Showing 12001 words to 15000 words out of 56867 words
a cikin ruwan, har yana shiga hancinsa amma gani yake da ace ya fito wurin micijin nan gwara kowa ta yi ta kanta dan ya san dai ba Sadiya ce kaɗai a gidan ba.
Inna sakkowa ta yi daga saman bencin, ta ɗakko ashana tare da buhun shinkafa marar komai, ta ɗaga ƙafa ta doki jikin lokar da matan nan je ciki, aikuwa suka ƙara sakin wani kukan, tsaki ta yi, ta juyawarta ta buɗe ƙofar kicin ɗin ta fito, ganin Hassan daga gefe ɗaya, ga kuma Shek tsaye bayan Sadiya dan tana motsawa yake take mata baya. Hanyar murhu ta nufa tana zuwa ta ce .
"Ihuuuu kwarto" Sai da ta tabbatar Imran ya ji da gangan ya ƙi fitowa, aikuwa ta sanya buhu a murhun dama cike yake da ita ce ta kunna ashana ta sanya nan sa nan wuta ta kama ci galgalgal, dariyar ƙeta ta yi tana jijjiga kai ta koma gefe ta tsaya ta ce.
"Kamar yadda na fara jin sanyi lokaci guda ya baibaye firinji, haka kaima za ka ju zafi lokaci guda ya baibaye tukunya"
Imran da ke cikin tukunya, ya ji wani zafi ya fara ratsa tukunyar, gyara rungisan sa ya yi amma sai ya ji abin na ƙaruwa, amma aai ya daure, jim kaɗan sai ya gabaɗaya kamar an sanyashi a ovin.
A mugun firgice ya bugi murfin tukunyar ba shiri, ji kake gwagwaraf, ya yi jifa da murfin, sai gashi yana fitowa jargaf da ruwa a jikinsa ga kuma uban gumi kamar an masa wanka ...
[24/03, 5:14 AM] Mom Mashkur First class: *MAMAN AFRAH DATA SERVICES*
*BUY DATA FROM THE AFFORDABLE PRICE*
*I selling MTN data with this cheap price*
*MTN DATA PACKAGE*
500MB@===150
1GB@=====250
2GB@=====500
3GB@====850
5GB@====1,400
Dial *312*4*7*4# to check Data balance.
*Validity 1 month*
*Airtel,9mobile and Glo* *also available.*
*Subscription for DStv gotv star time electric pay bills*
Act details FA'IZA ABUBAKAR unity bank 0020281885
Whatsapp OR
Call 09033283375
Wannan littafin kuɗi ne 300
Za a tura ta wannan accaunt ɗin Fa'iza Abubakar 0020281885 Unity bank shaidar biya ta wannan no 09030283375 idan katin waya ne mtn Ƴan Niger su tuntuɓi wannan no +22785885134
2️⃣5️⃣➡️2️⃣6️⃣
Wani ƙululun baƙinciki ne ya zo ya tokarewa yarinyar maƙoshi, jin abin da Inna ta faɗa, gabaɗaya sauran matan suka fara bin ƙirjinta da kallo suna so su gano asalin gaskiyar abin da Innar ta faɗa, aikuwa kowa ya shiga danne dariyar da ke cin sa ganin gaskiya Inna ta faɗa in ma akwai gyara a maganar to kuwa kaɗan ne. Ganin kowa ya zubawa ƙirjinta ido sai ita ma ta shiga kallon ƙirjin nata har da sanya hannu ta ɗan ɗame jikin rigar wai dan ta ga girmansa.
"Duba da kyau dai ɗiyar nan ƙarya zan miki, ai yanzu kya yarda da kika ɗame rigar ai kin ga girmansa bai fi ƙwayar ƙarago ɗan nera biyar ba idan ma ya kai kenan"
Magana yarinyar ke yi ƙasa-ƙasa da baka jin me take faɗa sai yafda bakinta kawai ke motsawa kake gani da alama rashin kunya take yiwa Inna.
"Wa ya ga banza ta kori wofi ai maganar ciki ba magana bace a fito fili a faɗa mana" Cewar Inna ta juya ta nufi ɗaki tana ɗan dudduƙawa dan har zuwa sannan hancinta bai daina zuba ba sosai mira ta mata kamun kazar kuku. Sai kuma wacce ta yi tusa aka cijeta ita ma ta fara magana.
