Showing 39001 words to 42000 words out of 56867 words

Chapter 14 - YAR ZAMAN WANKA BOOK 3

27 Sep 2024

3841

haɗe a goma da shirin saboda ya shaida Abid kuma bai manta da kuɗaɗe da kayayyakin da ya karɓa a wajensu ba kuma dai ƙarshe ba biyan buƙata dan dama ba wai ya iya ruƙiyyar bane kwai lalume yake a cikin duhu.

Yanzu dai burinsa bai wuce Inna ta sallame shi ba ya kama gabansa.

"Kai Imirana ka iya bakin ka da Azumi kake magana kura mai ban tsoro amma ba tsoro" Ta faɗa tana gatsinen gefen hanci. Wani takaici ne ya rufe Imran dan haka raɓawa kawai ya yi ta gefensu ya bar su da Abid.

" Abida yaushe rabonka da gidan nan tin lokacin da ka zo na baka labarin Sojojo ranar da ka kawo min abin arziƙin nan kai wannan yaro Allah maka albarka ba zan taɓa mantawa da abin arziƙin da ka mini ba, amma dai kuma ina ta jiranka ka zo ka sha labari labarai har sun gaji da taruwa" Ta faɗa tana kallon Malam da ya sunkuyar da kansa ƙasa tare da Ƙasimu da ya masa wani ɗogogo a baya.

"Ai ina nan Inna abubuwa ne suke shan gabana amma da tuni na zo kin ɗora min daga inda kika tsaya"

"Kai dai bari Abida
ai labari kala-kala, mutuminka fa ranar nan har da shiga tukunyar da nake dafa ruwan wankan jego" Cewar Inna tana ɗan rage murya take magana raɗa-raɗa ƙasa-ƙasa.

"Tukunya Inna?" Cewar Abid shi ma yana rage muryar dariya na cinsa dan har ya hango Imran a cikin tukunya.

"Tukunya mana, yo ba ƙwara shiga tukunya ba wallahi ranar nan idona idonsa yadda na ga Imirana da Rakiya Allah nuna min annabi S.A.W, wallahi rungumar juna suka yi saboda ruɗewa, yo kai ka taɓa jin wannan sabga aiki ɗanye sharaf siriki ya ƙaƙumi sirika" Inna ta faɗa tana ɗan waiwaya bayanta tana dariya ciki-ciki.

Dariya kawai Abid yake sosai yake hangowa kamar a gabansa komai ya gudana.

"Jeka ciki ina zuwa in sallami wannan Mololon dan ba malami bane, in zo" Ta faɗa tana jan wuyan Malam ƙiii shi kuma ya cigaba da hamimiyarsa da kallo kawai Abid ya bi su yana jinjinawa tsohuwar dan shi har ga Allah ba ya ganin laifin Inna komai tana yi a kan gaskiyarta ne kuma da hujja.

Inna kwa ko a jikinta wai an tsikari kakkausa haka ta ja Malam suka je bakin ƙofa, ta sanya Ƙasimu ya sauka ta nuna masa hanyar da zai yi haka ya fita a guje ko takalmi babu kamar yadda Habu ya tafi ya rage daga Inna sai Malam.

"Kai kuma daga nan har in daina hangoka da rarrafe za ka fita" Cewar Inna tana haɗe rai tare da kama tsantsa.

"Dan Allah ki rufa min asiri kamar yadda Allah ya rufa miki, dan Allah yanzu na fita da rarrafe gabaɗaya mutuncina zubewa zai yi kuma shikenan bare ga wandon nan nawa jagaf da shi da Allah ki taimaka mini" Cewar Malam yana durƙushe a kan gwaiwoyinsa.
Shiru ta ɗan yi tana kallonsa tare da taɓe baki ta ce

"To shikenan ka tafi da ƙafarka"

"Nagode Malama Inna Allah ja da kwananki ki daɗe ki yi ƙarko" Ya faɗa yana miƙewa tsaye dakyar dan gabaɗaya ƙafafunsa sun yi sanyi ga dila ma ya kama masa ƙafafu amma haka ya daure ya tashin yana raba idanu gashi ko takalmi bai ɗakko ba yana cikin gidan.

