Showing 1 words to 3000 words out of 48162 words

Chapter 1 - MUGUNTA-_FITSARIN-FAKO_-complete-by-MAman-Abdallah

10 Jul 2024

3347

???MUGUNTA FITSARIN FAkO ???

By

KADIDJAH BASHIR
Daga alqalamin ??????????
Maman Abdallah ??

YAR MUTAN AGADEZ CE


Free book
__________________________________________

?GORGEOUS WRITERS FROM?
?G W F
HOME OF GORGEOUS , INTERLLIGENT AND EXPRES WRITERS,WE THE BEST AMONG
?THE REST?
__________________________________________

wannan shine littafina na farko ina roqon Allah ya tabbatar mun da alkhairi a duk wani al'amarin danasa a gabana ina neman qoyan bayanku 100% Allah ya mana muwafaqa amine nagode ??

_Bismillahir rahamanir rahim_

Page 1

Tafiya take cikin sauri tana waiwaiye gudun kar wani idon sani ya ganta ,ba idon sani ba ko Wanda bata sani bata fatan ya ganta
yana daga cikin sharuddan aikin daya zame mata karfen qafa,ba latti kuma kar wani ya ganka yayin zartar da aikin
karfe 12h50 na rana adaidai wannan lokacin ta iso bakin qofar Wani madaidaicin gida,
gidan lakane amma an shafesa da siminti (ciment) 'qaramar kofar ta tura ta shiga tare da rufewa Kamar Kowane lokaci ,jingina tayi da bangon gidan tana maida nunfashi tana qara maimaita kalmomi guda biyu Wanda sune sanadin zuwanta gidan a wannan karon ,ina jinki taji Magana kamar Daga sama inda sabo ta saba haka halinsa yake tin tana jin tsoro intazo har ta saba yanzu tsoron ma bataji, barazanar dayake mata ita kadai take firgitata yariga da yasan rauninta siyasa yake bata wahala
yi magana inada abunyi yayi magana cikin yanayinsa na rashin walwala
Dama naji yana wayane amma ban fahimci komai a zancan saba saidai naji ya ambaci wasu kalmomi guda biyu *M K* se kuma *G Z J*. Shiru yayi yana ?ara maimaita abunda ta fadi a ransa kafin yace okay ba damuwa ni zanyi tafiya kuma inasaran 2week zanyi wannan aikin ma naki ne kitabbatar kafin indawo kinsamo duk wani informations akan wa'annan kalmomin kuskure daya da zakiyi daidai yake da nunfashin Muhammad na qarshe kinsan zan iya, yayi maganar cike da gargadi
da sauri ta girgiza kai tare da fadin insha Allah zan kiyaye nuni yayi mata da hanyar fita ?? batare da yayi magana ba ta fuce daga gidan
daidaita nutsuwarta tayi ta fara tafiya seda tazo bakin babban titi ta sami abun hawa tayi Sa'a daidai ya sauke wata mata ita kuma ta shiga.. aikin tunanin daya kasa qaremata ta shiga yi jin shurun yayi yawa ne dan adaidaita sahun yace hajia ina muka nufa ajiyar zuciya ta sauke me karfi kafin tace ( jaune cadre) batare da ya sake yin maganaba yaja suka fuce ,daidai wani tanqameman gida suka tsaya Wanda fadin haduwar sa bata lokaci ne,ko ta waje gidan ya tsaru ta ciki ko se Wanda ya gani
1000f(1k) ta bashi bata jira amsar canji ba tafara buga kofar gidan wanda ita kanta abin kallo ce ,baba habu me gadi ne ya le?o ta karamar ?ofa dan ganin ko wanene,ganin matar gidance yasa yayi saurin gotawa yana bata hanya tare da mata barka da dawowa cikin girmamawa
tana tafiya tana amsawa cikin mutuntawa hankalinta a kan motar megidanta yauma ya'rigani kenan tafadi a zuciyarta tura Kofar falon tayi bakinta dauke da sallama,kamar yadda zata haka ne yana zaune a kan kujera 2sit yana aikin danna wayya
Aikin kenan yafi bama waya muhimmanci akan laptop komi yasa ohoo
Kansa a 'qasa amma yaji lokacin data shiga fakon
daga ina kike yayi magana da Muryar da batayi daidai da yanayin saba a kausashe karasawa tayi ta zauna kusa dashi tana masa sannu da zuwa,tini dama ta tsara abinda zata gaya masa kamar kullum nashiga nan gidan murja ne takirani akan dan Allah inkai mata maganin ciwon kai,batada lafiya ko tashi ta kasayi gashi babu dan aike a gidan nakiraka a waya amma baya shiga shine naje nakaimata maganin.nace kai indan ka dawo sai ingaya maka ,ta karshe maganar da murmushi akan fuskarta,
Kallonta kawai yake ko ?iftawa baya yi wai taje gidan Murja,mamaki take bashi sosai tayadda ta ke iya tsara zance ta shirya ta fadi kuma kaji kamar hakan akayi
To Allah ya bata Lafiya tace amince inajin yunwa abani abinci ko shima zuwa gidan murjan ya hana a girkamin iyee
Ya fada ta sigar zolaya ..........



