Showing 87001 words to 90000 words out of 296878 words
ma, ta sha kyau over, dama ita ba gwanar ɗaura ɗankwali ba, sai ta saki wannan dark black curly hair nata har tsakiyar baya, tana rungume da Wolf nata dake barci.
Saman bed ɗin ta haye tana faɗin. "Aunty Chuchu what are you thinking?".
Nisawa ta ɗan yi tare da faɗin. "Am thinking about Yah Jawad, he said i should meet him in his part, so now am thinking about the reason of the call he called me".
"To ai babu abin da zai yi maki, so just fell free and go, ko dai kin yi mashi wani laifi ne?".
Da sauri ta ɗan girgiza kai tana faɗin. "No ban yi mashi komai ba".
"Okey tom ki je ba zai yi maki komai ba ai, wata kila ma aikanki zai yi wani wajen ko wajen Mammie".
Ta kai karshen maganar tare da kwanciya rungume da Wolf ɗin nata.
"Aunty Chuchu yau a bedroom naki zan kwana yau ma kamar jiya". Ta faɗa tana janyo duv ta rufe su ita da Wolf ɗin nata da take kiransa da sunan Felix.
"A'a zo mu je ki rakani part ɗin Yah Jawad ɗin, mu je tare mu dawo tare mu zo mu yi barci".
Ta yi maganar tana juyo da kallonta a kan autar.
"Kai Aunty Chuchu, am tied fa, am feeling too much of sleeping, kuma kinga my felix ma also ya yi barci, kawai ki je, ai Yah Jawad baya da faɗa, and kuma yana da kirki, da ma dai uncle Taheer ne sai na ce to ki shirya".
"Hmmmm a ganinki ne Yah Jawad bashi da faɗa ba? Ke ai auta a gidan nan ma kowa baya da faɗa ne a wajenki, saboda basa yi maki, for me uncle Taheer is better than Yah Jawad a saukin kai, seriously Yah Jawad he's acting like a tiger ne or Lion za'a ce, he can't talk at all sai zafin rai like Yah Jaish, amma uncle Taheer fa? Baya kwacewa mutane abinsu, kuma shi idan ka ce mashi sorry yana hakura".
Ta kai karshen maganar tana turo baki kamar Yah Jawad ɗin yana a gabanta.
"To ni dai Yah Jawad is better than uncle Taheer for me, dan haka ma ni good night".
Ta kai karshen maganar tare da jan duv ɗin har izuwa saman fuskarta ta rufe ruf.
"No auta please stan up let's go together, I can't go without you! Ina tsoro".
"Kai Aunty Chuchu idan da ban shigo bafa? Da waye zaki je?".
"Cikin bedroom naki zan je na kiraki mana, Please taso mu je".
Turo ɗan bakin ta yi, a hankali ta yaye duv ɗin ta fito, har ga Allah bata son zuwa, amma ya zata yi da Aunty Chuchu nan nata? Dole kawai ta rakata. Da yake Felix ɗinta ya yi barci sai ta kyale shi a saman bed ɗin suka tafi, dukkansu kai babu ɗankwali, sun saki gashin nan har baya, da yake auta tana da tsawo sosai kamar Mommarta, sai ya zamana ta kusa kamo Chuchu ɗin tsawo.
Kai tsaye part na Yah Jawad ɗin suka nufa, sai hira suke yi cikin nishaɗi kamar wasu ƙawaye. Ba su kai ga ƙarisawa part ɗin nasa ba suka ci karo da wani haɗaɗɗen matashi mai jini a jika, kyakkyawa kuma lafiyayye, yana da fusatatcitar fuska sosai, idan ka gansa ma sai ka ɗan razana, saboda yadda face ɗin take a ɗaure tamau, sai dai kuma ba karya akwai kyau, da alama akwai zafin kai da izzar jinin mulki, yana sanye da kayan barci shi ma a jikinsa masu bala'in kyau da tsada, sai tashin kamshi yake yi, yana tafiya yana latsa haɗaɗɗiyar wayar dake rike a hannunsa, a shekaru ba zai wuce 28 years ba.
"Good evening uncle Taheer". Suka haɗa baki wajen faɗa.
