Showing 1 words to 3000 words out of 51041 words

Chapter 1 - HAMSHAƘIYA-UWA-_3 BY HALIMA ABDULLAHI K/MASHI

05 Jul 2024

6834

Hamshakiyar uwa book 3

Ban an kara ba kawai sai ji nayi ya jani jikinsa, na fara mitar dan Allah a yi sauri kar Umma ta tafi yana fa?in "Haba Baby babu inda zataje." Nace bazan so ta gane me nayi ba fa kamar rashin kunya ne, ?an Allah nikam kayi saur.... Bakinshi ya saka ya datse surutu na, wanda haka ya tilasta min yin tsit.

Bayan ya samu kanshi na uzzira mishi ya yi wanka ya shirya amma dole na zura mishi ido ya yi salla saboda an riga anyi a masallaci. Ni kuwa ko wakan banyi ba burina dai ya fita. Kafin ya kammala na ?auki jakarsa na rataya a kafa?a. Yace "Yau a haka zan tafi bazan saka turare ba?" Nace E yau a haka zaka tafi, domin dama ai danni ake sakawa ko?" Yace haka ne amma ayi ha?uri a ?an yarfamin ko ba yawa." Na ?auki wanda hannu na yakai na feshe shi,sannan na ce mu tafi.

A falo Hajiya ce ka?ai take yin salla a gurin salarta,na shiga waige waige ina fa?in to ina ummana ta shiga kuma! Na kalleshi, cikin kukan shaga?a nace kaga ka gani ko? Gashinan ta tafi ina ta cewa ka yi sauri amma ka ?i gashi kuma ta tafi ko ?akina fa bata shiga ba... Da le?en shi ya nuna min bayana. Cikin sauri na waiwaya sai naga Umma ta fito daga ?akin Hajiya tana fa?in Baby kukan me kuma ki ke yi haka kamar wata ?aramar yarinya? Na saki dariya ga hawaye nace na zaci fa ko har kin tafi ne. Tace "Shi ne ki ke yin me?" Shamaki ya ce "Shi ne ta ke kuka dan shagwa?a." Umma tace Shaga?ar gaske kuwa banda shiririta ina ke ina kukan na tafi tunda ba tare zamu tafi ba.Ta zauna agurin zamanta na aje jakar nace Umma bari in saka miki abincin ko? Tace "Ka?an zaki sa min don banajin yunwa. Na sa mata ka?an na loda mata nama, da da hali saina kwashe mata naman ta kaiwa su Jafar, amma gudun zargi ko maganar Hajiya dale dai na ha?ura. Hajiya ta idar Shamaki dama ita ya ke jira, domin in ta fara salla sai mutum ya jira dan wani lokacin na kan tambayi kai na ko dai Hajiya sai an amshi sallar sannan take idarwa. Yace "Hajiya na gama shirin zan fita kasuwa. Ta dafa kanshi kamar yadda ta saba. Tace Allah ya yi maka albarka ya bada sa'a ya tsare gabanka da bayan ka."
Yace Ameen ya kalli Umma yace Umma a gaida su Jamila da Abba. Tace zan fa?a musu Allah ya bada sa'a da rabo mai amfani. Yace Ameen Umma na gode.

Na bishi da jaka ina jin takaicin banga ya ba Ummana komai ba har yana wani zai jira su gaisa, a zuciya ta nace sai na ro?e shi yau koda zai hana ni.

Sai da mukaje falon da nake tsayawa, na ha?e girar sama da ?asa, ya sa hannu ya ?ago fuskanta yace "Me kuma aka ce ya faru Baby?" Nace ce ina son in bawa Ummana wani abu na tsaraba koda ku?i ne ta saya wa ?anne na ,amma na kasance bana maganin ko sisi. Cikin shagwa?a na yi maganar. Ya kwaikwayi muryata yace, "Na ba Hajiya sa?o zata ba Umma shike nan?" Kai masa ?an dukan wasa nayi ina fa?in na gode. Ya saki fuska ta ya amshi jakar na ?aga hannu nayi masa bye bye.

