Showing 36001 words to 39000 words out of 56867 words
kuka almajiransa ya cika masa kunne.
Inna kuwa zuwa ta yi ta ɗakko wani dogon icce ta dawo windown ta tsaya sai da ta ga Malam ya juyar da kansa can baya hango ta sai ta sanya iccen ta cikin windown ta miƙa har sai da ta kai iccen wajen wuyan Malam ta zungura iccen ya dungurewa kan Malam ta kuma caka masa a wuya, da sauri ta janye iccen ba tare da Malam ya gani ba.
Wani uban ihu da Malam ya saki duk ya kiɗime ya gigice sai wata karkaɗa kai yake da sauri da sauri yana sanya hannu yana dukan wuyansa ya ce.
"Shikenan kuma yau aljannu za su yi yaƙi a ɗakin nan, dan sun fara caka mini farcensu a wuyan da kaina sun ƙi bayyana yau kuma sai yadda hali ya yi ni da almajiraina" Ya faɗa yana ɓare baki kamar wani ƙaramin yaro, Inna kuwa tsabar dariya ta kasa furta komai har sai da ta tsagaita da dariyar sannan ta ce
"Ka cewa aljannun su miƙo maka dorinarka da galan ɗin ruwan addu'ar da kuka zo da shi da kuma waccen hular ba kai bane mai fitar da su ai sai ku shiga fafatawa"
"Rufa min asiri dan Allah wallahi ba dai ni ba, ina ni ina yaƙi da iyayena"Cewar Malam yana kuka har lokacin.
"Iyayenka kuma aljannun ne iyayenka?" Inna ta tambaya cike da mamaki.
"Au wallahi suɓutar baki na yi, ku yi haƙuri mutanen ɓoye, yo abinka da su ba ganinsu ba ake yi" Cewar Malam yana wani waige-waige dan kar aljannun su fara masa hukunci tun ba a je ko ina ba.
Ganin miciji ya daina kai kaisa wajen su Habu ya miƙo wajen Malam tuni ya manta da batun aljannu wani irin haɗiye kukan da yake ya yi yana dannewa dan kar ya yi kukan, kallon kallo ake shi da micijin Malam ji yake kamar ya ɓace ɓat ko kuma ya suma dan ya daina ganin wannan micijin a kusa da shi in yaso idan micijin ya tafi sai ya farfaɗo. Ahankali micijin ya ɗauke kansa daga kusa da Malam ya koma da shi jikin fanka ya shiga warware jekar daga naɗewar sai da ya gama idanun Malam da su Ƙasimu sun zazzaro su har sai da suka ji jijiyoyin idanun sun ɗame duka wato babu yadda ma za a yi su ƙarawa idanun nasu fitowa saboda sun gama fitar d su har ƙarshe. Kafin meye wannan micijin ya yi wani tsalle sai gashi a tsakaninsu, dama Habu da Ƙasimu a jere suke sai Malam daga gefe, a tsakanin Ƙasimu da Malam micijin ya sauka sai Ƙasimu da Habu suka haɗe a wuri ɗaya Malam ya kasance warewa, shi kaɗai a gefe idanu ma Malam ya runtse saboda yadda zuciyarsa ke buga masa da mugun ƙarfi kamar za ta faso ƙirjinsa ta fito. A take micijin ya shiga juyi kamar mai rawa yake kawai, Inna kuwa sai dariya take cikinta har ciwo ta ji yana mata dan ta daɗe bata yi dariya haka ba, ko sararawa bata yi.
Wani uban tsalle Habu da Ƙasimu suka yi sai gasu sun diro a tsakar ɗakin sun bar Malam shi kaɗai a sama.
"Kash lallai in ba mutuwa to akwai tsofa, yau na ga ranar samartaka, in ba dan tsufa ba, ina za a barni a kan lokar nan, da lokacin samartaka ta ne ai da na riga kowa dirowa" Cewar Malam yana kallon micijin fuska shaɓe -shaɓe kamar dai ba shi ne Malam mai sittin wata kan wata ba.