Ɗan dakatawa daga tafiyar da yake yi ya yi, sannan gentle ya kawar da kallonsa daga kan screen ɗin wayar izuwa kansu, kallo ɗaya ya yi masu ya mayar da kallonsa a kan screen ɗin tare da cigaba da tafiyarsa, ba tare da ya amsa masu gaisuwar tasu ba ya ce. "Baby zo mu je ki rakani wajen uncle Abbas, can zan je".
Yana maganar ne yana cigaba da tafiyar da yake yi. Uncle Taheer kenan, ƙanin Mama ne, ba ɗan King Zuhair bane ba!.
Kallon juna suka yi ita da Chuchu, kamar Gimbiya chuchu zata sa kuka, uncle Taheer zai sanya ita kaɗai ta je wajen Yah Jawad, zai wani ɗauke mata abokiyar tafiyarta, wayyo Allah, gaskiya bai kyauta mata ba.
Ganin ya ɗan yi nisa da tafiyar da yake yi har ya kusa fita daga arear wajen ne yasa auta ta yi saurin barin Gimbiya Chuchu ta rufa mashi baya, dan ma kada ya sake kiranta.
Da kallo our fashion baby Chuchu ta bisu da shi har sai da suka kurewa ganinta, sannan ta kara turo ɗan bakin nan nata, ji take yi kamar ta juya ta koma ta fasa zuwa wajen Yah Jawad ɗin, amma ina ba hali, idan ta fasa zuwa ma wani laifin ta jawa kanta da kanta. Hakan yasa ta ɓata rai tana turo baki ba dan ta so ba ta cigaba da tafiya.
A bakin kofar shiga part ɗin nasa ta tsaya ta yi sallama. Shiru ba'a amsa mata ba, a lokacin ma kuyangun da suke yi mashi hidima a part ɗin nasa sun kammala aikinsu su tafi, so babu kowa a cikin parlourn, hakan yasa ba'a amsa sallamar ba.
Jin shiru babu wanda ya amsa mata har tsawon mintuna biyu yasa ta ɗan turo kofar ta sako kyawawan kafafunta da suke sanye cikin bedroom slippers masu bala'in kyau, ta sako ƙafafun nata ne tana sake rangaɗa mashi sallama.
Ganin babu kowa a parlourn yasa ta ɗan sauke nannauyar ajiyar zuciya tare da nufar kofar bedroom nasa.
A bakin kofar ta tsaya tare da dai'dai ta nutsuwarta tana sake sauke ajiyar zuciya, sannan ta yi sallama cikin nutsuwa.
Shiru shiru ba'a amsa ba, a karo na biyu ta sake yin sallamar. Nan ma shiru ba'a amsa ba.
Wani tunani ne ya faɗo mata a ranta na ko dai baya a cikin ɗakin ne? Ko kuma ya yi barci ne?. A hankali ta juya da nufin ta bar wajen ta koma part nata, sai kuma wani ɓangare na zuciyarta ya ce mata ta leƙa cikin bedroom ɗin mana ta gani ko barci yake yi ko kuma dai laifin da ta yi mashi ne yasa ba zai amsa sallamar ba. Yin wanna tunani yasa ta sake juyowa tare da ɗan tura kofar tasa a hankali. Kamar wadda kwai ya fashewa a ciki haka ta sako kafarta a cikin bedroom ɗin, tana ɗari ɗari.
Wani irin nannauyar ajiyar zuciya ta sauke lokacin da taga babu kowa a cikin ɗakin, sosai ta ji daɗi, Allah ya ceceta ya tseratar da ita, dan haka sai ta juya a hankali da nufin ta fice daga cikin bedroom ɗin.
Kome ta tuna kuma? Sai ta sake juyowa da sauri, ƙurawa wayoyin dake a saman bed nasa idanu ta yi, ga wayarta dana Fanan, sannan ga na Sarina sai nasa guda biyu a gefe, duk ya zubesu a saman bed ɗin, da alama bayan fitar gimbiya Sarina ya shigo cikin ɗakin kenan, dan kunga lokacin da Sarina ɗin ta shigo cikin bedroom ɗin babu wayoyin a saman bed ɗin.