Ya juya yana taka ƙafar dakyar Inna ta rafka masa wani uban kira da yasa gabansa bugawa da mugun ƙarfi, yana fatan ba cewa za ta yi ya dawo gidan ba, in kuwa haka ne ba zai yarda ya koma ba da gudu zai zuba sai dai in an kamo shi a yanka shi.

"Addu'ar fa" Maganar Inna ta katse masa tunaninsa.

"Kai wannan tsohuwa da masifa take wato dan jaraba bata manta ba, bayan ni yanzu komai ma na manta a kan nan nawa bare har in tuna da cewa wai na ce zan basu addu,a" Cewar Malam a zuciyarsa.

"Cewa na yi addu'ar da ka ce za ka bayar wacce za a yi taro lafiya a gama lafiya, duk da ka ce ba sai an tuna maka ba amma dai na ga kana ƙoƙarin tafiya, babu niyya ango ya kwana da wando" Cewar Inna tana kallon Malam da kunya ta gama rufe shi.

" Da ku na cikin gidan, da duk wanda zai zo suna, ku karanta Qulhuwallahu ƙafa uku bayan kun gama sai ku ce Allah raba mu da mugun ji da mugun gani" Cewar Malam a fili a ransa kuma ya ce

"Ba dole in ce ku nemi tsari da mugun gani ba dan wannan micijin ai ganinsa kaɗai tashin hankali ne"

"Haka za mu karanta to bari na mayar da kai ɗakin ku kwana da mugun ganin mu gani" Cewar Inna tana kallon Malam da har lokacin, carbunansa da hiraminsa suna wuyansa amma ba ta su yake ba, wannan magana da Inna ta yi ta, za ta maida shi ɗakin micijin nan ta sanya hankalinsa ya tashi dan haka ya yankewa kansa shawarar zabgawa a guje dan ya tsira da ransa. Kafin ƙiftawar ido Inna sai gani ta yi ya tattare babbar rigarsa gudun hantsilwa idan yana gudu ya zangaya a guje.

" Ka manta takalmanka da na almajiranka, da hular mai kayan aikinku da galan ɗin ruwan addu'arku, kuma baka karɓi kuɗin aikinka ba da sauran kayan aikin da ka ce za a baka" Cewar Inna da ta daddage tana faɗa masa.

"Na bar muku duka halal malak" Ya faɗa da ƙarfi har lokacin yana zabga gudu ko waiwaye ba ya yi gudun kar a samu matsala Inna ta biyo shi ta mayar da shi ɗakin miciji. Daga Inda Inna take tsaye daga ƙofar gidan da ta fito tana hango yadda ya sha wata uwar kwana a sukwane ko lanƙwasa babu.

Dariya Inna ta yi idanunta a kan motar Abid ta juyo ta dawo ciki tana ƙoƙarin rufe ƙofar sai gasu sun fito Imran da Abid.

"Innna har ya tafi baƙon naki?" Cewar Abid yana maida dariyarsa.

" Ya tafi mana amma dai ba baƙona bane baƙon Hassan ne kuma ya sallame su dan kuwa sun sha baƙar azaba kwakwa dai yau an sha ta a wajen miciji" Ta faɗa tana washe baki.

"Na gane Inna" Ya faɗa yana daria.

"Ba dai tafiya za ka yi ba?" Cewar Inna da mamaki.

"Ba tafiya zan yi ba kaya za mu ɗakko a mota kin san kayan rabawa ne gobe muka siyo"

"Ikon Allah wato ka ji kaɗan ka ji da yawa, yanzu baƙin halin Imirana har ya kai haka, a ce zai tafi siyayyar amma ina garin nan muna gida ɗaya ɗaki ɗaya amma ya kasa gayyata ta na raka shi sai ya je ya ɗakko ka".

Wani kallo Imran ya jefa mata irin na kina kai kan ki inda Allah bai kai ki ba, kafin ya raɓa ta ya wuce wurin motar.

"Au Allah wato ina maganar ma ka wuce ka bar ni wato ga karya yo in ba karya ba waye ake bari yana haushi shi kaɗai" Cewar Inna tana bin bayan Imran da harara.

