Showing 1 words to 3000 words out of 56867 words

Chapter 1 - YAR ZAMAN WANKA BOOK 3

27 Sep 2024

3830

[24/03, 5:14 AM] Mom Mashkur First class: Wannan littafin kuɗi ne 300
Za a tura ta wannan accaunt ɗin Fa'iza Abubakar 0020281885 Unity bank shaidar biya ta wannan no 09030283375 idan katin waya ne mtn Ƴan Niger su tuntuɓi wannan no +22785885134


2️⃣1️⃣➡️2️⃣2️⃣

Suna zuwa falon Imran ya ja tunga ya tsaya yana ƙoƙarin danne dariyar da take son fitowa ba tare da ya shirya ba, dan yadda ya ga Inna ta wani biyo su kamar wanda suka yi wani gagarumin laifi sai wani muzurai take kamar ta yiwa sarki ƙarya. Sadiya ma sai da suka dangana da falon ta fara jin haushin gudun famfalaƙin da suka yi, dan abin na Inna ya wuce misali.

Inna na fitowa falon ta kasa ta tsare riƙe da makamanta, kallonsu kawai take tana jin haushinsu gabaɗaya, dan kawai gani take shegiyar jaraba ce da rashin haƙuri ya sa suke nema su jiƙawa mutane aiki su ɓallo ruwan da tsayar da shi zai yi wahala, amma fa in ji Inna. Imran ƙarasawa kan kujera ya yi ya zauna tare da wani hakimcewa ya tattaro gabaɗaya jarumtarsa ya dake da ita, kamar ma bai san Inna na hasala tana hatare -harare ba kamar wacce aka yiwa ƙwacen kuɗi.

"Ni dai wallahi zuwa birnin nan da zaman gidan nan ya zame mini masifa da bala'i yo Allah na tuba idan ba masifa ba menene wannan a ce tun da na zo ZAMAN WANKAN nan da raina ban huta ba sai bala'i daga wannan sai wancan kullum da kalar wanda nake hantsilawa a ciki" Ta faɗa tana kallon Sadiya da ta sunkuyar da kai ƙasa.

Babu wanda ya tanka ta dan haka bata yi wata-wata ba ta cigaba da magana cikin hasala.

"Banda rashin mutunci a ce ina cikin gidan nan Imirana kake neman haikewa ƴar nan me ɗanyen jego, kenan ma bani da amfani? Ko dan baka san wahalar ɗaukan ciki da nakuda da kuma reno ba, abin da ka sani kawai ka yi fush ɗan ya faɗo duniya, ai ana barin halal dan kunya" Ta faɗa tana jin kamar ta hau Imran da duka.

"Dan Allah Inna ki yi haƙuri babu wanda ya san kin dawo ma gid...

"Rufe min baki algunguma, irinku ne daga an yi arba'in sai a ji kun fara amaye-amayen jaraba, har kin manta uwar wuyar da kika sha a naƙudar ku ne masu biyewa namiji ya ƙara ɗirka muku wani cikin saboda rashin sanin ciwon kai daga namiji ya fara muku daɗin baki sai ku bada kai bori ya hau a barku da wahala yo ciki da goyo ai wahala ne" Inna ta katse Sadiya cikin harzuƙa.

Shiru Sadiyar ta yi bata ce komai ba amma a zuciyarta sai ta ce

"Inna ke kika ga bala'i a zuwanki ko kuma mu muke ganin bala'i kala-kala, tun da kika zo wa ya huta jarabar yau da ban, ta gobe da ban, in ban da neman magana da hana rai sakat a ce muna cikin ɗaki ma sai kin bimu ko ke zaki yi rainon cikin" Cewar Sadiya a zuciyarta.


"Kai kuma Imirana na lura inda aka raba kunya ma baka bi ta wajen ba, lokacin da ake raba sanin ta ido kai kana bacci ina tsaye a ɗakin amma ka yi getse-getse riƙe da mace wai kai ɗan duniya " Ta faɗa tana kafe Imran da ido tamkar za ta sakar masa muciyar a kansa.

