Showing 27001 words to 30000 words out of 56867 words

Chapter 10 - YAR ZAMAN WANKA BOOK 3

27 Sep 2024

3835

gashinnan ya zame masa abin gorantawa. Amma dama ya san duk wanda ya sayi rariya ya san za ta zubda ruwa.

"Yo kuma ai sai ka tashi daga tsugunnen ka tafi masallaci tun da dai ka yi abin kunya yau" Cewar Inna.

"Dama tashi zan yi" Cewar Imran yana ji kamar ya kwaɗe Inna.

"Ba niyya ango ya kwana da wando, yo kana durdurƙusar da kai alamun kunya ka kasa tashi za ka ce wai dama tashi za ka yi, ai fa ka sanyawa zuciyarka dangana Imirana faɗan da ya fi ƙarfinka kake midashi wasa sai ka zauna lafiya da mutane, ai zama lafiya ya fi zama ɗan sarki"

"Wai kamar ya Inna" Cewar Sadiya da ta fara fuskantar wani abu kenan dai Inna ce ta haddasa komai.

"Abin da wancan ya ce shi na ce kirarin mai tsoro, wato ke uwar ƴan son miji shi ne kike bin ƙwaƙƙwafi, kawai ki barni da Imirana dan kura ce kaɗai ta san gidan mai babbar sanda" Ta faɗa tana niyyar fita daga ɗakin.

"Sadiya miƙo min riga a drower" Ya faɗa yana jin haushin Inna na ƙara azalzalashi a kan ƙin yin da na sani a kan abubuwam da ya aikata mata a baya da ma wanda zai aikata mata nan gaba, duk da dai ya san ramin ƙarya ƙurarre ne, kuma rana dubu ta ɓarawo ɗaya ce tak ta me kaya.
"Maza miƙo masa rigar ya tafi masallaci kar ya yi saki na dafe, na ga sai wani hararata yake abin da na masa bai gode ba yo Allah na tuba ban da dai abin kirki bai gaji kare ba in ya yi ma dukansa ake duk taimakon da nake yiwa Imirana a gidan nan ba ya gani kawai dan na sa ya min rawa na ce yake ɗan zazzakuɗa mazaunai yana kaɗa kai shi ne laifin da na masa" Cewar Inna tana kallon Imran fuskarta da alamar dariya, wata uwar harara ya doka mata.

"Wai tsohuwar nan ni za ta yiwa kissa, amma ba komai ki dai bi a hanakali kar tura ta kai bango, dan wanda bai ji bari ba zai ji hoho" Ya faɗa a ransa. Sadiya kuwa Hassan ta mayar kan gadonsa ya ɗakkowa Imran rigar dan gabaɗaya kanta ya kulle da abubuwan nan ko kaɗan Inna da Imran babu wanda ya ke tunanin halin da Hassan ke ciki, wai yana cikin halin ne ma har ya zama ana ɗaukansa dan cika wani buri, gashi kullum cikin ka ce suke ta ka gane dalili musamman ma shi Imran da, ko damuwa da bai yi ba da yawan magana amma yanzu sai take jin har magana yake yadawa Inna a wayance ta kasa gane bakin zaren.

Inna dai juyawa ta yi ta fice daga ɗakin ta je ta ɗauro alwala. Ta dawo tana ɗakko abin sallarta daga cikin jakarta sai ga Imran ya fito daga bedroom ɗin.

"Masallacin ne Imirana sauka lafiya" Ta faɗa tana ƙushe dariyarta ganin ya fito sai muzurai yake. Bai tanka mata ba ya cije leɓe ya sanya kai ya fita ya ɗaura alwala ya tafi masallaci dan zuwa lokacin ma har an kusa kaiwa raka'ar farko.


