Showing 231001 words to 234000 words out of 296878 words

Chapter 78 - RAWANIN ZALINCI BOOK 1 COMPLETE HAUSA NOVEL

20 Dec 2025

102

sam jininsa bai haɗu da ita ba, shi fa Jaish bayan mommarsa wlh jininsa bai haɗu da kowa ba a cikin matan nan, harta mummy da take sonsu ɗin ma, shi kowa ma bai ishe shi kallo ba, yana dai kaunar Yah Jawad sun fi shaƙuwa, kuma yana kaunar uncle Abbas sosai kamar ransa, amma ya tsani Mammie, baya son haɗa hanya da ita da kuma Mamma and Mummy.

A hankali ya miƙe tare da ɗaukar wayarsa, ya baro laptop ɗin a wajen bayan ya kashe wutar screen ɗinta, cikin gida ya nufa. Cikin nutsuwa yake tafiya. Kai tsaye part ɗin mommarsa ya nufa, da alama ba zai je kiran Mammie ɗin ba, dan ba part ɗin uncle Abbas ya nufa ba.

Zaune a parlourn ya isko mommar tasa tare da wasu kuyangunta guda biyu da suke zaune a gefe da gefenta, ga mama Haulat kuyanga ta musamman wadda momma ta aminta da ita, ita kaɗai take iya shiga har cikin bedroom ɗin momma, tana zaune a gaban mommar tana tsantsara mata zanen flowers lalle masu matuƙar kyau, zanen ya fita, abinku da farar fata ga zanen lallen baki da ja, sai ta yi wani irin kyau na musamman, ta fito a amaryar King ɗin da gaske.

Kusa da ita ya kariso saman sofar da take ya zauna, da yake a saman sofa mai zaman mutun uku take zaune, ta ɗaura kafafunta a saman throw pillows dake a gabansa, hannayenta da aka yi mata zanen flowers ɗin ta ɗaura su a saman wasu ƙananan throw pillows wadda kuyanga Mama Haulat ta ɗaura mata su a saman sofar da take zaune ɗin.

Zama ya yi ba tare da ya yi magana ba, cikin hanzari dukkan kuyangun har da Mama Haulat ɗin ma suka miƙe tsaye, a hanzarce suka nufi waje, dan su basu waje ita da ɗanta su tattauna.

"Jaish lafiya na ganka haka? Ko dai wani abin yana damunka ne?". Ta yi maganar tana dawo da kallonta a kansa.

"Momma lafiya lou, me kika gani?". ya yi maganar yana kamo hannunta dake ta kusa da shi.

"Momma waɗan nan flowers ɗin sun yi maki kyau sosai da sosai". Ya faɗa yana kallon face ɗinta.

"Na ganoka waskewa kake son yi, ba wani kyau da flowers suka yi, kana son ne ka mantar dani daga tambayar me yake damunka da na yi ko?".

"Kai momma ba haka bane, da gaske flowers ɗin sun yi maki kyau, ayiwa auta ma zata yi kyau sosai, kuma da gaske babu wani abin da yake damuna, gajiya ce kawai, kuma nasan dana ɗan huta zan wastsake".

Wani irin kallo ta wurga mashi wadda ya ɗan sanya shi kajeriyar murmushi. "Kai momma da gaske fa nake yi, wai meyasa ke da daddy idan mutun ya yi maganar da baku gamsu da ita ba kuke yi mashi irin wannan kallon da sai kun saka shi murmushi ne?".

Haƙiƙa murmushi da ya yi a karon farko yau ta yi mashi kyau matuƙa, kyansa ta kara bayyana sosai, sai ya yi kama da ita mommar da ya yi wannan murmushin.

"Hakan zai tabbar mun da ba abin da ka faɗa bane yake damunka, idan da shi ne da gaske in na yi maka irin wannan kallo ba zaka yi murmushi ba, sai dai ka ɗaure fuska, dan gaskiya ka faɗa". Ta bashi amsa tana murmushi.

"Oh momma dama wannan kallon tarko kenan kuke haɗa mana ko? Kusa mu faɗar gaskiya ba shiri, to yau na gano sirrin, amma momma daddy ne ya koya maki ko? Dan nasan ke ba haka kike ba tun farko......"