"Matarki ce?" Cewar Imran cikin izza ya kuwa make kamar ma bashi ya yi maganar ba.

Sakin baki kawai Inna ta yi galala tana kallon Imran cike da mamakin kalamansa, ta ma rasa bakin magana.

"Na ga dai sadaki na biya ko kyauta aka bani ita, in kuma...

"Lallai in da ranka ka sha kallo, duk mai rai ba ya rasa ganin abin mamaki, Imirana ni kake cewa Halima matata ce, ban da dai ka ga makwancina, to bari in tuna maka idan mantawa ka yi, ni nan Azumi ni na haifi uban Sa'adiyya tun kafin ai ɗaran akay kwanɗi, da kai yaushe ma ka san Halimar yarinyar da ka san ta bayan uwarta ta gama cin fitsarinta da kashinta"


"Bari na je masallaci" Cewar Imran yana kallon Sadiya ya nuna ma kamar bai san Inna da shi take magana ba.


"Au ga mahaukaciya tana magana, shi yasa za ka barni ina ɓaɓatu, ni na ma rasa me ya kaini na baro ɗakina, ina cikin rufin asirina a gidan Malam na kawo kaina nan inda ake cire min zane a kasuwa, ban da dai ka gan ni a gidanka Imirana har ka isa ka yi watsi da maganar da nake ka ce wai masallaci za ka tafi, in ban da dai ka raina ni kuma kana so dai ka fice ka barni wato ga karya tana haushi, yo na ga yanzu ma aka fara kiran sallar ko gama kiran ma ba a yi ba amma wai kai ga sallau shi ne za ka yi riga malam masallaci" Ta faɗa tana share ƴar ƙwallar takaicin da ta sirnano mata.

Shi dai ko kallon inda take bai yi ba ya sa kai ya fice abinsa dan Inna ta fara kai shi bango tun baya son magana amma duk zuwanta ta hore masa baki tana sa shi yawan magana. Jan hanci ta shiga yi tana cigaba da share hawayen, Sadiya dai bata ce komai ba ta nemi wuri ta zauna.

"Halima kina jin wannan kurman mijin naki wai shi ma ya waye ya yi baki, wai har ni yake faɗawa magana son ransa"

"Haba Inna shi fa babba shi yake siya wa kansa mutunci, duk da kuna kakata amma ai dole ki ja girmanki yadda Imran zai ke shayinki amma a ce abin da huruminki ba kina shiga duk yadd...

Salatin da Inna ta ɗauka kamar ta ga gawar da aka yiwa kisan gilla shi ya sanya Sadiya jan bakinta ta yi shiru dan sai da ta faɗi maganar ma ta gane katoɓarar da ta yi dan ta san ko sama da ƙada za su haɗe babu za a yi Inna ta fahimci maganarta.

"Halima yanzu kenan kin zaɓi mijinki kin bar Kakarki wacce ta haifi ubanki, to in banda ma na haifi uban naki ta yaya ke za ki zo duniya amma kin zaɓi mutumin da kika haɗu da shi da haƙwaransa talatin da biyu kin ajiye ni, ni da na haifi ubanki har ke ma kika samu dirowa duniyar"

"Ba baka nake nufi ba Inna ke ɗaukan ƙafarki yake sanyawa ki ga laifin mutum...

"Ɗakko... na ce ɗakko, ɗaukan hannu gareni ba ɗaukan ƙafa ba, in banda kin raina ni Sa'adiyya har ma ke faɗi in faɗa, to shikenan ɗan halak ka fasa tun da Imirana kika zaɓa daga yau ko gani na yi ya haike miki kina neman ɗauki ƙur'anin Allah ba zan kai miki ɗaukin ba, tun dai kin ce namiji ubana ne akwai ranar ƙin dillanci ranar da za ki mutu marainiya, tun da duk wannan jihadin da na yi, ki kalli hannuna na dama taɓarya, na hagu muciya duk dan in ceto ki daga ɓarakar ɗinki da kuma ciki da goyo amma saboda ke ƴar ƙundun uba ce baki gani ba" Ta faɗa tana yin jifa da taɓaryar da muciyar ta koma inda ledar kayan marmarinta ta faɗi ta ɗakko da ta ajiye, ta juya tana cewa.