"Aikin banza da wofi duk kin bi kin cije ni, haba wannan wane irin abu ne" Harara kawai ɗayar ta bita da ita ba tare da ta yi magana ba dan idan ta buɗe baki komai ma za ta iya faɗa, saboda yadda ta yi ta ƙwararta da warin tusa sannan ganin Imran ma a wajen ya sa ta ɗaga mata ƙafa.
Inna tana zuwa falo sai ganin Sadiya ta yi kamar an dasa ta a wajen tana tsaye a tsakiyar falon hannunta riƙe da Hassan a siffar miciji har lokacin bai dawo siffar mutum ba. Wani yawu Inna ta haɗiye ba tare da ta cewa Sadiya uffan ba ta nufi inda suka ajiye lalle, kowanne a leda aka kwaɓashi sai mai ƙunshi take ɗauka tana zubawa a cikin kwarkwaron da take ƙunshin. Lalle ne ɗan kwali sajen ne ja da kuma baƙi na fulawa. Da ɗan yawansa a cikin ledar, saboda gabaɗaya ta kwaɓe yadda zai ishe su. Inna baƙin ta ɗauka na fulawar ta ɗauki baƙar leda ta sanya a hannunta ta ƙulle sannan ta juye wannna lallen a kan baƙar leda Sadiya da ke cikin wani haki ko kallon Inna bata yi ba tun shigowar Innar da ta kalleta bata ce komai ba. Dan kawai gabaɗayansu mamaki suke bata na gudun da suke yi, duk da ita ma ta san da a ce Hassan ba ɗanta bane dole ta gudu dan tsoro amma yanzu babu yadda za ta yi ko da tana jin tsoron saboda ya zame mata dole.
Inna sai da ta juye baƙin lallan nan duka sannan ta juyo a dudduƙe ta fito daga ɗakin har lokacin dai kowa na tsaye carko-carko, me ƙunshi ta ɗan juya kenan kafin ta juyo sai ji ta yi an damƙeta an shiga lafta mata wani abu a fuska da ta kasa tantance menene.
Inna kuwa tun da ta damƙi wuyan me ƙunshi ta baya, bata saki ba ta dage sai lafta mata lallen take a fuska kamar wacce take fenti a bango, sai da ta lafce mata shi gabaɗaya a fuska har wuyanta sannan ta sake ta tana ta ihu dan ma dai ta rufe ido da har idanun zai shiga. Imran tun da ya kallesu sau ɗaya ya ɗauke kai dan shi baya son hayaniya kuma ya san da alama yarinyar wani abu ta yiwa Inna dan ba ya raba ɗayan biyu ita ce ta rufeta a freezer.
"Wayyo Allah na Allah sa dai ba kashi bane kika lafce min shi a fuska" Cewar me ƙunshin tana ƙololon amai lokacin da Inna ta sake ta.
"Shigiya kudurarriya ni da kashin ma na samu ai da wallahi har haɗiya sai na sa kin yi, har ni zaki garƙame a cikin firinji, sanyin duniyar nan na cikinsa ya ƙare a kaina, hancina banda yoyo babu abin da yake in ba ruwan zafi na yi ba ma masassara ce za ta kama ni, saboda rashin tsoron Allah duk sanyin nan da ake baki tausaya min ba kika rufeni kika kunna firinjin" Cewar Inna tana face hanci tare da sakin wani kuka na tausayin kanta irin yadda ta sha artabu a cikin freezer.
Gabaɗaya dariya suka kwashe dashi Inna da ke shirin magana ta dakata ganin Sadiya ta fito riƙe da micijin a hannunta ba Inna ba su duka ma masu dariyar dakatawa suka yi, Imran da ya fara wani ɗan kakkauda kai yana sosa ƙeya dan ba ya son Sadiya ta zo ta bashi micijin ta kunyata shi a gaban matan nan. Dan haka sai ya shiga muzurai yana ɗan babbasarwa shi a dole ba komai bane. Inna kuwa tun da Sadiya ta fito ta fara tunanin inda za ta garzaya dan ta tsorata da yaron yanzu dan bai taɓa kaiwa kamar haka bai dawo mutum ba amma yau ya yi dogon zango.