"Rabu da shi Inna ba gani ba zan tsaya mu yi hira abin mu kuma kwantar da hankalinki indai kina nan to kuwa kafin ki tafi xan kai ki yawo a mota ta mu yi siyayya ki zaɓo abin da kike so in biya kuɗin" Cewar Abid yana kallon yadda fuskar Inna ta saki lokaci guda kamar an mata albishir da gidan aljanna.

"Allah Abida ka ce akwai zaɓar abubuwa masu yawa to aikuwa har sa kishiya kuka da sa kishiya tagumi zan ɗakko a wurin siyayyar"

Galala Abid ya yi jin furucin Inna dan shi dai ya ji ana cewa sa kishiya kuka ko tagumi maganin mata ne amma kuma mai Inna za ta yi da maganin mata.

"Inna sa kishiya kuka da tagumi za ki ɗauka in mun je siyayya...

"Oh Abida rufani ka saya ni, dan Allah kuke bari sai mutane sun mutu kafin ku binne su.

, yo in ba fallasa auren bashi ba har na tsaya yin maganar maganin banza da kai(Maganin mata) Magano na ce magano, to indai abin da ka yi zato to Allah tsari gatari da saran shuka, to ni ina nufin kayan ƙwalam wato kayan ciye-ciyen ne zan ɗakko sa kishiya kuka da tagumi, abubuwa ne zan ɗakko masu daɗi wanda ba za su lalace ba har lokacin da zan gama ZAMAN WANKANA in tafi da kayana gidan Malam sai in ke ɗakkowa ina ci ina jefar da takardar ko ledar yadda Tasalla da ta gani za take rafka uban tagumi da hannu bibbiyu, idan ta shige ɗaki kuma ta yi ta rusar kuka saboda baƙinciki, shi na ce zan ɗakko kar ka kai ni inda Allah bai kai ni ba ka sa ni a bakin duniya" Ta kai ƙarshen maganar tana kallo Abid da ke ta faman dariyar maganar ta.

"Na gane manufarki Inna, sai Inna ta mu ta Malam bada kan ki a sare ki je gida ki ce ya faɗi"

"Rass kuwa Abida ai ni ce ɗaya tamkar da miliyan a wajen Malam, kuma wallahi da ka ce Inna tamu sai ka sani wata ƴar bazawarar dariya dan ka tina min da daren jiya" Cewar Inna tana ƴar dariya tana kallon Imran ta gefen ido dama ganin ya kwaso kaya a mota ya taho ta faɗa.

"Mai kuma ya faru daren jiya Inna?" Cewar Abid yana dariyar shi ma

"Hummm kai dai bari Abida wallahi daren jiya ne abokin ka Imirana ya shiga wani hali na a zo a gani, sai ji ka yi Imirana yana, Innarmu, Inna ta" Ta faɗa tana sakin dariya irin mai ƙular da mutum ganin Imran ya zo wajensu zai fice, wani irin haɗe rai ya yi tare da wurga musu wata uwar harara. Abid kwa kawai dariya yake dan har ya hango abokinsa tabbas ya san Imran ba ƙaramar wuya ce za ta sa ya ce Innarsa ba.

"Hehehehe na dawo in ji ɗan yawon duniya, to wallahi ban san ana yi ba kunu a maƙota, kuma ban san harara ba sai ido ya faɗo ehe" Cewar Inna tana jefawa Imran hararar ita ma har da gatsi ne.

"Ƙyaleshi Inna" Cewar Abid dariya har kasa magana yake.

"Yo dama ai ba biya shi zan yi ba da ina biya Imirana ai da zamana a gidan nan bai kawo yanzu ba, ni kuwa na faɗa masa zama daram, kuma nan gani nan bari farar tunfafiya, labari kwa dole na bayar tun da ya yi abin da za a faɗa dan labari sai ma na koma ƙauyenmu in samu abin da za mu ke maimaitawa ni da aminiyata Tsahare muna darawa yo labarin abubuwan da Imirana ya yi daga zuwana zuwa yau ai abin a bayar da labari ne, dan ba tsoronsa nake ba, bada labari kuwa farillah ne tusa a masallaci, dan wallahi ina sane wai karuwa ta taka matar aure, dan kuwa ni na san karambanin akuya yasa ta leƙa ɗakin kura" Ta kai ƙarshen maganar tana wani juya ido tare da gatsine kamar wata matashiyar budurwa.

