Showing 183001 words to 186000 words out of 296878 words

Chapter 62 - RAWANIN ZALINCI BOOK 1 COMPLETE HAUSA NOVEL

20 Dec 2025

79

space ɗin, saboda ƙarami ne.

"A'isha mu je ko?". Cewar wannan mata, ta yi maganar tare da sanya kai ta fito waje daga cikin motar, already driver ya buɗe mata mota. Gabaɗaya gidan tiles ne har harabar gidan, tiles mai mugun kyau launin sararin samaniya wato sky blue, hakan yasa ya haɗe da haske ya kara ƙawata gidan sosai da sosai. Ga haɗaɗɗun flowers masu bala'in ƙamshi da kamshinsu ya karaɗe ko'ina a harabar gidan, kamshin nasu irin mai daɗin shaƙar nan.

Duk Leesharh sai ta ji ta rai'na class ɗin matan ma gabaɗayansu, har mamaki ne ya ɗan kamata na ganin driver ya buɗewa wannan mata kofar motar, a ranta ta ce ashe ma gidan talakawa aka kai ni da farko, ina cewa ba dan dukiya zasu farauci rayuwar Ramish ba dan suna da ɗinbin dukiya, ashe ni mahaukaciya ce ban san komai ba, ashe ma talakawa ne na ƙarshe a gaban familyn Abu Abdussalam, lallai na yarda son kuɗi zai iya sawa su farauci rayuwar Ramish, wannan shi ne gaba ma da gabanta wai aljani ya taka wuta.

(Ku kuwa daga ganin irin wannan gida yakamata ku gane cewa dole Mommar Gimbiya Zunaira ta fita daban a cikin sauran matan King, nan fa gidan yayanta ne uwa ɗaya uba ɗaya, kuma ita ce kaɗai mace a cikinsu, kunga kuwa dole su kaunace ta over, dole komai nata ya fita na daban a cikin KINGDOM OF POWER.)

Tana can tana tunane tunane sai ji ta yi an janyo hannunta tare da fito da ita daga cikin motar suka nufi ciki. Gidan bashi da wata hayaniya, ma'ana ba part part bane, a cure yake waje guda gwanin birgewa. Kai tsaye elevator suka nufa wadda zai kaisu izuwa katafaren ginin da family suke.

Leesharh an saki baki, ido hanci, kunnuwa da komai da komai ana bin ko'ina da kallo, bata wahalar da kanta wajen ɓoye kauyancinta ba, ta fito da shi fili tana morewa idanunta kallo abinta, ta ki bari kanta ya yi marfi ato, har ta manta da cewa wancan mata ta ce kada ta yarda ta nuna kauyanci, kome zata gani ta dake irin ita ƴar birnin nan, tab aiko dai ga shi nan ta saki baki tana baza kauyancinta son ranta.

Ai bata ma karasa sakin bakin nata mai gabaɗaya ba sai da suka shiga katafaren parlourn gidan, a nan ne ta fito da tsantsar kauyancinta tana ganin royal furniture dake a ciki, ta buɗe kofofin hancinta dukka tana shaƙar wani ni'imantaccen haɗaɗɗen arab air freshener dake kwantar da hankalin mai shaƙa wadda ya karaɗe gabaɗaya parlourn da kamshi, ga tsabta da sanyin Ac.

Wata hamshaƙiyar hajiya kyakkyawa fara tas ne take zaune a saman sofa mai zaman mutun biyu, babbar macece ba yarinya ba, tana sanye cikin arab jallabiya, fara tas da ita, ta yi rolling veil a kanta, yatsun hannunta na sanye da wasu shegun ring na diamond masu bala'in tsada har guda uku, ta haɗu iya haɗuwa, ta ji hutu har ta ƙoshi, da alama itace matar gidan, ga wata kyakkyawar matashiyar yarinya da take kwance a kusa da ita ta tada kai da laps ɗinta, a shekaru yarinyar ba zata wuce mate na Leesharh ɗin ba, kyakkyawa ce sosai ita ma, tana da ɗan yanayi da wannan hajiya, da alama mahaifiyarta ce, da alama ita ce ƴar Abu Abdussalam da aka ce yana da ƴaƴa maza biyu da mace ɗaya, yarinyar ma arab jallabiya launin white ne a jikinta, kanta babu ɗan'kwali, wannan kyakkyawan arab hair ɗin nata an ɗaure mata shi gida biyu kamar yadda Gimbiya Zunaira da kuma Chuchu suke yawan ɗaure nasu gashin, haka ita ma aka yi mata.

