Showing 45001 words to 48000 words out of 296878 words

Chapter 16 - RAWANIN ZALINCI BOOK 1 COMPLETE HAUSA NOVEL

20 Dec 2025

33

mama, ni ina waje sama sama najiyosu suna tattaunawa da mama......".

Katseta mamar tasu ta yi da cewa. "To karya aka yi mashi ne? Ai idan da baya yi makotansu ma ba zasu sani ba, abin da kika ga har makota sun sani ai kinsan ba karamar abu bace ba, abin ya yi yawa kenan".

Dafe kansa ya yi, dan shi yasan ba wata matar da ta gaya masu, karya ne, Haidar ne ya kai masu wannan magana, dan shi ne mai kwasan duk abin da yake faruwa a cikin gidan yana gaya masu, kuma duk abin da Haidar yake yi mamarsa ta koya mashi, dan ita ce tun yana ƙaramin yaro idan ya je wajenta sai ta rinƙa tambayarsa me aka yi a gidansu Zainab ɗin, me yake faruwa a gidan, shiyasa babban kuskure ne idan yaronka ya je waje ya dawo ka rinƙa tambayarsa me aka yi a wannan gidan, ko me suka dafa da ya je, hakan ba ƙaramin mummunar dabi'a bace kake koyawa yaro.

Ni kuma PRINCESS TEEMA shawarar da zan bawa mata a nan shi ne, kuskure ne ki bari wani daga cikin familyn mijinki da kike rikonsa ya rinƙa sanin halin da kuke ciki ke da mijinki, ke ko ɗan miji kike riko, kada ki yarda ki bari su rinƙa sanin me yake faruwa a gidan, ko kuma ya tukunyarki take, ace komai mijinki zai saya maki sai sun sani, ko cefenen gida sai sun san komai da yadda aka yi. Kun dai san abin da yake faruwa a gidansu Zainab ɗin nan kaf abu ne da yake faruwa sosai a cikin al'umma, amma dayawa daga cikin mata basu san daga ina matsalar take samo asali ba, na tabbata mata dayawan zasu gyara wasu abubuwa nasu a dalilin karanta labarin gidansu Zainab, dan labari ne mai cike da darusa sosai, ko ya kike da mutu kada ki bari ya san abin da mijinki yake yi maki na kyautatawa, kome zai saya maki ya zama sirrin ke da shi, kada ki nunawa kowa sai iyayenki da kannenki idan kina da su, domin duniyar yanzu wlh ta wuce tunaninki, ke zaki gayawa mutun abin alkhari da mijin yake yi maki dan ya tayaki murna da farinciki kin yi dace, baki san shi haushin ki yake ji kin sami abin da shi bai samu ba, hakan zai sa ya yi duk yadda zai yi ya shirya maki mugunta, dan tsabar bakin ciki da hasada, dan haka mata sai ku kula, maman Zainab tun farko ita ta yi kuskure, ita ta yi ganganci da ta sakewa Haidar fuska, ta kyale shi yana shigo masu har cikin ɗaki, duk abin da Baban Zainab zai yi ma matarsa da ƴaƴansa sai ya sani, kome suke ciki yana sane, a lokacin maman Zainab tana ɗaukarsa yaro, a duniyar yau wlh yara sunfi manya iya gulma da munafurci, ta yi sake ga shi yanzu abin ya kwaɓe mata ba yadda ta iya, abu ya fi karfinta, Allah dai ya kyauta ya kawo mata mafita.

"Maman Hanif zaki iya gane fuskar matar?". Cewar baban Zainab ɗin, duk da zuciyarsa tana gaya mashi Haidar ne ya je ya kai masu rahoton ko ya kirasu a waya ya gaya masu cewa babansu Zainab ɗin ya dawo dasu laces and atamfofi a leda, sai dai bai isa ya nuna cewa yasan Haidar ɗin bane, dan idan ya ce shi ne to ba makawa wata ruwan bala'in ce zata sauko mashi, dan yanzu Maman Haidar ɗin zata yi tsalle ta dire ta ce ai ya zagan mata yaro, ita ma kakan ta hau kai ta zauna.

Amsa maman Hanif ta bashi da cewa. "Matar sanye take da nikaf a fuskarta, ban ga face nata ba".