Sadiya da take shirin buɗe baki ta yi magana Inna ta katse ta da cewa.
"Ke kuwa Halima baka tausayin yaron nan kika fito dashi da sanyin nan, ko dan kinnga ba a siffar mutum yake ba kike gani kamar baya jin sanyi" Ta faɗa tana wani karya kai gefe dan gabaɗaya ta matsu Sadiyar ta kuya ta koma inda ta fito dan kana kallon micijin duk jarumtarka sai ka ji tsoro saboda yanayin girmansa ma.
"Inna wallahi hannu na ya gaji da riƙonsa kinsan akwai nauyi fa kuma ina son na shiga bayi ne shi ne zan baiwa Abbansa ya riƙe min shi" Cewar Sadiya tana kallon Inna. Imran kuwa jin fitowar Sadiya saboda shi ta fito ta baiwa Hassan sai ya ji wani dammm ƙirjinsa ya buga dan shi yanzu har ga Allah ya tsorata da yanayin yaron.Wani yawu ya haɗiye da bai san lokacin da ya taru ba ya kalli Sadiyar yana shirin magana sai Hajiya da Mama da suka haɗu a ƙofar gidan yanzu suka shigo da sallama.
Ƴan matan nan duk sun sha jinin jikinsu, me ɗinki kuwa da fitowar Sadiya ta mantar da ita abin da Inna ta lafta mata a fuska da wuyanta tsabar tsoro, gabaɗaya ya mata baƙiƙƙirin a fuska kamar ta shafa baƙin gawayi dama ga ta sha uban bilicin sai ta koma kamar wata jimina.
"Yauwa ga kakanninsa nan" Imra n ya yi saurin faɗa ganin su Mama sun shigo. Idanun Mama da na Hajiya ne suka sauka a hannun Sadiya da ke riƙe da miciji, gabaɗaya wani tsoro ne ya rufe su dan su bai taɓa sawaya a gabansu ba, sai dai a basu labari ita kuma Hajiya dama ita ce me cewa ko ya zama miciji babu abin da zai yiwa mutane, sai dai ganinsa yau muraran ya kaɗa mata hantar cikinta, Mama kuwa cikin ficewar hayyacin ganin ƙaton miciji riƙe a hannun ɗiyarta ta buɗe baki ta ce.
"Sadiya me zan gani haka? Hassan ɗin ne ya zama wannan ƙatoton micijin kamar wata mesa? Kuma kika kama shi kika riƙe a hannu, me ye amfanin ubansa da yake tsaye?" Mama da soyayyar ƴa da uwa tasa ta manta cewar Hajiya na wurin ta faɗa tana kallon micijin.
"Haba Mamar Sadiya ai ana barin halak ma dan kunya, kuma uwa ai ita ce tushen ɗa, kuma da ita da Imran ai duk ɗaya ne ma in ta riƙe babu komai" Hajiya ma da son ɗanta ya rufe mata ido ta faɗa ita ma idanunta a kan Hassan ɗin.
"Wai ni kam me yasa kuke haka, ta yaya ma za a ce uwa ce rushen ɗa haba Amina wannan ma ai ba maganar ɗauka bace, uba ai shi ne tushen ɗa, lokacin da ya ɗirkawa ƴar mutane ciki take riƙitu da tsohon ciki baki ce haka ba sai yanzu da take riƙe da miciji aka ce a bashi ya riƙe?" Cewar Inna tana hararar Hajiya Amina da sai yanzu ta ga wautar ta amma ai da gaskiyarta ya za a yi a riƙe miciji da bbau tabbas a kansa.
Hajiya da ke shirin maida martani ta rufe bakinta ruf, ganin wani uban ƙwacewa da micijin ya yi daga hannun Sadiya ya wani zabura ya yi sama kamar wata iska ya bar hannun Sadiya. A tsakiyar mutanen nan ya tsaya tare da fasa kai yana wani wawwaiga idanu. Kowa ya matuƙar razana da yanayin yadda micijin ya yi, Mama kallon ƙofar gidan ta yi amma cikin rashin da'a sai ta ga a kulle dan dama Imran na shigowa sai ya manta bai rufe ba su kuma suna shigowa sai suka maida ƙofar suke rufe jamlock ɗin ya shiga.
