Showing 45001 words to 48000 words out of 56867 words
Ajimum Mayan suke cewa amma a haka suke ta yi suna dawo wa farko har sai da Inna ta gaji ta ce su dakata.
"Yanzu kuma abin nan da kuke cewa leee ray(left right) Wanda kuke yi kuna ɗaga ƙafa dama da hagu kuna bugawa a ƙasa wanda da ake cewa mai tsumman (letf) Marar tsumman(right) Shi za ku yi amma a maimaikon leee, ray, sai kuke cewa Azumi (left) Malam (right).
Babu yadda suka iya haka suka fara bin umarnin Inna suna buga ƙafa suna kiran sunanta da na Malam a maimakon left right.
Tun suna yi da ƙarfinsu har sai da suka gaji sun jigata sosai, sannan Inna ta dakatar da su, ta ce su fito su kalli gabas za ta shiga ɗakin su yi magana da Hassan ta bashi haƙuri ya ɓace, bayan sun mata alƙawarin mayar da ita gida ba tare da ko lakuci ba, har rige-rigen fitowa suke daga ɗakin da ta buɗe ƙofar suna fitowa suka kalli gabas wato sun baiwa ɗakin baya tana shiga ta kulle ƙofar sai da ta tabbatar basa gano ta sannan ta ɗaga micijin robar da ta tsinto a wannan gidan da ƴan kidnapping suka ɗauketa, lokacin tana ta zagayawa a cikin gidan ta ganshi, da farko ita ma ta tsorata amma daga baya sai ta gane ba na gaske bane saboda matuƙar dai baka taɓa shi ba ba za ka gane ba haka yake kamar micijin gaske sai ka taɓa za ka ji wani latsotso kamar wata leda mai laushi amma ba roba bane.
dan haka sai ka ɗaga wajen cikinsa a nan ne tillar da ake hura micijin take a rufe da murfinta, dan haka da sauri Inna ta buɗe tillar ta sace micijin ta linke ta mayar ɗan tofinta ta zige zip ɗin. Dama tun lokaci da ta gani a gidan ta ɗakko dan idan ta koma ƙauyensu take hurawa tana tsorata Tasalla, to ganin ranar nan daga fitowarta ana sace ta a matsayin wata dan haka ta ce yanzu duk inda za ta je da shirin ko ta kwana za take tafiya saboda tsaro ba dan tsoro ba. Shi yasa ma ta taho da ƙaiƙayinta mai barkono da ya daɗe a ajiye a jakarta ashe kuwa da walakin goro a miya sai gashi sojojo ya sa an ɗakko ta sai ta yi amfani da su ta dan ceton kan ta gashi kuwa sun mata rana.
Sai da ta tabbatar ta gama ta ce su shigo su gani, ai daga window ma suka leƙa dan a tsorace suke, ganin babu micijin babu dalilinsa sai suka ƙara shan jinin jikjnsu.
Haka ta ce sai abokin Imran ne ma zai kai ta gida haka ya shiga ya sako kayansa babu yadda ya iya ya buɗewa Inna mota ta shiga ya rufe kamar yadda ta buƙata. A hanya ma haka ta sa ya tsaya ta rinƙa sa shi siyayya ta babu gaira babu dalili har sai da ya ji ya yi da na sanin, sanin Imran ma ba ma da na sanin ɗakko ta kaɗai ba, har ƙofar gida ya kawo ta, ta ce ya shiga su gaisa da su Sadiya ya ce mata a'a .
"To sojojo ka gaishe da matarka tsohuwa mai shafa jambaki kamar akuya ta ci dusa" Cewar Inna da ke tsaye riƙe da ledoji hagu da dama riƙi-riƙe da kayan siyayyarta. Wani kallon takaici ya mata ganin sai dariya take ya ja motar ya bar wurin a sukwane.
" Sai ni Azumin Malam wallahi ni gaba ta kai ni gobarar titi" Cewar Inna tana juyawa ta shige gida abin ta.
Masu fitar mn littafi ku ji tsoron Allah, da tsoron haƙƙina.