Fuska ba yabo ba fallasa ta tarbi wannan mata da ta zo da Leesharh. Saman sofa matar ta zauna, ita kuma Leesharh ta zauna a ƙasa saman wani haɗaɗɗen Turkey carpet mai bala'in laushi, har wani lumewa zaka ji kafafunka sun yi idan ka taka carpet ɗin.

Cikin girmamawa wannan mata ta ɗagawa hajiya babba gaisuwa. Cikin mutunta zuna hajiya ta amsa, da alama tana da kamala da dattaku, babu alamar walaƙanta mutane a tattare da ita duba da yadda ta karɓi su Leesharh cikin mutunci duk da tasan cewa tabbas Leesharh ƴar aiki ce, domin tun kafin Leesharh ɗin ta zo gidan tasan da hakan, kada ku manta kafin ma su zo sai an san da zuwansu an kuma san su waye su, so tasan aiki Leesharh ta zo yi, amma bata nuna irin kyama ko kyara ba, ta tarbesu da mutunci.

Sosai Leesharh ta ji jikinta ya yi sanyi na ganin yadda matar ta mutuntasu, ko ba'a gaya mata ba ta san cewa wannan mata itace hajiyar wannan aljannar duniyar bakiɗaya, amma ji yadda ta tarbesu kamar wasu ƴan uwanta, duk sai ta ji jikinta ya yi la'asar da ta fara tunanin to meyasa ake son cutar da su tun da dai alamu sun nuna su ɗin mutanen kirki ne?. Yarinta bai bari ta iya gane cewa yanzu ai masu kirki ake cutarwa ba, da zarar kana da kirki neman ganin bayanka ake yi, musamman idan ta haɗo da kana cikin siyasa, sarauta, da dai sauransu, idan ka ce zaka yi adalci ko ka yi wa al'umma hidima ai kana tsaka mai wuya a hannun abokan gaba sai dai Allah ya tsare!.

A fili ta furta Allah masani wadda sam bata san maganar ma ya fito ba, sai da ta ga hajiyar tana kallonta ne ta fahimci ashe ta yi magana.

Cike da tsoro ta yi ƙasa da kanta. Ita kuma hajiyar sai ta ce. "Turai yanaga kamar ƴar aikin namu bata da lafiya ko kuma wani abin yana damunta?".

Wani irin dum dum Leesharh ta ji gabanta ya bada bugu.

Matar da suka zo a tare ɗin ne wadda Hajiya Babba ta kira da Turai ta ce. "Hajiya Babba ai dole ki ganta a birkice haka, kema kinsan duk wanda zai shigo wannan gida sai ya razana, securitys ɗin nan naku masu fusatattun fuska da babu amnurin nan ba dole su birkita mutum komai jarumtarsa ba!".

Ƴar murmushi Hajiya Babba ta yi kafin ta dubi ƴar matashiyar yarinyar da ta tada kai da laps ɗinta ta ce. "Sharifat jeki ki kira mun Radia ta zo ta wuce da wannan yarinyar izuwa part na ma'aikata dan ta je ta huta, da alama akwai gajiya da firgici a tattare da ita".

Miƙewa zaune yarinyar ta yi, ɗan waro idanu waje ta yi irin mamakin nan lokacin da ta kalli Leesharh, da ƴar siririyar zazzaƙar voice ɗinta ta dubi Hajiya Babba. "Ummie she's so beautiful, Allah kyakkyawace sosai, harta kalar fatarta ya yi mun kyau".

Ƙasa da idanu Leesharh ta yi tare da sauke nannauyar ajiyar zuciya, yanzu ta kara tabbatarwa da kanta waɗan nan mutane mutanen kirki ne, ji yadda yarinyar gidan ma ta karɓeta kamar ba ƴar aikinsu ce ita ba. Allah wadarar mummunar aikin da ta zo aikatawa a kansu ta fara yi, sai dai kuma bata fa da wani zaɓin da ya wuce dole ta yi wannan aiki ko zata mutu kuwa, dan mahaifinta shi ne duniyarta. Babbar magana, wlh akwai cakwakiya da tashin hankali ba kaɗan ba a wannan part ɗin!.

