Showing 237001 words to 240000 words out of 296878 words
ido ɓul ɓul, ai dole ne ma jikin Sweetie da Pretty ya yi kyau tamkar waɗan da suke rayuwa a cikin Ac cikin wata Daula mai girma, jikinsu luwai luwai saboda shan kayan marmari, ga su kuma ta ko'ina a cike ɓul ɓul, tsokar jikinsu masha Allah, shiyasa kullum Kamran yake karewa gurun wuyar nan nasu kallo, barema na Pretty, tsoƙar wuyar tata ya fi na Sweetie cikowa sosai, kun san fa ita dama acici ne mala'ikun tauna, bata wasa da ci, kuma a koda yaushe ka ganta sai ka ganta rike da ayaba ko lemu or kwakwa tana ɗan motsa baki, ita dai bata son zaman shiru, shiyasa ga shi nan tafi Sweetie cikowa ta ko'ina ɓul ɓul kamar wata mai shekaru 13 zuwa 14, alhalin nan ko 11 years basu cika ba.
"Haba Pretty please escort him mana". Cewar Sweetie.
Tana aikin tura ayaba a ɗan bakinta ta bata amsa da. "I can't, amma ke zaki iya miƙewa ku je ai, ni an ce maki na shirya mutuwa ba tare da na sake kallan mum ɗina bane? Ai sai mum ta dawo tukun nan koma me zai faru ya faru". Ta kai karshen maganar tare da miƙowa Kamran ɗin nonan ayaba guda ɗaya mai ɗan girman da akallah ayaba 12 ne a jikinsa.
Karɓa ya yi tare da ajiyewa a gefensa, dan shi kansa ayabar ta burgesa, kamar zai tambayeta a ina suka samo ayabar, sai kuma bakinsa ta yi mashi nauyi ya kasa iya tambaya. Shi dai yasan ba shi ya kawo masu wannan ba, wanda yake kawo masu ba irin wannan bane, red banana yake kawo masu, su ne suka fi yawa ta wannan yankin, wannan da ta bashi kuma green ne.
"Pretty yau Kamran ɗin kike gudu ko? To ni dai ban apple ɗaya bari na sha na kwanta na yi barci, malam Kamran yau dai Pretty na gudunka". Cewar Sweetie.
Yake ya ɗan yi mai kama da murmushi kamar Sweetien tanan kallonsa, sannan ya ce. "Bani take gudu ba, snake take gudu, ni bari na je zan dawo yanzu ba jimawa, zan duba tekun nan ne". Ya kai karshen maganar tare da ɗaukar ayabar da ta bashi ya miƙe tsaye.
"Kamran". Pretty ta ambaci sunansa a hankali. Zuba mata ido ya yi ba tare da ya amsa ba.
"Kuma tafiya zaka yi?". Ta tambaya ita ma tana kallonsa, kun san idan ya zo tafiya dama bata son rabuwa da shi, kuma tana jin tsoron rakasa, zai ta fi shi kaɗai kuma tana jin kamar ba zata iya zama ya tafi ya barta ba, bata son ya matsa daga kusa da ita ko nan da can.
Da e ya amsa mata, shi kansa baya son matsawa daga kusa da ita kun san haka, amma kuma neman hanyar da zata ɓulle masu abu ne mai matuƙar muhimmanci a garesa, so dole ne ya je domin neman mafita.
Narai narai da ido ta yi mashi zata yi kuka, ga gwandar daji a rike a hannunta ta sha rabi bata ƙarisa sha ba.
"Please Pretty don't let your tears to come out, zaki sanya zuciyata ta yi mun zafi, yanzu fa zan dawo". Ya yi maganar cikin wata iriyar murya wadda da ka ji ta zaka san shi ma baya cikin jin daɗi, dan sun shaƙu sosai har ta kasance in sun haɗu suka zo rabuwa zuciyarsa kuka take yi, ita kuma Pretty kuka a zahiri take yi, Sweetie ma kukan zuci take yi bana zahiri ba idan zasu rabu, Pretty ce sarkin hawaye mai yi a fili kowa ya gani.