"Gwara ma in je in yi abin da zai fishshe ni, na tsaya ina gwagwarmaya ba magriba gashi har ana kiran ishsha'i, kar ma in je ina nan ina ta alkinta miki mafitar ɗa (HQ) Mala'ikan ɗaukan rai ya zo, tafiya da ni, a je a binne ni in zo amsa tambayar kabari na rasa bakin magana idan an ce Azumi me yasa baki yi sallar magriba a kan lokaci ba, kin ga bani da bakin magana, sai dai in ta jejjefa ido yo ai dai ba na buɗi baki ba in cewa mala'ikan ina can ina gwawarmaya da ƙartin mazan da suka saceni, sannan na dawo gidan na shiga ƙwatoki a hannun wancan jarababben mijin naki ba"

"Sacewa kuma Inna? Ke da kika tafi gidan Hajiya waye ya saceki kuma gwagwarmayar me kika yi sannan ya ka yi Inna kika kuɓuto?"

Wani mugun kallo Inna ta jefawa Sadiya kamar ta hauta da duka, ta juya ta fice daga ɗakin ta ɗauro alwala. Sai da ta jera sallolinta ta idar sannan ta tashi tiƙis-tiƙis ta fita jimawa kaɗan sai gata da plate da wuƙa da roba me ruwa a ciki, zaunawa ta yi ta ɗakko ledar kayan marmarin take sakawa a robar tana wankewa sai da ta ɗauki iya yanda take so sannan ta buɗe frige ta sanya sauran a ciki ta shiga yankawa tana cin abinta.

Kallonta kawai Sadiya take tana mamaki ko ta yi bata mata ba kuma ta ma rasa ina ta samo wannan uban kayan marmarin tili guda.

"Meye kika tsareni da ido sai kace wata tsohuwar mayyar da ta daɗe bata ci jariri ba?" Inna da ke kallon Sadiya ta wutsiyar ido ta faɗa lokacin da take yanko wata ƙatuwar abarba ta sa a baki.

"Haba Inna wace irin magana ce wannan ni ce ma tsohuwar mayya, to idan ma ni mayyar ce ai ke ce kat"

"Yo na sani ko wajen uwarki kika yi gado" Ta faɗa hankali kwance.

"Ni uwata ciki ɗaya ce, wai dan Allah Inna ina kika samo wannan kayan?"

"Halima kenan a tarar aradu da ka mana na samo su, dan ke baki san irin sadaukarwar da na yi ba na san da Malam zai san na damƙi mazaƙutar maza har uku wallahi duk da larura ce ta sa na yi hakan da har ya bar duniya da kishi zai mutu" Cewar Inna a zuciyarta a fili kuma ta ce.

"Na faɗa miki saceni aka yi"

"Wai wace irin sata Inna, a sace ki kuma ki dawo har da kaya tili haka"


"Wallahi sace ni aka yi"

Kallonta kawai Sadiya take cike da mamaki

"Anya kuwa Inna bata fara shiriftun tsufa ba" Sadiya da ta yi niyyar faɗar maganar a zuciyarta bata san ta fito fili ba sai ji ta yi Inna ta ce.

"Bana son ƙaniyanci Halima, kar fa kaza ta tono wuƙar yankan ta fa, abin da kike min fa ya isheni tura ta kai bango aradu, ni ce nake shiriftun?"

"Allah Inna a raina na yi niyyar faɗa"

"Sai Allah ya toni asirinki ya fito min da ita fili na jita dama ai Allah ba azzalumin bawa bane"

"Yanzu dai ki yi haƙuri ki faɗa mini"

"Humm ke dai bari Halima ai yau na tsallake rijiya da baya, wallahi wani gida na je garin kallon gidan ƴan gayu wasu ɓarayi da suka zo satar wata mata muka yi arangama, aikuwa ji kike ƙiiii kamar sun samu tsohuwar motar da ta daɗe bata ga garejin gyaraba haka muka rinƙa nausawa daji kamar za mun doshi dajin sambisa, ke da na gaji dai na ga ana neman wuce gona da iri, ana neman a je a yi watanda da kaina, na yanke shawarar na fara yunƙurin ƙwatar kaina ta hanyar yin abin da ya dace" Cewar Inna tana gaftarar appale har tana lumshe idanu.