*HAJIYA*


Tun da ta baro gidan Imran bata zame ko ina ba sai gidan wani Malam Isuhu mai almajira ta daɗe tana jin labarinsa to da yake ma babu nisa sosai daga gidanta amma can sama da su yake. Tana zuwa ta tambaya aka ce yana cikin gidan da sallama ta shiga gidan bayan sun gaisa da matan aka faɗa masa ya yi baƙuwa, bayan an mata iso ta nufi ɗakin nasa tare da matarsa uwar gidansa ita ce ta raka ta har turakar Malam ɗin. Ɗakin cike yake da manyan qur'anai da littattafan addini a gefe guda, ga wasu carbuna manya manya da ƙanana hawan hawa. Zaune yake a kan darduma ya sanya gabansa gabas ga wani ƙaton carbi yana ja. Matar da ta rako ta tana shiga ɗakin ita kuma ta koma. Malam kuwa da ke ɗaura rubutu a leda rubutun cikin bokitin fenti babba, wanda ruwa ne kawai aka zuba tawada a ciki sai a ƙulla a leda ana baiwa mutanen da suka bayar da kuɗi a musu rubutu.
Dan haka ba ya rubutun tawafa kawai yake zubawa a ruwa yana ƙullawa jin an ce ana masa sallama shi ne ya rufe bokitin ya ɓoye wanda ya ƙulla ɗin. ya koma ya zauna a darduma ya fara jan carbi yana mismis da baki.

Sai da ya kai ƙarshen carbin Hajiya tana zaune sannan ya juyo gareta ta fara gaishe da shi tana masa ya fama da kuma ƙoƙari da jama'a, nan ya masa komai lafiya.

"Malam dama wani aiki ne nake so ka min a kan iska...


"Ai mun gama sanin me yake tafe da ke, duk na gani cikin mafarki tun jiya na san da zuwanki, dan haka indai ƙwanƙwamai ne babu abin da ya gagaremu ku da su sai dai ku ji ana labari" Ya katse Hajiya daga abin da take son faɗa masa a kan Hassan da take so ta ce ya je ya masa addu'a ko za a dace ya dawo mutum amma kuma shi sai ya nuna ya san komai ya hana ta ta masa bayani.

" To babu komai nawa ne abin sadaka?"

"Ai abin sadaka sai mun je muke faɗa, kuma yau ina da baƙi ba zan samu zuwa ba sai gobe da yamma"

"To babu damuwa, Allah saka fa alkairi"

"Amin" Cewar Hajiya, tana jin daɗi za a yiwa jikan nata magani.

"Ai kar ki damu mu nan fitar da mutsa mutsai ba komai bane indai muka karanta ayoyin qur'ani to tabbas Allah zai amsa"

Sosai ta ji daɗin maganar tashi, sai da za ta tafi ya ce

"Baki faɗa mini gidan ba"

"Yo ai na ɗauka har gidan ma ka sani a mafarki "

"A'a ki faɗa kawai an za a faɗa min gidan sai na falka daga bacci kin ji dalil"

Nan ta shiga masa kwatance daga ƙarshe ma dai sai ta gane ya san gidan Imran ɗin, dan ya faɗa mata wani gida da ke maƙotaka da gidan Imran ɗin dan haka sai ta ce masa maƙota ne da gidan da ya faɗa mata, sai da ta tabbatar ya gane sannan ta mas sallama ta tafi abinta.

" Wa ya ga taɓɗi ai ban da kin ce iska babu abin da na sani game da zuwanki amma yanzu ai na kama ki a hannu" Ya faɗa a zuciyarsa bayan fitar Hajiya yana janyo leda da bokiti ya cigaba da ƙulla maganin, rubutun, yana murnar samun aikin nan, kuma ma ya ce mata sai gobe yau yana da baƙi ne dan kar ta raina shi ta ce ba a kawo masa aiki.


Hajiya haka ta koma gida tana ta farincikin samun mafita dan haka ma sai ta ja bakinta ta yi shiru ko su Imran ba za ta faɗa wa ba sai gobe.

Wajen ƙarfe ɗaya da wani abu Inna tana zaune a ƙasa a falon tana cin abinci dan yau ita ra dafa abincin ma Ashrof bata zo ba, wai kanta na ciwo ko haka ne ko kuma saboda tsoratar da ta yi Allah kaɗai ya sani. Imran da ya ci abinci a bedroom ya fito jin ƙaran wayarsa da take caji a falo.

