Showing 51001 words to 54000 words out of 56867 words
da ya sha jambaki ta ce.
'Allah sarki Malam ni fa ba haka nake nufi ba ka dan san mu mata ba ma rabuwa da gutsuri tsoma dole dai idan aka haɗu a gidan suna ko biki sai an yi da mutum tun daga suturar da ya saka zuwa kwalliyar da ya yi kai hatta tafiyar mace ma sai an saka ido musamman kuma aka ce maka kishiya ce ya je dangin kishiyarta to qur'ani hatta ƙasan zanen da ta saka sai an duba an ga wace irin atamfa ce ko leshi shi yasa ka ga na faɗi hakan, kuma jambaki da na shafa ai ba haramun bane ko Malam, in kuma kana ganin na goge sai na goge, dama na siya ne dan kar a kawo maka raini"
"A kawo mini raini?"
"Eh mana wallahi idan ban gyara jikina ba na fito fes muna zuwa za a ke cewa baka adalci a tsakanin matanka banbanci kake nunawa a tsakaninmu wata tafi wata a wurinka" Ta faɗa cikin sanyin murya tana wani karkata kai kamar ƙadangaruwa ita a dole kissa.
"Kuma fa haka ne da gaskiyarki to in kwa haka ne ki gyara abinki fes ki fito ɗoɗar da ke" Cewar Malam yana washe baki dan yadda Tasalla ta yi magana da kissa sai ya ganta kamar Azumi dan ita ce mai irin wannan yanzu za ta sanya shi yin abin da bai yi niyya ba.
"Ka ce fa ai dama na ce bari in gwada yadda Azumi ke yi, dan ko ranar da za ta tafi birni ZAMAN WANKA haka ta shaƙe murya ta rinƙa karairaye murya har sai da ka barta ta tafi, shi yasa na ce ni ma yau dai bari na gwada sa'a ta" Ta faɗa a zuciyarta tana wani jin ita ma yau ita ce.
" Aikuwa zan gyara ɗin dan ba na so a yiwa Malam ɗina kallon marar adalci a tsakanin iyalansa" Ta faɗa tana rufe fuska da tafin hannunta, alamar kunya wai ta ce Malam ɗinta. Shi kuma wani irin murmushi ne da dariya suka haɗe masa lokaci guda yana jin wani kansa na neman fashewa.
"Wayyo daɗi kasheni wahala ta huta, ashe dai ni ma da saurana a fannin soyayya ashe dai matata bata ganin tsufana take ce min Malam ɗinta duk da dama masana fannin so sun ce soyayya bata tsufa sai dai masu yinta su tsofe" Cewar Malam a zuciyarsa yana jin zuciyarsa fes.
Haka dai ta cigaba da shirinta ta shirya tsaf ta shafa turare ta ajiye bokitin da ta zuba fura a ciki da galan ɗin nonon da za ta kai gidan sunan. Tana gamawa lokacin Malam ya shiga ɗakinsa ta fito ta galgala wuta ta ɗora ɗumamen tuwo, tana ɗorawa kuwa ta barshi kafin ya yi zafi ta tafi gidan Tsahare tun daga nesa ta fara hango Tsahare tana haɗa kan ita ce a murhu ko wanka bata yi ba wani takaici ne ya cikata tana ji a ranta dama da a ce ta san birnij nan da tafiyarta za ta yi in ya so ita Tsaharen ta taho daga baya, dan ta ga aminiyarta ce Azumin shi yasa take mata wani jan aji.
Da sallama ta ƙaraso a bakinta kana kallon fuskarta za ka fahimci cewa ranta a ɓace yake. Amsa mata sallamar Tsahare ta yi ta ɗago daga sunkuyen da take tana ƙarewa Tasalla kalko. Babu inda ya ɗauki hankalinta haɗe da bata mamaki irin bakin Tasalla da ya sha jambaki gashi ta zana jagira da kwalli sai ka ce wata ƙaramar yarinya.