Tarar numfashinsa ta yi da cewa. "A'a ni dai na koya mashi, kasan ai ni ta daban ce".

Shiru ya ɗan yi kafin ya ce. "Kai momma daddynmu fa na daban ne, ni nasan shi ya koya maki".

"To duk dai ba wannan ba, gaya mun menene yake damunka kada ka mantar da ni?". Ta yi maganar tana ƙoƙari janye hannunta daga riƙon da ya yi mata, dan ta lura suna hirar nan zai iya kyaɓe mata flowers ɗinta, saboda yana magana yana mancewa da cewa hannunta ya rike.

"Kai momma keko? Ba zaki bar mutun ba sai dai ya gaya maki ɗin, wai ma ni ya aka yi kika gane cewa ina da damuwa ne?".

"Saboda ni na haifeka mana, kuma ba zan bari ba sai na ji me yake damun mun kai".

Shiru ya ɗan yi yana jin kaunar mahaifiyar nan tasu, tun jiya yake fama da damuwa a kan aikinsa, ya so su zauna da Jawad su yi magana, amma ina bai samu dama ba, Jawad yana can yana soyayya, babu wanda ya iya gane cewa yana a cikin damuwa sai mommarsa, ya je wajen King almost sau uku, amma King bai iya gane yana cikin damuwa ba, ita kuma da kallo ɗaya ta yi mashi ta harbo jirginsa.

"Tunanin me kake yi?". Ta katse shi.

Ɗago da kallonsa ya yi izuwa saman face ɗinta, ba zai iya gaya mata abin da yake bincike a kai ba, saboda yasan halinta da zafin zuciya, yanzun nan sai ta ce da King dole a rufe wannan Company kuma dole a kama masu haɗa magunguna da kayan mayen nan, momma fa bata da sauki ko kaɗan wani lokaci, ko da yake su dama modarawa ina suka ga sauki? Ai da manya da yara duk a jininsu abin yake, akwai su da ɗaukar zafi ba wasa.

"Momma wani bincike nake yi yake saka mun zafin kai, ina ganin ma zan yi tafiya na ƴan kwanaki".

"Dubai zaka je?". Girgiza kai ya yi alamar a'a. Baya son gaya mata in da zai je, sannan kuma baya son ya yi mata karya, domin bai san me zai je ya dawo ba, saboda Company ne da suke da haɗaka da manyan campanoni daga ƙasashen turawan yamma, reshe suka zo suka kafa a nan, amma ainahin daga waje ake shigo da duk wasu gurɓatattun kayan aikin da sauransu, to idan ya banƙaɗo sirrin bai san a iya ina rigimar zata tsaya ba, dan abu ne na manyan kai, baya son ɗagawa mahaifiyar tasa hankali.

"Brazil zaka je?". Ta sake jefo mashi tambayar.

"Momma ban fa tabbatar da zan yi tafiyar ko ba zan yi ba, ina tunani ne kawai, sai na tabbatar". Ya faɗa a fili, a cikin zuciyarsa kuma ƙudurin tafiya binciken daga wani kamfani ne na waje ke turo waɗan nan kayayyakin, zai yi hakance kuma domin ƙara samun hujja, kunsan cikakken ɗan jarida komai da hujja yake yi, sai ya riƙe hujjoji masu zafi yake fasa kwai, to shi ma hakance.

Sallamar Obaid and Omaid ne ya katse masu hirar ta su. Ji suka yi tamkar su juya su koma na ganin Jaish a parlourn da suka yi, sam basu son haɗuwa da yayan nasu inuwa guda, domin kuwa ya rinƙa tuhumansu kenan, kuma ya rinƙa yi masu nasiha kenan, su kuma basu so. Amma da yake sun rigada sun shigo, sai suka ƙariso ciki kawai.

A kusa da mommar tasu suka zo suka zauna, sai dai a ƙasa saman carpet, sun wani nutsu tamkar wasu alaranmomi daga babban masallacin Madina, irin Jaish ya ce yanzu suna da nutsuwar nan, waɗan nan ƴaƴa sun san kan duniya.

