Showing 54001 words to 56867 words out of 56867 words
ranar da aka musu ƙunshi ƴan uwan su Imran amma ganin Inna shiru yau su ma sun fahimci akwai damuwa a tare da ita kowa sai ya tambaya ko lafiya sai ta ce lafiya lau wasu dai sun danganta hakan da cewa ko wani abu ke damunta kuma bata so ta faɗa. Dan dakyar ma ta yi wanka ko shi ma sai da Sadiya ta matsa mata, ko da ta fito babu abin da ta shafa kawai atamfarta ta ɗauka ta sanya ta ɗaura ɗankwali ta ɗauki carbinta ta zauna a kan kujera take lazimi tana kallon shige da ficen mutane ana ta hada hadar yin abubuwan suna. Dan ko lokacin da aka shigo da raguna manya -manya guda biyu da tinkiyoyi su ma manya guda biyu Inna tana gani aka shigo da su, jim kaɗan aka fita da su aka dawo da su a yanke aka rataye amma ko ci kan ka inna bata ce ba. Imran ma lemuka katan uku ya siyo mata da cake irin mai biyun nan ƙanana guda hamsin dan ta yi farinciki ya ce ga kashinya ta rabawa wanda take so amma haka ta karɓa ta yi godiya da fatan alkairi ta ajiye amma ba wai dan ta ji abin ya birgeta ba sai dai kawai ita yanzu komai na duniyar ya fice a ranta tafi so kawai ta ganta a gidan mijinta hankalinta zai fi kwanciya.
Tana nan zaune kamar an ce ta ɗaga kai sai kawai ta hango aminiyarta Tsahare riƙe da kaya ta shigo, tabbas ta ji daɗi a ranta amma ba kamar yadda take zaton ji ba a baya.Kafin ta tantance sai kawai ta hango Tasalla da wani bokiti da galan da wata jakar kaya madaidaiciya a hannnunta. Ai Inna da ta wani ajiye carbi a gefe ta ji wani takaici ya turnuƙeta ai cikin hanzari ta tashi tsaye kafin ka ce kwabo ita ma bata tantance ba sai kawai ganinta ta yi a bakin ƙofa ta taho a fusace kamar kumurcin miciji.
"Yau ake yinta lallai Tasalla kin ga makwancina har ni za ki zo wa sunan jika ban gayyaceki ba? Ni saboda bana son ki raɓeni na fi so kullum hawainiyarki ta kiyayi rama ta shi yasa ko da bikin Halima ban gayyaceki ba amma shi ne yanzu saboda ƙoƙari faɗawa mijin baya tariya, kika ɗakko ƙafa kika zo, duk da cewa na san ruwa baya tsami banza, amma ki sani sara da sassaƙa bata hana gamji toho, kuma wallahi iya gani iya ƙyalewa, wannan abin da kika yi wayon a ci ne an kori kare daga gindin ɗinya, amma ki bar murna dan karenki zai kama zomo, amma duk da haka na san ba za a tambayi kalwa zaƙin miya ba sai dai a tambayi barkono a sha labari, tabbas yau allura za ta tono garma, domin kuwa ba wahalalle sai mai kwaɗayi, duk da kin cika burinki na zuwa birni dama hausawa sun ce buƙatar maje hajji sallah, amma yau zan nuna miki zafin nema baya kawo samu, kuma duk esnda ya ce wutar kara ta kwana tana ci, to tabbas bai yi bacci ba, Tasalla yau zan nuna miki wanda zai je sama ya taka leda to haƙiƙa ya ci ƙarfin tafiya!!!" Cewar Inna a zuciyarta lokacin da ta taho a fusace gadan -gadan ta iyo wajen Tasalla.Tasalla wacce dama gabaɗaya zuwa birni take da na sani duk da cewa da na sani ƙeya ce amma kuma ita babban tashin hankalinta micijin da aka ce akwai a cikin gidan wanda ta ji labari cewar ɗaya daga cikin tagwayen ne yake komawa, ga kuma hango Inna ta taso kamar wata kububuwa ya ƙara tada mata hankali wato dai bokitin furarta da galan ɗin nono da take sa rai za su kankaro mata mutunci a wajen kishiyarta ta ba haka bane dan kwata-kwata bata ga kyan wuri a kunnen jaka ba, shikenan yanzu Azumi za ta kunyata ta a cikin jama'a duk da ta wani ɓangaren tana jin ƙwara dai ta kwaɓe tsakaninta da Azumin ko ta samu damar barin gidan dan ta san dai in suka kwashi ƴan kallo to tabbas ko dan neman masalaha a ce ta koma inda ta fito, ita ma Tsaharen za ta bata goyon bayan hakan wanda ta ƙi bata a ƙofar gida dan da ta barta ma da tuni ta kai tasha ko da kuwa a ƙafa ne dan sannu sannu bata hana zuwa sai dai a daɗe ba a je ba, duk da ta san ba lallai ta iya zuwa ba sai dai za ta yi tambaya dan matambayi baya ɓata.