Shiru ya sake yi yana tunanin irin wannan rayuwa, tabbas bai yarda da zancen Maman Hanif ɗin bama, ba wani bata gane wacece bace, gaya mashi gaskiyar cewa Haidar ne ya yi hakan ne ba zata yi ba, domin Haidar ɗin ne ya san cewa ya ɗauko atamfofi daga kasuwa, shi ne kuma yasan cewa ya sayo masu abubuwa na mata daga kasuwa, so dole shi ne ya kai rahoto.

Kakar tasu ce ta katse mashi tunanin da yake yi cikin faɗa da cewa wlh dukka kayan nan da ya kawo ya yi maza ya kwasosu ya kawo mata dukka.

Da yake zaman lafiya yake nema, sai ya ce da maman Zainab ta je ta ɗauko masu kayan, ya kudurci niyar zai kawo masu wani ba tare da sanin kowa ba, ko Sadiq ba zai bari ya sani ba bare Haidar.

Da sauri Maman Zainab ta wuce cikin parlourn, sai kuka take yi hawaye bibbiyu, wannan jarabar bala'i dame ta yi kama?

Kamar yadda ya kawo masu kayan a leda haka ta ɗauko ta fito masu da shi, dama can bata wani cire kayan daga ledojinsu ba, dama sun bari sai da safe ne su buɗe suga irin kayan da ya kawo masu.

Tana zuwa ta duka ƙasa ta miƙawa sirikar tata.

Cikin faɗa tasa hannu ta karɓa tare da cewa su Maman Haidar su wuce su tafi, sannan ta dubi baban Zainab ɗin cikin fushi ta ce maza ya sameta a gida, daga haka suka wuce fuuuu kamar wasu kumfaye suka nufi waje.

Suna fita Maman Zainab ta saki wani marayar kuka tare da juyawa da sauri ta koma cikin parlourn.

Bayanta baban Zainab ɗin ya bi, hakuri ya je ya rinƙa bata tare da yi mata alkawarin anjuma da rana zai kawo mata wasu kayan waɗan da suka fi wannan kyau.

Cikin kuka ta ce ita ba kayan ne ya dameta ba, meyasa zasu rinƙa zaginta haka? Su zageta su zage iyayenta, laifin me ta yi masu?.

Hakuri dai ya cigaba da bata, ba shi ya tafi kasuwa ba har sai da ya san ya sanyata murmushi ta cire damuwar a ranta, sannan ya fito ya nufi kasuwa, shi kuma Haidar sai zuba barci yake kamar wani gawa, duk wannan rigima da aka yi a cikin gidan sam bai sani ba, nauyin barci ke gare shi, idan ya yi barci kamar wanda ya mutu.

Baban Zainab na tafiya ta rufe kofar parlourn da key ta wuce cikin bedroom nata ta haye gado domin ta ɗan yi barci, dama haka take yi, zata tashi tun asuba ta yi aiki, idan ta sallamesu suka fita sai ta kwanta ta yi barci zuwa 11, sannan ta tashi ta hau aikin girkin rana, dan karfe 2 dai'dai Sadiq zai zo ya ɗaukawa baban Zainab abinci rana zuwa kasuwa, su Khadijah kuma karfe 3 suke tashi makaranta.

To bari mu waiwaya bangaren su KAMRAN, wato daji kuma muga me ake ciki tun da Maman Zainab ta yi barci.

🏞️FOREST🏞️

Tafiya Kamran yake yi cikin wannan shiga tasa dai da kuka sani, ya ratayo kwari da baka a bayansa, da alama farautar nama zai je yi, yanzu ya zama matashi, kyau da cikar haiba tare da kamala sun kara bayyana a tattare da shi, yanzu yana da 25 years, dan rabonsa da su twins yanzu shekaru 10 kenan, kirarsa na jaruman maza ya kara bayyana, Mamma ta iya reno sosai kam, cikakken jarumi ne mara tsoro, haka yake kutsa cikin wannan ƙungurmin dajin babu ko ɗar ɗar a tattare da shi.

Sai tafiya yake yi Rocky yana gefensa, yanzu Rocky ma ya tsufa, ya zama wani bujumi da shi, ya kara girma sosai.............


