tai tana cewa "a ina kuwa zasu kwanta baga shimfid'a nan anyi ba zata wadaci kowa".

Zaro ido Hussaini yai "kai akan tabarma kuma tabdijan gaskiya bazasu kwana a kasa ba".

Baki bud'e Bara'atu tace "au a sama zasu kwana kenan"?.

"A'a ba'a sama zasu kwana ba amma dai katifa zaki basu ko taki ko ta baba".

Kai Bara'atu ta jinjina tana cewa "lallai yaran nan baku da hankali nice zan baku katifa ta tana kan gadona na fito da ita wasu 'kattin su kwanta cab hummm".

Kallonta Hassan yai yana cewa "to meye ba surukanki bane basu isa kiyi musu haka ba ba'kin naku ne fa bikin 'yarku suka xo".

Kafin Bara'atu tayi magana Hussaini yace "abin haushin ma wai harda wasu 'kattin? Kai Hussainan tawa ce 'katti"?.

Wata uwar harara Bara'atu ta sakar masa tana cewa "au bazan fad'a ba sannu ubana saika rufeni da duka saboda nacewa wasu 'katti sai naga budurwa tafi uwa ko irinku ko"?.

Kau dakai Hassan yai "nidai Umma duk ba wannan ba kisan yadda zakiyi ki nemo musu katifa suna mota fa suna jiranmu Hassana har gyangyad'i take tsakani".

Tsaki Bara'atu tana cewa "wallahi indai bazasu zo ku kwanta a inda kowa ya kwanta ba saidai su kwana a motar wai me kuke haka ga guri nan malala da yawa amma dan masifa danku d'aga min hankali kunzo kun dameni haba da Allah gafacan kuban guri" ta karasa maganar tana wucewa ta koma cikin baranta ta nemi guri kusa da yan uwanta dake ta aikin yanka alayyahu dasu albasa za'ai sabuwar miya gobe ma gagarumin biki za'ai sannan da kusan magriba amarya tad'au hanyar birni kamar yadda take fata.

"Kan bala'i Hassan kaga wata shariya a gurin Umma wai da gaske take a cikin wadannan mutanen zasu zo su kwanta haka kawai su zuba musu 'kwar'kwata a kyakkyawan gashinsu🤣.

Tsaki Hassan yai yana cewa "wallahi bazasu kwana a kasa ba muje d'aki shegiyar amaryar ba bikinta suka zoba ta d'aga tata katifar ta basu ko naci ubanta" yana rufe baki sukai d'akin Nafisa a kwance suka sameta har tayi barci wani duka Hassan ya sauke mata wanda a firgice ta tashi cikin gigin barci ganin basawa tsaye a kanta yasa tace.

"Meya faru"?.

Harararta Hussaini yai yana cewa "ubanki ne d'aga mana katifa yan matan mu zasu kwanta".

Jin abinda yace yasa Nafisa tace "kai dan Allah Hussaini daga yau nima fa shikenan nayi bankwana da katifar kuma a kasa zan kwana"?.

Dundu Hassan yai mata yana cewa "a bola zaki kwana dan uwarki ba kasa ba har ana magana kina mayarwa mutane wato ke ga amarya ko rainin amarci ya shigeki wallahi so kike yanzu nan na karya miki qafa sai naga gaggawar zuwa gidan mijin shegiya 'kwartuwa🙈 zakici ubanki da qafafunki zaki nemi hanyar qauyenku ki gudu idan kikaji maza🙉.

SUBAHANALLAHI WADANNE IRIN YAYU NE WANNAN😂.

Tsayawa Nafisa tai tana kallon sa cikin tsawa yace "zaki d'aga ko saina hautsinar dake".

Ba arziki da gudu Nafisa ta d'aga tana ficewa d'aga d'akin tsaki Hussaini yai yana cewa "idan ba jaraba bama wannan yarinyar ina ta isa aure kaga fa yan matan mu dame muka fisu amma a hakan iyayensu sunce mana yara ne mud'an kara jira hummm zata ci ubanta ne kama muje" d'aukar katifar sukai waje.

Da gudu Nafisa ta karasa gurin Bara'atu tana kuka tace "Umma Kinga su Hassan sunje ina barci na suka daddake ni sannan suka qwace min katifa ta wai yan matansu ne zasu kwanta".

Dafe kai Bara'atu tai tana kallon ta tace "Kinga Nafisa daina kuka iya yau ne zaluntar taki gobe iyanzu koda kud'i bazasu ganki ba balle su zalunce kin saidai su zalunci kansu tashi kije d'akina ki kwanta" mi'kewa Nafisa tai tana shiga d'aki.

Bara'atu kuma ta tashi tana zuwa kofar d'akin su Hassan harsun shimfid'a katifar sun sa bargo su d'ame sun d'auko fulo guda biyu sun jera suna kafa 'kusa zasu daura musu net tabi Bara'atu ta ri'ke tana

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login