"To Kamran ka bari mana sai zuwa gobe sai ka je ka yi checking na abin da zaka duban, now ka zauna da mu please". Cewar Sweetie da a kullum kaunar Kamran ɗin karuwa yake yi a ranta, mutumin da bata san shi ba, bata taɓa ganin face ɗinsa ya yake ba, bata san ya zuciyarsa na ainahi yake ba, ta iya yiwuwa a wajensu ne yake mutumin kirki, a bayansu ba haka yake ba, duk bata san wannan ba, ita dai zuciyarta na sonsa, shi kuma zuciyarsa na son Pretty, son da yake yi wa Pretty ma ai ko kansa baya yi wa hakan, ta zama tamkar bugawar numfashinsa, komai yake yi yana tunaninta, tun ranar da aka haifeta, ya ɗauketa tana tsallara wannan ihu, tun da lokacin ta shiga cikin zuciyarsa, sau da dama idan zai yi tunaninta yana tunaninta ne a ranar da ya ɗagata tana jaririya ko cibiya ba'a yanke mata ba, ya ɗauketa ya kudunduneta a cikin rigar da ya cire daga jikinsa, tana ta tsallar ihu da wannan red lips ɗin nata suna ta kerma saboda sanyi, tun da lokacin ta dasu mashi a cikin zuciyarsa wanda cireta kuma ba abu ne mai yiwuwa ba, sai dai idan za'a haɗa da zuciyar tasa dukka a cire. To fah, babbar magana kenan, akwai cakwakiya ba kaɗan ba.
"Sweetie ba zan jima ba zan dawo kin ji? Kada ku damu".
Da okey kawai ta amsa mashi, amma daga jin yadda ta amsa kai kasan rai bai so ba, kawai ta amsa ne dan bata son ja in ja da shi.
Ita kuwa Pretty tuni idanunta sun ciko da kwallah, tasan cewa idan ya je zai ɗan jima kafin ya dawo, idan kuma ya dawo ba zai wani jima a wajen nasu ba zai ce masu zai koma, shikenan yau ba zasu jima a tare da shi ba, zai tafi ya barsu da kewa, in ya tafi kuma sai yamma zai dawo, wannan dalilin yasa duk ta ji babu daɗi.
Kawar da kansa ya yi tare da ficewa da sauri, dan baya son ganin kukanta, kuma shi gaskiya yana son sanin hanya cikin ƙanƙanin lokaci, dan a gaskiya ya gaji, yana son ganin duniya ya take.
Zuciyarsa sai yi mashi kuna take yi, amma a haka ya sa kai ya wuce hannunsa rike da ayabar da ta bashi.
Ita kuwa Pretty goge hawayen face ɗin nata ta yi tare da ture kayan cimar da suke a gabanta gefe guda, sannan ta miƙe ta koma kusa da ƴar uwarta tana faɗin. "Sweetie sam sam i don't want Kamran to go anywhere ya bar mu, am not happy at all, and am feeling very very bad mood idan baya nan". Ta kai karshen maganar tare da kwanciya ta tada kai da laps na Sweetien.
"Same here Pretty, ina jin kuna a cikin rai'na idan zai tafi".
Shiru ta ɗan yi kafin ta ce. "But Sweetie why not mu fara neman mum da kanmu? Maybe fa tana a cikin Forest ɗin nan kusa da mu".
"E kince wani abu, let Kamran come back sai mu gaya mashi, zai tayamu nemanta, maybe tana nan wani abin ne ya riƙeta, kinga idan muka ganta zata rage mana kewa, idan Kamran ya zo tafiya ba zamu damu sosai ba".
Allah sarki bayin Allah, ai ko dan kasancewarsu su kaɗai a cikin wannan ramin ma dole su rinƙa kuka idan Kamran zai tafi ya barsu, abin akwai taɓa zuciya, babu uwa babu uba, babu wani ɗan uwa, babu motsin halittar ɗan adam sai dai na dabbobi su tsuntsaye da sauransu, babu gida gaba babu gida baya, su biyun nan suke rayuwarsu kafin Allah ya kawo masu Kamran, gwanin ban tausayi sosai, dole ma su sha kuka a duk lokacin da zai tafi wajen Mammarsa, Allah sarki.