"Inna ba dai wani abin kika kwaɗa musu kika yi kisan kai kika gudo ba?" Cewar Sadiya a fili a zuciyarta kuma ta ce

"Na shiga uku kar dai tsohuwar nan ta sanyamu a uku a zo har gida a kame mu bamu ji ba bamu gani ba"

Ganin Inna tana ta dariya ko tsayawa bata yi sai Sadiya ta zuba mata ido kawai da mamaki.

"Wayyo Sa'adiyya ni na san abin da na yi yau wallahi ko ni na tuna abin da na yi sai na ji dariya da kunya sun kama ni, sai dai ranar biyan buƙata rai ba a bakin komai yake ba, yadda na ringa shaƙe ƴaƴan mutane kamar Allah ne ya aikoni wallahi, daga na damƙi wannan sai na damƙi ta wancan" Cewar Inna a zuciyarta tana ta dariya tana hango yanda samarin suka yi ta zare ido daga zarar ta ƙwamuso al'aurar su.


Nan ta kwashe labari kaf ta faɗawa Sadiya, Sadiya kwa dariya har da riƙe ciki, tana ta mamakin Inna tabbas tsohuwar ta san kan mugunta amma kuma sanin muguntar tata ya mata rana tun da ta ƙwato kanta har da tsarabar kayan marmari. Imran da tun da zai shigo ya ji Inna ta kamo labari ya dakata ya laɓe sai da ya gama ji kaf sannan ya yi sallama ya shigo yana ta danne dariyarsa dan sosai yake hango idanun samarin da Inna ra yiwa wannan ɗanyan aikin da a ce wani zai samu labarin cewar ba aljana bace ya san idan suka haɗa hanya ba lallai su barta da rai ba dan ko shi yanzu ya hasaso irin yadda zai ji jiki da a ce shi aka yiwa haka.


Haka dai aka cigaba da ZAMAN WANKAN ana karawa tsakanin Inna da Imran, har ya zamana saura kwana biyu suna, ranar ta kasance ranar laraba inda suna ya kama za a yi shi ranar juma'a dan haka ranar ana ta yiwa me jego ƙunshi da wanda suka zo daga dangin mahaifiyar Sadiya da da wasu daga cikin ƙawayenta na kusa, sai Ashrof da ƴaƴan ƙanwar Mama, Jan lalle ne ake zana musu sai kuma fulawa da ake zana musu Inna da ke gefe a zauna tana ta kallon budurwar da ta duƙufa wajen zanen fulawa kamar dama can da shi aka halicceta yadda take zanawa, Inna da ta gaji da taɓe baki ta ce.

"Kai wannan yarinya da kudura kike da shegen son kuɗi yo in banda neman kuɗi ke ɗaya da ranki amma kin kama ƙafafu sai zane su kike kamar kin samu bayan ƙwarya, ke bakya ma tsoron aljannu su tasheki tsakiyar dare su ce ki zana musu a hannu da ƙafafunsu, baki ji ba an ce kwalliyar aljannu ce, a ce ki rasa sana'ar yi sai zanen aljannu ban da ɗorawa kai jafa'i" Cewar Inna tana kallon budurwar da tun da Inna ta fara rattabo maganganunta ta dakata ta zuba mata ido cikin mamakin kalamanta.

"Kin ga Inna neman kuɗi halak ne, da a ce sata nake fa ai gwara na nemi halal ɗina, kuma da kika ce kwalliyar aljannu ce ni ban ma taɓa ji ba, kawai idan so kike a zana miki ki shiga layi idan layi ya zo kan ki in miki" Cewar budurwar dan dama da ganinta idonta a tsaitsaye yake kamar ma wata ƴar duniya-duniya.