Na dawo Umma ta aje abincin tana shan ruwa,na kalli naman kamar ma bata ci ba, nace Umma to ya ba?i ci naman ba kuma? Tace na ci Baby Allah ya amfana. Hajiya tace "Nima dai naga kamar bata ci ba, nan dai kamar gidan ki ne bakya yi fulako ba." Umma tace Alhamdulillahi ai na ci. Hajiya tace "To ko kuma dai a juye ta kaiwa yara dan kinga karnuka za'a baiwa?" Umma tace "Haba dai bazan ?aukii abinci ba ga shi can a gidan, zuwa zanyi ma in tafi,?arfe biyu Abbansu y ace in dawo. Gashi naga ?aya da rabi ta gota. Hajiya tace "To kuma baki shiga ?akin nata ba, ga mamakina sai naga Hajiya ta mi?e tana fa?in "Muje in raka ki, nima ban ta?a shiga ?anikinsu ba, me zakaje ka yi a ?akin yaro." Umma tace gaskiya dai, bare ko yaushe suna dabdala a nan gurin ki. Tace haka kuwa.

Mamakin Hajiya ya hana ni magana ina biye da su ina tunanin. Hajiya dai ?ila dan kar mu tattauna wata maganar da Ummane ta yi wannan katan katan ?in ta ?i bamu fili ko kuwa kulawa ce da mutuntawa ta yi wa Umma.? Bani da amsa dan haka naci gaba da binsu.

Ta nuna wa Umma ko ina tun daga ban?aki har saura ?akunan Umma dai tana ta addu'a da fatan alkhairi

Sannan suka zauna a kan kujera,na zauna a gaban su kamar mai nema gafara,Umma ta fara magana. "To Hajiya masan dai kuna ta ha?uri da ?uruciya,yaran yanzu sai anyi ha?uri, a daure ana tsawata mata in tayi ba daidai ba a sata a hanya na hukunci kuma a yi mata ba sai an sanar da mu ba,. Allah ya sa mutu ka raba tsakanin su." Hajiya ta amsa da Ameen, ai ita Rabi'atu bata da matsala yarinya ce mai biyayya laifin ta da nii ?aya ne. Na zaro ido cikin fa?uwar gaba domin inji laifin nawa. Taci gaba da fadin Duk yadda yarinyar nan zata so mijinta ba za ta yi ya ni Uwar da na haife shi ba Haka ne?" Umma tace "Ko alamar ?afar ki bata kama ba." Hajiya tace madalla, to wai yarinyar nan nace ta shirya za'a kaita gidan wani malami wanda zai bata taimako Allah cikin ikon sa sai yadda ta yi da mijinta, kina kallo gata dai a cikin irin wannan gida amma bata maganin kwabo ?aya,ko kina da shi?" Na girgiza kai tare da fa?in bani da shi. Tace yanzu dubi ke ba surukarsa bace, da fatar baki yace miki ki gaida gida,zancan gaskiya hakan ya kyautu?" Umma dai bata yi magana ba. Hajiya ta ci gaba da fa?in. Nasan har ma?ota da wasu a dangi sai sun yi da ku,suce 'yar ku tana aure a gidan Alhaji Baita amma har yanzu kuna nan jiya i yau. Koma ace laifita ne ta yi aure gidan daula ta mance da ku, wasu ma cewa za suyi ana baku kun ?i nunawa ne dan kar ku sammusu, maganar haka take?" Umma tace haka ne. Hajiya ta nuna ni da yatsa tace, "To kinganta nan fir ta?i zuwa gidan malamin har da ?auke min ?afa ina hankalce da ita,in ba mijin ta ne a gurina ba ta daina zuwa tunda ta san ba yadda za a yi in yi mata maganar a gaban sa. Ita bazata gurin Malami ba,ba kyau ba sai an mallake shi ba. Jifa sokonci. Kuma ita hakan zai wa amfani,nima kuma ta ?angare na wani abin in zai min gaddama sai in bi ta hannunta kin san dai ?an yau."

