Showing 111001 words to 114000 words out of 296878 words

Chapter 38 - RAWANIN ZALINCI BOOK 1 COMPLETE HAUSA NOVEL

20 Dec 2025

74

ba dai anjuma zai zo ba? Kafin ya zo mu zamu shirya shirin yin maganinshi, da kafansa zai gudu kamar yadda ya zo, ke dai kamar yadda aka saba ki shirya sosai dan ma kada ace baki son shi a gane shirinmu".

Wani irin shu'umin murmushi ta saki, don tasan Omaid bayi da wasa, yanzu zai iya shirya abin da zai tarwatsa gungun taro, shape brain ke garesu twins ɗin nan, kuma wlh duk nacinka ba zaka taɓa gane cewa sune suka yi abu ba idan suka aikata, saboda komai cikin kwarewa da kuma ilimi suke yi, kun ji da bakinsu sun gaya maku su tunani suke yi irin na actors ba boss ba, waɗan nan yara sai dai shirin Allah, ai da mutun ya takura maka kawai ka gaya masu, cikin ruwan sanyi zasu sanya shi ya rabu da kai, sun iya shiri, yanzu dai zamu ga me zasu shiryawa Yusuf bawan Allah........😅

Sai murna Gimbiya Sarina take yi, har ta sami kwarin gwiwar zuwa ta yi wanka, cikin sauri ta diro ƙasa daga saman bed ɗin ta nufi cikin toilet dan ta yi wanka. Su kuwa kwanciya suka yi a saman bed ɗin tare da fara tattaunawa a kan yadda zasu ɓullowa Yusuf idan ya zo, nan take suka fara shirya mashi kitimurmura wadda da wuya ya tsallake, bama shi kawai ba, da wuya twins su shirya maka gadar zare ka tsallake, ba'a taɓa wanda ya taɓa tsalleke tarkonsu ba, da zarar sun haɗawa mutun tarko to sai ya afka ko yana so ko baya so, kamar wasu aljanu, akwai basira, sun gado ta ɓangare dukka biyu ne yasa har basirar ta fara yi masu yawa, sun gaji basirar King Zuhair and gimbiya Rahilarh.

Gimbiya Sarina tana fitowa wanka ta hau shiryawa, fuskarta ɗauke da annuri, saboda tasan me suka kullah, har wani zumuɗi take yi, sai ka rantse da Allah tana son Yusuf ɗin, ita da bata murmushi ma sai ga shi har da murmushi yau, saboda zasu zalinci Yusuf......... Waɗan nan Team ɗin wato da Obaid and Omaid da kuma Sarina sai kun yi masu addu'ar Allah ya shiryi Team ɗin nan nasu.

A ɓangaren Jawad da Chuchu kuwa. Tun da ya ɗauketa bai direta a ko'ina ba sai a cikin tsadaddiyar dandatsetsiyar motarsa mai tashin kai.

Da gudu driversa ya ƙarisa wajen, a gidan baya ya sauketa shi ma kuma ya shiga gidan bayan, ba ɓata lokaci driver ya shiga gidan gaba, sai shessheƙar kuka take yi mashi, sam bai bi ta kanta ba, da ta ishe shi ma sai cewa ya yi ta yi mashi shiru ko kuma ya karya kafafun nata.

Tafukan hannunta ta kai ta toshe ɗan bakin nata, gudun kada sautin shesshekar kuka nata ya fita. Wayarsa ya ciro ya kira number Mammie ɗinsa, bugu ɗaya ta ɗauka.

Gaisheta ya fara yi kafin ya ce. "Mammie please ki bawa kuyanga hijab babba ta kawo mun parking space yanzun nan".

Kamar zata tambaye shi me zai yi da hijab, sai kuma ta fasa ta amsa mashi da okey kawai. Daga haka ya katse kiran tare da kashe hasken screen ɗin wayar, ya jingina kansa da jikin haɗaɗɗiyar kujerar motar yana shakar kamshin perfume ɗin jikin Chuchun haɗe da sanyin Ac mai ratsa zuciya ta kuma kwantar da hankali.

Ba'afi 5 mins da gama waya da Mammie ɗin ba sai ga wata kuyanga ta doso katafaren parking space ɗin hannunta na rike da leda.

Ƙasa ƙasa ya ce da driver ya fita ya karɓo mashi hijabin. A hanzarce ya amsa da okey sir tare da ɓalle marfin motar ya fito da sauri.

