Showing 48001 words to 51000 words out of 56867 words

Chapter 17 - YAR ZAMAN WANKA BOOK 3

27 Sep 2024

3845

sallama, Allah sarki ni Azumi ko wasiyya ban bayar ba, shikenan sai tafiya mutuwa haka take zuwa shi ma tashin ƙiyama an ce haka zai zo bagatatan" Cewar Inna tana runtse idanunta hawaye na kwaranya.

"Saura sati biyu ne ashe ba yau bane dan haka ki rufe idanunki sai kin daɗe sannan za ki buɗe" Ya katse wa Inna zancen zucin ta.

"Allah na gode maka ai har na bayar sa wasiyya in nemi yafiyar jama'a" Cewar Inna a zuciyarta.

"Kuma ba a baiwa kowa labari ki ja bakin ki ki yi shiru".

"Bakina ƙanin ƙafata" Cewar Inna cikin rawar murya.

Ai Inna da ta rufe idanunta gam, ko alamar ɗagawa bata yi ba, har Imran ya lallaɓa ya tsugunna ya fice daga ɗakin da rarrafe amma Inna ko fitarsa bata ji ba. Har lokacin gabanta bai daina faɗuwa ba jikinta kuma bai bar karkarwa ba, sai da ta kwashe tsawon awa guda sannan ta miƙa hannunta na dama ta taɓo hancinta jin iska na fita daga hancin ta tabbatar bata mutu ba a hankali ta shiga buɗe idanunta cike da tsoro tana so ta tashi Sadiya ta faɗa mata sai dai tana tsoro kuma an ce kar ta faɗawa kowa.

*IMRAN*

Tun da ya fito daga ɗakin ya dawo falo ya cire kayan ya maida wanda ya cire ya sanya su a ledarsu ya mayar ƙasan kujera ya ajiye yana so da asuba sai ya fice da su in zashi masallaci. Tun da ya kwanta yake ta dariya ƙasa-ƙasa ba abin da je bashi dariya irin yadda idanun Inna suka yi ƙulu-ƙulu ita ala dole za ta mutu, ga karkarwar da jikinta ke yi kamar mazari shi kaɗai ya isa ya sanya cikinka ya yi ciwo saboda dariya.

"Ko a ina ta taɓa jin mala'ikan mutuwa yana manta wa'adin mutum har ya zo ɗaukan ran mutum amma kuma ya fasa ya ce sai wani lokacin, har ya faɗa maka lokacin ka.

"Kai ruɗani bai yi ba wallahi" Ya faɗa yana ƙyalƙyala dariya a ɓoye.

Tun da ta buɗe idon nata ta ji wani fitsari ya cika mata mara, ga tsoro da fargaba duk sun tarar mata sai kuma karkarwar da take. Jin fitsarin na neman zubowa ta ƙoƙarta ta tashi zaune ta fara kiciniyar sakkowa daga kan gadon saboda gabaɗaya bata gama dawo wa dai dai ba. Da dibara ta sakko daga gadon amma ko ta kan ƙunshin ƙafarta bata bi ba dama tun lokacin da Imran ya ja ƙafarta ta haɗe ƙafafun waje ɗaya duk ta caɓe lallen amma ba ta shi take ba, ita dai yanzu burinta ta yi fitsarin. Haka ta tako da ƙafafunta tana jin yadda lallan ke mata santsi a ƙafarta duk ta take shi lallan da ta ci uban buri a kan sa za ta yi ƙunshin fita kunya da suna, lallan da ta taho da shi tun daga garinsu amma kuma gashi za ta ɓata shi a banza, lallan da ta yiwa mai ƙunshin nan kuri cewa ya fi wanda take ƙunsawa su Ashrof kyau amma sai gashi abu ya zo mata a hautsine, dan tun da ta ga mala'ikam mutuwa ya zo ɗaukan ranta duk da bai ɗaukan ba, sai ta ji duniyar ta fice mata a rai komai na duniyar ya ginshe ta. A haka ta taho ko fitilar ɗakin bata kunna ba saboda tana ƙiyasta, da an ɗauki ranta da gobe da safe za a sanya ta a kabari duhun kabari kuwa ya fi na duniya sai dai fatan Allah rabamu da shi.