"Yanzu ma lokci bai ƙure maka ba ka diro in ya so in ka karkarye sai a tattara ƙasusuwan naka a watsar" Cewar Inna da har lokacin bata bar masa dariya ba. Malam yana shirin bata amsa sai gani ya yi micijin ya ɗan tashi sama kaɗan sai da ya je saman kansa ya tsaya , Malam ba ɗaga kai ya yi ba idanunsa ne suke kallon saman kawai lumfashinsa ma ya tsaya cak, ko idanunsa ba ya so ya ƙifta tsabar tsoro da kaɗuwar da ya yi.
"Suma ka yi ko mutuwa ka yi, nanga ka kafe idanun naka a sama?" Cewar Inna sa ke kallon idanun Malam kafe a kan micijin. Malam dai babu bakin magana kawai kallon yadda micijin ke tsaye a kan iska ya miƙe duka tsawonsa.
Kafin Malam ya ankara kawai sai jin micijin nan ya yi a wuyansa gabaɗaya ya masa ƙawanya ya nannaɗe sai da micijin ya gama naɗe jikinsa tsaf a jikin Malam sai kuma ya kwallaso kansa ya dawo da shi saitin fuskar Malam ɗin ya zamana sun yi ido cikin ido. Malam bai san lokacin da ya saki numfashinsa ba wanda ya riƙe, ya maido da idanunsa daga kallon sama zuwa kallon fuskar micijin.
Irin halin da Malam ya tsinci kansa a ciki abun ba a magana shi kansa ba zai iya misaltawa ba ya san dai yana cikin gagarumar matsala da tashin hankali. Bakinsa yake so ya buɗe ko Allah zai sa ya iya tuno wata aya daga cikin qurani ya karanta ko kuma wata addu'a daga cikin addu'o i ya karanta dan neman ceton Allah maɗaukaki dan ya san yanzu shi kaɗai ne zai iya kawo masa ɗauki dan almajiransa ma sun juya masa baya, amma gabaɗaya sai ya ji bakin nasa ya masa nauyi ya kasa furta ko da kalma ɗaya ce. Cikin dddagewa ya fara iya motsa laɓɓansa suka fara ɗan motsawa kaɗan amma ba komai yake cewa ya, da ya fara ƙoƙarin maganar ma sai ya ji babu wani sauti da ke fitowa daga bakinsa. Abin da kawai ya sani yana iya jiyo saukar hawayensa daga idanunsa tamkar wani ne ya cika buta da ruwa yake kwararo masa a fuska haka yake jin zubar hawayensa da gudu ko ƙaƙƙautawa babu.
Haka dai ya rinƙa yaƙi da bakinsa dan karanto addu'a amma ina bakin Malam dai ya yi mirsisi tusar ango, babu alamar ma zai bashi wata dama da zai furta komai a fili bare kuma a zuciyarsa, zuciyar da tun da micijin ya naɗe wuyansa ya ji ta doka da uban ƙarfi har zuwa lokacin bata tsagaita ba da bugawa bare ta bashi wata dama ko ta samu natsuwar da za a yi addu'a a zuciyar.
"Ɗiɗiiiiit, jiiiiiin" Cewar Malam dan komai ya kwance masa shi yasa ya fara hourn ɗin mota. Ƙasimu da Habu duk da halin sa suke ciko sai da suka fashe da dariya.
"Minjaye" Cewar Inna da ƙarfi dariya na cin ta dan ta lura addu'ar ma ta gagara a wajen Malam, Malam kuwa da ke cikin halin neman taimako jin abin da Inna ta faɗa bai tsaya wata-wata ba ko tunanin me Innar ta faɗa na sai jin bakinsa ya yi kamar wanda aka yiwa dabaibayi a bakin aka kunce, haka ya ji, saurin fisgo maganar ya fara faɗar abin da Inna ta faɗa dan sai ya ji tamkar ta sanya shi a hanya ne ta sama masa mafita. A take ya fara biya abin da ta faɗa.
"Minjaye, mi'ara, ba ta ɗauri ba, baba kenan" Cewar Malam yana kuka yana fitar da maganar kamar wani ya masa dole. Tun da ya faɗa yake ta faman maimaitawa ko tsayawa ba ya yi Inna kuwa kamar ta samu Tv haka ta maida Malam babu abin da ke bata dariya iron yadda ruwan hawayensa ke kai komo, a fuskarsa kamar wanda ya wanke fuskar, gabaɗaya hankalinsa a tashe yake da yadda micijin yake har lokacin nannaɗe a jikin wuyansa kansa kuma a wajen fuskarsa.
