Showing 3001 words to 6000 words out of 56867 words

Chapter 2 - YAR ZAMAN WANKA BOOK 3

27 Sep 2024

3829

ma iyakarsa ya motsa jela ko kansa amma yau ya fito da kansa har tsakar gida, da alama farautar rai ya fito, aikuwa Inna ƙafa me na ci ban baki ba sai ta nufi hanyar kicin ko sauraren Sadiya da ke ta faman mata maganar ta kalli Hassan ya koma miciji ya fito bata yi ba ta faɗa cikin kicin har tana gware da bango sosai goshin ya bugu amma babu damar murzawa haka fa daure tana neman mafaka.


Tana shiga kicin ɗin ta hango ƙafar wata ta leƙo daga cikin lokar kicin ɗin da nan take niyyar shigewa, amma ganin kusan mutum biyar a ciki sun cunkusu wata ma a kan wata take sai Inna ta fara rarraba ido.

"Wannan tashin hankali da me ya yi kama ni Azumi, a ce kai kullum baka da kataɓus baka da kwanciyar hankali" Ta faɗa a ranta hankali tashe, hango yarinyar nan me ƙunshi Inna ta yi a bayan ƙofar kicin ɗin daga ciki sai raba ido take tana ƙifƙiftawa wata harara Inna ta doka mata tana juyawa ta fara waigen mafaka, ganin danƙareriyar freezer wacce suke ajiye kayayyaki, karamin frige ɗin kuma shi ne a falo da hanzari Inna ta buɗe freezer aikuwa ta yi sa'a babu komai a ciki ba ma a kunne take ba.

"Yawwa Allah ya bani mafakar ɓuya, haka kawai Halima ta haifa mana jaraba shi kuma wancan mijin nata me kai tun na haihuwa ya hana a kai yaron bakin ruwa su ɗau kayansu ya bar mana shi kullum mu hankali rabe a biyu" Cewar Inna tana kiciniyar shiga freezer, sai da ta shige ta miƙo hannu za ta rufe murfin sai ganin yarinyar nan me ƙunshi ta yi tana ƙoƙarin shiga ita ma da sauri Inna ta tashi tsaye daga ɗan ɗosana ɗuwawunta da ta yi a ciki ta tsugunna ta galla mata harara ta ce.

"Gidan uwaki za ki shiga, na ce gidan uwaki ne nan ɗin za ki shiga?" Cewar Inna tana yi tana dogon wuya dan kar micijin ya zo kicin ya farmata.

"Ki bari mana mu shiga tare baki ga na cikin lokar nan ba ma duk cunkusuwa suka yi wani kan wani, zama da ba na daɗi ba yaushe mutum zai ce baya son matsi"

"Ai wallahi ko haɗiyeki micijin nan zai yi sai dai ya haɗiye, ba ke taƙamarki fitsara ba to ma ji ma gani an rufe tsohuwa da ranta" Cewar Inna tana ture hannun yarinyar daga jikin freezer da shige tare da rufe murfin freezer.ƙwafa yarinyar ta yi ta duba mukullin freezer ta ga yana jiki, aikuwa ta kulle, ta ɗauki wayar freezer ta jona a socket ta kunna ta ce .

" Ma ga yadda za ki yi" Ta faɗa tana komawa mafakarta ta ɗazu bayan ƙofa ta raɓe tare da ɗaukan wani buhun shinkafa danya ƙare ta lulluɓa duk gudun kar miciji ya ganta.

A tsakar gida kwa Sadiya ta rasa yadda za ta yi, ta taɓa micijin ya fi sau a irga amma yaƙi komawa mutum kawai sai ta samu wuri ta durƙushe take rasgar kuka abinta da abin ya girmi tunaninta.

A kicin kuwa Inna da ke cikin freezer ta fara jin wani sanyi a ƙafafunta, dan babu takalmi a ƙafarta tun lokacin da ta kwaso fa gudu ta silleshi jin zai hanata wali wajen gudu. Jin wani sanyi yana ratsa ƙafafu da jikinta sai abin ya bata mamaki dan ta san dai da idonta ta ga wayar freezer ma bata jikin socket, amma kuma ya ɗauki sanyi sai hakan ya bata tsoro sosai, jim kaɗan kawai sai ji ta yi gabaɗaga freezer ta ɗauki mugun sanyi, a take ta fara karkarwa jin sanyi na ratsata ta ko ina.