Cikin girmamawa suka ce. "Yah Jaish ina wuni?".

Bai yi mamaki ba, dan shi fa yasan su waye su, fin haka ma zasu aikata in dai su ne.

Da lafiya ya amsa masu sannan ya ɗaura da cewa. "Me yau kuma kuka aikata?".

Ajiyar zuciya suka sauke a tare, faɗi suke yi a cikin zuciyarsu cewa ko zamu mutu sai Yah Jaish ya ɗaura mana ayar tuhuma, mu dai mun shiga uku, wai kullum mu cikin aikata abu muke yi.

A fili kuwa sai cewa suka yi. "Yah Jaish babu abin da muka aikata fa, mu fa yanzu we're so silent, innocent and babu ruwanmu da kowa".

Ita dai Momma sai murmushi take yi, dan tasan halin kayanta, tana da tabbacin sun yi wani abin kamar yadda Jaish ya zarga, baya zargi a banza ai. Kuma da gasken ne sun yi wani abin kamar yadda ya faɗa, mugunta suka shiryawa mama a daren yau, dan gobe zasu koma Dubai an buɗe school, shi ne ma yasa suka zo yin hira da mommsrsu, dan zasu koma, to tabbas sun aikata wani abin ne, shi ne dan iya shege har da wani kara nutsuwa kamar wasu limaman masallacin harami.

"Kun gama shirin ku ko?". Jaish ya tambayesu.

Har suna haɗa baki wajen ce mashi e sun kammala shiri.

"To ku dai tsaya ku yi karatu, kuma a duk in da kuke ku sani Allah yana ganinku idan mu bama ganinku, ku rage rashin ji, ku nutsu ku dai'na zalintar kowa, na gaji da jin sunanku a bakunan mutane, yadda kuka san ku kaɗai ne student a makarantar nan naku, ko ziyara na kai maku sauran students har tsayawa suke yi suna satar kallona, saboda yayanku ne ni, duk kun takurawa yayan mutane a makaranta, ku akwai wanda ya takura maku ne? To wlh ku nutsu, idan ba haka ba Allah next time na sake jin wani abin kun aikata, to ba makawa sai na miƙaku ga kasar Faransa ku je ku zama sojojinta na dai gaya maku, tun da ku dama wahala bata yi maku komai, kun saba da yin up and down".

Zaro idanu waje suka yi, har suna haɗa baki wajen cewa. "Allah Yah Jaish mu mun nutsu yanzu, ba zaka sake jin komai ba, mun tuba, dan Allah ka bar maganar ƙasar France ɗin nan, mu bama son ji".

"In dai baku son ji to ku nutsu, idan ba haka ba kun san dai bana magana biyu".

Omaid ne ya ce. "Ni dama can babu ruwana, Obaid ne baya ji"

(Tab wai kun ji Omaid babu ruwansa🤔 bayan kuma ya fi Obaid iya mugunta da rashin ji😅)

"Kai Omaid ni ma ai babu ruwana".

Momma dai murmushi kawai take binsu da shi, dan ita bata da ta cewa, yaran nan nata sai addu'a, dan ma yayyunsu maza sun tsaya tsayin daka a kansu ne, da wlh Obaid and Omaid sai Allah, rashin jinsu ba zai tsaya a iya nan ba, amma Alhamdulillah, a cikin kingdom of power idan suka zo su Jaish basu kyalesu ba, suna kula da su tare da yi masu faɗa da nasiha, dan nasiha tafi tasiri a zukatan mutane sama da faɗa ko duka, wani ma idan ka dake shi sai ya ce ba zai yi abin da kake so ɗin ba sai dai ka kashe shi, amma koya mutun ya kai ga taurin kai wlh nasiha tana tausasa zuciyarsa koda a iya wunin ranar ce kawai, bare kuma nasihar idan aka haɗa da annabi Muhammad (S.A.W) ta fi shiga cikin zuciya ta tausasa zuciyar bawa, karya ne a kirawa mutun Allah da annabi a sake kira bai ji zuciyarsa ta risina ba, sai dai kafurar zuciya ta kafuran farko. So a gaskiya nasiha ta fi faɗa ko duka tasiri musamman ga zuƙatan yara, ku rinƙa nuna masu Allah da annabi cikin ruwan sanyi tare da dabara ta yadda zasu fahimta ya kuma nutsa cikin zuƙatansu, hakan zai sa su taso cikin kamala da nutsuwa.

