Showing 21001 words to 24000 words out of 56867 words
jikallena, Halimatus Sadiya, yo dole a miki sannu irin wannan ruwan hawaye, ke baki da aiki sai kuka daga kin ga Hassan ya zama miciji ko kuma ana ta tseran gudun famfalaƙi memakon ke ma ki rattaba naki gudun sai ki zauna kina kuka, ai har idanunki sa ke miki ciwo" Ta faɗa idanunta a kan Sadiya da bata ce komai ba.
"To ai shikenan, tun da ba za ki yi magana ba na lura kin gama ɗauke halayen wancan kurman mijin naki Imirana, duk da dai na kula zuwana gidan nan ya sa ya yi baki amma dai da sauran rina a kaba, bari in tashi in je in sake alwala, yo ɗazu ina alwalar na zo wankin fuska na ga yaran nan sun fito a guje, da faɗa zan fara musu amma ganin Hassan ya fito ya sa ni ma na ce ƙafa me na ci ban baki ba, wallahi haka nan na bar yin alwalar na gudu na samu mafaka a firinji amma yarinyar nan me ƙunshi wacce na yiwa yaɓe da lalle ta garƙameni a firinjin ta kunna shi a haka na daskare kamar ƙanƙara" Ta faɗa kamar ta saki kuka da ta tuno da wahalar da ta sha lokacin da ta tsinci kanta a freezer.
Ganin dai Sadiyar bata sake cewa komai ba sai binta da ido take ya sa ta ce.
"Ni fa wallahi Sa'adiyya da a ce ba ni na haifi ubanki ba da babu dalilin da zai sa in kasa yarda ke mayya bace, ko da kuwa baki ci mutum ba, yo ina dalili ki yi ta kallon mutane ba ƙaƙƙautawa ina ga ma ko ƙiftawa bakya yi" Ta ce tana hararar Sadiya da ta ɗauke kanta daga kallon Innar jin abin da ta ce.
"Oh to bari na tashi da wannan in je in yi abin da zai fishsheni, ana zaune ana darun gudu ba azahar ba la'asar" Ta faɗa tana tashi ta fita waje dan yin alwala. Tana zuwa wurin alwala ta ƙyalƙyale da dariya ganin butar da ta bi ta kanta lokacin da za ta gudu da ta ga Hassan ya fito daga ɗaki.
"Allahu akbar kabiran, Allah sarki ni Azumi na haɗu da gararin rayuwa, kalli yadda na yi ƙwallo da butar nan a gudun ceton rai, garin gudu kaɗan zani na ya faɗi in je in yi tsirara a gaban jama'a a shiga uku, dan ma dai lokacin kowa ta kai ta kai yake kamar a filin ƙiyama, ba lallai su gani ba" Ta faɗa tana ɗaukan murfin butar tare da butar ta zuba wani ruwan ta sake shiga bayi ta fito ta zauna tana yin alwalar.
Imran tun da ya shiga ɗaki yake jin wani ƙululun baƙinciki ya tokare masa ya ƙi gaba ya ƙi baya, takaicin abubuwan da Inna take masa kaɗai ya ishe sa musamman yau da ta balbala masa wuta har da sanya buhu kamar ta samu ganda ko naman kai. Baki ya cije a ransa yana raya sai ya rama abin da ta masa in bata gaji ba shi ma ba zai fasa ba an ringa yi kenan, sai dai ramuwar gayya ta fi ta gayya zafi.Tasowa ya yi domin ya fito ya je ya yi alwala dan bai yi sallar ka'asar ba, dama daga masallacin azahar ya shigo gidan ya tarar da abin da ke faruwa.
Yana zuwa falo ya kalli Sadiya cikin jin tausayinta ya ƙarasa kusa da ita ya kama hannunta cikin taushin murya ya ce.
"Ki yi haƙuri Sadiya komai ya yi farko yana da ƙarshe, duk abubuwan nan da kike gani jarabawa ce akwai ranar da za ta wuce komai ya zama tarihi kamar ba a yi ba" Ya faɗa yana rausayar da kai idanunsa cikin nata.