"Habunallahu wa ni'imal wakil, kar dai shegiyar yarinyar nan ce ta rufeni a ciki" Cewar Inna lokacin da take ƙoƙarin buɗe freezer ta ji ta a rufe gam. Jin sanyin ya yi yawa ta fara share hawaye tana cewa.

"Malam ka ga Azuminka dai ko suna ba a yi ba amma ina karɓar uƙuba kala-kala daga wannan sai wannan sai ka ce wacce uwarta ta ce ki je kya gani, ko dai baka yarda da tahowata ba ZAMAN WANKAN nan ba har zuciyarka, a ce ina ganin ƙalubale kamar an min baki" Ta faɗa tana sa hannu ta bugi jikin freezer. Ƴan cikin loka da me ƙunshi da ke lulluɓe da buhu da bata gane daga inda ƙaran ya fito ba duk zatonsu miciji ne ya ƙaraso kicin ɗin, ƴan ckn lokar a take suka cure a wuri ɗaya kamar ƙarago, ta cikin buhu kuma ta tuƙunƙune gefen buhu ta cusa a bakinta gudun kar tsoro ya sa ƙara ya kuɓuce mata micijin ya ga maɓoyarta ya farmata.


09030283375
[24/03, 5:14 AM] Mom Mashkur First class: Wannan littafin kuɗi ne 300
Za a tura ta wannan accaunt ɗin Fa'iza Abubakar 0020281885 Unity bank shaidar biya ta wannan no 09030283375 idan katin waya ne mtn Ƴan Niger su tuntuɓi wannan no +22785885134

2️⃣3️⃣➡️2️⃣4️⃣

"Haba jama'ar annabi ku kawo min ɗauki mana, ni ba tumatur ba ba gwanda ba amma gani a firinji sai ɗaukan sanyi nake" Cewar Inna cikin ɗaga murya tana jin wani kuka na taho mata. Wata atishawa ce ta taho me haɗi da majina saboda sanyin da ya gama ratsa ƙasusuwanta, so take ta yi ihun da kowa zai ji ta, a san cewa tana cikin na'urar bada sanyi dan ta lura duk kwakwazon da take ba wanda ya ji ta.

"Halimatus Sa'adiyya, ki bar micijin nan ki taho ki buɗe firinji kafin in yi ƙanƙara, ko masasssara ta kamani Malam ba zai yafe muku ba, Asharofa, Asharofa, ki fito daga bayin nan ki zo ceton rai " Cewar Inna da sanyi ya gama ratsa muryarta har ta fara shaƙewa ta faɗa tana sakin kuka. Jin shiru babu alamar ma ana jiyo ta sai ta fara magana a ranta.

"Yau ni Azumi wannan yarinyar akwai ƴar ƙundun buhun uba, yarinya ƙarama cakuru kuci cikon bancin ta garƙame a cikin wurin nan firinji sai aikinsa yake ni kuma ina ɗaukan sanyi, wannan ZAMAN WANKA bai ƙare ni da komai ba" Ta faɗa tana sanya hannunta ta rufe hancinta saboda sanyin da take shaƙa kamar wanda aka jefa ƙanƙara a cikin hancin.

"Ƴan nepa ku taimaka ku ɗauke wuta dan shi firinjin ba hankali ba gareshi bare ya san Azumi ce a ciki, ya san ba fura bace ya dakata da aiki" Cewar Azumi tana ɗaga ido ta kalli ɗan ƙaramin ƙwan da ke cikin freezer ya kawo haske abinsa.Hannu ta kai ta zage ƙarfinta duk da a takura take saboda matsi amma a haka ta jimƙe hannunta ta daki jikin ƙwan tana cewa.