"Wa maa ƙadarullaha haƙƙa ƙadrihi" Cewar Habu dariya na cinsa ai kuwa Malam ya kama ayar gagam ya riƙe sai maimaitawa yake yana kuka.
Dan a take ya saki waccan jiniyar motar da yake yi ya kama wacce Habu ya faɗa masa. Sai da ya maimaita kusan sau hamsin ko dakatawa ba ya yi sannan a take ya tuno da wani karantun ya fara.
"Wallaili iza yagshe, wannahari iza ta jalle, wama kalaƙazzakara wal unsee, inna sa'ayakum lashatte,wa ammaa man a'aɗawattaƙe" Haka ya rinƙa janyo ayoyin yana kuka, amma daga ya je iya ayar da ya karanta sai ya dawo farko ya kasa ƙarasa surar har zuwa ƙarshe. Yana cikin yi sai Ƙasimu ya ƙara ɗora shi a kan wata surar.
"Wadduhe"
"Wallaili iza saje, ma wadda aka rabbuka wama ƙale" Cewar Malam cikin sauri-sauri dan duk wanda ya ji ya janyo masa aya sai ya saki wacce yake karantowa ya kama wadda aka karanto ɗin dan shi kawai so yake ya kamo ayar da za ta masa sha yanzu magani yanzu. Su Ƙasimu da Habu da kuma Inna da suka shagala da masa dariya ya yi dibara ya sauke idanunsa ƙasa ya hangi yadda suke dariya wani haushi ne ya turnuƙeshi ji yake da zai iya sai ya fita ya shaƙo Inna ta ƙarfin tsiya ya shigo da ita ɗakin ya sanya musu micijin a wuyansu ita da su Ƙasimun su ji yadda ya ji.
"Allahu, Arrahmanu, Arrahimu, Almaliku Alqudusu Assalmu" Malam da ya runtse idanunsa da ƙarfi dan ya daina ganin takaicin abin da almajiransa da Inna ke masa da kuma ganin fuskar micijin a kusa da tashi ya kamu sunayen Allah yake karantowa. Idanunsa na rufe ya fara jin riƙon da aka yiwa wuyansa ya sassautu, a hankali ya ɗan ƙyalla ido ɗaya ya buɗe aikuwa sai ya ga babu kan micijin a kusa da fuskarsa kawai sai ya buɗe ɗaya idon ma a take ya fara gani ashe micijin ne ya shiga warware jikinsa daga wuyansa, daɗi ne ya ziyarci zuciyar Malam yana ganin micijin har ya bar jikinsa ya yi wani uban tashi ya sauka daga kan drower ya je ƙasa wurinsu Ƙasimu ya nufa da ke yiwa Malam dariya ko lura basu yi da micijin ba sai ji suka yi ya nannaɗe wuyansu lokaci guda su biyun ya haɗa wuyansu ya kanannaɗe su.
[24/03, 5:14 AM] Mom Mashkur First class: *MAMAN AFRAH DATA SERVICES*
*BUY DATA FROM THE AFFORDABLE PRICE*
*I selling MTN data with this cheap price*
*MTN DATA PACKAGE*
500MB@===150
1GB@=====250
2GB@=====500
3GB@====850
5GB@====1,400
Dial *312*4*7*4# to check Data balance.
*Validity 1 month*
*Airtel,9mobile and Glo* *also available.*
*Subscription for DStv gotv star time electric pay bills*
Act details FA'IZA ABUBAKAR unity bank 0020281885
Whatsapp OR
Call 09033283375
Wannan littafin kuɗi ne 300
Za a tura ta wannan accaunt ɗin Fa'iza Abubakar 0020281885 Unity bank shaidar biya ta wannan no 09030283375 idan katin waya ne mtn Ƴan Niger su tuntuɓi wannan no +22785885134
3️4️⃣3️⃣➡️4️⃣4️⃣
"Duk kun sauka kun barni, aikuwa inda ba ƙasa nan ake gardamar kokawa, in ka ji kana ba za ka iya ba bai kama ka bane" Cewar Malam ya rintse ido ya diro daga saman, duk da ya ji zafin faɗowar amma haka ya jure tare da daurewa ya miƙe tsaye cikin hanzari, wurin window da Inna take ya nufa idanun nan jajawur da su, duk da yana jin kururuwar su Habu amma saboda abin da suka masa sai bai bi ta kan su ba duk da dama ko da ya bi ya kan nasu babu abin da zai iya kusu.