Hannunta da ya riƙe ta sanya ɗayan hannun da bai riƙe ba ta ɗora a kan hannun nasa da ke riƴe da hannunta, ta ɗan damƙe hannun tana kallon cikin ƙwayar idanunsa, tana jin yadda soyayyarsa ke huda kowane kungu da saƙo na zuciyarta a gefe ɗaya kuma wani tausayinsa ne ya mata dirar mikiyar da har sai da idanunta suka kawo ƙwalla, Allah sarki so, so hana ganin laifi in ji masoya.
"Babu komai masoyina na san komai dama muƙaddari ne amma kai ma ka daina sanya damuwar hakan a ranka kamar yadda ka umarce ni na daina, sheɗan ne ke maka jagora har yake neman nisanta ka da iyalinka"
"Allah sarki Sadiya nagode ƙwarai kuma ina ƙara yiwa Allah godiya ya azurtani da mace ta gari wacce ta san damuwata da kuma farincikina wacce ta san samu na da kuma rashina in sha Allah zan kiyaye tare da ƙoƙarin yaƙi da shaiɗan waje ganin bai cimma burinsa a kaina ba ya samu nasara" Ya faɗa yana sanya hannu ya shafo gefen fuskarta suka sakarwa juna murmushi a lokaci guda kowa ya ji zuciyarsa fes damuwarsa ta wanke, domin kowacce zuciya tana son lallashi da kuma samun jin ƙai daga abokin tarayyarta.
"Ni ma nagode kuma ina alfahri da samunka matsayin mijina kuma uban ƴaƴana" Ta faɗa ita ma tana ɗauke hannun da ta ɗora a kan hannunsa ta shafo fuskarsa kamar yadda ya mata.
"I luv u" Ya faɗa yana mata wani kallo da ita kaɗai ta san ma'anarsa.
"I luv u too" Ta faɗa ita ma tana sakar masa murmushi mai ratsa zuciya.
Haka ya tashi domin zuwa ya yi alwala har ya kai ƙofa ya dawo ya buɗe frige ɗin falon ayaba ya ɗakko guda ɗaya. Ɓarewa ya yi ya cinye Sadiya dai tana kallonsa sai da ya cinye ya fira riƙe da ɓawon a hannunsa yana zuwa kan barandar ƙofar falon ya faki idon Inna ya jefar da ɓawon. Zuwa ya yi zai shige bayin ta kallesa tana ɓoye dariyarta ta ce.
"Imirana na cikin tukunyar wankan jego, an sha zafin wuta" Banza ya mata ya shige bayi, har ta kammla alwalarta ta bar wajen, tana tafiya tana kallon tsakar gidan abubuwan da suka faru yau a tsakar gidan na faɗo mata tana ɗan murmushi, aikuwa tana cire takalmanta ta taka barandar ta sauke ƙafarta a kan ɓawon ayabar da Imran ya jefar, gabaɗaya ta tafi luuuu tana rafka uban salati ƙafar ɗaya ta yi gabas ɗayar ta yi yamma ji kake timmm ta rafku da ƙasa, Imran da ke laɓe yana leƙe ta bayi ta koma cikin yana shan dariya abinsa. Sadiya da gudu ta fito domin ganin me ke faruwa.
"Taimaka min Halima wallahi kamar wanda na yi hatsarin mota, motar ta yi sama da ni haka na ji"
Cikin tausayawa Sadiya ta shiga ƙoƙarin ɗaga Inna, hammatarta ta kama tana ƙoƙarin ɗaga ta.
"Sannu Inna da na ga ba da hammatar kika faɗi ba shi yasa ma na kama nan ɗin sa...
"Haba Sa'adiyya yo a yi zancen ma ba da hammata na faɗi ba, to billahil lazi ko ina na jikina ciwo yake, bakya ganin jikin tsufa ne dama kamar jira jikin yake in faɗi ko ina na jikina sai da ya amsa hatta gashin kaina ban ɗauke ba, har tsakar kaina amsawa yake" Inna ta katse Sadiya daga maganar da take son faɗa.
"Yanzu ina zan kama?"
