Showing 66001 words to 69000 words out of 296878 words

Chapter 23 - RAWANIN ZALINCI BOOK 1 COMPLETE HAUSA NOVEL

20 Dec 2025

44

harararsu har suka wuce.

Suna wucewa ta sanya kai ta wuce abinta tana mai kare masu zagi, dan bata ga alamar hankali a tattare da su ba a cewarta.

Pharmacyn dake a tsallaken titin ta je ta haɗowa babanta maganin ciwon kai, sannan ta kama hanyar dawowa gida, sai magana samarin layi suke yi mata, kamar dai kullum babu wanda ya isheta kallo daga cikinsu, in da ta sanya kai kawai take nufa abinta.

Lokacin da ta dawo gida Zainab har ta yi wanka ta fito parlourn. A kusa da baban nata ta zo ta ajiye mashi magungunar tana wani aikin yamutse fuska, sannan ta wuce cikin ɗakinsu dan ita ma ta yi wanka ta shirya.

Sai a lokacin kuma baban nasu ya miƙe jiki ba kwari ya nufi cikin bedroom na mamar tasu, da farko Khadija ta so ta shiga wajen mamar tasu kafin ta wuce ta je ta yi wanka, amma ganin babanta ya miƙe zai nufi ɗakin ne yasa ta wuce nasu dakin kawai.

Ya shiga cikin ɗakin dai'dai lokacin da maman Zainab ta farka daga barcin da take yi na wahala, idanunta har sun kumbura saboda kuka ga kuma barci, har ta yi barci ta tashi ɗin ma zuciyarta bai yi sanyi ba, tafasa yake yi mata sosai, musamman idan ta tuna cewa kakansu Zainab ta ce a tare da ita da kuma Amarya zasu koma sabon gida, duk sai ta ji duniya tana juya mata, yanzu ma basu zaune gida ɗaya da su ba ya ta kare da balaja'un bala'in tsohuwar bare kuma suna zaune gida guda? Ya kuke tunanin zaman zai kasance?. Akwai aiki ba kaɗan ba.

Kuma abin da baku sani ba a nan shi ne, duk abinda kakansu Zainab take yi fa zugin maman Haidar ce, ita ce nan take ƙoƙarin tura ƴar tsohuwar nan ga halaka, munafukar mata.

A gefen gadon baban Zainab ɗin ya zauna yana ƙoƙarin fara yi mata magana.

A daƙile cikin tsananin ɓacin rai ta ce. "Ba sai ka sake ce mun komai ba baban Zainab, wanda ka gaya mun ɗazun ma ya isheni har karshen rayuwata, dan girman Allah ka rabu da ni haka idan dai ba so kake kaga gawata ba".
Ta kai karshen maganar tare da zuro kafafunta ta sauka kasa daga saman gadon, ta wuce ta fice ta bar mashi ɗakin.

Bawan Allah duk sai ya rasa ina zai sanya ransa ya ji daɗi, haka dai jiki ba kwari ya sake miƙewa ya fito parlourn, nan ya isko tana shirya masu abinci, ɗaya daga cikin abin da yasa yake kara sonta kenan, komai ɓacin ran da take ciki baya hanata ta yi aikin da ta saba, baya hanata nemar aljannarta baiwar Allah.

A saman sofa ya zauna yana ta kallonta, ita kuwa ko kallon in da yake bata yi ba, abincin kawai take kwasowa daga kitchen tana shirya masu a parlourn, duk in da ta yi sai ya bita da ido bawan Allah, tana gamawa kuma ta nufi hanyar komawa cikin ɗakinta, da alama ita ba zata ci abincin ba kenan.

"Maman Zainab ina zaki je kuma? Ki zo mu ci abincin mana".
Ya faɗa yana kallon Zainab dake rike da wayar mamar tasu.

A takaice ta ce mashi. "Bana jin yunwa, so ku ci kawai".
Ta kai karshen maganar tare da shigewa cikin ɗakin abinta, har da rufo kofa ta murza key.