Tsahare ma ganin aminiyarta ta, ra doso su sai jikinta ya bata yau za a cancanre dan dama ta san da walakin goro a miya,dan ta san ko menene tsakanin Azumi da Tasalla to shigo-shigo ba zurfi ne, dan komai za a yi sai dai ya zamana bita da ƙulli ne dukan kabarin kishiya, dan dama ita ta san za a rina wai an saci zanen mahaukaciya. Inna kuwa da sai da ta zo dab da su sai zancen mala'ikan mutuwa ya faɗo mata na saura sati biyu ta mutu kuma dai yau ma tun da gari ya waye har ta ci kwana ɗayanta, saura sha uku, dan ita lokacin da ta hango Tasalla gabaɗaya sai ta ji wani kishi ya turnuƙeta a take ta sha'afa da halin da take ciki dan bata ma san lokacin data ajiye carbinta ba kawai dai ta ganta ta tunkaresu cikin zafin nama, amma tuno da mala'ikan mutuwa da kuma cewar in ma kishi take to wanda take kishin za ta mutu ta barshi da kishiyarta ta, ita tata ta kusa ƙarewa to ma menene na ɗaukan duniya da faɗi ita da za ta barta ma nan da kwana kaɗan.
Wani uban washe baki Inna ta yi na ƙarfin hali dan ita yanzu in ba larura ba bata ƙaunar ma a ga haƙorinta saboda ai wanda ke cikin farinciki shi ne zai yi dariya, amma kuma yanxu ya zama dole ta saki fuska da jama'a har ma da Tasalla dan an ce shimfiɗar fuska tafi ta tabarma kuma ta haka ne mutane za su yafe mata da mata addu'a in sun samu labarin mutuwarta, kuma wannan dama ce da za ta yi amfani da ita wajen gyara ma'amalarta da kishiyarta, wanda dama ya dace tun a baya hakan ya kasance dan ko da a ce mutum bai san ranar mutuwarsa ba to fa ya sani tabbas wannan ranar akwai lokacin da za ta zo ko ba daɗe ko ba jima sai kowa ya kwanta dama dan haka yana da kyau ka mu'amalanci mutane da mu'amala mai kyau, dan shaidar mutane ita ce ta ƙiyama, iya yabon da za a yiwa kyawawan halayenka iya yadda mutane suka ji daɗin mu'amalantarsu da ka yi ne, dan haka kyakkyawar mu'a mala tana da kyau.
"Gasu, gasu, sannunku da zuwa mutanen arziƙi sannunku da ɗabbaƙa zumunci " Cewar Inna tana ƙarasowa wajensu fuska a sake take kallon Tasalla da Tsahare. Ba Tasalla ba hatta Tsahare ta yi mamakin wannan tarɓar da Inna ta yi, kuma ta kasa gane dalilin yin hakan dan ta ga a yadda ta zo amma bata san ya ka yi ido ya juye da mujiya ba, dan ta saa halin aminiyarta Azumi babu tsoro kuma ba munafurci dan ta san Azumi dai bata san cewa wai dan tana ganin mutane ta ɓoye abin da ke ranta ba ita haka take fitowa ta nuna gaskiyarta, ita dama ƴar gaskiya ce. Tasalla mutuwar tsaye ta yi ganin Azumi ta sauya daga yadda ta nufo su da farko, sai gabaɗaya ta yi fosta mamaki al'ajabi suka dirar mata lokaci guda dan ita da a ce an wulaƙanta ta a bainar jama'a gwara ta bari in ta koma gida bayan ta gama ZAMAN WANKAN ta mata duk abin da za ta mata, sannan si ta ji daɗi da kuma buri d lafahrin yadda kishiyarta ta ta tarɓeta sai kawai ta ji babu abin da ya fi zaman lafiya daɗi, da a ce haka suke zaune tun farko da tuni ta yi zuwa Kano ba adadi dan da Azumi za ta gayyaceta wurin danginta in suna zama lafiya, kuma ko da a ce bata gayyaceta sunan nan ba sa zaman lafiya suke ba za ta ji ɗar ko shayin zuwa ba. A take ita ma Tasalla ta saki murmushi tana kallon Inna Azumi ai gabaɗaya sai suka zame wa Tsahare TV ta kalli wannan ta kalli wannan.
"Ke kallon ya isa haka" Cewar Inna cikin zolaya tana kallon Tsahare da ta saki murmushin jin daɗi lokaci guda dan ita ma ta ji daɗin yadda aminiyarta ta, ta tarɓesu.