"Kama ƙuguna daga gefen dama ki ɗaga ni"
"Haba Inna ta ya zan iya ɗaga ki kuma ta ƙugu, ni fa dama taimaka miki zan yi ki tashi amma ai kinsan dai ba zan iya ɗaga ki ba"
"Wato ga buhun gero, ai da uwaki Rakiya ce da tuni kin sunkuce ta kamar kin ɗauki auduga, amma da yake ni ce cewa kike nauyi gareni" Ta faɗa tana sakin kuka.
Imran da ke laɓe daga bayi yana leƙensu sai dariya yake ƙasa-ƙasa ko banza ya rama abin da ta masa.
Haka Sadiya ta yi dibara ta taimaka mata ta shiga da ita falon tana ta sababin wane shegen ne ya jefar da ɓawon ayaba a kan hanya. Sai da Sadiya ta zaunar da ita a kan kujera sannan ta ce.
"Inna ba fa cikin sani aka jefar da ɓawon nan ba, Abban twins ne fa yanzu ya ci ayaba shi ne da zai fita yin alwala ya fita da shi a hannunsa to ina jin bai san ya jefar ba ma, kin san shi dai da tsafta babu abin da zai sa ya jefar da abu a ƙofar falo dan...
"Ni kwa na san shi da tsafta, kuma na san shi da mugunta" Ta faɗa a zuciyarta a fili kuma ta ce.
"Guda nawa ya ci ayabar?" Inna da tun da Sadiya ta fara magana take kallonta da baki sake tana son gano wani abu ta jefa mata tambayar.
"Kamar ya guda nawa ya ci kuma Inna sai ka ce ayabar ajiya ko ta haram sai an tamabayi mutum nawa ya ci"
"Ke ba na son iskancin wofi ki bani amsar tambayata"
"Guda ɗaya ce fa ya ɗakko ya ci"
"Ɗaya tak?"
"Eh"
"Tabbas Imirana da gangan ya jefar da ɓawon nan dan in taka in faɗi amma kuma da Azumi yake magana indai ni ce mu zuba ɗan halak ka fasa"Cewar Inna a zuciyarta a fili kuma sai ta ce.
"Allah sarki Imirana kam akwai tsabta, bai san ya jefar ba" Ta faɗa tana sanya hannu ta dafe bayanta tare da yatsina fuska ta ce.
"Bayan nan nawa yadda kika san an yi yaƙi a kansa haka nake ji yana sara min wallahi ko ina ma ciwo yake"
"Bari in ɗakko miki aboniki ki shafa" Cewar Sadiya ta shige bedroom sai gata ta dawo riƙe da abonikin. Haka ta shiga shafawa Inna a ƙafafunta hatta kafaɗunta da wuyanta sai da aka lafta abonikin, tana ta rakin ciwo-ciwo.
"Bani in shafa a kwankwasona da haƙarƙarina" Ta faɗa tana karɓa ta shiga shafawa tana yatsina fuska.
"Sannu Inna"
"Yawwa Halima, ni wallahi wannan ba mini zai yi ba, ku nan ba a siyar da wasai?"
"Inna meye wasai kuma?"
"Ke dalla rufe min baki, yanzu wasan ne baki sani ba, mu a can akwai wani me siyar da maganin hausa, me suna wasai, za ki ji yana talla yana cewa, sai na ji wasai in baka wasai, to da wannan maganin na samu da tuni na ji wasai"
"Gaskiya ni ban ma taɓa jin sunan ba"
Shiru Inna ta yi ita kaɗai ta san me take ji a jikinta.
"Inna ki yi sallar mana"
"Haba Sa'adiyya ke ma tun da kika ga bam tashi ba ai kin san akwai magana ya za a yi ma in ƙi yin sallah da gangan bayan dama na san salloli biyu ne , a kaina ai sai dai Allah gafarta mana" Ta faɗa tana yin dibara ta sakko ƙasa ta dafe hannunta a ƙasa tana durƙushe. Imran kuwa dama tun da ya yi alwala ya fice daga gidan ya tafi masallaci duk da ba jam'i zai samu ba tun da an daɗe da idar da sallar, ransa fari ƙal ya rama abin da Inna ta masa.