Ganin wayoyin yasa bata san lokacin da ta saki cool murmushi ba kamar Yah Jawad ɗin ya mai do mata da nata ne. Da sauri ta karisa wajen wayoyin tana ta kara faɗaɗa murmushin da yake a saman fuskarta.
Tana zuwa wayarta ta fara ɗauka, dukka wayoyin nasu a kashe, wayoyinsa ne kawai a kunne.
Wani irin daɗi ne ya lulluɓeta, ta manta ma a ina take, tuni ta hau kunna wayarta, sai kara sakin murmushi take yi, wayyo ta mance ma da wanenen ya kwace wayoyin nasu, ita dai burinta ya cika ta ga nata, laifi kan laifi kenan take ƙoƙarin karawa.
Tana kunna wayarta ta sauke ajiyar zuciya, a hanzarce ta fara dube dube a cikin wayar, shap fa ta mance da cewa ba'a bedroom nata take ba, kuma yau ta manta da cewa tana tsoron Yah Jawad, daɗi ne ya yi mata yawa, kada ku ga laifinta.
Saboda jaraba abin ya bi jini tana ɗan yi shige shige kaɗan a wayar ta fita ta shiga Camera dan ta ɗauki hoto.
(Wanna jaraba ta Chuchu dayawa yake💔 yarinya mayyar hoto haka?🤔 Anya ba aljanun yin hoto ke gareta ba? Wai ma ina take kai hotunan ne?🤔 Me take yi da su?🤔)
Hotuna ta fara ɗaukar kanta, tana yi tana canza style, ta turo ɗan bakin nan ta sake ɗaga kyakkyawar gerarta guda. Wani irin rashin sa'a aka samu ta juya ta canza style kenan zata ɗauki hoton sai camerar ya haɗo mata da Yah Jawad dake tsaye a bayanta wajen kofar shiga dressing room nasa. Daga shi sai towel and single a jikinsa, wanka ya fito ɗaure da towel, lokacin da ta shigo cikin bedroom ɗin yana cikin dressing room nasa zai fara saka kaya kenan, ya saka single bai kai ga ƙarisawa ba ya ji motsi a cikin bedroom ɗin nasa, hakan yasa ya fito leƙawa ya ga wannen? Sai ganinta ya yi tana ɗaukar hotuna, shi ne ga tsaya tare da harɗe hannayensa a saman faffaɗar kirjinsa yana kare mata kallo yana ganin ikon god.
Ganin shi ta cikin camerar wayar ba ƙaramin razana ta ya yi ba ta yadda har sai da ta zunduma wani irin ihu tare da juyowa a dubu ɗari dan ta tabbatarwa da kanta abin da ta kallah a cikin wayar, sai yanzu ta tuna ashe ba'a bedroom nata take ba baiwar Allah.
Tsabar tsorata da ganinshi yasa ta sake wayar tata ta faɗi kasa a saman white tiles ɗin, kunsan ganin mutun un expect ba karamin razanarwa yake yi ba, barema ita da ta ganshi ta cikin camera, ai dole ta tsorata, ga shi dare ne, kuma ya kafeta da waɗan nan dara daran idanun nasa, ai tama yi ƙoƙari da bata sakar mashi fitsari a wajen ba.
Shi kuwa tunani yake yi ko dai ruƙuya za'ayi mata ne? Watakila aljanun ɗaukar hoto ne suka shigeta!.
Ganin ko motsi bai yi ba ya kafeta da idanu ne yasa ta ƙara sorata sosai, jikinta har ya suma kerma, ita tunani ma take yi shi ne ko kuma aljani ne? Dan a gaskiya yanayinsa ya tsoratata sosai, ga shi daga shi sai single ta sama, ta kasa kuma towel ne ɗaure a kugun nasa, yanzu ta gudu ne ko ta tsaya?.
(Ni dai na ce wlh ki zunduma a guje kiyi waje abinki ato😅 kuma kada ki tsaya a ko'ina sai wajen Momma, dan ita kaɗai zata iya kwatarki.🥰😅)
Almost 10 mins suna tsaye a haka an rasa mai bakin yin magana a cikinsu, sai kermar tsoro jikinta yake yi, shi kuma yana kare mata kallo. Sai da ya ga ta fara ruwan hawaye ta gaji da tsayuwar ne tunaninsa ya dawo jikinsa, nisawa ya yi kafin ya ɗan motsa lips nasa wajen furta.