Masu buƙatar littafin TRIPLETS daga farko harshen su yi mun magana ta wannan number tawa, 08161390581.*



🤍PRINCESS TEEMA taku ta amana🔥



Share fisabilillahi 👏



ALLAH KA KARA MANA SON MANZON ALLAH 🔥🤍

🤍🔥𝗥𝗔𝗪𝗔𝗡𝗜𝗡 👑 𝗭𝗔𝗟𝗜𝗡𝗖𝗜🔥🤍


🔥CROWN OF INJUSTICE🔥







𝗠𝗔𝗟𝗟𝗔𝗞𝗜𝗡

❤️‍🔥FATEEMA ZAHRA MUSA ❤️‍🔥
(❤️A-K-A 𝑷𝑹𝑰𝑵𝑪𝑬𝑺𝑺 𝑻𝑬𝑬𝑴𝑨🔥)

Writer of DUK KARFIN IZZATA, TRIPLETS, and now RAWANIN ZALINCI.








🔥🤍T🔥🤍T🔥🤍W🔥🤍......💻




❤️𝑫𝑨𝑻𝑬 9/7/2024.....✍️📚🌹






🤍𝑺𝑻𝑬𝑷 1......✍️📚🔥





اللَّهُمَّ صَلِّ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا صَلَّيْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ، اللَّهُمَّ بَارِكْ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا بَارَكْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ❤️









E____________10🔥


Sai tafiya yake yi Rocky yana gefensa, yanzu Rocky ma ya tsufa, ya zama wani bujumi da shi, ya kara girma sosai.

Sai kutsawa cikin dajin sosai suke yi, da yake basu saba zuwa wannan yankin ba a cikin dajin, sai Rocky ya fara yi mashi alamar sun wuce dai'dai in da suke tsayawa fa, sun fara shiga wani yanki na daban, sai alama yake yi mashi ta hanyar tsayawa yaki tafiya.

Sarai Kamran ɗin yasan me Rockyn yake nufi da shi, amma sai yaki kula shi, domin yau yana da burin ya tsalleke yankinsu ya shiga wani, dan shi ma dai ya kalli wannan dajin da kyau da kyau.

Da dai Rocky yaga da gangan Kamran ɗin yaki kula shi, sai ya sha gabansa tare da ɗaga kai sama zai zuba wannan kukan nasu mai rikita dabbobin dake yankin.

Hannu Kamran ɗin ya ɗaura mashi a saman kansa, still da wannan yare nasa dai ya yi mashi magana a kan cewa ya bari suje wasu yankuna koda guda biyu ne a cikin dajin dan suga abubuwa, wata kila akwai abin da akwai a sauran yankunan babu a nasu part ɗin, sai su ɗebo su kawowa Mamma.

Girgiza jiki Rocky ya yi kafin ya wuce gaba, da sauri Kamran ɗin ya ce lallai ya dawo baya ko kuma ya dawo su jera a tare kamar yadda suka saba tafiya.

Kin dawowa ya yi, sai ma cigaba da tafiya da ya yi.

Shi kuwa Kamran kamar ya kifa mashi mari dan haushi, sai dai koya mare shi ma shi ne zai ji zafin hannunsa, Rocky kam babu abin da zai ji.

Kamran yana matuƙar jin haushi idan suna tafiya Rocky ya wuce gaba, abin yana baƙanta mashi rai sosai, ya fi son shi ya yi gaba, a cewarsa idan Rocky ya yi gaba kenan tsaro Rockyn yake yi, shi kuma wai baya son ace ga wani yana bashi tsaro, yana ji da jarumta sosai, ya fiso ace shi ne a gaba shi ne jarumi.

Cak suka tsaya a wani wani mai cike da dogayen itatuwa masu yelwar cikar ganyayyaki korayen shar, kasancewar itatuwar suna da tsawo sosai, sai cikar ganyayyakin jikinsu bai sa wajen ta yi duhu ba, sai ma hasken rana da ya bayyana ta tsakiyarsu, abin ya kawatar da mai kallo matuka, kasan wajen ya kasance farin yashi ne tamkar yashin bakin manya manyan tekuna na ruwa.

Bin wajen da kallo Kamran ya fara yi, hakiƙa wajen ya yi matuƙar burgesa sosai, ga yanayin weather wajen is very very so nice, akwai yelwar ɗumi a wajen, tamkar ba a cikin dajin wajen yake ba, da yake dama dajin Allah mai girma haka ai sai abin da ka gani kawai, Allah ya yi ikonsa kala kala a ciki, duk abin da ka gani kawai ka gara jinjinawa iko da kudura ta Ubangiji.