09030283375
[24/03, 5:14 AM] Mom Mashkur First class: *MAMAN AFRAH DATA SERVICES*
*BUY DATA FROM THE AFFORDABLE PRICE*
*I selling MTN data with this cheap price*
*MTN DATA PACKAGE*
500MB@===150
1GB@=====250
2GB@=====500
3GB@====850
5GB@====1,400
Dial *312*4*7*4# to check Data balance.
*Validity 1 month*
*Airtel,9mobile and Glo* *also available.*
*Subscription for DStv gotv star time electric pay bills*
Act details FA'IZA ABUBAKAR unity bank 0020281885
Whatsapp OR
Call 09033283375
Wannan littafin kuɗi ne 300
Za a tura ta wannan accaunt ɗin Fa'iza Abubakar 0020281885 Unity bank shaidar biya ta wannan no 09030283375 idan katin waya ne mtn Ƴan Niger su tuntuɓi wannan no +22785885134
3️4️⃣7️⃣➡️4️⃣8️⃣
*TASALLA*
Gabɗaya ta kasa zaune ta kasa tsaye saboda tsananin murnar tafiya birni suna, sunan da ba a san da zuwanta ba kyma ba wai shiri suke dz wacce za ta je sunan domin ta bane kawai dai ƙarfin hali ne ɓarawo da sallama. Tun da aka ce yau alhamis take ta shirye shirye saboda Tsahare ta faɗa mata cewar da sassafe za su tafi sunan wato ranar sunan kenan ranar juma'a. Kuɗaɗe masu yawa ta karɓa a wajen Malam dan ta ce masa kar a je suna babu wani abin a zo a gani dan jaka ta yaudareshi kuɗaɗen da suka fi wanda za ta yi amfani da su yawa.
Fura dakan mai ta ce za a yi, ta sha sugar da man shanu dan haka hatsi ta auna ta bayar da duk abubuwan buƙata na aikin furar da ladan masu yin furar dan akwai gidan da ake yin furar in mutum yana so sai ya biya a masa. Galan kuwa ta samu ta ɗure nono a ciki wanda za a kai gidan sunan haɗe da furar duk tana yin hakan ne dan kar Inna Azumi ta kunya tata, tana ganin in ta je da ɗan abin arziƙi ko ma menene zai zo da sauƙi.
Ƙafar nan ta sha ƙunshi kamar ba gobe sosai lallan ya kama aka ɗauki wani baƙin gishirin ƙunshi aka sanya, ga ta tanadi kayan da za ta saka idan za su tafi da kuma wanda za a ta sa ranar da za su dawo washe garin suna duk da ba haka ta so ba da son samu ne ta fi so ta zauna ta taya Inna ZAMAN WANKAN ita ma ta ɗan murmure sannan idan Innar ra tashi dawo wa sai su dawo tare . A ɓangaren Malam ma murna yake da tafiyar da Tasalla za su yi zuwa suna saboda yana ganin wannan ne abin da zai shirya tsakaninsu, yana kuma addu'ar Allah haɗa kawunan su komai ya zo ƙarshe a tsakaninsu na rashin jituwa.
Hakan ne ya sa Malam yake bada duk abin da ta buƙata kuma shi daɗi yake ji da ya ga tana murna, dan da abin har haushi yake bashi yawan fitar ta zuwa gidan Tsahare wani lokacin ma baya sanin ta fita sai ta dawo idan ya tambaya daga ina take sai ta ce ta je tambayo Tsahare ne ya shirye shiryen tafiya, ko gajiya bata yi da zuwa gidan Tsahare zancen tafiyarsu dan idan ana maganar tafiyar ba ƙaramin daɗi take ji ba, duk ta bi ta bama yaɗawa cewa za su tafi birni. Dan haka yanzu komai ya haɗu gobe kawai ake jira a ɗau hanyar Kano suna.
*INNA*
Tun bayan da ta dawo Sadiya ta gan ta da kaya riƙi -riƙe lokacin suna zaune da Imran dan har magriba ma ta kusa yi, haka ta shigo da ledojinta tana ta washe haƙora bakinta ɗauke da sallama
amsa mata suka yi kowa na kallon hannunta da mamaki, haka ta shigo ta zauna abinta tana ta fito da kayayyaki tana washe baki.