Abid kawai dariya yake a haka ya je ya buɗe motar ya ɗakko wasu kayan da wata leda mai ɗauke da apple mai yawa fari da kore ya miƙawa Inna, ta karɓa tana ta godiya kamar ta ari baki, a haka suka baro zauren dan dama a can ne tun da ya same ta za ta rufe ƙofa suka tsaya suke maganar. Ko da suka dawo ma haka ta zauna tana ta baiwa Abid labari dan haka kuwa ya zauna yana ta dariya har da riƙe ciki, amma kuwa saboda soyayya da kuma kyautatawar da Abid ke mata, Inna bata bari Abid ya ga miciji ba, dan ƙofar ma ta kulle bayan ta maida Hassan ɗin kan gadonsa dan kar Abid ya gani ya firgita dama hausawa sun ce zuciya na son mai kyautata mata.

Bayan tafiyar Abid Inna ta buɗe jakar kayanta ta ɗakko wani abu ta saka a cikin ɗan tofinta (Siket da tsofaffi suke sakawa daga ciki wand ake ɗinka musu har da aljihu a jiki) Bayan ta sanya a aljihun ɗan tofin nata ta cewa Sadiya za ta fita ta ɗan zaga ƙafarta dan ita ta gaji da zama wuri ɗaya, Sadiya kwa ta ce a dawo lafiya dan ita ma so take Innar ta fita saboda ko kaɗan in tana gidan sai an samu wani akasin. Baki ta taɓe ta ɗauki mayafinta ta yafa sannan ta ɗauki goro guda ɗaya take ci abinta ta fita. Tun da ta fito hanyar da Malam Isuhu ya bi ta nan ta bi tana yi tana kallon sawun ƙafarsa da ya yi ta sheƙa gudu ɗazu dan sawun har wani nitsewa yake a cikin ƙasa saboda yadda ake taka shi da ƙarfi, kalla kawai ta yi tana dariya wai mai sittin wata kan wata sai gashi ko izifi ɗaya bai karanta ba a ɗakin Hassan. Tafiya take abinta hankali kwance, tana cikin tafiyar, wata mota mai baƙin gilashi da wasu ke ciki suna kallon hoto a waya ɗayan ya kalli ɗayan ya ce

"Ita ce"

Aikuwa da uban gudu motar nan ta sha gaban Inna dama wajen duk ba mutane Inna da ta tsaya kallon ikon Allah ganin mota ta sha gabanta kafin ta gama tunani sai gani ta yi an fito daga ciki an fisgeta an shiga da ita motar an banke ƙofa an kwasa da uban gudu...


Masu fitar min littafi ki sani haƙƙina ne, dan haka ke ma da kike karantawa haƙƙina ne kuma baki biya ni ba.



09030283375
[24/03, 5:14 AM] Mom Mashkur First class: *MAMAN AFRAH DATA SERVICES*

*BUY DATA FROM THE AFFORDABLE PRICE*

*I selling MTN data with this cheap price*

*MTN DATA PACKAGE*
500MB@===150
1GB@=====250
2GB@=====500
3GB@====850
5GB@====1,400

Dial *312*4*7*4# to check Data balance.
*Validity 1 month*

*Airtel,9mobile and Glo* *also available.*
*Subscription for DStv gotv star time electric pay bills*

Act details FA'IZA ABUBAKAR unity bank 0020281885
Whatsapp OR
Call 09033283375




Wannan littafin kuɗi ne 300
Za a tura ta wannan accaunt ɗin Fa'iza Abubakar 0020281885 Unity bank shaidar biya ta wannan no 09030283375 idan katin waya ne mtn Ƴan Niger su tuntuɓi wannan no +22785885134



3️ 4️⃣5️⃣➡️4️⃣6️⃣


Tun da suka saka ta a mota ta fara wurwurga idanu, mutum huɗu ne a cikin motar gabaɗaya suna sanye da kayan sojoji, ɗaya yana jan motar shi kaɗai ne bashi da kayan sojoji. Mutum biyu ne suka sanya Inna a tsakiya kallonsu take tana so ta ga ko ta taɓa ganin wani, amma babu wanda ta gane, baki ta buɗe za ta yi magana amma ɗayan ya ɗaga bindiga ya ɗora mata a kan ta hakan ne ya sanya Inna ta ja bakinta ta yi shiru dan duk abin ta bata wasa da rai da lafiyarta.