"Dan Allah dan darajar iyayenki da ƙaunar manzo S.A.W ki buɗe ƙofar nan wallahi wannan tashin hankali bashi ma da daɗi ji bare daɗin gani" Cewar Malam cikin sanyin murya tare da haɗe hannuwa alamar roƙo.
"S.A .W, aikuwa dai tun da ka haɗa ni da Allah da kuma manzonsa, da kuma iyayena, to zan buɗe amma da sharaɗi...
"Wallahi kowane sharaɗi ne zan bi, matsawar dai za ki buɗe ƙofar" Malam ya katse Inna cikin hanzari.
"Wallahi fa ka ce"
"Eh haka na ce wannan alƙawari na ɗauka, ko da cewa kika yi in baki gabaɗaya ladan aikin da za a bani wallahi duka zan baki ba zan ɗau komai daga ciki ba"
"Sai cewa kake ladan aiki wai shin ka yi aikin ma? Kai kan ka baka da nutsuwar da za ka yi aikin, kawai sharaɗi zan gindaya maka"
"To, to, to na yarda"
"Duk abin da na ce ka yi ba za ka mini musu ba"
"Wallahi indai ba saɓon Allah bane zan yi"
"Ɗakko hiraminka da carbunanka ka tsaya daga jikin ƙofar" Cewar Inna tana wani murmushi Inna ta yi tare da barin windown ta dawo falo ganin Sadiya zaune ta buga uban tagumi ta taɓe baki tare da ɗauke kan ta, ƙofar ta nufa ta buɗe. Malam yana jikin ƙofar riƙe da carbunansa, su kuma sauran har lokacin suna haɗe kamar yadda micijin ya haɗe su ta hanyar laulaye wuyansu da ya yi, sai kuka suke suna zare idanu.
"Bani su nan" Cewar Inna da bata wani buɗe ƙofar duka ba, sai da ya miƙa mata,ta ce ya durƙusa ya miƙo mata wuyansa. Mamaki ne ya cika Malam amma sabodanba ya sp ya musa mata ya kasa cika alƙawari, sai kawai ya zubar da gwiwoyinsa a ƙasa, carbunan wannan duka biyun ta saƙala masa a wuya da yake dama suna da girma, sannan ta saƙala hiramin ma a wuyansa ta ƙulle, yana durushe dai yana jiran tsammani.
Ɗan leƙa kanta ta yi sai ta ga Habu ya ci nasara micijin ya saka masa wuya sai Ƙasimu kawai ya naɗewa wuya, zo ya ka ɗan nan taho da rarrafe cewar Inna tana kallon Habu da sauri ya taho har yana ɗan neman faɗuwa, yana zuwa Inna ta ce to tashi yau za a rama maka abin da ka yi na shekara da shekaru, da kake riƙon aljani, tun da dai Malaminka ne ya gayyatoka wannan gida to bisa adalci shi ne zai fitar da kai" Cewar Inna su kuma sai kallonta suke burinsu kawai su bar ɗakin basa buƙatar wannan dogon zancen nata.
"Tashi ka hau bayan Malam" Cewar Inna tana kallon Habu.
"Bayan Malam kuma" Habu ya faɗa yana kallonta.
"Hau Habu babu komai ka san alƙawari kaya ne na kuma riga da na ɗauka cewa zan mata duk abin da ta buƙata. Cikin cika umarni Habu ya tashi ya ɗare bayan Malam, Malam ji ya yi kamar an jibga masa buhun hatsi biyu a bayansa, amma haka ya daure har da cije leɓe.
"To Isuhu za ka fara hamimiyar doki " Cewar Inna tana riƙe da hirami da kuma cabunan da ke wuyan Malam tamkar ta samu linzamin doki.