Shi kansa Rocky da yake yawace yawacensa son ransa, babu inda baya shi ga, tabbas wannan waje ta bashi mamaki kuma ta yi matuƙar burgesa. Shi dai Kamran yana zuwa bakin teku ya ɗebi wasu abubuwa daga cikin albarkatun cikin ruwa, amma bai taɓa ganin farin yashi (ƙasa) tas irin na wannan waje ba, dan wannan ya fi ƙasar bakin teku haske sosai, idan hasken rana ta haska yashin ma har wani kyalli sosai yake yi. Gabaɗaya ma yanayin tsarin wajen idan ka gani sai ka ji imaninka ya karu, domin babu ɗan adam da ya isa ya yi wannan halitta, yadda kasan a manyan wajajen buɗe idanu na duniya suke, tamkar ba'a cikin dajin ba.

Duk da cewa Kamran bai san Allah ba, bai ma taɓa jin sunan Allah ba, bai san a akwai Allah ba, bai san akwai wanda yake halittar abubuwa ba, amma da ya zo wannan waje ya ji a jikinsa yana son sanin wadda yake halittar waɗan nan itatuwa da sauransu, saboda itatuwa ne irin masu bala'in tsawon nan, bai taɓa ganin irinsu a cikin wannan dajin ba, dan suna da tsawo sosai gaskiya, shi ne yasa ya ji cewa gaskiya yana son yaga waye ne yake gyara itatuwar nan haka? Waye mamallakin wannan dajin? Ya kuma kudurci niyar idan ya koma gida sai ya tambayi mamarsa, sai ya tambayeta ta gaya mashi wanene mamallakin wannan dajin? Dan a ilimin da yake da shi dai yasan abu bata kyara kanta, dole duk abin da ka gani akwai makerinta, musamman idan ya waiwaya ya dubi yadda Mammansa take kyara tukanen dafa abinci da taɓon da yake ɗebo mata, sannan ta kyara kwanikan cin abinci da katakon itatuwa da yake saro mata, hakan ce ta kara tabbatar mashi da cewa lallai komai da ka gani akwai wanda ya yi shi......... Toh fa, Kamran ya ɗauko babbar magana, kuma ya fara tunanin ta gaskiya, domin komai da ka gani a duniyar nan baya taɓa kyara kansa, masu cewa babu Allah kowaye ya halicce su?🤔 A barka da iya dutse ma kawai ka gaya mana waye ya yi ta?🤔 Ko kuma ka kawo wani ya yi ta mu gani, an dai ba zata kyara kanta ba kam, idan ka kai dubanka izuwa kan motoci da abubuwan hawa, dukkansu akwai waɗan da suka kyarasu, to sai halittun Ubangiji ne za'a ce babu wanda ya haliccesu dan kin gaskiya da son dole sai an shiga wutar jahannama?.🤔 To Allah ya kyauta ya kuma yafe mana zunubanmu ya kara ɗauramu bisa tafarkin koyarwan fiyayyen halitta.

A hankali hankali kunnuwansa suka fara tsinkayo mashi sautin zubar ruwa sha tamkar ruwan sama.

Dawo da kallonsa ya yi daga kallon wajen izuwa kan Rocky. Kasa kunne shiru suka yi dan su ji menene yake wannan shahhhh kamar zubar ruwan?.

Karar tana ɗan nesa daga in da suke, hakan yasa Kamran ɗin ya kara gaba domin ya ga menene? Kai tsaye babu tsoro ko shakka ya nufi ta hanyar da yake jiyo wannan kara.

Da sauri Rocky ya rufa mashi baya, haka suka cigaba da tafiya, sai dai a wannan karon tafiyarsu ta sauya daga ta jarumta izuwa ta mutumin daji, wato tafiyar sanɗo kenan, tamkar wadda yaga wata nama zai farauceta, saboda basu san me yake wannan kara ba, gada ya zamana sun dimfari abin gadan gadan kuma ya fi karfinsu, gara koma menene su yi mashi tafiyar mage mai kwanciyar ɗaukar rai, idan yaso in sun ga menene, sai su san abin yi.