Cigaba da hira suka rinƙa yi suna neman mafita a tsakaninsu, da haka har barci ya ɗauke Pretty, ya rage Sweetie kawai da ta kasa yin barcin, tunanin mafita ta shiga yi tana ɗan shafa kyakkyawar gashin kan Prettyn wadda yake a saman laps ɗinta, tana matuƙar kaunar ƴar uwar tata, ita ma Prettyn tana matuƙar kaunarta, su biyun nan su ne duniyar juna, ita ce duniyar Pretty, Prettyn ma Sweetien ne duniyarta, komai nata, so suna tsananin kaunar juna.
Kamran kuwa tafiya ya yi wajen wannan teku na jiya dan ya duba ko akwai wata hanya mafi kusa ta gefe gefen tekun.
🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️
GIDANSU KHADIJAH 💔😥
After some days.
A cikin waɗan nan kwanaki da suka shuɗe dai maman Zainab ta yi nasarar samun sa'a wannan asiri na jikin Zainab dai ya karye, ta tsaya ne tsayin daka wajen ganin ta yi wannan haɗin maganin da mamanta ta gaya mata, so Allah da ikonsa Zainab ta dawo normal. Sai dai kuma wani tashin hankali shi ne tun ranar da baban Zainab ya fita gidan a tare da Hauwa bai sake dawowa gidan ba, su maman Haidar sai nemansa suke yi, amma ina basu gansa ba, sosai maman Zainab ta shiga damuwa maras misaltawa, ta yi mummunar rama sosai da sosai, kamar ba ita ba, har duhun wahala da damuwa sai da ta yi, sun dawo yin rayuwa daga ita sai su Zainab da Sadiq, Haidar ma yanzu sai gefi gefi yake shigowa gidan, watarana a gidan kakarsa yake kwana.
Ga wani bala'i da hajiyarsu ta taso masu da shi shi ne wai auren Khadija and Haidar za'a yi shi kafin ta rubuta Exams ɗin, sun fasa bari sai ta rubuta, saboda Haidar ya matsa masu sosai, shi fa sam bai damu da rashin sanin in da babanta yake bama, bai wani damu da halin da suke ciki ba, ko a jikinsa, abin da yake gabansa kawai yake yi.
Maman Zainab ji take yi kamar ta kwashi ƴaƴanta su koma wajen mahaifiyarta, Sadiq kuwa ya ce mata a'a ta yi fito na fito da su ta gaya masu Khadija bata son Haidar, dan haka ba za'ayi wannan auren ba, idan sun ki sun ce sai anyi aure to ta shigar da su kara ga hukuma a kwantar ma yarinya hakkinta, tun da yanzu baban Zainab ma ba ta su yake yi ba, dan haka ta tsaya ta kwatarwa ƴarta yanci.
Ta ɗauki kwanaki tana tunani a kan zance Sadiq ɗin, daga karshe dai ta kira mamarta a waya ta sanar da ita ga wani lukutar masifa da suke ciki, sannan ga shawarar da Sadiq ya bata.
Da yake mahaifiyar tata dattijuwan arziki ce sai ta ce mata. "A'isha duk abin da zaki yi ki rinƙa kallon Mamarsa tamkar ni ce, ki girmamata kada damuwa ko ɓacin rai or zuciya haɗe da shaiɗan ya ja ki ki yi mata wani abin da ba zaki iya yi mun ba, kada ki manta zamanku da ɗanta a baya, na baki izini ki kwatarwa ƴaƴanki yanci, amma kada ki wuce gona da iri, uwa bata fi uwa ba, mahaifiya dai mahaifiya ce, kada ki riƙi hujjar cewa hankalinsa baya a kanki ki ce zaki walaƙanta mahaifiyarsa, ki sani in shi baya nan Allah yana nan, kada ki yi wannan kuskuren, komai zaki yi ya kasance tsakaninki da Allah zaki yi, baki san me gobe zata haifar ba, Allah ya kyauta ya saita maki al'amuranki, ki cigaba da yin addu'a tare da yin azzumi komai ya kusa warwarewa In Sha Allah".
Sosai Ouumar tata ta yi mata nasiha mai ratsa jiki, daga karshe suka yi sallama. Tana ajiye wayar ta ɗaura ɗamarar rusa wannan aure ta Haidar da Khadija koma ta yaya ne.