"Inna ina kika samu wannan kayan?" Cewar Sadiya tana kallon Inna da mamaki.
"Kai haba Sa'adiyya wannan tambaya ina dalili sai ka ce wata budurwa tsofai-tsofai da ni ki zauna kina mini tambayoyi kamar wata budurwa, yo Allah na tuba ai budurwa ya kamata a yiwa wannan tambayar in an ganta da wasu baƙin kaya a tare da ita, dan gudun kar ta ɓaci amma tsohuwa da ni kike min tambayar ƙwaƙwa" Cewar Inna tana kallon Sadiya tare da maida kallonta kan Imran ta ce.
"Ko ba haka ba Imirana, ai gaskiya na faɗa ko?" Cewar Inna tana kallonsa.
Haɗe rai ya yi ya kauda kai gefe.
"Ikon Allah ni ma mai ya kaini tambayarka dan na san ko dai dai na faɗa ba zaka faɗi gaskiya ba uban mugun halin tsiya haushi kake ji na baiwa Abida labarinka to ya za ka yi da ni ai ni na ci dubu sai ceto" Ta faɗa tana cigaba da fito da kayayyakin.
"Wai dan Allah Inna wa ya baki kayan nan, ranar nan kin ce wanda suka ɗauke ki ne suka baki yau kuka fa"
"Oh ni Azumi na ga ta kaina, yanzu Halima dole sai kin tambaya saboda niyya, to yau ɗin ma ɗaukeni aka yi" Ta faɗa hankali kwance.
"Haba Inna kullum dai kika fita sai an ɗauke ki sai ka ce kuɗi"
"Ke dalla can yau sojojo ne abokin Imirana ya aiko sojoji suka ɗauke ni a mota suka kai masa ni, shi ne na yi yadda na yi na ƙwato kaina"
Gabaɗaya kallonta suke da mamaki sun san sai tabbas Inna babu yadda za a yi ta haɗa wannan maganar"
"Wai da gaske Inna" Cewar Sadiya tana kafe ta da ido shi ma Imran ɗin kallonta yake.
"Yo ƙarya zan miki ɗiyar nan wallahi da gaske, aikuwa sun ga tijara gaba da gabanta aljani ya taka wuta, hummm ai ni Azumi an buga an barni"
Nan Inna ta kwashe labari kaf ta faɗa musu, daga Sadiyar har Imran ɗin dariya suke yadda Inna ta yi wasa da hankalin sojojin kaɗai ya isa ya baka dariya, basu sha dariya sosai ba sai da ta fito da micijin nan ta hura ta ajiye shi suka yi ta dariya suna jinjina ƙoƙari da kuma ƙarfin hali irin na Inna.
Tun da aka yi sallar isha'i Inna ta kwaɓa lallenta dan ta ce da shi za ta kwana a ƙafarta dan ya kama sosai. Haka ta jiƙa lallen ta tanadi ledoji tana ta rawar ƙafa za ta yi ƙunshi gobe suna. Bayan ta kwaɓa lallen suna zaune da Sadiya suna ɗan taɓa hira Imran ya fita lokacin, Inna ta kalli Sadiya ta ce.
"Ke yanzu Sa'adiyya ina iliminki na mahammadiyya a ce kina da ilimin addini amma kin bari ana kawo miki Malamin da bashi da wani ilimi gida duk da dai ba da son ranki aka kawo shi ba, ai kamata ya yi ki zauna ki tofe ɗanki da addu,'a dan matsawar yaron nan yana siffar miciji to kuwa ƙwara ma ki haƙura da taron sunan dan duk wanda ya ganshi to tsoro zai sa ya gudu wasu ma ko tunkaro gidan ba za su yi ba.
" Cewar Inna tana kallon Sadiya da ta yi shiru tana saurarenta.