"Tsohuwa sai dai ki yi haƙuri kin haɗu da mijin jika ɗan zamani, dan dai dama ke ma ba a barki a baya ba" Ya faɗa yana tafiya ya ƙyalƙyale da dariya.
"Inna ya kika durƙusa kuma?" Sadiya ta tambaya da mamaki.
"Bari ke dai Sa'adiyya kwankwason nan nawa ne nake ji kamar ba a jikina yake ba, wallahi yadda kika san mace tana naƙuda take jin mararta kamar ba tata ba, tsantsarta kamar za ta ɓalle to haka nake ji"
"Me naƙuda kuma Inna?"
"Yo me naƙuda mana, ai wai na miki misali ne da yadda za ki gane, tun da baki daɗe da haihuwa ba na san baki manta yanayin da kika ji ba"
"Allah sarki sannu Inna zai daina in sha Allahu"
"Kayya Sa'adiyya baki ga na tashi daga zaune ba yo mazaunan nawa ne nake jin suna wani mamar-mamar sun ƙi zaunuwa dai dai ko za ki samu abu ki bubbuga mini su ɗan lafa in yi sallar ko da a zaune ne" Ta faɗa cikin murya kamar ta yi kuka.
" Buga mazaune kuma Inna?"
"Ke in ba za ki buga mini ba ƙyale ni, sai ka ce wani abu yo Allah ma tuba ma in ba larura ba mai zai sa in ce ki bubbuga min mazaunai,ai tun da na haifa miki ubanki na gama miki komai" Ta faɗa tana sababi. Ita dai Sadiya bata ce komai ba kuma bata buga mata ba, haka ta gaji da durƙuson da ya lafa mata ta yi sallar a zaune, tana idar wa ganin ta ji dama-dama kuma ta gama shirya abin da za ta yiwa Imran dan gabaɗaya ta gama gano da gangan ya jefar da ɓawon, dan ko bayan da ya dawo daga masallacin da Sadiya ke faɗa masa Innar ta faɗi lokacin yana bayi, dakyar ya iya danne dariyarsa kuma ya mata sannu kuma bai san cewa duk abin da yake Innar tana ankare da shi ba. Yana shigewa ɗaki ta ce.
"Halima tun da na ji dama-dama bari in je in kwalfe ruwan can da muka sha tsunduma ni da mijinki a ciki, in ɗauraye tukunyar in ɗora miki na wankan yamma wuri ma ya ƙure ki yi wankan a wanki Hussaini shi kuma wancan lokacin da ya sawaya ya dawo mutum sai a wankeshi dan wallahi ban iya wankan miciji da hannun nan nawa"
"To Inna"
"Kai ai yau dai an sha bidiri a gidan nan, yo wuta na babbakawa Imirana, ai yana jin ba kanta sai gashi ya fito a guje har yana gwara kansa a murfin tukunyar, ashe dara za ta ci gida, ni ma miciji an biyo ni sai gani ina iyo a cikin ruwan zafi" Ta faɗa tana dariya.
"Allah kyauta" Cewar Sadiya tana danne dariyarta.
"Amin dai wallahi ai na ji zafin ruwan nan, na ɗauka ma wutar za ta tashi, sai Allah ya dube ni bata tashi ba"
"Inna ki bar ɗora ruwan tun da bakya jin daɗi"
"A'a wallahi sai an ɗora so kike jikin ki ya yi tsami kike ciwon jiki, ai wankan jego shi ne zai sa kike jin daɗin jikin ki.
09030283375
[24/03, 5:14 AM] Mom Mashkur First class: *MAMAN AFRAH DATA SERVICES*
*BUY DATA FROM THE AFFORDABLE PRICE*
*I selling MTN data with this cheap price*
*MTN DATA PACKAGE*
500MB@===150
1GB@=====250
2GB@=====500
3GB@====850
5GB@====1,400
Dial *312*4*7*4# to check Data balance.