"Assalamu alaikum barka da rana Hajiya" Ya faɗa lokacin da ya kara wayar a kunnensa.


Amsawa ta yi tana tambayarsa mutanen gidan bayan sun gaisa, nan kuma ta ce.

"Imran na je wajen wani Malami Malam Isuhu zai zo da yamma. Shiru ya yi bai ce komai ba Inna da fa kasa kunne tana iya jiyo maganar da ake daga cikin waya, ba handsfree take ba amma dai volume ɗin a ƙure yake.Shiru ya yi yana son gama jin abin da take so faɗa masa.

"Gwara dai ya zo kam Amina dan yau ma micijin nan a wajen Imirana ya kwana a cikin rigarsa" Hajiya ta jiyo muryar Inna ta cikin waya hakan ne ya ƙara tada mata hankali. Wata harara Imran ɗin ya jefawa Inna da ke gatsina mas gefen hanci, haushi ma ya sanya bai ce komai ba jin Hajiya na faɗa a kan me yasa ya kwana da miciji kuma zuwan Malam Isuhu babu fashi dan haka sai ya zo. Hajiya na gamawa ta kashe wayarta ta bar Imran riƙe da wayar sai muzurai yake ya maida cajinsa ya koma ɗaki ya kwanta yana ta nazari tabbas ficewa zai yi daga gidan dan ba zai zauna a maida masa twins ba.A a zo wani maida masa ɗa miciji bayan Allahn da ya baiwa yaron baiwar zai dawo dashi a duk lokcin da ya so ita kuma mahaifiya ce a wajensa babu yadsa zai yi da ita. Sadiya da ke zaune tana shayar da Husaini ta kalli Hassan da ke kan gadonsa rufe da bargo, tana jin tausayin yaron har cikin ranta.

Imran ko da aka fara kiran sallar la'a sar sai gashi ya fito zai tafi masallaci, ya sunkuya zai ɗauki wayarsa daga caji Inna ta ce.

"Wai ni Imirana wannan uban lemukan robar da ka kawo aka jibge ba za a ɗauka min wanda idan Aminiyata Tsahare ta zo gobe ba zan bata da kuma wanda zan bata saƙo ta kaiwa jama'ar garinmu ƴan uwa da abokan arziƙi, ni kuma in yaso idan na gama ZAMAN WANKA zan tafi sai in tafi musu da namn sunan da zan sanya shi a kitse" Ta faɗa tana kallon Imran da ya ɗago riƙe da wayarsa tsabar mamaki ma ya rasa bakin magana, wai ashe har wata aminiyarta ce za ta zo suna lallai tsohuwar nan da ɗora hau take a gado baki kawai ya taɓe bai ce komai ba ya juya ya fice zai yi alwala.

"Uban shegen mugun halin tsiya, yo Allah na tuba meye a lemon roba ban da tsiya ma abu da bai fi a bani sinƙi biyar (cartoon biyar)ko shida ba in bayar a mini bajinta da shi a ƙaunyen kafin in koma" Ta faɗa tana kallon lemon da aka jibge wasu kan wasu.

"Haba Inna wai ke dai bakya ƙi ko gudun abin magana, yanzu lemon da za a raba na ƴan suna shi ne za a baki har katan biyar kuma ma maimakon ki tambayeni sai kika tambayi Abban twins, sannan Inna har Iya Tsahare kika gayyato"

"Halima wallahi ba na son kinibibi ki fita idona in rufe, kuma ni nan Azumi wallahi ban iya munafurci ba shi yasa kika ga ina tambayar abu kuma abin da yasa na tambayi Imirana na ga dai shi ya siyo ba ke kika siyo ba, in tambayeki in tambayi wofi, kuma nawa sinƙi biyar yake da har za a ce na yi zari, sannan Tsahare kuma kamar ta zo sunan nan ta gama dan takanas ta kano na tura ɗan acaɓa ya faɗa mata na tafi Kano kin haihu ta sameni a nan"