Gum ta yi da bakinta bata sake yinƙurin yin magana ba su ma kuma duk cikinsu tun da ta shigo motar bata ji wani daga cikinsu ya yi magana ba.

Wata unguwa suka nufa da babu hayaniya sosai a ƙofar wani get suka tsaya horn aka yi mai gadi ya zo ya buɗe ƙofar suka shiga ciki Inna kuwa sai rarraba ido take yi dan ta kasa gane dalilin da ya sa aka ɗakko ta. Tunani ta fara yi ko ƴan yankan kai ne suka ɗakkota, duk da dai ta gansu da kakin soja a jikinsu amma hakan ba zai hana ta zargesu ba saboda yanzu ƴan bindiga suna kashe sojoji su ɗauke kayansu suke sanyawa, dan dai ta san wancan karon da aka ɗakko ta daga gidan masu kuɗin wannan jeji aka nufa da ita saɓanin yau kuma da aka nufo cikin gari kuma ƙeraren gida na gani na faɗa.

Haka dai ta daure saboda bakin bindigar da ke kanta. Suna fitowa ita ma haka ta bi ayari ta fito bisa bin umarnin da aka bata, tun da suka fara tafiya zuwa ainihin cikin gidan take ta kalle -kalle har suka samu nasarar shiga cikin wani falo madaidaici mai shegen kyau. Su duka wuri suka samu suka ƙame babu wanda ya nemi wurin zama Inna kuwa ganin tsayuwar ba za ta mata ba sai ta zauna a ƙasan kafet gudun kar ta hau kujera a harbeta.

Suna nan, sai ga wata yarinya ta fito cikin wasu ƙananan kaya tana riƙe da abin wasanta, Tun da ta fito Inna ta ƙura mata ido tana mata kallon sani sai dai ta kasa tuna inda ta san yarinyar tana ta kiciniya da ƙwalƙwalwarta a kan ta barta ta tuna ina ta san yarinyar amma kafin hakan sai ganin mutum ta yi ya fito daga cikin wani ɗaki shi ma sanye da kaya amma ba na sojoji ba. Kallo ɗaya Inna ta masa ta gane shi a take ta tuna da inda ta san yarinyar ma.

"Sojojo kai ne dama nan gidan ka ne ina tsohuwar matarka mai shegen tsoron nan kamar farar kura, ko da yake ma ba ita kaɗai ce matsoraciyar ba har da...

Wata uwar tsawa da ya daka mata ita ce ta hana Inna da ta washe baki tana ta kauɗi da karaɗi ƙarasa maganar, dan tun kan ya ƙaraso ma tsakiyar falon ta fara zuba.

Cikin ɓacin rai ya ƙaraso tsakiyar falon gabaɗaya suka shiga sara masa kujera ya nema ya zauna har lokacin ransa a matuƙar ɓace yana aikawa Inna wani mugun kallo. Ƴar tasa ce ta zauna a kusa da shi tana ta raɓewa a jikinsa da alama dai bata manta da inda ta ga Inna ba.

"Ke inyamura ina uwaki take, yo ina so in miki magana amma na san bakya jin hausa, ina so in ce ki kira min uwaki tsohuwa mu gaisa ko yau ma tana can tana kwalliyar tana shafa jambaki kamar akuya ta ci dusa sai...

Ɗaya daga cikinsu ne ya ƙara yiwa Inna tsawar da ta sanya ta yi shiru sai dai yanzu tun da ta ga abokin Imran gaba yake da su, wato ogansu ne sai ta ji duk bata tsoronsu dan ta san dai duk tsiya ba lallai su harbe ta

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login