Kallonsa tayi tace "Abinci kuma ba wanka zaka fara yiba haka jiya kace sai kaci abinci kafin wanka amma kana ida cin abincin kace ka gaji wanka sai anjima karfi da yaji kana so ka zama qazami daga baya,
ni wallahi ban yaddaba dacan ai ba haka kakeba"
Cikin shagwa?a take maganar shiko gogan naku kallonta kawai yake daidai da tayi shiru yakai hannunsa ya ?an ja hanci ta yace "kinfiya rigima sayyada *Mariam* abun fa?a baya ka?an a gunki,Ni dai abani abinci da gaske yunwa nake ji" ya fa?a Tare Da maida hannayansa baya yana mi?a tace" ban girkaba,kaga ka canka daidai zuwa gidan murja bai barni na girka abinci a gidannan ba ta karasa maganar tana masa hararar wasa, kalar tausayi yayi yace " haba matar kinga nifa da Wasa nake
Ai ni nasan irin matar da na ajiye a gidanah irinku ne matan da mazajanku basa kaffara koda ko sunyi rantsuwa da Ubangiji akan ku ina fatan Allah ya tabbatar da zaman mu tare da juna har a jannatul-firdaussi"
Amine ta fa?a a ranta dan tini ta fara zancan zuci akan al'amarin mijn nata har cikin ranta tanajin dadin yabon da yake mata tasan shidin na daban ne, yasan yadda zai yi rayuwarsa batare da ya takurawa wani ba duk da tasan yanada rauni ta bangaran ilmin zamani kuma yanada zafi wani lokacin amma wayayye ne na qarshe koda bai mata anfani a bangaren ilmi ba, zata yi anfani da wayonsa ,?wazansa,da kasancewar sa namiji tunda ita macece bakomai zata iyayi da kanta ba,dole tana bu?atar mataimaki .
Tasan da ace yayi karatu da se anyi hazi'qi na gasken gaske yanada kaifin ?wa?walwa da saurin riqe abu tanada tabbacin zata samu nasara akan kudurinta matu?ar tayi anfani dashi a cikin al'amarin da tasa a gaban ta a yanzu.
Ganin tayi zurfi a tinani ne ya sa yatsunsa guda biyu ????ya karka?a akan fuskarta
Firgigit tadawo daga Duniyar tunanin da ta lula "lafiyarki kuwa naga kwana biyun nan duk kin taqurawa kanki da tunani ko da abinda Yake damunki wanda baki gayamunba" ya mata tambayar cikin jimami
Ajiyar zuciya ta sauke ta kalleshi sannan tace"ba komai kawai ina tuna alkhairan ka agareni yayana, Allah ya saka maka da alkhairi ya shiga al'amuran ka da duk wani abun da kasa a gabanka,Allah ya ji?an magabata ya musu gafara" Amine nagode matar aljannah har kinsa na fasa jin yunwar ma ya fada yana murmishi,da sauri tace "a'a yayana katashi muje kaci abincin kaga lokacin sallahr azahar ya gabato"
Mi?ewa tayi yabi bayanta yana ?ar dariya suka nufi dining table
Kujera ta jamasa ya zauna tana ?o?arin zuba musu abincin,kafin tayi wani yun?uri tini ya fara bu?e kwanon abincin wanda tun kafin ya ?araso wajen, ?amshinsa ya cika masa hanci"wayyo Allah na"ya fa?a da dan ?arfi kamar wanda ya ga wani abu daban ba tuwon shinkafar da yafiso ba,tayi masa malmala malmala kamar baza'a saka hannu a fasa acinye ba. ?ayan kwanon ko miyar ku?ewa ce da yaji busashan kifi se tashin ?amshi take "Mariam ta daban ce"ya fa?a a bayyane yana kallonta
ajiye plate din data zuba musu abincin dayi taja kujera ta zauna akusa dashi ruwa ta zuba a cups ta ajiye Kafin tace"Bismillah ranka ya da?ai kaci abinci banda zance kaga lokaci yana ?ara ?urewa" ta fa?a tana nuna masa agogon dake ajikin bangon dakin"murmushi yayi kafin suka fara cin abincin a tare.