Haka ta ƙara janyo ƙofar ta rufe tana jan hiramin wuyan Malam yana ta hamimiyar doki a haka suka fito yana ɗauke da Habu a gadon bayansa yana rarrafawa irin yadda yara ke wasan doki dakyar yake jan gwiwoyinsa amma haka ya daure dan kawai fatansa ya fita daga gidan ma baki ɗaya ba wai ɗakin kaɗai ba.
Sadiya kallonsu kawai take Malam ya daddage sai hamimiya yake ko hutawa ba ya yi, dariya haɗe da tausayi ne suka haɗewa Sadiya lallai Inna ita ce maganin kowane ɗan guguwa, a haka suka je har bakin ƙofar gida suna zuwa Inna ta ce Habu ya sauka haka ya sauka ta nuna masa gabas aikuwa da uban gudu ya zuba ko waiwaye ba ya yi. Sannan ta ƙara janyo Malam yana ta hamimiya ta dawo da shi falon ta tsayar da shi a wajen ƙofar bedroom ɗin ta buɗe ƙofar a hankali ta leƙa aikuwa sai ta ga micijin ya saka wuyan Ƙasimu ya kwanta a ƙasa da alama bacci ma ya yi, sai Ƙasimun yana rarraba ido.
"Ƙasimu" Cewar Inna.
"Na'am" Cewar Ƙasimu.
"Taho ka sha goyo" Cewar Inna tana dariya.
"To" Ya ce yana ɗan lallaɓawa ya kewaye micijin cike da tsoro ya nufo ƙofa ya fito haka shi ma Inna ta sanya ya haye bayan Malam ɗin duk da ba a san ransa ba, a haka ya hau Malam takaici ne ya cika masa ciki wai yau almajiransa da ke matuƙar girmama shi su ne a gadon bayansa kuma ma dan wulaƙanci yana hamimiyar doki, wannan abu ya ƙona masa rai sai dai ba yadda zai yi. A haka suka fito daga falon suna shirin nufar zauren gidan sai ga Abid da Imran suna ƙoƙarin shigowa kowa riƙe da kaya. Imran ya haɗu da Abid ne a wajen gyaran machine ɗinsa da ya lalace masa a hanya shi ne ya tsaya za a gyara a nan suka haɗu da Abid ya ɗaukeshi a mota suka bar machine ɗin a wajen gyara tare suka je suka siyo duk kayan da za a buƙata na rabon sunan. Da mamaki, bakinsu ya kasa furta sallamar da suke ƙoƙarin yi dama shi Imran ya yi mamakin ganin ƙofar gidan nasa jingine a jikin bango an barta a buɗe, gashi kwata-kwata ya ma manta da cewa Hajiya ta sanar da shi za a yi baƙon malami mai ruƙiyya. Abid kuwa baki ya saka galala yana kallon Inna riƙe da lunzamin wuyan da ta yiwa Malam da hirami da carbi shi kuwa ya tara gumi gabaɗaya ga wannan garsamemen ƙato a bayansa yana rarrafe da hamimiya tamkar a filin tseren dawakai.
"Woooo Inna tamu ta amana, waye kuma wannan ya yi arangama da hukuncinki dan na san dai ruwa baya tsami banza" Cewar Abid cike da sheƙiyanci dan ya shaida Malam Isuhu saboda akwai lokacin da ya je gidan wani ɗan uwansu zai yiwa wata budurwa ruƙiyya tana fama da aljannu haka kawai ya je suka yi ta libgarta da dorinai ashe ba wani ilimin azo a gani gareshi ba sai cin kuɗin mutane kamar masifa da shegiyar ƙafafa shi ala dole malami.
"Abida, kai ne yau a gidan namu lallai wata sabon gani, ni wallahi har na gaji da jajenka a zuciyata kwarankwatsa na ɗauka ma ko mantawa ka yi da ni" Cewar Inna tana washe baki ganinsu riƙe da kayayyki duk da dai dama ta yi murna da ganin Abid ɗin.
"Wai Inna meye hakan ya za ki kama babban Malami ki masa wannan cin fuskar...
"Kai yaro iya bakinka ni nan wannan abin da take min ba wani abin zafi bane a wajena, idan aka kwatanta da halin da na fito babu ruwanku ni nan na san duk cikin umarni ne da cika alƙawari" Malam ya tari numfashin Imran da ya haƙiƙice yana faɗa, shi kuma Malam abu ne ya