Sharifat kyakkyawar yarinya ce sosai, amma a rayuwarta tana kaunar kyawawan mutane, idan taga mace kyakkyawa sai ta ce su ƙullah abota, haka take yi, shiyasa take kaunar yayanta Omar, yayan gimbiya Zunaira kenan, saboda fa kyakkywa ne sosai kamar Zunaira ɗin shi ma, idan kuka gansa kamar shi ya yi kansa, ga idanun nan nasa ba'a magana, so suna mugun shiri da Sharifat sosai! Shi ma a gidan nan yake, ba'a gidan kakarsa yake zama ba, ya fi jin daɗin zama a gidan nan saboda Sharifat ɗin babbar kawarsa kenan.

"Sharifat kenan, ai haka Aisha take da kyau, sai ma ta yi make up". Cewar Turai.

Murmushi Sharifat ta saki tana faɗin. "Kai bari Yah Omar ya zo zan gaya mashi ankawo ƴar aiki kyakkyawa wadda ta fishi kyau".

Girgiza kai Hajiya Babba ta yi kafin ta ce. "Da kuwa kinci bugu a hannunsa, GUYSON ɗin namu ne zaki ce wata ta fishi kyau? Kin manta me ya gaya maki na cewa babu wanda ya kaisa kyau a duniya ko? Faɗa mashi wata ta fisa kyau ina ga yau ko Abbunki ba zai iya kwatarki a hannunsa ba".

Ɗan turo baki ta yi tare da miƙewa ta nufi wani haɗaɗɗen curtain, yaye shi ta yi ta shige ta kofar da yake a wajen, tana tafiya tana ɗan juyowa ta kalli Leesharh, ita dai har ga Allah Leesharh ta yi mata kyau ba kaɗan ba, ga shi a tsawo ma tsawonsu zai iya zuwa ɗaya, shekaru ma haka, sai take jin dama ace Leesharh ƴar uwarta ce ta jini, kasancewar ita kaɗai ce mace a gidan, hakan baya yi mata daɗi, ƴan uwa maza kawai take da su, ita sam bata damu da kalar African skin ɗin Leesharh ɗin ba, ita dai kawai ta burgeta tunda kyakkyawa ce. (Ni kuwa na ce a'a Sharifatu baiwar Allah, ki nesanta zuciyarki da Leesharh, dan ita ɗin kyan ɗan macijine a gareku keda ƴan uwanki, cutarku tazo yi, duk da cewa ba laifinta bane, amma dai ku yi nesa da ita, kada ma ku jata a jiki, idan kuka jata a jiki ne ma zata samu damar cutar da kuɗin yadda yakamata, amma dai nayi shiru......🥱)

Shiru parlourn ya yi na tsawon lokaci, har Sharifat ta dawo daga wajen kiran Radia. A tare suka dawo da Radia ɗin, tana gaba tana binta a baya. Saman sofar da ta tashi ta koma ta kwanta tare da tada kai da laps ɗin Ummie ɗin nata.

Ita kuma Radia a gabansu ta zo ta tsugunna, balarabiya ce ita ɗin ma. Cikin girmamawa ta ce. "Ummie gani nan".

Nuna mata Leesharh da hannu Ummie ta yi tare da faɗin. "Ki wuce da ita part ɗinku, already ɗakinta is ready tun da Abbu ya gaya mun za'a kawo wata ƴar aiki nasa su Fadila suka gyara mata room ɗinta, dan haka ki ce Fadila ta nuna maki room da suka gyara mata ki kaita can". Ta kai karshen maganar tare da dawo da kallonta a kan Leesharh.

"A'isha ko?". Ta tambayeta.

Da sauri ta gyaɗa mata kai alamar e kanta na'a ƙasa kamar wata sahabiya.

"Okey tashi kuje ta kaiki room ɗinki, ki yi wanka ki kwanta ki huta, su Fadila zasu baki abinci, yau ki huta gobe sai ki fara aiki ko?". Cikin sanyin murya Ummie ta yi maganar, tana da cool voice sosai kamar yadda yanayinta ya nuna ita ɗin so silent ce.

Duk maganar da suke yi cikin harshen larabci suke yinsa.