Tabbas yasan saboda ganin idon Zainab ne yasa ta bashi amsa, da Zainab bata parlourn ba zata kula shi ba bare ta bashi amsa. Macece mai hankali sosai, tasan duk in da yake mata ciwo, tasan da cewa abin da take yi wa babansu Zainab shi suma idan suka yi aure zasu rinƙa yi wa mazajensu, so bata son ginasu a kan turbar da bata dace ba, shiyasa kome babansu zai yi mata na ɓacin rai bata nuna hakan a gabansu, tana ƙoƙarin ta danne dan taga tarbiyar da take basu yana tafiya mata yadda ya kamata, ba wai tana basu tarbiya kuma tana sake rusawa da kanta ba, Allah yasa mata su gane illar faɗa da mazajensu a gaban ƴaƴansu, Allah yasa su gane cewa rugujewa ƴaƴan nasu tarbiya suke yi da kansu, Allah yasa su gane cewa duk abin da suke yi wa ubansu haka ƴaƴan ma zasu yi wa mazajensu idan suka yi aure, dan suna ganin mamarsu tana yi, so hakan zai sa su ce abu ne mai kyau.

Yau dai shi ma ya ci wannan abincin ranar ne kawai saboda Zainab da Khadija, ba dan su ba tabbas ba zai ci ba, amma baya son su san halin da ake ciki, dan haka sai ya zage yana ta ƙoƙarin ƙaƙalo murmushin da kuma yake wadda aka ce tafi kuka ciwo, a haka suka kammala cin abincin ya tashi ya nufi kasuwa bayan ya ɗaukawa su Sadiq nasu abincin a kula. Bai sake komawa wajen Maman Zainab ba, dan yasan har yanzu bata sauko ta huce ba, so ba zata saurare shi ba, hakan yasa ya wuce kasuwa kawai da nufin kafin ya dawo kila zuciyarta zata huce kaɗan ta saurare shi.

Haka su Khadija suka zauna a gidan har zuwa lokacin tafiya islamiya, lokaci na cika suka yi sallah tare da shirin islamiyar, ko da suka je yi wa mamar tasu sallama sam bata nuna masu kamar akwai wata damuwa ba, sai ma kuɗin sayan attarugu da Albasa tare da tumatir ta basu kamar yadda ta saba, sannan ta bisu da addu'a tare da fatan alkhari kafin ta ja masu kunne a kan biyewa ƙawaye ko kuma wani ya taresu a hanya su tsaya su kulashi, su kiyaye hakan dan su ƴan gidan mutunci ne, ba'a kan titi suke ba, wannan shi ne nasihar da take yi masu a kullum idan zasu tafi islamiyar, shiyasa kuka ga basu taɓa kula maza a hanya.

Da haka suka wuce Islamiya ita kuma ta tashi ta fito ta nufi tsakar gida, alwala ta ɗauro ta dawo.

Bayan ta gabatar da sallah ne ta nufi kitchen dan girka masu abincin dare, a haka Aunty Hauwa ta zo ta iskota.

Kamar yadda suka saba a parlourn suka zauna da Aunty Hauwar suna hira tana zuwa tana duba girkinta da ta ɗaura, cike da damuwa ta sanar da Aunty Hauwar bala'in dake shirin tunkarota a karona biyu bayan na auren Khadija and Haidar.

Aunty Hauwa bata yi ƙasa a gwiwa ba wajen kwashewa su maman Haidar albarka tare da banka masu tsinuwa kala kala, sannan ta ce mata to wlh gara ta tashi tsaye, idan ba haka ba tana ji tana gani zasu korata gidansu bayan kuma ita ce ta sha wahalar baban Zainab ta ci talaucinsa, yanzu kuma wata zata zo ta ci arziki, wlh kada ta yarda, ta miƙe tsaye, dan rayuwar yanzu ba'a zama........ Aunty Hauwa ba dai bala'i ba.😅

"Hauwa to ya kike son nayi da su? Kina dai jin abin da suke faɗa ko? Umarni Hajiya ta bashi fa".

Nisawa Aunty Hauwar ta yi kafin ta ce. "To ai idan ba zaki iya fito na fito da su ba sai ki biyo masu ta ƙarƙashin kasa, duk kici uban shegu marasa amana butulaye kawai".
Ta bata amsa rai a ɓace

"Hauwa kamar yaya na biyo masu ta ƙarƙashin ƙasa? Yimun bayani na ji".
Tana magana cike da damuwa a ranta, kamar zata yi kuka.