"To shikenan Inna amma ai dai kin ga yadda wurin kwanan ma yake aiki ne a gidan nan amma kika gayyato ta"


"Na shiga aljanna na maƙale saboda na ga wurin zama babu fitowa, yanzu Sa'adiyya ni Azumi da na haifi ubanki kike faɗawa wannan magana wurin kwanan banza da wofi wallahi a kan Tsahare za mu ɓata da kowa saboda ita ce ta gaban goshi kuma sai ta zo ta kwana dan wallahi ban gaji rashin arziƙi ba da zan ruge ido in ce ta koma inda ta fito a ranar da ta zo dan rashin tausayi ta yi doguwar tafiya ta koma a ranar to ba da ni ba gaɗa a hurumi, kwana daram sai dai mijinki ya nemi akurkin kaji ko ma zabbi ke wallahi ko na tattabaru ne sai dai ya je ya kwana in ba haka ba mu haɗu mu uku mu kwana a gadon ni ke da kuma aminiyar tawa, in ba za ki kwana damu ba sai ki je wajen mijinki ku kwana a falo, dama burinsa kenan ya jiki a kusa dashi, ko yau ya ɗauka Hassan ke ce baki ga yadda ya ƙwaƙumeshi ba kamar mayunwacin zakin da ke jin yunwa ya samu abinci kai ai wannan yaro da jaraba yake"

"Inna ya aka yi kika sani ke da ya tasheki a bacci ta yaya kila san ya rungumi Hassan ɗin" Cewar Sadiya tana kallon Inna da mamaki.

Imran kuwa da ya taho zai wuce masallaci bayan ya yi alwala ya jiyo Inna na wannan bayani hakan ya ƙara bashi tabbacin ita ce ta kai masa Hassan kai kawai ya gyaɗa ya sanya kai ya fita abinsa.

Inna kwa yatsina fuska ta yi ta taɓe baki ta sanya hannu ta turo ɗankwalinta gaban goshi tare da kauda kai, babu yadda Sadiya ta iya sai ƙyaleta ta yi.




*Masu fitar min littafi ku sani haƙƙina ne, kuɗin karatu kawai kuka biya, ke ma da kike karantawa baki biya ni ba haƙƙina ne duk ina so ku san da haka!*

09030283375
[24/03, 5:14 AM] Mom Mashkur First class: *MAMAN AFRAH DATA SERVICES*

*BUY DATA FROM THE AFFORDABLE PRICE*

*I selling MTN data with this cheap price*

*MTN DATA PACKAGE*
500MB@===150
1GB@=====250
2GB@=====500
3GB@====850
5GB@====1,400

Dial *312*4*7*4# to check Data balance.
*Validity 1 month*

*Airtel,9mobile and Glo* *also available.*
*Subscription for DStv gotv star time electric pay bills*

Act details FA'IZA ABUBAKAR unity bank 0020281885
Whatsapp OR
Call 09033283375




Wannan littafin kuɗi ne 300
Za a tura ta wannan accaunt ɗin Fa'iza Abubakar 0020281885 Unity bank shaidar biya ta wannan no 09030283375 idan katin waya ne mtn Ƴan Niger su tuntuɓi wannan no +22785885134


*Q* ➡️ *R*






"To Allah raya ya kuma ɗayyaba, ai sai na baku addu'a ma kafin na tafi wacce za a yi taro lafiya a gama lafiya" Cewar Malam yana ƴar dariya.

"Amin ya rabbi, ni kuwa zan tuna maka idan za ka tafi" Cewae Inna a fili a zuciyarta kuma ta ce.

"Tabbas lokacin da za ka tafi ba lallai ka tuna da takalmanka ba ma bare addu'ar da za ka bayar"

"Kar ki tuna min ai ni na ce zan bayar kuma ba sai kin tuna min ba dan ba na mantuwa"

"Ah to in kwa haka ne na yi katsalandan" Inna ta faɗa tana ƴar dariyar wasa.

Sa'adiyya ki zauna a nan ni zan raka su wajen marar lafiyar" Cewar Inna tana ƙoƙarin yin hanyar bedroom.