Haka Inna ta shigar da su tana murna, dan ita ta karɓi bokitin furar gannun Tasalla ma, tana zolayar Tsahare wai ba za ta karɓi kayanta ba kayan ƴar uwarta Tasalla za ta karɓa. Haka sai ta musu masauki tare da gabatar musu da abin kaiwa baka. Nan Tasalla ta gabatarwa Inna nono da fura a matsayin abin da Malam ya ce a kawo ita kuma ta fito da riguna da dubu biyu ta bai wa Inna wai a baiwa mai jego, aikuwa Inna ta yi godiya sosai amma ta ce ba za a karɓi kuɗin ba dan wahalar ta isa ita kuma ta rantse a kan ba za ta karɓa ba tun da ta yi niyya kuma ba Innar ai ta baiwa ba jikarta da ƴaƴanta ta baiwa, sosai Inna ta ji daɗin kyautar da Tasalla ta yi, dama zuciya tana son mai kyautata mata, kuma sai Inna take cewa ashe haka zaman lafiya yake da daɗi. Tsahare ma turmin atamfa da riguna biyu ta kawo haka dai aka sha godiya da fatan ƙara samun danƙon zumunci.
Sai da Tasalla ta tafi yin alwala Inna da Tsahare suka samu keɓewa.
"Wai amini mai yake damunki ne, ke da kika zo birni dan ki murmure abinki sai kuma na zo na ganki duk a wani firgice?"
"Ke dai bari wallahi ZAMAN WANKAN nawa ne ya zo da wani salo"
"Kamar ya?"
"Yo Hassan ɗin ne miciji yake zama, tun da na zo a harƙalla ake dan wataran ma ina ake zama a ci abinci ana ta gudun famfalaƙi gugun ceton rai duk fa hankali ba a kwanceka yake ba, dan ma dai ina da ƙarfin hali ma da wallahi ba lallai ki same ni yadda kika ganni ba" Nan Inna ta shiga baiwa aminiyarta labari tun daga ranar farko da ta yi arangama da aljani har kawo yadda aka sha artabu da miciji da jama'a babu abin da ta rage mata amma dai bata faɗa mata labarin mala'ikan mutuwar da ya ziyarceta a daren jiya ba wanda shi ne silar dawowarta yadda ta ganta ba ta dai faɗa mata gabaɗaya hankalinta ya yi gida so take ta tafi in son samu ne gobe idan za su tafi ta bisu.
Sosai Tsahare ta sha dariyar artabun mutane da micijin da Inna ta bata musamman zuwan Malam mai sittin wata kan wata, da zuwan su Mama ranar da Imran ya sha yiwa Nigeri'a ranar da ya shiga tukunya kai ta sha dariya a wajen da Inna ta ce an rufe ta a freezer, da yadda suka yi artabu da ajani a bayi duk cikin labaran babu na yarwa dan dariya dai ta sha ta. Sai da ta tsagaita ta ce.
"Akwai dai wani abi da zai sa ki tafi dan na san miciji ba zai sa ki tafi ba da zai sa ki tafi da tuni kin bar gidan menene wannan wanda ya sanya har kika nunawa Tasalla ƙauna da kulawa haka? Lallai wannan ba ƙaramin abu bane"
Shiru Inna ta yi tana so ta faɗawa aminiyarta tana tsoron mala'ikan ya ce kar ta faɗa Haka dai ta ce mata babu komai.
Da yamma haka su Tsahare suka sauya kaya, dan gidan suna ya cika taf, yadda ba a yi zato ba dan duk an ɗauka ba za a zo ba saboda micijin to kuma cikin ikon Allah sai ma Hassan ɗin ya zauna a mutum bai zama miciji ba ranar sunan. Haka aka sha kiɗe kiɗe har da ƴan kiɗan ƙwarya, dakyar dai su Tasalla suka ja Inna wurin kiɗan ƙwarya ta ɗan taka rawa dan har da liƙi Imran da Abid da Sadiya da Ashrof suka mata sai dariya jama'a suke da yadda Inna take rawa da kuma yadda ake zuba mata kuɗi kowa yana murna dan gabaɗaya hankalin mutane sai ya dawo wurin kaɗan ƙwarya dan sosai Inna ke ba mutane dariya.
Haka dai taro ya watse kowa da kayan rabo masu yawa sai dai fatan Allah raya yara. Haka Imran ya koma gidan Hajiya ya kwana saboda baƙin Inna dan daɗi yake ji da ya ga ta ɗan saki jikinta ma.Haka suka yi hira sosai amma suna yin bacci Inna ta tashi ta kalli gabas haka ta kwana sallah da kazimi.