"Wallahi gwara na fasaka firinjin ya lalace gabaɗaya a kan ina ji ina gani in ke zaune cikin ƙanƙarar nan, ni ba me rayuwa a turai ba, in zo in sandare in mutu a banza a ɗakko ni a daskare makara ma bata karɓeni ba dan ba tanƙwasuwa zan yi ba yadda nake a tsugunnan nan a haka zan ta zama, ko kabarin na san sai ko a gina min me zurfi a zura ni a ciki kawai, babu damar a kwantar da ni, ko ƴan gaisuwar mutuwata suka zo, na san sai dai suke cewa ashe azumi sa'i ya yi to Allah sa tsugunno hutu ne, dan babu me cewa kwanciya hutu ce, dan a tsugunne nake ba a kwance nake ba"

Ta faɗa lokacin da ta naushi jikin ƙwan amma ko gezau be yi ba bare ta sa ran zai fashe,ssi wani zafi da hannun ya ɗauka. Hannu ta kai ta shafo goshinta inda ta bugu ɗazu a garin gudun ceton rai, wurin ya yi ƙullutu ga zafi, tana taɓawa wani tausayin kanta ya kamata haushi ne ya sa ta shiga bugun freezer ba ƙaƙƙautawa dan ta san idan bata yi da gaske ba haka za ta mutu babu wanda ya sani.

Ƴan cikin loka ƙaran bugujn freezer da Inna take sai suka ɗauka micijin ne ya ƙaraso jikin lokarsu yake bugawa hakan ya sanya kowacce ta tsure, wata ƴar gidan ƙanwar Mama da yake ƴar siririya ce ita ce daga ƙasa sai wata bazawara ƙatuwa ƴar uwar Imran a kan ta tsabar yadda bazawarar ke da nauyi kuma a kan siririyar budurwar take dakyar take jan numfashi dan gabaɗaya ta danne mata har wajen kanta amma saboda tsoro sai bata ce komai ba, wannnan ƙaran da ya sanya suka firgita sai ƙatuwar ta ɗan muskuta ɗuwawunta aikuwa tsabar tsurewa ta saki wata uwar tusa da ta gama ratsa hancin siririyar ji ta yi kamar an saka hancinta a cikin kashi, tsabar wari har wani ɗaci-ɗaci ta ji a maƙoshinta. Kai ta shiga girgizawa, tsabar. Inna da bata san wainar da ake toyawa ba tana ta ƙoƙarin a zo a ceceta dan ta san har ƙwara na cikin lokar sau dubu a kan ita da ke ciki duk ta fara sandarewa dan da wani zai taɓa jikinta yanzu sai ya ji kamar ƙanƙara ya taɓa. Wani uban zabura ƙatuwar matar ta yi aikuwa kanta da ke dab da saman lokar ta ciki ya bada wani gum, gumewar da ta yi a kanta sai kuwa ta sake sakin tusar, gabaɗaya lokar ta haɗe da wari su duka a takure suke, ba dan micijin nan ba da babu wanda zai iya shaƙar numfashi saboda ɗoyi amma tsoro ya sa ba za su fito ba, siririyar nan jin an ƙara sakar mata tusa haushi da takaici ya sa ta ɗan gota kanta daga saitin ɗuwawun matar dan hancinta ma a wajen maraba biyu yake ta tsagar ɗuwawun matar aikuwa cikin fusata ta buɗe bakinta ta gantsara mata cizo a ɗuwawun wani azababban zafi ne ya ratsa matar da ta manta da cewar a ɓoye suke ta hangame baki ta saki wani uban ƙaran ta ce.

"Wayyo ya gantsara min cizo a ɗuwawu" Duk ta ruɗe da zafin cizo sai ta zata micijin ne ya shigo ya cijeta dan ƙuncin da suke ciki ko ƙasa baka iya kallo duka a wuri ɗaya suke a cure. Yarinyar nan me ƙunshi jin an ce an yi cizo a ɗuwawu sai ta fara karkarwa dan ta san ita ma micijin dole ya ganta tunda ya ga na cikin loka ma bare ita aikuwa ta saki wani kuka, ga buhun da ta tuƙunƙuna ta saka a bakinta sai sautin kukan ya bada wani wuuuuu kamar wata jiniya. Inna da ke cikin freezer jin ihun da kuma ambaton da aka yi na an yi cizo sai ta ce.

