Showing 42001 words to 45000 words out of 296878 words
labulayenmu a sake".
Shiru Khadija ɗin ta yi mata, bata sake yin magana ba. Zainab bata shiri da duhu ne, bata barci cikin duhu, idan kunga sun kashe wutar ɗakin nan nasu to sai dai idan Zainab ta yi barci ne, sai Khadijan ta kashe, wani lokaci dukkansu suna yin barci su barshi a kunne, sai iyayensu sun shigo yi masu addu'a, sannan ne suke kashe masu wutar ɗakin.
Kwanciya Zainab ɗin ta yi tana tunani rayuwar yayar tata.
A hankali Khadijar ta ambaci sunanta Zainab.
Juyawa gareta Zainab ɗin ta yi suna fuskantar juna.
"Lafiya Aunty Khadina?".
Ajiyar zuciya ta sauke kafin ta ce. "Babu komai, amma anjuma idan kin tashi yin sallar dare ki sakani a cikin addu'a sosai, dan ni yanzu na shiga lokacin rashin sallah tun bayan sallar issha da na yi, dan haka kada ki tasheni yau".
Shiru ta ɗan yi kafin ta bata amsa da cewa. "Aunty khadina ai kinsan kullum ina yi maki addu'a, da izinin Allah ba zaki auri Yah Haidar ɗin nan ba, Allah ni kakan nan ma wani lokaci idan tana masifar nan tata kamar na kifeta da mari nake ji".
Harara Khadija ɗin ta wurga mata kafin ta ce. "Ki mareta ta mutu ki shiga uku, wannan tsohuwa baki mareta ba ma tana rangaji ita kaɗai a saman iska, ai kina yin kuskure ko kaɗan ne kika bugeta wlh ranga ranga za'a kwasheta, kin ga daga nan ke kuma sai koma".
Guntun tsaki Zee ɗin ta ja tare da juyawa ta bawa Khadijahr baya tana wani ƙara haɗe rai. Da alama fa da Zainab aka ce za'ayi wa wannan aure to ba shakka zata yi fito na fito da su, sam lamarinta babu sauki, da wuya su Maman Haidar su sha a hannunta, dan da alama zasu gasu sosai, yanzu ma dan mamanta na taka mata birki ne, ba dan haka ba, da ba abin da zai hanata yi wa Maman Haidar ɗin tas idan ta zo gidan tana zuba masifa, amma Mamansu da yake macece mai tarbiya tana tsawatar masu sosai, tana gaya masu maman Haidar dai ɗaya take da babansu, so idan har Zainab zata yi mata rashin kunya, to kenan zata iya yi wa babanta, dan haka babu ruwansu, idan ma sun ga Maman Haidar ɗin ta zo maza su wuce cikin ɗaki, kada ma su kawo kunnuwansu a kan abubuwan da zata yi ta faɗa, su kyaleta watarana sai labari.
A can parlourn kuwa, Haidar ya zo da nufin su yi hira da Khadijah, babanta ya ce mashi ta yi barci, tsabar bashi da kunya wai a tasan mashi ita akwai abin da zai gaya mata ne.
Da farko Maman Zainab zata je ta tasheta, sai baban ya ce a'a a barta ta yi barci sai da safe ko idan sun dawo daga makaranta sai ya gaya mata koma me zai gaya mata, yanzu dai tun da ta rigada ta yi barci ya kyaleta.
Da farko kamar ba zai tafi ba, dan ba hakan ya so ba, ransa ta ɓaci, ya so ne su yi hira da ita, amma da yake kawun nasa ne ya yi magana dole ya hakura, da ace Maman Zainab ita kaɗai ce a gidan da ba abin da zai hana shi shiga cikin ɗakinsu ya tasheta ta fito ayi hiran dole, dan ba kunya ne ke gare shi ba, ga rashin hankali cikakke, kuma kun san ba ganin mutuncin Mamansu yake yi ba, tsab zai iya cewa zai shiga ya tasota da ace baban baya nan.