Haka ta fito tana taka ƙafarta dakyar dan duk ta yi sanyi, ko kallon inda Imran yake kwance bata yi ba ta zo ta wuce, shi kuwa yana kallonta har wani ɗan doro ta yi. Inna kuwa ko takalmi bata tsaya sakawa ba dama ga ledar lallan a ƙafar sai kawai ta tafi bayin a haka tana gama fitsarin ta yi tsarki ta fito, ledar lallan ta fusge ta watsar ta ƙarasa ta kunna famfo ta wanke ƙafar bata damu da ganin ko ya kama ƙunshin nata ba ko kuma ganin ya caɓe ita ba wannan ne a gabanta ba ita da za ta bar duniyar ma baki ɗaya nan da sati biyu to menene na damuwa da ƙafar da ta kusa komawa cikin ƙasa.Imran yana kallonta ta dawo ta shige ɗaki abinta jim kaɗan sai ya ganta ta kunna fitilar wayarta ta fito ɗauke da bargonta tana sanɗa, haka ta zo ta cikuikuya bargon ta saka a jakarta ta ɗakko sallayarta da hijabi a kan kujera su ma ta cusa su a ciki ta ɗakko mayafinta a kan kujera ta cusa ta ɗakko takalminta a ƙofar ɗaki ta cusa ta zige jakar. Duk abin da take Imran na kallonta kuma ya fahimci mai take shirin yi.
Sai da ta gama ta janyo jakarta a hankali.

"Wallahi guduwa zan yi daga gidan nan, na fasa ZAMAN WANKAN ƙwara in koma in mutu a ɗakina, na gwammace mutuwa ta ɗauke ni a ɗakin mijina a kan ta ɗauke ni a wani waje da ban, ƙwara in koma gida in roƙi yafiyar Malam dan dama ina zargin kamar ba da zuciya ɗaya ya barni na taho ba, dan tun da na zo birnin nan abubuwa suke faruwa da ni daga wannan sai wancan" Cewar Inna a zuciyarta tana sanya hannu ta share hawaye duk Imran yana kallonta. Sai da ta kai jakar ƙofar ɗaki ta dawo ta shige bedroom yana kallonta tana haske -haske a ɗakin da alama Sadiya da su Hassan take yiwa kallon ban kwana.

"Sa'adiyya ki yafe min na zo gidanki na hana ki sakat da sakewa da mijinki yau zan bar muku gidan ma baki ɗaya ko ma mai zai yi Imiranan ya je ya yi in ma kin samu wani cikin kin yi ciki da goyo Allah ne ya baki, kuma shi zai taya ki riƙonsu domin Allah ba ya ɗorawa bawa abin da ba zai iya ba Allah raya miki tagwayenki da ma wanda za su zo nan gaba na san wannan ne haɗuwarmu ta ƙarshe sai kuma in kin je jana'iza ta, ba zan iya tashinki daga bacci ba ki hana ni tafiya guduwa zan yi in ya so in kwana a tashar mota da asuba in samu mota in tafi gida. Kai ma Hassan ka yafe min saboda na maidaka abin zolayata kowa ya yafe min sai wata rana" Cewar Inna a hankali yadda ba za ta tashi Sadiya ba.

Duk abin da take faɗa Imran ya kasa kunne yana jiyo wa, sai da ta gama sai gata ta fito ta zo saitin katifarsa ta tsaya.

"To Imirana abokin karawata ka yafe min na tafi na bar maka gidanka da iyalinka Allah baku zama lafiya ya kaɗe fitina, in an samu labarin mutuwata nan da sati biyu a je jana'iza a min addu'ar samun dacewa mu tamu ta ƙare za mu tafi inda Baban Halima da su uwata mai daddawa da mai barkono suka tafi" Ta faɗa muryarta na karkarwa tare da juyawa ta nufi ƙofar ɗaki inda jakarta take duk Imran na ganinta.


Jakar tata ta kinkima dakyar ta ɗora a kan ta, sosai abin ya baiwa Imran dariya haka ta fara tafiya dakyar ga sanyin jikinta ga nauyin jakarta ga hawaye yana zuba ta nufi zauren ƙofar gida.