"Kamar ya Inna cikin ƙuryar ɗakin za ki kai su...

"Ikon Allah wai kina nufin marar lafiyar kuka haɗa ɗaki ɗaya da jaririn nan da aka fiddo? Kenan yana cikin ɗakin nan ba kwa tsoron faruwar wani abu?" Cewar Malam cikin mamaki dan shi ya ɗauka ɗaki aka ware wa marar lafiyar.

" Ah jikin ne dai yau da sauƙi amma ko jiyan nan gidan nan sai da kowa ya nemi mafaka har da masu shiga tukunyar jego, da masu shiga ƙasan gado, kai har ma da masu hawa saman bishiya, dan nan marar lafiyar yake bin kowa a guje" Cewar Inna cikin nuna tausayawa.

"Allahu akbar kin ga abin da ake gudu ko in ce dai ba makami yake ɗauka ba, ai wannan aikin manyan baƙaƙen aljannu ne" Cewar Malam yana kallon fuskar Inna da ya kasa gane kamar dai tana nuna alamar dariya.
"Ka dai bari Malam ai idan abin ya motsa sai dai du'a i"

"Yau kuwa za a yi maganinsu yau bacci zai yi har da munshari su kuma mu fatattake su, su bar jikinsa ba za mu ƙyalesu ba sai mun dangana su da kukar bulukiya, ko ma mu aika su bangon duniya, ke wasu ma har ƙasar sin muke aika su"

"Kai gaskiya gafarta Malam ka iya aiki yo irin wannan aiki ai ko miliyan aka baka ba a faɗi ba"

"Shi ya sa ai raina ya ɓaci da kika musa wato kika nuna na muku tsada in aka haɗa da ƙoƙarin da zan muku ai abin sadakar ba wani mai yawa na a zo a gani ba na faɗa"

"To ba komai " Cewar Inna tana yin gaba.

"Ai ba da ke za a shiga ba mu kaɗai za mu shiga dan ba ma son kowa ya shiga saboda idan muna dukan aljannu kar a samu mutum" Cewar Malam yana kallon Inna.

Sadiya saurin miƙewa tsaye ta yi jin an ce wai za a yi duka. Wata harara Inna ta doka mata ta ce.

"In ba a nema masa lafiyar ba haka zai yi ta zama"

"Rabu da ita mana a mata bayanin da hankalinta zai kwanta, ba fa shi za a duka ba aljannun za a duka kuma da zarar mun ga sun fita za a dakata da dukan ki kwantar da hankalinki, ina ga ma sai an rufe ƙofa in muka shiga saboda ƙara da kururuwar alajannu kar ma ta yi zaton marar lafiyar ake duka ta zabura ta je ɗakin ko kuma shi ya fito a guje ya je ya ji muku ciwo kun san aljannu da shegen ƙarfin tsiya dan ma dai na taho da Ƙasimu da Habu" Cewar Malam yana kallon almajiransa da suka washe baki jin an ambace su dan suna da ƙarfin danne mai aljannu.


"Koma ki zauna" Cewar Inna tana kallon Sadiya. Komawar kuwa ta yi ta zauna duk da ta san dai tun da ta ga Inna tana ɗan kanne mata ido a ɓoye tabbas akwai ayar tambaya.

"Ƙasimu ku ɗakko kayan aikin maza" Ya faɗa yana gyara zaman rawanin hiraminsa.

Inna ce a kan gaba sai Malam sannan ƴan rakiyarsa, sai da suka gama shigewa cikin ɗakin Inna ta tsaya a jikin mudubi, Malam kuwa ajiye carbunansa ya yi a ƙasa yana cewa.


"Sai ni Malam Isuhu mai maganin duk wani shegen aljani, ban fito ba sai da na shirya gaba salamun baya salamun" Ya faɗa yana wani sunkuyawa ya ɗan naɗe ƙafar wandonsa, su ma sauran tattare hannuwan rigarsu suka yi tare da na ƙafar.
"Ina yake ne?" Cewar Malam yana kallon ɗakin da mamaki ganin bai ga marar

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login