"Abin da nake nufi da ta ƙarƙashin kasa shi ne, tun da ba zaki iya fito na fito da su ba kawai ki yarda muje wajen Malam sha yanzu magani yanzu, muje mu gaya mashi ya rufewa ƴan uwan mijinki baki a kanki, ya kuma sanya masu kaunarki na fitar hankali, sannan a ruguje batun auren da suke son yi wa baban Zainab ɗin, kinga fa nima haka na yi wa ƴan balaja'un ƴan uwan mijin nan nawa, baki ga yadda suke so na bane? Ai kamar su goyani suke ji saboda so, baki ganin ko da yaushe su Khalid suna wajensu bane? Suke shan reno ni kuma ina neman kuɗi, kamar su haɗiye su Khalid saboda so, dan haka kema abin da zaki yi wa ƴan iska kenan, ai in sun san wata basu san wata ba".

Ɗan zaro idanu Maman Zainab ɗin ta yi, a ruɗe ta ce. "Hauwa kina nufin wajen boka kike zuwa?!".

Wani kallon banza ta ɗan watsa mata kafin ta ce. "Sai aka ce maki boka ne shi ɗin? Ko kin ji nace maki boka ne? Malam sha yanzu magani yanzu fa nace maki, shi ba irin bokan da kika sani bane, malami ne".

Shiru Maman Zainab ɗin ta ɗan yi kafin daga bisa kuma ta ce. "To Hauwa me marabansa da boka?".

Da sauri ta amsa mata da "Wlh suna da maraba, kuma ke da kike wannan magana ma kin san me wadda zai auro maki ɗin take yi ne? Su hajiyar tasa kin san me take shiryawa ne? Ki zauna ke kam, kada ki tashi tsaye, wlh sai sun rabaki da jin daɗin rayuwa, kina ji kina gani ki zama ƴar aiki jaka a gabansu".

KAI MY PEOPLE'S, WAI YA NAGA AUNTY HAUWA NA ƘOƘARIN GURBATA MANA TUNANIN MAMAN ZAINAB ƊIN MU NE?😥😳 BAN GANE BANE😳

TO SAI DAI MUN HAƊU ON MONDAY DAN MUJI ME MAMAN ZAINAB ZATA YI, WANI ACTION ZATA ƊAUKA A KAI, ALLAH DAI KASA MU DACE KA RABAMU DA JAHILAN KAWAYE!.



🤍PRINCESS TEEMA taku ta amana🔥



Share fisabilillahi 👏



ALLAH KA KARA MANA SON MANZON ALLAH 🔥🤍

🤍🔥𝗥𝗔𝗪𝗔𝗡𝗜𝗡 👑 𝗭𝗔𝗟𝗜𝗡𝗖𝗜🔥🤍


🔥CROWN OF INJUSTICE🔥







𝗠𝗔𝗟𝗟𝗔𝗞𝗜𝗡

❤️‍🔥FATEEMA ZAHRA MUSA ❤️‍🔥
(❤️A-K-A 𝑷𝑹𝑰𝑵𝑪𝑬𝑺𝑺 𝑻𝑬𝑬𝑴𝑨🔥)







🔥🤍T🔥🤍T🔥🤍W🔥🤍......💻




❤️𝑫𝑨𝑻𝑬 15/7/2024.....✍️📚🌹




For information 0816139058 Whatsapp me only!!.




Dedicated to Abubakar Sadiq.❤️ Baki ba zai iya faɗar alkharinka a gareni ba, ina matuƙar farinciki tare da godiya da irin kwarin gwiwa da karfafa mun da kake yi, a kullum nace na gaji cewa kake yi ki kara hakuri ki dage, ki jure ki daure, ba'a cin nasara sai an dage, kwarin gwiwar da kake bani ba zan iya biyanka ba, ban biyaka ko sisi ba, amma haka ka zage kake karfafa mun gwiwa tsakaninka da Allah da zuciya ɗaya, wanda nasan a duniyar yanzu ko kuɗi ka biya mutun ba zai taɓa yi maka hakan tsakaninsa da Allah ba, sai dai ya yi ta yi maka kauce kauce! Amma kai ba ko sisi kake karfafa mun gwiwa, da nace zan ɗauki hutu koda na wata biyu ne kafin na ɗaura da rubutu, bawan Allah cewa ya yi a'a Fatima, kada ki yi haka, ko dan masoyanki kawai ki ɗaura, ki huta kada ya wuce two weeks. Saboda shi da A'ishah Baita Jidda na fara yin posting ɗin RAWANIN ZALINCI, i really appreciate gaskiya.💘

Aisha Baita Jidda, kema kwarin gwiwar da kike bani bakina ya yi kaɗan wajen zayyano shi, ba abin da zan ce maku face Allah ya bar kauna ya kuma bar zumunci.