Kara matsowarsu ta in da wannan kara yake tashi ne ya bawa Kamran ɗin damar fahimtar cewa lallai ruwa ne yake zuwa daga ƙoramar dutse, duk da cewa babu irin wannan ƙoramar dutse dake zubar da ruwa a yankinsu, amma Kamran ɗin yasan da akwaita a cikin wannan dajin sosai, dan idan ya tsaya a saman ɗaya daga cikin tsaunikan dake ta kusa da su yana iya hango koraman dake kusa da yankinsu, waɗan da suke zubar da ruwa, sai dai kanana ne waɗan da suke kusa da su, ba katafare tamkar wannan da yake karan bane, su waɗan can ma ba zaka ji karar ruwan sosai ba, amma shi wannan karar ruwan tun daga nesa kunga suka fara jiyo shi, alamu sun nuna katafaren ƙorama ne sosai.

Jin cewa sautin zubar ruwan korama ne yasa Kamran ɗin nufar wajen cikin takun jarumta tare da isa da ƙasaita, akwai dogayen ciyayi a gabansu waɗanda suka kare masu hangen ƙoramar daga nesa, kai tsaye ya nufi wajen ciyayin. Shi kuma Rocky wata hanya daban ya bi, dan yana jin wata iriyar kamshi a wajen wadda sam bai yarda da ita ba, kunsan su dabbobi da kamshi ko wari suke iya tantance abu yana waje ko akasin haka, musamman ma ɗan adam, da kamshin mutun suke iya fahimtar lallai akwai ɗan adam a wannan waje, so shi Rocky ya ji kamshi ne ya tafi duba menene?

ROCKY BA DAI GULMA BA, WAI YA JE DUBA MENENE KAI JAMA'A 😅

Shi kuwa Kamran yana zuwa ya sa hannu ya ya ye waɗan nan dogayen ciyayi dake a wajen, nan take katafaren ƙoramar ta bayyana a idanuwnsa.

Zaro dara daran idanuwan nan nasa ya yi yana mai kallon ƙoramar, katuwa ce sosai, ruwan da yake taruwa a ƙasarta ma teku ne guda, ruwan yana ganganrawa ne har izuwa cikin tapkeken tekun dake gaba da ƙoramar, sam Kamran duk yawonsa a cikin wannan daji bai taɓa sanin cewa akwai wannan tapkeken tekun ba, haka zalika bai taɓa sanin da akwai wannan tapkeken ƙoramar ba.

A zahirin gaskiya kowa ya kalli Kamran a wannan hali da yake ciki da kuma irin wannan tsayuwa da ya yi zai ce wannan ƙoramar yake kallah, amma kuma sam ba ita yake kallah ba, shi kwata kwata idanuwansa ma basu sauka a kan ƙoramar ba, yana yaye ciyayyin idanuwansa suka yi wani irin kyakkyawar gani wanda bai taɓa yin irinsa ba, hakan tasa bai ma bi ta kan ƙoramar ba, kawai ya tsaya cak yana ta kare mata kallo.

Macece ƴar yarinyar da bata wuce shekaru goma ba a duniya, kyakkyawar gaske ce sosai, a kallon farko ma idan ka kalleta sai ka rantse da Allah aljanace ta rikiɗe izuwa siffa mafi kyau a duniya, sanye take da kaya masu bala'in kyau sosai, ba irin kayan dajin bane, hakan yasa ta sake yin kama da aljana, domin kuwa kayan jikin nata ba kaya ne kamar sauran kayayyakin da kuka saba gani yau da kullum ba.

Wata iriyar skit ce wadda daga kugunta zuwa mazaunanta ya yi mata daidai cif cif, daga dai'dai matsayar hips nata zuwa ƙasa ya yi wani irin bala'in buɗewa sosai, sai ƴar farar vest ta sama wadda ta tsaya mata a iya cibiyarta, launin skit ɗin pink color ne, yana da kyalliya sosai a jikinsa wanda kwalliyar ta mamaye ko'ina a jikin kayan, baka iya tantance ainahin yadin da aka yi amfani da shi wajen yin wannan sket ɗin, saboda yawan kwalliyar jikinta, ga kuma duwatsu masu haske da aka kawata ta da shi.

Zaune take a

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login