Mamakin Hajiya ya sa na kasa daina kallon ta, ko dai so take Shamaki ya fara yi mata sujjada. Mutumin da kara in ta aje ba zai ta?a tsallaka shi ba.
Muryar Umma ta katseni, tayi gyaran murya sannan ta ce, Wato Hajiya ni ma dai a nawa ganin sam bai kyautu Baby ta kai sunan mijinta gidan malami ba koda baya iya sauke hakkin da Allah ya ?ora masa nata na aure. Balle duk maganar nan ana yinta ne game da wata kyautatawa wadda in bai yi ba Allah ba zai kamashi da wani laifi ba. Babu shakka ban goyi bayan wannan abin ba. Kuma wai ma Hajiya dan mutane za su ce ko ma?ota za su yi damu, Allah na tuba zaka hana bawa ya ?auki zunubi ne, kace dole sai ya yi aikin lada? Kinga kuwa bamu isa mu hana a yi munafircinmu ba, kuma ko da me kuka bamu Hajiya wannan ba zai hana mai magana ya yi magar shiba. Dan haka don Allah Hajiya kar a nuna mata wannan hanyar, kinsan yaran zamani wataran sai ta tafi da kanta neman wata bu?atar da zata ?atawa kowa rai. Munriga mun ?ora ta a hanyar sallar dare,in wata damuwa ce ta fa?awa Allah,kuma ta ke yi wa mijinta addu'a Allah ya tsare shi. Ta dubi Hajiya wadda ta zuba mata ido tace, ki yi hakuri in na fa?i ba dai dai ba. Amma shawara ta ?arshe ku barshi ya ji da masu jiran shi na waje,kinsan 'yan kasuwa ba'a raba su da magauta, a gida sai a tsananta addu'a bare ta ku Hajiya, bakin Mahaifiya ya sha gaban bakin duk wani malami." Hajiya ta sauke ajiyar zuciya ta ce "To ai shikenan tunda kin goye mata baya, na kyale ku ,yanzu ita ko dan kishiyoyin da suka fita ko wasu da zasu shigo bakya bata ?warin gwiwa ta amshi taimako ba?"

Umma ta yi 'yar dariya tare da fa?in mijin mace hu?u kuma a tauye shi da mace ?aya Allah ya rufa masa asiri. Ai Hajiya duk namiji da burin aure ya ke mutuwa saidai in Allah bai ?addara mishi ba. Dan Allah ina neman alfarma Hajiya a bar zancan gidan Malamin nan, Abbasu in yaji ba ita ba har ni zai sa?a min ?warai.

Juma ta ?wan?wasa ?ofa da sallama . Hajiya tace ta shigo , ta mi?o wayar Umma
da ta aje a inda ta zauna a falo, tace "Ana ta kiran wayar ne." Umma ta amsa da sauri tana fa?in Abban su ne.Daidai lokacin kiran ya sake shigowa. Ta ?aga tana fa?in yi ha?uri wayar tana can sitirum ne mu kuma gamu a cikin ?ani. Muna jiyo murya Abba kasancewar wayar Umma ta samu matsala ko yaushe murya a bu?e ta ke. Yace "Kenan shantakewa ki ka yi a gidan yarinyar ke da na baki ?arfe biyu yanzu saura mintina ko baro gidan nakiyi ba." Tace yanzu zan taho muna 'yar hira ne da surukarta kaga gata ma ku gaisa.

Yace to bata, suka gaida shima dai ya bada ha?uri akan cewa su yi ha?uri da ni in har na yi ba daidai ba. Suka yi sallama yace da Umma ta gaishe ni, kuma ta taho domin gashi nan zai koma gidan yanzu.