"Hakane Inna bari to na gani" Cewar Sadiya cikin sanyin murya, ta tashi ta ɗakko Hassan ɗin daga bedroom ta kawo shi falon inda suke. Gadon dama kawai ta ɗakko
Sadiya ta yi bismillah ta fara karanta ayatul kursiyyu, falaq da nas da sauran ayoyin kariya cikin hikima ta ubangiji tana cikin yi sai yaron ya fara sawaya a hankali a hankali da haka ya koma mutum sak, a take a wurin aka shiga bashi nono ya sha aka wankeshi aka musu shirin bacci.
Inna sai da za ta kwanta ta ƙunsa lallenta ta ƙulle da leda ta kwanta da shi.
*DARE*
Gari ya yi tsit baka jin komai sai haushin karnuka a sauran abubuwa. Imran da dama bakam ya yi babu alamar bacci ma a tare da shi ya tashi ya janyo ledar da ya shigo da ita ya ɓoye a ƙasan kujera ba tare da kowa ya sani ba. Kaya ne ya siya baƙaƙe riga da wando sai wata wacce ake ɗorawa daga sama wata buɗaɗɗiya haka ya sanya baƙaƙen kayan nan.
Sai da ya tabbatar ba ya jin motsin kowa sai tashin munsharin Inna da ke cika ɗakin. Cikin sanɗa ya ƙarasa ɗakin yana fara da addu:a kar a gano shi. Kan gadon ya tsaya ƙarewa kallo ta hasken wata ganin kowa baccinsa yake hakan ya sanya ya tabbatar har ya gama abin da zai Sadiya ba lallai ta tashi ba saboda nauyin baccin ta.
Inna da ke ta shararar baccinta na gajiya sai sakin munshari take abin ta, a hankali Imran ya yi dibarar cire mata bargon da ta rufa da shi dama ko fuskar bata rufe ba. Hannu ya kai jikin ƙafarta mai ƙunshi ya ɗan ja ƙafar shiru bata motsa ba har lokacin tana ta bacci tare da sakin munshari, ƙara jan ƙafar ya yi zuwa lokacin ta ɗan motsa cikin bacci ta ɗan janye ƙafar. Ganin bata tashi ba sai ya ƙara jan ɗaya ƙafar lokacin ne ta ɗan kai hannu ta doke inda take jin an taɓa amma idanunta a rufe suke. Duka Imran ya sakar mata ɗaɗe ai jin zafin dukan nan Inna sai gata a zaune tana rarraba ido. Kafin ta tantance abin da ke faruwa, da kuma waye wannan mai baƙin kayan Imran ya kausasa murya yadda ba za ta gane shi ba ya ce.
"A yau ne za ki koma ga Allah, za a tambayeki duk abin da kika aikata a duniya dan haka yanzu ranki ne kawai za a zare"
Wani uban bugawa ƙirjin Inna ya yi lokaci ɗaya gumi ya baibayeta, cikin tashin hankali cikinta ya bada ƙululuuuuu.
"Wayyo Allah na mala,ikan mutuwa ne, ni Azumi kenan kwanakina sun ƙare wayyo shikenan tafiya zan yi ko sunan ƴan biyun bana nan za a yi, gashi zan barwa Tasalla Malam" Cewar Inna a zuciyarta har lokacin gabanta na mugun bugawa.
Ba ƙaramin tsorata ta yi ba ganin Imran da baƙin kaya dan ƙafarsa ɗaya ya ɗora a kan gadon sai ya ɗan ranƙwafo tare da baza baƙar rigarsa hakan ya sanya Inna da ke a tsorace ta ga wani girmansa ƙiba da kuma faɗi. Gabaɗaya jikinta karkarwa yake dan a duniya Inna tana tsoran mutuwa kuma a ce yau gata ga mala,ikan mutuwa zai ɗauki ranta, babu abin da ke ɗaga mata hankali sai kwanciyar kabari wannan abu yana matuƙar tada mata hankali idan ta tuna kenan yau ita ma za ta kwana cikin kabari, yau za ta tafi inda ba a dawo wa yau za ta tafi inda iyaye da kakanni suka tafi.
Hannu Imran ya miƙa wajen ƙafarta mai lalle. Inna da tunaninta ya bata cewa ranta zai zare bata san lokacin da ta haɗiye yawun da ya taru a bakint ba ta fara ƙoƙarin haɗa kalmomi sai kawai ji ta yi ta yi ƙarfin halin cewa.