Bayan sun ?are ta tattare kwanikan takai kitchen ko da ta dawo baya wajan tasan ya shiga dakinsa dan ya shirya kafin lokacin sallahr azahar,itama nata dakin ta fice tayi alwala daidai fitowar ta daga bayi taga ficewar sa ta gaban dakinta zai tafi masallaci dama bata rufe ?ofarba dayake sai ka fice nata dakin kafin ka isa nasa,?an le?owa tayi tace"???????? ???????????????? muna barar adu'a"ok insha Allah yace yana ficewa daga falon da murmushi akan fuskarsa yasan inya biya ta sai yarasa jam'i komawa tayi itama ta tayar da Tata Sallarh ......



Dasunan Allah mai rahama mai jin?ai

Bayan ta idar da sallar tayi adu'a ta tashi ta isa gurin wata ?ar kanta datake a ?akin,ta katako ce,amma aka mata gida-gida ta ciki.
Tarin littattafai mabanbanta ne a ciki kowanne da bangaren shi murfin glass ne a jikin ta,yanda ta zauna ta tsarasu kai kace wata ?aramar Library ce,karasawa tayi ta danna wani dan Madanni sai glass din ya zuge yayi ?asa gaba daya ,duddubawa ta shiga Yi tama rasa ta'ina zata fara.
Tabbas ta daukowa kanta aiki amma data tuna cewa aikin daukar fansa take sai taji wani ?warin guiwa,idonta ne ya sauka akan wani littafi wanda bazata taba mantasaba,shine kyautar ?arshe daga mahaifinta mafi soyuwa a rayuwar ta,dashi ta saba dan tin tana ?ar shekara bakwai mahaifiyarta ta rasu,shine komai nata shine ya maye mata gurbin uwa, share kwallar data taru a idonta tayi kafin takai hannu ta dauki littafin tana ayyanawa a ranta cewa ya zama Dole ta daure ta karanta wannan littafin da mahaifinta ya bata.
Acan baya bata ga wani amfanin zaman karanta wannan labari ba, tun daya bata shi take ajiye dashi saidai ta sauya masa waje.
Yazama dole yanzu ta karanta dan tasan makamar zaran tun farkon tafiyar ,dauko shi tayi ta koma bakin gado ta zauna ta fara duba wa tun daga farko



?????????? ????????