To haka dai muka sake fitowa gaba ?aya,domin Hajiya bata da niyyar bamu guri, muka dawo Falon Hajiya. Umma ta mi?o leda mai layi layi tace ga tafarnuwa da kayan ?amahi Hajiya, tsarabar ce sai na rasa me zan kawo muku tunda Allah ya sa kuna da komai.

Hajiya tace "To muna godiya Allah ya saka da alkhari. Hajiya ta dube ni, "Shiga ciki kan gado ki ?akko mata Envelope ta sayawa yara alawa a hanya. Ta dubi Juma da ke kwashe kayan abinci tace "Je ki fa?awa direba zai maida ba?uwa gida.

Har mota na raka Umma sai da naga motar ta bar harabar gidan sannan na dawo ciki. Hajiya ta kalle ni, ke ce "'yar fari ko?" Nace E. Hajiya. Tace. "Naga itama yarinya ce mahaifiyar ta ki. Nayi Murmushi tace "Gurinta ki ka samo wannan shegen ba?in wayon ko?" Nayi 'yar dariya nace bari in shiga ciki.

Na yi wanka na yi salla naji da?in zuwan Ummana duk da Hajiya ta hana mu sakewa. To wai ita Hajiya domin kar in fa?awa Umma cewa Shamaki zai ?ara aure shine ko kuwa dai tana zaton zan fa?awa Umma cewa bata min yadda kamata ne?

Bani da amsa don haka sai na tashi na ce bari in kira Umma inji ko sun isa gida.

Na fa?a kan gado na, na ?auki wayata na kira layin Umma, ta ?aga tace "Yanzu fa na ke shirin kiran ki in fa?a Miki cewa
Dubu Hamsin ne a 'yar takarda nan da Hajiya ta bani."

Na ja dogon numfashi nace amma angode Allah ya saka da khairan. Gashi bamu samu minti hira ba. Tace "To wace hirar ma zamuyi ko kina da wata matsala ne?" Nace "To ba dai wata ?atuwar matsala bace amma dai an saka mishi ranar aure da wata yarinya 'yar uwarshi, tana nan a gidan ko da kika zo tana ciki bata fita ne hatta makaranta ta daina zuwa. Umma tace "Tofa! Amma kin san abinda nake so da ke?" Na ce A a,Tace ki kama kanki ba ruwanki da auran sa. Sannan hanyar da da maganar gidan malami da Hajiya ke yi duk yadda aka yi so take ta gwada ki, ko dai wani abu mai kama da haka. Nima baki ga ta latsa min basira ba, kar nake kallon ta. Wata uwa ce zata ce a kai ?anta gidan malami ki kiyaye sosai wata kitimirmira take ha?awa. Kuma ki ke nazari ko magana zaki furta domin na lura cewa 'yar shan loga ce, ga ta da alaye. Sannan karki ta?a damuwa da abinsu. Baki gani ba,naman nan ina son inci shi amma ina jin tsoro kar in bar miki abin fa?a dan haka na kauda kai daga gare shi na ha?iye kwa?a yi na.

Nayi dariya nace zan kiyaye Umma, tunda ga ku?i nan kin samu sai ki siyo muku mama ku dafa.

Tace wannan ku?in zan ciri jari a ciki in ba Abbanku dubu goma shima. In sai wa Jamila tukwane, ba zan bari in maimaita kuskuren da nayi a baya ba a bikin ki. Nace haka ne Allah ya rufa asiri. Tace "Ameen dan Allah kar ki saka maganar aurannan ya dame ki, ke dai kiyi ?o?ari ki iya allonki. Nace Insha Allahu.

Muka ?anyi shiru can tace ina ganin fa kamar kin ?ara ramewa, anya babu wata matsala bayan wannan?" Nace babu, ai nayi zazza?i ne kwanaki harna kwanta a asibiti amma nayi ?iba, sosai. Tace Allah ya ?ara lafiya, yanzu dai ki kwantar da hankalinki. Nace to Umma.