Da okey Leesharh ta amsa mata tare da yi mata godiya, sannan ta miƙe tsaye, Radia ma ta miƙe ta yi gaba Leesharh ɗin ta rufa mata baya, sai kallonsu Sharifat yarinyar kirki take yi, taga Leesharh kyakkyawa jinin Africa tamu ta gida!.

Cigaba da hira sama sama Hajiya Babba da Turai suka yi, da alama sun saba. Ita kuwa Sharifat ta cigaba da kwanciyarta shiru abinta!.

KO YA RAYUWAR LEESHARH A WANNAN GIDA ZATA KASANCE?🤔 LOKACI NE ZAI NUNAMANA, ALKALAMINA KUMA YA BAYYANA MAKU KOMAI, AMMA DAI AKWAI GAGARUMIN CAKWAKIYA BA KAƊAN BA, DAN KUWA LEESHARH DOLEN UBANTA TA YI WANNAN AIKI IDAN TANA SON MAHAIFINTA!!.

🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️🌼🕊️

GIDANSU KHADIJAH 💔😥

Maman Zainab tasha madarar mamaki sosai lokacin da Baban Zainab ya dawo daga kasuwa, yadda kuka san bai san da zamanta a gidan ba, ko ɗaga idanu ya kalleta yaki yi, da alama ma haushinta yake mugu mugun ji, ko kallon in da take bai son yi. Ko da ta kawo mashi abincin dare ma a yau kam bai ci ba, yaki ko kallon abincin nata ma, abin ya yi mugun ɗaga mata hankali na ƙin karawa, hakan yasa ta shiga gagarumin tashin hankali a in da ta shige cikin room ɗinta tare da rufo kofa, ta murzaki, sannan ta ɗauki wayarta tana kuka hawaye bibbiyu ta kira Aunty Hauwa a waya ta sanar da ita maganin nan fa bai yi aiki ba, hasali ma baban Zainab yaki yi mata magana, ko sannu yaki ce mata, in fact ma yaki kallon in da take, yaki ya ci abincin dare, su Khadijah ɗin ma ya sharesu yau kam, dama wani lokaci saboda su yake daurewa ya danne zuciya idan ta yi mashi laifi ya ci, to yau dai a gabansu ya ce ba zai ci ba, ya kuma wuce cikin bedroom ɗinsa ya kwanta, wannan abin ya yi matuƙar ɗagawa Khadija hankali, da yake ita hankali da ilimi ya ratsata sosai a yanzu, ga nutsuwa da sanin yakamata, tasan baban nata bai taɓa yin makamanciyar haka a gabansu ba tun da suke da shi, to me ya sauya shi lokaci guda haka kenan?.

Zeezee da take karama ma hankalinta ya tashi yau, ta shiga damuwa, haka dai suka hakura suna ɗan ci abincin kaɗan, sannan suka nufi nasu ɗakin suma, domin mamarsu ta rufe nata bedroom ɗin tana ciki, shi ma baban nasu haka. Har sun kwanta Khadija ta gagara yin barci, barci ya ƙaurace daga idanunta baiwar Allah, damuwa sun taru sun yi mata yawa, hakan yasa ta miƙe ta sauke ƙasa daga saman bed ɗin nasu.

A lokacin Zainab barci ya fara ɗaukarta, lallaɓawa ta yi ta ɗauki hijabin sallarta ta sanya a jikinta ta nufo waje. Tana tsoron fitowa saboda Haidar, amma bata da zaɓi dole ta je wajen kawunta Sadiq ta gaya mashi abin da yake faruwa, dan shi ne kaɗai zai iya gaya mata kalaman da zasu sanyata jin daɗi har ta samu barci, amma sai fargabar haɗuwa da Haidar take yi, addu'a take yi Allah yasa ya yi barci, dan idan bai yi barci ba ta je room ɗinsu a yanzu tabbas sai ya tsayar da ita in ta gama magana da Sadiq, idan kuma ya tsayar da ita ba makawa sai ta taɓa mata jiki, sai ya yi ƙoƙarin taɓa mata breast ɗinta ko ya ce zai yi kissing ɗinta, sam bashi da hankali ko na sayan pure water.