"What are you doing here by this time around?".
Har ya manta da cewa shi ya ce ta zo ta same shi a cikin part ɗin nasa.
Hawayen da yake a saman fuskarta ne ya kara karfin gudun nasa, murya na kerma ta ce. "Yah Jawad kai ne fa ɗazun ka ce na zo na sameka a part naka".
"Sai kuma na ce idan kin zo ki shigo mun har cikin bedroom?".
Da sauri ta girgiza mashi kai alamar a'a.
"Waye kuma ya ce ki fito sanye da kayan barci babu ɗankwali bare hijab? Ki ka wuce kowani part dake arear nan kizo har nan? Are you out of your sense?!". Ya kai karshen maganar cikin faɗa da kuma ɗan ɗaga murya.
Nan ma girgiza mashi kai ta yi alamar a'a, ta kasa iya sake yi mashi magana, sai dai ruwan hawaye.
"Waye kuma ya ce ki taɓa mun abin da na ajiye? Ke kika ajiye mun wayoyin ne?".
Nan ma dai girgiza kan nata ta yi alamar a'a, wahayen face nata suna kara tsananta gudu, ta yi danasanin zuwanta ma, ashe shi ya manta ma da ya ce ta zo ta same shi a part nasa, ita ce take wahalar da kanta, yanzu ga shi ta kara laifi a kan laifi, ga laifin fitowa da kayan barci wanda ita ta manta da cewa sune ma a jikinta, sannan ga laifi ɗaukar wayar da ya ajiye da ta yi.
A nasa ɓangaren kuwa, kukan da take yin nan ne baya son gani, saboda suna kaunar kannen nasu sosai, ƴan gata ne da ba'a son su yi kuka sai ya zama dole, dan haka sai ya sassauta muryarsa ƙasa ƙasa ya ce. "Okey maza goge hawayen nan kiyi neel down a wajen ina zuwa, idan kuma kika bari na fito naga hawaye a saman face naki you now the rest".
Ya kai karshen maganar tare da wucewa ya koma cikin room ɗin dan ya kammala shirin da ya fara.
A hanzarce ta kai hannu ta goge hawayen nata tare da zube gwiwowinta a ƙasa, ji take yi wasu kukan suna zuwa mata, amma sai ta danne dan gudun kada ta kara laifi a kan laifi, ji ta yi gabaɗaya ta tsani Yah Jawad ɗin nan, duk cikin brothers ɗinta shi ne ya fara sakata kuka, ko yayansa wato first born ɗin uncle Abbas mai runa Rizwan bai taɓa sakasu kuka ba, duk da yake suna ce mashi mugu, amma bai taɓa dukansu ba, sai dai harara da daka masu tsawa, yau kawai Yah Jawad ya sakata kuka dan mugunta.
Ya ɓatawa fashion babynmu rai, gaskiya bai kyauta ba.....😥😅
To bari dai na koma wajen su Kamran, wata kila kafin mu dawo Yah Jawad ya kammala shirinsa, sai mu zo muga wani hukunci zai yi mata, ta yi laifuka har guda uku, zamu ga irin hukuncin da zai yi mata dai!!.
🏞️FOREST🏞️
Fitowa waje Pretty ta yi kai tsaye abinta, ta fito kuma tana mai kiran sunan Kamran a kan ina yake ya zo sun gama cin abinci!.
Ai yana saman bishiyar nan bai san lokacin da ya furta kash ba!.
Ita kuwa wani irin birki ta ja na ganin waɗan nan jiga jigan zakunan a gabanta, zaro idanunta ta yi tana kallonsu, sai kuma ta fara ɗan waige waige tana neman ta in da zata ga Kamran?. While su kuma warriors ɗin suka bita da kallon from head to toe!.