Dan haka babu hanyar fita dan yadda jikin kowa ke karkarwa babu inda za su iya buɗewa saboda a tsorace suke gabaɗaya sun gama tsurewa.
Inna kuwa tana ganin hakan sai bakinta ya fara motsi leɓanta na sama ya fara gwaruwa da na ƙasa alamar dai tana rattabo du'ai.
Kowa karkarwa yake kamar sun haɗiyi mazari.
"Wai shin Imirana duk wurin nan fa kai ne namiji, ka yi wani abu mana " Cewar Inna cikin sarƙewar murya.
" Haba Inna in shi ne namiji ma sai ya kai kansa ga halaka, kar ki manta ni fa shi kaɗai gareni, ga uwar yaro kya ke cewa wai shi namiji ne ai Sadiya ma mace ce me kamar maza kwari ne kawai babu" Hajiya ta faɗa har rana yin in'inna tsabar a ruɗe take.
"Oh ni Azumi na ga abin da ya turewa buzu naɗi wallahi yanzu Amina ƙin gaskiya ƙiri-ƙiri to wallahi ki ji tsoron Allah dan faga ƙin gaskiya sai ɓa...
Wani uban zillo da micijin ya sake yi tare da maida kansa ya kwantar a ƙasan sai kuma ya ɗaga jelar sama, shi ya dakatar da Inna daga maganar da take son ƙarasawa. Kowa ɗif ya yi babu me cewa uffan amma da ka gansu ka san a matuƙar tsorace suke. Imran kuwa sunkuyawa ya yi ya ajiye wayarsa a ƙasa ya ɗago tsaye ya sanya hannunsa na dama a haɓarsa ya shiga shafa haɓar da shi kansa bai san dalili ba, shafawa yake ba ƙaƙƙautawa daga gefe zuwa gefe, bakinsa kuwa sai mismismis yake shi kaɗai ya san me yake faɗa. Inna kuwa hannu ta sanya ta toshe hancinta da ke zubar majina, idanunta a kan me ƙunshi nan da take karkarwa fitsari na biyowa ƙafafunta sai buɗe baki take tana kuka amma marar sauti zuwa lokacin lallan ya gama haɗa mata fuska da baƙi ta yi baƙiƙƙirin da ita.
"Shegiyar yarinya ji yadda ta koma kamar bunsurun ɗan akuya, gabaɗaya ta yi baƙi kamar ta shafa baƙin bula, sai ta zama kamar irin baƙin bunsurun nan gemu ne kawai babu" Cewar Inna a zuciyarta tana dariyar ƙeta duk da halin da ake ciki amma fa ka kalli me ƙunshin nan sai ka kai zuciya nesa ne dariya ba za ta ƙwace maka ba. Gurbin idonta kawai ake iya hangowa ita kuwa sai ɓare baki take tana da na sanin zuwa gidan ƙunshin ma gabaɗaya.
Sadiya kwa gaban micijin ta je ta durƙusa tana kallonsa hawaye na zubowa daga idanunta. Mama kuwa so take ta ce Sadiya ta tashi faga gaban micijin sai dai tsoro da fargaba ya hanata magana tana ganin kar ta yi magana micijin ya iyo kanta ya sare ta a banza ta bar duniyar a wufi, dan haka sai ta ja bakinta ta yi shiru tana ta lazimi a zuciyarta lazimin da ita kanta da za a sanya mata wuƙa a wuya a ce ta faɗa ko kalma ɗaya ba za ta iya faɗa ba, dan ta kasa banbance ma addu'a take ko karatun qur'ani ko kuwa ƙasida, wani lokacin ma sai ta ji kamar waƙa-waƙa take amma Allah ne kaɗai ya san karatun kurma.
Da baya da baya micijin ya shiga tafiya aikuwa aka dare aka bashi hanya, kowa cikinsa na ɗurar ruwa ga miciji da shegen gudun tsiya idan ka ce za ka gudu idan ya biyoka ba lallai ka tsere masa ba saboda gudun da yake dashi. Dan haka sai kowa ya shiga taitayinsa aka shiga jiran ganin abin da zai yi. Sauran matan kuwa sai kuka suke marar sauti wata ta kama tsantsa wata ta ɗora hannu a ka har da wacce ta ɗaga hannaye sama irin yadda ake addu'a ta baza tafukan hannaye sai wani karkata kai take tana kai kukanta wurin Allah.