Amma fa duk rashin kunyar Haidar yana tsoron kawun nasa, dan fa baban Zainab shi ma mutun ne mai zafi sosai, kawai sai anyi mashi ba dai'dai ba ɗayar halin nasa ta zafin rai take bayyana, Haidar ɗin ya ci duka a hannunsa lokacin da yake kin zuwa makaranta, ya sha punishment, sai da kakansu wato maman baban Zainab ɗin ta ce bata so kada ya sake dukan Haidar, ya kyale shi mana tun da ba za'a ci karatu ba, har da cewa wai shi ma baban Zainab ɗin da ya yi karatun ai ga shi nan result ɗin bata amfane shi ba, ya ajiyeta a cikin akwati kawai yana kallo, to dan haka ya rabu da Haidar ɗin, kun san kaka dama yawanci haka suke, sai su hana a ladabtar da jikokinsu.
Haidar dai kamar zai yi kuka ya wuce ya koma cikin ɗakinsu, a lokacin shi kuma Sadiq yana zaune ya zuba abinci a cikin plate dan ya ci abinsa, shi ko zancen auren ma baya yi, yanzu haka master nasa yake haɗawa a ɓangaren computer engineering, ya gama degree nasa bawan Allah, akwai shi da ƙoƙari sosai, so baya batun aure ma, mata ma yanzu ba su ne a gabansa ba, ilimi da kuɗi kawai yake nema, mamansa ta ce ya nemi kuɗi da ilimi mata zasu biyo shi har in da yake ba sai ya wahalar da kansa ba wajen bin matan ba, ya bi kuɗi da ilimi a guje su kuma mata zasu biyo shi a guje, uwa ta gari kenan, saɓanin uwar Haidar da take cewa ilimi bashi da wata amfani.
Washegari da safe kamar yadda suka saba, tun karfe biyar na asuba bayan sun yi sallar asuba Maman Zainab ta wuce cikin kitchen, abinci mai rai da lafiya ta girka masu a matsayin breakfast, a tare da Khadijah suka yi aikin komai, ita kuma Zainab ta gyare masu gidan ko'ina tsab, ta zuba turaren wuta mai rai da lafiya kamar dai yadda suka saba, yanzu Maman Zainab ƴan'matanta sun girma, aiki ya ragun mata sosai, idan Khadija tana kitchen, ita kuma Zainab zata hau gyaran gida, komai a tare suke yi su ukun kamar wasu kawaye, haihuwan ƴaƴa mata akwai daɗi kuma akwai falala da rahama sosai, ƴa macece kawai Allah ya ce a ranar gobe kiyama zata kai iyayenta aljanna, manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallama ya ce duk iyaye da suka haifi ƴaƴa mata guda uku, suka tarbiyantaddasu har suka aurar da su ba tare da waɗan nan ƴaƴa sun taɓa yin zina ba, to ba shakka sanadiyar haka Allah ya bawa waɗan nan iyaye aljanna, ƴan macece kawai take da wannan falala, amma a duniyarmu ta yau dayawan iyaye maza basu son a haifa masu ƴaƴa mata, ɗa namiji baya kai iyayensa aljanna kai tsaye, mace kawai Allah ya bawa wannan falala, ai ko dan kwaɗayin aljanna dole muso ƴa ƴa mata, idan ka duba sahabban Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallama, irin shekarun da suka shafe suna aikata aikin Allah ba dare ba rana kafin su sami aljanna, wasu daga cikinsu ma kashesu aka yi, wasu daga cikinsu kafurai sun azabtar dasu azaba mafi muni, idan ka dube su ka dubi ɗan aikin da kake yi, sai ka ji aljanna fa ba abar wasa bace, ba'a samunta a sauki, Allah dai ya bamu ita ba dan halayenmu ba, sai dai mu roki cin albarkacin fiyayyen halitta.