"Haba Tsahare wai ma baki shirya ba kuma na ga kina ƙoƙarin haɗa wuta ga wani ƙullin ƙosai a gefe in ce dai wata za ki barwa ta soya miki" Tasalla ta katsewa Tsahare tunanin mamakin da take na mai ya kai jambaki bakin Tasalla har da su jagira da girmanta da komai.
"Wai kamar ya wace irin magana kike haka, kawai dan zan tafi suna sai in kasa yin sana'ata shin kin manta ba a ƙafa za mu je ba kuɗin mota za mu biya daga nan ma zuwa tasha sai mun biya kuɗin machine, a can ma in an sauke mu sai mun hau adaidaita sahu, ga kuɗin gudunmuwa mutum ba ya je baƙiƙƙirin ba" Ta faɗa tana kallon ƙafar Tasalla da ta sha wani uban vasiline sanye da takalmi ɗan madina kore.
"Haba Tsahare yanzu dan wannan ne zaki yi sana'a yau so kike sai shinkafar da za a dafa ta suna ta ƙare bamu je ba gaskiya dai baki kyauta ba"
"Dan Allah ki rabu dani da wani zancen shinkafa yunwa za mu je, da za a ke tunanin shinkafar rabo, duk wannan abin da kike fa har yanzu a ƙarfe bakwai saura ake dan Allah ki koma gida duka ƙullin ma na kwano guda ne yanxu zan gama kinsan dai na kwano uku da rabi nake yi kullum"
"To ai shikenan ya na iya da abin da ya fi ƙarfina ni da ko hanyar ban sani ba ai dole na jira ki" Cewar Tasalla tana taɓe baki ta juya ta tafi.
Da kallo kawai Tsahare ta bi bayanta tana mamakin irin kwalliyar yaran da ta yi a fuskarta, gashi har yanxu ta kasa daina mamakin wai Azumi ce ya gayyaci Tasalla suna, dan ta san dai basa ga miciji da juna.
Sai wajen ƙarfe tara suka baro ƙauyen, zuwa lokacin sawun Tasalla ya fi biyar gidan Tsahare a kan ta yi ta shirya su tafi ƙarshe dai sai da suka yi faɗa a haka dai suka samu mashinan da suka kai su Garki L.G inda suka samu motar Kano suka hau. Tun da aka fara tafiya bakin Tasalla bai rufu ba ta ce wannan ta ce wancan tun Tsahare na biya ta har ta gaji ta yi shiru dan ta ga abin nata ba na ƙare bane, kuma kamar ma duk murna da zazzaɗin zuwa birnin ne ya sanya bakinta ya ƙi rufuwa. Tun da motar ta shigo garin Kano ta dabo tunbin giwa sai kuma gabaɗaya Tasalla ta ruɗe bakinta ko rufuwa ba ya yi ta sake shi galala saboda kallon motoci da kuma gine-gine kai ba ma su kaɗai ba hatta mutanen da ta gani masu yawa kowa yana harkar gabansa suj zame mata TV saboda ita bata taɓa zuwa gari kamar Kano ba iyakacinta ƙauyukan wajejensu kawai.
Tsahare da ta ɗauke kanta ta mayar gefe daga kallon Tasalla saboda nune -nune abubuwa da ta dame ta da su, ta ji Tasalla ta saki kuka cikin sauri ta waiwayo wajenta take tambayarta dalili dan har lokacin fa basu sauka daga mota ba kawai dai sun shigo garin Kano ne, motar tana tafiya zuwa tasha ne dan ta sauke lodi.
"Dole na yi kuka Tsahare wallahi dole na yi kuka, kawai ki barni kar ma ki baiwa kan ki wahala wajen lallashina dan ba shiru ba zan yi sai na yi mai isata na ji zuciyata ta yi sanyi"
"To ikon Allah" Cewar wasu daga cikin motar da suka haɗa baki wajen faɗa.