Ashrof kuwa ta sanya hannu a fuskarta ta rufe fuskar da tafukan hannayenta tana kallon micijin ta tsakanin yatsada yatsa dan kar ta rufe idanun duka micijin ya iyo wurinta dan ita ganinsa kaɗai ma razana ta yake. Hajiya yadda micijin ya fara ja baya haka ita ma ta shiga ja baya, a hankali har sai da ta ga babu wurin gudu sannan tana tsoron ta zuba da gudu micijin ya tsallakr kowa ya biyo ta haka ta jure tana cewa a zuciyarta.
"Allah ka dubemu ka kawo mana mafita"
"Allah ka kawo me cetonmu, a wannan gida da muke ciki a rufe ga kuma ajalinmu a tare da mu" Cewar Inna a ɗan hankali kamar tana tsoron faɗa.
A hankali micijin ya shiga kanannaɗewa har sai da ya kanannaɗe duka jikinsa, sai kuma cikin hanzari da zafin nama ya zura da gudu, ya shiga zagaye gefen da mutanen ke tsaye kowa kallonsa kawai yake sai da ya zagaya kusan sau uku, sannan cikin tafiya ɗaya biyu ya yi sai gashi a gaban Imran yana zuwa ya fasa kai ya dakata a wurin ba tare da ya matsa ba.
"Ka min daidai Hassan, gwara da ka je gun ubanka da kan ka yau za mu ga ƙarshn ƙarya" Cewar Inna a zuciyarta tana ƙwafa.
"Wayyo Allah ɗana, ɗana guda ɗaya da nake da shi duk duniya yau ya haifi abin da zai zama ajalinmu" Cewar Hajiya a zuciyarta tana tana share hawaye.
"Gwara da ka je wurinsa tun da ba ita kaɗai ta haifeka ba da za take jigilarka ita kaɗai" Cewar Mama a zuciyarta a fili kuma sai ta dakata da motsin bakinta ta danne gefen keɓenta da haƙori, irin ka min daidai ɗin nan.
Imran kuwa wasu hawaye ne masu kamar an musu dole su fito suka shiga surnano masa a fuska, sai na ido ɗaya ya gama gangarowa sannan na ɗaya idon ma ya gangaro.
"Alwudu'u, alwala, kaifa tatawadda'u, yaya za ka yi alwala" Cewar Imran yana sakin kuka dan yau ya sadaƙar sai dai gawarsa tun da har kicijin ya je gabansa da kansa.
"Ɗan karan uwa ɗan gwafar uba da baka karanci yadda ake alwalar ba sai yau, to duk sallaolinka na baya aradu ka yi su a wofi tun da sanda ka yi baka iya ba alwala, sai yau da ka ji uwar bari, ka fara tuna karatun alwala ai bari ba shegiya bace da ubanta" Cewar Inna a zuciyarta.
Sauke kai micijin ya yi daga fasa kan da ya yi, ya wani kaiwa ƙasa sara sau biyu da mugun ƙarfi.
Imran idanu ya ƙwalalo tare da ɗauke numfashinsa ganin micijin ya sari ƙasa kusa da ƙafarsa, duk tunaninsa ma shi ya sara sai da ya zare idanu da kyau sannan ya gane ƙasa ya sara, sai dai yana rayawa a ransa shi ma ana daf da saransa. Ƙafafu ya ƙame a wuri ɗaya yadda sojoji ke ƙamewa, ya ɗaga hannu biyun duka ya ka gefen kansa yadda sojoji ko ƴan sanda ke yi idan za su sarawa oganninsu, amma shi da hannu biyu ya yi, a wannan ƙamen ya shiga jero taken Nigeri'a ba ƙaƙƙautawa, shi kansa ya tsinci kansa ne yana faɗa ba tare da niyyar hakan ba saboda gabaɗaya ya rasa me zai ce ma.
"Kai jama'a yau ake yinta, lallai gulma yau ya ƙare tun da uwar gulma ta yi cikin shege, wato saboda ɗaurewa Nigeri'a da harshen nasara tsantsa kaima yadsa abokinka sojojo ya yiwa Nigeri'a baitika kaima hakan take" Cewar Inna a ranta