Karfe 6 dai'dai suka kammala girki, ita kuma Zainab ta kammala gyaran gida har ta yi wanka ta shiryo cikin white uniform ɗinta, kal kal da shi, ya sha guga malam, ta fito fes, Zainab sarkin farin jini, kowa ya ganta sai ya ce yana sonta, sai dai akwai ta da mugun hali in ji matasa da suke biyota bata kulasu, suka ce mugun hali ke gareta......... Ni kuwa PRINCESS TEEMA na ce tsare mutunci da tsare kai dai, ba wani mugun hali munafukai, dan basu sami abin da suke so ba, bata kula kowa, ga shegen kyau jajir da ita, nan gani nan bari munafukai kawai.........😂😅
A parlourn suka zauna dan yin breakfast kamar yadda suka saba, Khadija ta wuce cikin bedroom nasu dan ta yi wanka ta shirya cikin uniform nata, ita kuma Maman Zainab ta wuce nasu bedroom ɗin dan ta taso baban Zainab ya yi wanka ya zo su yi breakfast, sai ya ɗauki su Zainab a kan mashin nasa zuwa makaranta, dama shi yake kaisu, lokacin tashi kuma sai ya bawa Sadiq key ɗin mashin ɗin daga kasuwa ya zo ya ɗauko su ya mayar da su gida sai ya dawo, islamiya kuma a kusa da gidansu yake, ba nisa sosai, so da kafa suke zuwa.
After some minutes
Gabaɗayansu sun haɗu a parlourn, baban Zainab ma ya yi wanka ya yi shirin zuwa kasuwa.
"Zainab ɗauki abincin su Sadiq ki kai masu". Cewar mamansu.
Babansu ne ya ce. "Ba na ce su zo su rinƙa ɗauka da kansu ba?".
"Yi hakuri na manta ne ban sanar da su su zo su rinƙa ɗauka ba, amma idan sun fito zan gaya masu, yanzu dai ta ɗauka ta kai masu".
Shiru ya yi bai sake magana ba.
Ita kuwa Zainab tamkar zata zunduma ihu dan bakin ciki, ga shi jiya ta yi wa Haidar rashin kunya ta gudu, yanzu in ta je idan ta yi knocking na kofar, in dai Haidar ɗin ne ya fito tasan confirm sai ya rankwasheta a kai ko kuma ya mareta, da dai Sadiq ne ya fito lafiya lou zai karɓi abincin ya koma ciki.
Rai a matuƙar ɓace tana hura hanci ta ɗauki kular abincin tare da plates ɗin ta fito.
Ta kuwa yi sa'a tana fitowa ta ci karo da Sadiq wanda ya fito a lokacin shi ma, ya fito zai fitarwa da babansu mashin nasa ne, yana shirye cikin white shaddarsa mai shegen kyau, ɗinki half jompa, ya sha hularsa, sai ya fito a babban mutun mai kima da mutunci, yanzu yana da 28 years, sai ya fito a cikakken matashi mai cike da nutsuwa da kamala.
"Kawu Sadiq ina zaka je?". Cewar Zainab ɗin.
"Babu gaisuwa sai tambayar ina zan je ko?".
Ƴar murmushi kaɗan ta yi, Zainab baka taɓa ganin fara'arta sai idan da Sadiq ko iyayenta or Khadijah suke tare, nan ne zaka ga tana murmushi.
"Ai mantawa na yi, naga kayi kyau sosai ne yau shiyasa na manta da gaisuwar, to ina kwana".
Ta kai karshen maganar tare da ƙarisowa gabansa.
Hannu yasa ya karɓi kayan abincin yana amsa mata gaisuwar kafin ya ce mata. "Ina da class 7:30 dai'dai ne, yau ba kasuwa zan wuce kai tsaye ba, shiyasa na yi kyau haka, ko baki son na yi kyau ne?".
Girgiza mashi kai ta yi tana faɗin. "Kawu Sadiq ai dama kai kana da kyau, ranar ba na gaya maka kafi mamanmu kyau ba? Baba ya ce mama dan ita fara ce kawai, da ita baka ce mummuna ce, wai ka fita kyau baba ma ya ce, so ko baka yi kwalliya ba dama kana da kyau sosai, yau ɗin ne naga kyanka ya karu sosai".
Cool murmushi ya sakar mata kafin ya ce. "Bari maman ta jiki kin ce na fita kyau, idan ta rikeki ba mai karɓarki a gidan nan, kin san ko lokacin da muke gida kafin ta yi aure bata taɓa yarda ace na fita kyau, Allah ki bari ta jiki zaki yi bayani ne ba ruwana, yadda take jin ita kyakkyawa ce ɗin nan".
Dariya sosai ta yi har sai da wishiryar dake tsakanin fararen hakwarantan ya bayyana.