Kuyangar bata ƙariso wajen ba ya yi saurin isa in da take ya karɓo hijabin a cikin ledarsa, da alama sabo ne gal. Tun daga yanayin nauyin hijabin a cikin leda zaka fahimci babba ne sosai, hakan ne kuma, ko da driver ya kawo hijabin Yah Jawad ya karɓa ya miƙa mata a kan ta sanya a jikinta, tana ciro shi sai taga ya fi karfinta wannan hijabi, zai ja mata har ƙasa sosai.

Ɗago idanu ta yi ta kalle shi, sam kallonsa baya a kanta, hasali ma idanuwansa a lumshe suke, bata da zaɓin da ya wuce ta sanya wannan zunbulelen hijabin haka a jikin nata.

Kamar zata yi kuka ta ware ta sanya, ya yi mata yawa over, harta wuyar hijab ɗin yafi karfinta, sai zamewa yake yi yana sulluɓewa ƙasa, ga gashin kanta dama da masifar tsantsi. Haka dai ta kai hannu ta rike wuyar dan kada ya zame, sai satar kallonsa take yi ko zai ce a canzo mata wani, amma ina idanunsa a lumshen nan yaki buɗesu kawai ya bawa driver umarnin ya wuce da su hospital.

Ba ɓata lokaci ya karɓi umarnin tare da kunna motar suka nufi asibitin nasu. Yah Jawad bai sake bi ya kanta ba har suka isa.

Katafaren hospital ne na gani na faɗa, kusan za'a ce ma da wuya a sami hospital mai girmansa a ƙasar, manya manyan masu faɗa aji a ƙasar ne suke kwanciya jinya a cikinta.

Abin mamaki dai baya karewa, da Yah Jawad suka shiga cikin hospital ɗin kuma sai yaki yarda likita namiji ya duba mashi kanwar tasa, wai sai dai mace ta dubata, ita dai tana fama da zunbulelen hijabin wadda ko matar limamin masallacin jumma'ar ƙasar saudiya bata saka kamarsa, ko kula shi shi da Drs ɗin ma bata yi ba, bama ta fahimtar me suke faɗa ba, ta dai kwantar da kanta shiru a saman gefen shoulder ɗinsa tana sauke numfashi a hankali hankali, duk gudun kada shessheƙar kukan da take yi ne ya bayyana, ya ja mata yanzun nan ya sauketa ya ce ta tafi da kafafunta, dan ƙaramin aikinsa ne ya sauketa ƙasa ya ce ta taka kafafun, hakan yasa ta kwantar da kanta shiru tana jin bakin ciki kamar ta shake shi, ya iya mugunta.

Shi kuwa sai da ya zaɓi nurse ɗin da ta yi mashi, sannan ya buƙaci ɗaki domin ya kwantar da ita wannan nurse da ya zaɓa ta duba ta.

Gabaɗaya ɗakunan da suke a cikin wannan katafaren hospital ɗin ba ɗakuna ne kamar ɗakunan sauran hospitals da kuka sani ba, waɗan nan ɗakuna sai ka rantse da Allah ɗakunan gidan wani ministar or governor ka shiga, saboda manyan kai ne suke kwanciya jinya a cikin hospital ɗin, kowane ɗaki ka shiga ɗauke yake da katafaren bed 6/7 wanda ya sha shinfiɗu na alfarma, sai ka rantse da Allah ba hospital bane, dan wasu shegun bed sheets dake saman beds ɗin ma kawai abin kallo ne, ga lafiyayyun freezers, Ac, kai harta shi kansa tiles na cikin wannan hospital ɗin na musamman ne, curtains da sauran kayan alatu na more rayuwa duk na musamman ne, kamar ba wajen yin jinya ba. Ka kwararrun likitoci da kuma kayan aiki masu inganci wanda ake kawosu daga kasar China, idan aka kwantar da kai jinya a wannan hospital ɗin kuma kaga baka sami sauki ba to sai in ciwon ajali ne wanda shi kuma bashi da magani ko kuma wani ikon na Allah, likitocin wannan asibitin kamar mayu haka suke, sun kware wajen iya aiki ne babu wasa.

Hospital ɗin hawa har biyar ne, so da haɗaɗɗe kuma tsadadden elevator suke amfani. A hawa na biyu aka bawa Chuchu ɗaki, can Yah Jawad ya nufa da ita.

Yana kwantar da ita a saman katafaren bed ɗin da za'a dubata wayarsa ta fara kara alamar shigowar kira.