Hjy Halimatus Sadiya, Ubangiji Allah ya baki ƴaƴa masu albarka waɗan da zasu kasance alkhari a gareki har bayan ranki, alkharinki a gareni ba zai faɗu ba, mace mai farar zuciya.💘

My admins godiya da tarin jinjina a gareku.💘



🤍𝑺𝑻𝑬𝑷 1......✍️📚🔥





اللَّهُمَّ صَلِّ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا صَلَّيْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ، اللَّهُمَّ بَارِكْ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا بَارَكْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ❤️









E____________14🔥




"Hauwa wannan fa bashi da maraba da boka wlh, in kuma haka ne ni ba zan iya zuwa wajen boka ba, mama zan iya neman wani abin a wajen wanin Allah ba, Hauwa kin canza, kamar ba Hauwar da na sani ba, ki ji tsoron Allah, wlh wanin Allah bai isa ya baki abin da Allah bai baki ba, ki sani in kina cikin ƙunci da bakin ciki kika nemi taimakon wanin Allah, to wlh kofofi sama da dubu ne na sabuwar ƙunci da bakincikin da baki taɓa zato ba zasu buɗe maki, matsaloli ta ko'ina zasu fara kunnu maki kai ki rasa yadda zaki yi da su, wlh Allah ne kawai zai iya warware maki halin kunci ba waninsa ba".
Ta kai karshen maganar zuciyarta cike tab da damuwa, haƙiƙa ta yi matuƙar jin rashin daɗi na halin da Aunty Hauwar ta faɗa, a tare fa suka yi makaranta suka yi komai, amma ace Aunty Hauwa ta canza cikin ƙanƙanin lokacin nan, abin da ban mamaki kuma abu ne da dole a tausaya mata, babu daɗi sam.

"Hmmmmm maman Zainab kenan, to ki zauna, wlh ki na ji kina gani bakin ciki zai kashe ki, yanzu an gaya maki ita wadda za'a auro ɗin haka take zaune ne? Ai ke yanzu ba cutar da kowa zaki yi ba, kare kanki zaki yi, to me laifi a kare kai? Baki cuci kowa ba, baki zalinci kowa ba, kawai kwatar hakkinki daga wajen waɗan da suka cuceki zaki yi, amma ki ke wannan magana ko? To ni babu ruwana, na yi maki iya abin da zan iya, kina ji kina gani dai zaki zama jaka a wajensu, kuma zaki ce na gaya maki, baban Zainab ma sai ya koma tsaginsu, sai dai ki zama ƴar kallo".
A faɗa ce ta kai ƙarshen maganar, ita a dole ranta ya yi mugun ɓaci.

Nisawa ta yi kafin ta ce. "Amma Hauwa in tambayeki mana?".

"Allah yasa na sani". Ta bata amsa a takaice.

"Idan kin ce ba cutar kowa zan yi ba kwatar hakkina zan yi, me zai haka ba zan roƙi Allah da ya kwata mun hakkin nawa ba? Kin dai sai babu wanda ya kai Ubangiji adalci da kwatawa mara karfi hakkinsa a hannun mai karfi ko?".

Shiru Aunty Hauwar ta ɗan yi, da alama tana sake tunano abin faɗa ne, dan ita dai zuciyarta ta rigada ta yi nisa, ta yarda da bokaye za'a ce, dan waɗan nan ba malamai bane ba.

"Maman Zainab ko kin roƙi Allah wlh ba za'a fasa wannan aure ba".
Ta faɗa tana duba time a wayar hanunta kirar Infinix note 10.

"Meyasa zaki ce ba za'a fasa auren ba?".