"Allah kawu Sadiq ka fi mama kyau sosai, amma na san mama da Oumma take kama shiyasa, kai kuma da Abba kake kama"
Abba shi ne mahaifinsu Sadiq ɗin, kakansu namiji kenan, Abba suke ce mashi, kakansu mace kuma Oumma.
"Kai, kai, kai, lallai Zainab yanzu kam ni ne zan zaneki, Oummar tamu ce kenan mummuna ko? Shiyasa da mamarki ta yi kama da ita ita ma ta yi muni ko? To baki isa ba wannan kuma, Allah duka zaki sha, ni Oummarta kyakkyawar gaske ce da babu biyunta a duniya, mamarki dai sai Allah kaɗai yasan da waye take kama".
Ya kai karshen maganar yana fitar da wallet nasa daga aljihunsa.
Sai dariya take yi tana kara gaya mashi Allah kakarsu mace mummuna ce, shiyasa mamarsu bata da kyau sosai sai hasken fata.
Kuɗi 1k ya ciro ya bata, sannan ya juya ya nufi cikin ɗakinsu yana faɗa mata su yi breakfast da 1k ɗin idan sun je makaranta, dan yasan ƴan makaranta ba'a rabasu da saye saye na kwalama.
Sosai ta yi mashi godiya sannan ta wuce izuwa cikin parlourn ita ma.
A gaggauce suka karya, dan lokaci karfe 7 ta yi, kuma 7:30 dai'dai suke shiga cikin school kullum, babansu baya yarda su yi latti, yana kula da karatun nan nasu fiye da tunaninku.
Bayan sun kammala sai suka fito harabar gidan da nufin tafiya, su Zainab kowacce ta goyo jakarta a baya, Mamansu ta rakosu harabar gida kamar yadda suka saba.
Jin fitowarsu harabar gidan yasa Sadiq ya fito domin ya fitarwa da Baban Zainab ɗin mashin ɗinsa daga cikin kitchen ya kai mashi waje, haka suke yi kullum, shi kuma Haidar sarkin son girma yana ciki. Kun san jahilci tana tare da girman kai, girman kai kuma yana tare da shegen son girma kamar me, mutun mai ilimi wanda yasan abin da yake yi ba zai yi girman kai ba wlh, wannan sai jahili, to dai haka Haidar yake da bala'in son girma kamar menene, ga shegen girman kai rawanin tsiya.
Ya fito da mashin ɗin harabar gidan kenan da nufin ya fitar waje, shi kuma Haidar yana ciki yana aikin zuba barci, dan shi kasuwar ma sai sanda ya tashi barcinsa yake zuwa, wani lokaci sai 11 na rana yake zuwa, shegen barcin safe ke gare shi.
Murmushi ne a saman fuskar kowannensu, musamman baban Zainab, sai tsokanar Sadiq yake yi a kan ya yi kyau sosai yau dan ba Kasuwa zai je ba, wato zai je school akwai ƴan'mata a can shi ne ya tsara kwalliya ko?.
Sai murmushi Sadiq ɗin ma yake yi yana cewa da ai shi babu ruwansa da mata. Maman Zainab kuwa ta ce ba wani nan idan ba dan ƴan'mata ba ai ba zai yi irin wannan shiga a kullum idan zai tafi makarantar ba, meyasa baya yi irin shigar idan zai je kasuwa? Sai dai ya ɗauki wasu tsofaffin kaya ya sa ya tafi kasuwar, makaranta kuma a tsantsara kwalliya.
Zainab sai dariya take yi mashi tana faɗin Allah ya kama kawu Sadiq, yau asirinsa ya tonu.
Khadija kam fuska kamar ko yaushe, sam bata a cikin walwala baiwar Allah.
Sadiq bai kai ga fitar da mashin ɗin ba suka ga an banko kofar gidan an faɗo masu cikin gida.
Zainab sarkin tsoro har ta juya zata zunduma cikin ɗaki da gudu, ita kuma Khadija da yake dama hankalinta baya a tattare da ita, sai bata wani tsorata sosai ba, Maman Zainab ma saura kaɗan ta zunduma da gudu izuwa cikin parlourn. Baban Zainab da Sadiq ne kawai basu tsorata ba, suna tsaye a yadda suke.