Zama ya yi a gefen bed ɗin tare da ciro wayar tasa. Jaish ne yake kiransa a kan ya zo su wuce office.

Shiru ya ɗan yi yana kallon call ɗin har sai da ta katse, sannan ya ɗan saci kallon Chuchu ta wutsiyar idanunsa kafin ya fara rubutawa Jaish ɗin sako kamar haka. Daddy and Akka sun sakani aiki, just go kawai sai mun haɗu da yamma.
Yana gama rubutawa ya tura mashi, sannan ya kashe wayar tasa ma mai gabaɗaya ya zura a aljihunsa, sai ya ciro ɗayar wayar kuma ya fara latsawa.

Nurse manyan mata biyu ne suka zo suka fara duba Gimbiya Chuchu, yana zaune a in da yake bai motsa ba, duk abin da suke yi yana kallonsu, sam hankalinsa baya a kan wayar da yake katsawa, ya dai rike wayar ne kawai, amma a zahirin gaskiya hankalinsa yana a kansu.

Gimbiya Chuchu tana son ta yi kuka saboda zafin da kafar tata take yi mata, amma kuma tana tsoron yin kukan, dan kada Yah Jawad ya kara nata wani punishment ɗin, idan baku manta ba ya ce idan ya sake kamata tana kuka sai ya hukun tata, hakan yasa ta nutsu tsit baiwar Allah, tana jin yadda waɗan nan nurse ɗin suke mammatsa mata kafafun nata, har zogi yake yi mata, sai aikin tsuke fuska da ɗan bakin nan nata take yi, amma babu halin yin kuka. Duk kuma abin da take yi a kan idanun Yah Jawad ɗin take yi, yana kallonta sarai, amma sai ya yi kamar bai san tana yi ba, dan mugunta, ko irin ya ce mata sorryn nan babu.

A ɓangaren Gimbiya Sarina kuwa, shiryawa ta yi cikin shiga na alfarma, ta fito a ainahin jinin sarautarta, kyau iya kyau, kayan jikinta wasu shegun tsadaddun kaya ne masu bala'in kyau Dubai make, goduwar riga ce ta ƴaƴan sarakuna, sai haɗaɗɗen alkyabbarta launin pink color, ta fito ras da ita, wlh ko baka so in dai ka kalli Gimbiya Sarina ta ci kwalliya to fa sai ka fola, shegiyar kaya ce, ta san kan duniya, idanunta a buɗe suke, wannan idan namiji ya shiga hannunta sai ta Allah, ko mata ƴan uwanta idan ta fito sai sun kalleta sun sake waigawa bare kuma maza, bata cika yin dressing da ya yi dai'dai da addinin musulunci ba, yawancin shigarta na turawa ne, sai dai idan a cikin masarauta take takan ɗaura alkyabbar a kan shigar tata gudun kada ta haɗu da su Jawad su saɓa mata kamanni, amma idan ta bar masarautar ko ziyara ta je wajen yan uwan mamanta ko kuma school ɗinsu, to fa ta soke sanya alkyabba, shegiyar kaya ce ta gasken gaske, ta wuce yadda kuke tunani, bata tarayya ko abota da mutun sai mai kaifin ƙwaƙwalwa da basira kamar twins Obaid and Omaid, kuma ita ɗin zata iya amfani da kai ta cinma burinta ba tare da ka sani ba, wayo gareta kamar dila, shiyasa da uncle Abbas ya lura da wayewarta ya fi shekarunta yasa yake son aurar da ita, bata bin maza, kai bama ta kula namiji duk haɗuwarsa da iliminsa ko kuɗinsa, ko ɗaga idanu bata yi ta kalli namiji, dan tana da wani abin da take shiryawa ranta za'a ce ne ko mamarta take shirya mata ne oho masu. A ɓangaren mahaifiyarta kuma burinta kawai shi ne da Sarinar da Fanan ɗin duk su auri ƴaƴan King Zuhair, saboda idan baku manta ba ita mamansu mayinwaciyar mulki ce, tana son taga ƴaƴanta a kan kujera mai matsayi, shiyasa take ƙoƙarin taga yayanta sun auri koda ɗaya daga cikin Prince na masarautar ne tunda uncle Abbas dai ya ce siyasa yake da ra'ayi.