Biyu ga watan uku 2/3/1970 a (kanyar waziri) ?aramar hukumar miriya dake jahar damagaram tarin dandazon Mutane ne cike abakin wani ?aramin gida ko ince dakin da aka kewaye da kara,se tururuwar shiga ake kowa so yake ya shiga ya ganewa idonsa
Jin labarin matar Gambo me wankin hula ta haifi yara ?an uku kuma duk maza abinda aka jima ba'ayiba a wannan ?auyan,yau se gashi anyi kuma a gidan mafi talauci da kas?anci a cikin su.
Dayawan su sunzo ne dan suga yanayin da hansai da megidanta suke a tunaninsu damai zasu iya ri?e yara har uku,suna su biyu ma wataran abinda zasu ci gagararsu yake ko ?ar gonar nan ta gado shi bashi da ita,sai dai idan lokacin aikin gona yayi,ya nemi aikin barema amma duk da haka watarana haka zai dawo gida kamar hadin baki ba wanda ya dauke shi aiki saboda tsabar ba?in ciki
Sun manta cewa bakin da Allah ya tsaga baya hanashi abinda zai ci.
Yanzu ma Allahn daya basu yaran shi zai basu abinda zasu rainesu dashi.
Ahaka da haka har ranar suna tazo wanda shi da soyayi ya ?aga sunan se mako me zuwa kafinnan sunada mako biyuda haihuwa wai ko Allah zai sa ya sami sauran abin yanka na ha?i?a, tunda tinkiya guda daya yatanada shima da kyar ya tara kudin ya saya,itama ba wata ?osassa ba.
To a jiya ne da marece Yana zaune yajera jariran da suke cikin tsummuna guda biyu a saman cinyarsa dayan kuma a hannunsa hansai me jego tana zaune tana cin abinci tuwo da miyar kuka,tun safe daya futa bai dawo ba se Yanzu dama ba suyi girkin rana ba Allah ya sa da ?an sauran burabuskon safe shi inna lami ta mata ?ar dubara tabata taci.
Kodaya shigo da gari a hanunsa, inna ta amsa tashiga aikin sarrafa shi nan da nan ta ha?a tuwo da miya wacce daga ita se dadawa da ?an magi ko arzikin mai da barkono bata dashi,ta zo bawa me jegon inda take zaune nesa ka?an da inda me gidan nata yake ta faraci. "Gambo kai yanzu zakaci ne a zuba maka"inna ta tambaye sa"a'a inna ki dai zuba kici kema,ai ana ?o?ari Allah shi kadai zai biya ki"
"Haba Gambo ai kai da ?a?an dana haifa duk daya kuke,munyi zaman amana da iyayanka har Allah ya musu rasuwa,a ranar damukayi zancan zata aurar da kai a wannan shekarar,a ranar akayi ruwan sama da maraice,cikin dare suna bacci daki ya fado musu daga ita har baban naka babu wanda yayi rai a cikinsu. lokacin ankaika dawan makaranta, Mahaifiyar ka Allah bai bar mata yaranta ba wabi take yi, kullum burinta taga ?an jikokinta,yau ga Gambon ta da ?iya har uku lokaci guda dan ma Allah ya jinkirta masa shekara kusan goma se Yanzu suka samu haihuwar Allah dai ya ji?anki rabi" inna ta ?arashe maganar tana fyace hancinta daya cika da majina dan tana magana tana ?ar kwalla ta tuna baya
Sallama wani yaro yayi yace wai ana sallama da malam gambo,kaje kace ganinan.
Koda ya fita malam liman ya gani da yara biyu ko wanne rike da dan rago musabaha suka yi malam liman yace Gambo gadan abinda aka samu tun ranar da aka maka haihuwa nake nace afara tara sadakar da za'a baka,to masha Allah ansamu ba laifi jiya wani bawan Allah ya kawo rago guda to danaga haka yanzu se na biyo ta kara(kasuwar dabbobi ce)na samu dayan ragon dan tini naji ana cewa Kanada tinkiya guda daya to gashi wannan sauran canjin ne a sayi kayan miya,
Godiya malan Gambo ya shiga yi kamar zai wa liman sujjada harda dan kukanshi ba komai ai yiwa kai ne fadin malam liman dayake abokin shi ne tun yarinta dan tarema akakaisu karatu a wancan lokacin.
Samun wannan alkhairin yasa ya fasa daga sunan aka yisa a washegari inda yara suka ci sunansu babban ne Hassan, Hussaini se na ukun adam a haka aka yini yin biki ana yin komai daidai da ?arfin me gayya me aiki baban ?an uku ..................