Sai dukan uku uku kirjinta yake yi, amma haka ta daure ta fito harabar gidan. Ai kuwa tana fitowa ta yi sa'ar cin karo da Sadiq ɗin yana tsaye a harabar gidan wajen fampon tsakar gida yana waya, da alama da mamarsa yake waya, shi ne ma yasa ya fito waje dan su sami keɓewa da sirri, ba zai yi waya da ita a gaban Haidar ba kenan, yadda ya nutsu sosai yake magana cikin mutunci da girmamawa ne zai tabbatar maka da cewa tabbas da mahaifiyarsa yake waya, dan idan da budurwace ba zai yi irin wannan nutsuwa ya bata dukkan hankalinsa tare da magana cikin girmamawa haka ba. Yaron kirki mai hankali da sanin darajar iyayensa.

A hankali kamar wata mai raɗa ta yi mashi sallama, tun fitowarta dama ya ganta, shiyasa yake ƙoƙarin yin sallama da mamar tasa, saboda yasan Khadija bata zuwa wajensa haka kawai, kuma idan ma kaganta a waje harabar gidan to fa girki take taya Mammarta, idan ba haka ba kullum tana ƙule a ciki abinta, ɗan gara ma Zainab tana fitowa waje jefi jefi. So yasan bazata fito haka kawai ba, barema a daren nan yasan dole da akwai matsala, hakan yasa ya yi sallama da mamar tasa a kan gobe da safe zai sake kiranta, daga nan ya kashe wayar tare da bawa Khadijahr dukkan attention ɗinsa.

Cikin sanyin murya ta fara gaya mashi halin da ake ciki, ta shiga damuwa sosai na ganin baban nata yaki ya ci abinci, bata ɓoyewa Sadiq komai ba ta gaya mashi tas, sannan ta kara da cewa abin ya hanata yin barci ne yasa ta fito.

Zama ya yi a bakin dakalin da aka kewaye fampon da shi, sannan ya ce ita ma ta zauna. Ba musu ta zauna a gefensa, hakika ya shiga damuwa sosai, irin wannan matsala yake gujewa maman Zainab tun tuniya yasa yake ta ƙoƙarin ganin bata sauka daga kan hanya ba, amma ta yi busur da zancensa ta yi son ranta, ga shi yanzu wankin hula yana neman kaita dare, tura ta kai bango baban Zainab ya fara juya mata baya, yanzu wa gari ya wayanwa?.

Rarrashin Khadija ɗin ya fara yi tare da bata hakurin, sannan ya sanar da ita dama a tsakanin mata da miji ana iya samun wannan matsala, aure ya gaji hakan, babanta mutumin kirki sosai da yake ɓuye masu ire iren wannan faɗa na mata da miji yasa basu san da hakan na faruwa ba, dan haka kada ta sanya damuwar kowa a ranta, ta yi hakuri zuwa da safe In Sha Allah babanta zuciyarsa zata sauko, dan shi mutun ne mai hakuri, ta yi hakuri komai ya yi zafi maganinsa Allah, ta koma cikin room ɗinsu ta ɗauro alwala ta gabatar da nafila raka'a biyu tare da rokan Ubangiji da ya kawo mata mafita, In Sha Allah zata samu dama ta yi barci, komai kuma zai wuce.

Haka dai ya cigaba da rarrashinta yana bata kwarin gwiwa har ta ji sanyi a ranta. Sai da ya tabbatar ta ji daɗi damuwarta ya gudu, sannan ya ce ta tashi ta shiga ciki. Duk da rashin yawan magana irin tata sai da ta ce. "Kawu Sadiq ka bari mu ɗan yi hira kaɗan, zan kara samun nutsuwa na sani".

Bai musa mata ba ya jata da hira har wuraren karfe 10, sannan ne ya ce ta tashi ta shiga ciki. Ba musu ta miƙe ranta a sake, fuska ba yabo ba fallasa ta wuce ciki tana yi mashi zai da safe. Shi ma sai da safe ya yi mata kafin ya miƙe ya koma cikin room ɗinsu a in da ya sami Haidar yana riƙe da wayarsa yana kallo, ko shakka bayayi fina finan batsa yake kallo duba da yadda ya takure jikinsa waje guda, kuma yasha kamasa yana kallon fina finan batsa dama, sau da dama yasha yi mashi nasiha a kan hakan babu kyau ya daina, amma ina ya yi nisa baya jin kira, hasalima idan bai kalli batsan ya samarwa da kansa nutsuwar hankalinsa da ya ɗaga ba baya iya yin barci, hakan yana ɗaya daga cikin abin da yasa yake son taɓa jikin Khadija sosai, shi bai kima

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login