"Haba ke kuwa baiwar Allah ana zaune ƙalaw muna murna Allah ya kawo mu lafiya saura mu sauka, kawai za ki fashe da kuka kuma ki ce wai ba za ki saurara ba sai ka ce wata ƙaramar yarinya, kuma mu babu wanda ya ga kin ɗaga waya bare a ce ko mutuwa aka faɗa miki" Cewar wani mutum da ke gefe.
"Wallahi bawan Allah ba mutuwa aka faɗa mini ba, kawai takaici ne na abin da ka mini, ni nan da kake gani ina da shanaye da dabobi da nake kiwo ina dai da abin hannuna amma a ce a duniya akwai gari ya Kano amma ban taɓa zuwa ba? Kuma ko bani da kowa a Kano wallahi da na san haka take da ko iya tasha ne na biya kuɗi na zo na ga gari na koma amma aka barni a can ƙauye a garƙame, kuma dan baƙin hali irin na kishiyata, bata taɓa gayyata ta garin nan ba wajen ƴan uwanta ai ko, dan na kashe ƙwarƙwatar idona a faɗa min Kano haka take"
Gabaɗaya motar dariya aka kwashe da ita kowa yana jin abin da Tasalla ke faɗa sai ya yi dariya, abin nasu sai ya sosa mata rai dan haka ta ɗauke kan ta gefe ta cigaba da baiwa idonta nama. Kowa ya fita daga motar Tasalla kuwa tun da ta fito sai idanunta suka kasa samun matsaya ta kalli can ta kalli nan, da yake bakin titi aka sauke su a tashar ba a shiga cikin tasha ba. Sosai Tsahare ta yi da na sanin zuwa da Tasalla saboda babu abin d take sai kalle-kalle, a haka dai ta samu dakyar ta tsayar musu da ɗan sahu suka shiga suka nufi gidan suna murna fal cikin Tasalla dan har lokacin ma a ɗan sahun kalle-kalle take.
"Taɓɗi shi yasa ashe ake cewa hankali shi ne gani wai wani ya je Kano bai ga mota ba, yo in ba haka irin motocin nan na garin Kano kwantsam kamar jamfa a jos duk da ban taɓa zuwa Jos ɗin ba, amma gaskiya yawan motocin Kano ya ɓaci yadda ka san ba mutane kaɗai ke hawa motocin ba har da aljannu" Cewar Tasalla da ke ta kalle -kalle. Daga Tsahare har ɗan sahun babu wanda ya tanka mata a haka suka cigaba da tafiya.
A daidai ƙofar gidan aka sauke su, suna sauka sai Tsahare t tsaya tana baiwa ɗan sahun kuɗinsa, Tasalla kwa dama ta biya shi, dan haka sai ta ɗan tsaya daga gefe take jiranta kusa da wasu mata guda biyu da ke ƙusƙus.
"Wallahi fa nake faɗa miki miciji sak Hassan ɗin ke zama ya yi ta firgita mutane, in kika ji irin uƙubar da mutanen gidan ke fuskanta za ki yi mamaki" Cewar ɗaya daga cikin matan da ke tsaye gefe, Tasalla da ke saurarensu cikinta ne ya bada wani ƙululuuuu ta fara zare ido a take ta ji gabaɗaya Kanon ma ta ginsheta ji take kamar ma kar ta shiga gidan.
"Ikon Allah shi kuma irin tashi baiwar kenan, to gaskiya dole mutane suke tsorata yo ina kai ina miciji"
"Himm ke dai bari kuma fa a haka suke kwana da shi ɗaki ɗaya har kakar mai jego kin jo sunanta Inna Azumi"
Ai sunan Azumi da aka ambata shi ya ƙara tabbatarwa Tasalla da jariran ƴan biyun da suka zo sunan ake.
"Mu je mana ga gidan fa kina gani mutane sai shige da fita suke ni wallahi na ƙosa na sanya amini a idanuna " Cewar Tsahare tana kallon Tasalla da gabaɗaya jikinta ya yi sanyi ƙalaw kamar dai ba ita ce ta ishi mutane da surutu ba ɗazu.