"Wallahi gwara ku a kaina duk tsiya ai inda sauran kwananku za a sa muku maganin dafin miciji ku warke, idan kuma kuka mutu ai zaku kwanta a kabarinku a kan ni da sai dai ake Allah sa Azumi tsugunno hutu ne" Ta faɗa tana sakin kuka tana da na sanin zuwa ZAMAN WANKAN ma gabaɗaya.
Sauran ƴan cikin lokar kuwa sai tsoro ya ƙara shigarsu ji micijin har ya shigo lokar ya yi cizo banda wacce ta yi cizon da ta san ita ce ta yi cizon ba miciji ba, hakan ya sanya ɗaya kama jikin ɗaya ta damƙe da hannu biyu aikuwa wacce aka damƙa ta wage baki ta saki ihu ta ce.

"Wayyo an damƙe min nono, wayyo ni Allah na, ni ba a min ƙunshi ba amma za a min lahani" Ta faɗa cikin kuka da azabar da ta ji a jikinta, da yake yarinya ce ba wata babba ba irin ƙirgen dangin nan ne ta fara wanda ko ɗan bigewa ka yi a jiki sai ka ji azaba. Ita kuwa wacce ta damƙi yarinyar bata ma san abin da ta yi ba, jin wai an ce ta damƙi nono da sauri ta saka dan ita bata ma san ina ta kama ba ta dai ji fitsarin yarinyar na gangara a kan ƙafafunta.

"Wayyo Allah wallahi da a taɓa min wurin nonona, ko da kuwa da ɗan yatsa ne gwara in bada kyautar naira dubu saboda azabar ciwo amma kin zo kin damƙa kamar kin samu ƙanzo" Ta faɗa cikin kuka, babu wanda ya ce wani abu dan yanzu ta kai- ta kai ake.

"Gwara ke nono aka damƙa, wayyo ɗuwawuna za a cire min fatar" Ta faɗa jin an ƙara cafka da haƙori dan tana sakin tusa ita kuma ta ƙasanta ke gatsara mata cizo.

Inna da ke cikin freezer ta ƙyalƙyale da dariya duk da halin da take ciki, amma jin ana damƙe-damƙen ɗuwawu da nono sai abin ya bata dariya ta ce a zuciyarta

"Yau dai ana dara ga kuma dare ya yi, Hassan duk ya rabawa kowa aikin wahala"

Me ƙunshi ma kukan da take ne ya haɗe da dariya a ranta ta ce.

"Taɓɗi yau da a ce ba a halin ƙaƙanikayi nake ba dariyar da zan yi sai cikina ya yi ciwo, dan ko ni lokacin da na fara ƙirgen dangi ko wanka na zo sai dai in zuba musu ruwa in ɗauraye su, ba na yarda in sa soso in wanke saboda azaba" Ta faɗa tana dariyar da ta kusa fitowa fili saboda yadda dariyar ke cinta.

"Inna! Inna!! Inna!!!" Inna ta jiyo muryar Sadiya tana ƙwala mata kira tun ƙarfi.

"Inna dan Allah ki fito ki tayani mu dawo da Hassan gashi can ya kama hanyar ƙofar gida zai fice kuma ƙofar ba a rufe take ba, ni kaɗai ba zan iya ba dan ya ƙi tsayawa ko ɗaukansa zanyi zulalewa yake" Cewar Sadiya tana kuka ta rasa yadda za ta yi hankalinta ya kai ƙololuwa wajen tashi, bata so ɗan nata ya fice duk da kasancewarsa a siffar muciji tana ƙaunarsa, Allah sarki uwa!

"Mtssss" Inna ta ja wani dogon tsaki ta ce.

"Banza ta kori wofi ma kenan yo Allah na tuba da ba a cikin firinjin nan nake ba ma babu abin da zai sa na zo wallahi, da kaina zan kaɗashi ya tafi, gwara ma ya je ya fice abinsa wataƙila ma wahalarki ce ta yanke, yo Allah na tuba zama da wannan abu a gida ai jafa'i ne, ya je can daji ya samu ruwa ƴan ruwa su ja abinsu mu huta, ga Husaini nan ya isa" Ta faɗa tana ɗaɗɗaga kai take kallon saman freezer.

"Dan Allah ku taimaka mini" Cewar Sadiya tana ɗaga murya.

Ashrof tausayin ƴar uwarta ya kamata amma ga kuma tsoro tana ganin kamar micijin zai iya cutar da ita, amma ita Sadiyar ba lallai ya cutar da ita ba saboda ita ce mahaifiyarsa.