A Dubai kuwa ga su Ramish, suma a kullum suna yin nasu iyaka baƙin ƙoƙarin wajen ganin kannenen nasu sun nutsu sosai. Amma kuma abin mamaki yadda kuka san ba lafiya ba, kullum rashin jinsu da taurin zuciyarsu karuwa yake yi, sun iya shirya mugunta daki daki babu ko ɗar ɗar, yanzu ga shi Yusuf saurayin Sarina da mu readers muke zargin su suka shirya mashi wannan mugunta, ga shi bawan Allah nan kafin a sakesa ya koma gida baya iya tafiya da kafafunsa, commander Zafar sai da ya ragargajesu kamar ba gobe, takawa da kafafunsu dai sun ƙasa iya yinsa, a haka aka kwashesu zuwa hospital, bayan sun sami lafiya aka sallamesu zuwa gida, wai a haka ma sboda uncle Abbas an yi masu da sauki, ba dan haka ba kaciya ta biyu za'ayi masu, commander baya ɗaukar wasa ai, kuma ba abin da iyayen Yusuf ɗin suka isa su yi, domin kuwa ba wanda ya isa ya ɗaga yatsa a kan wannan masarauta kuma ya zauna lafiya, sannan kuma ai hannu dumu dumu aka kama Yusuf ɗin ba zarginsa ake ba, so dole su ja baki su yi shiru.

Sosai Jaish ya yi masu nasiha mai rasa zuciyar mai sauraro, amma kuma su dai bai wani ratsa su ba, tabbas sun ɗan yi ladab, amma dai ba wai can can ba, abin nasu kamar dai ba lafiya ba.

Sun ɗan jima suna hira a tare da mahaifiyar tasu kafin su miƙe su ukun dukka, sannan suka yi mata sallama suka fita.

Addu'a da fatan alkhari ta yi masu har suka fice. Suna fita kuyanga Mama Haulat ta dawo cikin parlourn domin ta ƙarisar mata da lallenta, sannan ta wanke mata tare da yi mata hayakin turaren lallen da sauransu, lalle mai turare take yi mata, shi kwaɓinsa na musamman ne, ya fita daban da sauran dukkan lalle da kuka sani, shi yana yin two months kafin ya goge, kuma kullum zaka gansa kamar sabo yana kyalli, kuma zaki yi ta zuba ƙamshi mai bala'in daɗi har sai ranar da ya goge, larabawar Dubai ne suka fi yawan amfani da shi, yana da tsada sosai, ba ko'ina ake samunsa ba sai gidan mulki, shi ma sai wane da wane, to ita dai momma kowani lokaci irinsa ake yi mata, haka Gimbiya Zunaira da Chuchu ma.

A bangaren Mammien Yah Jawad kuwa, haka ta yi ta jiran Jaish amma ina shiru bai zo ba, dama tasan da wuya ya zo, saboda sau da dama tana aikawa a kirasa baya zuwa, idan kunga ya je kiranta to an aiko ya zo ɗin suna a tare da Yah Jawad ne, shi ne zai je, domin kada Jawad ɗin ya ji babu daɗi, amma idan Jawad baya nan wlh baya zuwa, ko kallo ma bata ishe shi ba.

Ranta ya sosu sosai da sosai, ga shi a duniya bata da burin da ya wuce Jaish ɗin ya auri Fanan, wato ƴar autarta kenan, kanwar Sarina, shi kuma abin da yasa ma kenan baya kaunar zuwa in da take, dan in dai ya je sai ta yi mashi zancen Fanan, bata ma san shi haushi Fanan ɗin take bashi ba, kai shi fa baka gane mashi, kowa ma haushi yake bashi.........😅