Da misalin karfe uku na yamma, Sadiq ya dawo da su Khadija daga makaranta, ya bawa maman Zainab ɗin kuɗin cefene, ya zama dai kamar shi ne mai gida, ya rikewa baban Zainab komai nasa da amana, yana kula da komai, kowani karshen sati zai zauna su buga lissafi shi da maman Zainab ɗin, ya ware ribar da kasuwa ta bayar ya zuba a cikin account ɗinsa, uwar kuɗi kuma ya koma da ita kasuwa, a cikin kuɗinsa da yake cirewa na sallamar da baban Zainab ya saba basu tun farko yake cirewa ya bawa maman Zainab ɗin kuɗin cefene, sam ba'a kuɗin baban Zainab ɗin yake ciyar da su ba, daga aljihunsa hakkinsa ya riƙesu bawan Allah.
Zai wuce ya nufi kasuwa maman Zainab ta dakatar da shi, ta ce ya zo su yi magana. Ba musu ya shigo cikin parlourn. A saman sofa mai zaman mutun biyu ya zauna, su Khadija kuma suka wuce cikin ɗaki domin su cire uniform su yi wanka kamar yadda suka saba.
Cikin rashin kwarin jiki ta gaya mashi yadda suka yi da mamar tasu, sannan ta ɗaura mashi da cewa idan sun ki rushe auren nan tabbas kara zasu kai su daga nan har kotu.
Ajiyar zuciya ya sauke, cikin nuna tsantsar kula tare da tausayawa ƴar uwar tasa ya buɗe baki zai fara magana kenan suka fara jiyo bugun kofar gida.
Haka kawai maman Zainab ta tsinci kanta da fargaba tare da faɗuwar gaba, kirjinta ne ya fara bugawa kamar wadda ta jiyo dukan kofar gida da tsakar dare. Hannunta ta kai ta dafe saitin kirjin nata, sannan ta furta Hasbunallahu wani'imal wakil.
"Sadiq duba su wanene?". Ta faɗa cike da fargabar su waye zata gani, ita a yanzu buga kofar gidan nasu ma bala'i ce a gareta, dan tasan ba alkhari take gani ba, wani lokaci bala'in su maman Haidar, wani lokaci baban Zainab da Hauwa, dukkansu kuma ganinsu tamkar ganin gagarumin bala'i ne a gareta, da zarar sun zo fa to shikenan ɗan sauran walwala da ya saura a tattare da ita ma zai tafi, zata faɗa sabon kuncin da sai ta fi kwana uku bata fita ba, so ganinsu ba alkhari bane a wajenta.
Miƙewa Sadiq ɗin ya yi hannunsa na rike da key ɗin mashin din baban Zainab da kuma keys ɗin shago a jiki, haka ya nufi wajen dan ya duba su wanene?.
Shi kansa sai da ya shiga fargabar abin da zai gani idan ya buɗe kofar, dan ya gaji da kallon wannan fitina da bala'i shi ma, amma da yake namiji ne shi sai ya ɗanne ya zare jam lock ɗin kofar.
Yana buɗe kofar ta fara zazzaga mashi buhun bala'i kamar dama ta tara bala'i ne tana jiran ta samu wadda zata zazzagewa shi a kansa.
"Wani irin iskanci ne wannan kusan minti uku kun bar mutane a tsaye a waje? Ku baku da tarbiya ko? Baku san darajar ɗan adam ba zaku barmu a tsaye!!".
Wani irin ƙululun bakinciki ne ya tokarewa Sadiq maƙoshi, ji ya yi tamkar ya tsinka mata mari sai ta sume a wajen, wata ƴar gajera da ita a gabansa, ba dan ganin baban Zainab da yake a tare da ita ba wlh yau ba abin da zai hana shi dalla mata mari shegiya. Amma haka ya danne ya kawar da kansa, ko sannu bai ce mata ba ya sa kai zai wuce cikin ɗakinsu kawai, ɓacin rai yasa ya mance bai gaishe da baban Zainab ɗin ba ma.
"Kai zo nan". Ta faɗa tana wani ɗage hanci sama. Da alama rashin mutuncin da take ji da shi yau yafi na kullum, da alama yau rabon babin rashin mutuncin ta buɗe.