Kamar yadda ake tarban baki a gidan sarauta haka aka tarbi Yusuf Abdulaziz Takur wanda ya zo da abokinsa guda ɗaya mai suna AL Amin Muhammad Zayyad.

A katafaren masaukin baki da yake ta ɓangaren King Zuhair aka sauke su, an kawata parlourn ya sha kyau, sai tashin kamshin yake yi, ga kayan cima kala kala wadda a kallah zasu kai kala 10 da aka shirge masu a sama katafaren dining table dake a cikin parlourn. Yusuf dai ya sami tarba ta musamman, dan uncle Abbas da kansa yasa aka shirya mashi abubuwa da dama, sai dai lokacin da ya zo uncle Abbas ɗin yana tare da King a fada, so kai tsaye masaukin da aka tanada masu aka wuce da su.

Wlh babu laifi, Yusuf haɗaɗɗen matashi ne kuma lafiyayye mai jini a jika, kyakkyawa ne ga shi dogo da shi, duk in da ake neman cikakken namiji mai kamala da riƙo da addini to Yusuf ya kai nan, bashi da makusa, haka zalika abokin nasa ma, basu da makusa, ga naira ta zauna masu, wasu fresh da su kamar suma jinin larabawan ne.

Tun da ya shigo cikin parlourn yake ta faman raba idanu ta ina zai ga tauraruwar tasa, haƙiƙa yana son Sarina sosai, ya sha suit ɗinsa launin navy blue mai bala'in tsada, kafafunsa suna a cikin cover shoe masu kyau, bashi da yelwar gashin kai sosai, amma ya sha gyara yana kwance luf gwanin birgewa.

Sai raba idanu yake yi yana jira yaga isowarta, abokin nasa ma burinsa ya ga isowarta kawai, dan Yusuf ya gama zuzuta masu kyanta, kuma ba karya ya yi ba, jinin Akka ba dai kyau ba, sun haɗu ne, bare ƴan'mata masu tsantsara kwalliya irin Chuchu, Zunairar da kuma Sarinar, ai idan ka yi ido biyu da su sai ka kalla ka sake waigowa, idan ma baka yi hankali ba a garin kallonsu ka je ka faɗi ƙasa.

Sautin takalmarta mai uban tsini ne ya fara dakar dodan kunnuwarsu, fuska ba yabo ba fallasa, irin waɗan nan high heel masu tsawo sosai ɗin ta sanya, gata da tsawo dama, sai dressing ɗin nata ya kara kawata idanun mai kallo, ta fito sosai fa ba karya.

Tafiya take yi tamkar wata hawayniya, kamar bata son taka ƙasa, tana sanya kafafun nan nata ɗaya bayan ɗaya a ƙasa, kai daga ganin tafiyar kasan ba yau bane farau, ta saba yin wannan shu'umin tafiyar mai ɗaukar hankali. Ga wasu kuyangunta biyu da suke binta a baya, ɗaya hannunta rike da kwando mai shake da kayan fruits, ɗayar kuma hannunta rike da wani katon try mai ɗauke da wasu shegun haɗaɗun cup's masu bala'in kyau, ga robar ruwa a shirye a saman, ruwa ne masu sanyi sosai, duk kayan cima da aka shiryawa su Yusuf ɗin a parlourn basu isheta ba, saboda munafurci dan ta nuna cewa tana son shi kamar yadda suka shriya da su Obaid yasa ta zo mashi da wasu, irin ta nuna shi na musamman ne a wajenta, waɗan nan Team ɗin sai dai shirin Allah na gaya maku, sun san kan duniyanci........😅

Duk in da ta wuce sai kuyangu sun zube ƙasa domin kwasar gaisuwa, amma kamar kashi haka take wucesu, sai ma yamutse fuska da take yi idan ta gansu kamar wadda ta kalli kashi, akawai ta da izzar bala'i tare da jiji da kai yarinyar.

Tana sako kafafunta a cikin parlourn Yusuf ya miƙe tsaye, kawai ido ya kafeta da shi yana kallonta daga sama har ƙasa.

Ita kuwa da yake ƴar duniya ce sai ta basar kamar bata san yanayi ba, ta cigaba da wannan ɗan iskan takun nata mai tafiya da tunanin mutum.

Shi kansa abokin Yusuf ɗin sai da ya miƙe tsaye yana kallon tsantsar kyan da Allah ya yi mata, bayin Allah sun faɗa tarkon jinin Akka, sai dai Allah ya fitar da su.