"Allah kiyashe ni aikin da na sani, ni Azumi dan asara in zauna a zana min wannan abin me kama da jelar saniya, kakar dai wata me budurwar zuciya dan na faɗa miki gaskiya za ki nemi ki faɗa min magana to wallahi kar ki min rashin kunya kin ji na faɗa miki" Cewar Inna tana wani hayayyaƙowa yarinyar kamar ta kai mata duka.
Sadiya da ta shigo falon yanzu ta ga abin da ke faruwa dan dama kitso ake mata ta fita ta yi fitsari, ta dakatar da yarinyar tana baiwa Inna haƙuri dan a zauna lafiya duk da ta san Inna ce bata da gaskiya amma haka ta ɗan yiwa yarinyar signa a kan ta ja bakinta ta yi shiru.

"Faɗa mata dai ku da kuka san darajar mutane, me zan yi da wannan zanen fulawar ban da ma toshewar basira a zana maka ka je ka mutu da shi a kai ka kabari mala'iku su kankare maka da dutsin wuta, gwara in yi da lalle na asali tun na iyaye da kakanni, saboda gudun matsala ma da kayana na taho daga garinmu yana cikin jaka lalle me kamu idan ka ƙunsa ka ga ƙafafunka babu banbanci da ƙafar ba'indiyar da aka yiwa ƙunshi, , sai gobe zan ƙunsa kayana, na san aminiyata Tsahare ma shi za ta ƙunso in ta tashi ziwa suna.Bari ma dai na tashi na je na yi sallar azzahar dan na ga ku wannan abin ma kafin ya kama ku cire sai dai ku harhaɗa sallolin haka kawai ko tsoron Allah bakwa yi" Cewar Inna ta tashi.

Me ƙunshin ce ta raka bayan Inna da wata uwar harara tana murguɗa baki ba tare da kowa ya lura da hakan ba, ji take kamar ta yi ta dukan tsohuwar nan me shegen rangwangwan da shiga shari ba shanu. Ji take da a ce za ta samu dama babu dalilin da zai sa ta rama cin mutuncin da Inna ta yiwa sana'arta.

Kowa dai bai furta komai ba, dan gudun Sadiya da Ashrof kar su ji haushi, a haka aka cigaba da zana musu ƙunshi ja da baƙi.

Inna kuwa tana fita ta nufi bayi ta yi tsarkinta ta fito ta fara ɗaura alwala. Ƴan falo ana ta hira kowa yana tofa albarkacin bakinsa, Hassan da Husaini kuwa Sadiya ta ajiyesu a bedroom saboda bacci suke kuma bata son hayaniya ta tashe su. Lokacin da Sadiya ta fita za ta jefar da gashin danya fita daga kanta da aka mata kitso, kawai ƴan falo sai ganin miciji suka yi ya fito zulululuu daga cikin ɗaki, gabaɗaya aka shiga gudun famfalaƙi kowa yana neman ceton rai haba wa Inna da ke zaune tana alwala lokacin tana wanke fuska sai ganin mutanen falo ta yi suna fitowa kamar ana korosu kowa yana kama gabansa, da mamaki ta dakata da alwalar da take tana so ta gano abin da ya sanya su wannan gudun. Sadiya da ta juyo daga wajen bola ta hango mutane kowa a ruɗe, Ashrof da ta yi wajen bayi ce kaɗai ta iya nuna mata hanyar falo da hannu alamar akwai wani abu tana nuna mata kwa ta yi wuff ta faɗa bayi ji kake gararaf ta banko ƙofa, ta jingina da ƙofar daga cikin bayin.

Inna ta kasa gane dalilin da ya sa ake tseran ta buɗe baki za ta fara sababin nata ba sai hango miciji ta yi ba ya fito daga falo, idanu ta zaro a kiɗime ta tashi daga kujerar da ta zauna take yin alwala, ji kake gwaraf ta bi ta kan butar alwala tana kama zaninta da ke neman faɗuwa, mamaki take duk sawayar da Hassan ke yi

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login