"Kai ai ni unguwar ce duk sai na ji kaina yaba juyawa da alama mutanen ɓoye na ne ke son tashi shi yasa, idan kika sa ni a ɗan sahu za su maida ni tashar mota in koma gida" Cewar Tasalla dan duk son da take yiwa birni gabaɗaya ya fice mata a rai dan gabaɗaya hanjin cikinta ya hautsina.
"Ki koma gida kuma garin yaya wato sai da kika zo har ƙofar gida sannan tsoron mai zai je ya dawo ya zo miki, ai ni dama na san babu yadda za a yi Azumi ta ce ki zo sunan nan" Cewar Tsahare tana yiwa Tasalla wani kallo.
"Eh bata gayyace ni ba da Allah yi maza ki sama mini ɗan sahu ya maidani tasha" Cewar Tasalla dan gwara Tsahare ta ce mata komai a kan ta shiga gidan da miciji yake.
"Ai fa tun da kin riga kin zo to komai ta famjama fanjam jam" Cewar Tsahare tana kaɗa kan Tasalla suka tasarma cikin gidan.
*INNA*
Tun sanda ta fara nafilfilin nan ko hutawa bata yi haka take bari sai ta yi raka'a huɗu sannan ta sallame ta rinƙa jero addu'oi ta rinƙa kuka hawaye na zuba tana ta neman yafiyar ubangiji.
Haƙiƙa Inna tana cikin tashin hankali domin ba ƙaramin abu bane a ce ka san ranar mutuwarka duk da zai kasance za kake neman yafiya kafin lokacin amma tabbas za ka shiga tashin hankali, shi yasa yana daga cikin hikima ta ubangiji da ya ɓoyewa bayinsa sanin ranar mutuwarsu, da a ce kowa ya san ranar da wa'adinsa zai cika tabbas zai cigaba da rayuwa a cikin tashin hankali to wannan halin shi Inna ta shiga. Tana jin sanda Sadiya ta tashi tana shayar da yaranta da suka tashi amma ko ɗaga kai bata yi ta kalleta ba. Har sai da aka kira sallar asuba tana nan tana ibada amma kuma ko alamar bacci babu a idanunta dan gani take ita da ke shirin barin duniyar ma baki ɗaya to bata da wani lokacin jin daɗi a cikinta.
Haka ta tashi ta je ta tsaya a kan Imran tana kiran sunansa, ya tashi ya tafi masallaci Imran kuwa dama shi ma bai koma bacci ba dan gabaɗaya sai ya ji tausayin Inna har ma yana da na sanin mata abin da ya mata, dan tun lokacin da ya kama hannunta irin yadda ya ga ta rikice da kuma bayyanar tashin hankali a tare da ita shi yasa ma ya yi saurin cewa sai nan d sati biyu amma da niyyarsa sai ya dinga ja mata rai yadda za ta tsure sosai amma ganin ta tsorata sosai shi yasa ma ya ƙyaleta. Kuma yanzu yana tsoron ya fito ya faɗa mata gaskiya ido ya kuye da mujiya dan ya san Inna ba kanwar lasa bace dole za ta yi shirin ɗaukan fansa dan haka sai ya bar maganar a zuciyarsa yana fatan Allah sa ta saki ranta ta yi rayuwa cikin salama a kwanaki sha huɗun da yace za ta mutu duk da ya san da kamar wuya gurguwa da auren nesa amma yana fatan hakan.
Tana kiran sunansa sai alerm ɗin wayarsa ya shiga ƙara dan haka sai ya yi kamar ƙaran wayar ne ya tashe sa.
"Inna har kin tashi ke ma" Ya faɗa cikin sanyin murya dan duk da a gabansa take tana kiran sunansa amma in ta kirashi sau ɗaya sai ta ja carbin da ke hannunta bakinta ya motsa sannan za ta ƙara kiran nasa abin ya so bashi dariya sosai amma sai ya ji tausayin ya danne dariyar.