"Ke dalla ɗaga ni kin wani min ɗirkaka a kaina kamar wani buhun hatsi" Ƴan cikin loka ke faɗa saboda sun ji an ce miciji ya kama hanyar fita waje.

"Kan ku ake ji wai mahaukaci ya faɗa rijiya ya ce ni wankana nake "Cewar Inna.

"Ƴan cikin kicin ga Hassan nan ya nufo kicin" Sadiya da ta shawo gaban Hassan daga hanyar gida ya iyo kwana ya dawo gida ta faɗa cikin ɗaga murya ganin gadan -gadan ya nufi kicin ɗin.

Ashrof da ke ƙoƙarin fitowa ta taimakawa Sadiya ta dakata daga ƙoƙarin fitowa daga bayi jin Sadiya ta ce ya nufi kicin.


"Hahahaa na dawo in ji ɗan yawon duniya, yau akwai gwarama" Cewar Inna tana dariya ido na zubar da ruwan hanci ku sai tsiyaya yake kamar an kunna fanfo tsabar sanyin freezer da take shaƙa.

Gabaɗaya masu faɗa a cikin loka sai suka sha jinin jikin su ko kyakkyawan motsi sun kasa yi, kowa bakinsa sai motsi yake alamar addu'a.

Sai da ya je tsakiyar kicin ɗin ya ja ya tsaya tare da fasa kai alamar sara, Sadiya da ke tsaye a bakin ƙofar sai kallonsa take so take ta koma ɗaki ta ɗauki wayarta ta kira Imran amma bata so ta matsa daga wurin wani abu ya faru kuma ma ta san shi ma Imran tsoron Hassan ɗin yake ji idan ya sawaya.

"Kar wanda ya motsa daga inda yake Hassan yana tsakiyar cikin kicin ɗin" Cewar Sadiya cikin muryar kuka.

Ɗif kowa ya yi, me ƙunshi kwa da ta buɗe idonta guda ɗaya ta ɗan leƙo daga cikin buhun da ta lulluɓa da shi. Ganin micijin danƙarere ya fasa kai da alama sara kawai yake son yi, gashi kuma ta san babu wanda zai fi saurin gani sama da ita, a take ta ji ina ma ita ce a cikin freezer kuma freezer a buɗe a kan wannan tashin hankali da take ciki.

Bum-bum ƙaran bugun freezer da Inna take ya karaɗe wajen, duk bugu ɗaya sai micijin ya zabura, zaburarsa kuma ba ƙaramin ƙara razana me ƙunshi take ba, Inna kuma dama da niyya take bugawa saboda ko banza ta san ta rama kaɗan daga abin da yarinyar ta mata.

"Wayyo wannan tsohuwa masifarta ta yi yawa, yanzu sai ta firgita micijin nan ya shiga neman mutumin da zai sara a cikin kicin ɗin, tsoratar da yake yana wata girgiza yana fasa kai ta ko ina hakan ba ƙaramin tsurewa ya sanya me ƙunshi ta yi dan ita kaɗan ke ganinsa na cikin loka da Inna da ke freezer ra san ba za su gani ba.

Shigowar Imran gidan ɗauke da sallama shi ya sanya Sadiya nufarsa da sauri tana kuka tana faɗa masa, wani yawu ya haɗiye muƙut jin wai micijin har ya fara fitowa ya yi waricinsa a cikin gidan lallai babar magana . Haka dai ya daure tare da majewa ya nufi kicin ɗin, a haka ya sanya Sadiya ɗaukan micijin ta nufi ɗaki da shi har lokacin kuka take yi. Imran ganin matan nan na cikin loka ya ɓata mas rai ganinsu cunkushe kamar alhazai ranar arfa, wata da take leƙo idonta ta tsakanin murfin lokar ita ya dakawa wata uwar hararar da ta sanya ta runtse idanu, ƙafa ya sanya ya daki jikin lokar tare da cewa su fito haka, haka suka turo murfin suka fito simi-simi suna ciccira idanu kamar waɗanda suka yiwa sarki ƙarya.Suna fitowa daga kicin ɗin ya tsaya a bakin ƙofar yana binsu da wani mugun kallo dan daga me zarnin fitsari sai wani

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login