"Ai yadda kika hana ni tafiya lokacin da na tsinci kaina cikin tashin hankali zan bi Hajiyata haka ke ma za ki dawo ki zauna" Cewar Imran ya tashi da sauri ya kunna fitilar falo da ta tsakar gida, Inna da ta kama jamlock ta cire ta fara buɗe a hankali, ta ga hasken fitilar ya mamaye tsakar gidan, da sauri ta fasa buɗe ƙofar dan kar a ganta ta dakata dan ta sa wataƙila Imran ne ya tashi fitsari ƙwara idan ya koma ya kwanta bacci ya ɗauke shi sai ta tafi. Imran fitowa ya yi ya fara sa takalmi Inna tana jinsa, ƙofar da ta cirewa jamlock ta ja ta bata gama buɗewa ba ce ta yi ƙara.

"Shikenan Imirana zai ganni" Ta faɗa a zuciyarta.

"Waye a nan? Waye a zaure?" Cewar Imran cikin maida muryarsa irin ta masu bacci ya nufi zauren.

"To Imirana an falka" Cewar Inna tana wayancewa.

"Inna lafiya ina zaki da daren nan?" Cewar Imran yana haske Inna da fitilar wayarsa da ya fito da ita, ganinta ya yi ta yi hirim da uwar jaka a ka, wata dariya ce ta kusa kufce masa amma sai ya maje.

"Kai dai bari Imirana wai da yau kwanan tashar mota zan yi saboda murna"

"Murna kuma?"

"Eh mana murnar tarɓar aminiyata Tsahare shi ne zan je in kwana a tashar in jira zuwanta gobe dan na san da wuri za ta taho, sai mu taho tare duk da ta san gidan dan kar ta yi ɓatan kai"

"Kuma da tsohon daren nan sannan kuma har da jakarki za ki je taryen nata?"

"Eh, eh, eh mana"

"A'a Inna ki dai bari sai gobe kya je" Ya faɗa yana ƙarasawa ya rufe ƙofar ya maida jamlock ɗin, yana yaƙi da bakinsa kar ya kunya ta shi ta hanyar dariya dan gabaɗaya Inna tana cikin yanayin da dole sai ka yi dariya.

"Haba Imirana ya da haka kuma, ya za ka shiga tsakani na da burina, za ka shiga tsakani na da tuba na, ya za ka shiga tsakani na da mutuwa a ɗakin mijina" Cewar Inna a zuciyarta tana jin kamar ta saki kuka ko ta samu sassauci.

"Ai fita cikin dare haɗari ne ga karnuka gashi baki san da wa za ki haɗu ba a hanya duniyar nan da ta ƙi daɗi ki je ma masu yankan kai su ɗauke ki su yi watanda da namanki" Cewar Imran yana kallon Inna da ta turɓune fuska.

"To, to, to, to" Cewar Inna a fili da ke ta furta to, har babu adadi dan ji take kawai Imran ya gama da ita.
"Ko ban samu masu yin watanda da namana ba ai sha huɗun rana i ta yau na daɗe a ƙiyama, un ma gudun mutuwa ake" Ta faɗa a zuciyarta.

"Yawwa ko ke fa, kawo jakar taki" Cewar Imran yana miƙa hannu ya saukewa Inna jakar daga kanta. Haka ta barshi ya sauke jakar ba dan ta so ba haka ya juyo cikin gidan da jakar a hannunsa tana jin kamar ta juya ta buɗe ƙofar ta gudu ta bar masa jakar.

"Shiga gaba mana Inna ai kamar ba girmamawa in barki a baya" Cewar Imran yana matsawa gefe Inna ta wuce gaba ba dan ranta ya so ba, sai dan babu yadda za ta yi kuma ma bata son yin hayaniya dan tana ganin kwananta ya kusa ƙarewa bata da lokacin ɓatawa.

Haka ta shige falon jiki sanyi ƙalau. Imran kuwa sai da ya tsaya ya ɗan matse dariyarsa sannan ya shigo ɗauke da jakar Inna ya ajiyeta a inda take ajiyewa. Kallonta ya yi ya ga ta zauna a ƙasa ta rafka uban tagumi.

"To Inna ya ga kujera kuma za ki zauna a ƙasa?"