Bayan mun yi sallama na yi shiru ina tunani, yaushe kuwa zanyi wata ?iba a gidan nan tunda nayi kuskuren duba wayar mijina.

Kuma gashi abin ya zame min masifa ko na ce bazan duba ba sai na duba. Gashi dole in ha?iye duk abinda na gani a cikinta tunda bani da damar fadawa wani domin in samu salama. Duk da cewa ina bukatar shawara amma bansan wa ya kamata in nema shawara ba, wanda asirina zai rufu. Zan ci gaba da mi?awa Allah kuka na shine mafi girman wanda zai bani mafita.

Azumi ya gabato bai fi sauran kwana tara ba, Shamaki baya samun zama yawanci sai na jima da bacci ya ke shigowa. Suna ta fama da lissafi za su cire Zakka. Za su tafi Umara,ita Hajiya acan zata yi Idi shine zai dawo kafin lokacin salla, amma sai an fara azumi da sati biyu zasu tafi.

Sun fara rabon zakka ina zaune ina jin su ana lissafin, masallatai da za'a kai miliyoyin ku?i. Sai kuma wasu marasa ?arfi, sai dangin su da za a baiwa dubu ?ari ?ari a Envelope da kayan abinci. Yayinsa kowa ta zo ta kawo list na mutanen da take son a taimaka. Ni kuwa matar gida ko oho,ina zaune bana maganin ahu, ko kitso da ?unshi ko wanke kai saidai direban ya kai ni in turawa Hajiya account ta turo musu ku?in.

?inki kuwa da yace in bada kayan cikin lefena duka a ?inka da na fa?a mata zan kai ?inki Unguwar mu sai tace a a,ta sa Maman Iman ta kawo tela har gida ya gwadani ya kwashi kaya, sai dai ?inki na gani bani da wata hanya da kwabo zai shigo min duk wani abu da nake bu?ata za a kawo min.

To irin wannan u?uba ta rashin ku?i dan ma dai dama can ban saba ri?ewa ba bare in damu sosai.

Ina kwance sai ga Juma wai inzo inji Hajiya. Na same ta a hakimce kamar kullum da carbi tana ja, ta bini da kallo har na fara tunanin ko nayi wani abu ba daidai ba. Na tsugunna nace Hajiya gani. Ta nuna gefen ta da yatsanta, "Ki ?irga min wannan Envelope ?in guda nawa ne." Na ce To. Na ?irga guda ashirin ne. Tace "Dubu ?ari ?ari ne a ciki ina son ki rabawa mutum irishin ma su bu?ata ciki harda su Juma, sannan yanzu zan saka Juma ta je ta rakaki can baya inda kayan abincin zakka su ke, na azumi , ki raba su ga masu bu?ata. Na zaro idanu ina fa?in Hajiya bazan iya ba." Ta ?ago ta dube ni cikin gimtsewar fuska,tace kina auren Shamaki amma baki san yadda ake raba taimako ba? Na kalli Juma wadda ta min alamar inyi shiru da ido. Na maida dubana ga Hajiya wadda ta kuma tattara hankalinta ga carbin da take ja. Na mi?e na ce Juma muje ki nuna min.....
....
Muka fita can wata haraba ta bayan gidan ina ta tunani yadda zan bigi cikin Juma.

Nace wai kuwa Baba Juma a ina ake rabon kuma suwa da wa ake baiwa.? Tace "To kowace mace dai da yadda ta ke rabon ta wata ta yi a cikin gida wata kuma a waje amma can da dai a cikin gida ake yi kuma ba a taruwa, yanzu dai naki sai yadda ki ka yi da shi."

Nace kina nufin duk sauran matan sun yi irin wannan rabo? Juma ta ja baya ta ri?e ?ugu sannan Tace "Babu wadda ba ta yi irin wannan rabon ba." Nace ni damuwar ban san su wa zan baiwa ba. Kuma yaushe zan bayar? Tace "wannan duk yadda ki ka yi

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login