Tun daga kofar gida ake surfa uban masifa, ba kowa bace face Maman Haidar, kakansu da kuma ɗayar ƴar babansu Zainab ɗin mai suna Zainab. Tun daga bakin kofar gida suke surfa uban masifa tamkar zasu tashi garin.
Da sauri Mamansu Zainab ta juya da nufin ta wuce cikin parlourn abinta, dan ba zata iya masu ba.
Sirikar tata ce ta daka mata tsawa a kan ta zo nan munafuka, ai wajenta suka zo, zata wani sa kai kamar wata tsohuwar munafuka zata wuce.
Cikin girmamawa ta ɗagawa surukar tata gaisuwa da "Ina kwana".
Cikin faɗa surukar tata ta ce. "Da ban kwana ba zaki ganni ne? Wato dama baki so na kwana a duniya ko? To na kwana na tashi, kuma ni dai nan gani nan bari, baku isa ku mallakeni ba, nafi karfinku".
Shiru Khadija ta yi tana sauraron kakar tata, idan kakan nan nasu tana magana sai ka rasa ina ma ta dosa, sam maganarta babu kan gado, idan ba rashin kan gado ba yanzu me ya kawo wani zancen mallaka da kuma zancen wai Mamansu bata son kakar tasu ta kwana a duniya, daga cewa ina kwana? Abin ma abin dariya, ko me haɗin ina kwana da kuma ba'a son mutun ya kwana a duniya? Kawai jaraba ce da dole sai anyi faɗa.
"Mama wai me yake faruw ne?". Cewar baban Zainab ɗin, ya yi maganar a nutse.
"Rufe mun baki hai, ai yau wlh kome wannan matar taka ta yi maka ta mallakeka sai ta karya shi".
"Sadiq ku je ka kai su Khadija makaranta daga nan ka ajiye mun mashin ɗin a kasuwa zan hau mashin ɗin kasuwa na je kasuwar". Cewar baban Zainab ɗin.
A hanzarce Sadiq ya amsa tare da jan mashin ɗin ya fitar da ita waje, su Zainab suka rufa mashi baya da sauri. Ran Zainab kamar bakar leda saboda bakin ciki, zuciyarta sai tafasa take yi, kamar ta tsinke kakan nata da mari take ji, mata ce sai jarabar bala'i, sai ka rasa me matar nan take so a duniyar nan, kamar wadda ake sakawa battery, idan ta fara zuba bala'i ita da kanta bata sanin me take faɗa.
"Mama mu je cikin parlourn koma menene sai mu tattauna a cikin nutsuwa ko?". Cewar baban Zainab ɗin dai. Ita dai maman Zainab bata da bakin magana.
Cikin faɗa mamar tasa ta ce. "Kai har kana da ɗakin da zan shiga in zauna ne? Babu in da zan shiga sai wannan bakar munafukar matar taka ta gaya mun uban me ta yi maka ka lalace ka dawo mata soko sai abin da ta ce kake yi".
Shi dai baban Zainab har yanzu bai gane a kan me mamar tasa take surfa wannan bala'in ba.
"Maman Haidar wai me yake faruwa ne? Waye ya taɓo mama yau kuma?". Cewar baban Zainab, ya yi maganar kuma yana kallon Maman Haidar dake tsaye tana wani cika tana batsewa.
"Ba gaka ga mamar ba, ai ita zaka tambaya, ni ka rai'na zaka tambaya ko?". Maman Haidar ɗin ta bashi amsa tana wani watsa mashi harara.
Nisawa ya yi kafin ya mai do da kallonsa a kan ɗayar yayar tasa dake tsaye shiru tana binsu da ido. "Maman Hanif ke ki gaya mun wai meyake faruwa ne? Me aka yi wa mama? Ko me aka ce nayi?".
Nisawa ita ma ta yi tare da fara magana a nutse.
"Wata ce nan ta je ta gaya masu cewa wai jiya ka sayawa matarka tsadaddun lace da shaddoji da sauran kaya namu na mata, ta dai ce makwabciyarku ce ita, wai maman Zainab ta mayar da kai wani soko, kai ne kake yin sharar gida da komai da komai, maganganu dai dayawa ta gayawa