"Yo ai da na ga ƙarshen alewa ƙasa"

"Kamar ya Inna?"

"Yo duk mai rai mamaci ne kuma dai da ƙasa aka halicce mu kuma cikinta za mu koma sannan daga cikinta za a ƙara fito damu" Cewar Inna tana tuna nan da kwana goma sha huɗu tana cikin ƙasa hakan ya sanya ta share hawayenta tana jin bata da wani abu da ya wuce ta cigaba da kusanta kan ta ga Allah har ranar da mutuwarta za ta riske ta.


" To Inna ai kowa ya san da hakan amma ai manzo S.A.W ya ce, ka zauna a cikin duniya kamar matafiyi, sai hakan hakan ba yana nufin ka bar komai na jin daɗin duniyar ba" Ya faɗa yana kallonta sai ya ji duk tausayinta ya kama shi.

"To haka ne Allah dai ya sa mutuwa ta zame mana hutu, Allah sa mala'ika mutuwa ya zare ranmu a hankali, Allah raba mu da duhun kabari, azabar kabari nauyin ƙasa ya bamu ikon amsa tambayoyin kabari ya sanya aljanna maɗaukakiya ta zame mana makoma kuma madawwama" Cewar Inna cikin sanyin murya.

"Amin dan alfarmar annabi da alqur:ani" Cewar Imran yana neman wuri ya zauna a kan katifarsa.

"Amma Inna ki tashi ki koma ki kwanta mana tun da yanzu fa dare ne"

"Ina ni ina runtsawa Imirana ai sai dai ko na tashi na rinƙa nafilfili har asuba ta yi sallar asuba sai na zauna lazimi har garin Allah ya waye"

"To ikon Allah abu mai kyau gaskiya hakan ma ya yi Inna Allah dai ya ja da kwana ya sa ki yi tsawon rai dan ki yi ibada mai yawa"

"Kayya Imirana ni da wa'adina ya kusa cika ina zancen dogon kwana sai dai a ce Allah sa mu cika da kalmar shahada"

"Wa'adinki ya kusa Inna ta yaya aka yi kika sani kuma?"

"Uhmm da wasa nake kasan ɗan adam ana so ko yaushe ya kasance cikin shirin tafiya, in ya wayi gari ya sanya a ransa ba zai kai yammaci ba in ya kai yammaci ya sa a ransa ba zai wayi gari ba haka ne kawai ya sa na faɗi hakan" Cewar Inna cikin wayincewa dan ta ga ta kusa yin ɓaran ɓarama sai kuma ta tuna mala'ikan ya gargaɗeta.

"Eh kuma fa haka ne"

"Bata sake tanka masa ba ta fita ta ɗauro alwala dan bata so ma zuciyarta ta cigaba da kissima mata dalilin sakkowar Imran har yana biya ta suna magana yana kuma nuna mata kulawa da tausayawa, ga sakin fuska, dan ita yanzu ta kanta take bata ma so ta fara tunanin wani abu ita da za ta bar duniyar ma dan me za ta damu kanta. Haka ta zo ta wuce ta ɗauki sallayarta da hijab a jakar ta nufi ɗaki.

"A sanya mu a addu'a Inna " Cewar Imran yana dariyar zuci.

"To Imirana" Cewar Inna a fili a zuciyarta kuma ta ce.

"Yo ni ina ma na ga lokacin yiwa kowa addu'a yau ai yau kawai nafsi - nafsi, ta kai-ta kai, kaina kawai zan yi ta roƙawa gafara da neman dacewa a lahira"


09030283375
*MAMAN AFRAH DATA SERVICES*

*BUY DATA FROM THE AFFORDABLE PRICE*

*I selling MTN data with this cheap price*

*MTN DATA PACKAGE*
500MB@===150
1GB@=====250
2GB@=====500
3GB@====850
5GB@====1,400

Dial *312*4*7*4# to check Data balance.
*Validity 1 month*

*Airtel,9mobile and Glo* *also available.*
*Subscription for DStv gotv star time electric pay bills*

Act details FA'IZA ABUBAKAR unity bank 0020281885
Whatsapp OR
Call 09033283375




Wannan littafin kuɗi ne 300
Za a tura ta wannan accaunt ɗin Fa'iza Abubakar 0020281885 Unity bank shaidar biya ta wannan no 09030283375 idan katin waya ne mtn Ƴan Niger su tuntuɓi wannan no +22785885134