"Kayya Imirana ni dama ina nan ido biyu ai ban ko yi gyangyaɗi ba"
"Allah sarki Inna ki ce dai yau duk mun sha addu'a mun more?" Ya faɗa dan ya ɗan jata da hira ta saki ranta ko yaya ne dan ya ji daɗi dan yana ganin ya tauyeta, saboda ita duk abin da take masa na iya duniya ne ma'ana bata masa abin da zai nuna barinsa duniya ba duk da miciji ma abin halakarwa ne amma ya san daga an raba shi dashi to zai daina jin tsoro ita kuma y mat abin da a ko yaushe za ta kasance cikin tsoro mai tsanani.
"An muku kam ba laifi, fa kaina kaɗai name yiwa amma daga baya sai nake yi da sauran al'umma ma dan addu'ar da ka yi a jama'i tafi saurin karɓuwa a kan wacce ka yiwa kan ka kai kaɗai"
"Allah sarki Inna mun gode, bari na yi sallah a je a shigo da abin yanka na suna wanda tun ranar da kika zo kikr yi da bakin ki cewa ba a kawo ba" Cewar Imran lokacin da ya tashi yana ƴar dariya duk dan ya sanya Inna farinciki.
"To Imirana" Cewar Inna cikin halin ko in kula ɗin nan. Haka ta shige ɗaki ta barshi dan bata so ta yawaita magana lokacinta ya tafi a banza ba tare da ta yi istigfari ba.
Haka dai Imran ya yi shirin zuwa masallacin zuciyarsa duk ba daɗi bai taɓa jin ya yi da na sani ba a kan abin da yake yiwa Inna sai yau, duk da a da ya ɗauka cewa duk abin da ta masa sai ya rama har ma yana ikirarin ramuwar gayya ai tafi ta gayya zafi, amma kuma yau ya ji ba daɗi sosai. Yana dawo wa daga masallaci ya samu suna ɗan zantawa da Sadiya amma har lokacin carbinta yana hannunta, haka Inna ta fito dan ɗora ruwan wanka a lokacin ne kuma Imran ya ɗauki kayan nan da ya yi amfani da su ya ɓoye a drowersa kafin gari ya waye ya fice d su dga gidan.
"Wai ni Inna dama kin san bakya iya kwanciya da ƙunshi kika yi kika kwanta, kalli yadda kika ɓata ƙafarki ai dama baki yi ba da dai wannan caɓe ƙafar da kika yi, kuma gashi ya kama sosai sai dai gabaɗaya kin caɓe shi" Cewar Sadiya da za ta tafi ta shiga wanka tana kallon Inna da ke ajiye ruwan wankan za ta fara yiwa yaran wanka. Kallon ƙafar kawai Inna ta yi ta sauke wata ajiyar zuciya tana rayawa a ranta cewa ƙafar da saura kwana sha uku a binne ta a cikin ƙasa menene ma na damuwa da caɓewar kunshi. Sadiya jin Inna bata, bata amsa ba sai kawai ta kaɗa kanta ta fita dan ta lura Inna shiru ya fiye mata yau ko magana bata so ga babu walwala a tare da ita bare ma ita da ke murna aminiyarta za ta zo yau amma sai ta ga yau ko murna fa maganar Tsaharen ma bata yi kawai ko yaushe bakin motsi yake alamar tana karanta wani abu ta kasa gane dalilin yin hakan. Ta san halin Inna dai bakinta baya shiru baya rabuwa d abin faɗa amma kuma yau sai ta ga Innar ta canja mata.
Bayan Sadiya ta yi wankanta shirya abinta tsaf lokacin har Mama da Ashrof sun zo ga kuma ƴan uwan Mama duk sun fara zuwa haka zalika Hajiya ma da maƙotanta da wasu dga cikin danginta sun iso gidan dai sai san barka amma gida ya fara cika, kuma sai maganar miciji ta kwanta kamar ma babu ita dan kowa sai sabgar gabansa yake. Ashrof da Mama da Hajiya kai da duk wani wanda ya san Inna kawai mamakin ta yake yau dan akwai wasu daga cikin matan nan da suka zo