Ɗan zaro idanunsa kamar na Zainab ɗin nan ya yi tare da juyowa ya kalleta.
"Yeah da kai nake yi, na ce ka zo nan! Ko ba zaka zo bane?". Hauwa duniya, akwai ta da son nuna isa da taƙama! Burinta ta ganta tana fadanci a waje jama'a suna yi mata biyayya, tana da son duniya da sharholiya sosai!. Sai kace Sadiq ɗin ɗanta ne, ta wani kirasa kamar ita ta haifesa, kira ma na walaƙanci.
Kai kallonsa a kan baban Zainab dake tsaye a gafenta ya yi. "Ba zaka zo bane tana kiranka?. Ka tsaya kana ganina?". Cewar baban Zainab ɗin.
Ɗan lumshe idanunsa ya yi yana ƙoƙarin danne zuciyarsa, dan wlh in ya biyewa zuciya harda baban Zainab ɗin zai haɗa duk ya ci ubansu, dama a wuya yake da su, suna son kashe mashi ƴar uwa ɗaya tilo, duk time da suka zo gidan idan suka tafi sai ta fi kwana uku tana fama da ciwon kirji, Allah ne kawai yake tsareta wani ciwon bai kamata ba, so a ƙule yake da su, idan ya biyewa zuciyarsa tsab zai sumar da su dukkansu biyu wlh.
Juyowa ya yi ya dawo gabanta. "Gani". Ya faɗa yana kawar da kallonsa gefe guda.
"Ba zaka tsugunna ba ka wani tsaya a gabana, so kake wuyana ya yi ciwo wajen ɗaga kaina na kalli fuskarka idan zan yi magana ne? Wannan ai rashin tarbiya ne, haka kake tsayawa a gaban mamanka gangan da kai ka sakata ɗaga kai sama dan ganin fuskarka kafin ta yi magana........."
Aikuwa bata kai karshen maganar ba ya dallah mata wani irin gigitattacen mari. Cikin tsananin ɓacin rai ya ce. "Iskancinki ya tsaya a iya kan maman Zainab, dan itace kuka haɗa wani abin da ita, kuma ko ita ɗin ma idan kika sake kuna wani magana da ita kika saƙo mamarmu a ciki sai kin gane ke karamar maras kunya ce! Mahaifiyarmu ba sa'ar ki bace, idan baki ɗauki taki da daraja ba mu tamu tana da daraja.......".
Shi ma bai kai karshen maganar ba baban Zainab ya dalla mashi mari tas a kumatu.
Wani irin ajiyar zuciya ya sauke tare da ɗaura hannunsa ɗaya a kumatun nasa, nan take idanunsa suka yi jajir kamar jini, da alama ransa ya ɓaci sosai. A hanzarce ya sanya kai ya fice daga gidan, domin gudun kada abin ya kwaɓe masu sosai, yasan idan ya tsaya zuciya zata ɗebesa ya daki baban Zainab ɗin ma, idan ya yi hakan kuma sam bai kyauta ba, yana da halinki sosai, baya manta alkhari, ba irin Haidar bane shi ɗin, yanzu ma ba dan ya lura Hauwa na ƙoƙarin saka mahaifiyarsu a cikin rai'nin wayonta ba da ba zai sanya mata hannu ba, yasan idan bai dakatar da ita ba tabbas zata cigaba da kiran mahaifiyarsu a cikin maganarta, shiyasa ya yi saurin taka mata birki, ban da haka da zai danne zuciyarsa ya shanye walaƙancinta ko dan saboda baban Zainab ɗin.
Kafin baban Zainab ya yi wani magana tuni ya fice daga gidan da sauri.
Kukan munafurci Hauwar ta saka mashi, cike da makircin tana kukan munafurcin ta fara magana. "Wlh baban Zainab ni ba zan yarda ba, kana gani wani ƙato ya dakeni ina matsayin matarka, dole a bi mun hakkina".
(Matarsa kuma?🤔 Yaushe aka yi hakan?🤔 Dole su yi mana bayani)
Hakuri ya fara bata tare da gaya mata to ba ga shi ya rama mata marin ba. Kafewa ta yi a kan ita fa ba zata yarda ba, wannan