Takowa ta yi har izuwa wajen tsala tsalar sofas na parlourn, kamar ba ta kalli Yusuf da ya saki baki yana kallonta ba, zama ta yi a saman ɗaya daga cikin sofas ɗin, ko da ta zo zaman ma sai da ta yi wani rangwaɗa mai kara birkita tunanin duk wani lafiyayyen namiji, sam bata sanya idanuta ta kalli Yusuf ɗin ba har sai da ta zauna a saman sofa ɗin.

"Kana iya zama yanzu ai malam Yusuf".
Ta faɗa cike da izza sosai a muryarta, ka kwainane da kisisina, tana magana tana wani dakewa.

Wani irin nannauyar ajiyar zuciya bawan Allah ya sauke kafin ya iya komawa saman sofarsa ya zauna.
"Barka da isowa gimbiya kuma tauraruwar mata".
Ya faɗa muryarsa cike tab da tsantsar so da kuma kaunarta.

Wani irin ɗan iskan shu'umin murmushi kaɗan ta saki wanda ya kara fito da tsantsar kyanta, hakan kuma ya kara tafiya da imanin bawan Allah Yusuf.

Shi ma abokinsa ya ƙasa iya kawar da kallonsa daga kanta, gata ƴar caras da ita.

Juya waɗan nan fararen dara daran idanuwan nata ta yi kafin ta ɗan ja gajeran numfashi.
"Yauwa barka dai malam Yusuf, fatan ka zo lafiya?".

Ina ai ta gama tafiya da imaninsa, kara rikicewa ya yi a in da ya amsa mata da lafiya lou da hanzari.

"Bari na zuba maku ruwan sha ko?".
Ta faɗa ba tare da ta kawar da waɗan nan shegun idanun nata daga kan Yusuf ɗin ba.

Da mamaki kuyangun da suka rakota suka bita da kallo, wannan yarinaya akwai shegen makirci, ita da ko kanta bata zuwaba ruwan sha idan zata sha, komai yi mata kuyangun nata suke yi, bata son yin aiki ko kaɗan, amma wai take cewa bari ta zuba mashi ruwan sha? Duk dan ace tana son shi kenan? Kai Sarina duniya.

Ni ko na ce ko ina su twin's? Ko me suke shiryawa Yusuf bawan Allah? Ga shi dai ya gama afkawa gogin sonta, sai Allah sai kuma alkalamin PRINCESS TEEMA ne kawai yasan me waɗan nan Team ɗin suke shiryawa, sai mun haɗu da ku gobe idan mai dukka ya kai mu, amma fa akwai kallo ba kaɗan ba, dan nasan za'ayi dirama a cikin wannan KINGDOM ɗin yau, dan haka ku gyara zama!!.


🤍KADA KU MANTA WANNAN DADDAƊAR LABARIN DAGA ALKALAMIN FATEEMA ZAHRA MUSA A-K-A PRINCESS TEEMA TAKU TA AMANA YAKE🔥💘



Share fisabilillahi 👏



ALLAH KA KARA MANA SON MANZON ALLAH 🔥🤍



🤍🔥𝗥𝗔𝗪𝗔𝗡𝗜𝗡 👑 𝗭𝗔𝗟𝗜𝗡𝗖𝗜🔥🤍


🔥CROWN OF INJUSTICE🔥







𝗠𝗔𝗟𝗟𝗔𝗞𝗜𝗡

❤️‍🔥FATEEMA ZAHRA MUSA ❤️‍🔥
(❤️A-K-A 𝑷𝑹𝑰𝑵𝑪𝑬𝑺𝑺 𝑻𝑬𝑬𝑴𝑨🔥)







🔥🤍T🔥🤍T🔥🤍W🔥🤍......💻




❤️𝑫𝑨𝑻𝑬 25/7/2024.....✍️📚🌹




For information 08161390581 Whatsapp me only!!.



🤍𝑺𝑻𝑬𝑷 1......✍️📚🔥





اللَّهُمَّ صَلِّ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا صَلَّيْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ، اللَّهُمَّ بَارِكْ عَلَى مُحَمَّدٍ وَعَلَى آلِ مُحَمَّدٍ، كَمَا بَارَكْتَ عَلَى إِبْرَاهِيمَ وَعَلَى آلِ إِبْرَاهِيمَ، إِنَّكَ حَمِيدٌ مَجِيدٌ❤️








E____________22🔥




Malam Yusuf dai ya ƙasa iya cigaba

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login