3️4️⃣9️⃣➡️5️⃣0️⃣


*LAST PAGE*😿😂

Barkanmu da kasancewa a ckn watan rahma watan ibadah RAMADAN MUBARAK😍


*RANAR SUNA*


Rana bata ƙarya sai dai uwar ɗiya ta ji kunya, Tasalla dai yau yadda ta ga rana haka ta ga dare, dan gabaɗaya bacci ya kasa zuwar mata, tsaf ta nemesa ta rasa bacci ya ƙauracewa idanunta sai zumuɗi take d murnar a kan gari ya yi ya waye su ɗauki hanyar birni, tun kiran sallar farko ta tashi ta yi alwala ta zauna tana lazimi, ita kana murmushi sai ƙwace mata yake ita kaɗai ta san irin daɗin da take ji da irin farincikin da take ciki.

"Kai Allah da ikonsa komai sai Allah ya nufa shi yasa wasu ke cewa kishiya in alkairi ce Allah tabbatar da alkairi to ni dai gashi kishiya ta wani wajen ta zame mini alkairi tun da gashi sanadin kishiya (Buk ɗina, labarin yadda sanadin kishiya ta haɗu da ƙalubale gidan aurenta tun daga ranar da ta sanya ƙafarta a gidan aure ta fara arba da bala'i kala-kala har makancewa sai da ta yi sanadin kishiya) Duk da dai ta wani wajen Azumi ba kanwar lasa bace amma dai yau ta mini rana har da yammaci ma" Cewar Tasalla da ta tashi daga kan abin sallah tana linkewa da hijabinta.

Babu ɓata lokaci ta shiga wanka ta fito ta shiga shiryawa cikin atamfarta mai kyau, tana cikin sanya kwalli sai ga Malam ya shigo ɗakin nata daga masallaci yake, ganinta zaune da ƙaramin madubi a hannu tana gwale ido yake kallonta da mamaki, washe haƙora ta yi tana kallon Malam da ke mata kallon mamaki.

"Malam har an dawo daga masallacin"

"Eh na dawo" Ya faɗa yana kallon wani jambaki sabo da ta fito dashi daga wata baƙar leda ta daddage za ta shafa.

"Tasalla menene hakan kike yi dan Allah" Cewar Malam yana kallonta.

"Wai a ina ?" Ta faɗa tana kallonsa.

"Wannan ba gazar bane da yara ke sanyawa?"

"Au wai wannan? Ba gazar bane Malam jambaki ake ce masa fa"

"Ko ma dai menene, ba dai sawa za ki yi ba"

"Shafawa zan yi mana Malam, saƙo na yi kasuwa aka siyo mini saboda na shafa, ko so kake in tafi birni suna dangin kishiya ake nuna ni da baki ana gulmata ko kwalliya ban iya ba bare kuma dama Azumi da ke min kallon ban taɓa zuwa birni ba ta faɗa musu cewa babu abin da ma iya wallahi ba zan juri baƙinciki ba gwara dai na cancaɗa adona da kwalliya yadda babu mai mini kallon raini alqur'an"

Ta faɗa tana wani shafa jambakin tare da haɗe laɓɓanta waje ɗaya ta daidaita jambakin.

"Ni na ga ikon Allah saboda zuwa birnin ne za ki shafa gazar da girmanki da komai tsofe-tsofe da ke saboda gudun magana za ki shafa, kuma ma da kike cewa Azumi za ta faɗa musu magana a kan ki bake kika ce mini ita ta gayyaceki ba, kin ga Tasalla wallahi bana son tashin hankali kar fa ku je cikin mutane kuke raba jaha ke da ita ij kin san da matsala kamar kullum kawai ki yi zamanki dan ni ba na son haɗin gurugudu"

Wani uban bugawa ƙirjin Tasalla ya yi da ƙarfi jin Malam zai shiga tsakaninta da burinta na zuwa birni, sai yanzu ta gane ɓaran ɓaramar da ta yi na cewa Azumi za ta faɗi magana a kan ta ai da sauri ta washe bakin nan na tsohuwa

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login