Gabaɗaya wani irin mahaukacin tsoro ne ya kamata, bata taɓa ganin halittu irin waɗan nan ba, kamar ba mutane ba, bugu da ƙari ga hular kayan yakin nan nasu a kansu, kuma su nasu hular mai design ɗin kan ɓauna ce, hakan tasa kan nasu ya kara girma ta yadda ya yi matuƙar sakawa hantar cikinta ya kaɗa, ƴaƴan hanjinta ya yi masifar kaɗawa, tsoro ne ya dabaibayeta ta ko'ina, kan kace me jikinta ya fara kerma.
Kobaka san su waye waɗan nan warriors ɗin ba idan ka gansu dole ka razana, dole hantar cikinka ta kaɗa, saboda basu yi kala da masu ɗigon imani ko miskala zarratin a cikin ransu ba, ga bala'in kwarjinin da yake lulluɓe da fatar jikkunansu, gasu wasu bujumaye da su kamar wasu zakuna, dole Pretty ta tsure na kin ƙarawa, Kamran ma ya tsorata da ganinsu bare kuma Pretty, ai tama yi ƙoƙari da bata sume masu ba.
Kallon juna warriors ɗin suka yi a in da suka fara yin magana da wannan yaren nasu dai da bamu jin me suke faɗa, Kamran dai yana bala'in son ya ji me suke cewa, amma babu hali, hakan yasa ya zuba masu idanu kawai ya ga me zasu yi idan suka gama maganar nasu, sai alama yake yi wa Pretty da hannunsa a kan ta gudu ta wata hanyar, kada ta koma cikin ɗakinsu, hakan zai sa a gane maɓoyatsu.
Amma ina ita Pretty sam bata ma san yana saman bishiyar ba, bata ganshi ba, ita dama take tsaye tana jiran kiris ta saki fitsari a wando saboda tsoro, ina ita ina wani kallon sama kuma? Har ma ta ganshi a saman! Ai babu wannan zance.
Kamran ya yi nisa cikin tunanin mafita bai ankara ba sai gani ya yi warriors guda biyu sun diro kasa daga saman dawakansu, cikin takun tsantsar jarumta suna taka ƙasa tana amsawa dip dip dip suka nufi Pretty ɗin.
Tana tsaye ta kasa iya guduwa, tamkar wadda aka sarewa gaɓɓan jikinta ko aka dasata a wajen, ba komai bane ya ja mata hakan kuma face tsoro, tsananin tsorata da ta yi ne yasa gabaɗaya gaɓɓan jikinta suka yi la'asar babu laka.
Ganin sun tunkareta gadan gadan ne yasa Kamran bashi da wani zaɓin da ta rage mashi face ya sauko ya fiskancesu gaba da gaba wata kila su yi mutuwar kasko, dan ba zai iya bari su cutar da Pretty ba, ko da kuwa zasu kashe shi, shi da kansa yasan wlh waɗan nan jiga jigan warriors ɗin sun fi karfinsa, ba zai iya yin faɗa da su ba, dama dai su huɗu ne to zai iya cewa zai kashesu, amma har su takwas shi kaɗai ai kowa yasan idan ba aljani ne shi ba wane kaniyarsa ya iya faɗa da su, amma ya zai yi? Da dai su kashe Pretty gara mashi ya sauko su buga da shi ɗin, idan ya so Pretty ta gudu ta samu ta tsira!.
Hakan yasa shi ya diro ƙasa daga saman bishiyar, bai yi tunanin wani hali Mammarsa zata shiga idan aka kashe shi ba, yasan shi kaɗai take da shi a duniyar nan, tana bala'in kaunarsa fiye da tunaninku, ya zata yi da ranta idan aka ce waɗan nan azzaluman sun kashe shi? Ai ina ga ita ma mutuwa zata yi ko kuma ta haukace kawai!!.
Ganin dirowar mutun yasa warrior da suke tunkarar Pretty suka dakata daga tafiyar da suke yi, tare da ɗaura kallonsu a kan Kamran ɗin. Ya yi tsayuwar cikakkun jarumai! Babu alamar tsoro ko kuma sarewa a tattare da shi, yadda kuka san zai iya da su dukkansu.
Ganin irin tsayuwar da ya yi cike da jarumta babu ko ɗar ɗar ne yasa warriors ɗin suka fara tunanin ko dai da akwai abin