Bayan suna taro ya watse lafiya an bar me jego da ?a?anta ?an gulma da abin fada baya musu ka?an,tun zamansu da ita kusan shekara goma kenan basu ta?a ganin wani nataba,sunyi tsammani Yau da tayi dalili zasu ga danginta sai sukaga akasin haka,dayake ita ba ?ar garin bace.
Jalmari sunan ?auyen su,bayan dawowar Gambo daga dawan makaranta ne ya tarar da mummunan labari cewa Shekara biyu kenan da rasuwar iyayen sa a wancan lokacin ba kowa yakeda wayaba sai wane da wane shiyasa beji rasuwar ba saida ya dawo dan kansa, yayi kuka kamar ba gobe gashi bayada wajan zama dama gidan nasu ?aki ?ayane kuma shine yayi sanadiyar iyayen sa,Sai gidan ?anin mahaifinsa ya koma da zama to shima bawani ?arfine da shiba sai rayuwar ta zama se a hankali yau da da?i gobe akasin haka
Haka rayuwa taci gaba da tafiya a hankali ya fara tada ginin ?aki a filin gidansu,tare da tallafin abokinsa Abubakar wanda yanzu shine babban limamin ?auyen su a kanyar wazirin, yana ?are ginin dakin ya koma can da zama yahada Kayan gyaran takalmi ya fara,karatu ko sai da dare idan ya dawo yake biya allonsa,idan akace yau ranar Lahadi ce to ya tafi cin kasuwar (miriyah) acan yake yini se kusan dare yake komawa gida.
Awata ranar Lahadin ne yana tattara kayansa ganin rana ta kusan fa?awa zai tafi gida, Wasu ?an mata biyu ya gani sunata jibgar wata yarinya da bazata huce shekara goma sha hu?u ba,tanata kuka da cewa Wallahi bada gangan bane amma basu bar taba,da sauri ya isa wajan su ya shiga tsakaninsu yana basu ha?uri,da?ar da tafi ?ar'uwarta daukan zafi tace dan ubanki yau kowa ya miki tsaye se kin biyani duka kudina,kuma dama inajin haushinki saboda ke iliya na koda namasa magana baya kulani,se yanzu ne Gambo ya gane cewa a fa?an nasu harda kishi aciki,?ayar ya kalla wacce tini jikinta yayi sanyi ganin hancin hansai na zubda jini"yace nawane ku?in naku"tace saura dari ai munkar?e wanda aka aiketa dashi yanzu
Allah yasa yanada ku?i yau yadan sami aiki ba laifi,?arin ya ?auko ya basu sukai tafiyarsu jiki a sanyaye ,irin ruwan da yake zubawa a robar faro ya ?auko ya bata ta wanke fuskarta,daukan kayansa yayi yace muje
Sai da suka fita daga kasuwar yake tambayar ta inane garinsu,tace masa Jalmari ,saida ya rakata har garinsu, sun iso ana kiran magariba dayace zai fuce ganin kar yayi asarar sallah a jam'i yace bari su isa gidansu yayi alwala sai ya sami masallacin da yayi Sallah kafin ya wuce
Laure matar mahaifinta da take tsaye abakin ?ofar gida dan ganin ta ina hansai zata fito,ita fah dama bata yarda da itaba,tin rana ta aiketa ta?an tsinto mata yan kayan miya akasuwa shine bata zoba sai yanzu
Tana hango su da wani mutum gashi tana dan ?ingisa ?afarta kuma ga jini duk ya
?ata mata hijab kawai sai baba lauren tasa kukan mutuwa wai hansai zata tona mata asiri, malam idi me goro da fitowar sa kenan Daga cikin gida yace wai kekuwa laure sai yaushe zakiyi hankali zaki fito waje kina abu kamar wacce batada hankali , maganar sa ce ta katse ganin mutum a tare da ?iyar data da?e da fice masa arai
Kallon Gambo yayi yace Kanada alwala girgiza masa kai yayi,cikin gida ya koma ya ?auko buta me ruwa ya mi?a masa,kayi alwala ka fice muje,ba musu ya ajiye kayan aikinsa yayi alwalar suka fice masallaci kowa da abinda yake ransa,ana ida sallahr magariba malan idi mai goro ya jaku?a kusa da liman ya masa ra?a,liman yayi Magana cewa kar a tashi akoy daurin aure yanzu,juyawa yayi yace malan miye sunanka,kansa a 'qasa yace Gambo to malan Gambo ka kawo Abin da yake hannun ka,ka biya sadaki za'a daura maka aure da ita abokiyar shashancin naka,yaji zafin maganar amma ya dake ya ?auko ?ar ledar sa da yake kulle ?an kudinsa a ciki ya bada duka,nan take aka daura auren malan Gambo da baban hansai gida suka koma a inda suka bar hansai anan suka isketa hannunta baban nata

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login