*Validity 1 month*
*Airtel,9mobile and Glo* *also available.*
*Subscription for DStv gotv star time electric pay bills*
Act details FA'IZA ABUBAKAR unity bank 0020281885
Whatsapp OR
Call 09033283375
Wannan littafin kuɗi ne 300
Za a tura ta wannan accaunt ɗin Fa'iza Abubakar 0020281885 Unity bank shaidar biya ta wannan no 09030283375 idan katin waya ne mtn Ƴan Niger su tuntuɓi wannan no +22785885134
3️
*E* ➡️ *F*
~DARE~
Bayan kowa ya kwanta a makwancinsa kamar kullum, Hassan dai a haka yake bai dawo mutum ba dan haka, kwantar da shi kawai aka yi a gadonsa. Inna da ke ta jiran dare ya tsala ta aikata abin da ta shirya, dan haka bakam ta yi babu wani bacci da take. Bayan ta ga dare ya tsala ta tashi zaune ganin Sadiya tana ta bacci abinta ta taɓe baki ta ce.
"Oh ni Azumi yarinyar nan shegen nauyin bacci gareta kullum bacci kamar wata kasa, ni dai ba ni kika biyo ba, dan ni ina cikin mutane wanda basu da nauyin bacci" Ta faɗa a zuciyarta tana sako ƙafafunta ta sakko daga gadon, a hankali ta nufi falon tana zuwa ta kunna fitilar falon ganin Imran lulluɓe a cikin bargo yana ta zabgar bacci ta taɓe baki tare da jijjiga kai ta yi dariyar ƙeta a ranta ta ce.
"Imirana ba dai ni ka jefarwa ɓawon ayaba ya niƙa ni da ƙasa ba dan mugunta, to zan nuna maka kowa ya ci tuwo d Azumi miya ya sha, in dai Azumi ce an buga an ba mu. KoTasalla ta yi iya yinta ta gaji ta bari, a hankali ta shiga janye bargon da Imran ya rufa da shi sai da ta cire gabaɗaya ta ga har lokacin baccinsa yake bai ma san abin da take yi ba. Ƙwafa ta yi a ranta ta wuce bedroom cikin sanɗa saboda tsabar ƙarfin hali Hassan ta kinkimo a siffar miciji, falon ta dawo, Imran ta kalla da ke sanye da singlet sai dogon wando na bacci, cikin sanɗa ta nufi wurin Imran, ajiye micijin ta yi duk da faɗuwar da gabanta yake amma saboda ƙarfin hali ɓarawo da sallama ta daure tare da danne tsoron da take ji, dan ta yi alƙawarin sai ta aikata abin da ta shirya. Singlet ɗin ta ɗan ɗaga daga ƙasa sai da ta tabbatar ta buɗu ta ɗakko Hassan da ta ajiye a gefe guda ta sanya shi daga ƙasan singlet ɗin Hassan da ke ta bacci ya ɗan motsa sakamakon ɗan jijjigashi da Inna ta yi, tana saka shi cikin singlet ɗin sai ya fara tafiya a hankali sai da ya sanyo kansa ta wuyan singlet ɗin Imran, sai ya kwanta a jikin Imran ɗin.
Inna kuwa ganin komai ya mata yadda take so sai ta yi dariya a ranta ta ce.
"Mu zuba mu gani"
Imran da ke bacci jin sanyi na shigarsa sai ya ɗan motsa kaɗan, ya ɗan takure jikinsa, jin abu manne a ƙirjinsa cikin giyar bacci sai ya miƙa hannayensa ya ƙara rungume abun tare da sakin ajiyar zuciya kallonsa Inna ta yi a ranta ta ce.
"Kudurarre me shegiyar jarabar tsiya duk tunaninsa Sa'adiyya ce ya runguma, da ni kake zancen" Ta faɗa tana ɗaukan bargonsa ta rufesu shi da micijin, a hankali ta kashe fitilar ta lallaɓa ta koma makwancinta.
*IMRAN*
Baccinsa yake cikin kwanciyar hankali, dan da ya ji ɗumi ma lokacin da Inna ta maida masa bargon ta rufa masa sai ya ƙara ƙanƙame micijin ya cigaba da yin baccinsa abinsa. Da yake wajen sha biyu da wani abu ne Inna ta yi masa wannan aiki, wajen ƙarfe haɗu da wani abu na asuba sai ya ɗan yi juyi kaɗan ya miƙa hannu idanunsa a rufe ya ja bargo ya rufe ƙafarsa da ta