Tana burin Fanan ta auri Jaish ɗin ne saboda dalilai da dama, kaɗan daga ciki sun haɗa da kasancewar Jaish jika ne ga the most powerful King Badeen, and kuma ƴan uwansa daga sama har kasa part na mommarsa daga masu mulkin siyasa sai masu sarauta, sannan Jaish yana da tarin dukiya duk da bai kai mommarsa ba, momma ta fi shi kuɗi sosai, amma dai shi kuma ya fi uncle Abbas kuɗi, sai kuma kasancewar ƴaƴan Momma sun fi zama mafi soyuwa a wajen King, wannan ma yana ɗaya daga cikin dalilan da yasa take son Jaish ya auri Fanan, a ganinta idan Allah yasa Jaish ya auri Fanan zasu samu dama sosai a cikin masarautar, King zai zo Fanan kamar yadda yake son Jaish ɗin, ƙudurin da take da shi na son ganin ɗanta ne a kan kujeran King zai iya cika, amma fa a nata tunanin.

Sam ranta bai ji daɗi ba na rashin zuwansa, da alama akwai abin da ta shirya mashi ne wadda bata son ya tsallaka, sai kuma ga shi ya tsallaka, ranta ya sosu sosai, cikin fushi ta ƙuduri niyar sai ta yi maganinsa, zata gyara mashi zama, shi da yana can bai ma sani ba tana nan tana haukarta, har da wani ɗaukarwa kanta alkawarin ko yana so ko baya so sai ya auri Fanan, bata fa da tabbacin cewa ita Fanan ɗin tana son Jaish ɗin, ita dai tsarinta kawai take tsarawa kamar yadda take ƙoƙarin ruguje soyayyar Jawad ta gina na Rizwan, abin nata dai sai ita ta san me take nufi da bayin Allahn nan, duk so take taga kowa a cikin ƙunci ne ko yaya ne oho mata dai, lokaci ne zai nuna mana ainahin me take da buƙatar cinmawa a ranta.

A bangaren su Jawad kuwa, kamar yadda ya sakata kuka ta hanyar sanyawa a ɓata mata abinci, haka ya sake sakata dariya ta hanyar kaita yawo duk in da take so, sai dai duk in da suka je sai ya tsokaneta ta ɗan yi kuka hankalinsa yake kwanciya, ita dai auta ta tara abubuwan da zata gayawa Chuchun wanda Yah Jawad ya yi mata da gangan idan suka koma gida.

Ko da suka je gidan zoo ma sai da ya tsokaneta, sun je wajen wasu irin macizan mesa masu haɗiye mutane, macizan suna cikin wani irin glass mai kyau aka sanyasu, sai yawaro wasu daga cikinsu suke yi, wasu kuma sun haɗiyi saniya suna ƙawance bata gama narkewa a ciki cikinsu ba, so sun zo wajen suna kallo, sai ɗaukarsu a video suke yi, auta ta tsaya sai magana take yi wa macizan wai su nannaɗu kamar taya yadda take gani a film bari ta gani a zahiri, sai ka ce an ce mata macizan dama magana ake yi masu sai su nannaɗu ɗin, ita kuma Chuchu ta tsaresu da ido tana kallon ikon Allah, idanunsu kawai take kallo, sai dai ta takure jikinta waje guda, da alama tsoro take ji, kawai ta dake ne ta cije ta tsaya a wajen.

Cikin zolaya ya ce mata. "Jannat menen a wajen kafafunki kamar kamar snaka? Kamar fa ɗan snake ɗin dake cikin glass ɗin ne ya fito......."

Bai iya kai karshen maganar ba ya dakata saboda wani irin ihu da ta zunduma, a guje ta bar wajen tana ƙoƙarin cire alkyabbar jikinta kamar ance mata a jikin alkyabbar macijin yake, kunsan irin wannan abin sai ka ji kamar da gaske yana taɓa maka jiki, musamman ma idan tun farko kaga macijan da idon ka, to wlh ko baa tsoratar da kai ba sai ka rinƙa jin kamar suna taɓaka, to ita ma haka ta ji, sai ta ji kamar da gaske yaron macijin ne yake taɓa mata kafa, ai kuwa ta rinƙa tsalle tana kakkaɓe kayan jikinta tana ƙoƙarin cire kayan ma gabaɗaya, sai ihu take yi.

Cikin sauri ya

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login