Nan ma shiru ta ɗan yi kafin ta ce. "Maman Zainab kin taɓa ganin wanda ya yi addu'a ya roki Ubangiji da ya ruguje wani sunna na ma'aiki ko kuma wani abin da annabi ya halakta ya kuma kawata shi wa al'ummarsa kin taɓa ganin wanda ya roki Allah ya ruguje wannan abin kuma Allah ya amsa ya ruguje shi? Ai ba'a ta'addanci a cikin addu'a, Allah ba zai amsa ba, dan haka ko kin roƙi Allah a banza kika yi, Allah ba zai ruguje aure sunnar ma'aiki babu gaira babu dalili ba".

Nan fa zuciyar maman Zainab ya shiga ruɗu da tunani, Aunty Hauwa anyi ƴar duniya, tabbas a nan tana da gaskiya, babu wanda ya isa ya sanya Ubangiji ya rusa faɗar manzon Allah (S.A.W) koda kuwa kwana dubu zaka yi kana sallah kana addu'a, idan ka yi wasa ma a kan hakan sai Allah ya hallakar da kai, sau nawa zaku ga rabon aure yana kisa, sai kuga mutum ya kafe a kan ba'a za'ayi wannan aure ba ko ba zai bada ƴarsa ga wani ba idan yana raye, to idan Allah ya ƙaddara akwai auren a tsakanin wannan family, sai kuga Allah ya kawar da wanda ya hana ayi auren ɗin, ya mutu kuma a ɗaura auren zam zam a zauna babu mai hanawa, so da dama hakan tana faruwa, sai kiga mutun yana mutuwa bai fi da sati biyu ba anyi bikin ƴarsa ko wani makamancin haka, so rabo tana kisa har lahira, dan haka mu guji kin abin da Allah ya halakta mu ce mu sai mun haramta.

"To Hauwa in dai haka ne nima sai na hakura kawai na bari baban Zainab ɗin ya yi auren ko?".
Ta yi maganar muryarta a sanyaye, da alama jikinta duk ya yi sanyi.

Wani irin harara Aunty Hauwar ta wurga mata kafin ta sake fara wannan shegen dogon jawabin nata.
"Hakura fa kika ce? Lallai maman Zainab har yanzu baki da hankali! To idan kin hakura ya yi aure hajiyarsa fa? Ita ma haka zaki zauna da ita a tare da amaryar suna yi maki cin kashin da suke so? Kin dai san ƴar cikin dangi zai auro ko? To tasu ce ita ɗin, zasu goya mata baya ne ta taka ki son ranta ba yadda zaki yi, bare kuma ke da basu son ganinki a gidan, ai kin shiga ɗari ma kenan ba uku ba, malama kawai idan zaki tashi tsaye ki nemawa kanki mafita ki tashi tsaye, idan kuma ba haka ba wlh bakinciki ne zai zama sanadiyar ajalinki kin ji na gaya maki, waye ya ce maki yanzu ana zama shiru? Ai a zamanin da ne aka yi wannan haukar, yanzu ko mahaukacin kura aka kwanto maki maza ki yi fito na fito da shege, ke baki ga ko aljani idan kika nuna baki da tsoro shakkarki yake yi ba? Ai kawai haukacewa ƴan iska zaki yi duk kici ubansu, ki gasawa shegu aya a hannu, barema wannan Uwar Haidar ɗin, shegiya mai kafa kamar na shamuwa, saboda ita mijinta soloɓiyo ne ko abinci baya iya neman masu, baya iya ciyar da ita shi ne take yi maki bakinciki da hasada, wannan da ace ba ubansu ɗaya da baban Zainab ba da tsab zata aure shi, shegiyar mata dangin mayu"

Ta kai karshen maganar tana cikin kunar rai, ta kuma kai karshe tare da miƙewa da nufin tafiya.

"To Hauwa ina kuma zaki je?".
Still dai cikin sanyin murya ta yi maganar, da alama jikinta ya yi sanyi sosai.

"Ina zan je kuwa maman Zainab? Gidana mana zanje, me zan zauna nayi maki? Ina ce maki ga shinfiɗaɗɗiyar hanya mai kyau kina ce mun lallai ke ta saman dutse zaki bi ki wuce, ba dole na kama kai'na ba, kuma kada ki sake gaya mun wannan kayan takaici na

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login