"Da lalle a ƙafar, ƙunshi ne" Wai tunaninta idan ya ji da lalle ko za a ɗaga ɗaukan ran nata wataƙila ma ba ɗaukan ran mutum idan yana da ƙunshi, amma a tunaninta.
"Ba ma son magana ki koma ki kwanta ki miƙe" Cewar Imran a fili a zuciyarsa kuma ya ce
"Ashe kina tsoron mutuwa to kuwa yau sai na tsurar da ke gabaɗaya kamar ydda kike surar da ni ki tsoratar da ni ki sani cikin bala'i da miciji"
Jirif kake ji Inna ta koma ta kwanta jikinta gabaɗaya ya saki, tana zazzare ido sai hawaye da ya fara kwaranya daga idanunta ganin ga ta ga Sadiya amma za a ɗauki ranta Sadiya bata sani ba. Ita kanta ji take kamar ta tashi ta gudu sai dai ta san ba a tserewa mutuwa duk inda ka je tana biye da kai ko yau ko gobe ko ɗazu ko yanzu ko anjima.
"Sa'adiyya gaki da nauyin bacci da na tada ki kin ga tafiyar kakarki Azumi mai ƙaunarki ina ƙaunarku Sa'adiyya ke da Asharofa da Malam amma zan tafi in barku fatana ake min addu'a bayan mutuwata" Cewar Inna a zuciyarta tana zubar da hawaye. Imran kuwa dariya ce ke neman ƙwace masa yadda yake ganin Inna na rarraba idanu ta saki jiki gabaɗaya ita ala dole mai mutuwa.
Ganin ya miƙo gannunsa sai jikinta ya fara karkarwa tana raya wa a ranta shikenan ita kuma tata ta ƙare shikenan ranta zai zare.
"Kai gwara dai ki miƙa hannu ki tashi Halima ai gwara dai a ce da wani a kusa da ke lokacin ɗaukan ranki lokacin da za ki bar duniya, oh ni Azumi duniya budurwar wawa duk ƙaunarka da duniya haka za ka koma ka barta to Allah kasa can ta fi nan" Cewar Inna a zuciyarta tana ƙoƙarin kai hannunta na hagu mai lalle wanda shi ne daga gefen da Sadiya ke kwance, tana ƙoƙarin miƙa hannunta kan Sadiya Imran ya lura sai da sauri ya ce.
"Ba a son motsi in ba haka ba za a zare miki ran da ƙarfi"
Da sauri Inna ta janye hannunta tana ta addu'a a ranta kar a zare mata rai da ƙarfi saboda ta san an ce fitar rai akwai azaba bare kuma a ce da ƙarfi.Hannu Imran yake miƙowa yana ƙoƙarin kai hannun jikin Inna ita kuma sai ɗan takure kan ta take tana ɗan ƙoƙarin matsawa ji take kamar ta tashi ta gudu sai dai ba dama.
Hannunsa ya miƙa ya kamo hannunta na dama saitin dantsen ta ya riƙe gam sai ya sanya ɗaya hannun ya kamo yatsanta na tsakiya, ai gabaɗaya sai Inna ta fara wata karkarwa, karkarwa take gifgifgif gadon har jijjigawa yake ita ala dole an zo mawar zare mata rai.
"La'ilaha illalahu, muhammadur rasukullahi, S.A.W" Cewar Inna tana kuka gabaɗaya ta sanya a ranta shikenan ita da duniya kuma an yi ban kwana tana ta fatan ta samu dacewa a can.
Wannan karkarwar da take da salatin da take ita ala dole shirin ɗaukan ranta ne da ake take yi dakyar Imran ya iya danne dariyarsa saboda bai taɓa ganin Inna ta shiga ɗimuwa da tashin hankali haka ba ya so akwai haske yadda zai ke ƙare mata kallo amma ina.
"Kai ni Azumi ashe haka tafiyar za ta zo, ashe haka mutuwa za ta zo mini ban shirya ba, duk da dai dama babu wanda yake mata shiri haka kowa ke tsintar kansa haka take zuwa ba sanarwa bare