Washe gari haka aka yiwa su Tsahare sha tara ta arziƙi lemo Tasalla da Tsahare kowa katan Inna ta basu cake guda ashirin ashirin. Sannan ga wanda Sadiya ma ta basu sosai Inna ta so binsu amma Imran ya hanata dan yana so ta zauna a nan ita kuma ta zauna a nan dan yana ɗauke mata kewa haka dai ta zauna ba dan ranta ya so ba. Bayan suna da kwana biyu Imran da Abid suka zo da wani Malamin sunna ya shiga yiwa Hassan addu'a ya daɗe yana yi sannan aljanin ya bayyana kansa ya yi magana, a nan ya faɗi cewa tun lokacin da aka haifi yaran ya shigi Hassan, dan ko yadda bayan Hassan yake alamarsa ce ba wai a haka aka haifeshi ba duk da ana samun a haifi tagwaye da baiwar zama micijin amma shi na Hassan aljani ne. Haka aka fitar masa da shi sosai kowa ya yi farinciki da murnar hakan.
Inna dai ta ci gaba da rayuwarta wurin ƙanƙan da kai da komawa ibada da kasancewa da mahaliccinmu ko yaushe tana bauta masa, a haka ta cika kwana sha uku ana gobe kwananta sha huɗu za su cika sosai aka kasa gane kan Inna haka ta wuni kuka da neman yafiya kuma taƙu faɗar dalili, har Malam ma sai ta kira sau ba adadi tana neman yafiyarsa.
Ranar da kwanaki kuwa suka cika Inna bata magana sai ta bebaye dan kawai a sallaya take sai dai ta tashi ta sako alwala ta cigaba da sallarta. Kai har gari ya waye Inna bata mutu ba kwanaki sha huɗu sun cika har da kwana ɗaya amma shiru kake ji wai malam ya ci shirwa sosai Inna ta yi mmaki tana ta tunanin shin su ma mala'iku suna mantuwa ne? Ko kums yawan ibadarta ne ya sanya aka ƙara mata kwanaki, a haka dai ta ɗan saki jikinta amma kuma yawan ibada da lazimi ya gama shige mata jiki sun zame mata jiki duk da dama kasancewarta mau yawan ibada amma dai ta ƙara fiye da sanin mutum ga zuhudu (Gudun duniya) da ya ƙara shiga zuciyarta sosai. A haka ta yi kwana arba'in ɗinta ta haɗa kayanta ta je yiwa Hajiya da su Mama da Ashrof sallama suka haɗa mata sha tara ta arziƙi haka ta baro Sadiya da jariranta cikin ƙoshin lafiya duk da tana jin ba daɗi da za ta rabuwa da su Imran da Abid ne suka kaita har gida a motar Abid sosai su ma suka ji ba daɗi lokacin da za su baro garin su Inna sabo tirken wawa.
Imran ya nemi yafiyar Inna kan abubuwan da suka faru, har dai ma sai da ya bayyana mata cewa shi ne aljaninta kuma shi ne mala'ikanta.
"Kai Imirana amma ka iya shegantaka wallahi, yo Allah na tuba ai ka tsurar danu gabaɗaya ka sanya ina jiran ranar mutuwa ta" Cewar Inna tana dariya shi ma da Abid dariyar suka yi , aikuwa Inna ta ce ta yafewa Imran shi ma ta nemi yafiyarsa, suka baro Inna suna kewarta dan har suka shiga garin Kano labarin Inna kawai suke suna dariya irin yadda ta sha yin abubuwan abin dariya da cikin mutum zai ƙulle.
Tun da Inna ta koma gidan Malam zaman lafiya ya wanzu tsakaninta da Tasalla sosai Malam yake jin daɗin zama da su yanzu. Inna kuwa kullum ta tuno Imran ne silar gyara rayuwarta sai ta ji daɗi ta rinƙa sanya masa albarka.
"Ina son ku masoyan ƳAR ZAMAN WANKA KWANA ARBA'IN, musamman ƴan paid grp wanda suka biya kuɗinsu domin cigaban labarina da na Hassan da kuma Imirana, yo Allah na tuba ai ba zan manta da ku ba" Cewar Inna tana ɗagowa masoyanta hannu🙌
Alhamdulillahi kasiran, ina godewa Allah dabya nuna mini farko da ƙarshen littafin nan, ina godiya ga masoyana a duk inda kuke musamman wanda suka biyani kuɗi dan bibiyar labarina na gode sosai da sosai son so fisabilillahi!
Ina neman afuwar dj wanda na ɓatawa a ckn rubutun nan da ya yafe mini ko ma ba a kan rubutun bane ina neman afuwar kowa, dama ɗan adam ajizi ne😿🙏
ALƘALAMIN MMN AFRAHH BA YA RUBUTA SHIRME😍🙋♀️
Allah bamu ikon gabatar da ibadunmu lafiya Allah sa a sallace da mu muna raye lafiya🙏
🙋♀️🙋♀️🙋♀️